Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

talaka sai yaran shugaban kasa ko Gomna,nasan Address din Amma na nuna ban sani ba sai Dr who ne ya rakani sannan ya koma wajen Nanee Ni Kuma na Shiga room din da Sallamata.

Danbaturena ya rike Hannuna Daddy kam Yana zaune gefen bed din,Nan Kuma ga Saddiqa da yaran gida maza da Mata sun cika dakin kowa yayi jugum jugum, mun gaisa nayi musu ya me jiki na ajiye musu abincin,Saddiqa tace kamar kin San yanzu ake tunanin aje gida a kawo abinci, Nanee da Dr who tun jiya suna Nan asibiti Basu ci komai ba,Bari suzo suci,Murmushi nayi kawai muka hada Ido da Dan Bature ya min signa tare da kashemin Ido daya,Nima Haka na Masa Saddiqa Yar sa Ido ita kadai ta ga abinda mukeyi,Aiko sai muka ji tace Fadila da aurenki babu kyau wlh Zaki Shiga sabanin sharia.

Babu Wanda ya San me take nufi anyi tunanin shirmenta ne data Saba.
Na Dade a zaune lokacin Nanee da Dr who suka shigo su Kuma Yan gidan suka tafi gida suna cewa da yamma Karimatu zata zo, Nanee ta zauna gefena sannan tace kamar kin San yunwa muke ji,Dr who ta zubawa itama ta zuba suka ci da yawa tare da Hada tea me kauri su Sha abinsu,yayin da Police suka zo zasuyi bincikensu Akan abinda Mum ta aikata, muna zaune Inspector ya fara yiwa Nanee tambayoyi yace Maryam matar Daddy tace ba ita ta aika ba,sannan tace ke ta samu a toilet din Daddy kin fito? Kuka Nanee ta fara tace sharrin Maryam ne lokacin Daddy ya sani na wanke Masa toilet sabo da bani da Amfani a wajensa face Yar aikin gyara Masa part dinsa wanda kowa ya san da hakan a gidan,ina ciki ina wanke toilet naji maganar maryam suna hira da Daddy har yayi bacci sabo da ya gaji bashi da hutu,sai kakarin Daddy naji kawai da gudu na fito na iske Maryam dauke da wuka a hannunta duk jini.
Haka Asiya Allah sarki tayi ta bayani tana kuka,Amma dan sanda yace tunda su biyu ne suka Shiga part din Daddy a ranar Dole a tafi da Asiya itama a kulleta sabo da aci gaba da bincike zuwa nan gaba a tura su kotu,ko a jira Daddy ya warke sannan ya fadi wacce tayi niyyar kasheshi sai a yanke hukunci, Tausayin Asiya naji sosai,Ice ma haka muna gani aka tasa keyarta zuwa kurku ku, Danbature yace ki zauna a wajen Daddy tunda Kinga Ba kowa Dr who ma ya tafi gida zai samu yayi bacci zuwa dare zai dawo,Ni yanzu zanje police station Zan kashe kudade a maida Mum da Nanee wuri me kyau inda baza a musu komai ba, farin ciki ya kamani.

Ganin ba kowa na matsa jikin Danbaturena na rungumeshi sosai tare da cewa Ina sonka Mijina Allah bawa Daddy lfy a hankali yace Ameen,idan na dawo kawai ki tafi gida zanzo da dare yanzu Mum na kulle Kinga gida ya rikice Babu me sa Mana Ido Kinga kullum muna tare ba wani boye boye,Murmushi nayi tare da furta Allah yasa komai yayi settling da wuri mu nunawa duniya mata da miji ne,auren sunna,Hmm ai har yau Addua nakewa Abbunki da ya daura min Aure dake,Daddy Yana warkewa Zan fada Masa a sirri, Kiss ya manna min a goshi yace bye tare da daga min hannu ya fita,Ni Kuma naci gaba da Zama Ina kula da Daddy har Karimatu da wasu yaranta masu aure suka zo,Hanna,Murja da Haneefa suna kuka, Karimatu tace Fadila uwar shishigi da kinibibi Nan ma sai da kika San ya akayi kika zo kenan har da barinki jinya kamar babanki, to masu shi sunzo sai a tafi ko uwar iyayi son a cuso Kai gidan masu kudi, tunda kinyi Aure ai sai a barmu musha iska.

