Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fa bakici komai ba tun safe har yanzu. Haka ma jiya da kyar aka samu kika saka wani abu a bakin ki."


Hamrarh ta faɗa daga tsayen da take bakin gadon da Samira take kwance sai dai an ɗa go da ita kaɗan ba'a kwance take ba, ta jingina bayan ta da abin da aka saka domin ta jingina jikinta.


Gefe tayi da fuskarta alamar dai ba zata sha abin da Hamrarh ke miƙa ma ta ba.


"Kin gani ko Mumma gashi dai a gaban ku nayi nayi amma taƙi tasha gashi taƙi cin komai."


Hamrarh ta faɗa cike da damuwa tana mayar da kallon ta kan mutanen dake zagaye da Babban Room ɗin gaba ɗaya Familyn Raees sannan ta sauke idanunta akan Mahaifiyar tasu tana zama saman ming chair dake gefan Gadon da Samira take a kai.


Lumshe kyawawan idanunta tayi a hankali ba tare da ta ce komai ba. Wannan lokaci ya yi daidai da turo ƙofar Room ɗin da aka yi Arissa suka shigo ita da Taufan bakunan su ɗauke da sallama. Samira tanaji mutanen Room suna amsa sallama da aka yi bayan an shigo sai dai hakan bai saka ta buɗe idanun nata ba, sai ma nutsuwa da tayi tana shaƙar wani daddaɗan ƙamshi mai sanya nutsuwa da ya kaima ƙofofin hancinta ziyara, ji tayi kamar ta san ƙamshin kamar ta taɓa jin kalar kamshin, sai dai a'ina?. Abin da ta kasa tunawa ke nan.



"Taji sauƙi Alhamdulillah sai dai ƙafafuwan ta ne da suka bugu ne, da ba'a lura ba sai daga baya su ne kawai matsalar amma da tun tuni an sallame mu. Gashi taƙi taci komai."


Hamrarh ta faɗa idanunta akan Handsome Guy ɗin da ya shigo Room ɗin lokaci guda ƙamshin sa ya cika ko'ina yana tare da wata Cutie Girl da tafi zaton ƙawansa ce, Bayan Arissa ta tambaya lafiyar Samira ɗin domin duk a zaton su Bacci take yi ba idanunta biyu ba, da kallon yadda Hamrarh ta ƙarishe maganar zaka fahimci a fusace take da Samira domin kuwa ba ƙaramin haushi ta bata ba.



"Buɗe bakin ki."


Shi ne Kawai abin da taji an faɗa cikin wata kalar sassanyar kamilalliyar murya mai daɗin saurare ta buɗe kyawawan dara daran idanunta tare da zaro su gaba ɗaya cike da mamaki na ganin sa zaune saman Gadon daga gefanta hannunsa riƙe da Cup da Hamrarh take ƙoƙarin tasha abin da yake ciki da ita kanta batasan ko mene ne ba amma taƙi, tsaban mamakin ganinsa ne yasa ta buɗe baki ba tare da tayi shawara da zuciyarta ba. Aikuwa ga mamakin ta ya hara bakin nata da Cup ɗin sannan ne ta fahimci kakkaurar tea ne a cikin bayan ta karɓa kaɗan, ta lumshe ido tare da buɗewa tana kuma kurɓa bayan ta shanye ya kuma bata a baki.

Kowa dake Room ɗin ya saki baki cike da al'ajabi na ganin yadda Samira take shan Tea ɗin a hannunsa, take Miss Asfiya da Yaranta da sauran mutane suke kira da Momma yayin da wasu suke kiran ta da Miss Asfiya ta saka ayar tambaya tsakanin Samira da wannan Handsome da ya shigo da abin mamaki garesu, Arissa tayi Murmushi tana lura da yadda idanun mutumin nata Althaf suke a kanta yana ta ƙoƙarin ganin sun haɗa ido sai dai taƙi basa damar hakan, tana daga zaune gefen Ambrah dake zaune cikin kujerar ta na guragu sakamakon da wannan lalura na rashin ƙafa aka haife ta, akwai ƙafafun sai dai likitoci sun tabbatar da ba zata iya taka su ba sakamakon dannesu da aka yi tun tana ciki, twin's ne su ita da Hamrarh sai dai basa kama sam domin ita Hamrarh irin matan nan ne 'yan duma duma bata da tsayi sosai sai dai ba gajeruwa ba ce, kuma fara ce hasken ta mai silkin ja akwai ta da dara daran idanu, yayin da Amrarh ta kasance doguwa ce ita duk da kuwa ba tafiya take ba kuma siririya ce mai sanyin hali fara ce ita sosai domin hasken ta bai silka da ja ba, sam ɗabi'un su basu zo ɗaya da biyunin ta Hamrarh ba.


