Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zakayi Dan kayi Masa aski kyauta shine zaka zage shi ga hamsin Dinka Nan bama son kyautar.

Me aski ya taso da masifa kamar zai mareni Yana kamar ba Ke ba Fadila,kin canja ke da kike me hakuri da kunya ga kawaici Amma akan Mahaukaci kin lalata rayuwarki,idan Baki sani ba ki sani kaf garin Nan ba a kallonki da mutunci zaginki akeyi, tsakiya Bature ya Shiga ya kareni wani kallo ya watsawa me aski sai gashi yayi mukus.
Gidan wasu samari na tsaya nace Dan Asabe Dan Allah ku bashi aron bayinku zaiyi wanka Baki bude suke kallona,Rabiu yace Fadila ko dai kema kin zare ne Taya Mahaukaci zaiyi wanka?,a wajen nace idan zaku bashi ku bashi, daya cikinsu yace wlh kika sake sai na fadawa Abbunki kin San dai halinsa,Nan tsoro ya kamani na tuna dukan Dana ci nace Allah baku hakuri naja Bature muka tafi Rafi da ruwa ke zuwa garai garai.

Da kaina na gwada Masa yanda ake wanka Amma yaki yarda sai na bashi sabulun da soso nayi kamar na tafi na labe a Bayan bishiya,ya Dade Yana tunani sai Naga ya cire kayansa kaf daga shi sai Boxers ya Dan Shiga gefen kogin abin mamaki yayi wankansa tas yanda kowa keyi har ta cikin boxers din Bayan ya Gama ya fito kawai sai na rufe idona Allah yasa wajen ba mutane ya buya Bayan bishiya ya Sa boxers dinsa Dana wanke da singlet,sannan yasa shardarsa Tasha wanki da guga.

Ina kallo yayi aswakinsa tas,sai da ya Gama na dawo, na kwashe kayan daya cire na zuba a ledar.sai Hamma yake da alama yunwa yakeji.
Haka na siyo Masa soyayyar doya da kwai da ruwa na dawo na kawo Masa,hayam hayam ya cinye ya shanye ruwan da gani ya Dade rabonsa da abinci tausayinsa ya kamani,na koma na Kara siyo Masa shinkafa da Miya da wake Nan ma ya cinye tas ya watsar da sauran ya Sha ruwa, sannan nace taso muje yawo kaga gona alama na Masa da hannu ya biyo Ni.
Yana Bina muna tafiya Ina ta Masa labari iri Wanda Bai ko kulani ba.










AsmaBaffa
[9/4, 10:25 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕








3









Official








By
AsmaBaffa













MARCYCOOL, FLOWER,AUTA,ASYCOOL and JANNAT TA SALIM page dinku ne fa.ku kwashe min da tafi😆.







Muna tafiya dashi wani munafukin ya ganmu da sauri ya Kira Abbu a waya ya sanar Masa ga Fadila can sun tafi yawo cikin daji da Mahaukaci,ba tare da na sani ba sai ga Ya Musa tare da Ya Salman a fusace, ya Salman bai jira komai ba ya kifa min Mari har biyu,Dan Bature a hasale ya shaki wuyan ya Salman tare da yarfa Masa Mari sai da jini ya fito ta Hancin Ya Salman,Kuka na fara ya Musa da Ya Salman suka hada karfi da karfe suka fara dukan Dan Bature sosai,Gefen kansa ya fashe jini ya fara tsartuwa,Ni Kuma Ina kuka na Kare Dan Bature Ya Musa ya kawo Naushi ya sameni a Hanci Nan take Hanci na ya fashe jini na fita,Dan Bature Yana ganin haka ya Kara haukacewa ya mike ya Shaki Ya Musa da Salman ya gwara kansu,wani Naushi da yayiwa Ya Musa sai da ya zube har kasa,mutane dake kusa suka fara kawo dauki sabo da Dan Bature yayiwa Ya Salman jina jina Haka ya Musa ma tuni yaci dukan kawo wuka,Mutane da yawa suka taru tare da rirrike Dan Bature dake Huci kamar Zaki,Wata girgiza yayi gaba daya ya watsar da mutanen da suka rikeshi sannan ya Fadi a kasa shi kadai ya fara jijjiga kamar me fyarfyadiya sai dai wannan har wani gurnani ya yakeyi ya dafe kansa,Gigicewa nayi Ina uban kuka Ni Sam Bata su Ya Salman nakeyi ba hankalina Yana wajen Dan Bature,Addua na Shiga tofa Masa tun Yana yi da karfi har ya dawo yi a hankali sannan jikinsa ya saki yayi luf a kasa kwance Nan da Nan bacci ya kwashe shi, lokacin na cire gyalena na daure Masa kansa da Gyalena inda jini ke zuba.

