Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake kamar gonar auduga.


Fira suka ci gaba sai dai Arissa taƙi sakin jikinta kamar farko sai can Althaf ya rakata ta koma gida dan ma gidan nasu babu nisa da masarautar.



______
_AMBRAH POV_




*NEWARK LIBERTY AIRPORT (EWR) NEW YORK.*


Ta yi shu'umin murmushi ganin Oumun nata tayi picking call da tayi ma ta tun bayan fitowarta daga harabar airport ɗin lokacin da jirgin su ya sauka ta kunna wayar nata dake kashe sannan ta canza layi zuwa na kasar dama already tana da shi.



"Hello Oum Ya kike ina fata kun tashi lafiya dama na kira ki ne na faɗa Miki cewa ina New York yanzu haka saboda haka karku ɓata lokaci wurin nema na, tun da kinƙi faɗa min gaskiya a kan wurin da Masoyina yake shi ya sa nayi gaban kaina na taho sannan sanin kanki ne ban san ko'ina ba ki turomin da address na Gidan Uncle Ali Taj ta message sannan Please ki turomin kuɗaɗe domin na hannuna sun yi kaɗan ba zasu isheni ba Bye."



Ta faɗa tare da katse kiran ba ta bari ta ce komai ba.


Ta ɓangaren Dr Aadnah kuwa a zabure ta miƙe tsaye cike da tashin hankali gefe guda na zuciyarta na tafarfasa akan wannan rashin tarbiyya na Ambrah kasa faɗin komai tayi har Ambrah ta katse kiran kawai sai tabi wayan da kallo baki sake.


"Lafiya kuwa Mene ne ya faru lokaci guda kika sauya?."



Kamar wata wacca bata a hayyacinta ta juya tana Kallon mijin nata da ya yi ma ta tambayar.


"Mene ne ma bai faru ba uhum Prof yanzu rashin tarbiyyan Ambrah har ya kai ta tafi zuwa wata ƙasar ba tare da mun sani ba kuma har ta kirani tana bani umarni kamar wata 'yar cikin ta."


Shiru ya yi cike da ɓacin rai na abin da Ambrah ɗin ta yi gaba ɗaya Yarinyar tasu ta sauya daga halayenta tun dawowarta daga karatu.


"Kayi Shiru bakace komai ba?."


Ta faɗa tana fashe masa da kuka. Da sauri ya janyo ta zuwa jikinsa yana lallashi ya ce.


"Kiyi haƙuri kinji Ambrah bata kyauta ba sai dai taja ma kanta wannan mahaukaciyar zuciyar ta ta da take tunzurata tana waɗan nan abubuwan lallai zan ɗauki mummunar hukunci akan ta kuma ba zai ma kowa daɗi ba domin kuwa muddun ina numfashi da raina bazan taɓa bari Ambrah ta aura Taufan ba koda kuwa shi ne ya ce yana sonta balle kuma bana tunanin hakan Aure Tsakanin Ambrah da Taufan babu har abada domin basu dace da juna ba kwata kwata...."!


A fusace kuma a zafafe ya ƙarishe maganar domin kuwa yau Ambrah ta kai sa bango.



_Ambrah kuwa_


Taxi ta tara sannan ta shiga ba'a jima ba message ya shigo wayar tana dubawa tayi taga address ne Oumun nata ta turo ma ta, tayi Murmushin gefan baki. "Oum ke nan wato kina ta jamin rai a tunanin ki zan tsaya bayan irin marmarin son ganin Taufan da nake yi ina masa wani Irin makahon Tsantsar so da bana jin kira."




*157 West 57th street, Manhattan.*





Fitowa tayi daga Taxi ɗin da yake ba kuɗi ne a hannunta ba yasa tayi ma mai taxi ɗin transfer. Jan ye Butterfly Sun Glasses dake idanunta tayi tana ƙare wa wani makeken gida mai masifar kyau da take tsaye gabansa kallo ko ba'a faɗa ba tasan nan ne gidan da Uncle ɗin nata yake. Ta sauke Ajiyar zuciya daidai lokacin da wasu mahaukatan tsalatsalan motoci na alfarma masu masifar kyau da tsada suka fito guda shida a jere daga cikin Gidan bayan an wangale makeken gate ɗin tabi motocin da kallo ko kafin tayi wani yunƙuri gaba ɗaya motocin suka tsaya da alama umarnin hakan aka basu. Mota ta uku ce ƙirar Bentley Mulsanne white color ɗaya daga cikin securities ya ƙari sa ya buɗe ta, a hankali ƙafafuwan sa dake sanye cikin wasu tsadaddun takalma wholecuts baƙaƙe da Safa ita ma baƙa daga ciki ya zura su kafin daga bisani gangar jikinsa gaba ɗaya ya biyo baya Dogo Kyakyawan gaske Matashin Dattijon mai kammala da cikar haiba ga kwarjini yana sanye cikin wani dakakken Suit Marron color.