Shuru nayi Mata Kuma ban tafi ba Ina jiran Mijina ya dawo sai na tafi kamar yanda ya Umarceni,Hanna da Murja ne suka dinga yiwa Umma Nasiha kan Bata kyauta ba,mutum yazo dubiya Amma taci min mutunci Haka,Mikewa Karimatu tayi tare da ficewa waje fuuuuu tace na gaji da Zama a asibiti na tafi gida idan kun Gama ku taho,mamaki ya kamani Wai matar Daddy guda Yana wani Hali Amma ko 30mnt Matarsa baza tayi na jinya ba, dasu Hanna muka dinga Zama muna Hira sama sama sannan sukace yanzu Dr who zaizo Bari suje su ga Doctor zasu yi magana dashi, suna fita Ni kadai naci gaba da Zama da Daddy Ina kula dashi duk da cewar baya motsi Amma Ina kusa dashi har yamma tayi lis 5pm sannan Danbature ya dawo lokacin muna zaune dasu Murja Yana shigowa na kalleshi gaba daya hankalinsa a tashe yake,idonsa jajir,da gani Yana tashin hankali,Murja tace sannu Ice sai hakuri ka dinga kwantar da hankalinka,Ido na tsura Masa nima hankalina ya Gama tashi kamar zanyi kuka,Ni Kawai tausayin Mijina nake ji,ya Zan iya tafiya na barshi a wannan halin tsoro nake ji Kar wani abin ya sameshi idan bana kusa,kallonsa nayi tare da kwabe Masa fuska kamar Yar yaye zanyi kuka na kasa saita kaina,ganin Haka yasa ya Dan yi dariyar yake da gani iya labbansa ce,ya kyafta min Ido Yana tuna min da mutane a kusa Kar a gane mu, kafada na makale irin bazan daina ba,Murmushi yayi ba shiri,su Murja Basu San me muke ba hankalinsu na kan yaransu da suka zo dasu,da yatsa ya nuna min Haneefa Wai suna gani,Baki na murguda Masa irin Ina ruwana Ina Kuma nuna Masa idonsa da hannu yayi red,Yana gyarawa Daddy kwanciya ya nuna min kofa da kafarsa Wai na tafi gida,Yana shafa cikinsa yunwa na damunsa maana naje gida na Masa girki.
Da sauri na mike tunawa da Bai ci komai ba na yiwa su Hanna Sallama na tafi, shima yace Bari naje Naga Doctor yanzu Zan dawo.

Ina tafiya naji kawai an jawoni wani lungu da karfi,Ina Jin kamshin turarensa na gane Danbaturena ne,da sauri na juya na rungumeshi ganin ba mutane a wajen abinka da private hospital Kuma a Lagos Wanda kowa harkarsa yakeyi, fuskarsa na shafa kamar Zan shige cikinsa nace mene ne?Dan Allah ka kwantar da hankalinka,yanzu Dr who zai zo Yana zuwa ka taho gida kaci abinci ka huta sai kazo ka karbeshi shima ya huta yau ka kwana da Daddy, Ok yace min ki kular min da kanki kinji, Inshallah nace ka daina damuwa kaji,yace to, Shagwaba na fara Masa Ina doka kafafu Allah idan baka dawo ba komai dare sai dai kaga nazo Hospital din nan na kawo maka abinci,samun kwanciyar hankalinka kazo gida kayi wanka ka huta sannan ka dawo asibiti,Zanzo Mana tunda kince ai nace zanzo ya zanyi tunda gimbiya tace ai ban Isa ba,Murmushi nayi tare da saka Hannuna cikin nasa nace take heart my Love,Kai ya jinjina min tare da manna min kiss a hannu na, hannu na Mika Masa muka tafa tas nace sai kazo Zan yi girki me dadi na tafi,Yana murmushi,gaba daya bakin cikinsa ya yaye ji yake kamar ya hadiyeni ya huta.

