Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jawo Hanan tace wlh akan kici abincin Dana dafa gwara na zubar, ta kwada flask dinta da kasa sabo dashi, abincin ya watse ,Naila tace ikon Allah haka abin yayi tsamari? ashe haukar kullum shahara take.

Hanan kuwa tana huci ta chakumi wuyan Naila tana zage zage Naila ba karfi,kokawa suka fara Hanan ta hankada Naila Jikin kofa Naila ta bige kafarta,kofa ta ji mata rauni a kafa jini Yana zuba,turo Naila tayi waje tafado kasa,kafarta dayar ta gurde ta kasa tashi,Naila tace wlh sai nayi sanadin barinki gidan Nan sai an sakeki,kin jawa kanki,Kuma baza a sakeki ba sai kin Sha wahala a gidan Nan sannan a miki korar kare shegiya, sai kin koma gidan ubanki,dama ai kin tsufa tsohuwar banza

Mohsin ne ya shugo ya samu Naila a kasa ta kasa tashi tana ta kuka kafarta daya wajen yatsa Yana ta jini,Mohsin ya dagata da sauri yace sannu nace miki karki biye mata bata da hankali, muje na Maida ke gida,Kinga abinda nake gudu ko,yace yanzu idan na saketa ko na koreta mutane zagina zasu yi ace sabo da zan Kara aure ne,Naila tace karka saketa wlh sai ta kunshi bacin rai,tana dingishi ta dauki Jakarta da mayafi suka tafi,a chemist ya tsaya aka mata dressing suka koma gida.

Tana kuka tana Bada labari,Umma tace bar shegiya aure ne dai sai ya Kara,Abba yace Naila kema da tsokana ai dole tayi kishi ko wacece, baki kyauta ba ai sai ki kyaleta, Nan ga darasi a gidan nan nace zan Kara aure uwarku wacce hauka ce bata yi ba,Umma tace yaushe nayi haka? Hashimu kaji tsoron Allah,to ai dama ita uwa tana so ace Danta zaiyi aure musamman in basa shiri da uwar gidan Danta, amma idan akace ita za ayiwa to Kuma sai tsiya,Allah ya kiyaye min nayi wannan haukar a kanka cewar Umma.

Hashimu yace na nawa Kuma,a Hakan ana rainani a haka akayi kuka kina tsoro zan dinga yiwa wata girki,Umma tace to ka karo matar yanzu,yace sai da kika ga nayi kwantai zaki ce na Kara kowa ta gujeni,Batoolar ma ta gujeni, amma sanda Naje zance ai ta iya baza kunne taji Ina koya mata girki,Umma tace au har girki ka koya mata? Kaci Amanata,Abba yace Kinga ki gasawa Naila kafarta ni na riga nayi kwantai Kuma a gari, ya zanyi Kubra dai kullum Kubra kamar masifa,dariya Umma tayi tace Allah ya kyauta Maka Dan Yagana.

Abba yaji sabon Suna harda sosa keya Yana murmushi,yace Uhum Uhum Uhum...Allah yaji kan Yagana ana lahira,Uhmm ko su Yagana kamanni sun canja oho, su Yagana an mutu ana gulma,sun zaci ni Dolo ne sai su dinga gulmar mutane Ina jinsu ni kuwa in nade tsab a kaina, sai naje na fadawa mutumin da suka yi gulmarsa nace Yagana tace Maka kaza,Naila ta kwashe da dariya tana kuka tana dariya,Babar Hashimu ce guda amma yake fadar haka,Umma tace Inshaallah tana Aljanna Allah zai yafe mata, Abba yace Ina mata addua kullum Allah ya yafe mata amma har ta mutu tana zuwa wajen malamai wai sai ta Kara haihuwa,nace Yagana nima da ya kuka sameni ki fawwalawa Allah, amma Yagana taki ji,kullum baza suyi hirar duniya ba sai zancen wasu,ni Kuwa Ina ji duk na kwashe naje na fadawa mutumin,Ina ta mata nasiha sai ta zazzageni,to yanzu wa gari ya waya? Sai dai nayi mata addua idan Allah ya yafe mata shike nan,idan Kuma bata dace ba yanzu walakiri ya sassaba mata kamanni,Umma tace Dan Allah ka dinga fadar Alkhairi,Abba yace ni na sata tayi gulmar? yanzu haka da za a dawo da Yagana duniya bazan ganeta ba tsabar dukan walakiri.
Naila sai dariya suke kamar ba gobe.

