Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wankan tsarki zakayi Wanda mukeyi din Nan kullum ka tuna? Na tambayeshi,Kai kawai ya daga min ya mike tare da daura towel yaje yayi wanka da sabulu sannan yayi na tsarki ya fito.

Lokacin na gyara dakin neat na fesa turaren kamshi wani yard ruwan Milo ya dauko ya Sa abinsa kamar zaije wani waje sai nishadi yakeyi ya koma kasa ya kwanta Nima na kwanta gefensa ya Kara rungumeni sai bacci ya kwashe mu.

Ranar bakin ciki a wajena,ranar da bazan manta da ita ba a rayuwata bamu farka ba sai da Rana ta fito ya fara farkawa a matukar gigice ganin mace kusa dashi a kwance,dakin da yake ciki ya kalla yace what....da karfi Wanda yayi sanadiyar farkawata a bacci,nace lfy Dan Baturena? Dake Haka nake ce Masa,wani yare naji Yana yi Wanda ban San wanne yare bane sai Kuma naji ya koma turanci, Who are u? Who the Hell are u?, ya shako wuyana ya fesa min mari,ga dakin mun kulle ko Ina duhu, sai Kuma naji yayi Hausa uban waye ke, wacce kazama ce ke da Zaki kwanta a jikina? Mum? Mum, where am i? Ya Kara shako Ni ya jijjigani da karfi a Ina nake Nan dakikiya? wani tsoronsa ya kamani da Alama ya warke nace a Dingawa kake kauyen Gombe state Nigeria, Kuma Ni matarkace kafin na rufe Baki ya zuba min Mari matata kazamarki nonsense kin San ko Ni waye? Karuwan banza Ni Aliyu Hydar oh..God fuck u ya kalli kayan jikinsa ya kalli dakin baya ganewa sabo da duhu,,nace ciwon hauka kayi na aureka Dan na taimaka maka wlh Ina sonka,karka min Haka karka gujeni,ka tsaya na baka labari a Mahaukaci kazo garin Nan,da farko ba sonka nakeyi ba tausayinka Dan na taimakeka yasa na aure ka,Babu wahalar da ban Sha ba akanka har sonka ya kamani hannunsa na ruko....

Maruka ya Kara zuba min har uku ya Sa kafa yayi ball Dani na nayi taka taka na bigi jikin bed ji kake gwaf,kaina ya fashe ,jini ya zubo ta hancina gashi mun rufe ko Ina duhu kamar dare bana ganinsa baya ganin fuskata ko kadan ya bude kofa kamar zai jijjigeta ya fice da sauri Yana kiran Dad da Mum tare da wasu mutanensa Kuma sai wani yare yakeyi Wanda ban San na wanne kasa bane.

Koda ya fita ba Ba mutane a garin kasancewar yanzu gari ya waye wani me machine ya tambaya ya kaishi cikin garin Gombe city,ya kaishi kuwa Yana sauka ya tare wani a hanya tare da tambayarsa Dan Allah ya ara Masa waya ya bashi ya Kira Mum dinsa Yana wani irin yare Wanda kamar na kasar waje ne, Nan take 30mnt sai ga Motocin sojoji sun zo Dalla Dalla guda biyu da gudu suka bude Masa mota ya Shiga tare da kamewa a Bayan mota Nan ya mikawa me machine dubu goma cash, me machine ya dinga ihu da tsalle abinda naira hamsin suke Kai mutane yau gashi da 10k, wannan motoci Basu tsaya ko Ina wani katafaren Hotel Yana ta masifa da turanci da Hausa ko yarensa,a hotel ya dinga wanka Yana darje jikinsa da Bakinsa yafi awa a toilet Yana kakale kakalensa dinsa ga masifa Yana ta yi da yarensa da Kuma turanci watarana Kuma yayi Hausa,Kaya na Alfarma kana Nan Kaya ya saka sun hadu kamar yanzu ya sauka daga London abin kallo ne ga waya har an siyo Masa iPhone tafkekiyar da sai wane da wane, takalminsa wow sai Wanda ya gani idan ba saninsa kayi ba baza ka gane Dan Bature ba sabo da ya gaji da haduwa, sai Airport ya shige jirgi sannan ya Kira Dad dinsa yace Dad London Zan wuce a duba lfy ta na huta sai na dawo Nigeria pls Dad,wata aljana ce ta sace ni can wani daji I'm 100% sured Aljanna ce Dad,Bayan sun Gama waya jirgi ya Lula sararin samaniya abinka da masu hannu da shuni kudi Kare magana idan da kudi yanzu zakayi komai a wuce wajen.