Koda na Isa gida kitchen na wuce kawai nasan yana son pounded yam da miyar kwai Tasha Naman rago Haka na shiryata sannan na hada Fruit salat sabo da baya cin abinci barkatai,Bayan na Gama tare da Binto me aiki muka Kara gyara gidan ya dauki kamshi da kyalli sannan na fada toilet nayi wanka tare da Sallar Magrib,Ina azkhar har Isha tayi nayi sallar sannan na zauna na tsara kwalliyata na hade cikin gown iya gwiwa ce ta cikin lefena take, tayi min kyau sosai na zauna a Palo Ina jiransa,ban Dade ba naji dirin motarsa farin ciki ya ziyarceni da sallama ya turo kofar kawai ya shigo a nutse na mike na Isa gareshi.

Murmushi na Masa kamar yau na taba ganinsa Haka nake murna,shima Haka sosai ya rungumeni a jikinsa Yana kallon shigar danayi,na Masa kyau yace wow kinyi kyau I missed u ya Kara hugging dina a hankali nace I love you Danbaturena, muje kayi wanka ka kaci abinci ka huta sai ka tafi Hospital Kaine Babba ya Dace kana kwana kaima ba Dr who ba,dadin kalamai na yaji ya Kara Sona a ransa a fili yace Allah ya Miki Albarka Baby,Ameen na furta kana muka haura sama cikin bedroom, na tayashi ya cire kayansa Haka wanka ma na tayashi,kafin ya shafa Mai na zabo Masa kayan da zai sa ya sasu kuwa kana Nan Kaya ne na bashi har winter jacket sabo da Ana sanyi sanyi ko zai jin sanyi a hospital sai yasa Abarsa,tana sakale a hannunsa ya rike Ina taje Masa sumarsa,sai kamshi yakeyi sannan muka sakko Dining na zauna na dinga dura Masa abinci sai da ya koshi yaci da yawa sannan na kyaleshi.

Ya huta na 1hr 9pm nace to tashi ka tafi,kwanciya ya gyara a jikina tare da cewa ban son tafiya na barki Ina sonki,Hmm Daddy ne fa Oya tashi na rakaka mota,a kunne ya rada min yau bazan yi ba kenan? Me zakayi na furta Ina dariya Dan na gane me yake nufi,Daddy ba lafiya mu muna shagali bazai yuwu ba,rowa kawai Zaki min dama Baki damu Dani ba Haka Zaki Bari na tafi so kike tunaninki yayi min yawa?

Sai Gobe yau Hutawa zakayi,kawai bakya so ki bani shi yasa kike damuna na tafi,Baki na bude nace na Isa amma yau Allah na gaji kayi hakuri sai Gobe,ok na hakura Amma Gobe da Asuba Zaki ganni,dariya nayi na furta sabo da nacinka?Yeah ya furta Yana Mikewa,muka fita har jikin mota na rakashi na sa Masa bargo tare da flask na ruwan Na'a na'a tea a Bayan mota ko zai nema nasan kullum sai yasha,ya Shiga mukayi sallama ya tafi Ni Kuma na koma ciki nayi Shirin bacci na kwanta.