Naila tana hawaye Umma ta gasa mata kafa, Spark Yana ta kira,yau bugu daya Dake shagwaba ce har ta daga tana kuka,yace menene? tace uwar gidan yayavce ta kusa karyani,Spark yace amma dai baki karye ba ko? tace ae tana shesheka tana cewa kafata jini take yi sai da aka kaini asibiti yanzu ma Likita yace gobe da sassafe lallai na karya da hantar rago,Spark dariya yayi yace to ai ta kwana gidan sauki indai zaki warke.
Tace Kuma yace da ice cream da daddare kullum sai na Sha,sai me? Spark ya tambaya,tace da tsire me Laushi,yace wannan ciwon ai da sauki,yace wannan bata da Imani gaskiya,Naila tace ai shegiya sai nayi sanadin sakinta wlh bazan yarda ba,an fasa kawo Maka Amarya Nan da kwanaki kadan sai na dau fansa,Spark yace a'a please Dan girman Allah a kawoki sai muzo tare mu dauki fansa,amma Ina wani kar a kawoki ai bazai yuwu ba,Spark yace ki rabu da ita Allah zai saka miki,ai dama na ganta duk wata ya muka kwana ce,duk ta zama wata Rasss da Kwassss,Naila tayi dariya tace ko tayi kwalliya ma bata kyau,Spark yace ai shine Rasss da Kwass din tayi expire kenan.

Yace ki rabu da ita a kawoki gidan mijinki yarinya Kisha madarar Nido inji Scoler,dariya suka yi,Naila bata San Hallare ba Sam ta zaci wasa ne,tace Yama sunan style din da akeyi? Spark yace suna da yawa fa akwai su
Snake in the monkey shadow, su Bend down,Naila tace na gane bend down dai kamar zaka Koma shekarar 2001? Spark yace Ehem ashe kin gane, sun Dade suna hira kamar zasu kwana a haka, yau Spark yasha nishadi da farin ciki da wuri ya Sha baccinsa me dadi,Naila kuwa sai bayan sun gama ta tuna ai aji take ja fushi ma take yi da shi.

Shuru tayi Umma ta fito daga daki tace lafiya? Naila tace nidai soyayya tana cutata Umma idan ya kira sai na manta komai na dinga farin ciki,Abba da yanzu ya shugo ya tsinci zancen,yace ai haka so yake Naila ki tambayi Kubra,Kubra ya sanda aka turani zance wajenki na dinga guduwa Ina Jin kunyarki,Umma tace Dan Allah daga masallaci ka dawo ka tafi Palo a kawo Maka abinci,Naila tana ta boye dariyarta,tace ko Dan Abba ai ka so zaman gidan nan wlh.

Su Naila ana ta gyaran jiki ba daga kafa ko Ina gyara yake Sha ita da beauty,sunyi kyau sun Kara haske ko Ina suka gifta sai kamshi,Naila har wani kiba ta danyi, Hanan taga biki ya taho ta haukace,Mohsin yayi mata lefe akwati uku Amarya akwati shida amma tace bata so,ta fatalo akwatunan kofar gida sai kwashewa yayi ya Maida su gida wajen Umma,Ya Bata kudi ko zata yi wani abu taki karba ta watsa Masa abinsa,Baban Beauty shi ya zuba musu furniture amma kowacce da kalar nata,Hanan sabo da kishi da tasan zata tare duk tasa almajirai suka fitar da kayan ta kaisu ta siyar da na bangarenta ta dauke kudin kayan ta Kai gidansu ajiya,ta kawo kwararrabarbun kayanta tsofaffin ta zuba a part dinta,gidane hadadde yasha alatu part biyu ko wacce 3bedroom da Palo,ko Ina a tsakar gidan yaji flower da interluck, ga motarsa shi Mohsin lafiya Lau abinsa,Chikar gayu anyi dinkuna sunyi anko har Naila da sauran kawayen su Beauty Naila ita bata da kawaye a birni sai kauye,Kuma sai da ta fadawa kaka a gayyato mata kawayenta na kauye,Kuma an basu alawa zasu zo su hudu.

