Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gefe sannan ta zage ta fara gyara Kakar tata sai da ta fara wanke ta sannan tayi ma ta wanka ta naɗo ta a zane kamar ƙaramar Yarinya ta fito da ita nan da nan ta sauya ma ta kaya sannan cikin ƙanƙanin lokaci ta gyara ɗakin fes kamar ba shi ba ƙamshi ya cika ko'ina domin kuwa Aaqilah tana da tsabta sosai kuma ta tsana ƙazanta shi ya sa ko yanzu da zata taho kamar ta sani turaren ta ta taho. Bayan shafe tsawon lokaci tana gyaran ɗakin ne bayan ta kammala gaba ɗaya ta dawo madaidaicin Palon gidan mai matsakaicin kyau ta danna wata wayar tarho dake gefe ta danna kira ta layin da gaba ɗaya yake haɗe ne da layukan yaran Kakar nasu sannan ta sanar da announcement ga kowa na cewar gobe kowa ya da kowa ya hallara gidan Alhaji Sale wato gidan da Kakar tasu take zaune ta sanar da cewa akwai taro na gaggawa kuma ana buƙatar kowa ya hallara kwansu da kwarkwatan su....



___
*Samira Adila Dina (SAM POV.)*


*Around 8:37pm.*


"Assalamu Alaikum Barka da dare Ɗan uwa shin zan iya zama?."


Ta faɗa bayan tayi sallama lokacin da ta ƙari so wurin. Althaf dake zaune ya kalleta bayan ya amsa ma ta ta zauna daga gefansa saman ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun dake zagaye da wurin hutawan da yake daga wani sashe na masarautar wurin.


"Kamar dai tunanin wani abun ne ya ɗauke wa Ɗan uwa hankali har ya yi tsit haka nan?."


Ta faɗa tana jingine bayan ta jikin kujerar da take kai wacca take fuskantar wacca Althaf yake zaune.

"E, to wani abu dai kamar hakan sai dai tunanin Cutie na shi ne yaja hankalin har haka."


"Wow cutie is it your cat?."


Ya juya ya kalleta ta zuba masa ido tana danne dariya.


"No, ba mage ba ce mutum ce kuma mace sannan Budurwa ta da Soyayyarta yake neman yimin illa a zuciya duk da cewa bani da matsala da ita domin da daɗewa mun fahimci juna duk cewa ban bayyana ma ta ina son ta ba."


Gyara zama Samira tayi da kyau tana dubansa ta ce.


"Amma wace mace ce mai zarra hakan?."


"Arissa ce mana sanyin idaniyata."



"Arissa. Arissa.."


Ta maimaita Sunan tana ƙoƙarin tuna Inda ta sani tsawon sakanni talatin sannan ta kalle sa da sauri ta ce.


"Badai Arissa dana sani ba wata fara hasken ta mai haɗe da ja Cutie da ita mai yawan fara'a sannan tana da Yaya is Like Taufan Teema ta cemin sunan sa ko, wani Dogo haka kyakyawa na gaske mara hayaniya."


"Yes ita fa wacca suka zo Hospital wurin ki ita da Yayan nata, e Taufan sunansa Abokin Arkan ne kinsan shi ma ɗin ba mai yawan surutu ba ne wata ƙila shi ya sa suka kasance abokai."



"Okay na fahimta amma mene ne ka sani dangane da ita Arissa ɗin kuma Tsawon yaushe kuke tare sannan matsalar naka da waye bayan kace Yarinyar Kum fahimci juna da ita. Kodai saboda baka faɗa ma ta kanason ta ba ne shi ya saka ka tunani?."


Althaf ya yi Murmushi mai alamomi biyu, takaici, ban Tausayi.



"Tun Watanni Goma baya na haɗu da ita lokacin ko Hausa ba sosai ta iya ba."


Ya yi Murmushi tuna lokacin da ya fara haɗuwa da Arissa sannan ya ci gaba.


