Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mummy zata dace mijinta ya warke ta haihu.

Naila bata gane batu ba,sai da Mummy ta shaketa tare da kifa mata Mari tana jijjigata tana cewa matsiyaci ashe maganin kisa ka bani ka kashe min mijina ta dinga zabgawa Naila Mari, Naila zuciya ta ciyota ta dauki sandarta ta bugawa Mummy iya karfinta a kanta Nan ma Mummy da sharri ta sulale ta fara suman karya farrrr farrr, Naila ta jefar da sandar ta haye ruwan cikin Mummy ta dinga rama marinta mummy duk ta shanye Marin nan wai bata sani ba suma take, Naila ta daga hannaye sama tace a tafi dani da hujja Allah shine shaidata,wacce Bata San alkhairi ba butulu.

Da ace baki saka Masa guba ba maganin Dana baki kika saka Masa wallahi da aurenki ya daidaita maybe ma ke da kishiya shike nan watakil ma ki haihu kinwa kanki, ta ciro takalminta ta bugawa Mummy a Baki baki ya fashe amma duk Mummy wai suma take bata sani ba bayan tana Jin komai.

Mutane kafin kace me gida ya cika dam ko Ina manya Maza da mata,ga dangi ta ko Ina suna ta parking motoci ta bangaren mata da Maza,da kyar aka banbare Naila daga kan Mummy, kuka ta saki taje ta shaki Hajiya Tagwadas tace Allah ya isa d...da ...da .kika...kawo ni Nan...duk kafin kace me sojoji ta ko Ina a gidan matasan samari hadaddu suna ta dira dangi, a tsakiya aka saka Naila duk an zagayeta ana kallonta mutane har sun firfito da waya,ba Wanda ya gane macece,Misam ne ya Dana bindiga yace wallahi duk Wanda ya daukar mana hoto sai na harbe shi,ai kowa a tsorace yayi kasa da waya wasu ma jiki na rawa suka kashe wayar,Mummy dai tana can mata suna ta yayyafa mata ruwa da ta farfado tace wayyo mijina sai tayi farrrrr luuuuu da Ido sai suman karya, suna ta fama sai da kyar ganin za a gane ta sannan ta farfado gaba daya ta kurma uban ihu ta fado cikin mutane da gudu ta isa Inda Naila take ta Kai hanu zata shaki Naila,lokacin Naila zuciya taci karfinta hannunta ta rike gam iya karfinta ta lankwasawa Mummy yatsu,Kara da Ihu Mummy ta tsala tace a dake ka a hanaka kuka ga Mari ga tsinka jaka, ta sake Kai daya hannun Naila kamar Dan biri tayi tsale ta dane Mummy ta shake Mummy,Misam a ransa yace tunda yaron can yake fada haka yana da kamshin gaskiya ya kamata ayi bincike me tsanani.

Mummy ta kwace kanta da kyar tace namiji ya rungumeni Kuna kallo wayyo...namiji ya rungumeni fasiki ne, Naila hawaye baya tsayawa a kumatunta Taga dai Maza manya sun shiga part din Alhaji Aliyu ana Masa sutura, da kanta ta taka gaban police da suka shigo ta mika musu hannayenta biyu tace cikin turanci ku tafi dani muje nasan Allah zai fitar Dani,sai lokacin kowa yayi mamakin Jin turancinsa ba kowa ne ma ya iya irin nasa ba Dan kuwa Naila ta iya turanci ba karya.

Yan sanda suka sa mata sarka a hannu ta shige mota da sauri domin kallon da ake mata gwara ta shiga motar taji sauki tsoro take ji kar a gano macece ce shine damuwarta kawai, suka ce ai kuwa duk mutanen Dake gidan abin ya faru sai an tafi dasu har Mummy, Tagwadas itama kuka take domin itace ta jawa Naila wannan masifar haka ta daka tsalle tace nima a tafi dani,sai masu gadi suma an tafi dasu,Mummy tana an kashe min masoyi ta shiga motar Yan sanda aka tafi dasu,sai Yan uwa a gidan suna zaman makoki aka Masa sutura aka kaishi makwancinsa aka ci gaba da zaman makoki,wayoyin Ashraf Spark sunki samuwa dama haka yake yi ya tafi waje bazai kira kowa ba,da yawa ko number dinsa ta Nigeria wasu basu da ita,ko ka kira ma sai yaga dama zai dauka.

