You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ba Naila,Naila tace ai na wuce haka ma,mu da muke zama a cinyar Maza watarana ma Affa ne ya min duka yace idan na sake sai ya yanka ni,shine ban Kuma ba,Mohsin ya saki salati yace Allah ya hadaki da mijin da zaici ubanki yayi maganinki Naila,dariya ta sheke da shi tace sai dai naci nasa uban Yaya,idan ba duk Wanda ya aureni ya auri masifa da kudinsa ba Allah ya konani,Mohsin yace Baki hadu da Wanda ya fiki bane,dole kizo ki buwaye mu ashe kin lalace da yawa
Naila tace ba karamar lalacewa ba Yaya Dan Allah yasa ma na tsaida Sallah wata daya da suka wuce,Mohsin ya sake bude Baki yace dama bakya sallah duk shekarunki har Sha Tara 19yrs to 20yrs? Naila tace wallahi sai bana Allah ya nufa,ai azumi ma sai shekarar Nan data wuce na tsayar da shi amma duk na karya nake yi sai na buya na Sha ruwa da Koko,watarana Kuma idan naje kiwo sai mu kafa baki a nonon saniya direct musha mu koshi.
Dan Allah full stop zo ki tafi gida goma tayi,a kauye ma sai na Kai 12 na dare a waje muna wasa bare Nan birni fitila ko Ina gari kamar rana,to naji ke duk turancin da kika iya a Ina kika koya? Makaranta mana,na yarda ai kina da brain,bature ne yazo dajinmu yawon bude Ido Ina zuwa makaranta,sai watarana zan baka labari,yanzu ka kaini gida Yaya,bacci nake ji na fada miki ki shiga napep,to kuwa sai dai na kwana,tsaki yaja yace jeki Palo bari nayi wanka nazo,Palo ta dawo ta zauna tana kallo har yayi wanka ya fito cikin 3qurt fari da t-shirt brown,yace muje mana kina ta kallona kamar baki sanni ba.
Naila tace, kayi kyau Yaya Ina ma ba Umma ce ta haifeka ba,gaskiya Umma Bata kyauta ba ta cuceni data haifo ka Kuma ta haifo ni ai sai ta tsaya idan ta haifeka ma ba laifi sai ta bari ni a haifeni a wani gidan can sai mu hadu sai muyi aurenmu ko ya kace,ai haihuwa ta mana illa kawai yanzu sabo da Allah sai a haife mu a gida daya the same father and mother haba haba,ai da ba gida daya bane ni nasan ma da Kai zan hadu dole in aureka, da anga 'Ya'ya wai wai zuky, dariya ce ta kwacewa Mohsin sabo da suna masifar kama da Naila duk gidan sunfi kama kowa ya gansu basai ance Yan uwa na jini bane.
Dariya ya dinga yi sosai tana kallonsa tana murmushi Yana dariya yace taso mu tafi ya riko hannunta, ta mike ta dauki sandarta da bata mantawa da ita,shi ya manta ma da shegiyar sandar yasan wannan sandar baza ta kwatu ba,ya bata rai yace ajiye sandar nan,haushi taji tace idan baza ka kaini ba ni zan tafi a kafa,ba yanda ya iya haka ya fitar da machine dinsa lifan.
Tace ban iya hawa machine ta gaba ba mu zaman dare muke a kaikaice muke Hawa, Yaya sai an dorani,ko Affa dorani yake yi,tayi tayi ta kasa hawa sai faman juye juye takeyi da kyar dai ta hau ta juya Masa baya maimakon ta Kalli gaba sai ta Kalli baya ma'ana sun hada baya da baya,ga sanda sakale a wuyansa, Mohsin yace wallahi idan kika fado ba ruwana Dan iskanci kinyi kusan wata guda a birni kina kallo yanda ake Hawa machine sai ki juya baya zaki fado kinji na rantse"
Naila tace to Yaya kaifa yayana nane na jini yanzu idan na juyo Enndu(Boobs) Dina suka taba jikin ka fa,mu mun iya hawa machine a haka,yace ke kika san Enndu shashasha, yaja machine dinsa suka Kara gaba ana ta kallo ta zauna daram amma dole ta rike machine din ta Dafe da hannaye biyu sanda Kuma ta tsakiyarsu a kwance.
