Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hadu da mace ba ji yayi kamar ya rungume Jamilu Terror, ai tashi yayi ya fice daga dakin Yana salati a ransa,shi kadai uban zufa ya hada

Yace Ina zan sa kaina yau naji Ina son Namiji,a daren malam Jilani yace saukar Qur'ani ya zama dole, a daren haduwa sukayi kowa ya bude Qur'ani kwana suka yi suna addua Allah ya cire musu son Da namiji Jamilu,Naila tana ta baccinta gefe daya ita hankali kwance ta samu dakin malamai ba ruwanta,su kuwa suna ta surfa addua akan Allah ya tsare su da Jamilu.

Washe gari da safe mazan gidan yarin masu uban yawan masifa Yan matasa dattijai,tsofaffi duk gasu nan iya kallonka da munana da masu kyau duk gasu nan,duk kalan laifinka akwai ubanka a ciki ko wanne da bangarensu, bangaren mata daban na maza daban,haka ranar ziyara sai an gama da maza sannan a bude mata ba Wanda ke haduwa da wani tsakanin mata da maza,gashi Sabo da lalacewar ta kasar mu dakuna sunyi kadan,toilet,komai babu na kirki,haka uniform ma babu sai wata riga da ake bawa Maza lokacin ziyara,sai sutura kayan gida amma basu wuce kala uku ko hudu,haka bangaren matan yawanci basu da bra,wasu Kuma suna da ita,wacce tafi wata karfi ma zata kwacewa wata ko an kawo mata daga gida,Naila dai itace mace daya kwal a bangaren Maza Wanda babu Wanda yasan Hakan har Ma'aikatan kaf a namiji ne Kuma ana zargin Dandaudu ne,Naila bata da ko bokiti ,gashi wai a gidan Yari zata yi gayu.

Yanda take nunawa Dandaudu ne kawai, tana zaune a cikin dakin Malaman tace akwai ruwan zafi? Ya Sheikh bana tsarki da ruwan sanyi sabo da na koma mace ni, na hana kaina amfani da ruwan Sanyi,tana magana tana zuba uban karairaya wai dole Dandaudu ne,gaba daya malaman Nan suka saki baki suna kallon Jamilu duk ya tafi da Imaninsu,cikin rada da tsoro Malam Sharu yace addua bata karbu ba mu sake dukufa wlh, Mallam Garzali ya a hankali ya saci kallon Jamilu sai kuwa suka hada Ido,fari tayi Masa,da sauri ya yayiwa Sharu magana kasa kasa yana yi min fari wallahi,kansa ya sadda kasa duk ya rasa Inda zai sa kansa.

Naila ce ta shiga aika musu da fari tare da dage musu gira,Kasa karatun suka yi,Kamar ruwa ya cinye su ba Wanda yayi motsi,sai zuwa mazan bangaren nasu keyi suna kallonta ana labarin an kawo kyakyawan Dandaudu Dan matashin yaro,kowa yazo sai ya tafi da kaunar Dandaudu Jamilu a ransa sabo da kyau da farin jini irin na Naila,Naila taga suna ta zuwa kallonta ita bata sani ba,tace bayin Allah ruwan zafi nake tambaya zanyi tsarki mu yanda muka koma mata ai mata sai da ruwan zafi harda yin tafi da hannu Irin na Yan Daudu,suka dinga tuntsira mata dariya ganin namiji matashi me kuruciya ta karfi ya koma mace, a dakin malaman ba Wanda ya bata amsa karshe ma kowa Uzurinsa ya fita,Naila tashi tayi tana tafiya tare da zuba hannayenta a aljihun bujen wandonta ta fito