Sakin baki Ambrah tayi tana kallon sa kafin daga bisani ta ƙari sa wurin sa da sauri tare da Hugging ɗin sa cike da farin ciki ta ce.


"Uncle Taj..."



Ya bubbuga bayan ta a hankali yana sakin ƙayataccen Murmushin da shi kansa ya manta rabon sa da ya yi.




"Ambrah Mene ne abin da ya kawo ki nan New York babu sanarwa sannan ita ma Dr Aadnah ɗin bata faɗa min ba?."


Ya yi ma ta tambayar lokacin da suke zaune a katafaren palo na gidan da kai tsaye za'a iya kiransa da Aljanar daula na Duniya. Bayan awanni Biyu da zuwanta ke nan zuwa yanzu har tayi wanka ta shirya cikin wata Doguwar English Gown Marron mai adon stones ta saka hular Gown ɗin.


Gabanta ne ya faɗi jin irin tambayar da ya yi ma ta. Sanin wane ne shi da kuma halinsa na rashin son wasa ne bawai kuma dan bashi da kirki ba yasa ta saita kanta ta ce.


"Dama Surprising naku naso nayi shi ya sa ka ganni ba tare da sanarwa ba, amma Uncle Taj ina Arissa da Yaya Taufan ɗin suke ne naga tun da nazo ban gan su ba?."



Ta ƙarishe maganar tana ɗan dube dube a palon a tunaninta ko zata gansu. Yayin da ya yi shiru yana bin ta da kallon cike da nazari.....





_________
*Jos, Nigeria.*



"Inna-lilahi Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un wayyo Allah na wannan wacca kalar Rayuwa ce da rashin tsoron Allah ya yi yawa cikinta wayyo ni Khadijatu amma dai su Lami sun cuceni cuta ta har abada."


Kuka sosai Mamansu Aaqilah take yi kanta har ciwo yake yi cike da tashin hankali tun lokacin da Zahrah ta gama bata Labarin dukkanin abin da taci Inna Lami tana faɗa wa Aaqilah.


Ita ma Zahrah kukan take yi tayi datasanin faɗa wa Mamansu Aaqilah gaskiya da tayi ganin yadda take kuka kamar wata ƙaramar Yarinya.



Lallashin ta take yi sosai tare da ban baki sai dai da alama kamar hankalin ta ba'a jikinta yake ba wani irin tausayin 'yar nata Aaqilah ne ya far ma zuciyarta lokaci guda.



___
Ta ɓangaren Hajiya Umma kuwa a Ranar da dare bayan ta koma Gida ta sama Mijinta Alhaji Nawaz da maganar bayan ɗan lokaci da ya ɗauka yana tunani ta samu da kyar ta shawo kansa ya amince Aikuwa cike da farin ciki ta shiga yi masa godiya. Washe gari wuraren ƙarfe sha biyu na Rana tsadadiyar motar ta ƙirar Hyundai Black color tayi parking a bakin ƙofar Gidan da Mamansu Aaqilah take Aure. Ba tare da ɓata lokaci ba ta fito daga motar tana baza ƙamshi sanye cikin wata tsadadiyar Lace white color Mai ratsi ratsin gold da kuma adon stones ta yafa mayafi hannunta riƙe da tsadadiyar jakarta idan ka kalleta ka rantse ba tafi shekaru talatin da Biyar ba tsaban yadda hutu da jin daɗi ya sama muhalli a jikinta. Da sallama ta shiga gidan Mamansu Aaqilah da Teema da suke zaune saman tabarma suna gyara shinkafa ga Zahrah zaune gefansu suna ɗan taɓa fira duk da yadda Mamansu Aaqilah ɗin take jin ta kamar ba ta da lafiya tun bayan faɗa mata maganar da ya yi matuƙar tasar ma ta da hankali da Zahrah tayi a jiya a halin yanzu burin ta bai wuce ganin ɗiyarta Aaqilah ta dawo gare ta ba sannan kuma su fara nema ma ta maganin da zai karya baƙin Asirin dake tare da ita. Amsawa suka yi a tare suna mimmiƙewa tsaye cike da Mamakin ganin Hajiya Umma matar da kafin a ganta sai an yanki ticket.