Sai Kamal aka sanarwa ya sanar Masa,yace shima Bai kirashi ba,Daddy yace to idan ya nemeka ka fada Masa tunda shi bashi da hankali,Dake da yawansu sojoji ne wasun su duk basu wani ji abin sosai ba sun Saba ganin mutuwa da kisa da cases daban daban.
Bayan kwana uku ana bincike amma Naila baza ta fita ba Sam, gaba dayansu case din kotu aka mika su,amma Mummy sai da tayi kutun kutun aka Maida karar can kotun Kano sai kudi take kashewa lallai ayi sauri a yanke hukunci kar bincike yayi tsanani a ganota.

Sanda aka sanarwa da su Mohsin me ke faruwa hankalinsu ya tashi matuka ba kamar Mohsin da suke shiri da Naila,yafi kowa shiga wani hali sai Abbansu shima ya damu sosai,Umma kuwa bala'i ta hau yi tace Yar iskar yarinya ce bata Jin magana,taurin Kai da ketare maganata shi ya jefa Naila a wannan halin,nayi Imani ko kaffara bazan yi ba kin Jin maganata da Naila ke yi shi ya jawo mata sai da nace kar ta siyar da maganin Nan bana so Bada yawu na ba,amma jarabar taurin Kai da jahilci da hauka shine ya ja mata ai gashi Nan hukuncin kisa za a yanke mata Allah yasa ba ita kadai na Haifa ba,nayi nayi tayi aure gata da masoya taki ji ai gashi Nan,Kuma wallahi babu Mai zuwa Kai mata ziyara a nan gidan sai taji jiki a gidan yari.

Abba yace koma mene ke kika jawo ke kika turata,to na turata baza kaje ko kotun ba wallahi,ance an kawo shariar Kano to baza kaje ba,nima baza ni ba Kai duk gidan Nan,Hidaya tace Haba Umma ke kika haifeta fa Dan Allah kiyi hakuri sharri aka mata wlh baza ta iya kashe wani ba,shima kaninsu yace wallahi sister baza tayi ba ni dai Ina tausayinta,kanwarsu ta karshe itama tace nima haka bana bayan Umma.

Umma da bala'i tace to naga Wanda zaije kotu ko an yanke hukunci naga me zuwa ziyara gidan yari,Hidaya tace nidai ance soyayyar Uwa da yaranta daban ne amma ke Umma taki ba haka bane, Umma jaka ta dauka ta fice an rasa Ina take zuwa tunda cikin ya Dan Kara girma Umma kullum sai ta fita ta dawo ko ina take zuwa oho Kuma idan zata dawo sai a ganta da fara'a ashe warin gardi take shakowa ko warin taba sigari.

Mohsin Kam baya iya bacci sabo da halin da Naila ke ciki kullum a cikin damuwa yake,gashi su ba masu kudi bane sai rufin asiri,ita Kuma Hanan matarsa ta takura Masa ita baya mata soyayya baya kulawa da ita sai tunanin kanwarsa,bashi da lokacin fada da ita sai dai addua da yake faman yi Allah ya fitar da Naila.

Gashi Umma ta Hana kowa zuwa kotu har sai da Alkali ya bukaci ganin iyayen Naila sannan ala dole yau za ayi zama na biyu a kotu shine Umma,Abba da Mohsin suka halarci kotu,ana jiransu ana cewa zasu shugo aka yi yuuuu dangin Mummy da na mamaci mijin Mummy suka zuba musu Ido,ga sojoji a kotu da kaki duk a layin Mummy suke tun a Nan Mohsin a ransa yace Nailansa baza ta kubuta ba dole tayi prison,sai dai ko nan gaba Allah yayi ikonsa.

Naila tana tsaye a cikin Inda Wanda ake tambaya ke tsaiwa ta Kalli Umma suka hada Ido,Umma kuka ya taho mata tayi sauri ta dauke kanta sabo da uwa ai dole uwa ce,Abba kuwa tuni Yana ta sharbar kukansa dama kadan yake jira,Mohsin ne ya Kalli Naila tana Nan da riga da wandonta na Maza,suka ga ta koma namiji ko hular babu a kanta an cire a Inda take tsare, dama Tagwadas ta fada musu komai tace su rufa mata asiri kar kotu ta sake ganowa macece tayi shigar Maza Naila baza ta tsira ba za ace lallai tayi kisan me yasa tayi shigar Maza.