Ko Ina mutane ne lungu da Sako ba masaka tsinke,Naila tace ashe duniya ce guda a gidan Yari,tana zuwa taga uban layin botikai da fanteku harda languna tun na zamanin da,tana zuwa ta dauki botikin wani na roba an cika shi da ruwa ta dauke ta Kara gaba, da tambaya ta samu taga Toilets gasu nan ko wanne ta leka duk an lalata su wasu Kuma Kashi ko Ina dama maza ba tsafta ba wasu,Naila ta rasa inda zata shiga dole sai da ta wanke toilet din sama sama sannan tayi wankan ba sabulu ta, ta daure kirjinta tam tam da yankin Atamfa ta Maida kayanta ta shirya tsaf sannan ta fito ta Maida botikin,wasu shahararrun kartai suka taso zasu yi mata duka Allah ya kawo DanIndo wanda kowa tsoronsa yake a gidan mugu ne na karshe,yana kallon mazan yasan yaran Goje ne,yace me Jamilu ya muku? suka ce ruwa muka ebowa Goje tun safe muke layi kafin muje mu dawo ya dauke yayi wanka,Naila tace ku fadawa Goje din Dan babansa na dauka kayan gomnati ne muna da hakki,dariya wasu suka dinga yi da kyar DanIndo ya kwaci Naila yace ku bari zai zuba masa,wani ya gama buga ruwansa Sabo da zalunci Dan Indo ya dauke ya zuba a bokitin Goje yace kuje,Ya Kalli Jamilu Terror wato Naila kenan yace jeka ka bugawa yaron can wani ruwan

Naila tace bazan buga ba,wani gigitaccen Mari Dan Indo ya hada mata kumatu biyu sai gani akayi Jamilu tuni ya fara buga ruwan tana kuka sai da ta cika botikin sannan Dan Indo yace ware daga nan.

Dan Indo bai taba jin fata me laushin ta Jamilu Dandaudu ba,ya tsaya sai kallon tafin hannunsa yakeyi shima Yana mamaki,Sam ba fatar namiji bace da shi.

Naila tana sakkowa sai ga wani Ma'aikaci ya tari Naila yace kai waye da za a hana Hawa Saman tuka tuka kazo ka hau, uban waye ya aikeka? Naila da taurin Kai take kamar ba ita ke cin duka ba,ta Kalli Ma'aikacin ta nuna kanta da yatsa tace nice Tantiriya Jamilu ko a garinmu haka sunana yake kaina akwai kwari ba a cina da yaki,ma'aikacin ya Kalli Naila an zagaye su ana kallo,yace Zaka ga Tantiriya munga Iyayenka a taurin Kai ma sunyi laushi a nan gidan bare Kai da ka Maida kanka Dandaudu gafalalle, Naila tace banda ni cikakken Tantiri ne ni Ina kallon ku Ina Maida kaina namiji,Kai Ma'aikaci kayi a hankali zan iya tsille ma takashi ato, su kansu ma'aikatan tsoro suke ji,juyawa yayi zai tafi, Naila tace nayi marking dinka sai na sa maka guba,sai na farke Maka takashi,Dani kake zance,ma'aikatan sun Saba da tsagerancin Yan bangaren daurin rai da rai tunda suna gani shine karshen hukuncin,dole ya tafi.

Naila ta fashe da kukan karya tace Allah ka Saka min ni Jamilu Ina ganin rayuwa Yar Takashin ma ban samu ba tunda nazo naki yin farin jini,ana ta kyalkyala dariya,tace Mummy data yi sanadin zuwana gidan nan ya Allah kasa Danta ya mata dukan tsiya watarana.

Akwai Yan Daudu da yawa a gidan Yari da Kuma Yan luwadi wasu ma a gidan suka lalace sabo da rashin mace a kusa, tunda suka ga Jamilu Tantiriya gaba daya sai hadiyar yawu suke gashi kyakyawan gaske komai irin na mace gaba dayansu sai kaunar Naila,har da Wanda ke ciki masu hanu da shuni sai suka fara neman gindin zama wajen Tantiriya Jamilu,Naila a ranta sai dariya take shekawa su sun zaci namiji ne kowa ya kaimu da sonta har Wanda ba Yan luwadi ba.