"Ban san komai akan ta ba sai dai ina so na sani amma ban san wa zan tambaya ba ita kuma taƙi faɗa min. Sannan damuwata sun kasu kashi biyu ne, na farko shi ne Umma (ma'ana mahaifiyar su) so take ta haɗani da Husna Ɗiyar ƙawarta ni kuma sam yarinyar bata burgeni ta cika rawar kai, sai na biyu shi ne, Arissa ta faɗa min nan da wasu ‘yan kwanaki zan nemeta na rasa domin zasu koma ƙasar su ta faɗa min ba'a Nigeria suke ba Kawai daga haka bata kuma cemin komai ba, wannan shi ne abin da ke damuna a yanzu."



Samira taja ajiyar zuciya tana kallon gefe guda sannan ta juyo da kallon ta gare sa ta ce.


"Yanzu abin da zaka farayi shi ne ka tuntuɓe ita Arissa ɗin ta faɗa maka ainihin Labarin ta idan zata iya sannan maganar auren ka da Husna da Umma take son haɗawa zan yi iya ƙoƙarina wurin ganin hakan bai faru ba tun da bakason Yarinyar ni kuma farin cikin Ɗan uwa na shi ne a gabana."


Ta ƙarishe tana murmushi shi ma Althaf dariya yake yi. Suka ci gaba da fira cike da Nishaɗi iskar damina tana kaɗasu, suna nan zaune sai ga Canal Nubaid nan ya ƙari so Aikuwa fira ta dawo sabuwa domin kuwa ba ƙaramin shaƙuwa ba ce tsakanin Samira da Uncle ɗin nata Nubaid da ya kasance Canal ne na sojoji Matarsa ɗaya Khairiyya ‘ya ɗaya garesu Baby watannin ta biyar kacal a Duniya.





Misalin ƙarfe Biyar na marece washe gari ke nan. Zuwa lokacin kowa da kowa na Dangi na nesa dana kusa sun hallara Gidan Alhaji Sale sai gidan ya zama kamar ana sha'ani domin ba laifi suna da yawa kam.


Ta ɓangaren Arissa da Althaf kuwa zaune suke a wurin da suka saba haɗuwa shi da ita fira suke yi kaɗan kaɗan Althaf ya jefo ma ta tambaya akan sanin ko ita wacece gaba ɗaya. Arissa tayi shiru da alama tunani take yi akan ta faɗa masa ko kuwa dai.

"Althaf tabbas na yarda da kai saboda kai ɗin mutumin kirki ne wannan dalilin ne yasa zan baka labarina da babu wanda na taɓa faɗa ma sai dai kai da zaka sani yanzu."


Ta faɗa tana kallon sa sannan tayi shiru tana nazarin ta inda zata fara yayin da ya zuba ma ta ido cikin wannan taƙin Arissa ta fara bawa Althaf gaba ɗaya labari akan Rayuwarta da irin gwagwarmayar da suka sha ita da Yayan ta mai ƙaunarta da son farin cikin ta wato Taufan. Tun da ta fara bata dakata ba har sai da takai aya zuwa lokacin Althaf ko kwakwkwaran motsi ya kasayi cike da al'ajabi, ruɗani, mamaki yake bin ta da kallo, yaba Tsantsar jarunta irin na Taufan yake yi lallai ya cika ɗa kuma ɗan uwa na gari domin a yadda Arissa ta basa labarin ya yi matuƙar yabawa ƙoƙarin da Taufan ya yi.



____
*Ko mene ne abin da Samira zatayi?.*
*Shin Mene ne labarin da Arissa ta bawa Althaf wani irin gwagwarmaya suka fuskanta a rayuwarsu?.*
*Wani mataki Aaqilah zata ɗauka da ta haɗa taron family na gaggawa, shin zata tonawa Inna Lami ita da Sahura Asiri ne??.*

*Ku kasance masu bibiyar wannan labarin domin yanzu aka fara har yanzu ba'a fara komai ba chakwakiyoyi ma suna gaba.*
___
# Khadeejarth Sabi'u Yahyah
# Nainarh KD
# 08081129487 Or 07085212808.
# Nkd's ce ✍️💖🌹👑
_____________________



*Ep_Twelve.*
👑🌹 TSANTSAR SO.
*Pure Love.💖*

*_©Nainarh KD....✍️_*


*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*


_Aaqilah Means = Beautiful radiant light_

______
💞Wukar fiddar giwa ba kaifi gare ta ba sai girma💞


______
_AAQILAH POV_



"Kamar yadda kuka sani ana shirya taron Ahali ne bayan an saka rana da lokaci. Sai dai wannan karon lokaci guda gaba ɗaya kuka sama kira domin taro na gaggawa gashi kuma gaba ɗaya kun hallara har da waɗan da ba'ayi tsammanin ganin su ba ko nace ba'a ganinsu a wurin sai yau cikin nufar Ubangiji sun hallara."