Naila Mohsin ta kalla idonta ya ciko da kwalla ta shanye kukanta sai hannu ta dagawa Mohsin tana murmushin karfin hali, an hana magana ba dalili amma sai ji aka yi tace Yaya Sandata itace gadonka tana gidan munafukar nan wacce ta min sharri,magana alkali yayi ko kulashi bata yi ba tace Yaya ka tabbatar ka dakko sandar nan tana dakin da aka bani ka rike ka dinga tunawa dani kafin na dawo,Abba ka daina kuka zan dawo fa Inshaallah verysoon ana yanke daurin rai da rai Banda ni ban aikata ba Allah zai fitar dani ko Bada sanadin kowa ba,ka rubuta ka ajiye kamar na fito,ku daina wani damuwa ni jajirtaccen namiji ne, zuciyata da karfinta zan iya da gidan yari ko sojoji ne a ciki fitowa zanyi bare wasu gandrobobi,Ni Jamilu na fada muku ko ta Yaya sai na fito Dan bakin ciki sai dai ya mutu ta Kalli alkali ta karasa da gwalo tana Masa gwalo .

Naila tana ta masifa a kotu ko alkali shuru yayi Yana kallo wani abin ma dariya Jamilu yake bashi sai ya ganshi kamar mace in yana wani abin,ta Kalli su Misam da sauran matasan kyawawa kamar su suka yi kansu ga kudi,tace kartan banza kartan wofi kunyi kunyi kyawun banza banza,sojanku bai da amfani tunda baku da CCTV, baku iya kama me laifi a family dinku kunyi asara,Kuma wallahi idan na fito a kanku zan dira duk sai na fanshe wahalata ta gidan yari,haka kawai ko uwata bana yiwa aiki zaku sani bautar iska a gidan yari,ta Nuna Mummy tace kanki kika cuta,naji ana ta zancen wani Dan iskan danki a nan wai Ashraf ku fada Masa sakona kafin na fito ya saurari zuwana gare shi har ta kansa zan bi,gwara da naji kinfi sonsa zaku ga tsiya,Naila bata San Spark ake cewa Ashraf ba,bata ji sunce Spark ba gashi baya kasar ma amma ta dauki Karan tsana ta dora Masa tace a kansa zata huce.

Mutane suna ta kunshe dariyarsu,Alkali kuwa sai da ya Dara a wajen,Sabo da ba wata hujja Naila bata da hujja yaso ya kubutar da Jamilu amma rashin hujja shine sannan yaji kudi ta wajen Mummy ta antaya Masa kudade, Kuma ba kotu ce ta musulunci ba bare yace suyi rantsuwa.
Lauyan Mummy daga ya tambayi Naila Abu sai tace ae hakane nayi, in ta gaji da tambayoyi tace na gaji ni ku yanke min hukunci na tafi na huta anbi an isheni, Duk da haka ba a yanke hukunci ba sai da Alkali ya dake sharia yace sai an sai an sake zurfafa bincike,Nan ma Mummy ta saki kudi ta karkashin kasa.

A zama na uku binciken gawar tun kafin a binne
Gawar da aka auna an tabbatar guba Alhaji yaci ya mutu,sannan an dakko jakar Naila an kawo kotu an tattara maganin gargajiyarta an Kai an auna suma suna dauke da sinadarin guba Kuma irin wacce Alhaji yaci ya mutu,Mummy sai murna take tasan kulla kullar da tayi,babu yanda za ayi da Naila dole hukunci ya hau kanta,ita ta matsu ma a yanke mata hukunci ta huta da tsareta da akeyi cikin Wanda ake zargi sannan tsoro take ji kar a gano ita din macece, dole Alkali ya yanke mata daurinta na rai da rai a gidan yari yace kamar yanda ka furta in kana da gaskiya Allah zai fitar Da kai kayi lafazi me kyau kana da tauhidi Jamilu.