Tana ganin me tsire Yana yawon dashi a Kai a bude tace Mohsin tsaya na siyi tsire,da karfi tayiwa me tsire magana Kai me tsire da zafinsa? Mohsin yace wannan abin ya gama Shan iska duk kwayoyin cuta sun hau Kai,tace mu haka muke siya a can kauye idan munje kasuwa,ta sake cewa da me tsire kaga ya hanani siya Kuma Ina so,kowa Yana jinta duk na gefen titi tana cewa ya hanani siyen tsire Kuma Ina so, sai dariya ake musu ga hanyar gefen tasha ne,Mohsin Yana ji yace nan ba haka bane to ba a wannan shirmen, sai da ya karasa waje me kyau Wanda nasu a cikin glass yake yace na nawa zaki siya? Tace na dari biyu
Uban wa zai baki nama a dari biyu,sauka tayi shima ya sauka ya siya mata na dubu daya,ya siyi na dubu biyu yace gashi nan ba yawa wannan nasu Umma ne da yaran,tace to mun gode ta sake juyawa zata hau machine irin dazu,Mohsin yace wallahi kika hau da baya sai dai na barki a nan,dole ta juya gaba ta shako wuyansa sannan ta hau ta rirrike shi Kam a haka ya kaita har gida,yace to shiga Kinga ma basu rufe gida ba da alama ke ake jira ta sauka
Tace Yaya? Ya amsa da Naam,tace ka dinga yiwa Umma fada ta tsaneni su Hidaya take so kullum suyi tace min Yar kauye jahila,Wani furucin da Umma take yi wallahi tambade yaranta take bata sani ba,kanaji wai naje Abuja na samu masu kudi na dinga cin kudinsu ai wannan jefa yarinya ne a hanyar banza,ni da nayi haka ai gwara na bada kaina a caca, nace sana'a zanyi taki yarda yanzu sabo da Allah wa na sani a Abuja da za ace nabi wata Hajiya Tagwadas,Kai daga Jin sunan kasan ba na kirki bane wai Tagwadas,Kuma idan nace bazan je ba ta dinga zage zage da lafazi marasa dadi,gaskiya kayi mata magana ato ana shiga hakkina a gidan nan,gashi nan sai ramewa nakeyi kullum,Mohsin yaga yanda take uwar kiba da kyau amma tace ramewa take.
Mohsin murmushi yayi yace ashe dai kina da hankali Kanwata,Ina da shi mana amma Kai kadai nake nunawa hankalina a wajen kowa ni bani da hankali ato Kuma bance ka fadawa kowa ni Ina da hankali ba,abin sirri ne,dariya Mohsin yayi ya mika mata hannu yace give me five, ta mika Masa hannu suka tafa,yace idan ta takura kije kawai amma ki nutsu ai tace rako zaki yi just 2weeks zaku dawo ko ai ba matsala idan ta takura kije, shike nan ta furta tace sai da safe,idan ka koma kar ka kula Yar banzar matar Nan taka ko kaji sha'awarta ka makale kafada kace a'a,idan yaki hakura ka fada min zan baka magani shike nan sai kayi wata baka ji kana son mace ba, Baki Mohsin ya tabe,tace ka daina rainawa da gaske nake nazo dasu ni nake da sirrin,lakani ne Dani I can fix you, gwasaleta yayi yace oummm ke dalla rufe min baki,jeki good night ta shiga ciki ta rufe gidan gaba daya .