Ta ɗan daka tana kallon gaba ɗaya mutanen dake zazzaune wasu saman kujeru daga cikin babban baranda da aka sassaka kujeru sannan aka shimfiɗa tabarmu da wasu suke zaune. Ita tana dage tsaye ne hannunta riƙe da loudspeaker ya yin da hankulan gaba ɗaya mutanen yake a kanta.


"Ba da ɓata lokaci ba zan yi bayanin dalilin haɗa wannan taron Ahalin na gaggawa badan komai ba ne sai dan na nusar da ku wani kuskure da kuka aikata ko nace kuke aikatawa jiya na shigo wannan gida domin nayi kwanaki duk da hakan ba daɓi'ata ba ne bin gidajen 'yan uwa. Sai dai da isowa ta na tarar da abin da ya yi mugun bani mamaki kuma ya sosa rai na sosai."

Ta basu labarin irin halin da ta tarar da Kakar ta ta ciki da take Matsayin mahaifiya wurin gaba ɗaya manyan mutanen wurin sannan ta ɗaura da faɗin.

"Ku sani cewa Mahaifiya fa ta wuce duk inda ake tunani, Mahaifiya ba abin yarwa ba ce, amma ku duba ku Yaranta mata huɗu ne waɗan da kuke gidajen auren ku amma kun wofin tar da ita gefe ku sani ba ko wani abu ba ne za'ace Umma uwani da Umma Rayya zasu ke ma ta (tana nufin matan Alhaji Sale da Kakar tasu take gidan sa).
Wai shin kun manta cewa kuma kun haifa yaran ne Bakwa fata yaran ku suyi muku biyayya ko idan kun mutu su dinga bibiyarku da addu'a duka kun manta da waɗan nan abubuwan ne kuka wofin tar da wannan Dattijuwar Baiwar Allah haka sai kace ba sanadin ta kuka zo Duniyar ba. Kuyi haƙuri nasan dole maganganuna zasu ɓatawa wasun ku duba da cewa Matsayin iyaye kuke wurina amma ƙoƙarin nusar da ku kuskuren ku kawai nake yi. Domin ita Mahaifiya aljanna ce ta duniya, dukkanin wani gata da yalwar da zaka samu a duniya matuƙar baka da mahaifiya a raye, to haƙiƙa ba zaka ji daɗin wannan wadatar ba kamar ace Mahaifiyar ka tana raye, kullum kada ka dinga mantawa da ita cikin Addu'o'in ka na yau da kullum domin haƙiƙa ba zaka sami me maye maka gurbin ta ba, domin ita ce ta salwantar da dukkanin wani jin daɗinta don kawai kai kaji daɗin rayuwarka. Na roƙe ƙu da ku taimaka ku dawo da hankulanku akan mahaifiyar ku ita da take raye domin tana matuƙar buƙatar kulawar ku, kuyi ma ta biyayya ku kyautata ma ta ga dukkan abin da bai fi ƙarfin ku ba, ku sani wasu neman mahaifiyar suke yi amma bata nan garesu wasu rasuwa tayi wasu kuma ƙaddara ce ta rabasu."





Tun da Aaqilah ta fara maganar babu wanda ya iya furta komai cikin mutanen wurin mazan su da matan su ta burge wasu yayin da ta ɓatawa wasu a ganinsu ita har Wacece zata tarasu tana musu wani wa'azi ta fara gyara kanta da ɗabi'unta mana.
Murmushi kawai Hajiya Umma take yi cike da alfahari take kallon Aaqilah sam bata san Yarinyar ba domin ba son shiga Dangi take yi ba, tun da kuwa ta yi aure ita kanta zata iya ƙirga adadin biki ko suna na Dangin da ta taɓa zuwa kusan shekaru talatin da Aurenta. Ta dubi Umma Rayya dake gefanta ƙasa ƙasa ta ce.


