Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*CAPTAIN KABEER*



*RUBUTAWA*


*HASSY SOJA ce*✍🏻


*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

```BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN```



*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA'DI*


*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎


*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

🅿️1️⃣%5️⃣


*________________*🖊️
Wata tsaleleyar budurwa ce kwan ce take tana kuka sosai kamar ranta zai fita ta rike mararta tana juye juye ta dafe marar ta da har ta fara fita hayancin ta.


Shigowar wata Hajiya ce ya sanya ta hankalin ta ya dawo gurinta tace "shalele na lfy klau kike kuwa meya ke damunki?.


Kuke take jikinta har rawa yake saboda azabar da take sha nuna mata take tana girgiza mata kai.


Da sauri ta karaso gurin tace tace "ko ciwon marar ne"!?.


Daga mata kai tayi tana kuka sosai kamar ranta zai fita.

Dauko waya tayi ta kira doctor sai gashi yazo yayi mata allura sannan yace "gaskiya Hajiya ya kamata ace kunyi mata Aure saboda irin wannan period yana bukatar Namiji kusa da ita.

Shiru tayi na dan wani lokaci sannan tace "to doctor insha Allah dama zamuyi magana da Alhaji idan ya dawo Nigeria insha Allah.


Jin jina kan sa yayi yayi gaba abun sa.


*America*

Wani soja ne zaune yana kallon ruwa Amman tunani yake ina zai sanya rayuwar sa ne wato Capital kabeer fari tass kamar balarane shi ba dogo ba kuma shi ba gajere ba babu abun da ya tsana duniya kamar tuwon dawa ko na shinkafa abun da yake so kamar shinkafa da wake da lemon juice da yanboll yana mutuwar son su kayan sanyawa kuwa black and fari da yellow da green.


Mota kuwa fara da black sosai yake hawansu bana son yawan surutu baya son kazanta baya son shishigi ko kadan.


Baya dariya ko murmshi ko dogon surutu sai mahaifiyar sa ita kawai ce ka ganin dariyar sa da surutun sa gashi sarkin shagwaba mahaifin sa ya rasu tun lokacin yana karamin sosai ya barmasu dukiya mai yawa sosai.

Babu abun da ya tsana duniya sama da Aure baya son maganar Aure ko kadan bayaa kula yan mata da yawa yan mata na son sa Amman be basu fuska ba .


Dafashi akayi sannan Abba yace"Captain kb lafiya Qlau kake kuwa"!?.


Ajiyar zuciya yayi sannan ya mik'e tsaye yana kallon gefen sa yace "ku shirya zamuje Nigeria yau ko da dare yayi sannan ya wuce office din sa.


Dama Abba ya san halin abokin sa baya magana da kowa koda shawara ce bayayi da shi ko fuska baya saki bale wata shawara.


Cikin mintin kadan suka gyara har jirgein Nigeria sun samu d'aya yazo ya fada masa lokacin ya gama hada kayan sa sannan yace "to duk abun da kuke bukata ku dauka saboda ba zamu dawo kasan ba sai muje wata kasa wuce wa yayi ba tare da ya kalle inda suke ba.


Cikin dan kankani lokaci suka shiga cikin jirgein Nigeria ahankali ahankali ya iso filin jirge sai da ya dauki mintina 30 sannan ya fito cikin ransa yace "Alhamdulillah nadawo k'asata.