"Maraba lale lale marhaban Sannun ki da zuwa Hajiya Umma ce fatan kin ƙari so lafiya?."


Mamansu Aaqilah ta faɗa lokacin da Hajiya Umma ta ƙari sa ta zauna saman tabarman bayan ta amsa gaisuwar da su Teema da Zahrah da ta tare a gidan suka yi ma ta.


Sannan suka gaisa da Mamansu Aaqilah nan dai take faɗa ma ta da magana mai muhimmanci tazo jin haka yasa Mamansu Aaqilah ta ce su shiga daga cikin ɗaki to, babu musu Hajiya Umma ta amince suka shiga ciki suka bar su Teema suna ci gaba da gyaran shinkafa da suke yi....




________________________✍️🔥🔥🔥🔥💋💋💋💋


# Khadeejarth Sabi'u Yahyah
₳.₭.₳
# Nainarh KD ✍️👑



https://chat.whatsapp.com/EbOQsBuVulF6V1iYl9WASE

*KUYI FOLLOWING WHAT'SAPP CHANNEL NAWA DOMIN SAMUN TSANTSAR SO TUN DAGA PAGE 1 ZUWA INDA AKA TSAYA, MASU NEMAN LITTAFIN ANEESERH MA ZAKU IYA FOLLOWING DOMIN SAMUN DAGA FARKO SHIMA ZUWA INDA AKA TSAYA.*

________________________✍️🔥🔥🔥🔥💋💋💋💋


*Ep_Thirteenth.*
🌹💖TSANTSAN SO.
*💞💞 Pure Love.*

*©The Nainarh KD...✍️👑*


*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*


_____
Arissa Means= Beautiful name💖

______
🌹Wuyar noma kunyar fari🌹
_____




"Zan iya ganin lafiyar ƙafarta ta ki?."

Ya faɗa yana juyo da kallon sa a gare ta. Da sauri ta yi gefe da ƙafar nata gabanta na faɗuwa ta zaro ido ta ce.


"A'a wallahi ka barshi kawai ai da sauƙi ma Doctor ya ce bada jimawa ba zan warke."


Zuba ma ta ido ya yi yana kallon ta ba tare da ya ce komai ba domin shi ɗin ba mutum ne mai yawan surutu ba ita ma ta fara fahimtar hakan. Ta murmusa tana tuna haɗuwar bazata da suka yi ɗazu ta fito ita da Teema da take taimaka ma ta suna tafiya cikin garin sun yo ta bakin ruwa shi ne fa ta hangosa zaune saman wata doguwar kujera irin ta bakin ruwa nan, maganar da ya yi ne bayan ya miƙe ya dakatar da ita daga Duniyar tunani da ta fara lulawa.


"Zan wuce gida nasan yanzu haka Arissa tana jirana."


Miƙe wa tayi tana riƙe sandar crutches ɗin ta ce.


"Tohm shikenan mu tafi tare da ma kaga Teema da muke tare ta tafi gida."


Bai ce da ita komai ba ya fara takawa, tayi Murmushi da sauri tabi bayansa tana faɗin.


"Sorry ka jirani mana bakaga irin tafiyar tawa ba sai da bi a sannu."


Jerawa suka yi suna tafiyar babu um bare um um. Jin shirun ya yi yawa ne kuma a yadda ta fara fahimtar ɗabi'unsa ba maganar zai yi ba yasa ta yi gyaran Murya tana faɗin.


"Wai kai baka magana ne?."

"Mene ne nake yi yanzu?."

Shima ya tambaye ta.


"A'a ina nufin baka da hayaniya i Like it zamu iya zama abokai ai koda yake ma mun riga mun zama sai dai har yanzu baka faɗa min sunan ka baz ni kuma na faɗa maka nawa."

