Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ta wuce Arissa da Yayanta suka zo nan ƙasar wurin Kakannin nasu nan ne suke basu labarin sun zo ne su zauna da su tsawon shekara ɗaya daga nan zasuyi musu bayanin dalilin dawowarsu garesu ba tare da Mahaifiyarsu ba. Wannan shi ne abin da zan iya ce Miki na sani Dangane da Arissa da Yayanta nima dai a wurin Mamana nakejin wasu abubuwan."


Samira tayi Shiru cike da mamaki tana nazarin wannan labarin da Teema ta bata.




Daidai lokacin kuma suka ƙari sa bakin entrance na Apartment ɗin shiga ciki suka yi da sallama Aikuwa Samira tayi kyakykywan gani.


____
https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20

*KUYI FOLLOWING WHAT'SAPP CHANNEL NAWA DOMIN SAMUN TSANTSAR SO TUN DAGA PAGE 1 ZUWA INDA AKA TSAYA, MASU NEMAN LITTAFIN ANEESERH MA ZAKU IYA FOLLOWING DOMIN SAMUN DAGA FARKO SHIMA ZUWA INDA AKA TSAYA.*



____

# Khadeejarth Sabi'u Yahyah



*Ep_Nine $ Ten.*
*💫 TSANTSAR SO.💫*
*The Pure Love.*


*Daga Alƙalamin Nainarh KD Nkd's.🤞*


*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*


_This page is honestly dedicated to Anty Aysha JB Amincin Allah ya kai miki Ubangiji ya ƙara kaifin basira da zaƙin hannu.🙏💖_


______
_Samira Adila Dina - Means= Extraordinary woman of just faith_



_____
"Anty Khairiyya kece a garin saukar yaushe?."


Samira ta faɗa cike da mamakin ganin Khairiyya Matar Canal Nubaid da tayi, ke nan dai zuwa suka yi babu sanarda wa.


Kyakyawar Matar da ba zata haure shekaru Ashirin da Takwas ba ta juyo fuskarta ɗauke da murmushi tana kallon Samira da ta ƙari so wurin ba tare da jiran Komai ba tayi hugging na ta cike da farin cikin ganin ta.


"Dina ke nan dubeki kamar wata Yarinya ƙarama zaki ɓallani fa."


Samira ta zauna saman Sofa tana faɗin.


"Ba dole ba duka a cikin farin cikin ganin ki ne ai, ina fata dai kun iso lafiya, ina Babyna take?."


Sai da Khairiyya ta zauna sannan cike da al'ajabi idanunta akan Samira ba tare da amsa maganar da tayi ma ta ba ta ce.


"Ikon Allah ke kuma mene ne ya sameki haka na ganki da crutches Hatsari kika yi ne?."


Samira ta dubi crutches ɗin da ta a je gefe bayan ta zauna sannan ta dube Teema dake tsaye gefe ta ce.


"Teema jeki gida kawai sai gobe ki gaida Mama."


"Tohm Anty Samira Allah ya tashe mu lafiya."


Teema ta amsa tare da fita daga Palon.


"Ba wai Hatsari nayi ba kawai dai tsautsayi ne da baya wuce Ranar sa amma Doctor ya ce ba daɗe wa zan yi a hakan ba."


Samira ta faɗa bayan ta amsawa Teema.


"Ayya, Allah ya kare gaba. Amma dai Madam Sarah bata sani ba ne ko, i wonder ma ya aka yi ta bari kikazo Nigeria."


Karo na biyu Samira ta murmushi har haƙoran ta farare ƙanana da su suka bayyana tuna Wacece Mahaifiyarta da kuma irin kyakyawar tsana da tayi ma Nigeria ba a dalilin komai bayyana ne ba.


"Hummm Anty Khairiyya ke nan a tunanin ki Mom zata bari nazo Nigeria ke nan bayan na faɗa ma ta nan zan zo, ai daga ita har Dad ce musu nayi Dubai zan tafi bikin wata School mate nawa shi ya sa suka bar ni, Direct ni kuma nayo nan."


Samira ta faɗa hakan tana Dariyar sheƙiyanci.


"Ya Allahu mai yadda ya so, Sannu fa Dina da ƙoƙari yanzu bakya tsoron su sani?."