Fuskata ta kumbura sumtum,ga Baki ya fashe,ga hanci jini da kyar na lallaba na mike nayi wanka na Dan gyara kaina,Ina rusa kuka Hawaye ya gagara tsayawa,takaicina ba dukan ba kawai sonsa da ya rigada ya dagargaza min zuciya,bazan iya rayuwa Babu Dan Bature ba,gashi abin haushin sanda yake da hankalin Bai ga kalata ba Bai San fuskata ba bare ya ganeni watarana, sallah kawai nayi na kaiwa Allah kukana tare da karatun Qurani, Yini nayi Ina kuka a daki nayi tunanin komawa gida na tuna furuncin Abbu Kar na soma zuwa inda yake da matsala akan aurena.
Me machine kuwa tunda ya dawo ya baza labarin a kauye Yana fada Dan Bature ya warke ya bar garin Nan Ashe Hamshakin me kudine zance har yaje gidanmu,Ya Salman yazo ya buga min kofa.

Idona a kumbure jajir nazo na bude kofa da sauri tunanina Mijina na ne da sauri na bude cike da farin ciki baya laifi a wajena,Ni Akan Ya warke ya rabu Dani gwara ya zauna da cutar haukarsa mu dawwama tare ,Ina ganin Ya Salman ne na rushe da kuka tare da fadawa jikinsa, tausayina ya rufe shi tabbas abinda yaji a gari gaskiya ne, Kuma abinda ake gudu shi ya faru,cikin gidan ya Jani tare da zaunar Dani gefensa, ya rasa ma ta Ina zai fara,ina kuka na bashi labarin abinda ya faru kaf ya tausaya min,Ya Salman yace hope dai kwanciyar aure Bata hadaku ba, Ina Hawaye nace sau daya ne Yaya Kuma jiya ne a Daren da yayi bacci ya warke ya dawo hankalinsa.

Yaya Wlh Ina sonsa na Shiga uku ya zanyi da rayuwata wlh Ina sonsa Don Allah Yaya nasan kana Sona ka Nemo min shi idan ban ganshi ba mutuwa zanyi, kafafun Ya Salman na rike na dira gwiwoyina a kasa Ina gunjin kuka Ina rokonsa,Nasiha ya Shiga yi min Amma Sam bana jinta burina kawai Naga Danbature na ya dawo gareni,kafin kace me zance ya baza gari mutane suka dinga turuwar zuwa gidan da nake Ana min jaje wasu suna Allah ya Kara dama ai an fada Mata taki ji, wasu Kuma sun tausaya min ganin halin da nake ciki kamar mahaukaciya na koma.Anty Amarya da tazo shewa tayi tare da shekewa da dariya tace Rana dubu ta barawo Rana daya Tak tame Kaya,yarinyar har Kara kika Kai ubanki mahaifinki wajen Yan Hisba Akan ya zaba Miki miji ke so ya rufe Miki Ido, yau wa gari ya waya? Shuru nayi ta Gama ta tafi tana dariya.

Hajiyarmu itama kuka take na tausayin yarta ga Abbu ya tabbatar Kar na doso gidansa shima yaji labari,Anty Amarya sai Murna take tana Kara yayatawa a gari, Haka Matan su Kawu Salisu da yaransu Mata Banda Mahmood sai gulmata sukeyi Ana Allah ya Kara.

Talle me lemo labarin na zuwa Masa ya raba lemonsa kaf kyauta sabo da murna Yana Allah Kara yanzu sai kuma Nan gaba a hakura a dawo a aureni Dole uwar naki.
Bayan kwana biyu Ni kadai nake kwana a gidan Ina Addua da kuka Ya Salman,Musa da Mahmood kullum a gidana suke yini anan muke cin abinci tare suna debe min kewa suna min Nasiha da tayani Addua,duk na rame nayi duhu kamar ba Ni ba.

Bani da aiki sai tunanin Mijina Wanda kullum kayan sawarsa da ya Bari nake Shimfidawa Ina kwanciya a Kai,Haka kuma na dinga gasa kaina har na warke sumul, Ya Salman da Whot card suke zuwa mu yini muna buga game suna ebe min kewa.