Mum kuwa kafin Aliyu yaje ya biya kudi ba karamin duka taci ba a hannun police sun sauya Mata kamanni, Asiya kanta sai da Tasha nata da farko Allah ne ya taimakesu Aliyu yaje ya kashe makudan kudade baza a taba kowacce ba sannan wuri me kyau aka ajiyesu Ana ta bincike Amma har yanzu Mum ta rantse ba ita bace shine kawai suka Mika su kotu jibi Monday za a Fara Shiga kotu,Mum ta dauki lauya,Asiya kuwa Aliyu shine ya daukar Mata kwararren lauya da zai kareta shi ya tsaya Mata sabo da yanda yake son Nanee dinsa ba ruwanta da duniya,Mum kuwa Tata ta Kare duk su Linda da Yan uwanta sun yanki ticket sun gudu France dinsu Dan karma a nemesu sheda ko a hada dasu har mazan sun tafi,Meena kawai kanwar su Ice ce ta rage ta maida kurkuku gidanta ko yaushe tana can ganin Mum Bata zuwa ma Hospital ta uwarta take kawai.
Asiya tana ta rantsuwa itama ba ita bace,bincike da yayi tsanani sai akace Dole a Kama Karimatu ma itama ai Matarsa ce sabo da Haka tana komawa gida da tabar Hospital Bayan ta ci min mutunci sai ga Yan sanda sun tasa keyarta aka tafi da ita itama Ana gana mata azaba kan su fadi gaskiya Amma ko wacce ba ita bace tace, Bayan kowa yasan Mum ce ta aikata hakan.

Aliyu Yana karasawa Hospital Dr who ya tafi gida aka bar Aliyu shi kadai Yana kula da Daddy,Cikin dare na farka 2:30am na Kira Aliyu a waya yayi mamakin ganin banyi bacci ba,ya kashe ya kirani back yace Me yasa bakiyi bacci ba? Farkawa nayi naji ina tunaninka ya jikin Daddy? Da sauki,Kai bakayi bacci ba? Kin taba ganin me jinya yayi bacci,Ana danyi Mana tunda ba motsi yakeyi ba nasa ma Blanket a mota ka dauka ka kwanta pls ka samu bacci ko Yaya ne,da safe Zan dawo gida sai nayi,ok nace yace kwanta kiyi bacci my wife I love u,me too nace sannan na kashe wayar naci gaba da bacci na.








AsmaBaffa
[9/4, 10:26 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕









81-85









Official









By
AsmaBaffa





Sameeran Gaya, Sajnah,Fatima Maina,Khadija A Hamza,H B K,Maman Meenat,Yar Aliyu ce,Hauwa j,Adama suleiman.
Ina matukar Godiya gareku.
Thanks


Ga page naki manyan fans..
Gimbiya safeeyya,Maman khalifa,xeee Gwanda,Mm Sadiq,Faiza Usman,Ummu Ikraam,Ummi,Nusaibatutu and Haulat bawa kamba.







Washe gari yace da safe zai dawo ban shirya breakfast da wuri ba,Sai 10am na Gama komai har gyara gida etc sannan naci uwar wanka cikin material me tsada Riga da skert nayi mahaukacin kyau kamar zanje fadar shugaban kasa.ina fesa turare sai mutum kawai na gani naji Sallamarsa a bayana,nayi mamakin ya akayi banji Karar motarsa ba, juyowa nayi tuni har ya rungumeni, a Kirjinsa na kwantar da kaina tare da Kara shigewa jikinsa sannan nace Ina kwana,ka tashi lfy? Ya jikin Daddy? Lfy Alhmdllh,da sauki ya furta sannan yace Bari na fara wanka na gaji,Toilet ya Shiga yayi wanka ya shirya cikin Shadda light blue yayi kyau sosai, Abincin ma cewa yayi na kawo mana Bedroom ya gaji baya son zuwa Dinning,Bayan na kawo muka ci muka koshi sannan ya kwanta bacci me nauyi ya daukeshi.

Bayan kwana biyu Duk wani shirye shiryen Shiga kotu anyi,da dare Dr who yau shine a Hospital Ice Yana gida muna tare dashi Ina kwance a jikinsa nace Ni kuwa Danbaturena sai nake ganin Bai Dace ace kunje kotu ba,domin wani tonon silili ne ga Family naku a idon duniya,Mai zai Hana a San yanda za ayi a dakatar da kotu sai Nan gaba tunda Ana sa Rai Daddy zai tashi sai ayi abin a gida.
Murmushin takaici yayi tare da cewa kina tunanin ko mun Hana hukuma Kuma zata Bari? Ai matsalar a hukuma ne Dole zata ce sai tayi aikinta, Ni Kuma nafi son ma aje a gano Mum ko Daddy ya Fahimci makircinta,Uwa uwa ce fa ka daina furta haka,Amma ai ta saba dokar Allah duk da cewa Ina son abata hakan bazai hanani fadar gaskiya ba,kotu kuma bamu mukayi Kara ba Hukuma ce take aikinta.

