Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawarta Linda,key yasa a kofar yace I'm coming,wurina ya dawo Wanda jikina ya dauki mazarin tsoro, toilet ya bude min na Shiga Yana min Dariya kasa kasa yaga yanda nake a firgice,ta baya yasa key ya kulle Ni a toilet ya cire key yasa a aljihunsa.

Kofar ya bude Mum ta Fado ciki uban me kakeyi ciki ka shanyani Ina tsaye?,Ina kaje kwana biyu? Wato kullum zaka yi tafiya a matsayin na uwarka baza ka fada min ba sai wata banza, wace matarka a kasar Nan? Naji ance kana da Aure yaushe kayi Aure ban sani ba munafuki?fada min wlh ko naci ubanka.
Fuskewa yayi yace ban gane aure ba? Kan uwarka nace cewar Mum, to Ni bani da wani aure Taya zanyi aure baku sani ba,ki dinga kwantar da hankalinki Mum kowa ya fada Miki makaryaci ne ban San komai ba.

Tunani tayi maybe Bokan Karya yakeyi dama tasan makaryata ne watarana, Ice dinta baya karya kawai sai ta yarda tace na yarda Amma idan Nagano ba Haka ba zaka gane kurenka,take ta saki ranta zuciyarta tayi sanyi tana son danta Amma ta jefa kanta masifa Akan duniya,Gefen bed dinsa ta zauna tare da riko hannunsa sunansa ta Kira Aliyu me yasa baka so na? Me nayi maka Ina mahaifiyarka sai dai na ji labarin baka kasar Nan? Why? duk tsiya nice na haifeka ba wacce kake so ba,sai ka kwashe wata baka zo ko gaisheni ba, nifa mahaifiyarka ce .

Ba abinda kika min Mum kawai ki daina abinda kike yi babu kyau,abinda kikewa Daddy yayi yawa,ya kamata ki daina girma fa ya kamaki ba Wai bana sonki bane bana son nazo na sameki kina shaye shaye da sauransu, Kallon Dan nata tayi baza ta iya canja halinta ba kawai sai ta mike ta bar dakin ba tare da tace Masa komai.
Sai da yaga Shigarsu Part dinta sannan ya budeni Ina fitowa Nima ban kulashi ba da sauri nayi waje Ina gudu gudu,sosai abin ya bashi dariya Ina jinsa yace Kwartuwa Goodnight,fasa tafiya nayi naja birki Jin ya kirani da Kwartuwa,jikin kofarsa na tsaya na harareshi tare da murguda Masa Dan Baki na sannan nace to kwarto na tafi da sauri.

Zan kamaki Zaki San wa kika Harara cewarsa,washe gari da wuri nayi Shirin schl Ina da lecture 10am, 9:30am na fito Zan wuce schl sai na hango Maman Ice tare da Ice da Kuma Dr who sun fito suna Hira sun jero,da gudu Meenal kanwarsu ta fito sanye da Uniform sai yanzu zata je schl, Danbature yaga nayi kyau da yawa sai kallona yakeyi,Mum Dinsa tana Masa magana ko jinta bayayi,har motarsa ta rakashi zai fita,Driver ya bude Masa ya Shiga baya ,a Raina nace kalleta kamar mutuniyar kirki,dama suna Hira da yaranta? Ta ganni na karaso inda take da sauri na rusuna tare da gaishe ta sai ta amsa min da Dan sakin fuska,Dr who yace Yan makaranta shima na gaidashi,Meenal kuwa ko kallo ban isheta ba taje ta Shiga mota driver ya jata itama.

Ice kuwa zai min magana ba shiri nayi Masa signa da ido irin Mum na wajen Kar tace akwai wani Abu tsakaninmu,fuska ya daure Mum ta leka ta window din motar tace a dawo lfy yace Ameen tare da cewa Mum na tsani yarinyar can Yar aikin Nanee,wani sanyi Mum taji karya boka yake da gaske bamu da wata alaka,Hmm kyaleta watarana zansa Daddy ya koreta kwana Nan.
Yawwa Mum bana son ganinta a gidan Nan a koreta.

