Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din nan dariya kake bani,Naila tace ke Chikar gayu da munafunci,to Kuma mu ai kowa kallonsa muke tsaf, ko zaren dinkin shaddar mutum ma sai mun kalla.

Palo suka koma ta zauna Chikar gayu taje ta dafa shayinta na Wiwi ta dawo da abinta a cup,Naila tace shedan yau aiki zaibi ta kanka Chikar gayu kiyi Bismillah kafin Kisha shayin Wiwi din nan tunda shedan komai za aci sai yazo ya tsoma baki, Maza ki Masa bakin ciki kar ya Sha miki dadi,Chikar gayu tayi Bismillah ta fara kurba tace ai da ta hayakin nake Sha bazan Bismillah ba zan fara zuka sabo da shima shedan ya zooka ya shake a makoshi.

Chika tana zuka Naila ta kwace ta hankade keyar Chikar gayu tace ke a gidan yarin har wiwi kika koyo sha? Da Allah ku dinga sanin abin kwaikwayo,mene wani Wiwi kina mace dan Allah ki bari ki gama min aiki na lafiya idan yaso daga baya ai Kya Sha abarki,taje ta zubar,Abinci suka ci sannan suka kwanta suna hutawa.
Zuwa dare Sheyi ta Dora girki ta kira Naila tazo ta koya Naila ta shugo kitchen,tukunyar ta leka tace yawwa ai na gane wannan girkin miyar Egusi ce ko zamu yi,yawwa Sheyi idan kika wanke namanki sai ki watsa a tukunya Yana tafarfasa Yana zabalbala sai ki yanka albasa Sheyi ki barbada curry da Maggi,Maggi ki samu me karfi yanda zai bada dandano,ki dakko manjanki idan ya daskare ma ba matsala duk daya Sheyi.....Sheyi ce ta tadakatar da Naila tace ni nake koya miki ne ko ke kike koya min? Naila tace kece mana ai practical nake,Sheyi tace ki tsaya ki koyi Abu idan kinki ke zaki ji kunya a gidan miji,Naila tace Allah ba yasa ba bakinki ya biki, yanzu na tsaya nuna min,Ehem haka zaki ce Yan mata,Sheyi ta shiga koyawa Naila girki har suka gama tare Naila ta gane yanda zata yin miyar da tuwo ko Sakwara ko Amala etc.

Chikar gayu tana Palo tana kallon tashar wakokin Nija,a haka Naila ta dawo ta sameta ta zauna tare da yin shuru ta lumshe Ido tana Jin wakar tace na Lula tunanin Spark gamu can mun fito daga mota mun shiga shopping mall Yana rike da hannuna,gamu can na rakashi Office...muna soyewa a cikin Office,ya dannawa kofar key, yasa key Chikar gayu,gamu can ya kaini awon ciki asibiti mum fito a hadaddiyar mota,ya tafi dani aikin hajji,Gani ga ka'abah,daga can mun wuce America,laaaa snow.....na haihu a can mace na samu,Chikar gayu tana kallonta ta rufe Ido wai tunani take yi,daga Jin kida sai haihuwa Kuma,Naila tace baza ki gane ba,ni nasan me nake ji na rashin Spark Ina zan ganshi?

Ranar haka suka kwana Naila tana zancen Spark Ina zata ganshi,washe gari bayan sunyi Kari me kyau Chikar gayu ta dakko kayanta kodaddu jemammiyar atamfa riga da zani dinkin me Fadi ta saka tayi daurin zani me Bakin almakashi gefe ya zobe baya a dangale ta daura dankwali dan kanti, ta fito da kullin kayanta a leda viva ta rungume a kasan hannunta,tace to matar Spark kira Hajiya Tagwadas,Naila tace ai sai ta gane Kuma na fito a gidan yari.