Ana gobe daurin aure ko wanne bangare an cika gida ana shiri har dinner Mohsin zaiyi lafiyayya,Naila da iyayi harda kiran Spark lallai sai an kawo mata motar Hawa sabo da zirga zirga,yo abinka da amarya ana zumudi sai gashi ansa wani ya kawo Mata in ta gama amfani da ita za a zo a dauka.
Gobe ce ranar Dinner Hanan tace dole taje da kawayenta sai sunga tsiyar da za ayi a can,Naila itace gidan Beauty itace gidansu,gata itace babba mace a gidan da ita Umma ke shawarar komai,abinci ma duk an Bada kwangilar yi,tukunya ko digo baza a a Dora ba a gidan sai dai a kawo a dire,Naila tace Umma Spark ni fried rice zan basu kar a kawo min wani abinci idan ba ita ba ranar daurin aure zaizo,Kuma zaizo Dinner ma gobe,Umma tace ai dai ranar daurin aure ai za bashi ko? Dinner ai akwai acan,ae ranar daurin aure,Allah ya kaimu.

Abba an kawo goro da yawa da alawa na daurin aure,sai cewa yake ni ta Hanan nake so a raba abata nata Dana danginta,ana rabawa cewa yake a fitarwa da Hanan fa nata Dana Yan uwanta.
Spark shi duk burinsa yazo Kano ya sace Naila a rubibi su kwana a masaukinsa,har Allah Allah yake gari ya waye ya tafi Kano.




A dinga sharhi fans
Masu Sharhi Ina godiya



AsmaBaffa
[12/20/2023, 12:35 PM] AsmaBaffa: Paid group only 300

Accnt no
0175487861
Asmau Garba Muhammad Gtbank

Katin MTN
08061929616

Yan Niger
+22790795939

🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN YARI

BOOK1

71-75


Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM


PAGE NAKI NE
Baby Ak

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LAizQA6PofSLoFhQ7XeaQx

Ina kuke masu burin suga sun kawata gadajensu da hadaddun bedsheets? Ko Kuma blankets kike nema? Masu aurar da yara ko kannai da ke kanki uwargida indai kitchen utensils kike bukata
To kukanki yazo karshe.kuyi joining group din R&U exclusive kitchen and more
Ku more wa idanun ku da kayan kitchen Yan yayi na gayu da zannuwan gado na kowanne kasa Zaki samu acikin farashi Mai sauki
Kuma Maza Bata barku abaya ba idan Kuna bukatar a hada muku lefe nagani na fada na amarya Kona uwargida wato na fadar kishiya duk Zata hadamuku acikin kwanciyar hankali.idan ma akwatunan kawai kuke bukata duk inkuka tuntubi Rumaisa zaku ganewa idanuwanku
Tana Kano state Kuma Tana tura Kaya kowanne state afadin nageria harma da kasashen da muke makwagtaka dasu
Zaku iya tuntubarta ta wannan number
07034559202



Washe gari kuwa Spark ko fadawa Naila baiyi ba ya taho sabo da sai taga dama take daga Masa waya,kawayenta na kauye sunzo da shigar Yan Fulaninsu gasu kyawawa sai kalle kalle suke yi,Rayya, Jidda,Nafee,Dije su hudu Wanda gasu yara ma Naila ta girme su duk an musu auren Fulani sun gudu daga gidan Mijin ma basa auren, yara kanana duk an sake su sabo da ba a basu time sunyi zabin su ba, wasu ma auren hadawa kawai akeyi yarinya ta dinga guje guje,karshe idan ta Saba da namiji tayi ta sheke ayarta.