"Sannu."


Ya faɗa yana kallon ta kaɗan cikin kamilalliyar Muryarsa da ta sanya ta cikin nutsuwa a lokacin.


"Yauwa Sannu."


Ta amsa.


"Mene ne yasa ƙika ƙi cin komai bayan kinsan hakan Hatsari ne ga lafiyarki?."

Ta dubesa jin tambayar da ya yi ma ta, sai dai maimakon ta basa amsa, sai ita ma ta jefo masa nata tambayar da faɗin.


"Kana lafiya babu abin da ya sameka?."


Bai bata amsa ba saima kallon ta da ya yi kaɗan cikin sakanni biyu sannan ya kawar da idanunsa daga gare ta yana sakin ɓoyayyiyar Murmushin da shi kaɗai yasan ya yi abin sa.


"Sorry ka ceci Rayuwata ban maka godiya ba, saboda wannan lamarin da ya biyo baya ya kasance, na gode."


Cikin daddaɗar Muryarta mai kamar sarewa tayi maganar kuma a hankali domin ko Hamrarh da bayan Taufan babu wanda yake kusa da Samira cikin mutanen dake Room ɗin bata ji abin da ta faɗa ba.



Miƙewa ya yi a nutse yana kallon agogo da yake ɗaure a tsintsinyar hannunsa. Samira ta bisa da kallo ganin ya ƙari sa wurin Arkan ɗa wurin Uncle Nawaz da suke kira da Ustaad suka yi misabaha kamar yadda suka yi lokacin da ya shigo Room ɗin, sannan suka yi ma mutanen Room ɗin sallama tare da ficewa daga Room ɗin. Mutumin nata da Arkan sai kuma wata Cutie da take da tabbacin ƙanwarsa ce duba da yadda suke kama. Ta kuma lumshe ido tana jin yadda Hamrarh take ma ta tsiya ta hanyar faɗin.


"Oho Owkay na fahimta Tabbas kuwa ashe shi ya sa."


Banza tayi da ita don kuwa sarai ta fahimci abin da take nufi. Muryar Barrister Aeshah Ɗiya ta Biyu wurin Umma Safiya Matar Sarki Muhammad Raees ta Biyu da yara Biyu kawai gareta tare da mai martaba, Canal Nubaid shi ne Babba sannan sai Aeshah da ta kasance Barrister ce babba tana Auren wani Tantirin Matashin sanannen mai Dukiya lamba ɗaya sunan sa Sartaj Khamis Taj ana masa laƙabi da S.K Taj suna zaune a garin Abuja bata taɓa haihuwa ba.



"Adila kina lafiya kuwa?."



"Lafiya Qlau Anty Aeshah mai kika gani?."


Samira ta amsa ma ta bayan ta buɗe idanunta karo na farko a taƙin da tayi Murmushi kaɗan.


"No, tun da kina lafiya shikenan. Kai Althaf sai kuyi magana da Doctor akan sallama domin naga ƙafafuwan nata ba wani damuwa ba ne sosai kawai sai ta ci gaba da amfani da crutches kafin komai ya daidaita."


Althaf da tun shigowar hasken ruhinsa wato Arissa ya susuce da kallon ta har fitar su, yaja dogon numfashi kamar wanda ya sha gudu, ganin yadda mutanen Room ɗin suka zuba masa ido ne, yasa cikin sosa ƙeya ya nufa hanyar fita yana amsawa Barrister Aeshah da faɗin.