Ni kaina ba kaunarta nake ba Son za ayi maganin abin kwana Nan Nan,motarsa Driver yaja suka bar gidan,Ni kuwa tuni Ina waje gefen titi Zan Shiga taxi motarsa ya tsaya inda yake zaune Nima na bude na Shiga kusa dashi, ina kwana na furta ya Amsa Yana kallona yace lfy kullum ke in Zaki fita sai kinyi kwalliya harda Jambaki,Shuru na Masa,Handkerchief ya dakko ya tallafi kaina da kansa ya goge jambakin.

A Raina Dadi nake ji Yana kishi na,har cikin schl ya kaini sannan ya karbi jakata ya zuba min kudi nayi Masa Godiya na Shiga class.
Yau cikin dare Hajjo kakar su Ice tayi mafarki wani yace next wk Zaki Shiga wutar jahannama,tunda ta farka abin duniya yayi mata zafi ta fashe da kuka Nan da sati daya shike Nan Zata mutu tunda ai Dole sai an mutu za a Shiga wutar Jahannama.
Bata fadawa kowa ba take ta faman kuka,ta daina cin abinci,kwalliya duk ta daina ta,Gulma data Saba sai ta daina,ta dauki carbi ta rike kullum tana ja tana kuka.

Yara da manyan gidan ta Tara tace akwai me Bina bashi? Kowa yace a'a tace to ku yafe min abinda nayi muku,Babu Wanda yasan Hajjo mafarki tayi ance zata Shiga wuta cikin wani satin, kafin sati daya Hajjo ta rame ta kwarjale,ta fita daga hayyacinta,an rasa gane meke damunta.
Next wk tazo satin da akace Hajjo zata shige wuta Zazzabin me zafi ya kamata sabo da tunanin mutuwa,asibiti aka kaita aka samu Hawan jini ya kamata sosai,Nan Hajjo a ranta tace cutar ajali ce kawai baza ta tashi ba,kayanta kaf tace a bada su sadaqa,Babu Wanda ya San Dalilin tace Dole a bawa tsofaffin irinta sadaka,Daddy tunda yaji rashin lfyr ya tattaro ya dawo gida Wajen Mahaifiyarsa.

Sati daya ya wuce Hajjo shuru Bata mutu ba,tace watakil Next wk ne,shima ya wuce Shuru,Hajjo tace to ko sati Uku ake nufi,shima ya wuce Shuru har taji sauki ma tana gida kayan sawarta saura kala uku Rak duk tasa an sadakar dasu,Wata daya Shuru,Hajjo tace sai wata uku ake nufi taci gaba da jiran mutuwa Bata da aiki Sai kuka da Jan carbi.
Ga zumunci ya motsa tana zuwa garin danginta yanzu,Bata gulma.

Shekara ce abokiyar munafuncinta ta shigo tare da Zama Bayan sun gaisa tace Hajjo kinji Asiya Wai zata tafi Kauyensu next wk Allah yasa ba wajen malamai zata je ba,carbin dake hannun Hajjo ta shaudawa Shekara a jikinta da karfi,Shekara ta kwalla Kara tare da ja baya,Munafuka Ni yanzu ba ruwana da duniya Ina Zama na Zaki sa na kwashi zunubi Yar kauye kawai Allah ya shiryeki.