"Wai kuwa Rayya wannan wace yarinya ce haka na lura tana da hankali da kuma nutsuwa."


Rayya da bita da kallon mamaki ganin yau Hajiya Umma ita ke yaba wata watan ma kuma Aaqilah, ta tabbatar Hajiya Umma batasan wacece Aaqilah ba shi ya sa take tambaya koda yake ma taya ya zata sani bayan ba shiga mutane take ba.


"Aaqilah ce ɗiyar maragayi Malam Umaru mai rasuwa."


Hajiya Umma ta zaro ido cike da mamaki jin abin da Rayya ta faɗa wai dama wannan ita ce Aaqilah da take jin labarin ta bakin Mutanen gari da Dangi ikon Allah amma ta shiryu ne daga irin halayenta marasa ɗa'a da take samun labari akai ko ya ya?. Wannan ce Kawai tambayar da Hajiya Umma take yiwa kanta babu mai bata amsa.



Sosai Aaqilah ta yi ma iyayen nata wankin Babban bargo (bawai cin mutunci ba, a'a cikin hikima da tausasan kalami take nusar da su kusakuren su na wofin tar da Mahaifiyarsu da suka yi abin da ya zama Ruwan dare a wannan al'umma tamu sai dai fatan Ubangiji ya sa mudace kawai) Ita kanta Aaqilah har mamakin kanta take yi yadda ta saki jiki ana wa'azi kamar wata ta Allah. 😂
(Abin da Aaqilah da Inna Lami basu sani ba shi ne babu abin da zai karya wannan Asiri sai Ranar da ɗaya daga cikin su wato Inna Lami ko Inna Sahura ta faɗa wa ita Aaqilah ɗin gaskiya sannan Asirin zai fara karyewa a hankali a hankali ba kuma lokaci ɗaya ba, so wata ƙila Asirin ya fara karyewa ne)🙀


Ta daɗe ta yi kafin daga bisani kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa daga ƙarshe taron ya watse.


Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga Ɗakin. Zama tayi bayan ya amsa ma ta dama tun tuni sun gaisa hakan ya sa ba tare da ɓata lokaci ba ta fara faɗin.


"Dama Yaya Sale wata magana ce nake tafe da ita da ta shafi Aaqilah."

Ta faɗa cike da ladabi ga Yayan nasu Namiji ɗaya tilo da ya yi saura dama su Biyu ne maza to Malam Umaru ya rasu saura shi ɗaya sai kuma ƙanninsa mata huɗu har da ita Hajiya Umma ɗin duk da ba Mahaifiyar su Alhaji Sale ce ba ta haifeta tun tana Yarinya ta rasa Iyayenta Mahaifin ta ƙanin Mahaifiyar su Alhaji Sale ɗin ce hakan ya sa ta karɓe ta ta ci gaba da kula da ita ta taso cikin yaran ta kuma ta haɗe da su tamkar ciki ɗaya suka fito bayan ta yi Aure ne ma da yake Ɗan Adam haka yake mai manta Alkhairi da bin ruɗin Duniya da sheɗan tun bayan tayi Aure ta rage shiga Dangin ta sosai ta rage kula kowa ko sha'ani a ke yi bata damu da ta je ba domin a ganinta tafi kowa tun da mai Dukiya take Aure kuma ɗan Sarki Muhammad Raees guda wato Alhaji Nawaz Yaransu huɗu Babban shi ne Arkan Soja ne sai Althaf bai daɗe da kammala karatun sa ba sannan sai mata Biyu ɗaya tana aure a can Jigawa State ɗayan kuma karatu take.


Alhaji Sale ya nusa tare da gyara zama yana mayar da gaba ɗaya hankalinsa a kan ta ya ce.


"To Aaqilah kuma Allah ya sa dai ba maganganun ta na ɗazu ba ne suka ɓata miki sai dai a ganina Yarinyar tana kan gaskiya duk da cewa ga kalarta ana ma ta wani kallo daban saboda ɗabi'unta amma Yarinyar kirki ce ni na tabbatar da hakan ji nake da'ace zata amince tabbas babu abin da zai hana na haɗa Aurenta da Yaron wurina Bello."😳

Ya kai zancen yana sakin Murmushi domin koba komai ai ɗiyar ɗan uwan sa ce ita duk da cewa ya san wane ne yaron nasa Bello sai dai kallon da ake masa sam ba haka yake ba.