Naila duk ta kira me lalle tayi musu,kayanta ma sun musu yawa ta fisu kiba da tsayi sai ta samo kayan Hidaya ta basu kala bibiyu,Hidaya tasan Naila zata basababbi bata ko hana ba ,sannan Kuma ta siya musu anko an Dinka musu su hudun tunda tun a waya tasan zasu zo,sai murna suke yi,ta siya musu Yan takalma haka masu kyau flat da wata ke siyarwa a makwafta,tace ko wacce ta zabi Wanda ya mata har da Yar jarkarsu Naila tayi musu kokari, dama sunyi kitsonsu gasu da gashi,tunda suka zo basa Hausa da Naila fulatancinsu suke ta yi Naila an samu Yan uwa,Umma sai da ta gaji tace Dan Allah kuyi Hausa ai sai ace gulma kuke ba dadi mutane na zaune Kun juya harshe.

Naila an Sha lalle hannu da kafa ya zuba kyau,sanye take cikin vest me siririn hannu da skert Dan kanti sun mata kyau abinka da me kyau gata Yar bulbul,gashi yasha gyara ya koma baki ta dole,babu ko dankwali a kanta tana zaune ana karasawa Rayya lalle tana cire mata na hannu.

Ta juya baya tana aikin cire lalle taji Mohsin ya shugo danginsu Yan Fulani sai tsokanarsa suke yi ango ango, kado baya Jin fulatanci,Sallamar Spark Naila taji ashe tare suke da Mohsin,Naila a hankali tace Kai ga mijina nan,Rayya tace wayyo kunya ku miko Hijabi aradu a lullubeta,ango ne zai ganta tsirarar babu sutura,Dije tace shike nan Tantiriya ta gama yawo aradun Allah wai Ina zaki je da abin kunya hoodi jam,aradu ban iyawa cewar Nafee,Naila tace ni an fada muku kunyarsa nake ji,ai dama ke baki Jin kunya ko kado haka ya ganki ya kyaleki Tantiriya,tunda Yan kauyen suka zo ba Wanda ya kirata da Naila sai Tantiriya,Umma tayi tayi su daina fada sunki ji.

Spark kuwa da ita ya fara tozali Yana ta kokonto ko ba ita bace ne irin wannan chanji haka yayi yawa,ya sake kallonta a ransa yace Janare wannan haske da taka Kara haka,gashinta ya kalla yasan itace sabo da askin da taba yi gefe da gefe da aka kwashe Bai Kai tsakiya yawa ba.
Naila tana jinsa ma Bata juyo ba sai murmushi take ita kadai.

Umma suna daki da baki,saitin Inda Naila ke zaune ya yazo ya tsaya kamshinsa duk ya mamaye gidan,Hannu yasa a wuyanta ta baya ya kama sosai kamar me shaketa ta baya a hankali ya girgiza wuyan ya saki ya wuce abinsa,Dariya Naila tayi tace ai nasan kazo Malam,Dije tace kunya ta kamani ta jawo hijab ta dukunkune kanta,Rayya tace Ina zan sa kaina yau da abin kunya ku matsa na buya, Tantiriya tace kwayi Kwa gama me za a fasa mutuwa ko hisabi? tamike taje ta wanke yatsunta da taba lalle, Umma tana ta faman kiranta,ta tafi palon,Spark a cikin Yan kauyen Daji sai kallonsa suke.

Masu wasa da Naila suka fara tsokanar Spark,Suna cewa wannan ma ai namu ne Kai yaro wannan da Fulani yayi kama,Spark yace a'a yanzu ba a alfahari da ku,wato yanzu a kasar Nan kowa ya tsani Fulani sabo da Bata gari sun watsa mu,Spark an daina alfahari da Fulani yanzu bana ciki ni,Naila ce ta shugo suka koma kanta su Tantiriya an dawo Yan birni iya shege ya kare sai dai kiyi a dakin mijinki,Naila tace wlh bai kare ba kawai dan nayi aure sai ace tawa ta kare sai kace wacce ta tsufa ni wlh shi yasa ma bana son auren ai su Yaya ne suka jawo min.