Ashe Abbansu Yana waje bai shugo ba,
Naila tana shiga ta same su masu Assignment duk suna ta yi wasu suna kallo,Umma zaginta tayi tace Dan iskanci sai ki tafi waje ki Dade haka har dare ki zauna baza ki dawo ba,sabo da ni ban isa ba ubanku dolo ne,ni Kun rainani banza bagidajiya,Naila tace amma ai na fada miki na tafi gidan Yaya,shine zaki Kai dare haka sabo da hauka irin taku ta Yan kauye, Naila baki bude take kallon Umman tasu, ledarsu ta mika musu tace gashi inji Yaya,da sauri Umma ta fisge ledar tace miko min waccen ta hannunki
Ai nawa ne wannan shi ya siya min daban,to Baki isa kinci ke kadai ba,Naila ga taurin Kai tace wlh bazan baki ba ai nawa ne ai ga naku na baku,kune bakin nama ni a can ci muke mu koshi sai ya ishe mu kullum,Naila kika sake fada min magana baza ki samu albarkata ba,da sauri Naila ta bude baki,tace wai ku me kuke yi haka ne komai akayi sai ku dinga furta munanan kalamai akan yaranku wani abinda da iyaye basa ganewa duk Baki ne,amma ni kikewa su Hidaya me yasa ba a musu wai? Ko sabo da ba a nan na girma ba,karku bari nayi fushi wlh Ina da taurin Kai duk duniya babu me sakko Dani,ai samun lafiyarki Naila kiyi aure ko ki bi Hajiya Tagwadas Abuja kiyi kwana biyu kiyi samari ki dawo masu kudi nake so yawwa.
Naila tace ai bance miki bazan je ba amma ni ana matsa min zan fasa Kuma babu me sani,ai kuwa da na tsine miki,Su Hidaya suna jinsu, Hidaya irin mugayen nan ne da basa magana sai bakar zuciya da hassadar tsiya,amma a haka sai ka rantse tafi kowa hali me kyau,tunda taga Naila ta fita kyau da komai shike nan take Dan Jin haushi amma ba sosai ba.
Naila tana cin Dan tsirenta Umma tasa hannu ta kwashe guda hudu ta karawa Hidaya biyu ta bawa Zara daya sai Aslam ta bashi shima suna ci,Naila zuciya tayi ta tura musu tsirenta tace ku hada ku cinye na koshi,suka dauke kuwa.
Sai lokacin ta lura ba Abbansu ta shiga nemansa tace Umma wai Abba fa? Shi yasan Inda yake cewar Umma ta share zancen,
Naila ta mike zata bude kofa tace idan kika bude wallahi sai ranki ya baci,Umma a waje zai kwana fa,ya kwana a bola ma mece matsalarki uwar shishigi cewar Umma.
Tsabar dolonci irin na Abban su Naila da yazo yaga an rufe gida bai iya kiran kowa a waya ba,har yayi niyyar bubbuga musu kofa ya Kai hannu kenan sai ya fasa yace bazan tashe ku ba haka kawai,uhm uhm Ina Sam sai ya juya ya koma masallaci ya kwanta a ciki,a Nan yayi bacci idan ya farka ya tashi yayi Ibada ya koma bacci a haka ya kwana,bayan anyi Sallar asuba ma bacci ya koma a masallacin,yace bazan shiga hakkin su ba suyi baccinku, sai 10am ya fito ya nufi gidan.
Lokacin su Hidaya duk sun tafi makaranta sai Naila sai Umma,Naila ta tasa kokonta a gaba da ta Saba da dashi kullum ita bata Shan shayi kullum sai ta siyo Koko da kosai, Bata ga Abba ya dawo gida ba sai ta kasa Sha ta zauna tayi tagumi,Umma kuwa ko a jikinta wanke wanke take yi a Jikin pampo tana faman zubar da yawu, 10:11am Abba ya shugo gidan dauke da Sallama,Naila tace ahhh.... Alhmdllh Abba Sannu da zuwa Ina ka tafi ne?