Nari kiji ta jawo wayarta ta kira Mohsin ya daga tana jinsa suna fada da Hanan ita magungunan basa yi ciwonta yaki warkewa ya maidata asibiti,Naila tace kaga kyale wannan banzar ka kira Hajiya Tagwadas kawar Umma kace address din gidan Mima kake so sun kiraka Abuja akan case Dina,Mohsin yace to ya kashe ya kira wayar Hajiya Tagwadas,tace Dana Mohsin Allah ya Maka albarka Dana Mohsin,Kuma gashi har yanzu naga Hanan taki ta sake haihuwa ko planning take ne?,Mohsin yace kaji gulma a ransa,a fili yace uhm Allah ne bai kawo ba,to Mohsin ko aure zaka Kara? Mohsin yace haka nace miki? a'a wai dama akwai wata ne da nake Maka sha'awarta a makwaftanmu Iklima yarinya me hankali,bana sonta komai hankalinta Mohsin ya furta yace address zaki bani please zanje Abuja an Gayyace ni akan case din Naila ance naje gidan Mima,gidan Ahmad Maleek,Hajiya Tagwadas tace to bari na turo Maka a rubuce ai yafi Mohsin Dan Albarka,yace Ina jira na gode.

Mintuna kadan ta tura Masa a rubuce shi Kuma yayiwa Naila forwarding,Nan take ta mikawa Chikar gayu tare da kudi 3k tace ko me kika gani ki kirani,Kinga maganin nan dana baki ki tabbatar idan kika ji Ashraf zaizo gidan to kisa Masa a abinci yaci shike nan Hallare Kuma sai idan ni naga dama na tashe ta,Chikar gayu tace an gama zanci uban kowa,Naila tace kiyi ba komai yi nane ni na saki a kotu harda wani zuwa suna Jin sharia suna kallo aka daure ni,Allah ya tsare.

Chikar gayu ficewa tayi daga gidan ta shiga taxi tabi address har kofar gidan Mima,aka sauketa taje tayi knocking,kofar aka bude ko Ina sojoji ne a gidan suna muzurai suna zare Ido,Chikar gayu ko jikinta tace da Allah yanlabai Wajen Mima aka turo ni,mutum daya ciki yace bari ayi mata magana aji, ya wuce ciki ya Samu Mima a Palo ta hakimce,yaranta duk basa nan sai Misam da ya dawo jiya daga Barikin sojoji, Yana zaune ya harde kafafuwa Yana kallo ba Wanda ke wa daya magana tsakanin Mima da Misam,Misam wani karkada kafa yake irin Wanda Jin dadi ya ratsa shi, fuskar nan a hade Yana ta fushi da alama fada suka yi da Mima,sojan ne ya shigo yace Ma kinyi bakuwa daga kauye tace turota akayi,Mima ta yatsina fuska tace Kai masifa wai ba anyi zakka ba an Kai, me suke nema Kuma?
Kai kasar Nan tamu akwai masu matacciyar zuciya,let her in,ya fita ya koma,Misam yace Yan uwanku ne dai,au Kai banda Kai? Yace a'a Banda ni wlh na sansu ne,Kai fa baka da mutunci kaima,shuru yayi sai ga sojan ya dawo tare da Chikar gayu,Chikar Gayu tayi sallama tare da zubewa a gaban Mima ta kwashi gaisuwa,Mima ta amsa tana wani cin magani

Meke tafe Dake waye ya turo ki? Chikar gayu wacce babu digon tsoro a fuskarta tace Hajiya Tagwadas ce tace kina neman Yar aiki Dan Allah Hajiya kiwa Allah ki bani ko me wanke kashin yara ce,ke ko naki ma zan iya wankewa,Da sauri Misam ya rufe baki Yana dariya kasa kasa,sai dai ki wanke na uwarki cewar Mima,Chikar gayu tace Allah ya huci zuciyarki tuba nake sarauniyar dattawan Abuja,Misam ya sake rike dariyarsa da kyar Yana kulle bakinsa da hannu,mikewa yayi ya shiga kitchen ya saki dariyarsa ya dinga dariya Mima tana jinsa taga abinda yake yi,sai da ya gama ya maze ya fito harda daure fuska ya sake zama.