"Okay Sis B.B." (Big Barrister)


___
A Ranar wuraren ƙarfe Biyar Na marece Doctor da yake kula da Samira ya yi Discharging nasu domin kuwa Matsalar ƙafarta nata ba wani mai yawa bane sun bata crutches da zata ci gaba da amfani da shi kafin ƙafarta ta ta koma normal, kanta ma da ta Bugu tun washe gari ya dena ma ta zafin da yake ma ta. Sun koma can Masarautar Raees an ci gaba da kula da ita 'yan uwa suna zuwa du ba ta danma kusan yawancin su suna nan a masarautar sakamakon hutun ƙarshen Shekara da suka zo kamar yadda aka saba. Duk wannan lamarin da ake ciki, Samira taƙi bari a sanar da iyayenta, da Mai martaba Muhammad Raees ya tambaye hujja, sai cewa tayi hankalinsu ne zai tashi idan suka sama labari kuma da wuya wata shekarar su bari ta sake zuwa ita kuma tsakani da Allah tanason zuwa Nigeria kodan ta haɗu da 'yan uwanta dangin Mahaifinta sai dai Iyayenta ba son zuwanta suke ba, daga cikin dalilan ta na neman a ɓoyewa iyayenta zancen shi ne basu san Nigeria tazo ba, ƙarya tayi musu da cewa zataje Dubai Bikin School mate nata shi ne ta gudo Nigeria babu wanda yasan wannan gaskiyar sai ita da Ubangijinta.



_Kwanaki Biyu Gaba_


Alhamdulillah kam domin a halin yanzu ƙafar Samira ta fara warkewa sai dai still bata dena amfani da crutches ba Doctor ya ce ta ci gaba zuwa wani lokaci a ga abin da hali ya yi. Tun bayan komawar ta Masarautar bata kuma fitowa wajen masarautar ba, duk kuwa da son fitowa da take yi.


Daga ɓangaren Hazel kuwa sun kammala Secondary school saboda haka bata fita sosai a halin yanzu haɗuwa da Labib yana ma ta wuyar duk da kuwa da Irin son su haɗu da yake yi ba dare ba Rana idanunsa na kan ƙofar gidansu ko zai ga fitowarta sai dai Shiru.





Daga can Zamalek dake Cairo cikin Egypt kuwa Ambrah duk yadda taso da iyayenta na su barta ta tafi New York ɗin domin ganin masoyinta kuma Ɗan uwanta Taufan abu ya cutura domin duk ta inda ta ɓullo musu sun ƙi yarda har hakan ya ɗarsa kokwanto a zuciyarta game da lamarin ta fara tunanin an ya kuwa iyayenta babu abin da suke ɓoye ma ta, Gashi ko waya sun ƙi bari tayi da Taufan ɗin ta, ta dai kira Daddynsa wato Ali Taj Ozan sun gaisa daga haka babu wanda ta kuma kira domin ita Arissa bata da waya dama shi kuma Masoyin nata layin nasa ma gaba ɗaya baya shiga.
Sosai Ambrah ta shiga damuwa na wannan lamari.
Fitowarta ke nan daga Bathroom tayi wanka ta hango tsadadiyar wayarta dake saman Bed daga gefe tana ruri alamun shigowar kira, ta ƙari sa da sauri domin picking sai dai tun kafin ta ɗa ga kiran ya katse, ta sauke numfashi mai nauyi ganin sunan mai kiran.


"Dole yau na fita kota halin ƙa ƙa."


Ta faɗa a fili tana furzar da iska.


Nan da nan cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya cikin wasu arnun dress. Body wrap gown iya gwiwa mai adon stones Mai kyalli daga gaba sannan mai igiya da wurin Bottles sai coffed trouser mai launin kore mai haske ya matseta tsam yana da yanka yanka kamar irin crazy ɗin nan ta gyara gashin kanta ya yi kyau tayi make-up saffa saffa sannan ta ɗauki Heeled Boots Shoes Black ta saka ta dubi kanta a mirror tayi Murmushi sannan ta ɗauki wata Abaya ta ɗaura saman Dress na jikinta ta ɗauki jakarta da wayarta ta fito bayan ta saka ƙaramin lufaya ta yane kanta da shi.


Sauri sauri gudu gudu take taka Benen lokacin da take saukowa Sannan bayan ta ƙari sa saukowa Down ta ƙari sa wurin iyayen ta suke zaune a Palo da alama fira suke yi ta rungumo su gaba ɗaya a tare tana Murmushi tare da manna musu sumba a goshi da yake tare suke zaune saman Sofa.