A matukar fusace Salman da Ya Musa suka mike jikinsu duk jini suka fara cin ubana,Bulala suka Sa suka zaneni tas sannan Musa ya sabani a kafada suka tafi Dani giga,Ni Kuma kuka kawai nake Ina kallon Dan Bature cikin jini ya Dan bude idonsa da kyar Jin muryata Ina kuka Ina kiransa Dan Bature Ina Miko Masa hannu,Ya Salman ya lankwashe Hannun da na Mika sai da yayi Kara,na tsandara ihu,Dan Bature Yana yashe a kasa abin tausayi ya bude idonsa Yana kallona bazai iya tashi ba,shima daga kwance ya Miko min hannu,karfin kukana na Kara.

Muna zuwa gida Abbu yau Bai dakeni ba, meeting din gaggawa ya hada tare da iyayensa,Iyayen Hajiyarmu da kannensa sai Kuma Yan gidan namu kaf yaro da Babba, a tsakiya suka sani Ina Hawaye.

Abbu cikin sanyin murya yace Fadila nace Naam Ina kuka,yace na biki ta lallami na biki ta lumana,na fada Miki a tsaye na fada Miki a zaune,sannan jikinki ya Gaya miki, yanzu gashi Ina fada Miki da sanyi karki kuskura na fada Miki da zafi wannan bazai Miki kyau ba,me na rage ki dashi? Kinki aure yanzu Kuma kina bin Mahaukaci,Yar iska kike nema ki dawo? Kai na girgiza alamar A'a, yace to bakya kaunarmu mu iyayenki da Yan uwanki kike aikata haka Dan ki zubar Mana da mutunci? Kai na girgiza, yace dubi Yan uwanki na jini yanda Dan iskan Mahaukacin da kike bi ya aikata musu yanzu dadi kike ji kenan? A hankali nace a'a Amma ai su suka jama kansu tunda sune suka tsokaneshi,Duka Hajiyarmu ta kai min Ana magana bakya ji ko, Abbu yace ai ke ta gado halinki tayo Hadiza munafukar banza ai ke kike zugata,Wai an tabo Fada Nan Hajiyarmu tace yanzu dai da tayi abin Tsiya sai ace iyaye Mata ke zuga yaro,Amma sanda yaro yayi abin kirki baza a taba godewa uwa ba ace anyi tarbiya me kyau sai marar kyau sannan miji zai dinga ganin laifin mace, Yafendo tace ke rufe mana Baki yo ke har wani halin kirki ne da ke,Anty da ke gefe tace badan Allah yasa an aure Ni ba ai da abinda yaran Hadiza zasu yi sai yafi Haka,nice nake sasu a hanyar kirki.

