Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

San Dame Zan kwatanta muku ba,ga wani sanyi da kamshi ta ko Ina,mun Dade a zaune Ina ta kalle kalle.
Daga baya muka ji wani kamshi na daban ya gauraye Palon tare da kwas kwas na takalmi,wata dattijuwace Fara irin na Igbo Sai hancin Nan kamar carpenter yasa guduma ya dakeshi, ga Baki chokoko lebe shaftarere,sai kiba dum gashinta wani kwaikwaye kamar birbiri ya yada zango a kanta,sai dai gashin yasha gyara Yana kyalli da sheki,Riga ce ta material me hannun bra har kasa ta sata ga wata sarka ja me kululai kafta kafta,abin hannunta sai Kara suke da gani arniya ce ta gaske,anci haram an koshi,Zama tayi da kyar tana yanga yanga,kafin tayi magana sai da ta dauki dogon lokaci mun gaji da jira sannan, Attine ta gaisheta tace Good Evening ma,Hope u r fine ma? Da kyar tace im fine thank u, Nima da guntun turancina na gaisheta ta amsa.

Da harshen turanci tace itace me Taya Ni girki? Attine tace itace,hope she's clean? Yes Ma so very clean cewar Attine, Ijeoma ta danyi Murmushi kadan sannan ta zaro kudi a Jakarta dubu ashirin ta mikawa Attine tace na Bata Number accnt dina ita a accnt take biyan maaikanta salary,Nan take ba kuskure na bata, Attine sallama tayi min zata tafi, hawaye na fara ta dinga lallashina tace ke da zaka nemi kudi kizo ki gyara kanki kafin Dan Bature ya dawo kwana Nan,wani sanyi naji sannan nayi Murmushi na nace Haka ne Anty sai nazo weakend munyi sallama ta tafi,Ijeoma tasa wata Charity ta kaini part din Yan aiki.

Ijeoma tace idan har taga kyan aikina sannan kuma tana jin dadin Zama Dani to part zata canja min na dawo part dinta muna ci gaba da yiwa me gidanta abinci tare, ko part din Yan aiki ya Hadu kamar bana Yan aiki ba,daki kowa Mata biyu Amma Ni tace a bani daki guda sabo da kwar jini irin na addinin musulunci,Haka Yan aiki duk nayi musu kwar jini sai Nan Nan akeyi Dani sabo da musulunci da yawan addinina.

Yau da dare misalin 8pm Bayan nayi sallar Isha Ma ta Aiko nazo zamu Shiga kitchen mijinta ya kusa dawowa,dama nayi wanka na na canja Kaya naje palonta Wanda ya gaji da haduwa kallo ta Kare min ta ganni fresh neat tsaf Dani Murmushi tayi hankalinta ya kwanta Dani tace let's go na bita a baya har hadadden kitchen dinta,muka fara aikin dake kalar abincinsu daban Dana Hausawa sai tace na dinga dauko Mata Abu Wanda ya kama a yanka tasa na yanka Mata,Wanda za a wanke na wanke,Wanda za a markada nayi ban samu matsala ba ko kadan tana nuna min Ina kallon yanda suke kalar abincinsu tana yi tana koya min Nima,muna Yar Hira sama sama tana tambayata kalar namu girkin Ina Bata labari da guntun turancina tana ganewa Kuma ba wulakanci ba komai muka Gama na shirya Dining na gyara kitchen sannan tace na ebi nawa naje part dinmu naci, na eba duk abinda Naga Zan iya ci sannan na Mata sallama, wanka nayi naci abincina na kwanta bacci da wayata wacce nake bincike a ciki.

Washe gari ma Haka muka shirya break lafiyayye tana jin dadin aiki Dani ga Tsafta ta,yaranta Yan Mata Amaka da Emmanuella Wanda suka dawo daga turai ne suka sakko Amaka Tasha wando short da Yar Riga taci kwalliya Wai Shirin fita tayi Nan ga wani gashin doki brown tayi kyau sai dai fuskar Nan kamar an taka Kashi sai farin kawai shima da Karin Mai,Haka Emmanuella ita Kuma bakin gashi dogo tasa tana sanye cikin wata Yar Gown da kadan ta wuce duwawunta itama ta cakare da makeken glass a Fuskarta Baki ga takalmi me tsini sunsha da jaka masu tsada sai uban farce da suka Sa yasha paint zako zako kamar na horro.