Mamaki Shekara takeyi na canjawar Hajjo gaba daya lokaci guda,Hajjo ta karfi ta koma waazi a gidan kowa yaje gaisheta sai ya tafi da mamakin canjawar Hajjo.
Anty Maryam tunani takeyi yanda zata gano gaskiya tsakanina da Danbature ta kasa ganewa,Linda ce ta Bata Shawara cewar ta jawo Ni a jikinta sosai har na saki jiki da ita tasan gaskiyar lamarin, Bata San ta makara ba domin na Riga nasan halayenta bazan taba sakin bakina ba.
Kwana biyu tsakani Anty Maryam ta canja gabaya har Part din Asiya take zuwa nemana,tace kwana biyu bakya shugo min ki dinga zuwa muna Hira Mana,ko ta turo Yar aikinta ta kirani naje wajenta tana nemana tayi ta faman bugar cikina..

Yau ma Ina Gama aikina da yamma ta Aiko nazo wajenta Zan tayata gyara kitchen, Dana je ba wani gyara tana Murmushi tace me yasa bakya son Shigowa Fadila?Murmushi nayi kawai nace ba komai Mum,Hmm Fadila shekarar ki nawa ne? Nace 18 yanzu na kusa Shiga 19yrs, Lallai kin girma sai aure ko? Ya kamata tunda kina zuwa University ki fito da mijinki,aure shine darajar mace, Murmushi kawai nayi nace Nafi so sai na Gama Degree na sai nayi aure na,Amma Kuma naji kamar ance kina da aure Fadila cewar Mum, gabana ya Fadi Ras nace bani da aure kawai sharri yaran gidan Nan suke min,Uhm halayenki suna birgeni ko Zaki auri Dana Dr Who na hadaku aure? Baki bude nace kiyi hakuri Mum Ina da saurayi na Masa alkawari n aure schl dinmu daya dashi an kusa Kai kudin aure ma.

Farin ciki taji a ranta tace yaushe Zaki kawo min shi ya gaishe mu? Nace sai na tambayeshi sai yasa Rana da kansa,murna sosai ta kamata bani da alaka da Danta DanBature.
Muna Hira Aliyu ya shugo da sallama,muka amsa yayi mamakin ganina Ina part din Mum dinsu,kallo daya ya min ya nemi waje ya zauna kusa da Mum dinsa Yana gaida ta,sai kallona takeyi ko zata gane wata Alama da zata nuna Mata cewar muna da alaka Amma Bata ga komai ba,Muryarta naji tace Fadila kawo Masa abinci da ruwa,bana cin abinci juice kawai Zaki kawo min,ya furta Yana me hade rai.

Ina tafiya yace kin San Ni bana son abincin Yan aiki lemon ma wannan ce zata bani Mum,Bari na dauko da kaina,Mum tace me tayi maka Naga kamar baka kaunarta,Na tsaneta ne Mum ya Bata amsa kawai tare da Mikewa ya nufi kitchen, farin ciki ya Kama Mum.

Yana Shiga kitchen ban sani ba sai ji nayi ya fincikoni yana fada ki daina zuwa Nan na fada Miki me ya kawoki? Banza na Masa yace ke zanyi maganinki wlh kin rainani Naga Alama, Shuru na Masa na turo Dan bakina gaba nace to Ina ruwanka wai? Mijina ne Kai ko me? Kafa takura min,juice din ya fisge a Hannuna dai dai lokacin Mum ta shigo taga ya fisge lemo Yana hararata, wani Murmushin farin ciki tayi a fili tace mene Haka Son ? Ina ruwanka da ita.
A kitchen din ya barmu yayi gaba abinsa.

Nanee ta Fara canja min tana Jin haushina kasancewar tana ganin ko yaushe Anty Maryam tana kirana part dinta,sai ta Shiga zargin Kar a hada Baki dani a cutar da ita shike Nan ta daina sakar min fuska Abu kadan idan nayi fada da masifa,Sam ta tsaneni yanzu,Dalilin Haka yasa bana Jin dadin zaman gidan,tunani nakeyi ma yanda Zan bar aikin gaba daya na huta tunda Nasan inda Danbature na yake.
Yau Friday yau Kuma na tambayi Nanee Zan tafi gidan Attine zanyi weekend a can Bata hanani ba tace na shirya driver ya kaini,kayana na hada Sun Kai kala uku na tafi abina.