Abbu yace na sani Sarai Allah Miki Albarka Antyn Yara,Hajiyarmu zatayi magana Ya Salman ya Mata alama da ta kyalesu,Yafendo ce tace to Fadila tunda tsiya kike ji muma mun shiryeki aurenki saura sati biyu da Talle Mai lemo,Abbu yace Kuma wlh kika gudu daga garin Nan ban yafe Miki ba na cireki a yarana.
Ihu na Shiga tsalawa Yafendo tace kyayi Kya Gama Nan kowa dake wajen suka rufeni da fada kowa Yana tofa albarkacin Bakinsa, sai da suka Gama nace Wlh na daina hakuri daga yau na Zama marar hakuri da mutunci,tunda Haka ne tantiriya zan koma,Kuma matukar aka bani Talle sai na zuba Masa shinkafar bera.
Baki Kawu Salisu ya tabe yace munga irinku kun fi Dubu sai anyi aure ajiku luf.
Mikewa nayi na fita abina ba tare da an bani izinin tafiya ba.

Yau kwana nayi Ina kuka karshe dabara ta Fado min,na koma wajen Abbu Bayan na gaisheshi nace Abbu Dan Allah to Ni dai daka aura min Talle gwara ka aura min Dan Bature ko a daji zamu na kwana zan zauna,Salati Abbu ya saki kana ya fashe da kuka,Ya Salman suka afka dakin Abbu da gudu sun zata wani gagari min abune ya faru da har Abbu ya fashe da kuka Haka har tsakar gida Ana jinsa.

Musa yace Abbu lfy?, Abbu ya Kara fashewa da Kuka Yana nuna Ni da yatsa kamar yaron yaye ban San sanda na kwashe da dariya ba nace Wai Dan nace ya aura min Dan Bature Abbu Ashe Saurin kuka ne da Kai? Ya Salman ne ya Kore Ni shima Yana kunshe dariyarsa.

Gaba daya na canja halina na hakuri da kawaici tunda aka ce zan auri Talle me lemo,yau shiryawa nayi fes nayiwa Hajiyarmu sallama nayi karya nace zanje gaida dangi, harda murna tana sa min albarka, ban tsaya ko Ina ba sai rumfar Talle me lemo,ga lemo ya kasa harda kankana,Talle tunda ya ganni yake faman washe jajayan hakoransa, Ina zuwa da gadara cike da Isa nace Dattijo fere ka yankamin na dari biyar,Talle ya washe Baki yace ai Amarya kyauta za a baki, jiki na rawa yace wannan kwalliyar tawa ce? Kaina na dauke nace ta hadadden saurayina ce,Kai nifa dana maka kwalliya gwara nayiwa Mahaukacin Kare,Baki bude Talle ya kalleni kawai sannan ya yanka min lemo da yawa,nace kankanar fa ko a banza zaka aureni,Nan ma na zabi katuwa nace yanka ta,yamin yanda nake so Yana wani washe Baki na dauki ledojin nayi tafiyata.
Na Shiga gida kowa Yana sa rai zasu Sha lemo da kankana sai suka ga na wuce na dauko Sallayata katuwa Ina budawa da gadara tunda yanzu na canja halina tunda akace za ayi min auren Dole,ficewa nayi daga gidan da kayana,inda nasan zanga Dan Bature naje,Allah sarki na ganshi futu futu duk yayi dirty ya rame sabo da yunwa yau kwana hudu kenan bamu hadu ba,ji nake kamar na Shekara wani dadi nake ji Dana ganshi,tunda ya Hangoni ya mike tsaye da sauri Yana Murmushi Wanda shima na farin ciki ne, wani azabar kyau yayi ga kwarjini.

Duk da Dirty da yayi bana kyankyaminsa na Shimfida Mana Sallaya tare na zauna sannan na nuna Masa shima ya zauna tun kafin na bude ledar ya fisge ya bude,Amma bazai iya Sha da kansa ba sai dai ya dinga damalmalawa ta baci,da kaina na Shiga bashi Yana Shan kankanar, har Hannuna yake rikewa ya zuke har cizona yakeyi sabo da sauri, idan muka hada Ido Ina ta murna Ina Murmushi burina ya cika Yana cin abin da na kawo,idan muka hada Ido indai yaga Ina dariya sai shima yayi Murmushi Yana min wani kallo me zautar da hankalin duk Wanda ya kalla,ga wani kwarjini,kyau,sura da cikar zati.