Mum dinsu suka rungume suna gaisheta ita Kuma mundukar arniya tana manna musu kiss, Wani kato,murjeje,wani dunkulelen gardi Dattijo ne ya sakko Baki wuluk dashi ga sandar girma ta kudi ya rike a hannunsa wuyansa yasha murjani,wani Zanin atamfa ya daura ga wata rigar yard me Masifar tsada da kyau 3qtr ce, kamshi kawai suke bulbulawa tare da warinsu na arna, saman Dining gaba daya suka zauna,Ma da kanta tayi serving nasu,duk abinda suke Ina labe cikin kitchen Ina gani, naji Ma ta kwalla min Kira Fadila kamar ita ta Rada min Sunan, yes Ma nace daga kitchen,Mijinta David yace who is she? She is my new House made, the name saund like Hausa, Ma tace Yeah ofcourse she's beautiful Hausa Girl, very Beautiful girl and clean,that girl she's different Imfact I like the girl so cool,friendly and Nice.
David yace da turanci ai dama a Hausawa akwai mutanen kirki sosai wasu kuwa Sam Basu da amana sannan gasu da kyawawa.

Baki Amaka ta tabe tace those criminal Hausa people Mum kika dauko Mana Yar aiki sai ta harbe mu ko ta saka Mana Bum a gida mun Kone gaba daya,Dirty people begas, Dariya Emmanuella tayi tace nawawo Aboki hmm ahhh fear them wooo,Zaki gansu so silent kamar baza su aikata tsiya ba, Baki Amaka ta tabe tana wani shanye hannu tace Almajiri people.

David Dad yace be quite let them be pls Akan ko wacce alumma Ana samun na kirki Dana banza,Ma sai lokacin tace Ina ruwansu ma suna maganarsu da turanci Ina ji,a tsorace na fito kusa da Ma na tsaya nace Good morning Dad, da Faraa yace morning, Suma Yan Matan na gaida su sai lokacin suka kalleni, Amaka ta zabura tace Chineke God Beautiful girl like u as House made ahhhh.
Emmanuella sai kallona takeyi kamar zata Hadiye Ni,kyau na ya gigita su,yanda suka yi zaton ganina ba Haka suka gani ba.
Ma dariya tayi musu sannan tace naje Driver zai kaini kasuwa na siyo abinda Babu ta bani kudi masu yawa tare da jotter inda ta rubuta komai.

Bayan na tafi suka dinga gulmar Wai bana Jin turanci sosai ai Hausawa Basu damu da ilmi sosai ba Kuma gaskiya suka fada.
Ban Saba zuwa kasuwa ba Amma Haka na zage na siyo komai, sannan muka Shiga store Nan ma na jido kayan girki muka dawo na shirya komai inda ya Dace sannan na kaiwa Ma canjinta tace na rike ta bar min na dinga murna naje Driver ya kaini banki na saka dubu Bakwai dina a accnt.

Yau da dare Amaka ta kirani Wai na hada Mata fresh Juice na Apple nayi Mata yayi Masifar dadi Ma ce ta fada musu yanda na kware wajen hada juice, ta harde a kujera tana karanta jarida na zuba Mata a cup na Mika Mata kenan ta kula da agogon Hannuna,mamaki ya kamata taga agogo na diamond me tsadar gaske da kyau,kirji na ta kalla taga sarkar Dana sa zoben azurfar Dan bature.

Tace wannan agogon a Ina na sameshi dake su babu boye boye nace na Mijina ne,tace zoben fa?nace shima Haka,tace Jesus yanzu kamata Haka Ina da aure?nace ae amma Mijin bama tare,tayi tunanin sakina yayi tace eyya sorry eh? Nace thank u.
Ta fadawa Dad da Mum tare da Emmanuela suka min jaje,tun daga lokacin suke Jin tausayina, suka ce a schl Ina na tsaya? Na nuna musu takardu na na ssce ,Ma tace zata sani a University makarantar kudi, na dinga murna na bugawa Attine waya na fada Mata taji dadi,Haka Yan gidanmu Ya Salman yafi kowa Murna.

Bayan na kwashe wata guda gidan Ma mun Saba dasu sosai,turanci na ya karu na fara kwarewa,ga albashina farko da aka min transfer naje na cire dake duk sati daya ko biyu Ina zuwa gidan Attine,Haka na Kai Mata albashina nace na Bata 20k na dauki dubu goma,da kyar ta karba sai da taga Raina ya baci ta karba.