"Hey Abhie and Oum Morning ya kuke zan fice ƙawayena suna jirana ina nan dawowa ba daɗewa zan yi ba nayi alƙawari."


Lokacin da ta ƙari she maganar har ta fice daga Palon ba tare da jiran ta bakinsu ba, suka bita da kallo kawai.



Wata tsadadiyar mota Lexus LS500 Black color ta shiga sannan ta kunna ta fita daga gidan.


Da isarta wurin da ya fi kama da Hotel bayan ta shiga ciki tayi parking wurin da ya kamata daga cikin motar ta tsaya ta cire Abaya da ta saka tare da lufayan sannan ta saka kettle brim hat Mai launin baƙi da ratsi ratsin kore ta fito daga motar sannan ta shiga cikin kai tsaye ta wuce zuwa Ɗaki mai lambar da aka faɗa ma ta ta cikin wayar dake kare a kunnen ta, bayan ta shiga ta rufo ƙofar garam.🌚


Tsawon awanni biyu ta share tana cikin sannan ta fito kai tsaye ta fito daga hotel ɗin ta biya Boutique tayi siyayya Daga nan ta wuce Wurin ƙawarta tun ta Yarinta Atyaf ta daɗe sosai gidan su Atyaf daga bisani zuwa lokacin yamma tayi liƙis ta wuce gida a gajiye.




___
_Jos Nigeria_


_Samira Adila Dina (SAM POV)_



"Sannu fa kece Aaqilah da aka ce kinzo wurina ke nan."


Samira tayi maganar tana kallon Budurwar da suke tare da Teema suna zaune ne cikin wani keɓantaccen Palo. Tana Bedroom nata data sauka wata hadima take faɗa ma ta Teema sun zo wurinta ita da wata sunanta Aaqilah shi ne da jin haka Samira ta ce a kaisu Palon baƙi dake ɓangaren sannan ta fito daga Bedroom ɗin ta, ta wuce palon da Ganin Budurwar ta saki Murmushi sannan bayan ta zauna ta faɗa maganar da tayi.



Bata jira Aaqilah ta amsa ma ta ba fuskarta wadace da murmushi ta ci gaba da faɗin.


"Dama ina so nayi miki godiya na ceton mu nida Teema da kikayi, har kika so samun rauni saboda hakan ina mai baki haƙuri."


Aaqilah ta kalleta karo na farko taji ta burgeta ganin yadda take maganar ta Babu girman kai a tare da ita ko kaɗan balle alamun wulaƙanci tunda har take ma ta godiya da bata haƙuri.


Taja Ajiyar zuciya a nutse ta ce.


"No Karki wani damu dan yiwa kai ne tun washe gari na Ranar da abin ya faru ma naso nazo Asibitin na dubaki Allah bai nufa ba sai yau."


"Allah Sarki bakomai hakan ma na gode."


Samira ta faɗa.


Yayin da Teema ta zubawa Aaqilah ido cike da mamaki jin yadda tayi Maganar a yanzu babu wannan ciccijewa da take yi kuma a nutse tayi maganar.


Aaqilah ta watsa ma ta harara, sannan ta miƙe tsaye tana faɗin.



"Bari na wuce gida, ke Teema zaki tafi ne ko kina nan?."


Tayi Maganar tana sauke coals eyes nata akan Teema.


"E, nima komawa zan yi ai yamma tayi sai dai gobe nazo aiki."



"Badai tafiya zakuyi ba yanzu yanzu?."


Samira ta faɗa tana Miƙewa tare da Gyara crutches ɗin.


"E tafiya zamuyi Anty Samira Allah ya baki lafiya."


Teema ta amsa ma ta.



"Okay na gode amma kafin nan please kinsan gidan da wannan Handsome Guy ɗin yake shi da ƙanwarsa?."


Teema ta dakata da tafiyar da suka fara ta juya tana kallon Samira jin abin da faɗa.


"E Anty ai nan kusa ne ma Babu nisa."

Teema ta faɗa domin ta gane ko wa Samira take nufi.



"Okay inaso zaki rakani ne yanzu."