Yasha fruits din da yawan gaske musamman kankanar na zuba Masa ruwa ya wanke hannunsa Amma ya kasa wanke hannayen Haka na kwara musu ruwa ya janye hannayensa da sauri ya boye abinsa,faratansa nagani Sunyi zako zako,wani yaron Almajiri dake kiwon shanu a Bayan gari na aika shago nace sauri ka siyo min Reza, Bai dauki lokaci ba ya kawo min Reza, hannu na Mika zan jawo hannunsa Amma yaki yarda sai ma bar min wajen da yayi tare da shigewa cikin Dajin abinsa.
Gida na tafi Ina sauri sabo da na Dade.

Ina sauri sabo da gaskiya na Dade,ina komawa gida Hajiyarmu tasa Salman da Musa suka zaneni Nasha kuka Amma kamar me kunnen Kashi washe gari ma saida na saci jiki naje wajen Dan Bature.
Ranar Kuma Abbu yace ya haramta min fita ko kofar gida,Amma kwana uku na karya dokar sabo da yanda tunanin Dan Bature ya addabeni bani da sukuni Sam tunanina tausayinsa nake ji kawai.

Abbu tunda ya samu labarin yau na karya dokar na fita ya samu Yara majiya karfi mahaukatan fulanin daji suka kamo Dan Bature har kofar gidanmu na fito Ina kuka Ina bada hakuri me ya Muku Dan Allah kuyi hakuri karku taba lafiyarsa,Abbu indai zuwa wajensa ne wlh na hakura bazan sake ba Dan Allah karku yi Masa komai zaku dauki zunubi,a gabana Abbu yasa kartan Nan suka fara jibgar Dan Bature da makami,suka Masa jina jina sannan suka jashi can gefen titi suka yasar dashi Ina ta uban kuka na fito da gudu zan bishi Abbu yasa Musa suka rikeni suka maidani gida,yau nayi kukan da ban taba yi ba a duniya duk me Imani sai ya tausayawa bawan Allah Nan.

Abbu yasa na daina fita ta Dole Haka Dan Bature ya karaci jinyarsa ya warke duk ya Kara lalacewa ya rame,ga dirty Yana cikinsa farcen Nan zako zako Suma ta Kara taruwa.
Yau ya rage saura kwana daya a daura min Aure da Talle,kasa jure bacin Raina nayi na saci jiki na tafi Office din Yan Hisba dake kauyen na Kai Karar Abbu za ayi min auren Dole.

Nan danan Yan Hisba suka min Nasiha sannan suka je har wajen Abbu suka kwatar min yanci na,suka yiwa Abbu nasiha sosai,Abbu yace naji na hakura Amma bazan daga ranar daurin aure ba ta kawo min Wanda take so yau.
Ba tare da tunanin komai ba nace na Amince, da yamma na fito neman Dan Bature can kusa da wata bola na hangoshi Yana kwance a tsakiyar Rana,sai karkarwar sanyi yake yi da Alama zazzabi ne ya kamashi,tausayinsa ya kamani jikinsa duk raunikan da Su Ya Musa suka dake shi.

Chemist naje na taho da me chemist din ya ganshi ya bani Magunguna yace a bashi,nace nawa? Me Chemist yace kyauta na bashi idan Bai warke ba ki dawo a canja wasu.