Tunda naje gidan Attine na Samu nutsuwa ban boyewa Attine komai ba na Bata labarin komai har zuwa kauyenmu da Danbature,ta Taya Ni murnar ganin Mijina,sannan tace kawai na bar aiki a can na dawo mu zauna tare,sabo da idan naci gaba da Zama a gidan tofa za a samu matsala Nan gaba.nima na yarda da shawarar Attine.
Attine da kanta ta shirya taje ta sanarwa Asiya cewar aure za ayi mini a kauyenmu Dan Haka na bar aiki gaba daya,Asiya dama haushina takeji yanzu sabo da Anty Maryam Bata ji wata damuwa ba sai ma murna da tayi,Sha Tara ta arziki ta hada min ta shirya kayana kaf a mota,tace Driver ya Kai Attine da kayana gida.
Duk abinda ya faru karaf a kunnen Danbature,har Wai yaji za ayi min Aure a kauye,to a kauyen Shi Kuma aurensa dake kaina fa ina Zan kaishi, Driver na tafiya tare da Attine Dan Bature ya fito a hargitse da sauri ya fada motarsa yabi bayansu Yana ganin Ina Attine zata je.
Haka suka dinga tafiya har suka je kofar gidan Attine ba tare da sun San Danbature na binsu a baya ba.
Nesa yayi parking da motarsa ya gani na sanda na fito daga gidan Attine na taimaka Mata muka kwashi kayana muna shigarwa ciki har muka Gama Driver ya tafi abinsa.

Shi kuwa Yana mota Bai tafi ba har na sake Fitowa zanje siyo danyen kifi,Yana kallona na wuce ta kusa da motar Sa Amma ban ganshi ba sam, Mahaukacin Horn ya Danna min saida na toshe kunnena,murfin motar ya balle ya fito sanye da farar jallabiya fitted yayi kyau matuka,mamaki ya kamani ya akayi yasan inda nake,kallonsa nayi shima ya kalleni kawai yaja tsaki ya koma motarsa ya finciketa a tamanin ya bar layin.
Baki Nima na tabe nayi tafiyata abina.
Ta bayana naji Karar motarsa ya shararota kamar zai takeni na matsa gefe,glass ya sauke yace ke Kinga na juyo na kalleshi yace na daina kulaki ya finciki motarsa ya Kara gaba.
Dariya ya bani sosai nayi na gaji sannan na tafi inda zanje.
Na siyo kifi na juyo kenan na sake ganin motarsa yayi slow saitina yace idan kika Kuma Fitowa ban yafe Miki ba indai ba da Izini na ba, Duk inda Zaki as from today sai kin nemeni a waya idan na yarda,wlh ko kofar gida kika fita ba Izinina ban yafe Miki ba.
Baki bude nake kallon ikon Allah,Number dinsa ya jefo min a farar takarda yayi tafiyarsa a fusace kamar zai cire titin layin.











AsmaBaffa
[9/4, 10:26 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕








51-55









Official








By
AsmaBaffa









Bayan na koma gida na bawa Attine labari,tace Oh Anya Fadila danginsa zasu yarda ya zauna dake? Abinda nake so dake ki rage ja Masa aji ki dinga Dan saurararsa ta Haka Zaki Kara Shiga ransa ya fada sosai sannan ku daidaita, hmm Attine mazan Nan musamman irin su Danbature sai da Jan aji Kinga yanda ya wulakantani a farko? kiyi dai a hankali a ilmince ba kawai ai ta Jan aji Ana wulakanta mutum wannan ba na masu ilmi bane,kiyi ajin na wise people ba Shirme ba.
Inshallah na Bata amsa muna kitchen muna shirya abincinmu.