Ita kuwa Kubra Umman tasu ko kulashi Bata yi ba sabo da bashi da kudi gashi baya iya komai,shi ba a fada da shi,yace Naila a masallaci na kwana nazo naga Kun rufe kofa kar na tashe ku Kuna bacci shi yasa na kwana masallaci,Yanzu ma nasan Kun tashi shi yasa nazo gidan,Tausayin Abbanta ya kama Naila matuka
Tace Abba kana zuwa ka dinga bugawa komai dare Kai da gidanka,tsaki Kubra ta ja tace gidan Mohsin dai ai shi ya siyi filin ya gina mana da ai a wani wulakantaccen gida muke ,wannan me zai iya tsinanawa kansa bare wani ta ja tsaki taci gaba da wanke wankenta karshe ma ta gaji tace na gaji ka gama kazo ka karasa wanke wanken,da sauri Abba yace to,Naila ta fara hawayen Tausayin Abbansu tace haba Umma haba Umma ni zanyi a madadinsa,Abba bai iya cewa komai ba,.
Naila tace sai kiyi ta cewa Abba bai iya komai ba bayan gashi ya haife mu ai kuwa ya tsinana miki,tunda gashi ma yanzu wani cikin ne Dake na Abba ai kuwa shike tsinana abubuwa, Naila ta mike ta riko hannun Abba ta kaishi Palo ya zauna a kujera tace Abba kaima Dan birni ne shayin? Yace ae Ina da ulcer bana Shan Koko,Naila ta mike ta shige kitchen ta hado Masa tea ta fito,Umma ta mike tana harararta tace dan ubanki mu gani
Ta sa cokali ta juya shayin tace madarar da kika gambaza Masa a ciki shi yake siya mana ko kece? Ai Yaya Mohsin ke siya dansa ne Kuma ai kuwa kayansa ne cewar Naila
Ae to naji bread din da kika dakko na ubanki ne? Ko kina sana'a ne Umma naga dai Mohsin shi ke bada kudin sabo da haka Abba Yana da Iko da shi,kwafa Umma ta ja haka Naila ta kaiwa Abba,shi Kuma ba zuciya ya fara Shan abinsa, Naila juck din kokonta daga kwat kwat kwat sai da kusa shanyewa ta huta ta sake yin kwat kwat kwat, sanye take cikin dan gajeren wandonta buje da shi ba kyan kama da vest a jikinta wai kayan baccinta ne tun a dajinsu, gashinta buzu buzu a cukurkude
A haka Mohsin ya isketa ya Sha wankan shadda fara ya zuba kyau Yana ta kamshi ya shugo,Umma ya fara gaisarwa har kasa,kamar wani sarki ne yazo haka Umma take murna sabo da shike daukan nauyinsu komai da komai, Cikin Palon ya shiga Naila ta kalle shi sama da kasa ta juya ta Kalli Abbansu ta tabe Baki ta zurawa Abban ido.
Abba yace lafiya Naila? Naila tace me yasa kuka haifo wannan a Nan gidan ne muka zama Yaya da kani,ai kunyi hadama sai ku barshi a haife shi a wani gidan mu hadu can muyi aure,har Umma dake waje sai da tayi dariya,tace wannan kwai sakara, Mohsin Yana dariya yace sannu Naila,hannu ta mika Masa suka gaisa harda dunkule hannu ta mika Masa shima ya dunkule nasa ya mika suka hade yanda gayu suke gaisawa.
Naila tace kayi kyau Yaya.
Abuja birnin tarayya Zaune yake a katafaren palonsa Saman kujera ta alfarma da files a gabansa Yana ta rubuce rubuce ga laptop a gefe Yana dubawa,babu Sallama Asmau ta fado palon tare da furta hey Baby,ko kallonta baiyi ba bai ma San iskar data ajiyeta ba,kamar ba mutum take yiwa magana ba,gefensa tazo ta zauna, wata uwar tsawa ya buga mata wacce ba shiri ta mike tsaye zumbur, ba tare da ya kalleta ba yace waye yace ki shigo min gida har Palo ba sallama ba komai, zata yi magana kenan cikin tsawa yace get out.