Safarau ma Ina Kai Mata ziyara itama tazo min gidan Ma sau biyu,Bayan sati daya Ma ta kawo min Admission da komai anyi min registration a Health education zanyi Degree na Shekara uku,na fara zuwa schl ba,driver ke kaini ya dakko Ni, Emmanuela da Amaka suka ce ya kamata na waye na dinga matsewa cikin kana Nan Kaya,nace mu addininmu sai Miji ake sawa ko a gida,Haka suka suyo min Kaya kana na iri iri Amma bana sawa ganin Haka sai suka dinka min su atamfa da materials laces,shadda Riga da skert da dogayen riguna tare da mayafai na sirara masu kyau,takalma da jaka iri iri, idan kun ganni kamar bani ba,tsofaffin Kaya na Attine na kaiwa ta San yanda zata yi dasu.

Karatu da aikina nakeyi lfy lfy ya rage min tunani da yawa sosai na Kara girma,kiba skin Dina tayi fresh sai sheki nakeyi kullum kamar wata Amarya haka nake, ga Saloon Ina yawan zuwa Ana wanke min gashi na,lokacin dasu Amaka suka ga gashina haukacewa sukayi, Ma ta dinga mamaki kamar gashin Baturiya.
Yanzu tuni na dawo saman Benen Ma a Nan ta bani daki kusa Dana yaranta komai akwai kayan kwalliya iri iri,gashi Hawa biyu ne,Ma da mijinta a saman karshe yaranta a hawan farko.
Mun Gama girki munci mun Sha nayi Shirin kwanciya Bayan na Gama karatuna na mike jikin window na dake kallon gidajen waje kullum sai na leka na kalli unguwar da tsaruwarta.
Yau ma labile na zuge Ina tsaye da tea cup a Hannuna Ina kurba wani gida nake ta kallo nesa da mu sosai kaf unguwar Babu kamarsa a kyau duk da kyan na Ma ba komai bane Akan wancen gidan,wani daki na gani an kunna Kwan lantarki taram ya gauraye da haske,wata Yar aiki ce Naga ta wuce da plate, ta sake dawowa ta wuce tare da wata mace dattijuwa fara kamar Baturiya ban fiye gani tar tar ba Tunda da Nisa,Yar aikin ta sake ficewa Matar na gani ta saka jajayen kaya wani yadi kamar dodon tsafi Haka ta dawo Fuskarta ta rufe tana motsa bakinta da Alama magana takeyi,sai Naga ta Zama kamar horro ta Bace bat,tsoro ya kamani Bayan 30mnt sai na ganta wukil ta dawo inda take da wata tukunyar shirka a hannunta,ta ajiye tare da cire Kaya ta canja nata na farko ta kashe wuta duf sannan ta bar dakin,steal Ina tsaye bul Naga a dakin an Kara kunna light wannan namijine fari tar shima kamar Bature Amma Banga fuskarsa ba ya juya baya rigarsa ya cire gabana ya Fadi exertly jikin Danbaturena sai dai wannan yafi fari da mirjewar skin kamar ka tabashi jini ya fito,ko Dan Danbature a kauye muke ne ga Ciwon hauka shi yasa,ga wani uban gashi a kansa Wanda yasha askin irin shegun turawan Nan mawaka ko Yan film kyau iya kyau,gashin Nan Baki,shi ba gajere ba, ba Kuma dogo can ba,ba rammame ba ba siriri ba, so nake kawai ya juyo Naga fuskarsa, na bude kofata ta baya dama akwai corido Dan nafi kallonsa sosai na tsaya a Nan,barin wajen yayi ba tare da ya juyo fuskarsa ba ko yasan da wata tana kallonsa ba, ya Dade Nima Mayyar naki tafiya,sai gashi ya dawo sanye da rigar wanka fara Kal da Alama wanka yayi,jikin window dinsa ya tsaya shima dake facing nawa Amma Sam kasa yake kallo Bai kallo saitin gidanmu ba,
Gani nayi kamar Danbature ne ke min gizo nace Kai wannan idan ma ban samu Danbature ya dawo ba to Naga Mijin aure,Dole ne ma ya aureni tunda suna Kama, Dole na San yanda zanyi na Kulla alaka dashi, Kuma sai Naga Danbature na kamar yafi wannan kyau da komai,sannan ya fishi kira da cikar zati har ma kwarjini da komaima.