Mima tace zan daukeki kinci darajar mutanen kauyenmu suna da alheri, amma sai dai ki shiga cikin masu girki,Chikar gayu tace na gode Allah ya Kara girma dama Babana ya sa min albarka, shi yasa duk Inda naje ko badan Allah ba sai an amsheni hannu bibiyu,Misam yayi sauri ya dauke Kai zaiyi dariya,Mima tace zan koreki wlh wai wacce irin yarinya ce ne ke? Ko Yar kunya ta mutam kauye babu idonki a soye,Chikar gayu tace sorry Mima Tsohuwar Yar Wiwi ce ni yanzu Allah ya shiryeni to chajin ne bai gama sakina ba,karki damu na daina yanzu a hankali zata sakeni,shi yasa na fito neman na kaina,Misam Yana ta dariya ya dauki magazine tare da kare fuskarsa wai kar Mima ta ganshi,tasan me yake yi jaridar ta fisge ta kwala Masa a jikinsa tace tashi ka tafi gidan uwarka, Chikar gayu tana zaune tana satar kallon Misam wani kyakyawa da shi hadadden gaske sai kamshi yake, shi Kuma ko kallonta ma baiyi ba,Chikar gayu tace Masa Ina Kwana? Yana kwano ya furta ba tare da ya ko kalleta ba ya mike ya fice abinsa,Chikar gayu da sauri ta bude ledarta ta dakko biro da Dan littafi ta shigar da sunan Misam ciki ma'ana ta rubuta a gaba tace tarbiyya dole Kaine zaka fara karbanta.
Mima kallonta tayi tare da Jan tsaki ta mike tace kice a nuna miki wajen Yan aiki ki koma can,Chikar gayu ta sake rubuta Mima a littafinta,Bata tashi a wajen ba Yan gidan suna ta shugowa daya bayan daya ba Wanda ma ya kalleta,ita Kuma sai aikin rubutu take.

Naila kuwa Beauty ta kira tace motarfa? tace bari a kira Daddy ya turo driver ya dinga koya miki Kinga ai zaki San gari sannan ki fara zuba wanka.
Naila tace an gama,a ranar kuwa driver yazo ya fara zaga garin abuja da ita Yana koya mata sosai,Naila sai murza kan mota akeyi kamar ta Ubanta,ko wanne namiji ta gani sai ta kalle shi tace to ko Spark ne wancen oho.