"Taufan Ali it's my name, and I don't like we be friends."


Samira ta kuma murmusa wa ita fa wallahi Muryarsa daɗi take ma ta shi ya sa take ƙaƙale ƙaƙalen fira da shi.


"Wow nice name and nice to meet you Mister gentle handsome but mene ne dalilin ka da ya baka sha'awar mu zama abokai?."


"Oh sunan nawa ke nan Gentle handsome?."

Ya yi ma ta tambayar yana kawar da tambayar da ita tayi masa.

"E, mana gani nayi da hakan ka dace." Ita ma ta basa amsa a gajarce.


Tafiya suka ci gaba a hankali Samira tana jansa da fira wasu ya bata amsa wasu ya shareta sai dai bakinta yaƙi shiru kamar wacca dama can surutun ya dame ta ne, duk inda suka wuce sai an bisu da kallo da yake bakin ruwan gefan gari ne shi ya sa akwai 'yar tafiya kaɗan kafin a ƙari so zuwa gidan Sarki Muhammad Raees.




*Teema Silent POV*



Da hanzari ta a je butar Hannunta bayan fitowarta daga Ban ɗaki data shiga, hanyar fita daga gidan ta nufa sai dai Muryar Mamansu da taji tana kiranta ne ya sa ta juyo tana amsawa.


"Ke ina zaki tafi haka?."


"Na'am Mama wurin Anty Samira zan koma nasan tana jirana kuma Mama wai sai kace Ni ɗin 'yar fari ce da bakyason kirana da Teema sai dai Ke, ita kuma Anty Aaqilah da take 'yar fari sai ki kirata da Ita."


Teema ta faɗa tana gwaɓe fuska.


"Oh oh oh ni Khadijatu wannnan Samira ai ko Ƙanwa ta ce ƙarshe ke nan aikin ki ke nan Samira ina kika fito Samira. Ina zaki Samira."


Teema tayi dariya.


"Wato dai Mama ba zaki kulani da magana ta ta ƙarshe ba ke nan."


"Ke ki kiyaye ni fa maza kije gidan Alhaji Sale wurin ita kice da ita ta zo gobe ina son ganinta kinji kuma bance ki daɗe ba."


"Tohm Mama bari na shiga ɗaki na canza Hijabi tukunna na tafi."


Teema ta amsa tana shiga ɗakinsu ta sauya Hijab sannan ta fito.


"Un go Wannan ki hau abin hawa kiyi sauri ki dawo."


Karɓan kuɗin da Mama take miƙa ma ta Teema tayi zatayi magana Zahrah ta shigo gidan da sallama ɗauke a bakinta.


"Wa'alaiki Salam oyo yoyo Anty Zahrah gwara da Allah ya sa kikazo kinga sai mu tafi tare ma."


Teema ta faɗa cike da murna.


"Ina ke nan zamu tafi taren?."


Zahrah ta tambaya bayan sun gaisa da Mama.


"Mama ce ta aike ni Gidan Kawu Sale wurin Anty Aaqilah please muje ki rakani?."


"Tohm shikenan muje."


Zahrah ta amsa, sallama suka yi ma Mama sannan suka fita basu daɗe da fita ba suka tare mai a daidaita cikin ƙan ƙanin lokaci ya kai su can unguwar.


"Allah ya sa ma tana gidan dai."


Teema ta faɗa daidai lokacin da suke ƙoƙarin shiga cikin gidan bata ƙari sa ba taji tayi karo da Mutum tana ɗagowa suka haɗa ido da Bello ya zuba ma ta jajayen idanunsa gabanta ne ya faɗi amma ta daure ta ce.


"Lah Yayah Bello kaine ashe kana nan?."


Ta faɗa tana kallon sa.


"Teema kike ko Ƙanwar Aaqilah?."

Ya tambaye ta, da sauri ta amsa masa da faɗin.

"E, ni ce."


"Oho to sannun ki."

Ya faɗa yana raɓa wa ta gefanta ya fi ce. Ita kuwa ta bisa da kallo tana murmushi.


"Ke Teema mene ne kuma haka kardai ace son wannan mutum kike?."

Zahrah ta tambaya tana zaro ido.