Mohsin yace kika jawowa kanki dai dama mene amfaninki,Ango Spark in banda kallon Naila ba abinda yake,sabo da iskanci Kuma taga Yana kallonta ta fuske tana surutu tana girgiza,Spark sai ya susuce,Umma sunga yayi shuru sun zaci kunya yake ji,Umma tace ki kaishi Daya dakin ga key can,Naila ta dakko Key tace muje,Mohsin yace dama gidana kuka kaishi ba mutane can,Naila tace a'a tasan halin Spark,yace Hanan fa tana tsohon gidan har yanzu bata koma sabo ba ta dai kwashe kaya ko Ina yanzu ba komai wai sai ranar da za a Kai amarya itama kawayenta zasu sake rakata dakin miji,Spark yace ko Maza ne suka kaita ana farko,kara'i zatayi kenan ko babanta ne ya kawota ne farkon aure yanzu take so kawaye su Kai ta,Mohsin yace iskanci ne kawai ya fice.
Dakin Naila ta bude ba komai ciki sai katifa ta Sha gyara da bedsheet, Spark yace Alhmdllh sa key,Naila tace ban gane ba.
Key din ya kalla yace bani key din idan wani ya shugo fa.

Wai me zaka yi? hanashi key tayi ta fice daga dakin tare da Maida key din wajen Umma ta saka bra ta saka riga me dogon hannu sannan ta zuro hijab ta dawo dauke da ruwa da lemo a tire,wai security kika saka kenan? Naila tace ba dole ba ka bari mana a kawoni ko mene sai kayi,shike nan ba abinda zan taba? Naila tace ae,zaki zo ne ai zan fanshe,komawa tayi ta kawo Masa sandwich da Samosa duk ita tayi abarta Kuma sabo da shi tayi,Naila an dage da koyon girki sabo da a birge miji,ganin tana so yaci, sai ce Masa take yi Kaci kaji,yace bazan ci komai ba sai kin koma kin cire rigar Nan da kika saka,kina yi zan ci,Naila ana so aci girkinta,tace yaushe zan koma cire riga a cikin mutane,cire a Nan yanda kika saka ki cire, sai na ci abincin, ta cikin hijab ta cire ta zauna da vest dinta ko bra din ya ce ta cire.
Yace hijab fa a'a cire,Sai dai idan baza Kaci ba ta furta,fisgo hannunta yayi ta fado Saman katifa.

Tsaya nifa ba abinda zan miki hugging naki kawai zanyi,rungumeta yayi a jikinsa,tasa hannaye tayi hugging nasa back,Naila da anji Jikin Spark sai jikinta ya mutu murus,abinka da shakuwa an Shaku,kasa katabus tayi sai ma sake kankame shi da yi,a hankali ya dago fuskarta tare da tallafar fuskarta ya fara aika mata da kiss,Naila Idanuwa ta lumshe tsayawa yayi Yana karewa fuskarta kallo Yana dariya kasa kasa yace bude idon to,suna a rufe tace baza su budu ba yanzu, ci gaba yayi da tsotse bakinta,tun tana Dan sharewa har ta kasa ta fara Maida Masa martani , tana juya bakinta cikin nasa kamar zasu cinye juna,Spark yace kaga Yar gari,kin gama wayewa,Naila taji kanta ya Kara girma an yabeta har da sake bada himma zata nuna wayewar,Batasan Wato yake mata ba.