Asmau ta Sha Abaya me tsada tayi kyau itama kyakyawa ce wankan tarwada taci make up,tace karfa ka manta Spark an mana baiko aure zamuyi,kwana nan zamu zama miji da mata,tunda Mummy ni ta zaba Maka a matsayin mata amma sai ka dinga wulakanta ni,ko da yake ai kowa ma Kai wulakantashi kake yi, Mima ma baka kyaleta ba bare wasu Kai kawai wacce ta raineka itace mutum a wajenka, ko wacce mace an kawo Maka kaki aurenta gashi Nan har ka Kai 31yrs baka yi aure ba ga kannenka nan su suke Shirin yin aure, anya kuwa kalau kake baka da wata cuta ko aljana ta aure ka,Kai duk wankan da mace zata yi bata birgeka duk kyawunta ko kallon mata baka yi,ai kuwa ni nasan Aljana ce ta aureka ma.
Waya ya dauka fuskarsa kyakyawa a murtuke ya kira securities suka shugo mutum biyu yace ku dauki wannan abin kuyi waje da shi karku sake na sake ganinta a gidana ,sorry sir suka furta suka dauki Asmau tana ihu da karaji tana tsine tsine suka jefo ta waje, dama bata shigo da motar ba haka ta shiga motarta sai gidan Mummy wacce ta raini Ashraf Spark.
Spark kuwa wata ajiyar zuciya ya sauke yace an maidani yaro,matar aure ma ace sai an zabar min a rayuwa ni bani da yanci,me yasa ni ake takura min ne,ba laifi na bane,nayi soyayya da yawa,nayi Yan mata daban daban baza su irgu ba at the end zan gano kudi na suke so ko kyawun da Allah ya min bani ba, sabo da haka soyayya ban Kara yi har abada aure na hakura bazan yi ba dama ban taba yinsa ba.
Kwanciya yayi a Saman 3str ya baje kafarsa daya tana kasa daya Kuma tana Saman kujera,kansa ya dafe yana kallon sama ya Lula tunanin duniya.
Babban Amininsa ne ya shugo Kuma cousin brother dinsa Kamal,Sallama yayi ba tare da ya kalle shi ba ya amsa Masa, Kamal ya kare Masa kallo sanye yake cikin jallabiya coffee color me tsadar gaske kawai shining take tana sheki, hannu Kamal ya mika Masa suka gaisa sannan Kamal ya tambaya Spark how far?
Ashraf Wanda aka fi sani da Spark Sam Ashraf asalin sunansa ya buya kowa da spark yake kiransa har iyayensa,sabo da kalar idanuwansa da kwayar idonsa suke kamar blue kamar baki Kuma irin kalar na wasu turawan, yace I'm good bro,Kamal yayi dariya yace dan wulakanci shine ka Kori Asmau? Kafin ya rufe Baki Spark ya furta mind your Business,ya ja tsaki ya Mike,shi dama bashi da mutunci baya ragawa kowa duk abinda yaga dama kawai zai yabawa mutum a haka ma Dan Kamal ne shi yasa ya raga Masa,mikewa yayi a fusace ya tattara tarkacensa ya bi steps zai haura sama
Kamal ya sheke da dariya yace an dai yi baiko ya zakayi rana za a saka Dan ubanka,Spark Yana bin steps yace sai dai a daura da ubanka,Ubana? Yeah you heard me clearly a daura da Ubanka, Kamal yaji haushi amma ya zaiyi da Dan uwansa abokinsa Kuma yasan halinsa ba wata rayuwa yayi a kasar Nan ba sosai shi yasa yake wasu abubuwan ba tunani,bashi da mutunci ko na kobo,Kamal kwafa ya ja tare da mikewa zai tafi sai ya tsinci Muryar Spark yace kazo upstairs,Yana fadan haka ya juya,Kamal kamar bazai je ba dai sai ya hakura ya haura sama, Saman lafiyayyen bed dinsa na alfarma suka zauna,kawai spark Yana daukan wayarsa yaga sakuna suna ta shugowa ta WhatsApp,budewa yayi sai yaga Asmau ce ta turo Masa pics dinta sun fi ashirin Nan take yayi cilli da wayar ya kwadata da kasa tayi kwatsa kwatsa, yace zan iya kashe yarinyar nan,can you Imagine,Kamal ya rude ya zaci wani Abu ne babba yace me tayi,pics ta tura min sunfi 1million shegiyar yarinya mayya,to taga handsome ba dole ta rude ba cewar Kamal.