Yauma muna yin game din ban San sanda na koma tunanin Baturena ba yanda mukayi rayuwa tare nake matukar kaunarsa kuka na fara Wanda ban San na fara ba sai sheshekar kukana suka ji Wanda sun rigada sun Saba da hakan, Ya Mahmood yace Sister mene haka Kuma again? Katin Yana Hannuna na jikesu da Hawaye na daga kaina sama Ina kuka nace Ina sonsa ya zanyi Ina kaunarsa na Kara rushewa da kuka duk suka tsaya suna saurarena cike da tausayi sukayi jumgum jumgum.

Ya Mahmood ne ya katse shurun yace ya kamata kawai muje mu roki Abbu ta koma gaban Hajiyarmu sabo da zatafi samun nutsuwa,sannan tunda result dinta ya fito Kuma sunyi kyau sai mu kaita ko college ne tayi karatu ko ta rage tension.

A hankali Ina share hawayena nace bazan iya karatu ba a halin da nake ciki bazan iya komai ba face sallah da Addua Allah ya hadani da Mijina karku Bata kudinku.
To Amma ai Zaki koma gida kici gaba da Zama ko? Ae idan Abbu ya yarda ba.

Bayan kwana biyu Suka roki Abbu da kyar ya hakura na dawo gida shima saida manyan gari da su Kawu suka Sa Baki sannan ya yarda na tattaro kayana na kulle gidan mukaje har gidan me gari na bashi key mukayi Masa godiyar aron gida da ya bamu kyauta.

Bayan na dawo Gaban iyayena Babu abinda suka sassauta a gareni yanda suke min da Haka ma yanzu,ga tunanin Mijina,na rame na fige nayi duhu kamar ba Ni ba, Bayan na kwashe wata uku a gida jahilcin mutan kauye suka fara maganganu ya kamata na manta da auren dake kaina nayi aure Nan gaba dama ba a sani ba ko ba sunansa Aliyu ba kawai aka daura akayi Masa waliyai.

Bana fita ko Ina kullum Ina gida Ina kiyaye igiyoyin aurena na tabbatar sunansa Aliyu kenan tunda naji ya fada da kansa Bayan ya dawo hayyacinsa,kullum burina na zauna ko na kwanta nayi ta tunano rayuwata tare da mijina watarana nayi dariya watarana kuka, nayi tunanin saduwata dashi daya Zan samu cikinsa da nayi murna Amma Ya Salman ya kaini har asibiti Babu ciki a tare dani banji dadi ba naso zanga Dana jinin abin kaunata Danbature.

Me machine da ya Kai Dan Bature Gombe city na Nemo na tambayeshi labarin abinda ya gani Aiko ya bani labari karshe yace naji da turaci ya ambaci a kaishi airport Kuma da Alama ba Dan kasar Nan bane Don yaren da yeke Babu shi a kasar Nan kalar fatarsa ma ta nuna, Hawaye ya ziraro min nasan ma har abada bazan sake ganinsa ba ya kamata na hakura Amma zuciyata ta kasa hakan kawai naci gaba da kaiwa rabbil kuwwati Wal jabarut kukana,na Kara kwashe a kalla 5mnths Amma na kasa hakura anyi fadan anyi nasihar an gaji an kyaleni Haka. Inda Allah ya taimakeni ya bar agogonsa na diamond me tsadar gaske da kyau,ga zoben azurfarsa me kyau,chain din sarka na Samu na zura ta cikin zoben ya Zama kamar sarka me zobe nasa a wuyana da ita nake kwana Ina tashi,Haka agogonsa duk da yayi min yawa Haka na daurashi a Hannuna ya zauna dadas yayi min Masifar kyau kowa sai ya kalli Hannuna.

Attine yar Uwar Hajiyarmu wacce ke Zama a kudu can bangaren Iyamurai itace tazo gida tare da yarta budurwa Safarau,sunzo gidanmu taga halin da nake ciki tace Hadiza me zai Hana na tafi da Fadila can kudu ta samu salama sannan zata samu aiki tana kula da kanta,yanzu Kinga Safarau a Company na arna take aiki tana goge goge da shara da kin bar Fadila sai na kaita aiki ko wani Company ko gida ko office din wasu tana Dan aiki suna biya da tsada musamman idan mutum ya iya aikin ga Tsafta.