Naila tace oho Kuma dai nidai bazan ga mutuncinka ba tunda ka kare sharia da wuri ba wani bincike,a wannan na karshen Mohsin ne yazo kotu kawai shi kadai,baiyi kuka ba,Naila ta kalle shi tace karka yi min Kuka ni ai zaka dinga zuwa ziyara, ni Namiji ne me dauriya, Ma'aikatan ne suka tasa keyar Naila wato Jamilu gaba,Zasu wuce ta gefen Mohsin ta dafa shi tace sai kazo ziyara ranar akwai shoki wlh, Yaya ba komai karka damu....karka damu Yaya.....zan rike kaina, a haka aka wuce da ita Jikin kowa a sanyaye,babu Wanda baiji Tausayin Jamilu ba,Shariar Sam da ganin yanda aka yita kasan alkalai da lauyoyi sun Sha kudi,kowa Yana da kokonton ba Jamilu ne ya aikata ba da alamar tambaya kawai babu mafita ne,ga Mummy ta iya kulla kullar tsiya.

Mohsin ya fito zai hau lifan dinsa Yana goge kwallarsa da handkerchief Misam ya dafa shi ya tsaya,hannu ya mika Masa suka gaisa,yace karku damu ku bari danta ya dawo ya iya kwatowa mutane hakkinsu Yana da tausayi na tabbatar da Yana kasar wannan abin bazai faru ba baza a kulle Jamilu ba, Mohsin yace kaddara ce ba damuwa,bani number Dinka sabo da duk halin da ake ciki gaba zaka ji,Mohsin ya bashi number suka yi Exchange sannan kowa ya tafi,su suka bi jirgi suka koma Abuja,Mohsin yayi gida.

Yana shiga gida ya iske Umma tana ta kuka a Palo tana cewa duk rashin Jin Naila ne ya jawo gashi Nan nasan ma an yanke mata hukunci,Mohsin yace ai kuwa sai dai ayi mata addua,wlh ba Wanda zaije mata ziyara da wuri tunda taurin Kaine da ita taurin kanta ya ja mata,Abba Yana zaune ya zuba tagumi Yan gida sunyi jugum jugum ana ta zuwa musu jaje,Matar Mohsin tana zaune a gidan da yarta ko a jikinta ita a ranta ma Allah ya Kara takeyi ta tsani Naila,Hajiya Tagwadas itama tana gidan wajen Umma harda zazzabi tace jarabar kwadayi na ne ya kaini, gashi ta hannuna abin ya biyo wayyo ni Tagwadas Ina zan sa kaina,Mohsin ficewa yayi kawai ya tafi gida.

Spark bai San komai ba sai da yau Allah yasa ya kira Kamal,Kamal ya haushi da bala'i yace wallahi abinda kake yi ba tsari bai dace ba,sai ka bar me kake yi ka dawo Nigeria Mijin Mummy Dinka ya rasu,kamar saukar tsawa haka Spark yaji maganar, yace me ya same shi? sai da cuta ake mutuwa magana baza ta yuwu a waya ba malam kawai ka dawo kasar sai kaji komai.

Spark kashe wayarsa yayi ya kira Mummy tana kallo taki dagawa tayi fushi da shi,kiran duniya taki dagawa,Mima ya kira duk suka ki dagawa,kowa ya kira a family bazai daga ba,sabo da ya batawa mutane rai,a ranar da yamma ya tattara ya sauka a Nigeria, Kamal yaje ya dakko shi a Airport suna tafiya Yana bashi labarin komai tiryan tiryan har ya gama Jin komai da ya faru,yace wannan yaron karya mummy ta masa,ai shi yasa aka so kana gari time din cewar Kamal.

Spark ya furta yanzu Yaron life in prison? Wlh baka ganshi ba son kowa kin Wanda ya rasa kyau dai a wajensa har da na siyarwa wlh kamar mace mace,tsaki Spark yaja yace ana zancen hankali sai ka kawo shirme, bari zanbi a hankali Inshaallah wannan yaron bazai yi life in prison ba,idan Mummy ce ta aikata gwara ita tayi zaman gidan yarin.