Dogon numfashi naja kana nace to Allah bayyana gaskiya,Ameen yace muka ci gaba da hirarmu ta masoya daga Nan salo ya canja muka koma soyewa rabon da muyi tunda aka kwantar da Daddy a Hospital sai yau,munyi missing juna sabo da Haka ba karamin darzar juna mukayi ba,wannan Rana itama ta Shiga tarihinmu sabo da ba karamin farantawa juna Rai mukayi ba munji a jikinmu,Ni kaina lokacin ji nake kamar Zan Kama da wuta.
Washe gari fresh muka tashi ko wannenmu zuciyarsa fari Kal muna Kara kaunar junanmu.
Yaune Monday yau Kuma za a je kotu.

Munyi shiri muka tafi,Amma Ni a taxi naje daga baya Dan kar ma a ganmu tare da Ice,Kotu ta cika makil da mutane,dangi da Yan uwan Daddy,Haka yaransa kaf,shi Kuma Yana asibiti tare da Hanna da Murja suna kula dashi.Lokacin da aka kawo Mum,Nanee da Karimatu abin ya bawa kowa tsoro,kowannensu Kamanninsu sun canja,Sunyi duhu,sun rame ga jikinsu gaba daya duka ne musamman Mum,Ice Bai iya kallonsu ba,Dr who Kam hawayen tausayin Mum dinsa yake kamar ba ita ba.
Ina zaune aka gabatar da Kara.

Lauya me Kare Nanee ya mike ya dinga kwadowa Mum tambayoyin da suka Sa ta rude ta gigice ta Kuma kasa amsawa,Haka yayiwa Karimatu ma ita Karimatu ma Kuka ta saki duk Masifar Nan Babu anyi laushi.
Nanee kuwa a nutse ta amsa tambayoyinta fes ba tare da tsoro ba,Haka Shima lauyan Karimatu shima ya mike ya Shiga zazzageta da basirarsa har kan yaran gida,ya gama ya zauna,Sai na Mum ya mike ai sai akaji na Mum yafi kowa hazaka da sanin aikinsa Wanda ya birge mutane sai dai an rigada an San bazai yi nasara ba sabo da Mum Bata da gaskiya, Haka aka tashi Ice ya Fadi duk abinda ya sani dangane da halayen Mum dinsa duk da cewa wani abin duk ya rufa Mata asiri Bai fada ba,itama Karimatu Haka aka sa yaranta Kuma suka Fadi gaskiya,Nanee ma Haka,shi kanshi alkalin ya san Nanee Bata cikin wacce zata iya ko Marin wani bare kisa Amma Dole ayi bincike da ita.

Alkali yace ya dage Kara zuwa kwana Bakwai ko wacce ta kawo shedu masu karfi sannan aka fita daga koti Mum tasan baza tayi nasara ba.
Tuni Ice yace a Basu belin nasu sannan aci gaba da zuwa kotu sai daya kashe kudi masu yawa sannan aka bada bail nasu.

Bayan an koma gida kowa ya dinga Sharhi Akan shariar har a gidajen radio,Mum kuwa tuni nadamar muna Nan halayenta takeyi tana tuba tana Rokon Allah ya yafe mata ita kadai tasan abubuwan da take aikatawa Marasa kyau, Karimatu anji wahala an gane shayi ruwa ne tausayin kanta take ji kawai tasan itama Halayenta Basu yi ba Sam Shi yasa Allah ya jarabceta da hakan,gata cikin mawuyacin Hali.