Da gudu wani soja yazo Sir ana waya dago idanuwan sa yayi ya Mike masa hannu koda ya duba wayar sunan my life mom ya gani dan murmshi yayi sannan yace "Assalamu Alaikum my life mom.


Zaune take tana kallon tv falon kuwa kamshi turaren wuta yake murmshi tayi tace "Amin wa, Alaikum sallama Naam my son har kun iso kenan ko"!?.


Langwabe kansa yayi yace "Eh yanzun dai ina hanya ne zakije insha Allah.

Ta fahimci akwai masu kallon sa sai tayi murmshi tace "to Allah ya kawo mani kai lafiya sai ta kashe wayar ta.


Bude masa kofar motar akayi sannan ya shiga ciki ya Zauna yana kallon gefen sa driver ya shiga ya fara jan motar ahankali sai da ya kai bak'in titi sannan ya sharara gudu sai cikin Unguwar masu kudi mai cike da mutane dai dai wani hadaden gida ne yayi hon da sauri mai gadi yazo ya bude masu jin jina kan sa yayi yace "Alhamdulillah oga yadawo gari.


Sulalawa yayi cikin gidan dai dai lokacin yan aikin gidan suna tsaye shi kawai suke jiran fitowar sa Captain kb kuwa ya dauki tsawani mintina 30 Zaune cikin motar da sauri wani soja yazo ya bude masa kofar motar kafarsa ya fara saukowa.


Wow masha Allah Allah yayi halita gaskiya oga kb ya hadu sosai.


Fitowa yayi daga cikin motar kallon gidan yayi sannan ya sanya kai ya wuce cikin gidan.


Koda ya shiga falon kamshin turaren sa ne ya game falon shine ya tabbar mata da cewar d'anta yadawo jiyowa tayi tana murmshi.

Da gudu yazo ya rungume ta sosai yace "miss you my life mom.

Mommy tayi murmshi cikin jin dadi tace "miss You my son dafatan kadawo lafiya!? .


Kwantawa yayi saman kujera yace "to Alhamdulillah Amman dai na gaji sosai wallahi bari dai na watsa ruwa sannan.


"To madallah Allah yayi maka Albarka.

"Amin ya Allah"



A hankali ta fara bude idanuwanta kai masha Allah Allah yayi halita gaskiya wannan gurin kallon dakin take sannan tayi ajiyar zuciya tace "Allah na gode maka da kabani lafiya.

Hajiya tace "sannu ya jikin naki ne yanzun"!?.

Tashi Zaune tayi tace "Alhamdulillah naji sauki sosai.

Cikin tausayawa tace "yanzun babu wata matsalar komai dai ko"!?.


Daga mata kai tayi tana kallon sama Amman bata ce komai ba ajiyar zuciya tayi tace "Hajiyar mu anjima zanje gurin mommy na dan Allah..

Tabe baki tayi tana kallon ta sannan tace "salon Kabeeru yadawo ku kama fada ko"!?...


Cikin jin haushin sunan da ta fada tace "wai ke Hajiya ni ina ruwa na da shi ni fa gurin mommy zanje fa dan Allah ki daina hada ni da shi dan mugun ne wallahi...


Dariya Hajiya tayi tace "to Allah ya sauwaka yanzun dai daga ke har shi baku zaman lafiya!?...


Turo baki tayi tana kallon gefen ta ........



*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*



*CAPTAIN KABEER*



*RUBUTAWA*


*HASSY SOJA ce*✍🏻


*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

```BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN```



*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA'DI*


*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎


*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

🅿️1️⃣1️⃣%1️⃣5️⃣


*________________*🖊️
Turo baki tayi tana kallon gefen ta saboda haushi maganar take duk abun da take Hajiya na kallon ta sai tayi murmshin manya tace "to shalelen na adawo lafiya ki gaidan mani da mommyn ta ki.


Mik'ewa tsaye tayi sannan tace "amm kuma kice zan shigo insha Allah sannan ta fita daga cikin dakin tana mamakin irin halin su girgiza kanta tayi.


Tsalle tsalle take saman gado saboda da farin ciki da take ciki tunda Hajiya ta aminci to yanzun zataje gidan mommy dama tayi kewarta da sauri ta sauko daga saman gado Jakarta da mayafin ta dauko fitowa tayi daga cikin dakin doguwar riga ce tasari green ajikinta saukowa tayi daga saman bene Zaune ta iske Hajiya tana kallon sunnah tv kamshin turaren tane ya game falon shine ya tabbar mata da cewar khadeejah ta fito.


Karasowa gurin tayi tana Murmshi tace "Hajiya na shirya sai nadawo ko"!?.


Kallon ta tayi tace "shalele na kin dauko key dinki ne"!?.


Murmshi tayi tace "eh yana cikin Jakata ne mota green zan hawa kinji Hajiya"!?.


Kallona take tace "uhm to menene na tambaya na ai na kine ko tafi Allah ya tsare.


Amin ya Allah shiyasa nake kara sonki Hajiya ta sai nadawo bye bye da sauri fita daga cikin falon koda ta fito sai ta ga mai gadi ya gama goge motar ta kallon sa take sannan tace " Baba mai gadi har kagama ne"!?.


Washe baki yayi yace "wallahi kuwa y'ata Allah dai ya kaiki lafiya.


Dubu biyu ta Mike masa tace "to gashi kasai goro ko"?.

Amsa yayi yana sanya mata Albarka bude kofar motar tayi ta shiga ciki ta rufe sulalewa tayi da gudu tana fita daga cikin gidan sai ta kuna wa'kar Husaini danko.


Zazzaune suke cikin falon da mommy da baba mai aiki kallon ta mommy tayi tace "Amma hajara kin sani danki yadawo ne"!?.


Washe baki tayi tana kallon mommy tace " A'a yaushe yadawo kin san lokacin na tafi gida ne".


"Ok babu damuwa kin sani baya son hayani ne shiyasa.


Baba mai aiki tace "wallahi kuwa ai Allah dai ya bashi mata tagari.


Cikin jin dadi tace ""Amin ya Allah nagode sosai yanzun dai akwai kin gama aikin ne"!?.


Baba tace "eh Hajiya ai tunda zu na gama aiki na.


Horn tayi da gudu mai gadi yazo ya bude ganin hadadar mota green ya gani shigowa cikin gidan tayi dai dai kofar shiga cikin gidan tayi parking ma, aikanta gidanan kowa ya saki baki yana kallon yaga waye acikin motar shalelen kuwa sai da ta gama gyarawa sannan ta bude motar idanuwant sanye take da glass fitowa tayi daga cikin motar gaba d'aya kowa yace wow gaskiya gurin nan Allah yayi halita Allah yayi mata kyau sosai cikin ranta tace"o ni khadee to su wannan kallo haka sai kace tv girgiza kanta tayi tace "Allah ya kyauta.

Da gudu mai gadi yazo yace "A'a yar India yaushe kika dawo "!?.


Dariya maganar sa ta bata sai dai tayi murmshi tace "to wa ya fada maka tafiya nayi babu inda naji kaji sarkin tambaya.


Wuce tayi ta shiga cikin gida, cikin falon ta shigo lokacin Mommy tana magana da Baba kamshin turaren taji ya daki hanci su da sauri mommy suka jiyo kallon ta suke.


Cikin shagwaba tace "Uhm uhm uhm mommy na kin manta da ni ko"!?.


Dariya tayi sannan ta bude mata hannuwa tace "karaso mana Auta ta takaina.


Da gudu tazo ta rungume mommy tace "miss you my mom nayi kewarki sosai.


Ita ta kara rungume ta sosai tace "nima Kullum sai nace wai ina Auta ta tashiga ne".


Dariya Baba tayi tace "ikon Allah wannan soyayyar taku akwai ban sha,awa kuwa bari dai na tashi naje gida ko.


Tashi Zaune tayi tace "Alhamdulillah yau gani ga mommy na sai abun da nace nake so ko"!?.


Kwantar da ita tayi saman kafafuwan ta tana dariya tace "sosai ma kuwa sai abun da kike so Auta ya Hajiya dafatan dai kuna lafiya da ko"!?.


Gyara kwanciya tayi tace " wallahi nayi ciwo kwana biyu mommy ko magana bana iyayi.