Naji mutuwar nan sabo da mijin Mummy shi yace na daina Masa magana,na biye Masa sai watarana kawai nake Masa sannu amma baya amsa min ban so Hakan ba bro gashi ya wuce,ban kyauta ba,Kamal yace shi yasa aka ce a dinga hakuri da rayuwar duniya yanzu gashi nan ai ya mutu,idan ance ka canja hali Kai a'a.

Ya isheka Kamal a cikin zafin mutuwa nake karka dameni cewar Spark,mutumin nan sai na bi Masa hakkinsa,Allah sarki rayuwa,Kamal yace watarana mutuwar kanmu zata zo,a fusace Spark yace kanka dai Banda ni,yaushe nazo duniyar ni yaro Dani,Kamal ya dinga dariya yace ake dauke jariri ma karewar rashin dadewa a duniya,Ashraf yace to na ebo shekaru da yawa inshaallah
A haka suka karasa gidan Mummy.


Labarin abinda ya faru kenan Naila ta tsinci kanta a gidan Yari bangaren Maza.

Ci gaban labari.


Free page

Masu bukatar siya 300

0175487861
Asmau Garba Muhammad Gtbank


Katin MTN
08061929616


Yan Niger ga number ku nemi wannan
+227 90 79 59 39




Sharhi please




AsmaBaffa
[12/5/2023, 2:05 PM] AsmaBaffa: 🏫 TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI



16-20


Official

By
AsmaBaffa



SADAUKARWA
GARE KI❤️
AIDA MAMAN TASNIM




Page naku ne
Najida Aliyu Bicca
Mhiz Awwal






*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262





Yau ma akwai kidan koroso da rawa kusan kullum sai an musu kidan koroso da rawa a gidan yari amma iya bangaren masu daurin rai da rai watarana harda Yan solo ana kawo musu domin nishadinsu,wani lokacin Kuma akwai ranar Yan drama suma suna zuwa ciki bangaren Yan life in prison a musu sabo da nishadi,yau ranar koroso ce za ayi da yamma har zuwa magriba.

Ko wanne yazo Inda Tantiriya Naila yau tazo tayi kallo itace bakuwa, Naila tace ba kidane a gabana ba in fita daga gidan nan shine target dina,duk kansu Jin Jamilu suke a shashasha,Dan Indo Yana Shan sigari yace idan ka fita kayi magana na baka babban aiki wlh,kaje a baka bindiga banza ka zauna ana maka sharri a banza kayi na gaske akwai binda Dan kutmar...kai Allah, Naila dariya tayi tace Allah ya tsare ni da kisan Kai tana maganar Yan Daudu harda shanye hannu, tace ni Jamilu duk wani iya shege Dani ake farashi,ai mune wakilan shedan ehehehayye...Dan Indo zuciyarsa ta buga wani birge shi Jamilu Dandaudu yayi,haka kawai yaji Yana masifar kaunar Jamilu,a ransa yace Ina ma mace ne Jamilu,ko ace ni Dan neman Maza ne da na kwashi harka a wajen Jamilu.

A hankali ya faki idon Naila Tantiriya ya rike damtsenta tare da jawowa,yaji wani laushin masifa ya wani jawo shi talau,ashar ya dura tare da ja da baya ya dafe kirji Yana kallon Jamilu yace amma Kai tun a cikin uwarka dama Dandaudu ne?, Naila ta tsuke baki tare da furta tunda na fado duniya ni dama babarmu tace kukana da nake yi maimakon aji Inya Inya sai aji Ina cewa Zaniiiiii....Zaniii....idan na shide sai aji kukan ya canja sauti Dan.....Dankwaaaaaa......liiiii....DanIndo ya kwashe da dariya, Muler Dake gefensu Yana Jin hirarsu Yana ta dariya yace Kai Jamilu amma uwarka ta haifo Dan iska,Naila tayi fari da Ido tare da shanye hannu tana tsuke baki ta wani lashi labbanta sannan tace ya ranka ka daina gatsa sunana kamar kana gatsar rake ka kirani da Jamilu Tantiriya haka nake,sai ta dauki mintuna kafin tayi magana sai ta tsaya ta gama karairaya da wani lankwashewa sannan take magana.