Baki na tabe nace me zanyi a kudu Ina da aurena,Hajiyarmu tace to da surutun da mutanen garin Nan sukeyi ai gwara ki koma can ko banza ma huta da munafunci, Hajiyarmu ta shawarci Abbu,shi Kuma yace a dawo lfy Ni da zagin da take jawo min ai gwara ta tafi can tazo Mana da yawo,Anty ma tace da mun huta wlh.
Ya Salman na kaiwa Kara Amma Nasiha ya min gwara na tafi Amma na rike mutuncina da igiyar da take kaina,ya dinga min Nasiha Kar na bijirewa Hajiyarmu again kaucewa Umarnin iyaye Yana kawo matsala,ba a son Raina ba ranar da Attine zata tafi tare da yarta Safarau na shirya da akwatita katuwa na bisu munyi sallama da iyaye Yan uwa da abokan azirki,Ya Salman ba,Musa,Mahmood har Tasha suka rakamu tare da bani dubu ashirin cash,ba tare da na San wannan state zamuje a Nigeria ba.
Gani nake kamar Watarana Dan Bature zaizo nemana kauye har sallahu na Bari idan ya dawo Zan siyi waya acan Zan na Kiran gida mu gaisa idan ya dawo a sanar min.

Ban San birni ba sai da yawo a Shiga a fita bare kudu,Haka muka je Tasha naji tace Lagos Baki na hangame nace Lagos kuma Hawaye ya zubo min shike Nan Dan Bature bazai ganni ba har abada Ina zai ganni Ina gari kamar Lagos,Attine kuwa haushi nake bata sai masifa take min muka Shiga mota katuwa doguwa, ita ta biya kudin da komai muna tsakiyar arna karfe 4 na yamma motar mu ta hau titi.

Tafiya muke ba ji ba gani Safarau sai dariya take min yanda nake ta sheka bacci,ita Kuma wayarta tecno take dannawa tana chart,tasa earpiece a kunnenta kujerarmu kusa muke a jere Attine Kuma tana gabanmu tana sheka bacci,Safarau tace Fadila ungo sa kunne daya na sa daya muyi kallon Nigerian film a wayata,kafada na make nace A'a ke nifa da nayi komai arayuwata Wanda ba addini ba gwara nayi tunanin Mijina yafiye min komai nishadi.

Attine ce ta zuba min rankwashi shashasha kina wahalar da kanki akan mutumin da ya rigada ya manta dake Bai sanki ba marar zuciya, Jin tace Danbature ya manta Dani wani kukan rashinsa ya taso min na fashe da kuka, Baki Safarau ta rike tace ke kuwa Fadila wanne balain kaddara ce ta afka Miki ta soyayya? Allah ya yaye Miki,kukana nakeyi har bacci ya sake kwasheni ban farka ba sai da mota ta tsaya za ayi sallah masu fitsari da siyen abinci ma suyi,sallah mukayi Attine ta siya Mana kaza da yogurt har gurasa,mota taci gaba da tafiya muna cin abincinmu har muka Gama.

Sai da gari ya waye 11am muka Isa Lagos lokacin Ana shara ruwan sama Amma Haka mutane ke harkokinsu abin ya bani mamaki sabanin mu Arewa idan Ana ruwa to ba me fitowa, Attine ba ruwanta ta tare Mana taxi Muka Shiga sai Unguwarsu ta talakawa Wanda Hausawa Yan ci rani da talakawan Hausawa da Kuma arna talakawa Yan bariki etc Nan muka nufa,wani gida me bene sama da kasa duk da cewa tsoho ne ya kwararrabe Amma dai Yan haya ne sama wasu yare ne Yoruba kasan Kuma na Attine ne ta kama haya.amma ciki yasha gyara.

Palo ne sai daki biyu da toilet sai kitchen ba laifi akwai rufin asiri na talaka, gidan muka gyara fes sannan Attine ta dafa Mana jallof din taliya da kifi muka koshi sannan muka kwanta baccin gajiya.

Sai yamma lis muka tashi wanka mukayi da sallah sannan muka daura abincin dare Ni da Safarau tuwon shinkafa miyar alaiyahu mukayi me dadin gaske ko Attine ta jinjina mana, Attine tana da kirki ba laifi ga son Dan uwa Bata so taga Dan uwanta cikin damuwa, Haka take koya min aiki da kayan Yan gayu sabo da Kar naje aiki gidan masu kudi na kasa komai,har girke girke na Yan gayu take koya min,waya tecno Yar dubu ashirin da biyar ta siya min Nan Safarau ta dage wurin koya min yanda ake Amfani da har browsing yanda ko girki Zan iya koyar Abubuwa ta YouTube etc, tace Bari na bude Miki Facebook da WhatsApp Kya dinga rage tunanin da kike na masifa,Baki na tabe nace tunda dai kin koya min Google da YouTube ya Isa bana fatan muamula da kowa idan ba Mijina Zan gani ba,Dariya Safarau tayi tace to Allah ya shiryeki nace Ameen.