Da karfi na kwalla tare da Mika Hannuna Ina tsalle nace Danbature......Baturena .....kaiiiiii.....Dan fari ....juyo.....Nan...gani .....kalleni......Kai......Malam.....nice Fadila......dolene ka aureni......gaba daya dake dare ne duk kusan layin wasu da dama sunji Ni, amma ba wasu Hausawa Basu san me nake cewa ba,shi kanshi Wanda nakeyi dominsa Bai ji ba gani nayi ma an kawo Masa lemo Yana kurba Yana shafa sumarsa, dagowa yayi kadan sai da na firgita da kyansa, wannan ai Danbature yafi shi, Amma suna mugun Kama, wata budurwa na gani itama zukekiyar gaske fara tas tazo ta rungumeshi ta baya.

A fili nace na Shiga uku kaga tsinanniya Karuwa,Anya wannan ko dai Matarsa ce wash na dafe kirjina, kishinta naji na Kara kwallawa da karfi Ina nunata da yatsa kee....Mayya....matsa daga jikinsa....Mijina..nane....Arniya.....Arniya....Allah ya tsine Miki na Kara tsalle kamar zararriya na Dane karfen jikin corridor din nace Mayya....ke...uwarki Ina Mata dakuwa kuwa Allah yasa karaf ta hango,ban hakura ba nace karbi Nan ungo na Kara Mata zagi da tafin Hannuna Ambola dakuwa.
Kirjinta ta dafe kamar taga Aljana tayiwa Namijin nuni da ya kalli Aljanna a sama can gidan,ai kuwa ya kallo wajena gabana yayi mugun bugawa daram kamar Danbature,Amma Ina wannan ya take Danbaturena kyan fata sabo da hutu ya ratsashi,na tabbatar da Danbature ne ya samu hutu Haka to ya ninka wannan komai,to me ma zai kawo shi Lagos.
Haka na dake na nuna shi da yatsa sannan na sarke yatsuna kana Nan biyu maanar aure, Ido ya zaro,kiss nayi Masa ta iska sannan na hura Masa ta iska, dariya ta kamashi sai yayi Alama shima ya cafke ya lika a zuciyarsa dariya na kyalkyale da ita na tafa Masa sannan na daga Masa Babban yatsa irin Good. Tunawa nayi Ina da aure fa sai na fara istigifari.

Budurwarce ta dinga kwasa dariya tana ganin haukata gani Yar yarinya tace kawai irin Yan iskan yaran Nan ne kawai yayan masu kudi fasikai,shima Haka yayi tunani sai Naga sun koma ciki matar ta fice shi Kuma ya gyara labilensa tare da kashe light alamar ya kwanta.

Ban taba samun jindadi irin wannan ba Tunda nake a duniya sai lokacin da muke tare da Danbature na,fes nayi bacci na tashi,inayin sallah da azkhar na Kara lekawa ta kofar dake dakina ta baya ko zanga me kama da Danbature Amma ban ganshi ba gani nayi ma an rufe window din ruf,jiki ba laka na wuce kitchen inda na iske Ma ta fara aikin,na gaisheta muka ci gaba da aikinmu Ina ta faman tunanin Danbature da mutumin jiya me kama dashi.
Bayan na Gama komai nayi Shirin schl na wuce,su Ma da yaranta duk sun wuce Office Suma ba zama.karatuna nakeyi sosai.
Yau ma dai dai lokacin jiya da dare Naga me kama da Mijina ya sake fitowa Yana Shan iska direct window na yake ta faman kallo,katsam na sake Nima fitowa, hannu na daga Masa shima ya dago min Yana Murmushi,Alama ya min wai na sakko na zagayo gidansu,kafada na makale nace sai dai shi yazo, katuwar paper ta Zane ya dakko ya min rubutu da Babban Baki Ur Name pls? Nima na rubuta na nuna Masa ya karanta Fadila.
Hausa girl ko? Ya sake nuna min,Nima nace ae Ashe kana Jin Hausa? Yace ae Babanmu bahaushe ne mun zauna a Kano,Adamawa, jigawa duk gidanmu kowa najin Hausa nace to yayi kyau.
A Haka muka dinga Hira sosai cike da nishadi Ina magana da me kama da Mijina.

Yau mun kwashe kusan sati Uku kullum sai munyi Hira da wannan mutumin Wanda yace min sunansa Doctor who ake ce Masa,kowa na tambaya Dr Who za a nuna min shi da gidansu.
Sosai muka Saba da juna, Amma dare daya ya nuna min manufarsa Yana so yayi xxx Dani shi manemin matane tun daga lokacin naji bana sonsa na tsaneshi, ba wani boye boye yazo wajena har gidan Ijeoma ya fada min halayensa da niyyarsa a kaina,zuwansa wajena biyar tunda Naga ba mutumin kirki bane na daina saurararsa Amma Kuma sai suna matukar Kama da Danbature.