A dinga sharhi pls bana son godiyar nan da stickers ni Kam 😅
BOOK 1
Free pages
300 ne ga me bukata
Accnt no
0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank
Katin MTN
08061929616
Yan Niger ku nemi
+227 90 79 59 39
AsmaBaffa
[12/4/2023, 1:28 PM] AsmaBaffa: 🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN TARI
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA
GAREKI❤️
AIDA MAMAN TASNIM
11-15
Page naki ne
BESTYNBEELAT
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/J0ZFfbvon6ZGASEYAwZX5s
*Ina mata yan gayu yan kwalisa*
*Ina iyayen da suke so yaron su sufito fes*
*Albishirin ku kuzo gidan sauki da rahusa anan za a share hawayan ku*
*Munada kaya masu inganci nagarta gakuma sauki kayan mu sune kamar hak*
*Atampa*
*Les*
*Abaya*
*Sleep dress*
*Shoes*
*Mayafi*
*Hand bag*
*Misk*
* ETC*
MASU AUDIO BAN AMINCE A JUYA MIN NOVEL BA IZINI BA PLEASE.
Hannu Spark ya mikawa Kamal yace bani wayarka ya mika Masa ya danna wasu numbers yace a kawo Masa sabuwar wata waya wacce taci uwar iphone a tsada da komai,ba ko Ina ma aka San da irin wayoyin ba,a wani kwali take kamar kwalin turare,ba a dade ba aka kawo Masa ya cire layikansa ya Maida cikin sabuwar wayarsa ya mikawa Kamal yace jefa a Dustbin,Kamal yace kana raina min hankali wlh, ai bata wani fashe da yawa ba sabo da almubazzaranci sai a jefa a shara a siyar da ita kayi sadaka da kudin ai yafi,harara ya aikawa Kamal yace ance banda kudin sadaka dalla ka bawa me so bana bukata, Kamal yace an gama ni Ina so tsaf zan gyarawa budurwa ta,idan na bata har ihu zata yi, Spark yayi dariya tare da furta Dan gargajiya ne Kai ai,suka fara hira da surutunsu na abokai a haka Kamal Yana hakuri sosai,Spark yace wai wani ne ya kawo min aiki kaji kudin kuwa ya raina min hankali, Kamal ya kwashe da dariya,Spark baya dariya shi a rayuwa sai tayi bala'in kamawa kullum a Shirin masifa da rashin mutunci yake, yace ai wlh gwara na zauna kullum nayi ta danna ashar,Kamal ya saki dariya yace wannan Dan rainin hankali ne,Spark yace Allah yasa banyi signing ba Kuma kasan company ne,better cewar Kamal haka suka ta hirarsu ta abokai.