Rafeeq zaune yake gaban Mahaifiyarsa Mima wacce ke faman kallonsa tana bin Aljihunsa da kallo tana zaro idanuwa tana kallo tace banga Aljihun ya dago ba? Na shiga uku kar dai ace haka kazo hannu yana dukan cinya, Rafeeq ba tare da ya sake cewa komai ba ya jefa hannunsa a aljihu Kudi ya zaro Wanda sun kusa dubu hamsim ya Mika mata,jiki na rawa kamar yau ta fara ganin kudi kamar ba a gidan kudi take ba ,Allah ya maka Albarka wannan waje naka na Shawarma Allah ya karo customers

Sam baka yi kalar me Shawarma ba wlh yaro kamar Dan gidan Salman Khan kalar kudi amma ficika babu,Yan mata sai rububi aljihu ba komai wannan kusan dubu hamsim din wata nawa kayi kana Tarawa? Rafeeq wani takaici ne yake kamashi a duk sanda Yazo gidan iyayensa,mikewa yayi yana Shan kamshi fuskar nan a murtuke da kyar ya iya bude Dan bakinsa yace na wuce ni yana cewa haka ya fice daga daga katafaren Palon Mima din Wanda ya gaji da tsaruwa, compound ya fito motoci ne gasu nan iri iri a gidan masu tsadar gaske gidan ko Ina sojoji ne ke tsaronsa kana gani kasan na babban Soja ne gidan..

Gate aka wangale Khalid babban Da a gidan ya shugo da motarsa lafiyayya,yana yin parking ya fito cikin kakin sojojinsa ya zuba kyau ya nufi wajen Rafeeq dake hanyar fita,Rafeeq Kai dai baza ka canja hali ba wlh kana ganina na shugo zaka tafi ai ka tsaya mu gaisa ko,Rafeeq juyowa yayi da kyar da shegen Iyayinsa ya mikawa Khalid hannu suka gaisa kana gani kasan Yan uwa ne na jini ba karya suna kama sai dai Rafeeq yafi Khalid kyau na gaske,sannan yafi gayu Dan gayu ne shi sumarsa ma askin Yan duniya aka mata,suna gaisawa ya juya yayi tafiyarsa ya bar Khalid a tsaye da mamaki yace yaron nan fa takamarsa ta fara yawa nema yake ya Koma kamar Spark, tsaki yaja ya wuce abinsa.

Shawarma Joint me kyau da shi Wanda ke dauke da katuwar wata rumfa an zuba kujeru da table masu kyau na Passion Wanda Idan mutum na bukatar zama yaci a wajen zai zauna,haka daga ciki ma akwai katon daki ya gaji da alatu Shima ciki kujeru ne da table na Yan gayu na cin abinci ga masu son zama cikin sirri,daga kofar wajen kuma ga hotunan abinda ake siyarwa nan shawarma,burger,chips and chicken da kayan sha Kuma, aikinsa yake yana ajiye Dan littafin Menu karami Wanda ke rubuce da iya abinda ake siyarwa yana bin ko wanne table yana ajiyewa da sauri,sabo da yana da lecture 4 to 5,a hankali wata mota me kyau tayi parking a gabansa da sauri ya barwa yaransa aikin ya koma ciki ya shirya cikin kana nan kaya masu kyan gaske ba karya yayi kyau ya fito rataye da jakarsa ya shiga gaban mota,ko kula abokin nasa baiyi ba,a hankali Abokin yace Rafeeq halina da Kai yanga sai kace masifa magana ma ta gagara wlh har mamaki nake da ake zuwa joint dinka siyen Shawarma Kai da Spark halinku baiyi ba,Spark ma ya fika rainin hankali duk da Yayanmu ne amma shi kake bi wlh Dan wulakanci ne turai ta kwance Masa Kai,mutum kullum ba Rahma ga shegiyar yanga kamar Dan gomna ga bala'i Kuma a gidan ma Spark ba Soja bane kaima haka amma kunfi sojojin ma,kaima ka koyi halinsa sabo da kuna gadara da kyau ko me oho, ka kyale spark yayi ya fika indai kyau ne,gashi da kudi shi idan yayi ba matsala tunda ya fika komai, shi dai Rafeeq ko kala bai ce ba wayarsa ya zaro Samsung yaci gaba da dannawa abinsa,a hankali cikin muryarsa me Dadi ya furta next month zanje Kano,me zaka yi? Ban taba zuwa ba yaron da akace yazo aiki ko ziyara ko me ya sawa Daddy guba an Yanke masa daurin rai da rai,yace kasan lokacin Makaranta sun Kai mu Egyft branch dinsu,so ban San yaron ba ban ma taba ganinsa ba,Islam Abokin Rafeeq yace Kai mene naka a ciki? dama Yan aikin nan Yan iska ne zasu iya gashi ance Dandaudu ne ma,Rafeeq yace Yaya Spark ne zai aikeni can wai yana da ja sabo da yasan Mummy dinsa yasan Halinta,yasan Kuma halin da suke ciki da mijinta Daddy, to me zaka masa Dandaudu na tsani Dandaudu? yace zanje ne nayi masa Yan tambayoyi ance sunansa Naila Hashim naji gidan Jamilu,Islam yace alright amma da mota zaka je? Kasan bani da mota muje ka rakani kawai,Allah ya kaimu no wahala,shi Spark din bazai bamu kudi ba? Yama bamu fa Yana accnt,tun daga haka Islam ne kadai yake labarinsa Rafeeq bai iya magana ba.