"E, to ban yi tunani akan wannan ba tukunna sai dai abin da na sani shi ne bani da kalmar kare kaina wurin su especially ma Momna a duk lokacin da suka gane ina a Nigeria duk da banajin cewa nayi wani rashin kyautawa domin kuwa wurin Dangin Mahaifina nazo ban san mene ne dalilin da ya sa ita Mom bata son su ba kuma Dad yake biye ma ta kuma nima basaso nake shiga cikin Dangin Mahaifina sosai."


Samira takai zancen tana sauke ajiyar zuciya kai daga jin yadda tayi maganar kasan ba ƙaramin taɓa ma ta zuciya tayi ba. Yayin da Khairiyya ta zuba tagumi hannu bibbiyu tana sauraren ta, tabbas ta fahimci Samira kuma sosai ta bata tausayi. Ta buɗe baki domin magana. Hamrarh ta shigo palon hannunta riƙe da Baby Ɗiyar Khairiyya tana faɗin.


"Wannan 'ya batasan abin arziƙi ba sam, daga reno sai uban ihu take ma mutane duk ta hana mu sukuni ni ban ma san lokacin da ta fara ƙiuya har haka ba."



Ta ƙarishe maganar daidai lokacin da ta shigo ta ƙari sa ta miƙawa Khairiyya 'yar sannan ta zauna saman 1 sieter gefan Samira da take zaune saman 2 sieter.


Samira ta mike tana faɗin.


"Anty Khairiyya bari na shiga daga ciki zan watsa ruwa. Sister Hamrarh Barka da Rana."



"Barka dai Adila ta ya kike ya yau ɗin ya kuma ƙarfin jikin?."


"Alhamdulillah Sister na."


Samira ta amsa tana murmushi na jin daɗin irin caring da Hamrarh take bata shi ya sa take son ta kuma suka fi shaƙuwa sosai sai dai shaƙuwar da suka yi da Hamrarh bai kai kwatankwacin yadda suka shaƙu da Amrarh ba domin kuwa ita Amrarh a can Turkiya ta taso hannun Mahaifin Adila saboda yanayin halittar ta ana nema ma ta magani domin kwararrun Likitoci na Duniya sun tabbatar da cewa zata iya samun waraka daga rashin tafiya da ƙafafuwan ta da take fama dasu, shi ya sa tun tana Yarinya ta taso wurin Chief Sulaiman Mutallab Raees Mahaifin Samira, daga baya ne ta dawo Nigeria wurin Mahaifiyar su Miss Asfiya Matar Judge Junayd Muhammad Raees da suke da yara uku kacal tare kuma Triples ne maza biyu mace ɗaya, Hamrarh da Amrarh ba judge Junayd ne ya haifesu ba mahaifin su daban kuma ya rasu da daɗewa. Akwai wani sarƙaƙiya mai ban mamaki cikin labarin Miss Asfiya da yadda aka yi ta haifa Yaranta na farko twin's mata Hamrarh da Amrarh.



Direct haɗaɗɗen bedroom ɗin ta Samira ta wuce yayin da a palo Khairiyya suka ci gaba da fira ita da Hamrarh suna jiran Samira ta shirya ta fito su wuce shashen matar sarki ta farko Hajiya Bilkisu da suke kira da Ammie domin kowa da kowa duk suna can ana ta fira ita ma Khairiyya wurin Samira tazo cikin Apartment ɗin kuma ta tarar ba ta nan, shi ne tana ƙoƙarin fitowa daga Palon suka haɗu da Samira ɗin.