Da kyar a cokali na jika maganin ya narke Ishu me chemist ya tallafa min na bashi maganin da kyar ya Sha.
Haka Ishu ya Kira min wasu maza suka dauki Dan Bature aka kaishi inuwa Nan bacci ya kwashe shi,a wajen na yini Nima sai da yaci baccinsa ya koshi sannan ya farka da sauki Don maganin yayi Masa aiki,Abinci na naje gida na dakko taliya da miyar kifi na siyo ruwa na zauna na bashi da kaina Yara an taru Ana ta kallonmu, saida na tabbatar ya koshi sannan na sake bashi maganinsa lokacin Ishu me chemist yazo duba shi, na mike zan tafi gida naji ya rike min hannu, juyowa nayi Ina kallonsa nace me zanyi maka? Ina Masa Maganar kurame, Hawaye ne Naga ya zubo Masa sharrr....Ishu yace subhanallah wannan wlh duk yanda akayi haukar tasa me Tsafta ce,ba shahararriya bace Amma Mahaukaci shahararre ba Haka yake ba Sam, Allah Baki ladanki Fadila tabbas kina kokari Kuma sai Allah ya Baki Lada.

Komawa nayi na zauna kusa dashi na Shiga lallashinsa cikin sanyin muryata nace kayi hakuri anjima zan dawo kaga Abbu na zai dukeni, ya sunanka? Kallona yayi baice komai ba,nace ur name pls, kansa ya dafe ya Lula tunani da sauri ya zabura ya tuna kenan yace Aliyu Hydar,Murmushi na saki nace nice name, na Dade ina lallabashi sannan na mike na tafi ba tare da ya rikeni ba sai Murmushi da yayi min kadan.

Misalin Karfe 10 na dare Hadari ne ya Hado sosai,ba abinda ya dameni irin tunanin Dan Bature gashi bashi da lfy idan ruwa ya zaneshi shike nan Kuma.
Zumbur na mike na lallaba ba tare da kowa ya sani ba na bude gidanmu na fita da gudu naje inda na Saba ganinsa, hannunsa na jawo da sauri muka tafi gidanmu dashi,ina ta jansa,tsorona idan na barshi a zaure za a ganshi ayi Masa wani abun kawai na kaishi dakina na nuna Masa bed dina nace kwanta yaki kwanciya,nayi nayi Amma yaki kwanciya sai ya koma kasan ledar dakina ya kwanta,Bargo na lulluba Masa ya cire tare da jefarwa Yana Bata fuska.
Kofar na kulle Masa sannan na koma dakin Hajiyarmu nace Tsoron tsawa da walkiya nakeyi yau a Nan zan kwana,Hajiyarmu tace Kya karaci gulmarki gulmawuya.

da Sassafe na farka kafin nayi sallah na budewa Dan Bature kofa Wanda dama ya gaji da Zama a dakin Ina budewa ya fice daga gidanmu da sauri,Abbu Yana kofar gida lokacin sai ganin Dan Bature yayi ya fito daga gidansa.

Abbu yace Kai Kai.....Amma ko kallonsa baiyi ba yayi gaba abinsa, da sauri Abbu ya dawo gida kafin nayi magana ya rufeni da duka tako ina,.
Yau zan daura Miki aure Dan ubanki tunda Baki da mutunci Haka ya fice a fusace ya sanarwa Talle da danginsa,nan danan aka taru a kofar gidanmu,gashi yace idan na bar gari Bai yafe ba bare na gudu.
Office din Yan Hisba na koma Ina kuka nace Abbu baiji nasiharku ba,Haka muka taho da Yan Hisba filin daurin aure an cika makil.

Dan Hisba ya fara waazi da Nasiha,Abbu yace nace yanzu ta kawo Wanda take so idan Bata kawo ba to wlh na daura da Talle,Talle ya washe Baki yace Bata da wani sai Ni a daura kawai, Ina Hawaye nace Ni Dan Bature nake so.
Abbu yace to kunji Mahaukaci take so,Dan Hisba yace a kawo Mana shi muji idan yasan sunansa sai a daura dashi tunda tace ita so take ta taimaka Masa ta ceto shi daga halin da yake ciki,,Nan mutane suka tafi neman Dan Bature suka ganshi a zaune kamar me hankali, mutanen kauyen har Yan hisban ba wani ilmin addini garesu ba, sukayi juyin duniya ya tashi bare ya bisu sai da nazo wajen da kaina sannan ya bini,nace ka fada min sunanka Dan Allah kayi magana sunanka za a daura Mana aure yanda zan kula dakai daga halin da kake ciki,wannan itace damar da zan iya yi maka komai,zan aureka ba Wai Dan Ina sonka ba,don kawai na taimaka maka,ka duba irin wahalar Dana ke Sha a kanka.