Naila tana gidan Yari kwananta biyar taga zalunci iri iri,ma'aikatan ma Idan kayi laifi zasu iya maka duk muguntar da suka ga dama iyakaci Idan ta asibiti ce a kaika asibitin gidan kason,ga wahalar ruwa,sai mutum yayi sati baiyi wanka ba sabo da kasar tamu ba ci gaba,kazanta kadai ya Isa ka kwashi cuta,komai yayi karanci a ciki,ga mutane masu laifi sunyi yawa ba wajen Saka mutane tunda Wanda ya saci akuya ma kaishi ake gidan Yari,a masu kudinmu Babu Wanda zai Kai musu agaji ya gyara musu tuka tuka ko toilet da dakin kwana musamman gomnati wannan hakkinta ne,musamman bangaren maza yafi Muni da kazanta za a hada mutum biyu a sarka daya a daure su ko Ina zasu je tare Idan daya zaiyi Kashi ko fitsari dole agaban daya zaiyi ko mene,Hakan yasa da yawa sun zama Yan gay suna Neman Yan uwansu maza haka matan ma da yawa Neman junansu suke maimakon a samu gyaran Halin sai Kuma a lalace a ciki,harkar daba da rashin gaskiya wasu duk a ciki suke koyowa,rashin kunya,taurin Kai da fitsara iri iri duk koyo akeyi a cikin gidan gyaran hali,Naila tana zaune a jikin wata bishiya sunci aiki sun koshi tun safe suke noma a can wani bangare suna gyara ciyawa,sun hada uban zufa,Basu samu Salama ba sai da suka yi nisa,duk haskenta tayi Dan duhu , jikinsu furu furu,Dan Indo ne ya zauna kusa da ita su ko a jikinsu har kiba ma wasu keyi a ciki,Naila bata San sanda hawaye ya fara zubo mata ba.

Dan Indo ya kalli Jamilu yayi dariya sosai yace ashe dai Jamilu Tantiriya Kai karamin dan iska ne? Da kace baka ji kai Tantiriya ne, Naila tana share hawayenta tace kana gani a haka zan kare rayuwata a wannan masifar wallahi sharri aka min ban aikata niyyar ko kisa ba,DanIndo yace da ka adana kalamanka ba maganin da zan Maka,kawai abinda zan fada Maka tunda baka da karfi sai taurin Kai ka kiyaye yiwa mutane nan rashin kunya,wlh watarana Idan suka gaji zasu karairaya ka su watsar,kayi biyayya,mun fika iskanci,Kai iskancinka na Daudu ne Amma tunda kaga muna musu biyayya to kawai kayi, kana gani dai a gabanka suka sa karfe suka cirewa Hamisu farcen babban yatsa Kuma ko a jikinsu, Naila ta goge hawayenta ba tare da tace komai ba,kafin ta rufe Ido a cikinsu aka zabi shugabanni suna sasu aiki Wanda ya kamata na tsafta da gyaran wajen kamar a makaranta,mazan sun dawo da tsawa da duka sun kora kowanne aiki,Amma Naila kin tashi tayi suka zaneta kuwa Amma ko gezau da uban taurin Kai take,Inda taci Sa'a duka gidan kaunarta suke haka kawai basu San ba gender dinsu daya ba.