_SAMIRA SAM KUWA_


Akalla takai kusan mintuna bakwai cikin Bathroom tana wanka sannan ta fito ɗaure da towel white color ga ƙarami a hannunta tana goge doguwar sumar kanta mai two color kuma a haka aka haife ta sai faman sheƙi take zubawa.
Samira Adila Dina dai wata kyakyawar matashiyar budurwa ce da a ƙiyasi shekarunta ba zasu haura goma sha tara ba. Doguwa ce dirarra mai kyan diri da a turance ake kira da Hourglass Shape irin wanda mata masu zarra ne kawai suke da shi domin kuwa yafi coca cola shape kyau da kyau da kuma burgewa ga kyawawan mata da suka amsa sunan su kyawawa.
Fara ce mai masifar kyau na ƙin ƙarawa idanunta masu Shape na Almond kuwa dara dara ne gasu farare kyawawan gaske tabarakallah gata da wani cute mouth ɗan daidai kuma ɗan ƙarami domin kuwa da wuya idan mutum ya yi ƙoƙarin zura yatsun sa uku su shige ciki, hancinta dogo da shi ma sha Allah ga tsini sai dai bashi da irin tsinin nan da ya wuce kima daidai yake kuma yana daidai ne da yanayin Diamond Beauty face nata da a koda yaushe take ɗauke da murmushi saman ta. Samira irin mutanen nan ne da ake kira masu farin jini domin kuwa koda baka son ta kana haɗuwa da ita zakaji kana masifar son zama da ita koda kuwa so ɗin ba na Soyayya ba. A halayya Samira ta kasance bata da girman kai ko kaɗan sannan bata zama kusa da masu shi, tana da kirki daidai ita amma fa tana da saurin fushi, shagwaɓaɓɓiya ce ta ƙin ƙarawa, tana son mutane sosai kuma tana da ilimin boko dana addini wadatacce domin kuwa sosai iyayenta suka yi ƙoƙari wurin ganin sun ɗaura Rayuwarta bisa turba ta daidai basu ruɗata da kyalekyalen Duniya ba kuma arziƙi da jin daɗi da ta taso ta tarrar iyayenta da su bai saka tana banbance kanta da kowa ba wai taji tafi kowa sam wannan baya daga cikin halayyar Samira Sulaiman Mutallab Raees. Mom nata tana kiranta da Adila a wasu lokutan kuma Mira yayin da Daddynta yake kiranta da Dina sauran mutane kuma suka haɗe sunayen gaba ɗaya ya bada Samira Adila Dina wasu da haka suke kiran ta wasu kuma da Samira wasu da Adila wasu kuma da Dina har masu kiranta da Mira da Sam ma duka akwai domin kuwa Jarumar tamu tana da jama'a.

_BRIEF EXPLANATION KE NA AKAN SAMIRA. KU KASANCE CIKIN WAƊAN DA ZA'AYI TAFIYA NA WANNAN LABARI DA YAZO DA SALO NA MUSAMMAN DOMIN SANIN IRIN DARUSSAN DAKE CIKI_
______________________________________✍️The Nainarh KD Nkd's Ce👑
_____________________


Cikin ƙan ƙanin lokaci ta shirya cikin Capricorn shirt pink da wando High waisted flare Jeans Black sai hula turban da ta saka sannan ta saka flat shoes make-up dama already saffa saffa tayi, tayi kyau sosai kamar a wanke hannu a taɓa sannan a zura cikin jaka kana a ruga 360.🤪


Direct palo ta fito tana baza ƙamshi sai dai babu Hamrarh da Khairiyya da ta bari hakan yasa ta gyara sandar crutches ɗin ta kana ta fito daga Apartment ɗin gaba ɗaya ta wuce sashen uwar gidan mai Martaba Fulani Bilkisu....



_HAZEL POV_


Cikin waɗan nan kwanaki biyar na Rayuwar da suka gabata ta wuce su tare da wani irin shaƙuwa da ya fara shiga tsakanin ta da Labib sakamakon yawan nacinsa a gare ta yasa tun bata kulasa har ta fara sauraren sa da kuma yawan kyautata ma ta da yake ƙoƙarin yi koda yaushe ba tare da gajiyawa ba ko kyashi duk da sanin cewa ba addininsu ɗaya ba da ya yi, dama ita zuciya haka take tanason mai kyautata ma ta a koda yaushe hakan ya sa Hazel ta saka Labib cikin zuciya a ɓangare na mutane masu matuƙar muhimmanci a wurin ta ban da mahaifinta Father da Kakarta Granny Za'a iya cewa Labib shi ne mutum na uku da yake da muhimmanci wurin Hazel duk da cewa mahaifiyar tana ta raye amma bata ɗauke hakan da wani muhimmanci ba sam, domin ta taso ko fuskar mahaifiyar ta bata taɓa gani ba sai a hoto gani a hoton ma sau ɗaya kacal ta taɓa yi sam bata damu sanin wani hali mahaifiyar ta take a halin yanzu ba hasalima tayi matuƙar tsanar mahaifiyarta a Rayuwarta....