Sai da na Dade ina Masa maganganu nayi Masa Zancen kurame ya fada min sunansa,da kyar kamar me koyon magana yace Aliyu Hydar.

Mutane suna kallon ikon Allah Dan na birge mutane da dama,su Ya Salman duk suna wajen,Mahmood yaji tausayin bawan Allah yace na biya Masa sadaki,aka dauki kabbara Banda Abbu da Yan gidanmu babu Wanda yake murna,Hajiyarmu kuwa tana can tana ta kukan bakin ciki, Me gari yace Nima na bashi karamin Gidana na kusa da bakin titi Dana Gina kwana Nan, Allah yasa ban zuba Yan haya ba,na Basu aro su zauna har lokacin da Allah zaiyi ikonsa ya warke.nan ma aka Kara kabbara,Wani Alhaji me kudi shima yace zan Mata kayan daki,Abbu ya tabe Baki.
Kawu Salisu da Kawu Usman suka ce a matsayin mu na iyayen Amarya zamuyi Mata lefe,sannan zamu dinkawa mahaukacin nata Kaya kala goma da takalma kala uku.

Wani cikin dattijai yace zan zuba Musu kayan abinci dai dai gwargwado.
Farin ciki ya kamani Lallai Dan Bature Yana da kashin arziki.

Nan take aka Kara tambayar Dan Bature Sunan mahaifinsa yaki yin magana Dole aka Kara Nemo ni da kyar ya Kara lulawa tunani yace Sulaiman Saleh,nace Aliyu Sulaiman? Yayi banza Dani ya koma can jikin bishiya yayi kwanciyarsa bacci ya kwasheshi,Nan Kuma na fada musu me yace Nan take aka daura min Aure Aliyu Sulaiman da Fadila Tahir kan sadaki Dubu ashirin Mahmood ya biya cash, Ana daura aure Ina dakina Ina kuka yanda duk Yan uwana da iyayena suka tsaneni.

Hajiyarmu da Yan uwanta tare da Kakanninmu sai fada suke min Ina ta kuka,Anty ma tazo ta dinga habaici,Ya Musa zagi ba Wanda ban Sha ba,Ya Salman da Mahmood ne kadai suka dinga min Nasiha tare da lallashina,Abbu kuwa yace duk abinda ya faru ko ya biyo baya Kar na sake na doso gidansa,bazai min Baki ba Amma ko me ya sameni nayi kuka da kaina.
Hajiyarmu tana Hawaye tace yanzu Fadila kin zabi Zama da Mahaukaci? Yanzu kika yarda aka daura muku aure? Idan ya warke yaki kulaki fa? Idan ya warke kika ji ba sunansa Aliyu ba fa? Baki sani ba ko Arne ne kawai ki Kai mahaifinki Kara har wajen yan Hisba akan Namiji Mahaukaci da ba a San asalinsa ba.

Ni kaina sai da na tabbatar da Hajiyarmu gaskiya ta fada nace ba komai Allah na Bayan me gaskiya Hajiya kuyi min addua Ni Dan na taimaka Masa na aureshi,Bayan Haka ma ai kun tsaneni kowa ya tsaneni akan Allah Bai bani Mijin aure ba,gashi na Samu ai sai kuyi murna.