"Okay babu damuwa ai."


Teema ta amsa.


Samira tayi Murmushi sannan Teema ta taimaka ma ta wurin kama ma ta ta gyara sandar crutches ɗin nata dama Doguwar Gown ce a jikinta sai veil da ta yafa ba tare da ta rufe dogon gashin kanta da tayi style nasa in ponytail da hula ba, tayi rolling kanta da veil ɗin.

Fitowa suka yi su uku tare da Aaqilah ɗin da zata wuce Samira da Teema kuma su wuce gidansu Arissa...





______



# _👑Nainarh KD✍️👑_




*_The Nainarh KD_*

_Proudly Present_


*Ep_Eight.*
*❣️ TSANTSAR SO.❣️*
*The Pure Love.*


_❣️Destiny, Struggle, Inclination, Merciless, suffering, Excruciation, and Negate Pure Love.❣️_



~_From The Pen Of Nainarh KD Writer Of Sarauniyar Kyau And Aneeserh (Innocent Girl.)_~


*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*





A hankali ta juya ta kalla Teema dake zaune gefe da ita saman tabarma da aka shimfiɗa musu lokacin da suka ƙari so gidan, tayi Murmushi kaɗan tana kuma bin gidan da kallo, maganar da taji an yi ne yasa ta juya domin ganin mai maganar.


"Lah Anty Samira kece a gidan namu lale lale."


Tayi Murmushi ganin wannan cutie Girl ɗin ne da har zuwa yanzu batasan sunanta ba, buɗe baki tayi zatayi magana Kakus ta riga ta da faɗin.


"Allah mai iko daga shigowa babu sallama balle gaisuwa kin zo kin cika mana kunne da ihu."


Arissa tayi Murmushi bayan ta ƙari sa wurin su ta zauna daga saman tabarman ba tare da ta kalle Kakus ba ta ce.


"Uhum ai nayi sallama kece kawai baki ji ba. Ina wuni Anty Samira ya ƙarfin jikin naki ya ƙafar?."


"Alhamdulillah naji sauƙi kina lafiya?."


Samira ta amsa ma ta sannan ita ma tana tambayar ta.


"Lafiya Qlau wallahi bari na cire hijabin nan Nazo muyi fira.".
Arissa ta faɗa tana tashi tsaye ta cire Hijabin islamiyya da ta dawo dake jikinta sannan ta kai Alkur'ani mai girma Ɗaki ta a je, ta fito tana faɗin.


"Teema yau baki tafi Tahfiz na yamma ba ina fata lafiya?."


Teema taja ajiyar zuciya ta ce.


"Kedai Arissa bari kawai Hadda ne ban wani mayar da hankali na iya ba, shi ya sa ma ban je ba domin kuwa nasan yadda zata ƙare ni da Malam Mahmoud karon ba zai mana kyau ba."


Ta ƙarishe maganar tana dariya ita ma Arissa Dariya take yi domin kuwa sarai tasan Teema da irin show da ake kwasa tsakaninta da malamin ajin nasu wato Malam Mahmoud.



"Ki dage dai nasan baki manta muna gab da yin sauka ba ki daure ki mayar da hankali."


Arissa ta faɗa.


Teema ta amsa da. "Shikenan in sha Allah zan gwada."


"Sannun ku bayin Allah na barku zaune ina tuƙa tuwo ke Arissa zo ta nan ki tayani kawo ma baƙi tuwo miyar kuɓewa nasan dai ba zasu ƙi ci ba."


Amsawa Arissa tayi tana Miƙewa tsaye yayin da Samira ta bita da kallo Teema kuwa ta ɗauki Ruwan dake gabansu wanda shigowar su gidan Kakus ta kawo musu bayan sun ma ta Bayanin godiya suka zo yima wanda ya taimaki Samira godiya acewarsu, har take faɗa musu baya nan sannan ta ce su zauna susha ko ruwa ne sun kwaso tafiya shi ne ta shimfiɗa musu tabarma ba tare da gardama ba suka zauna.



"Anty Samira ga fa tuwo raɓa raɓa Allah ya sa kin san shi?."


Arissa ta faɗa lokacin da ta ƙari so wurin sannan ta a je kwano da tuwo ke ciki sai kuma wata roba daban miyar kuɓewa ɗanya yaji haɗi sai ƙamshi take fitarwa a ciki.