Washe gari da misalin 5pm lokacin Attine Bata Nan taje business dinta sai dare take dawowa,banyi girki da wuri ba sai 4pm na Gama,na Kara gyara gidan tare da wanka nayi sallah,ba wata kwalliya nayi ba powder kawai na shafa da Maroon Jan Baki Na shirya cikin Riga da skert na atamfa nayi kyau dinkin kamar a jikina aka dinka,rigar me tattara da dogon hannu Wanda ake cewa kaci uwaka.

Nasha kyau Ina zaune na ebo abinci da littafi a Hannuna Ina karatun schl jibi zanyi test, knocking naji tunani na Attine ce Ina budewa numfashi na ya dauke na wucin gadi ganin Danbature yaci wanka kamar zai je fadar shugaban kasa,Kofar na tare sannan na Bata fuska nace me ya kawoka gidanmu Malam? Bai ko ce kala ba ya tureni ciki ya shigo abinsa kamar gidansu,Palon ya zauna ya harde kafafu sannan ya kalleni yaci gaba da latsa wayarsa, bance Masa komai ba Nima naci gaba da cin abincina Ina Shan Lemon Dana hada, sai da na gama na mike na kawo Masa Lemo da ruwa,kafin na ajiye yace kwashe abinki ban so sai da kika Gama koshi Zaki kawo min, Baki na tabe na kwashe na maida kitchen na dawo na zauna kasa tare da canja channel daga BBC zuwa Bollywood, ba tare da ya kalleni ba yace ki maida Min BBC News nake ji, ikon Allah na furta a fili nace Wai gidanku ne Nan da zaka zo ka Dame ni.

Hakura nayi na maida Masa BBC dinsa na kyaleshi,ya Dade a Haka bamuyi magana ba ya mike ya fita abinsa ya tafi , Attine tana dawowa na Bata labari,tace Yana sonki wlh farin ciki ya cika min zuciya,ki Shirya da dare mu fita Mana mu zaga gari cewar Attine,Kin manta yace in na fita Bai yafe ba, ba sai ki tambayeshi ba ai ya Baki number ya kike Abu kamar sakarai kina nesanta kanki dashi har ya gaji ki fara fita a ransa.
Haka Bayan nayi Magrib na saka number din da ya bani,sai da tayi ringing har sau uku Bai daga ba,sai Kira nagani ya kirani back, ya akayi ya furta,mamaki ya kamani dama Yana da number ta, unguwa zamu je da Attine anjima.
Ashe kin yarda Ni mijinki ne? Share zancen nayi nace naje ka amince? Wani Murmushin farin ciki yayi sannan yace karfe nawa zaku fita? 8pm na bashi amsa alright ba damuwa kuje.wayar na datse na fara shiri.
8pm muka fito zamu Shiga Taxi kenan wata dalleliyar mota tayi parking a gabanmu,Driver Danbature na gani yace Hajiya Oga yace nazo na kaiku duk inda zaku je, mu baza mu Shiga ba na bashi amsa,Attine tace ke wanne Shirme ne Haka? Dalla Shiga muje, Bayan mota muka Shiga tare da lafewa ac na watso Mana raba,har wani gadara da ji da Kai nakeyi, duk inda zamuje Haka ya kaimu har gidajen kawayen Attine yawo harda Wanda ma bana kirki ba munyi ganin mota Free.

Abinda ya bani mamaki yanzu duk ranar da zanje lecture sai dai kawai Naga Driver yazo yace Oga Ice ya turoshi,ashe time Table namu ya karba, kafin kace me na Zama babbar yarinya a mota kala kala ake kaini schl na Alfarma.yau ma Driver na zuwa nace ya na ganka da bakar motar Nan Bayan jiya na fada Masa Fara nake so ban son wannan bakar,Nan take na dakko wayata na kirashi bugu daya ya dauka cike da Muryar bacci Alama bacci yakeyi.
Pls Ni farar motar Nan Marcedes Benz nake so ba wannan Ba,karfin Hali ya furta a ransa Lallai wasu Basu iya samu ba,idan baza ki hau ba ki tafi a taxi, to Ni bazan Shiga ba ya dawo ma da motarka, banyi zaton zai amince ba,Nan take ya Kira Driver yace yazo ya dauki Farar ya kaini a ita.haka kuwa akayi Nan da Nan sai ga Driver da farar ya dawo ya kaini schl,tabara nakeyi iri iri Kuma Yana biye min Bai taba nuna gajiyawarsa.