Cikin damuwa sosai tace "har yanzun ciwon marar ne"!?.


Daga mata kai tayi ta lumshe idanuwanta.


Kamshin turaren sa ne ya game falon shine ya tabbar mata da cewar ya fito dagowa tayi tana murmshi tace " Aa my son har ka fito kenan"!?.


Gaban ta yace rasss wani irin tsoro ne da tashin hankali tashige ta rufe idanuwanta tayi Amman tana jin muryar sa.


Be ma kula da wata kwan ce ba yace "washiii na gaji sosai wallahi my love mom aiki akwai wahala sosai fa.

Cikin kulawa tace " ayyah sorry my son ai dole akwai gajiya sosai.


Motsi yake ji kusa da shi da sauri ya duba ya ganin sai yaga mutum kwan ce saman kafafuwan mommy zaro manya manya idanuwan sa yayi yace "keeeeeee cikin tsawa.


Tashi Zaune tayi tana masa kallon tsana yatsane fuska tayi.


Mommy tace "A'a my son daga zuwan yarinya sai taya mata da hankali "!?.


Cikin bacin rai yace "Haba my love mom ya zaki bari wannan kazamar yarinya nan ta kwanata saman kafafuwan ki saboda rainin hankali"!?.


Murguda masa baki tayi tace "to sannu sarkin tsafta kaji ni fa wallahi bana son shishigi fa.


Girgiza kanta mommy tayi tace "Auta ta ina zuwa Mik'ewa tsaye ta ta wuce ciki Captain kb da khadeejah kallon tsana suke ma junan su.


Bayan minta gama shabiyar Mik'ewa tsaye tayi sannan zata wuce yace "keeeee baki iya gaisuwa bane"!?.


Dariya maganar sa taba tace "Allah ko kai ko kunya bakaji ba mtsss ni ko mutum ban gani ba bale kace wai ban gaida kai ba.


Wata irin tsawa ya daka mata idanuwan sa sukayi jajaru yace "ni sa,an ki ne da zaki fada masa magana son ranki"!?.


Ta tsorota sosai Amman sai ta dake tace " nayi din ina ruwanka da ni ne daga zuwa na zaka fara mani matsifa mtsss wuce wa tayi part din mommy.


Mutuwar tsaye yayi yana tunani kalar rainin da tayi masa cikin zafin rai yace" yasin Sai na dauki mataki akanki............