____

Granny cikin ɓacin rai ta kalla Hazel dake zaune gefanta tana kallon Wayarta ƙirar Infinix Smart 6 da Father Mahaifinta ya bata tun bayan kammala Secondary school da tayi sannan ta ce.


"Yake Hazel wai Mene ne kike nufi da kika kawo mana wannan baƙin mutumin da ya fita yanzu cikin Gidan nan me kike nufi wai da gaske ne abin da nake ji cikin gari yana yawo wai kina Soyayya da wannan Ɗan musulman?."


Hazel ta ɗa go ivy eyes na ta a daƙile take bin Granny ɗin nata da kallo karo na farko a Rayuwarta da tayi ma wanda ya girme ma ta irin wannan kallon.


"E, tabbas gaskiya ne maganar da kike ji a gari na muna Soyayya Ni da Labib kuma ina tabbatar Miki da aure zamuyi kwanan nan kiji da kunnen ki kuma shi ba baƙi ba ne domin kuwa kyakyawa ne duk da ba fari ba ne amma a hakan nakeson abina domin yana da kyakyawar zuciya kuma da kike maganar Ɗan Musulmai ai naga matan mu zasu iya auren mazan su, sai dai matan su ne Bazai yiwu su aure mazan mu ba."


Hazel ta faɗa a fusace tare da Miƙewa zata bar wurin ita kanta mamakin irin baƙaƙen kalamin da ta watsawa Granny ɗin nata take yi duk da kuwa da cewa ita taja.


Fashewa Granny tayi da kuka daidai lokacin da Father ya shigo gidan. Cikin fa ce hanci kuma da ƙarfi yadda Hazel zataji ta ce.


"Lallai Hazel kin bani mamaki kuma ki sani ina mai tabbatar miki ba zaki taɓa Auren wannan Ɗan musulman ba idan ma hakan ta kasance sai dai idan bana raye ne cikin wannan Duniyar."


Da ƙarfi kuma cikin fusata Hazel ta banko ƙofar ɗakin ta bayan ta shiga, ji kake garam gam gagam...! Har sai da ƙarar ya tsorata Granny dama kuma hakan Hazel takeso. Sai dai duk da hakan bai saka Granny ta dakata ba sai ma juyawa da tayi ta duba Father ta ce.


"Astrid kana dai ganin abin da wannan ja'irar Ɗiyar taka tayimin. Ina tsoron Tarihi ya maimaita kan sa Wallahi."


Ta faɗa a fusace tana watsa masa harara.

Nan da nan Father ya fara haɗa uban gumi duk da iskan dake kaɗawa jin kalamin mahaifiyar tasa. Hakuri ya fara bata domin ban da hakan bai san mene ne ya kamata ya yi ba, sai dai Granny taƙi sauraren sa sai ma ci gaba da sababi da tayi. Yayin da shi kuma ya yi Shiru cikin rashin abin yi domin kuwa bai san lokacin da ya yi sake har Hazel ta sake da mutane haka ba har suka fara Soyayya da wani kuma Ɗan musulmai sai dai bai ɗaura laifin hakan akan kowa ba sai a kansa gefe kuma yana tabbatar da maganar Mahaifiyar tasa Granny da ta ce tarihi zai maimaita kansa. Aikuwa Indai hakan ta kasance yana cikin wani hali mara misaltawa domin kuwa ƙiri ƙiri yake Ganin cewa reshe ne zai juye da mujiya. Babu abin da yake rayawa a Ransa fa ce na yadda zai yi ma tufkar hanci cikin sauri sauri...


___
*LABIB LAHAM POV.*
Labib ainihin Sunansa Labib Laham Asalin 'Yan Kaduna State ne iyayensa gaba da baya. Su uku ne wurin iyayen su Labeer shi ne Babba Engineer ne sai kuma Lipika mai bi masa ita kuma sannan sai Labib Auta.
Shekaru biyu da suka wuce yazo Jos yana zaune ne wurin wata Iyami Dangin Mahaifiyarsa ce Dangi na nesa sosai ma tunda yazo bai koma gida ba sai jifa jifa yake zuwa Kaduna State ya yi musu kwanaki ya dawo Jos domin anan ne yake Aiki kuma sanin hakan ne yasa iyayen sa basu taɓa masa magana akan hakan ba duk da hakan yana damun su sai dai basu da yadda zasu yi saboda irin aikin da Yaron nasu ya zaɓawa kansa na sirri fatan Nasara kawai suke bin sa da shi.