Ijeoma tayi mamakin alakata da yaron masu kudi Haka Wanda Babu kamarsu a Lagos, ji akeyi dasu kowa yasan da zamansu.
Yau Sunday kowa Yana gida yau Amaka zata kawo Mana saurayinta Dan Rivers Wanda tare sukayi karatu a turai Kuma shi zata aura,sosai aka shirya Masa liyafa,matashin Igbo me kudi gurjeje dashi katon Arne, yazo Ni nayi serving Nasa abinci Wanda sai kallo na yakeyi kamar maye,Silvester sunansa Ma tabar Palon,Emmanuella Bata nan,Amaka ta mike tace Bari ta dakko wayarta zata Kira Emmanuella tazo taga mijinta,Yana ganin Haka ya matso kusa Dani Yana fada min wai yanzu Ni yake so nafi matar da zai Aura Amaka kyau,Amaka karaf a kunnenta da ihu ta karaso tare da rufe Ni da duka Evil hausa girl, Silvester da sauri ya bar gidanta, Amaka tace zamu hadu da Kai I will kill u.

Ma ta fito taji labari Haka ta dinga zagina tana Harara ta da kyar na Basu hakuri suka hakura Wai laifi nane.
Bayan sati biyu Emmanuella ta kawo nata Richard Wanda zata aura a gaban kowa ya dinga min signa,ranar kaca kaca suka Bata da saurayinta,Nima Ma tace you again ta fara min gorin abubuwan da suka min wai naci Amana suka kamani suka yi min dukan kawo wuka naji jiki duk sun kumbura min jiki, ranar Ma ta bani ragowar kudin aikina ta sallameni,duk abinda suka siya min na kayan sawa da kayan kwalliya sai da suke cika min akwati biyu da komai Basu kwace ba suka sani a taxi sukace na tafi gidan ubana bazan zauna musu a gida ba,schl Kuma Ina level 1second semester suka ce naje naci gaba da zuwa har na Gama level 1 na biyawa kaina sauran shekarun ko na tsaya iya nan na karbi transcript.












AsmaBaffa
[9/4, 10:25 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕








16-20








Official








By
AsmaBaffa









Ina sonku fans a zubo min Sharhi naji dadi typing kunayi Ina Jin dadi💋😍😍


MAMAN ABBA,HABIBA,AICHA,AUNTY SUMEE,ZAINAB ATIKU SALAMA,MAMAN MEENAT, OUM page naku ne Yan gayu na.








Katsam Attine ta ganni da Kaya Niki Niki cike da bacin rai kamar zanyi kuka,Attine tace karki yi kuka fada min me ne ya faru nasan Baki da laifi Fadila,abinda ya faru na kwashe na sanar Mata,tace to kyalesu idan sun gane gaskiya zasu nemiki na tabbatar Babu Wanda zai zauna dake Baki Shiga ransa ba Fadila.

Zamanmu Shar nida Attine muyi hirarmu.
Kwana uku tsakani Ma da yaranta su Amaka suka ga amfanina a gidan,suka gane gaskiya bani da laifi mazan ne masu laifi maciya Amana.
Wayar Attine ce tayi kara Ma ce da kanta ta nemeta tana dagawa ta Bata hakuri tace sun gane gaskiya da Allah a sani a taxi da kayana na koma,murna da farinci ya kamani sabo da naji dadin Zama dasu ga kyautata min da sukeyi inyi abinda nake so kamar Gidana,wanda musulmammu baza su zauna da Yar Haka ba bare har a wani sani a University, Kuma bana so na daina ganin Dr who me kama da Dan bature.

Inda yake birgeni yanda zaka San wayayye ne idan ya nemi kuyi fasikanci kika Ce no to bazai Miki Dole ba,Kuma bazai Kara miki Zancen xxx ba sannan bazai fasa muamula ta mutunci da ke ba,ta Nan zaka San Dr Who ya Gama wayewa baya Dole,sannan kyauta da mutuntawa zai Miki,sabanin wasu mazan Wanda idan ba wani Abu zasu samu wajen mace ba to fa ba ruwansu dake.