Waya mukeyi da Ya Salman yake bani labari Danbature yazo last weak duk Wanda ya karbi takardunsu sun samu Babban aiki a cikin garin Gombe, sannan ya siya musu Dalla dallan motoci na zuwa aiki dake Basu da Nisa da cikin garin, Ya bawa Abbu jari me kauri da kudin gyaran gida.
Murna nakeyi son Danbature ya Kara kamani Nan na bawa Attine labari itama Murna tayi sosai tace wannan Mijin aure ne kinyi Dace samun irinsu sai an tona,mazan yanzu macen ma da ya suke Mata abin kirki bare danginta,wani ma da ya aureka sai ya koma yiwa danginka kallon banza.

Yau satina uku da komawa gidan Attine ban sake ganin Danbature ba,Wanda hakan ya jefani a damuwa,sai dai ko yaushe Driver dinsa ke kaini inda nake so, kwance nake saman 3seater Ina Danna waya,Attine Bata gida knocking naji na bude,kamshinsa ya bige Ni zuciyata tayi wani sanyi gefe na matsa na bashi hanya ba tare dana kalleshi ba,ledojine a hannunsa manya sunkai hudu na Shopping mall,Ajiyewa yayi ya zauna Yana nuna alamun ya gaji,Ina yini na gaidashi lfy Alhmdllh kawai yace Yana Bina da mayen kallonsa Wanda ke rikita ni.

Ruwa da lemo tare da farfesun kaji na kawo Masa na ajiye tire a gabansa,a ransa dama yunwa yake ji,a hankali yace wannan ai ba abinci bane,Allah yasa Pounded yam da miyar kwai Tasha Naman rago,kawo Masa nayi ya bude ya gani,Murmushi yayi kadan tare da furta da kin San da wannan Zaki bani wani Kaji.
Murmushi nayi Nima kadan tare da serving dinsa.
Ya Shiga ci sosai yayi missing girki na Ina gefe Ina satar kallonsa Ina Jin wani Dadi a Raina.

Bayan ya Gama lemon kawai yake kurba Yana lumshe ido, bude kayan ki gani,siyo Miki nayi Kar Allah ya kamani bana kula da matata, ledojin na Shiga dubawa kayane na sawa iri iri masu tsadar gaske, cosmetics,da inner wears,takalma da bags masu tsada, wata karamar Leda ya Miko min Atamfa super,lace da shadda tare da kudi dubu Hamsim yace na wannan matar ne da naji kina ce Mata Anty ance Yar uwarku ce, sabo da farin ciki kasa dannewa nayi na dinga washe Baki shi Kuma farin ciki ya kamashi na Yaba kyautarsa.

Dubu dari ya Miko min gashi in Zaki siya Abu,Kai na girgiza nace a'a,yace an kusa kaiki Gidana gwara ma ki karba,gabana ya Fadi ko shine Dalilin da ya kaishi kauyenmu again, Ya Salman yace ka samo musu aiki da sauransu mun gode...katseni yayi da Ina ruwanki wlh na fada Miki kima shirya Zan tona asiri kwanan Nan kowa a gidanmu zai San tsakaninmu.