Cikin sauri Hajiya Umma ta ce.


"A'a Wallahi Yaya ai Bama sai an yi hakan ba domin kuwa da kallon ta nayiwa Arkan na wurina riƙo yanzu haka ma akan maganar ne na taho wurin ka domin banaso a ɗauki lokaci so nake ka bani dama tun da kaima uba ne a wurin ta ina so na haɗa Aurenta da Arkan Indai ka amince haka ita ma ta amince."


Alhaji Sale ya yi Shiru da alama zancen nata yake tunani akai. Sannan ya yi 'yar Dariya kaɗan.

"Hajiya Umma ke nan ta yara duk da bakyason mu Sosai amma kinason yaran mu, to shikenan ni dai ta ɓangarena babu wata damuwa domin Arkan da Bello duka ɗaya suke a wurina, yanzu abin da za'ayi gaba shi ne tuntuɓar yaran sannan a haɗa su ma'ana su gana idan sun amince da junansu shikenan babu damuwa Allah Ubangiji ya sanya Alkhairi, sai dai kafin nan yana da kyau kiyi shawara da mijin ki sai ita Khadijatu mahaifiyar Aaqilah ɗin yana da kyau ita ma ta sani."


"E, wannan gaskiya ne Yaya Tohm shikenan in sha Allah gobe zan je gidan ita mahaifiyar Aaqilah ɗin domin mu tattauna akan lamarin kuma in sha Allah yau zamuyi maganar da Alhaji."


"Ma sha Allah Allah ya kaimu."


"Ameen."

Ta amsa, nan suka ci gaba da fira akan lamarin ta daɗe kafin ta fito ta fara shirin komawa gidan ta.



______
_SAMIRA ADILA (SAM POV)_


Tana shirin fita daga Palon ta hango Althaf shi da Arissa suna ƙoƙarin Shigowa hakan ne yasa ta koma ta zauna.


"Tun da mun shigo ba zaki saki jiki ba ko so kike ta ji babu daɗi ne dana san haka zaki koma ai da ban tambaye ki komai akan labarin ki ba."


Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba.


"Sorry Yah Althaf kawai tuna rayuwata ce ya sakani kuka kuma nasan zan yi kewar ka."

"Ba nace Wannan Yah ɗin ya fita daga bakin ki ba ni ba Yayan ki ba ne Althaf sunana."


Ta yi Murmushi dama da gangar ta faɗa tana sane bayason tana Kiransa da Yah Althaf ɗin.


"Lah Anty Samira wai dama kece wato shi ne Yah Althaf ka ƙi faɗa min wurin Sister na zamu so ko?."

Ta faɗa lokacin da suka ƙari sa wurin suka zazzauna. Jefa ma ta wata uwar Harara ya yi bai ce Komai.


"To Ɗan lelen Hajiya Fulani wannan hararar fa sai kace zaka faso idanun waje?."

Samira ta faɗa tana ɗan darawa.


"Ki barni da ita Kawai sister ko yaushe ma ta sanki da take kiran ki da Sistern ta oho."


"HHh ai ina ga nafi ka alaƙa da ita ma."


"Kai ke a wa ke nan, Idan baki sani ba bari ki sani Samira ƙanwa ta ce ta jiki."


"Oho dai ni kuma ai surukata zata zama."


Arissa ta faɗa ƙasa ƙasa.


"Mai kika ce?."


"A'a ban ce komai ba."


Ta faɗa tana dariya tare da mayar da Kallon ta kan Samira dake bin su da kallo tana murmushi Arissa ta ce.


"Ina wuni Anty Samira ya ƙarfin jikin har kun dawo ke nan?."


"Lafiya Alhamdulillah daga ina ke nan?."

"Daga wurin da kikace Yayana zai dinga rakaki Kullum mana kuna zagaye gari har kiji sauƙi ai jiya ina jin komai lokacin da kike faɗa masa."


Samira ta zaro ido tana murmushi ita fa sam ta manta ma wallahi.