Spark kuwa an taho zance wajen Jamilu,Yana sauka drop motar airport ya dauka zuwa gidan yari,Yana zuwa ma'aikata suka dinga murna suna tarbarsa,suka gaisa tare da tambaya oga ya akayi ne wajen wa kazo? Yace Jamilu Tantiriya nayi mantuwa ne a hannunsa,ma'aikatan suka ce tab ai kuwa Jamilu baya gidan Nan ya gudu rannan baka ga abinda ya faru a labarai ba ai yana daga cikin Wanda suka gudu,kuma mun samun labarin ta gudu wlh an duba file dinta ko sama ko kasa an rasa shi so muke aje gidansu a nemota amma abin ya fassakara,ga wani mummunan laifi data yi wai Ashe Jamilu macece,haba ana fada nace biri yayi kama da mutum, dukkan ma'aikata mamaki suke yi Jamilu ashe macece,Yan gidan yari Maza basa so a fada amma ta riga ta furta da kanta sanda zata bar gidan yari a kunnen wasu ma'aikatan ta furta,yanzu baka San kowa na Jamilu ba? Spark yace Innalillahi wa innailayhirrajun,sai da ya maimaita sau uku yace yanzu Ina zanga Jamilu,na gama sanin nine nan zan taimaki Jamilu ya fita,kash wannan taurin Kai da me yayi kama,sai kaje yanlabai ka ajiye mana number Dinka idan an sameta sai mu kiraka,Spark ko magana baiyi ba ya Bada number ya basu kudi yace duk Inda Jamilu yake a Nemo shi,suka ce ya zama dole ai kotu za a koma a Nan za a bibiyi Inda dangi suke,Spark yasan Naila baza ta kamu ba Kuma baya fata a sake kamata ma, jiki a sanyaye ya juya tare da shiga mota sai airport ransa a mugun bace idonsa yayi ja sabo da bacin rai,Naila sai yau ta taba nata Masa rai a rayuwa,a cikin jirgi sai huci yake shi kadai kowa ya kulashi sai masifa,yace wlh dole sai na aureta ashe dama ba Sona take ba ohhhh ya ja tsaki tare da dafe Kai haka ya dawo Abuja,gidansa ya wuce direct ya kulle kansa a daki Yana ta faman bakin ciki wayoyinsa ma kashe su yayi gaba daya har tsawon kwana uku,Naila ita kanta tunanin Spark take har ta kwashe kwana uku a Abuja Chikar gayu ana gidan Mima ta rasa ma ta hanyar da zata yi maganinsa sabo da su basa ko bi ta kanta,Naila tana kwance a gida,Chikar gayu ta kira waya tace ke naji wata a gidan yau tace Ashraf zaizo,Naila tace yawwa ki shirya ki sa Masa tace angama,sai da aka gama girki tas sai ta dawo kitchen din Mima ta buya,bata Dade ba spark ya shugo duk ya fita a hayyacinsa,sama ya hau wiurin Mima,Yana shiga Mima tace ya na ganka haka kamar baka da nutsuwa? Kamar baka samun bacci ma lafiya Spark? fuska a hade yace ni dama tambaya ce ta kawoni,Mima tace to Dan Jarfa ko gaisuwar ma babu? Yace ni tambaya nazo yi amma dai Ina Kwana? tace lfy Alhmdllh Ina jinka,yace da karfe nawa kika haifeni? da rana,ko dare ko safe? Mima tace menene? Nifa kawai tambayarki nayi please,Mima tace da safe na haifeka Kuma ranar juma'a yace to ya aka yi bani da albarka an haifeni ranar juma'atu babbar rana da safe Bada duhun dare ba Kuma ace ni komai nayi bazai tafi dai dai ba a soyayya,Mima ta kalleshi tace Allah ya shiryeka,yace Ameen a haihuwata kuwa an samu alheri anya? Kuma kin samu kayan barka?dariya Mima tayi tace to haihuwarka tafi ta kowa wallahi Nasha kyautar da har na mutu bazan manta ba,Baki Spark ya tabe yace uhm bada zuciya daya suka bayar ba to,duk yanda akayi cikin biyu akwai Daya ko dai an sa min kayan Haram a jikina ko an ci Dani da Haram ko Kuma ba a yanka min ragon suna ba,idan kuwa anyi min hakika an yanka rago to ragon Nan na sata ne aka siya ba a sani ba,wani ne ya sato ya siyar muku a kasuwa aka yanka min,amma in ba haka ba taya za ayi Jimiluta ta gudu ai na tabbatar tana Sona ta ya za ayi haka,gaskiya Ku bincika ko Kuma Papa gaskiya ya manta baiyi addua ba a daren....Mima ce tace baka da hankali Spark,Ashe ta tabbata namijin kake so da gaske oh ni dai na shiga uku da wannan jarabawar rayuwa,Spark yace ai taki jarabawar kadan ce Mima idan aka hada da tawa ya furta a sanyaye yace ku kunci duniyarku da tsinke mu kuwa har yanzu rako muka yo.