Washe gari Monday sai 11am Mummy ta kirashi a waya bai daga ba sai lokacin da ya tashi a bacci, yayi wanka ya shirya tsaf cikin kana Nan kayansa na kirki Yan gaske kana ganinsa kasan ba pure Dan Nigeria bane,ya fito ya Sha kyau Yana kamshi tare da taku cikin kasaita ,da gudu Securities suka bude Masa bayan motar da suka ga ya nufa wata bakar mota,Yana shiga bayan motar shi kadai sai driver,Wata motar securities dinsa suka shiga suka wuce,a hankali yace gidan Mummy,Driver yace okay Sir, Yana hakimce a bayan mota Yana kallon gefen titi karaf ya hango wata budurwa tasha gayu tana tafiya wata tsohuwa tukuf da kyar take tafiya tazo wucewa da abincinta a kwano tana tsaye tana ci,jiri ya kwasheta tayi sauri ta rike budurwar, a haka hannayenta da manja ta shafawa matar manja a Jikin kayanta, budurwa ta saki wawan ihu ta juyo tare da shararawa Tsohuwar Mari ta hankadeta ta Fadi da abincin nata,Nan take Spark yace da driver kayi parking a wajen waccen matan,driver yayi sauri ya tsaya a hankali ya karaso saitinsu sannan yayi parking,Spark ko gama parking ba ayi ba ya bude mota ya fito, nan take budurwar data juya baya taji an fisgota da mugun karfi sai da gwiwarta taje kasa,ta mike zumbur kawai taji Mari ta ko Ina kamar ba mutum bane yake marinta ta zaci Tsohuwar data mara Aljana ce itace ta rikide haka ta dawo namiji saurayi kyakyawa,kyawunsa data Gani ta tabbatar sai aljani,tace iya Dan Allah ki yafe min,Iya kiyi hakuri,sai kace ubanta cikin sojojin da suke tsaronsa ya karbi bulalarsu da suke tafkar mutum da ita ya samu budurwar Nan ya zaneta tas duk sai da ya fasa mata jiki har fuskarta kafin kace me kamanninta sun canja mutane sun taru a wajen ana kallo,su tunaninsu ma kanwarsa ce sabo da yanda ya zaneta,yace mahaukanta jahilai kawai tsohuwa dan ta rikeki zata fadi mummuna irinki ma har wani yanga zakiyi,wahala tasa budurwar ta kwashe takalmanta a hannu ta zura da gudun tsiya tana kuka har tayi gaba sai ta dawo tayi reverse ta juya sai hanyar gidansu Inda ta fito.
Tsaki yaja ya juya ya Kalli Tsohuwar dake yashe a kasa tana ciwon kafa da kyar take tafiya,zuwa yayi ya dagata yace Iya tashi,ku ma tsofaffin nan bakwa ji wasu duk Kuna da gata sai ku fito titi Kuna wulakanta kanku,Tsohuwar tace Dan nan Allah Maka albarka na gode wannan ba yinka bane yin Allah ne,shi ya turoka ka rama min, na tabaka da Alheri wajen Dana nazo tunda ya taho cirani yau Shekara biyu kenan bai dawo ba babu aike ba waya,ya manta Dani uwarsa,shine abokinsa ya taho Dani wajensa ka ganshi can ma shine ya bani abincin nawa Allah ya Masa albarka, Spark yace Uhm tsallakawa zakiyi wajensa? tace ae Dan Albarka,kawai Spark ya dauketa kamar ya dauki tsinke ya tsallakar da ita,ya zaro kudade sababbi Yan dubu dubu Bai ma irga ba ya bata,ya juya abinsa,tana Masa godiya ko waigowa baiyi ba ya koma mota suka Kara gaba.
Gidan Mummy ya nufa ya isa gidan cikin takunsa na mazaje masu ji da kansu,gidane na alfarma me tsari Wanda ba kowa sai masu gadi mutum biyu,Yana parking masu gadin suna gaishe shi ko kula su baiyi ba ya dai mika musu hannu kala bai ce ba ya wuce abinsa,Wani Babban mutum ne ya fito Wanda yasha wankan shadda da alama me gidan
Book Chapters
Chapter 5
Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40