"Lallai kam Arissa ai wasa nake masa fa, haba sai kace wata mara hankali taimakon da ya yi min ma ai ya wadatar kawai jiyan na faɗa ne da wasa."


"Allah Sarki."


Arissa ta faɗa sam bataji daɗi ba taso ace da gaske Samira take yi, tun da har Yayanta ya yarda wata ƙila ai daga nan abin da take mafarki tsakanin Yayan nata da Samira ɗin ya tabbata gaskiya, sai dai ya ta iya dole ta kyale zancen tun da Samira ta ce wasa take yi.


Fira suka ci gaba yi su ukun Althaf da Arissa sai kuma Samira da jifa take sako musu baki a zancen nasu. Domin hankalinta ya fi karkata akan Wayarta dake hannunta tana sarrafa ta.


Suna nan zaune can sai ga Khairiyya ita da wata kyakkyawar Mata gefanta sun shigo suna taɓa fira.


"Barrister Aeshah ko?."


Arissa ta tambaya Althaf da yake zaune kujarar da take kusa da nata, ƙasa ƙasa tayi masa tambayar.

"E, ita ce a'ina kika santa?."


Ya tambaye ta lokacin da su Barrister Aeshah ɗin suke gaisawa da Samira har suke tambayar jikin nata dama ita suka zo dubawa da yake Barrister Aeshah da Khairiyya ƙawaye ne sosai domin sanadin ƙawancen nasu ne har Khairiyya take zuwa wurin Aeshah ɗin har Allah ya haɗa ta da Canal Nubaid suka fara Soyayya kafin daga bisani suka yi Aure.


"Kawai a TV nake ganinta idan muna kallon labarai gaskiya kyakyawa ce sosai kuma tana da kyan zuciya domin ita ɗin Barrister ce mai gaskiya a kan aikin ta Mutuniyar kirki."


Althaf ya murmusa cike da alfahari shi ma kansa kyawawan halayen Barrister Aeshah suna matuƙar burgesa babu ruwanta bata da girman kai ga kirki kowa nata ne. Yana shirin magana yaji Muryar Khairiyya tana faɗin.


"Althaf Ɗan lelen Hajiya Fulani dama kai ne anan ke nan wannnan cutie ɗin kuma Wacece kodai ita ce Cutie Arissa ɗin taka da kake bani labari?."


Ta faɗa lokacin da suka zauna gefan Samira da take kan 3 sieter gaba ɗaya suka zuba masa ido, Arissa kuwa tayi ƙasa da kanta cike da kunya ta ce.


"Ina wuni fatan na sameku lafiya?."


"Lafiya Qlau Alhamdulillah kece Arissa ɗin dai da gaske ke nan finally dai yau mun haɗu."


Suka amsa ma ta da murmushi Barrister Aeshah ɗin ce ta ci gaba da faɗin hakan.


Arissa dai Murmushi take yi ba ta ce komai ba.


Sosa ƙeya Althaf ya yi ya ce.


"Ita ce Arissa da nake gaya muku ɗin fa fatan dai matar tawa to be tayi muku?."


Gaba ɗaya Murmushi suka yi cike da farin ciki.


"Wow ma sha Allah Aikuwa gata cutie da ita kamar ɗiyar larabawa tabarakallah gaskiya tayi ɗari bisa ɗari."


"Yauwa Anty Barrister na gode sosai. Sis saura ke shin Arissa ta tayi Miki ko kuwa?..."


Ya faɗa ba tare da ya kalla Arissa da ta saki baki tana bin sa da kallon mamaki ba sai ma mayar da hankalinsa kan Khairiyya da ya yi.


"Kai kai Ai Arissa ɗin nan ita ce ƙarshe Indai wurin haɗuwa ne fa kyau komai ya yi daidai kuma ga dukkan alamu zatayi biyayya."


Gaba ɗaya suka saka dariya jin abin da Khairiyya ta ce. Harda Arissa sai da ta murmusa.


"Yauwa Sister kema godiya nake, Mira saura ke."

Ya yi maganar yana mayar da kallon sa akan Samira.


"Ikon Allah wai ita Anty Samira har sunaye nawa gare ta ne?."