Lauyoyi sai aikin hada shedu kowannensu keyi,sabo da sun San alkalin ba ruwansa da wuri yake yanke hukunci a wuce wajen,kusan kullum sai naje Hospital duba Daddy, yau ma daga schl asibitin na wuce kawai,Nasan Danbature Yana can wajen lauyan Nanee suna aiki sabo da ya tsayawa Nanee sosai yasan ma Bata da laifi,Koda na Shiga ba kowa a dakin Daddy sai Saddiqa aka Bari jira duk kowannensu ya bazama wajen lauyan da yake goyawa baya.
Saddiqa tace sannu da zuwa Fadila gwara da kika zo sai ki tayani Zama,ya gida muka gaisa tayi kyau sosai ta waye gashi ta iya dressing nace Saddiqa kinfi da hankali yanzu,Murmushi tayi tace ai na girma bakya ganina cikakkiyar budurwa,Muna zaune muna Hira sama sama Daddy ya motsa kafa Saddiqa tace yee yayi motsi tsaya ki gani pls, ai kuwa Yana motsi ya bude idonsa kadan sannan ya budeshi tar tare da kallonmu, da sauri muka je jikin Bed din muna sannu Daddy ya jikin? Muka ji yace da sauki yarana, dukanmu ya sanmu sai ya danyi Murmushi kadan yace sirri zanyi daku na Fahimci Kuna da nutsuwa da sauri nace to Daddy,karku fadawa kowa na farka,kawai kuyi shuru da bakinku,da sauri mukace to Inshallah munyi alkawari mukayi Murmushi,da kansa ya mike tare da Shiga toilet ya Dade sannan ya fito da Alama har wanka da brush yayi,da sauri yace nasa key a kofar Kar wani ya shugo,Saddiqa tasa lock sai da yayi Sallar Azahar da laasar,kafin ya idar na hada Masa tea me kauri yasha tare da chips da kwai sannan ya koma ya kwanta kamar yanda yake da.

Knocking muka ji Ina budewa Naga yaran gidan ne suka yi ayari suka zo,farin ciki kawai nakeyi Sabo da nasan Danbature kwana Nan zai daina tunanin komai,hankalinsa zai dawo jikinsa, sai Magrib na tafi gida Ina zuwa Naga Ayman tare da Ice suna palo Yana ganina yazo ya rungumeni da sauri Yana ke da nace ki dawo gida,Ina can Asibiti kafa sani,to ya Naga kina wani nishadi?, Ba komai kawai nace sabo da munyiwa Daddy alkwarin rike Masa sirri,sannan magana idan aka fada maka ba sai ance karka fadawa wani ba itama Amana ce Babba rike Maganar wani,shi yasa duk yanda muke da Danbature ban fada Masa ba Nima.
Ya kamata a kiyaye a alumma wasu duk abinda ka fada musu sai sun kwashe sun bada labari,ko mijinsu suce ai Mijina guda ai Dole na fada Masa, magana ma Amanace ba sai ance karka fada ba.

Bayan mun gaisa da Ayman na Shiga kitchen na kawo musu tarkacen motsa Baki,Ayman yace Dan iskan yaron Nan ko ruwa Bai bani ba tun Rana Wai sai kin dawo shi tsoronki yake ji,Kinji sharri ai tasan bazan Ce Ina tsoronta ba cewar Ice,Dariya mukayi sannan na wuce sama na barsu a Nan.

Hajjo Maman Daddy har yau itama tana gadon asibiti Bata motsi sabo da Haka itama likitoci suna ta faman kula da ita,lauyan Mum Yana wajenta Yana Mata tambayoyi ta yanda zaiji dadin kareta,yayin da lauyan Nanee ma Yana wajenta, Karimatu kuwa sabo da Bata da mutunci masifa tayiwa Lauyan nata har ta fusata shi yace ya fasa yi Mata aiki yayi tafiyarsa.
Lauyan Mum yace Da kika Shiga me yasa aka kamaki da wuka? Sannan yaranki ma sun furta a kotu cewar kina furuncin halaka mijinki me yasa?
Kuka Mum takeyi cike da Nadama tace tabbas na Fadi Haka da dama sannan sunji a waya Ina magana da boka na Amma harga Allah na kasa aikata Masa hakan.