Juyata yayi tare da zaunar da ita tsakanin kafafunsa bayanta Yana Saman kirjinta,A hankali yana shafa wuyanta har ya gangara tare da sa hannunsa ta cikin vest Abu ko bra,Naila zama ta gyara tana Jin dadi,harda ajiyar zuciyar bata sake magana ba sai dai tayi ta faman Sosa idonta, tana tsoro kar tayi Nishi sauti ya fita, yace bata da kunya,yace Ko ba Tantiriya bace ne? Naji tayi mukus,Ido ta Sosa tace itace mana,ya naji kinyi shuru ke da zanji kalamai na tashi,Naila tace nayi hankali tare da dawo da hannayenta ta bayansa ta rike shi Kam,Spark yace au baza kice komai? Haka kawai nayi ihu ka dinga min dariya daga baya, na daure abina,kiyi abinki ni ba abinda zan miki Kinga a musulunci ba a so duk abinda kayiwa matarka idan tayi ihu ta nuna taji dadi daga baya ka dawo kana mata dariya ko kana tsokanarta to zata dinga Jin kunya ta daina shi yasa akace ba kyau,nima Kuma idan nayi ihuna kika min dariya daga baya ba kyau,Naila tace ni dai wlh sai na Maka dariya sai na tsokaneka,dariya suka yi.

Sandwich din ta dakko ta fara ci sai ta yi wayo wai tana cewa sandwich dadi,a ranta tace karya nake Kaine me dadin bari na fake da dadin sandwich nake ji,Ido ta lumshe tana taunawa tace dadi kashe ni wlh dadi,Spark ya ganeta shi dai yace ko dai nine Sandwich din? Naila dariya tayi tace na rasa me yasa motsi nayi sai ka gane,Spark shi Kam boobs yake aikin sarrafawa sai mutsu mutsu Naila take yi.
Ta bayanta ta miko Masa Samosa, kansa ya duko da shi saitin hannunta Yana gutsira,Naila tace Kwalbewa duniya ce,kwanciya yayi ya dawo da ita samansa,Naila ta Kalli Hallare harda dagawa Spark riga ta ganta kuwa a wando duk tana fitar da ni'ima,Naila ta rufe da sauri tace Allah ya baki hakuri,Bai San ma ta daga masa rigar ba,yace me? tace to Hallare ce take dalalar da yawu fa,ke fa? tace bado wai? Tace ae me yake ciki? tace aradu Hawaye ne yake ta zubowa,Spark dariya yayi yace Bado na hawaye,ya dauki lokaci Yana murzata sai da taga duk ya fara fita hayyacinsa ta kwaci kanta da kyar tace a bari sai an kawo Amarya please,yace ni da nazo yau daga dinner sai hotel zamu kwana, Naila tace Bada ni ba wlh haka kawai aje na samu ribar Hotel,ni kwana nan gaba daya ban yarda da Kai ba,da a baya wani Dan Salihi da Kai yanzu Ina abin naka kullum shahara yake.

Snacks dinsa ya zauna Yana ci yace ah yanzu an fara iya abubuwa,ai dagewa nayi naga za a barni a baya kullum girki nake koya,yace good girl ga Indomie da bishiyar salat ai kina kokari,kwana nan zaka yi tumbi,sun dade suna hira kafin yace zan wuce hotel naje nayi baccina kafin lokacin dinner,tace to shike nan abincin fa? Kadan Kaci,kafin na fito naci a gidane ai naci snacks dinki da yawa abincin ne ban ci da yawa ba,mikewa yayi yace yau hannuna albarkar da take jikinsa tayi yawa,dariya tayi yace you are so sweet,komai naki me kyau Allah ya miki baiwa,Naila tace Alhmdllh bari na kira kawayena na kauye ku gaisa,yace alright ya koma tare da kwanciya a katifar.