Wani me suna Farau Farau shine ya Kalli T.k ya Masa rada yace nifa tunda aka kawo yaron can Jamilu wlh na fada matsananciyar kaunarsa ni ba me neman Maza ba abin nan Yana damuna,Tk yace abinda zan fada Maka ka rigani kenan wlh abin Yana damuna,kusan duk mutanen gidan Nan kaunar Jamilu suke anya ba asirin farin jini ne da shi ba kuwa,Cikin rada Farau Farau yace kaga kaga kalli Yana murmushi Kalli... Dan Allah baiyi kama da mace ba? Tk yace a macen ma full option,ance jikinsa laushi kamar me,muje mu taba Muji,Muler da Tk suka taso da niyyar taba hannun Jamilu su ji,sai kuwa Dan Indo yaji wani uban kishi ya make hannun Muler yace wlh kana taba Jamilu sai na rushe Maka hakora,sun san DanIndo sai suka koma Inda suka taso,Naila a ranta taji dadi Sam DanIndo ya tsaya mata ba Wanda ke kawo mata wasan shirme sabo da suna ganin abokin Dan Indo ne.

Naila ta juya ta Kalli Dan Indo tace Ina baka labari abokina,yace Ina jinka,ai Ina fada Maka ni idan nazo waje shedan ya kan bace yace oga tazo har gisuwa yake kawo min ida na shirga wata tsiyar,badan gidan yari ba da yanzu na kashe auren Yaya na, amma kisan Kai bada ni ba,Dan Indo ya furta mene a cikin kisa ai kawai Wanda yayi akuya kawai ka caccaka Masa wuka,ai ni billahillazi da me zarto nake amfani cewar wani me suna Baballe da ya tsomo musu baki, shi da yake babban Dattijo ne ma,ya kunna sigari yace maganin shege sai Dan Banza Tantiriya Jamilu,ai karka sake a kawo ma raini ko a gidanku ne,Naila tana Jin halin kowa iri iri.

Tunda tazo gidan yari Dan ragowar tsoronta ya gudu, Uban Dawa yana wajen yace ni ka san daga Ina tsiyata ta fara? Maza nakewa fyade,in ketawa Namiji haddinsa ba komai bane duk girman gardi nayi niyyar lashe Masa Timber karya yake ko ubansa waye,Baki suka hada suka yi wata shaharriyar shewa da ihu harda,suna da masifar yawa a wajen sun hada uwar daba,wani da ake kira da Goje yace ke Tantiriya wanne tsiya kika yi a kasar Nan ta alfahari? Wacce kai da kanka Jamilu idan ka tuna kake jinjinawa kanka? Naila tace Ni Jamilu nine wanda na saka Budurcina a caca tun farkon fara Daudu nawohoho suka furta kamar Wanda suke shuka abin arziki haka suke hirarsu,

Fitsara da rashin mutunci a cikinsu ba a magana,akwai Yan iskan da su tsirara ma sukeyi watarana a ciki uban kowa ya gansu,duk wani sabon me laifi da aka kawo shi gidan yari Wala mace ko namiji tofa kowa sai yaji labarin an kawo sabo, sai Kuma an San waye,duk iskancin mutum akwai Wanda ya ninka shi sau dari a ciki,suna zaune Naila taja DanIndo da Goje wanda suka fi mutunci tace kwana nan zan bace a gidan nan,Goje yace ta wacce hanya Tantiriya? Naila tace ta bangaren Mata zan koma nayi shigar mata,dariya suka saki,tace wlh da gaske nake,ta bangaren Mata Anfi samun damar guduwa idan ta kama,daga part din Mata sai bayan Daji Kunga kuwa sai fecewa,Goje yace ai kuwa kana haurawa zaki karairaye, ka Kalli uban katangar gidan,tunaninka katangar banza ce,a banza zaka ga kartai sun kasa tserewa, gashi yanzu an Kara kwalabe da wayoyin shocking kana tabawa sai mutuwa,Naila tace bazan yarda daku ba,to munji yanzu ta ya zaka shiga bangaren matan har ka zauna ba a ganeka ba,Bari zaku gani bari yayana yazo zai kawo min kayan Mata ku gani.

Bikin Spark an saka rana an saka bikin a kurkusa, babu bata lokaci Mummy ta matsa Masa ba yanda ya iya,sai masifa yake yi,yau gidan su Asmau yaje har

Please Login or Register in order to submit comment