Indo ce ta kwala mata Kira da Tantiriya dake yanzu kowa haka yake Kiran Naila da Jamilu Tantiriya domin ita ta radawa kanta sunan gata gata da farin jini Allah ya bata kowa Yana sonta suna daga mata kafa sosai amma bata da kunya ga taurin Kai,ta matsu iyayenta su kawo mata ziyara ko zata samu kayan canjawa da Dan kudin siyen abubuwa,a haka sai da taga dama sannan ta mike ta shiga cikin Yan gidan suka ci gaba da aikinsu amma sun rasa dalili Bata son cudanya da Maza sai ta ware kanta gefe,sannan namiji Bata bari ya riketa sai idan Bata sani ba,Hakan ya tabbatarwa da kowa ta shahara a harkar Daudu.

Naila tana noma ta Kalli wani Dan saurayi matashi kamar sa'anta ne amma ya fita girma da komai namiji da mace ba daya bane ko a halitta, suna Shiri dashi Amjad, tace Amjad ban taba ganin mace ba tunda nazo gashi har na kusa sati,oh ashe kallon mata ma Rahma ne,dariya Amjad yayi yace wlh ai in ba a Yan uwanki mace ta zo Miki ziyara ba baza kiga mace ba,Kai da kake Dandaudu Ina ruwanka da mata,Tantiriya tace to ai munfi Jin dadin rayuwa cikin mata sune muke kama, Allah sai dai irinku Maza haba shi yasa naga maza suna ta Neman junansu.

Ni a dangina ma bamu da mazaje Samari sai wani Dan banzan kanina me tafiyar tolo tolo sai uwata sai ubana, Wanda zai iya zuwar min Yaya Mohsin ne,kaga Ina da saurayi Kuma nasan zaizo, Amjad Baki ya tabe tace Dan uwanka ne fa namiji,Jamilu yace kamar ka sani yanda nake son Gambo beauty sai baza ayi ba ta furta da sugar Yan Daudu,Amjad ya sheke da dariya yace kunyi asara wlh.

Amjad ya sake cewa hala kai Hariji ne ne ko kana sex tun a gida? Yo mu yai muna layin gidan Kashi cewar Naila.

Naila a ranta tace a gidan Nan nasan ma cuta ta kamani ta ciwon sanyi sabo da kazanta wlh har kaikayi nake ji a gabana tabbas na kamu da ciwon sanyi.

Wani shahararren Dandaudu ne da ake kira da Skoler yazo wajen Tantiriya Yana rangwada yace Kawas ya kamata na fada miki kiyi taka tsantsan da toilet mu mata muna kamuwa da ciwon sanyi in kinji gaba na kaikayi sai kiyi magana zasu kaiki asibiti a baki magani ahayye ya tallafe kirji ya zaci da gaske Naila Jamilu ce,suna ta hirarsu har kusan dare sannan suka hau layin karben abincin dare abincin Dan kadan gashi ba Dadi,masu kudi suna ta siyen abinda suke so,a hakan ma Idan wani yafi karfinka ya samu ya masgeka ua kwace ya hade du ya cinye.