Kullum sai nayi zazzabin dare, Mima tace ba dole ba tunda kaki aure ai dole kayi zazzabin dare abinda ma yafi zazzabi zaka yi tunda ba mace,Spark yace Kai Mima a dinga sakayawa karki Ganni yaro nasan komai,tace uhm naga alama ai muje to wlh yau sai Kaci abinci a gidan nan ko naci ubanka,yace uhm Mima a daina kalamai haka a gaban yara,kawai Mima ta kalle shi yanda ya juya mata magana Kuma kamar ba shi ya fada ba sai ya fuske abinsa,haka suka fito ta taso keyarsa gaba,tace Dan Allah kayi sauri wannan uban gadarar taka ni bazan iya ba.

Chikar gayu ta kwalawa kira wai Chika...Chika...tana boye a kitchen tace gashi Nan a dining ya fara dashi kafin na fito,a ranta tace Allah ka bani sa'a a kansa yaci, ta zubo abinci me Dan ruwa ruwa ta zuba magani ta kawo dining ta koma kitchen ta buya,Spark sai gashi sun fito da Mima tana cewa muje muje Kaci abinci wlh ko naci mutuncinka,Spark ba yanda zaiyi yazo ya zauna Mima tace ga wani nan ma dauki Kaci ai kana son dankalin turawa gashi Nan yasha hadi,Spark badan ya so ba yaja plate gabansa ya fara antaya girki a cikinsa,yaji ya masa dadi ya cinye tas yace a karo,Mima taji dadi ta kwalawa Chikar Gayu kira Chika fito ki karowa Dana abinci, Chikar gayu a ranta tace sai kace wani yace dansa ne wai Danta,bari dai naje naga uban waye Ashraf din ne, ta fito tazo gaban Mima,Spark ne ya dago a hankali ya Kalli Chikar gayu itama ta kalle shi,yace ke ba kece ta prison ba? Tace ae nice ba dai Kaine Ashraf ba? Spark yace nine mana Ashraf amma amfi sanina da Spark,Chikar gayu nan take ta fara hada zufa tace a ranta Naila ta kashe Halleren mijinta ta shiga uku,a gigice taje ta karo Masa ta same su Yana bawa Mimi labarin Chikar gayu yanda ya fitar da ita,daga Nan sai taji tana kaunar Chikar gayu,a ranta tace dama ita na aura Maka ba komai bari na tambayeta naji.

Chikar gayu Kuma da gudu ta fece daki ta kulle sannan ta kira Naila tana dagawa tace aiki ya Baci.
Me ya faru ashe Ashraf shine Spark,Naila tace ban gane ba,wlh Ashraf din shine Spark Wanda kika ce na sawa magani Kuma na saka ya cinye,kizo kofar gidan idan ya fito ki ganshi da idonki,Naila tace gani Nan,motar su Beauty ta dauka hannunta ko kwari baiyi ba haka taje har kofar gidan Mima,tana zuwa tayi parking a baya can ta tsaya,sai ga Spark kuwa ya fito driver na jiranshi a waje da mota,gaba daya tunda yaci abincin yake Jin Hallere dinsa tayi kwanciyar mutuwa,shi dai yasan a mike yazo gidan Mima da abarsa managarciya ,haka dai ya shiga mota a gaban Naila,suna tafiya Naila ta kira Chikar gayu tace fito Dan uwarki fito waje Ina jiranki.

Chikar gayu tace gani Nan ta fito,Naila ta fito daga mota tace Amma Chikar gayu ke ba karamar matsiyaciya bace mutumin Nan Kinsan saurayinane zan aura kika kashe min Hallare yanzu Bado shike nan bashi da Besty, wayyo na shiga uku,,Yar iska mahaukaciya baki da hankali baza ki leko Kiga waye Ashraf ba sai ki sa Masa magani,Chikar gayu tace ah haka fa kika umarceni dama duk marar hakuri da son ramuwar gayya ai Yana tare da haka

Naila hannaye ta Dora a kai tace Ina mafita Hallare ta shiga jalala dole fa sai na sake Masa magani wannan Kuma sai na ganta da idona,Chikar gayu tayi dariya tace ah ai a dadinkinki ke da kanki zaki shafa mata maganin ko kuwa? tsaki Naila taja ta shiga mota tana furta ta kwabe ba kanta na kashe kaina,sai ta fisgi mota kamar wata gwana tana cewa na kan hanya ya matsa ko azumi sittin ya hau kaina yau.