Fadila Babu iyayen da zasu tsani dansu sanin darajar aure yasa muka matsu kiyi cewar Hajiyarmu,nace yanzu ba da kuka ga na auri Mahaukaci Amma da wacce tsana ce ba a nuna min,mene ba ayi mini ba sai yanzu Dana auri Mahaukaci koma mene kune kuka ja min kowa Yana zagina Taya bazan auri ko waye ba na Kara rushewa da kuka me tsuma zuciya.

Haka muka yini Ana ta gulmata a garinmu,Anty ganin ba mutumin kirki na aura ba Mahaukaci ne yasa ta zage da ita aka yi min jeren kayan daki a sabon gidan da aka bamu na wucin gadi,2 bedroom sai Palo da bayi,ko Ina shafe sumul da siminti ginin bulon siminti,gidan Dan dagwas dashi harda fentinsa Shar milk color,mutumin da yayi alkawari shi ya min kayan daki sosai Palo sunsha kujeru da labule sai Gado a bedroom biyu sai mirror da Sip dai dai rufin asiri,kayan kitchen Yan kadan akayi min da resho na,Kawu Usman ya Kai kerosine paster guda,aka zuba min kayan abinci sosai a matsayin garata,da Kuma na ddattijon da ya bamu sadaka, Bayan sati biyu kamar yanda Kawu Salisu yace an min lefe katuwar akwati daya kayan duk birni aka kaimin dinkin,Takalma kala uku da jaka kala biyu Sai kayan kwalliya,da slifas na tsakar gida,shima ango sun dauki size nasa an gwadashi sun Masa dinki kala goma da takalma kala biyu Sai slifas.

Ranar Saturday Abbu ya Tara kowa a dakinsa yace yau za a Kai Fadila dakin mijinta ta zauna da mahaukacinta,Kuma bazan taba ci da su ba idan abincinsu ya kare,Mahaukaci ya Nemo Mata,sannan duk abinda ya faru Kar na ganki a kofar Gidana sai da zuwa gaisar da dangi.
Alhmdllh mun fita hakkinki mun Miki komai Wanda ya cancanta iyaye suyiwa yarsu sai kuje ku karata aci soyayya lfy.

Kuka nakeyi sosai Ina Dan Allah Abbu kayi hakuri wlh Nima bada so na na bijire muku ba, Allah ne ya kaddara,Ya Salman yace karki damu Fadila kawai muyi Addua Allah ya bashi lfy,Allah yasa idan ya warke ya tuna dake kema ya Miki halacci.

Ina kuka haka naci wanka da kwalliya sosai tare da kawayena Yan uwana Kuma sai Anty da kakannina da Matan su Kawu aka tafi rakani dakin Mijina Ana guda Ana ayyiri da gayya suke yi suna dariya Ana gulmata,kicibus sai ga Dan Bature dukun dukun dashi yasha dirty, Bai San me akeyi ba tunaninsa ma yawo muka fito,duk da kaina a lillube yake sai da ya ganeni kawai ya shige cikin ayarin Yan Kai Amarya aka jera tare dashi gashi yamma ce lis maza duk sun fito Majalisa duk inda muka wuce Ana ta sheka uban dariya.

Suma masu Kai Amaryar Haka kamar ciki zai ciwo,ganin Haka sai ya firgita yayi sauri ya dawo kusa Dani tare da rike min hannu,kunya ta kamani Ana ta dariya da ihu,Haka aka Kai Amarya duk inda nasa kafata shima Haka zai sa, Ana kaini Yan Kai Amarya suka watse kowa yayi gida ana uban sheka dariya.

Ganin ba kowa na mike naje na rufe gidan,abin farin ciki harda rijiya a gidan,ba Bata lokaci na fara kokarin cire Masa Riga zan fara duty na gyarashi dama sabo da Haka na aureshi,kokawa muka farayi dashi ina dariya sai na cire shi Kuma ya hade Rai,da kyar na cire masa,ya cire wandonsa daga

Please Login or Register in order to submit comment