Arissa ta faɗa a ranta, a fili kuwa ta mayar da kallon ta kan Samira ɗin domin jin mene ne abin da zata ce.


"Gaskiya kun dace sosai na tayaka murna da ka sama wannan Kyakykywar matsayin matar ka to be ina muku fatan Alkhairi."


Arissa ta kuma zaro ido cike da kaɗuwa da jin abin da Samira ita ma ta faɗa, ita fa ta fara shiga confusing fa wai Mene ne abin da Althaf yake nufi ne?. Ta tambaya kanta, sai dai kafin ta gama lalubo amsar da zata ba kanta ta tsinkayi muryar sa da sauri ta dubesa sai taga baya saman sofa da yake kai, tayi saurin kallon wurin da ta jiyo Muryarsa. Ta kuma zaro ido tana Miƙewa tsaye da sauri ganin Althaf tsugunne saman gwawowin sa ya yi kneel down kamar mai neman gafara, ko kafin ta gama tantance abin da take gani taji Muryarsa yana faɗin.


"Arissa kiyi haƙuri dana kasa sanar dake Sirrin dake Zuciyata sai yanzu a wannan lokacin, Arissa ina matuƙar ƙaunar ki na bayyana miki hakan ne a gaban mutanen da nafi shaƙuwa da su bawai don yaudara a gare ki ba kuma bazan tilasta sai kin soni ba, Please Arissa i you winning to marry me?..."!


Hannu takai cike da mamaki tana toshe baki domin batayi tunanin hakan ba sam. Kasa ce da shi komai tayi sai idanu da ta zuba masa suna kallon tsakiyar idanun juna, yayin da mutanen palon suke bin su da kallo suna jiran amsar Arissa har Hamrarh da ta turo Amrarh a keke suka shigo Wurin babu wanda ya lura da su.


"Althaf kai ne mutum na farko da yake kula dani da damuwa ta bayan Yayana kai ne ka ke tare da ni ko wani irin hali nake farin ciki ko damuwa koda yaushe burin ka shi ne ka ganni cikin farin ciki ina walwala kamar kowa baka taɓa kyamata ta ba, ni kuwa Althaf mene ne abin da zan yi bayan damƙa ma ka zuciyata tabbas kai kaɗai ne Namijin da ka dace da Rayuwata kuma nake fata ka zama Miji na gari gareni sannan uba na gari ga Yaran da zamu haifa. Sai dai abu ɗaya Althaf kamar yadda ka sani rayuwata akwai banbanci da kalar taka Rayuwar ka san Wacece ni a halin yanzu ka kuma san Tarihi na. Tabbas kai ɗin na musamman ne ina ƙaunar ka nima."


Ta faɗa yayin da takai left hand nata tana sha re wasu siraran hawaye da suka zubo ma ta. Yayin da Right ɗin tuni ta miƙa masa aikuwa ya zura ma ta wani Ring na Diamond mai matuƙar tsada da kyau na gasken gaske a hannun.



Gaba ɗaya Palon tafi ya ɗauka tafi raf raf cike da burgewa abin kamar irin a series film ɗin nan ya kasance.


"Wow very Amazing Althaf da Budurwa no wonder kake kakkaucewa Haneefa ashe Akwai sarauniyar zuciyarka."


Hamrarh ta faɗa lokacin da suka ƙari sa wurin da yake Haneefa ɗin ƙawarta ce ta nuna tanason Althaf shi kuma yaƙi bata fuska harta haƙura.

"Kyakykywa kuwa Sannu da ƙoƙarin sace mana zuciyar Ɗan uwa koda yaushe bashi da aiki sai Labarin ki, finally dai yau gamu mun haɗu."


Ƙasa Arissa tayi da kanta cike da kunya ba tare da ta ce komai ba tana murmushi domin kuwa Ranar yau jin ta take yi ta musamman a Rayuwarta Ranar da Althaf ya bayyana ma ta soyayyar sa gare ta.



"Kardai a takuwa surukata ehe kinji dawo nan kusa dani ma domin Hamrarh ta cika takura."


Khairiyya ta faɗa tana Dariya suma gaba ɗaya Dariyar suka saka barin ma Althaf washe baki

Please Login or Register in order to submit comment