*HASSY SOJA CE*✍🏻✍🏻

*COMMENT AND SHARE*



*CAPTAIN KABEER*



*RUBUTAWA*


*HASSY SOJA ce*✍🏻


*MAMA NA DA BABA NA ALLAH YA JIKANKU DA RAHAMA YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKU AMIN YA RABBI*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

```BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI GODIYA DA AMINCI SU TABBA GA ANNABI MUHAMMAD S. A. W ALLAH YA KARA MASA DARAJA AMIN```



*WANNAN LABARIN NAWA GAJERAN LABARI NE*😀😀😀😀😀😀

*WANNAN NOVEL DIN BA NA KUDI BANE RASHIN COMMENT ZAI SANYA YA KOMA NA KUDI YASIN*

*GARGA'DI*


*BAN YARDA WANI KO WATA YA SU JUYA MANI LABARI BA SAI DA IZINI NA YIN HAKA KUSKURE NE DAN HAKA SAI AKIYA YI*😎😎😎😎


*SADAUKAWAR GA MASOYANA AKO INA KUKE AFADIN NIGERIA WANNAN NAKU NE*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

🅿️1️⃣6️⃣%2️⃣0️⃣


*________________*🖊️

Mutuwar tsaye yayi yana tunani kalar rainin da tayi masa cikin zafin rai yace "yasin Sai na dauki mataki akanki Zaunawa yayi saman kujera Amman ya kasa natsuwa Mik'ewa tsaye yayi ya fita daga cikin falon.


Khadeejah kuwa koda tashi cikin dakin bata ga mommy motsin ruwa tajiya shi ya tabbar mata da tana toilet Zaunawa saman bakin gado tayi tana tunani cikin ranta tace"o ni khadee to wai meyasa duk lokaci da nazo gurin mommy sai na hadu da wannan mugun mutum himm yasin ba zan dauki wula'kanci ba,


Fitowa mommy tayi cikin toilet tana goge ruwan wanka sannan tayi ajiyar zuciya tace "Auta ta lafiya kikazo kikayi Zaune ke d'aya ina dan uwanki ne"!?.


Dagowa tayi tana kallon mommy wasu abubuwan suna mata yawo acikin zuciyar ta tace "ya fita ne.


Murmshin manya tayi tace "ko kin san bana son kuna fada ko"!?


Shiru shalele tayi saboda haushi yake bata bata ce komai ba Amman azuciyar ta tace "yasin duk abun da yayi mani sai na rama.


Shiru yayi yawa sai ta dafata tace "Auta ta lafiya Qlau kike kuwa"!?.


Murmshi tayi tace "lafiya Qlau mommy na ina tunani wani abu ne shiyasa.


Bata ce komai ba ta dauko turare ta feshe jikinta da shi tace "Amman daddyn ki yadawo ne"!?.


Kwanta saman gado tayi tace "A'a ina tunani sai wani sati zai dawo.


"Ok babu damuwa bari na barki kiyi bacci ko"!?.


Shalele tace "to mommy na" rufe idanuwanta tayi ahankali ahankali har bacci yayi gaba da ita.


Fitowa mommy tayi falon sai bata ga captain kb ba zama tayi saman kujera tace "to ko ina ya shiga ne oho" kallon tv take.


Captain kb ne Zaune bariki yana aiki Amman hankalin sa na ga tunani irin matakin da zai dauka akan khadee shiru yayi sai ya cire wayar sa ya kira mommy lokacin kuwa tana lazumi ne ringing din wayar ta taji ya sai ta duba sunan my son ta gani dauka tayi tace "my son lafiya tunda zu baka dawo gida ba"!?.


Ajiyar zuciya yayi yace "ki kwantar da hankalin ki my love mom ina gurin aiki ne".


Ajiyar zuciya tayi tace "sai yanzun hankalina ya kwanta fa to kadawo gida kaci abinci.


Yatsane fuska yayi sannan yace "abinci kuma ni fa bana cin kazantar yarinyar nan fa".


Mamaki da al,jabi ya rufe ta tace "my son gidan ku wai kai yaushe zakayi hankali ne kanwar ka ce fa".


Shiru na dan wani lokaci sannan yace "to shike nan my love mom zan dawo Amman zuwa anjima.


Murmshi tayi tace "yauwa dan albarka sai kazo.


Kashe wayar tayi tana mamakin irin halin su girgiza kanta ta cigaba lazumi lokacin sallah la,asar yayi tashi tayi ta shiga cikin dakin ta tashe da khadeejah sai ta sameta Zaune tana lazumi sallama tayi tace "au ashe ma har kintashi"!?.


Shafa addu,a tayi sannan tace "ai tunda zu na tashi daga bacci mommy".


Murmshi tayi tace " to shike nan babu damuwa dama zuwa nayi nagani ko kintashi baccin.