Hawaye ta fara tun a mota tana Tausayin Spark dinta ta manta ma da shine fa Ashraf,motar tasa tabi sosai Allah yasa ta hango su ya dauki hanyar gidan Mummy duk da ba wani gane hanyoyi take ba sai da tambaya take iya zuwa waje,gida ta koma a hanyar gidan ma sai data bata,tana komawa kaya ta canja ta zuba sabuwar shaddarta me tsada a gurguje ta saka hular gashi me kyau dogon gashi ta daure da ribbon kamar nata ya zubo kadan a gefen fuska ta shafa powder da jambaki pink dama shaddar pink tayi kyau duguwar riga me aljihu ta Sha dinkin zamani ta dauki takalmi da jakarta silver ta yafa mayafi ta fito tare da Maka glass dinta a fuska ba karamin kyau tayi ba babu Wanda zaice Naila Jamilu ce zaka rantse Yar gidan wani ce,Mota ta shiga da sauri tayi hanyar gidan Mummy ko zata ga Spark a can da kyar ta gane gidan, Parking tayi a waje ta fito tare da yin knocking aka bude,suna Ganinta kamar Yar me kudi sunga tazo Kuma da mota tana karkada key sai masu gadi suka bude mata ana cewa sannu da zuwa Hajiya,Naila hannu kawai ta daga musu ta wuce ciki tana Izza tana karkada key.

Palon Mummy ta wuce direct taji Muryar Spark Yana cewa Dan Allah ku kyaleni naji da abinda ya dameni,budurwata ta bace na rasa Inda zan sa kaina amma ke da Mima sai zancen wani aure kuke min idan so kuke na bar duniyar ba sai na mutu ba kawai wannan wacce irin rayuwa ce,ko Dan halinku ma wlh a Hana mutum aure,ni nasan halinku ne ke biniyata,Mummy tace nayi shuru tunda Kai sunna ce baka so ka raya,yace sanda zan raya sunnar Kun ma sani ne ni ku rabu dani Dan Allah, wlh in na gaji zan bar muku kasar,To ubanmu cewar Mummy.

Naila ce ta makale Murya ta koma ta Yan gayu masu yanga tayi sallama a hankali,Mummy tace shugo ta zaci kawayenta ne sai taga wata Yar Gayun,Mummy tace wannan ko Yar film ce ne sai naga kamar na Santa,gaskiya sai dai idan a film nake Ganinta,Baki ta washe tace shugo mana Baby,Naila ta shiga tana kallon Spark da yaki dago Kai ya kalleta kawai waya yake dannawa,ji take kamar ta fada kansa ta cinye shi tayi missing dinsa matuka,wuri ta samu ta zauna,sannan tace Ina yini ta gaida Mummy da ladabi,mummy ta amsa tana ta wani fara'a tace kamar na sanki a wani film, Naila tace Ohhh Ashe kin gane ni tabbas nice cikin wani film YANKAN KAUNA ko? Mummy tace wlh na manta sunan dai ni dai nasan tabbas na taba ganinki a film,Murmushi Naila tayi kadan tace ae tabbas ai sunana Nasiba Yankan kauna Dake a film din nayi tashe duk da cewa nayi films da yawa,Mummy tace ikon Allah kice duk su Alihu kin sansu? Naila tace laaaa ai yau ma aikinsa zamu fita wani film dama location muke nema me kyau to sai muka ga gidan Nan yayi mana to shi yasa nazo neman izini ko kudi ne zamu biya,Mummy sarkin son wayayyu tace nooo ba sai Kun biya ba kuzo ku fara idan ma zaku dinga kwana ba matsala,Naila tace watarana dai ni zan dinga zuwa Ina Kwana kafin a fara film din sabo da na gaji da zama a hotel sai a dinga ganinka kamar baka da mutunci da kima.