Tsoro ya kamani nace Dan Allah kayi hakuri sai Nan gaba,ko gidanka kake so na tare to muyi a sirri pls,Mikewa yayi yace ki shirya Zan ballo ruwa kwana nan yayi waje abinsa.
Attine tana dawowa na kwashe komai na fada Mata,To sai me? Ke tsoronsu kike ji? In kina Haka sai Naga ma kamar ba kece kike damuwa da Danbature ba kamar Zaki kashe kanki a kansa,ga dama ta samu kin tsaya Shirme ko so kike ya auri wata ko ayi Masa Mata a danginsa,idan Zaki mike ma ki mike ki daina tsoro ki daura a niyar kula da mijinki,abinda ya faru ya rigada ya faru tunda har yanzu Yana sonki to karki yi Wasa da damarki,gyaran jiki zamu Fara Miki yanzu na Yan birni sannan mu koma kauye a kawoki dakinki kamar kowa gobe zamu fita akwai kawata me gyaran jiki.

Ni dai Jin Attine kawai nakeyi tsoro ya Gama kamani nasan tawa ta kare kawai sabo da Ni Naga abinda na gani bangaren Mum Ice,inda Bata kaunar wani ya rabe ta da jininta ace Ni danta guda ya aureni Ina Yar talakata talak.
Attine ce ta katse min tunani da idan Zaki mike da Addua ma ki mike sannan ki cire tsoron banza a ranki ki daina tunanin komai ki rike mijinki wlh ba Zama zaiyi baiyi aure ba an fada Miki jiranki zai tayi kina Masa Shirme Yana gajiya zai ajiyeki gefe ya auri wata ko Uwarsa ta kawo Masa wata Kuma ki Raina kanki kinsan dai Babansa Mijin tace ne sai abinda Anty Maryam tace dashi, kin zauna kina harkar kauyanci,Ni wlh yanda Naga kina sonsa Haka nayi tunanin duk yanda Zaki ki fara juyashi kin sani,Amma har yau an kasa wuce wajen haba.
Haka Attine ta dinga fada sosai Ina jinta.

Tunda Danbature ya koma gida ya kasa fita a motarsa yana ciki yana aikin tunanin yanda zai bullowa lamarin Zama tare Dani,yasan Mum dinsa baza ta yarda ba sannan idan Daddy ma ya yarda a banza tunda tafi karfinsa ita ke juyashi sai abinda tace,kakarsu kuma ba wata ta kirki bace,shi Kuma yana son Zama da matarsa ga Mum Kuma da tsafe tsafen masifa,ya Dade yana tunaninsa ya kasa samun Mafita gashi ya Gama tsantsara gidansa da zai zauna Kuma ga aure Yana bukata,sannan ga masoyiyarsa ta hakika ya samu tana sonsa ba Dan komai nasa ba Dan Allah wacce ta zauna dashi lokacin da ba kowa zai rabeshi ba,shi Taya zai iya biyan Fadila ma abinda tayi masa.

Fitowa yayi a fusace da sauri Hadi da kwarin gwiwar tinkarar Mahaifiyarsa ya fada Mata ko a mutu ko ayi Rai,fuuuuu yake tafiya cikin Takama Yana Shiga palonta yaji tana waya da bokanta tace ko wace matar tasa kawai a kashe min shegiya,yaron Nan Yana tarayya da ita komai nawa rushewa zaiyi, jikinsa ne yayi sanyi ya juyo baya a hankali ya dawo yace to shike Nan na fasa nuna matar ma kawai Addua zamu dage muyi zamanmu a boye suje su karata.

Kwana biyu in Banda tunanina ba abinda Danbature keyi,ya kasa sukuni gaba daya Yana tuna rayuwarmu a kauye lokacin Yana Mahaukaci,yanda nake kula dashi,bacci ma baya iya yinsa sosai,gani yakeyi wani zai iya kwace Masa Ni,kyawuna yake tunawa da yanda nake komai nawa a nutse,bacci ne ya kwasheshi da yamma lis,Bai farka ba sai 8pm wanka yayi tare da sallar Magrib da Isha,dazu cikin

Please Login or Register in order to submit comment