Murmshi tayi tace "na tashi tunda zu yauwa kuma Hajiya tace tana gaishe da ke zan koma gida yanzun saboda gobe muna da lechers insha Allah".


Mommy bata ji dadin maganar ba taso ta kwana anan sai tace "haba dai Auta ta bazaki bar sai gobe ki tafi gida ba kin sani inason ki zauna atare da ni fa".


Ita ma bata ji dadi ba tace "am sorry mommy na insha Allah zan dawo na kwana biyu atare da ke kinji ko"!?.


Ajiyar zuciya tayi sannan tace " to Allah ya kaimu lokacin lafiya.


"Amin ya Allah ina tunani ko zuwa jibi ko gobe zan dawo kinji kada ki damu dan Allah cewar khadeejah tana kallon ta"


Murmshi tayi tace "babu damuwa Allah ya kaimu yanzun tashi muje sai ki hada kayan marmari sai ki tafi da su ko"!?



Dariya shalele tayi tace "mommy na kenan ki bar su zan dawo na ci abu kawai.


Mik'ewa tsaye tayi sannan suka fito daga cikin dakin koda suka fito waje dai dai gurin motar ta ta tsaye sai ga Captain kb ya shigo cikin gidan lokaci mommy na tsaye tana magana da khadeejah parking yayi sannan ya fito hango khadeejah yayi tana kokarin shiga cikin motar ta daure fuska yayi kamar be taba dariya ba karaso gurin mommy yayi yace "my love mom lafiya kikayi tsaye nan gurin"!?.


Baki ta saki tana kallon sa sannan tace "my son baka ga kanwarka zata wuce gida ba "!?.


Yatsine fuska yayi yace "my love mom kin san abubuwa sun mani yawa sosai ne shiyasa ban kula da ita ba".


Jiyowa tayi suka hada ido ta watsa masa harara sannan tace " Mommy na sai nadawo sannan tashiga cikin motar ta rufe mai gadi yazo ya bude mata fita tayi daga cikin gidan.


Bayan ta fita daga cikin gidan sai mommy ta jiyo tana kallon sa tace "my son wallahi abun da kukeyi bashi da kyau sosai fa dan Allah ku gyara zaman ku please.


Captain kb yace "o, o my love mom kin san halin yarinyar nan bata jin magana ne Amman zamu gyara insha Allah acikin zuciyar sa kuwa yace "sai na koya mata hankali kuwa afili kuwa sai yayi mata murmshi.



Mommy ta shiga gaba sannan ya tsaya wayar sa ce ya cire ya kira wani yace "kana jina yanzun nan ta fito daga cikin gidan fa ku shirya.



Kamar suna gaban sa yace "to sir shirye muke.


Gudu take shararawa sai ta hango mutum kwan ce saman titi da sauri tayi parking tace "to wannan bawan Allah lafiya ko ya mutu ne"!? Waya dauko ta kira Hajiya ta fada mata sannan ta kashe wayar ta.


Fitowa tayi sai ta duba ko ina babu mutane tace "ko lafiya babu mutanen da zasu taimaka masa karaso gurin tayi tana kallon sa cikin tausayawa tace "sannu bawan Allah bari na kira doctor ta dauko waya kenan ta jiya sai ta gani mutane sun zagayeta sai dariya mugunta suke mata tana kallon gabanta tayi sai taga mutum tsaye yana dariya gabanta yace rasss wani irin tsoro da tashin hankali sunka bayana a fuskar ta baki na rawa tace "dan Allah ku su waye daga ina cikin tashin hankali take tambayar su"!?.


D'aya daga cikin su ya hada ido da yan uwan sa da sauri yazo ya shaka mata kokin sulalewa tayi kasa da gudu suka tura ta cikin mota suka gudu da ita.


Mommy na Zaunawa saman kujera taji gabanta yace rasss wani irin tashin hankali tazo mata da sauri tace "my son kira mani Auta ta yazon dan Allah please.


Kallon ta yake sannan yace "my love mom lafiya kike kuwa yanzun fa ta fita daga cikin gidan fa".


Kai dan ubanka ka kira mani ita yasin akwai matsala sosai.


Hankalin sa ya tashi sosai be taba jin mommy ta zage sa ba sai yanzun wayar sa ya dauko yace "my love mom bani da number ta bani wayarki.


Da sauri ta mik'e masa ya kira ta yana jin tana ringing bata dauka ba kallon mommy yayi yace "bata dauka ba.


Mommy tace " *innalillahi wa inna

Please Login or Register in order to submit comment