"Nasan shi mana sai dai ban taɓa ci ba, amma me yasa kika ce ko zan iya ci?."



Samira ta jefowa Arissa da ta zauna gefan su bayan ta a je musu tuwon tambayar tana kallon ta.


"Ah bakomai kawai saboda naji ance daga ƙasar waje kika zo ne shi ya sa."


Arissa ta bata amsa tana dariya.


"Allah Sarki ai Mommyna tana yiwa Daddyna domin yanaso sai dai ban taɓa ci ba ita kam tana ci sosai."


"Ikon Allah."


Arissa ta faɗa. Tana shirin sake magana Kakus ta riga ta da faɗin.


"Ku Dena biyewa wannan kuji tuwon ku kunji domin kam ita bata ci sam 'yar gayu ce na lura so take ta hanaku ci."


Samira da Teema suka yi Murmushi tuni Teema ta janyo kwanon tuwon gaban ta, Arissa da ta miƙa musu ruwa da roba da zasu wanke Hannu ta ce.


"HHhH Kakus shagali kishi kike dai banacin tuwo balle nayi saurin tsufa kina kishi kar ɗan mijin naki ya susuce."



Ta faɗa tana dariya.


"Ja'ira Kawai."


Cewar Kakus tana ɓallawa Arissa harara na wasa.


Samira ta yi Murmushi tana ganin Drama da ake kwasa tsakanin cutie ɗin da taji Teema ta kira da Arissa da kuma Dattijuwar da take da tabbacin Kakar Arissa ɗin ce.

"Anty Samira kici mana."


Cewar Arissa tana kallon yadda Samira ta zubawa kwanon tuwon ido tana kokwanton ci.


"Yanzu kam a ƙoshe nake amma nayi alƙawari idan na dawo next time zan zage naci na ƙoshi."


Suka yi dariya gaba ɗaya har da ita.
Suna ɗan taɓa fira sama sama da mafi yawa Arissa ce take yi da ita Kakus nata Samira Sai dai ta bisu da ido, yayin da Teema ta zage ta buɗe ciki taci tuwo ta ƙoshi domin kuwa ba ƙaramin daɗi ya yi ma ta ba dama tayi missing tuwon Kakus sosai domin rabon ta da gidan an kwana biyu.


Bayan Teema ta kammala ta wanke Hannu suka miƙe da niyyar tafiya suka yi musu sallama sannan suka fito domin tafiya.


Idanunta suna kallon ƙasa daidai lokacin da suka fito daga gidan taji ta yi karo da Mutum ga wani daddaɗan ƙamshi da ya ziyarce ilahirin ƙofofin hancinta.

Ta sauke ajiyar zuciya ɓoyayyiya tana ɗa go softly Blue eyes nata masu matuƙar shaining tare da ɗaukar hankali ta sauke su saman kyakyawar fuskarsa mai cike da tarin annuri da haiba, sam batayi tunanin da shi tayi karo ba sanadin haɗuwar da idanunsu suka yi ya haddasa ma ta jin Damm bugu da ƙirjin ta ya yi. Ta lura da yadda ya waro ido yana bin ta da kallon mamaki sai dai tayi mamaki jin bai ce da ita komai ba koda yake duba da yanayinsa na kamala kallon farko zaka masa ka fahimci baya daga cikin waɗan nan mutanen masu hayaniya balle kuma surutu, ta sauke ajiyar zuciya a karo na ba a dadi tare da faɗin.



"Barka dama kuwa kai nake nema."


Ta faɗa idanunta akan sa fuskarsa ta nuna tsantsan mamaki bata bari ya ce komai ba ta ci gaba da cewa.


"A wancan lokacin sanadin wannan gunguren da muka yi ƙafa ta ta gurɗe shi ne sanadin da nake riƙe da crutches yanzu kuma dama kai nayi ƙoƙarin ceta har hakan ta sameni saboda haka kai ne kake da alhakin kula dani har ƙafar tawa ta warke, abin nufi shi ne kaso hamsin na lokacin ka zai koma kana kula dani da su ne har ƙafa ta ta warke duk da Doctor ya ce ba daɗe zatayi sosai ba warke ba ina fata ba zaka min mummanar fahimta ba daga gobe Deal ɗin namu zai fara."