______
*AAQILAH OMAR POV.*


Koda isarta gida tasha mamakin garin Dawowar Inna Lami daga anguwa da ta faɗa ma ta ta tafi kuma ce ma ta tayi a can zata kwana. Ba ta ce komai ba tasa kai zata nufa ɗakin 'yan matan gidan da nan ne suke zaune ita da Zahrah da sauran 'yan matan gidan, dama sallama baya daga cikin ɗabi'un ta, hasalima ta manta yadda ake yi domin rabon da tayi ita kanta ta manta, abu mai kyau da ta san take iya yi a halin yanzu shi ne kawai gaisuwa shima Dan bata da yadda zatayi ne da ta yaki ce shi shima.


"Umm Aaqilah Dan Allah ki shiga Ɗakina yanzu akwai maganar da nakeso zamuyi dake ne."


Inna Lami ta faɗa cikin sanyin murya tana nufar Hanyar ɗakin ta yayin da Aaqilah tayi kamar ba zata ba sai kuma ya tafi.


"Wato Aaqilah dama bakomai ba ne dalilin da ya sa na kiraki fa ce akan wata magana mai muhimmanci da nakeso na faɗa miki duk da ban san yadda zaki ɗauke ta ba, amma ya zama dole na faɗa miki saboda hakan shi ne kawai mafita a halin yanzu."

Inna Lami ta faɗa bayan ta zauna saman tabarma a ɗakin nata. Ba ta bari Aaqilah ta ce komai ba duk da kuwa bata jin zatace wani abun ta ci gaba da cewa.


"A shekarun baya Malam Umaru wato Mahaifin ki, matan sa Biyu ni ce ta farko da aka yi mana auren haɗi kuma Auren saurayi da budurwa, sannan sai Sahura ta Biyu, sai kuma Mahaifiyar ki da ta shigo gidan nan matsayin mata ta uku wurin Malam Umaru.
A baya kafin Mijin mu Malam Umaru ya Auro Dije mahaifiyar ki sam ni da Sahura bama zaman lafiya kona misƙala zarratin domin kuwa kullum makwabta cikin rabamu faɗa suke yi masifar yau daban ta gobe daban haka Mahaifin ku malam Umaru mutumin kirki kuma mijin mu maragayi ya ci gaba da haƙurin zama da mu har Allah ya nufa ya Auro Mahaifiyar ki.
A lokacin ne kuma muka yi wani abu shi ne muka haɗe kan mu ni da Sahura kamar ba mu ba muna zaman lafiya a fili yayin da na ciki ke ciki kowa da mummanar ƙudurinsa. Watannin Mahaifiyar ki Biyu a gidan nan ta sama ciki da dalilin hakan shi ne Babban abu na farko da ya kawo haɗin kai da bana tsakani da Allah ba ne, tsakani na da Sahura muka haɗa kai muna matuƙar jizgunawa Mahaifiyar ki da uƙubobi kala kala kuma muna ma ta bazara akan muddin Malam ya sani sai mun kasheta tare da ɗan cikin ta, babu irin zalunci da mugunta da bamuyi ma Mahaifiyar ki ba daga ƙarshe ma boka muka samu muka tafi wurin sa da mummanar ƙudurinmu na hallaka Dije mahaifiyar ki da abin da yake cikinta, sai dai boka ya yi mana ɓakar ishara da faɗin babu wani asiri ko tsafi da zai yi tasiri akan ta domin kuwa bata wasa da ibada sam musamman azkhar hankalin mu ya tashi sosai da jin hakan domin kuwa boka ya tabbatar mana da mace Dije zata haifa. Abin da Malam Umaru yake mafarkin samu ke nan wato ɗiya mace domin yaran mu duka maza ne a wancan lokacin. Jin hakan ne ya sa ba tare da tunanin komai ba muka saka boka ya yi mana wani baƙin aiki akan Yarinyar dake cikin mahaifar Dije wato ke na ya ɗai ɗai ta rayuwar ki, ki taso bakya sauraren kowa kuma bakya ganin kowa da Gashi kuma ki kasance muguwar sheɗaniya da Sanadin hakan har Malam Umaru ya tsine miki kibi Duniya.
A lokacin Tabbas kishi ya rufe mana ido mun aikata abin da har mu mutu Ubangiji bazai taɓa yafe mana ba.
Domin kuwa kamar yadda mukaso haka Boka ya gudanar da aikinsa bayan haihuwarki masifa kala kala ta fara samun malam Umaru kullum babu zaman lafiya tsakanin sa da Dije yayin da ke kuma sheɗanun aljanun da aka turo suke tare dake suke sakawa kike aikata sheɗanci da rashin mutunci ga kuma rashin girmama mutane tun tasowar ki daga ƙarshe ma sanadin haka Dije ta rabu da Malam Umaru.
Sosai muka yi farin ciki da hakan domin kuwa bazan manta ba har ruwa a ƙasa Sahura ta zuba ta sha tsaban farin ciki..."