"A'a kam nima har yanzu ban tabbatar ba sai dai abin dana sani shi ne kawai yana matuƙar burgeni."


"Lallai Teema na lura kin fara zarewa fa yanzu ko akai aka ɗaura Miki Bello ai babu abin da zakiyi da shi."


Zahrah ta faɗa cike da takaici sanin ko wanene Bello da tayi.


"Hummm Anty Zahrah ke nan ki sani shi so baya ji baya gani, amma fa ni ba cewa nayi ina son sa ba kawai burgeni yake yi."

"Chabbb Allah ya kyauta to. Amma wallahi Teema duk da cewa shi ɗin Ɗan uwa ne a wurina bana miki sha'awan aurensa haba mana."


"Kedai Anty Zahrah mu bar maganar tun da har nace ba son sa nake ba shikenan magana ta ƙare."


"Oho dai ke kika sani."


Zahrah ta faɗa cike da takaicin Teema ɗin suka shiga cikin Gidan.



"Ah Bahbah kaine a garin Yaushe ka dawo ke nan aikuwa yanzu muka haɗu da Mutuniyar taka."

Bello ya faɗa lokacin da ya ƙari sa majalisar su na Samari irin sa marasa aikin yi.


"Kaidai bari kawai Bahbah gani nayi ƙurar ta lafa tun da har Sarki bai neme ni ba, na taɓa jikarsa da nayi shi ya sa na jamo amma wacece Mutuniyar tawa?."


Dariya Bello ya yi yana dafa Sule ɗin ya ce.


"Matsoracin kaya ai ba Sarki zakaji tsoro ba a halin yanzu Aaqilah ce domin kuwa kasan ba zata kyaleka ba na abin da kayi ma ta sannan Zahrah nake nufi mana Mutuniyar taka."

Ya mutsa baƙar fuskarsa ya yi yana faɗin.


"Bahbah kyale ni da zancen wannan Zahrah domin tafi ƙarfina so nayi na ɗan kwashi rabona sai dai na gano ba 'yar Duniya ba ce shi ya na fita harkar ta."





_____
"Hazel kamar akwai abin da yake damun ki ko?."


Arissa ta faɗa tana kallon Hazel da tayi Shiru kamar mai tunani suna tsaye ne ƙofar gidansu Hazel Arissa ta kawo ma ta ziyara da yake yanzu ba school suke zuwa ba shi ya sa haɗuwar take musu matuƙar wuya gashi sun saba da juna.





_____
*_Kamar yadda na faɗa muku Tsantsar so is Paid Book 500₦ ne kacal wacca ta shirya biya ta tuntuɓe ni ta wannan lambar 08148330075 via WhatsApp Only. Sannan Free Page's suna dab da ƙarewa kuyi ƙoƙarin ganin wannan tafiyar daku zata kasance 🔥❣️_*



___
*_Muddun bana ganin comments tohm next page will be delayed. 😁_*


*Ep_Fourteen $ Fifteenth.*
*The Last Of Free Page's.🙌*
💖🌹TSANTSAN SO.
*❣️The Pure Love.*

*© Nainarh KD...✍️*

*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*

____
Arkan Means = The solid pillar of life.💖
________

💞Wanka da gari baya maganin yunwa💞
______


*Around 8:10pm.*

"Yah Arkan kai ne a wannan lokacin haka ina fata dai lafiya?."


Samira ta faɗa lokacin da ta ƙari sa daidai bakin ƙofar da zata sadata da Apartment nasu ta hango Arkan ɗin tsaye kamar yana jiran wani ko wata.


"Ah Mira daga ina haka?. Ƙari so mana dama wurin ki nazo akwai maganar da nakeso muyi dake yanzu idan babu damuwa?."


Ya yi maganar fuskarsa ɗauke da ƙayataccen Murmushi na musamman da ya bawa Samira mamaki domin ita a iya sanin ta da kuma yadda su Hamrarh da ma ƙannin sa suke faɗa sam Yah Arkan bashi da fara'a ga yawan muguntar sa da suke faɗa sai dai ita duk bata san da hakan ba domin bayi ma ta yake ba koda yake ma a'ina zai ganta?.



"E, wallahi daga ɓangaren Fulanin Sarki nake shi ne fa na hango ka, Tohm shikenan babu damuwa ga wuri can sai mu zauna daga can ai."