Satina uku a Lagos nayi kyau da kiba hasken fatata ya dawo har nafi sanda nake kauye haduwa lokacin da Dan Bature Yana Nan,Attine sai Jin dadi takeyi tana fadawa Hajiyarmu kasancewar kusan kullum Attine sai ta Sa min katin waya nayi waya da Yan gidanmu.
Ni kaina Ina Jin dadin zama.watana daya Safarau ta koma can Company inda take aiki a wani reception Ana biyanta.
Attine kuwa Yar kasuwa ce tana Saro irin su Maggi,Omo,katin waya etc tana siyarwa sannan itama tana aikin kula da wata dattijuwa Igbo wacce danta Hamshakin me kudi Ne,kullum Ni kadai ce a gida,yan kudu ba Zama Mata da maza neman kudi,Ni nake aikin gida sannan na dafa abinda nake so,Lallai cimar mu danan da kudu ba daya ba,su Dole sai anci dadi iya talaucin mutum sai yaci Mai kyau Lallai Dole sufi mu girma da komai.
Attine ce ta dawo nayi Mata sannu da zuwa,da Murmushi ta amsa min tace kina Nan ke daya ko sai tunani,a hankali nace ai na rage Auntynmu,da dai yafi sauki ki taimakawa kanki,me kika dafa Mana? Pounded yam with egusi soup,to Bari naci na huta sai mu fita yawon zaga gari kema kina ganin duniya,dake Attine kyakyawace itama Yar gayu ta waye sosai,dama na fada duk danginmu kyawawane masu hasken fata.

Hmm da kin bar fitar Nan Antynmu komai baya gaba na Ni dama Danbature na Zan gani,fada Attine ta fara min ke Baki da hankali Naga Alama so kike ki kashe kanki akan wani banza Wanda Bai sanki bama yanzu, Idan Attine tace Danbature ya manta Ni Bai sanni ba shine ke matukar daga min hankali kamar Ana zuba min garwashi a zuciyata,kukan tausayin kaina na shigayi sosai har sai da ta tausaya min ta lallasheni,tace Fadila kiyi hakuri kamar yanda kike da addini ga sallah da yawan adduoi ina so ki fawwalawa Allah lamarin kici gaba da Addua sai kiga Allah ya kawo Miki canjinsa ko ya hada ki dashi again ba abinda yafi karfin Allah.
Sai kikaga ya dawo ya daukeki,inye ya kaga Fadila ga Dan baturenta ku santalo yaranku kyawawa,ban sanda na fashe da dariya ba tare da share hawayena na Kara gyara zama, nace Auntynmu sai fa kiga ya dawo ko watarana? Attine a ranta tana mamakina tace kwarai ma kuwa,nace Alhmdllh Antynmu ya kamata ki Nemo min wurin aiki na fara zuwa sabo da nayi sauri na Tara kudin da Zan gyara kaina sannan da yanda Zan kashewa kaina kudi kafin Danbature na ya dawo Kar ya dawo ya iske banci gaba ba banyi kyau ba,Dariya Attine tayi tana ganin shirmena zalla.

A fili tace inshallah kin kusa tafiya aiki kema sai dai kizo wajena da yawo Kinga Safarau a Company nasu har Wurin kwanan aiki ne dasu 24hrs ba hutu Amma akwai samun kudi kema Nemo Miki inda Zaki samu kudi nakeyi inda baza ki Sha wahala ba.
Murmushi nayi nace Allah yasa.

Bayan sati biyu zazzabi me zafi ya kamani Attine ta kaini asibiti hankali tashe,Bayan gwaje gwajensu ya nuna Hawan jini ne kadan,jini na ya hau kadan,Doctor yace ya kamata idan akwai abinda ke damuna na rage na daina damuwa sannan ya rubuta Mana Magunguna Attine ta siyo min,Bayan na warke Ras,yanda na Kara dagewa da Addua naji sauki a Raina yanzu gani da damuwa Amma Bata damuna sosai sabo da Qurani Dana rike ya Zama abokina dare da Rana,Kar nazo Danbature ya dawo ya iske bani da lfy ai abin baiyi ba Sam shi yasa na dage na rage sabo da Danbature ya sameni lfy lfy muci soyayyarmu.
Tunanina Kullum yanda muke romancing juna,muci abinci tare, wanki tare,unguwa tare,ko Ina muna tare.