Naila tana layi aka zubo mata Miya da Katon sandararren tuwon masara,ta Kalli abincin ta bata fuska tace Kai masu girki kuji tsoron Allah Miya kamar yawun kaza haka gomnati tace kuyi? Wani Ma'aikacin cikin fursunonin yazo zai kwade Tantiriya Naila da duka sai yaji ya wani shiga ransa sai ya koma yayi mukus ya juya, amma Naila harda tana Allah ya Isa wlh ma'aikatan har sun gaji da Halin Jamilu Tantiriya duk abinda akace kar yayi sai yayi, duk mugunta iri iri Amma bata jin magana,rashin kunyar ta da taurin kanta kullum karuwa yake sabo da basa taba dukanta kowa jinta yake a rai tunaninsu ma namiji ne.

Washe gari da yamma yau ta samu tayi wanka Dan Indo ne Ara mata sabulu ta fito gabanta Yana ta mata kaikayi cutar sanyi ta kamata,ta rasa Inda zata sa kanta gashi ba abin ta fada ba a gano ta,Dama kayan Dan Ido ta Ara ta barma a jikinta a wanke suke,ta wanke nata tas ta shanya su,kayanta suna bushewa ta koma toilet ta shirya ta Saka abinta, yau fes take sai kaikayin da gabanta ke mata na hauka cikin dakinsu ta shiga Wanda yake da malamai a ciki,gado ma Babu na kirki wasu duk a kasa suke kwanciya ko shimfida babu a masu kwanciya a gado har Tantiriya Jamilu,,ta Ari bargon malam Sharu tace bani da lafiya bani aro ta kwanta ta lullube jikinta da shi a ciki ta samu ta tattale kafa ta hau sosa gabanta ba ji ba gani,a hankali kasa kasa tana cewa a bani cokali wannan susar sai da cokali.

Naila tana susarta tace yau Bado Yana cin ubansa da Susa,a fili Ashe ta furta Dariya su Malam suka yi sun zaci iskancin Yan Daudu ne kawai,Malam Jilani yace mene Bado? Naila tace gaban mata, ku baku ga yayi kama da Bado ba? Bado wannan Abar da take fitowa a cikin ruwa,Idan baku San Bado ba kuje kuyi bincike,malamai sai kunya ta lullube su,Malam Sharu yace Dan Allah ka koma cikin Yan uwanka Dandaudu Bai kamata kazo cikinmu ba muna malamai.

Rafeeq gida ya shugo cikin takunsa na yana kamshi yayi Sallama a gidan ShimaA wannan gidan da gani kaga gidan me hanu da shuni gidane na gasken gaske komai na more rayuwa akwai duk da gidan da iyayen Rafeeq suke yafi kyau sosai Amma wannan ma ba baya ba,ga motoci nan hadaddu masu tsada daban daban,Rafeeq yana shiga katafaren Palon gidan wata matashiya ce baza ta wuce 50yrs ba da kuruciyarta kyakyawa son kowa kin Wanda ya rasa ga kyan Kira da diri,tana ganin Rafeeq ta saki murmushi tare da amsa sallamarsa,kallonta yayi ya zauna a hankali yace Aunty barka da hutawa,Wacce ya Kira da tace Dana ya aiki ya Kuma school kana garin shine sai yau zaka zo min? Sai da ya dauki lokaci sannan yace kiyi hakuri Aunty Exam muke yi ne,kin San indai lafiya ai zanzo ko? tace na sani to ya school? normal Aunty,bari na kawo maka abinci,me kika dafa ne? Hmmm zai wuce tuwo ne da kyar fa ma ya bari nayi tuwon, kasan komai dai yau ma ko kudin cefane bai bayar ba,ayi mutum kamar talaka Wanda bai gaji arziki ba,Hawaye ne ya zubo mata tace Ina so ko Yaya ne ya so ni ya kyautata min amma Hakan ya gagara sai ma kuntata min da yake kana gani dai, Aunty wai waye naji ance an kaishi prison akan gidan su Spark? Hankalin Aunty ya dawo kan Rafeeq, tace wani Dandaudu ne marar Imani ya kashe shi,daga kawoshi gidan mutane,Aunty ta kwashe labari ta fadawa Rafeeq,Rafeeq yace Allah ya kyauta shi kam a ransa bai yarda ba Sam, yana da ja akan kisan domin yasan tsakanin Mummy da Mijinta irin zaman da suke, tace sunansa ma wai Jamilu Hashim.