Tun da ta fara magana Aaqilah tayi shiru tana sauraren ta tsaban mamaki, kaɗuwa, ruɗani, al'ajabi tare da tashin hankali ya hanata faɗin komai har sai da taji tayi Shiru sannan ne ta sama damar faɗin.


"Yanzu da kika tsare ni kike faɗa min Sirrin ku Mene ne abin da hakan yake nufi?."

Aaqilah ta jefo ma ta tambayar ba tare da ta kalleta ba.


Inna Lami tayi Murmushi mai ciwo na nadama mara amfani ta ce.




______
*Labib shin mene ne aikin da ya kawo shi garin Jos ne?.🤔*
*Hazel sannu da ƙoƙari kam.🌚*
*Inna Lami Aikuwa ke da Inna Sahura baku kyautawa rayuwarku ba sam.*
*Turƙashi...!*
*Reader's kunji fa. Ko ya ya zata kaya???.*
*Ku sani ba'ayi komai ba cikin labarin har yanzu... Muje zuwa...!🔥*


_______
*KUYI FOLLOWING WHAT'SAPP CHANNEL NAWA DOMIN SAMUN TSANTSAR SO TUN DAGA PAGE 1 ZUWA INDA AKA TSAYA, MASU NEMAN LITTAFIN ANEESERH MA ZAKU IYA FOLLOWING DOMIN SAMUN DAGA FARKO SHIMA ZUWA INDA AKA TSAYA.*





*Ep_Eleven.*
*💫 TSANTSAR SO.💫*
*❣️The Pure Love.❣️*


Nainarh KD ✍️


*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*


_Taufan means= A strong storm._


____
"Tabbas nasan na aikata kuskure masu yawa a Rayuwata ta baya sai dai a halin yanzu na tuba kuma ina ƙoƙarin ganin cewa na gyara koda kaɗan ne daga cikin kusakuren da son zuciya tare da sharrin shaiɗan suka saka na aikata. Sai dai kuma bakin Alƙalami ya riga ya bushe a halin yanzu bani da wata sauran mafita fa ce na sameki na faɗa Miki gaskiyar komai wata ƙila idan mutuwa ta tazo na mutu cikin salama domin kuwa nasan nawa ta riga da ta ƙare..."


"Wai Mene ne kike nufi ne Inna Lami nifa sam ban fahimci abin da kike nufi ba kin sakani a gaba kina wasu surutai kamar bakya a cikin hayyacinki.


Aaqilah ta faɗa tana taɓe baki domin a irin mugayen abubuwan da Inna Lami ta faɗa ma ta ta aikata kuma yanzu take ma ta wannan hawayen na munafurci a wurin ta shi ya sa ko tausayi ba ta bata ba.



"A yau na shirya na tafi wurin Bokan da muka saka ya yi mana aikin a wancan lokacin da nufin ya ƙarya komai da ya yi ki dawo hayyacinki sai dai mummanar labarin da na tarar shi ne ya yi matuƙar ɗa gamin hankali sosai kuma ya sakani a ruɗani sannan tsoron Allah ya kuma shiga ta na kuma tabbatar wa da Duniya da abin da ke cikin ta ba'a bakin komai muke ba. Allah ya yi ma Bokan da ya yi wannan baƙin aikin rasuwa shekaru biyu baya Gashi bayan shi babu wani mai iya karya baƙin Asirin sai dai wata ƙudurar ta Ubangiji."