Fita Naila tayi bayan ta Maida hijab dinta tace Rayya tunda an gama lalle Kun wanke ku zo zaku gaisa,Rayya tace wayyo ni Allah kunya,Dan birni haka,Dije ita gwana tace ku fa baku waye ba aradu ku taho mana,suka tashi a kunyace suka shiga dakin,Spark Yana kwance abinsa Saman katifa suka durkusa har kasa tare da gaida shi Ina yini,yace lfy Yana fara'a a fuskarsa, Yana dariya a ransa kuma irin daurin da suka coka goshi kwal,ya musu irin gaisuwar su,yace ya gida? Suka ce lafiya Lau mun sameku lafiya? Spark yace lafiya Lau..lafiya Lau,ya manyan? Sukace lafiya kalau kalau wallahi,ya sake cewa ya shanu ya masu gidan naku? Rayya tace nidai Dan marakina Daya bashi da lafiya ciwon hanta ta kamashi,Spark yace to a yanka shi mana a Sha dadi, suka ce kaiiiiii hodi jam suna dariya Rayya tace ai Affana sai ya kusa kasheni,sanuwar fa wacce ta haifi Dan marakin gadonta nayi wajen kakana,Spark Yana jinsu,Dije tace nidai tsakani da Allah mijina ya sake ni dukkan mu auren mu ya mutu,gwara ma Nafee ita ta samu ciki ya zube mu kuwa shuru,Spark ya kallesu wannan tsigi tsigin yaran ma me za a tsinta a jikinsu,Jidda tace mudai Allah ya kiyaye mu musamman ni Iro Allah Bai bashi sa'ar iskanci Dani ba da tuni na boni la lalashe ,Spark Yana ta dariya a ransa yace a ransa Iro anyi dakiki marar rabo,Rayya tace kaga ni dai Ina son Sagiru na wlh amma iskancin Sagiru bazan iya ba nace ni da Sagiru kaadii fau fau aradu,Spark yace uhm Sagiru ya cuci kansa, Rayya tace Tantiriya ta dawo birni kowa a riga Yana ta kewarta.

Spark yace na manta ban tayaku jimami ba ya akaji da rashin Tantiriya? Suka ce ohh Tantiriya ta barmu sai hakuri muke ta yi Allah yasa hannun na gari ta fada? Spark yace na gari ne mana tunda gashi ta hadu da Tantirinta,dariya suka yi suna Jin kunya suna rufe Baki suka ce to mun tafi,yace na gode ya mika musu kudi suka ki karba sai Naila ce ta karbar musu.

Suna fita suka dinga labari wlh kirki ne da shi Ashe suna ta bawa Umma labari ai har Hira suka yi dama Yana da magana,har wasa ya dinga yi mana wlh akwai kirki, a farko mun zaci bashi da mutunci mun ga Yana gadara da takama Ashe shima Tantiri ne a nutse yake magana baza kice shi ya fada ba,Spark fitowa yayi zai tafi Naila tazo zata raka shi ya Dan matsa nesa da ita kadan yace kar ace bani da kunya a gidan surukai,suna zuwa kofar gida yace koma gida,karki min make up lokacin dinner kuma na tsani wannan kwalliyar da mata keyi,duk kyanta Bata birgeni Sam,kiyi da kanki kawai ni bana son make up duk ta canjawa mutum kamanni,Naila tace to na huta nima.

Ana ta Shirin Dinner da yamma Chikar gayu itace babbar kawar Beauty an dauki wanka kamar me,Amarya kuwa tana wajen make Up tare da wasu kawayen ta Sha farin bride material me tsadar gaske an mata wata gown me kyan gaske ta zaratan amare,an nada mata dauri da silver gogoro, takalmi Silver jaka ma haka,make up din tayi kyau an dora mata mayafin amare a Kanta sharashara sai walwali take ta ko Ina,Ango Yasa Shadda Yar ubansu Silver kalar takalmi da jakarta da gogoro.

Su Chika duk anci ankon Leshi me kyan gaske Blue and white,kawaye an Sha wanka sunyi gayya kamar me, Yan mata tamfatsa tamfatsa sunzo duk kawayensu ne yawanci daga gidan yari suka fito,Kamal ne zaizo shima sabo da abokinsa Spark ai kuwa Rafeeq yace akwai dinner? akace ae yace ko banza na Kalli mata

Please Login or Register in order to submit comment