Yau kwana biyar kenan kullum sai Attine ta fita Dani yawon zaga gari gaskiya Lagos ta hadu domin wani yankin ko a Abuja baza a Sami wuri me kyau Haka ba,sai ko turai shima ba ko Ina ba.













AsmaBaffa






AsmaBaffa
[9/4, 10:25 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕









11-15










Official








By
AsmaBaffa








Hajara Atiku sallama (laver),
Zahrau Abubakar Dambuwa
Sadiya Abubakar Dambuwa.
Ina kaunarku wajen Sharhi ga page dinku fans na kwarai.











Na kwashe wata daya da kwanaki a Lagos muna yawan Fita da Anty Attine tana aikena yanzu na fara sanin gari sosai,kasuwanni super market etc,Yau da Wuri Attine ta dawo tace maza shirya kije ki siyo kayan kwalliya ke ko kwalliya kin daina sai dai kiyi wanka kawai kisa Kaya ba kwalliya kamar ba mace ba.
Murmushi nayi kawai nace wa Zan yiwa kwalliya? Wanda Zan Masa kwalliyar yayi min Nisa sai sharrrrr....Hawaye suka tsiyayo min masu dumi,Attine jikinta yayi sanyi tace Dole ki tafi aikin Nan ko aikin ya Isa ya hanaki tunani, saman kujera na zauna dama hijab ne jikina kaina na rufe gaba daya Cikin hijab Ina ta kirsar kuka me sa Wanda ya saurara tausayi,Attine tayi Shuruuuuuu tana ji har na Gama Bata ce komai ba tace zo muje yawo kiga gari,haka muka fita Ina ajiyar zuciya,wani eatery muka je ta siya mana snacks da Ice cream sai wata burmukekiyar cinyoyin kaji.

Sosai na Samu nishadi sai na tafi tunanin inama da Danbature nazo wannan wajen ba da Attine ba, washe gari da yamma likis Attine tace na shirya yau Zan tafi gidan aiki,Attine tace sai dai kiyi hakuri ba a samu Company ba sai Gidan wata Igbo Ijeoma girki kawai Zaki dinga tayata a kitchen,mijinta baya cin abincin Yan aiki so Bata son wahala da yawa girma ya kamata kuma,wata zata dinga biyanki dubu ashirin ya kamata ki bude accnt sai ki dinga Tara kudin, farin ciki ya kamani har dubu ashirin nace Antyna ai Ina da accnt a gtbank ya Salman yaje Dani na bude ina da komai a kaina,good cewar Attine Dan Allah ki tsare mutuncinki da addininki,Kinga gidan arna Zaki je ki kula ki Zama wise, nace inshallah wacce unguwa ce Anty? Tace Island unguwar masu kudin gaske ce sai wane da wane, idan kika Shiga Zaki ce a kasar waje kike aljannar duniya ba hayaniya Shuru,gidaje na alfarma.
Matar tayi senator sau uku sannan tayi Yar majalisar tarayya sau biyu,ta rike ambasador a kasar India yanzu Kuma Minister ce har sau uku Ana Bata mukamin minister ta Tara kudi,mijinta Steven Defence permanent secretary ne a Nan Lagos ki kula gidane gari guda dauke da securities ko Ina ga Yan aiki iri iri, yaransu biyu kacal Emanuella da Amaka dukkansu matane Yan Shekara 36 da 33yrs a turai suke rayuwarsu Amma tace yanzu sunzo Nigeria kafin su koma.

Hmm to Anty nifa bana wani Jin turanci da yawa,Haka Zaki ta jagalgalawa har ki kware Nima ai a Haka na koya,Murmushi nayi sannan na hada komai nawa na bukata muka Shiga taxi sai unguwar.

Unguwar ma ba a barmu mun Shiga ba saida Attine ta Kira Babban yaron Ijeoma sannan aka barmu muka Shiga da taxi har kofar gidan,gaba daya na rude sai kalle kalle nakeyi sabo da tsaruwar unguwar, gidan Ijeoma yafi karfin a kwatanta shi karshen haduwa ne gari guda part part Babu Bata lokaci Yaron Ijeoma Dennis ya Mana iso ko Ina matakan tsaro ne da Maaikata suna zirga zirga, ganin Palon da muka Shiga sai na susuce ban

Please Login or Register in order to submit comment