Wani irin tsoro ne da tsananin firgici na jin kalaman Inna Lami suka jefa Zahrah dake tsaye bakin ƙofar ɗakin laɓe tana sauraren Komai domin tun lokacin da Inna Lami ta ce Aaqilah ta same ta a ɗaki haka kawai taji bata yarda da Inna Lami ba dalilin haka ya sa ta tsaya laɓe bakin ƙofar gashi ta jiyo abin da ya girme ma tunaninta. Ban da zufa babu uwar abin da take haɗawa duk tayi sharkaf da gumi ta rasa ma ya zata yi da Rayuwarta, tayi da ta sanin tsayawa bakin ƙofar har taji wannan BAƘIN SIRRI (BY Jiddarh S Mapi) ya fi cikin kwando.


Ɗakin su ta shiga ta kasa zaune ta kasa tsaye. Jin alamun motsin za'a shigo ne ya sa tayi saurin zama gefan katifa tana ƙoƙarin gyara nutsuwar ta.


Aaqilah ta shigo cikin wani irin ɓacin rai da Zahrah bata taɓa ganin ta ciki ba. Direct ta nufa Ghana Most Go da kayanta ke ciki. Ta fara kici kicin fito da kayan daga cikin.

‘‘Anty Aaqilah ina ne zaki tafi haka naga kina haɗa kaya?.’’

Ta tambaya cike da tsoro da kuma tausayin 'yar uwan nata da basa zama inuwa ɗaya ganin yadda take fito da kayan tana zubawa cikin wata madaidaiciyar trolley.


"Barin Gidan zan yi domin ba zan iya ci gaba da kwana a cikin ba har abada kuwa.’’

"Saboda me Anty Aaqilah wani abun ne ya faru?."



Zahrah ta tambaya da kyar cikin matsanancin tashin hankali tana ƙoƙarin ɓoye hawayen dake barazanar zubo ma ta.


"Zahrah..! Ki Dena pretending domin nasan kin saurare komai sannan kin san komai sannan ina mai gargaɗin ki da Babbar murya akan kada kowa ya san wannan maganar, idan kuma ba haka ba.."


Ta kaɗa kai tare da taunar harshen ta. Ta fi ce daga ɗakin riƙe da trolley da ta zuba wasu daga cikin kayanta. Zahrah ta bita da kallo baki sake cike da Tsantsar Mamaki.

Aaqilah kuwa bata kula kowa ba, tun bayan fitowarta daga ɗakin riƙe da trolley Direct hanyar waje fa nufa ta fi ce daga Gidan tana fita kuwa taci Sa'a ta haɗu da wani Ɗan Unguwan Lawal da Machine ɗin sa irin ta ‘yan acaɓa. Tare sa tayi tare da masa kwatancen gidan da zai kaita. Sannan ta hau Machine ɗin suka tafi. Zahrah da ta biyo bayan ta ta koma gida da sauri tana hawaye tun da take bata taɓa jin tausayin ‘yar uwan nata ba kalar yau a yanzu, da yake Inna Sahura Mahaifiyar Zahrah ɗin bata nan cikin gidan domin ta fita gidan sha'ani. Inna Lami kuwa kuka sosai take yi cikin ɗakin ta kukan data sani da nadama mara amfani.


_Aaqilah Kuwa._


Gidan Kakansu mahaifiyar mahaifinsu ta saka Lawal ya wuce da ita, koda isarta ta tarar da wani kayan takaici da ɓacin rai domin kuwa tarar da Kakar tasu tayi cikin hali na ciwo gashi ɗakin nata ita kaɗai matan Gidan su biyu matan Yayan Mahaifin su Aaqilah ɗin ma basa nan a gidan suna makwabtan su ana biki.

Tayi bayan gari caɓa caɓa ga ɗakin da yake wani uban wari kamar ba mutum ke Rayuwa ciki ba. Cike da Tsantsar takaici Aaqilah ta a je trolley na kayanta

Please Login or Register in order to submit comment