A ranar Attine ta kaini again gidan Ma da kayana,suka tarairayeni tare da bani hakuri Akan abinda ya faru,nace ba matsala,Attine Tasha kyautar Atamfa me tsada turmi guda da kudi masu kauri.
Dr who Bai San Ni Yar aiki bace Amma Yana mamakin musulma a gidan arna,sai daga baya yaji labari ba karamin mamaki yayi ba Jin Wai Ni me kyau Haka a matsayin yar aiki,Bayan masu kyau da dama gasu Nan Akan son Kudi sai karuwanci sukeyi suna Zama hamshakan masu kudi sai kaga mace tana Hawa dalleliyar mota Wanda gidansu Gawayin girki ake siyarwa,Makkah duk Shekara Ana daukan pics Ana sawa Dan kawai q burge mutane anje Makkah da kudin Haram anyi shawagi an dawo.Allah ya shirya.

Bayan na dawo da sati biyu Emmanuella da Amaka suka koma London abinsu,daga ni sai Ma muke rayuwa kowa Yana addininsa, ga schl dina Ina zuwa ina karatu na.
Daga makaranta na dawo a gajiye,Ma tana wajen aiki Bata dawo ba wanka nayi tare dasa gown marar nauyi iya gwiwa Zama da arna har na fara koya Nima kwanciya nayi na huta.

Wani Cikin Securities ne yazo yace Wai nazo inji Dr who,a wata arniyar mota yazo sanye cikin kayan likitoci nasa hijab naje, Bai fito daga mota ba ya sauke glass muka gaisa yace masu Hijab gashi ya Miko min wata Leda cike take da snacks sai Ice cream,Godiya nayi na karba Bai jira nace komai ba ya ja motarsa ya tafi na koma cikin gida Ina daukan abinda nake so Ina ci.

Satina Uku da dawowa Mijin Ijeoma ya fara shaawata a gidan yanda yaga Ina kwalliya da gyara kaina,kullum muka hadu sai ya faki idon Matarsa ya dinga min maganganun batsa, na Masa magana yaki ji ba yanda zanyi dashi,idan yaga Ijeoma Bata Nan sai ya dawo gida daga Office ya takurawa rayuwata,har schl Bina yakeyi,Ni Kuma Ina tsoro na kasa sanarwa Ma yace idan na fada zai batar Dani.

Gajiya nayi sabo da ina kitchen ya shigo ya fara shafa min Mazaune Ina guduwa tuni na fara hawaye Ina fada Masa Ina da aure Amma yaki ji kicif sai ga Ma ta Fado kitchen Ina kuka nake fada Mata ba laifi na bane wlh gwara ma ta sallameni tunda matsala nake zamar Mata a gida,karshe Nace na tsani gidan Baki daya sabo da cin mutuncin aure na da yayi bazan yafe Masa ba.

Ma tasan bani da laifi kawai Haka ta sallameni again salin alin tayi min kyauta me yawa,sannan tace naci gaba da karatuna zata dinga biya min nayi ta Godiya na tafi gidan Attine na sanar Mata komai taji dadi sannan tace inshallah zata Nemo min gidan musulmai.

Hankalina kwance nake zuwa makarantata sannan muna zaman mu lfy da Attine, na Kara wani wayewa ga kyau na ya ninka nada,na Kara girma da tsayi shape dina ya fito sosai Duk Wanda ya ganni sai ya Kara son sake ganina.ina da kawayena na schl Amina da Rahina yaran mutunci.

Safarau ma ta samu hutu yau tazo zata yi weekend a gida,tace mutuniyar wannan kyau Haka da Alama an daina tunanin Dan Bature,dariya nayi nace Anty Attine kinji ta ko?ai Yana Raina har abada yarinya, hmm kin fara chart? Cewar Safarau nace Allah kiyaye, wayata ta karba ta tura min Hausa novels iri iri ta koya min yanda Zan bude na fara karatu,ai kuwa tunda naji dadi love iya love ga koyon abubuwan rayuwa yanda zaka kula da Mai gida,na tuna idan Danbature ya dawo haka Zan dinga nuna Masa love kawai sai na dage da karatu ba dare ba Rana,watarana Har masifa Attine ke min.
Na waye sosai na Karu ta hanyar karatun Novels Ina yin na schl abina ras.

Bayan sati hudu lokacin mun Gama second semester Ma tayi min registration da komai na level two muna hutu bamu koma ba,Attine ta rafka sallama ta dawo daga unguwa, sannu da Zuwa Anty ya hanya, Alhmdllh tace sannan tace kafin na zauna Bari na Miki albishir na

Please Login or Register in order to submit comment