Mummy tace ba damuwa idan da wasu duk ku taho akwai abinci da komai baku da matsala.Naila harda zamewa daga kujura tace mun gode Umma,Ai mummy ake ce min Umma ai sai Yan gargajiya cewar Mummy,Naila tace gaskiya fa sai local mutane Ina yinki uwar dakina,Spark Muryar ce take Masa gizo a kunne sai yaji kamar yasan Muryar,kallon Naila yayi yaji kamar Jamilunsa wlh,amma ai Naila bata waye haka ba,Yana ta kallonta a sace duk ta rufe fuska da gashi da glass ya kasa tantancewa amma wlh kamar Jamilunsa,Mummy ce ta mike tsam tace Nasiba Yankan kauna bari na kawo miki abin motsa baki,Mummy tana tashi Spark ya mike zai fita Naila ta kurawa saitin Hallarensa Ido,kallonta yayi yaga ta kurawa jikinsa Ido,fuska ya daure kamar bai taba dariya ba,yace ke lafiya? Ina Naila ai ta Lula kallon Hallare ya ta koma,yace ke wai baki da hankali ne me kike kallo,Naila tana kallo tace wait sir, are you out of your mind? are you normal? Naila tana kallo tana matsawa tace Sir sorry Ina bada magani baka da lafiya,abarka bata aiki,Spark tsaki ya ja ya juya ya fice Naila ta tsaya a palon tace yaki ya bari a gani amma ba komai dole sai na ganta bari naga gidansa.

Ko Mummy bata jira ba ta jira ba ta fice ta shiga motar tabi bayan motar Spark amma Ina motarsa ta bace mata gidan Mummy ta koma,tana shiga Mummy tace Ina kika shiga ne? waccen Dan naki Aljanu sun aure shi bazai taba aure ba sai Kun tashi tsaye Mummy tace ke Dan Allah wlh anyi anyi yayi aure yaki baya son ko wacce mace,Naila tace sai an Masa maganin aljanu Kinga ni yae film ce amma Ina Bada maganin aljanu,Mummy tace wlh indai zai warke ba matsala bani da burin da ya wuce naga Spark Dina yayi aure,Naila tace dole sai na tare a gidansa idan ta kama har kakana zan kawo ayi Masa magani,Mummy sun matsu Spark yayi aure suka ce ba komai kawai zan Masa dole ma ya bari ayi Masa magani.

Naila a ranta tace oh na canja shigar Maza nazo Dan na samu shiga karshe na fada prison,gashi yanzu a banza nazo a Yar gayu sun yarda dani Kuma,Mummy tace idan zaki iya farawa to gobe ki ajiye film din nan Ali nuhu ya canja wata idan ya warke kina da 1million,yanzu zan sa a miki kudi dubu dari biyar a accnt in kin gama aikinki zan baki cikon kudin,Naila tace an gama yo film din banza na fada masa ya nemi wata suyi rawarsu,gobe zanzo ki kaini gidan da kanki,Mummy tace ba damuwa,Naila tace karfa ki Ganni da shiga me kyau wlh bani da wani kudi mu kin san harkarmu ta celebrities haka muke da karya da fake life amma idan kika ga gidanmu kare bazai shiga ba,Kinga Ina Hawa mota na gyara jiki na sa kaya masu kyau to da cuta zata kamani shike nan sai dai aji ana neman taimako a gidan radio,Mummy tayi dariya tace ai mun sani dama.

Naila ta gama ta fito tace yanzu ta spark nake tukun kafin na dawo kanki,wai dama Ashraf shine Spark amma ba karamin munafuki bane Yana jina Ina nemansa Ashe shine ya min banza sai ya gane kurensa tunda ya raina min hankali bazai taba gane ni Naila bace sai na sake cin tudu biyu a soyayya,tunda ya Soni a Yar gidan yari to yanzu Kuma

Please Login or Register in order to submit comment