Ta basa amsa tana Kallon sa kamar yadda shi ma yake kallon ta da alama maganar da zai ma ta na musamman ne, ƙari sawa suka yi wurin da wasu ƙayatattun kujeru na zama suke da aka zagaye su daga can gefe na wurin tsakiyar su kuma madaidaicin table ne na ɗaura abubuwa Like cups of water e.t.s.
Akalla sun shafe kusan mintuna bakwai da zama shi bai ce da ita komai ba, haka ita ma batayi magana ba sai ma wasa da zara zaran yatsun hannunta da take yi. Gyaran Murya da taji ya yi ne ya sa ta ɗa go a nutse ta kallesa yana faɗin.


"Mira ki bani aron hankalin ki Dan Allah akwai magana muhimmanci da nakeso zamu yi yanzu, zan iya samun aron lokacin ki mai tsada da nutsuwar ki da yafi komai burgeni?."


Da sauri ta ce.


"E, mana Yah Arkan ka faɗa koma Mene ne ina sauraren ka."
Ta faɗa hakan tana sauke idanunta ƙasa daga kallon sa domin haka kawai taji gaban ta na faɗi tun bai faɗa abin yake son faɗi ba. Yayin da shi kuwa ya yi Shiru da alama yana nazari ne akan ta inda zai fara, ajiyar zuciya ya sauke a hankali cikin kamilalliyar Muryarsa ya fara magana nutsatsitsya kamar haka.


"Mira ban san ya zaki ɗauka maganar da zan faɗa miki yanzu ba, amma Dan Allah ina so kiyi min kyakyawar fahimta akan maganar da zan faɗa miki yanzu kinji?."

Shiru ya yi bai kuma bari ta ce komai ba ya ci gaba.


"Mira Ina son ki, ba yanzu ba, ba kuma shekara ɗaya baya ba, abin da na sani shi ne kina burgeni sosai kuma kina daga cikin irin matan da nake da muradi a rayuwata tun kina ƙaramar Yarinya nake fama da ɗawainiyar soyayyar ki, ba zan takuraki akan sai kin so ni ba, amma zan baki iya duk adadin lokaci da kike buƙata domin kiyi tunani akan lamarin."


Duk da cewa cikin nutsuwa irin tasa da kuma kamilalliyar Muryarsa yake ma ta maganar, amma hakan bai hana Samira haɗa uban gumi ba tana sauraren sa yayin da zuciyarta take tattaro ma ta wane ne Arkan da kuma irin alaƙar dake tsakanin su an ya kuwa?...


*After Some Minutes.*


Tuƙi yake yi Sannu a hankali zuciyarsa fal tunani akan shin Samira Mira ɗin sa zata amince da shi ta karɓa Soyayyar sa ko kuwa?. Tun da ya faɗa ma ta Sirrin dake Zuciyarsa kuma ta daɗe tana naƙarƙasarsa bai bayyana ma ta ba sai a yau, gashi a yau ɗin ma bai da tabbaci akan zata amince da shi As a future husband da zasu rayu tare har mutawa. Bai san iya adadin lokacin da ya ɗauka yana tunane tunane ba har lokacin da ya isa katafaren gidan Alhaji Nawaz mahaifinsa sannan ne bayan ya shiga ya ƙari sa parking lot ya faka motar a wurin da ya dace, sannan ya fito cikin nutsuwa yake tafiyar yana kiran Allah a zuciyarsa kamar koda yaushe. Tsararren part na mahaifiyarsa ya nufa kai tsaye domin tsawon yau basu gaisa da ita ba, bata nan a palo sai ƙanwarsa da yake shi Althaf kusan gaba ɗaya rayuwarsa a can Masarauta yake gudanarwa wurin Fulani Bilkisu tun yana Yaro bayan an kaisa ya ye. Kai tsaye Up ya nufa yana taka Staircase's ɗin in twins fuskarsa ɗauke da murmushi domin so yake ya faɗa wa mahaifiyar tasa babban albishir a yau na cewa yana daf da kawo ma ta Future wife tasa da ta daɗe tana masa naci akan ya yi aure duk da cewa Samira bata basa amsa ba sai dai bayajin cewa Samira zata ƙi sa wannan ne Babban gwarin giwar Arkan.