Shiru Taufan ya yi ya harɗe hannu bibbiyu a ƙirji cike da mamaki yake bin ta da kallo sai dai ya kasa furta komai tsaban al'ajabi.


Samira tayi Murmushi tare da yin gifgif da ido ta ce.


"Zan tafi gida yanzu Gobe mu haɗu anan misalin ƙarfe Biyar na marece zuwa lokacin nake so na ɗan yawata cikin garin nan kuma Kaga yadda ƙafata take saboda haka kaga sai mu tafi tare."


"Okay."


Ya tsinci kansa da faɗin hakan a gajarce.


Tayi Murmushi sannan ta riƙe hannun Teema suka yi gaba. Arissa dake tsaye gefe babu wanda yasan da wanzuwar ta a Wurin ta tuntsire da dariya da ya saka Taufan da ya yi nisa a Duniyar al'ajabin Samira ya juyo ya kalleta.


"Mene ne kuma kike ma Dariya?."

Ya tambaya yana ɓata fuska.


"A'a ba komai kawai dai mamaki nake yi yadda ka kasa koda magana ne a gaban Anty Samira sai ma amsa ma ta umarnin da kayi kamar yaro da uban gidan sa."

"Umarni kuma?."

Ya tambaya da mamaki.


"E mana Yayana haka nake nufi ai yadda Anty Samira tayi maganar kuma baka mata ja'inja ba kowa ya gani kai tsaye zai ce umarni ta baka."


"To kaska uwar surutu naji mu shiga daga ciki."


Ya faɗa tare da riƙe hannunta suka shiga cikin Gidan yana shafa stubble short hair style na fuskarsa.


*_Samira Sam kuwa_*


Suna tafe babu um bare um um har suka ƙari sa masarautar Raees a tafiyar da suke yi a ƙasa domin ba wani nisa ba ne na azo a gani tsakanin gidan su Arissa da masarautar. Aka buɗe musu gate suka shiga ciki suna gafda da shiga Apartment ɗin da aka warewa 'yan matan kuma suke zaune ita da Hamrarh da Amrarh da sauran 'yan matan dangin Raees a ciki ta dubi Teema ta ce.




"Mene ne abin da kika sani game da Arissa da Yayanta kuma mene ne sunansa. I mean Tarihin su kuma Kinga ai ban san sunan su ba."



Tayi maganar tana kallon Teema.



Teema tayi Shiru kamar mai nazari sannan ta ce.


"E, to abin da na sani dangane dasu dai kaɗan ne kuma Sanadin Arissa ce da muke Class ɗaya da ita a Tahfiz. Abin da na sani shi ne kuwa. Shi dai sunan sa Taufan Arissa tana kiransa da Yayana ita kuma kamar yadda kika sani Sunanta Arissa wasu suna kiranta da Cutie domin kyau da Ubangiji ya halicce ta da shi, Alhaji Muhammad Ali Nakowa da Matarsa Hajiya Sumayya da Arissa take kira da Kakus muma muka kama. Aamalah ita ce kaɗai 'ya a wurin Muhammad Ali Nakowa da Matarsa Sumayya. Yayin da Taufan da kuma Arissa suke 'ya 'ya a wurin ta magana dai jikokin Kakus da Alhaji Nakowa."



"Ikon Allah amma me yasa suke zaune tare da Kakannin su na wurin uwa kuma Mahaifin su fa da ita mahaifiyar tasu Aamalah?."

Samira ta tambaya cikin sauri.


"E, to abin da na sani dai shi ne Aamalah ta tafi ƙasar Egypt domin karatu na University bata dawo ba sai da yaro da kuma wasu Larabawa kuma sojoji ne wai tayi Aure a can ne kuma ta haihu shi ne a lokacin Alhaji Nakowa da Matarsa ransu ya yi mugun ɓaci na abin da Aamalah tayi Aure ba tare da ta sanar da kowa ba har suka ƙi kulata daga ƙarshe ma suka koreta. Daga nan ba'a sake jin labari akan ta ba. Sai shekara ɗaya

Please Login or Register in order to submit comment