Rafeeq yace hmm kawai sannan yace kina da kudi kuwa? tace da kyar ma na samu na siyan kayan Miya Sweetheart, Rafeeq ya mike tare da zaro kudi dubu goma yace kiyi hakuri da wannan kin San Yan Makaranta,ta Mika hannu Zata karba kenan me gidan ya shugo sanye cikin wata peach shadda Yar gaske yana sheki yana kamshi Shima ba wani babba bane,Rafeeq yace Sannu da zuwa wani kallon banza yayiwa Rafeeq yana daure fuska yace bana hanaka bata kudi ba,iyalina ko naka bana son shishigi,wato kana nuna min ban iya ruko ba ko?to baza ta karba ba jeka da kudinka,kafa dameni Karka bari na hanaka zuwa gidan nan,Ina daga maka kafa baka gani, Rafeeq kudinsa ya karba ya Kalli Aunty a sace suka hada Ido ya faki Ido ya tura mata kudin a kasan kujera tana kallo ya ajiye ya fice abinsa,Wanda ta Kira da Abban Na'eem da Na'eema ya fara yayyafa mata ruwan masifa yace wlh ki kiyayeni Rumaisa Ruma ki kiyaye ni banza shashasha,wato tona min asiri kike sabo da kin raini Rafeeq gani kike kamar ke kika haife shi karki manta Dan Yar uwarki ne,Yar uwar taki ma da bata son kike shiga sabgar danta in Banda masifa ma kina juya bakya haihuwa ki hakura da rike Dan wani mana yaja tsaki,tace kayi hakuri abincin fa? Bana ci ya juya ya wuce part dinsa fuuuuuu dama ya Riga yaci nama me rai da lafiya a wani joint me tsada a koshe yake abinsa.

Su Naila ana gobe ranar ziyara dukkansu murna suke musamman Wanda Suke da tabbaci za a zo musu daga gida,ita kuwa Naila bata murna domin Iyayenta Basu yarda da ita ba shi yasa suka ce ba ita ba su Kuma babu Wanda zaizo wajenta ko an kaita can,tasan halin Ummanta ,Amma haka suke ta tsafta suna gyara jikinsu kar azo a gansu cikin kazanta,Naila tana Kallonsu ta zuba tagumi a inda ta idar da Sallar la'asar Sallar ma a boye take yinta,a haka ma da ya ta shugo da Karamin mayafin a cikin wandonta a boye,duk Allah ya tsallakar da ita ba a kamata ba,Addua take Allah ya rufa mata asiri kar a tarfa ta,sai ta bari an fita makaranta take buya tana yi ba nutsuwa sabo da tsoro, kullum itace karshen fita school tace ya Allah karka bari a kamani ko a ganta da mayafi kowa yasan iskancin Yandaudu sunyi Imanin baza a kawo musu Mace gidan ba shi yasa duk suka amince Dandaudu ne,Allah yasa ma basu kamata ba har yanzu,kullum addua take kar a kamata har ta fice a gidan,kullum cikin faduwar gaba take.

Wani Wanda ake kira da Skoler Dandaudu baki har kunne ya samu Dandaudu me kyau kamar mace,wajen Naila ya karaso Yana rangwada ya furta budurwata ke wai baza kiyi wankin ba? Ai ko sabulu sai na Ara Miki ki wanke kayanki, ga wando da t-shirt Dina ki Saka,Naila tace ni ai ba Wanda zaizo min wa nake da shi Babana da Ummata sunce baza su zo min ba,nafi sa rai ma da Yaya Mohsin amma nasan halin Ummanmu ko zan mutu baza su kawo min ziyara ba,Dandaudu Skoler yace iyyee ke

Please Login or Register in order to submit comment