Wadatacciyar sallama ɗauke a bakinsa ya shiga Bedroom ɗin bayan ya kwankwasa ta basa izinin shiga daga ciki. Zaune ya hangota daga gefe saman Royal Bed nata tana folding Hijab da alama sallah ta idar.


"Umma Barka da dare fatan na sameku lafiya?."

Ya faɗa bayan ya ƙari sa ya manna ma ta sumba a goshi sannan ya zauna daga ƙasa saman Sallaya da tayi Sallah akan ta bata riga ta nan na ɗe ba.


"Alhamdulillah Ustaad ka baro su lafiya ya Samira da jiki?."


"Duk suna lafiya Umma ta sun ce ma a gaishe ki ita ma Samira ɗin tana lafiya Alhamdulillah."

"Madallah."


Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani ta katse Shirun ta Hanyar faɗin.


"Ustaad nayi maka laifi fa ban sanar da kai ba."


Dariya ya yi a nutse kamar yadda yake komai nasa a nutse shi ya sa Umman tasu ma take kiransa da Ustaad tun yana ƙarami daga haka kuma kowa ya kama.


"Laifi kuma Umma ta wani kalan laifi ke nan?."

Hajiya Umma ta murmusa tana basa amsa da faɗin.


"Aure zan maka babban abin da kaƙi jini ke nan kuma bakwa haɗa hanya shi ya sa nace nayi maka laifi."


"Aure kuma Ummata seriously?."


Ya faɗa a ɗan daburce ba wai kuma don maganar nata ya rikitasa ko saka masa faɗu war gaba ba. Coz this is not the first time da Umma zata ce zata masa aure kuma wasa take yi ita da kanta take faɗan hakan daga baya. So shi ya sa ma bai ɗauka wannan maganar nata serious ba.


"Yeah Ustaad da gaske nake in sha Allah nan da sati biyu masu zuwa za'a ɗaura auren ka da Aaqilah domin mun gama magana da kowa har an tsayar da lokaci dama kai ne baka sani ba gashi yanzu na sanarda kai ina fata babu wata matsala ko?."


"Matsala babba ma kuwa Ummata mene ne dalilin ki na yimin haka ba tare da sanina ba Why Umma Why?.."!


Abin da yake iya furta wa ke nan a ƙasar Zuciyarsa. Yayin da a fili kuwa cewa ya yi.


"Duk abin da kika yi nasan ba kinyi ba ne domin ki Cutar dani sai ma domin tsananin ƙaunar da kike yimin. Bakomai Umma Allah ya kaimu lokacin kuma ya bamu zaman lafiya."


Ya faɗa yana Miƙewa tsaye domin a wannan lokacin shi kansa bai san inda ya kamata ya a je ƙwaƙwalwar sa ba da take barazanar tarwatse wa, zuciyarsa kuwa kamar zata buga tsaban tashin hankali da magungunan Umman tasa ta saka sa. Tun da yake bai taɓa yi ma ta musu ba akan komai kuma bayaji zai taɓa ma ta musu akan wani abun ita ɗin mahaifiyarsa ce Komai tayi daidai ne.


Sam Hajiya Umma bata lura da irin halin da ɗan nata ya shiga ba saboda farin ciki na amincewa da ya yi duk da cewa sanin kanta ne ba musu zai ma ta ba.


"Yauwa Baka jiba nace gobe ka shirya zaka ce ku gana da ita Yarinyar."


Har ya kai bakin ƙofa ya tsinkayi Muryarta tana faɗin hakan.


"A'a Umma ba ma sai mun gana ba, na yarda dake ba zaki taɓa haɗani da abin da zai cutar dani ba Allah Ubangiji ya bamu zaman lafiya kawai."


Cike da alfahari Hajiya Umma take kallon yaron nata sannan ta amsa da. "Ameen ya hayyu ya qayyum. Ustaad Allah ya maka albarka ya kuma baka yara da zasuyi maka biyayya fiye da yadda kake yimin."


Da Ameen kawai ya amsa yana ficewa daga Bedroom ɗin domin ji yake kamar ya yi hauka. Shi kansa bai san lokacin da ya ƙari sa part ɗin sa ba. Kai tsaye Bathroom ya shiga ya sakar ma kansa shower Mai sanyi a hakan da yake domin

Please Login or Register in order to submit comment