Dama Ni gani nakeyi kudi sune kadai Jin dadin duniya shi yasa nake burin mallakarsu har nayi tunanin kashe Daddy Amma wlh na gwada hakan Amma na kasa,wukar Kuma a kasa na ganta kusa da Daddy na dauka sabo da na rude har mutane suka kamani, Sannan Ni Kishiyata Nanee ita ta fito daga toilet sannan sai ga Karimatu ta ukun ms ta fito ta Bayan labile tana Salati,to Ni an kamani da wuka,Nanee tana toilet mijinmu ma ko kulata bayayi ta Zama Yar aikinsa,Karimatu ta fito a Bayan labile wa zaka ce ita tayi kisa? Dole ace nice tunda Ni aka gani da wuka.

Haka suka dinga maga na da lauya sannan ya tafi,Ice kuwa ko ta kan Mum baya bi Yana bangaren Nanee dinsa Wanda hakan yasa Mum cikin bacin rai Amma tasan laifinta ne babu Wanda zai damu da uwa irinta,sabo da Haka gaba daya ta samu kayan tsafe tsafenta ta tarwatsa su ta zubar da komai ta tuba ga Allah ta daina Shan komai,ta daina Abubuwa Marasa kyau zata gyara rayuwarta,Haka taje wurin bokanta ta Basu makudan kudade kan a karya duk wani tsafin da ta yiwa Daddy da sauransu,dama Imaninsu kudi Nan suka lalata komai,Daddy Yana bacci ya farka yaji jikinsa Fresh kamar an cire Masa nauyi,Nan take hankalinsa ya saitu ya dawo normal,Haka ragowar ma Ice ya bar jikinsa,Dr who kuwa kakarin Amai ya fara yi kafin kace me ya fara sheka uban Amai duk Aman nasa wani baki ne a ciki tare da wasu tarkace sai da ya amayar dasu tas sannan ya dawo garau.
Nanee kuwa burburwa ta fara da Shure Shure karshe bacci ya kwashe ta,Haka Karimatu ma taji canji a jikinta.

Babu Wanda ya gane tsafin Mum ne sai Dr who kadai da yayi aman tarkace a toilet sannan yaji lafiyar jikinsa ta canja Bai San Kuma na me Mum tayi Masa ba wannan amsa sai daga bakinta.
Daddy Yana kwance har yau Bai nuna ya warke ba,muma kuma da muka sani bamu fadawa kowa ba,ko yaushe aka Shiga kotu Yana Jin labarin yanda aka Kare har yau wacce tayi kisan yake so ta fada da kanta Amma har an Shiga kotu sau Uku Babu labari,an kasa gano gaskiya a cikin Matan,Haka bincike har yaran gida da makwafta Amma Babu labari,Daddy ya yanke Hukuncin Shiga kotu na hudu zai halicci zaman yasan wacce tayi hakan zata ganshi taji tsoro ta bayyana kanta.

Danbaturena duk ya Shiga damuwa sabo da ba hutu ba Zama kullum suna kan case din,sai wahala yake akan Nanee ganin itace baiwar Allah, Karimatu kuwa Bata ma da me kareta kawai tambayoyi take Shiga ana Mata tana amsawa,an kwashe fin wata guda Ana tafka Sharia Amma ba labari.
Gone ne za a Shiga kotu na hudu ko wanne bangare a shirye suke.

Ni kuwa tunda Sharia tayi karfi Danbature baya Zama ko kwana baya yi a gida daga asibiti wurin Hajjo da Daddy sai wajen lauyoyi kullum a gurguje yake zuwa yaci abinci da wanka ya fita Haka Ina kwantar Masa da hankali ganin

Please Login or Register in order to submit comment