Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba kowa ke damuwa da hannun da yaransu zasu fada ba,to gashi Allah ya nuna Mana shike tsarawa Dan Adam rayuwa,sannan ko waye ka gani ka guji wulakanta shi shima ba Haka ya so ba Allah ne ya tsara Masa Haka,bamu taba zaton Aurenki da Aliyu zai Zama Alkhairi ba sai gashi Ashe Allah shi yasan meke boye,to mun godewa Allah,Allah Kuma yasa mu gane ya Dora mu Akan hanya,ki dage da biyayya kibi mijinki kinyi dace ba sai ma na fada Miki rayuwa ba Tunda ke kin San yanda kike kula da abinki sai dai kiwa wani fada,Allah ya albarkaci rayuwarku.

Ameen na amsa sannan nace Abbu ai baku da laifi Ni kaina da matsalar ta faru nayi Nadama,ashe Alkhairi ke Bina dan ma baka ga yanda yake so na ba na furta Ina boye fuska,Murmushi Abbu yayi sannan yace nafi ki sanin haka,yanzu Baki ga yanda Yan uwanki duk suka Samu Madafa ba ta sanadin mijinki,suna ta kantama katon gida a birnin Gombe zasuyi aure ga motocinsu,Gidana sun maida shi sabo sai abinda muke so muke ci,kwana Nan ma Salman ya kusa Gama Mana katon gida a Cikin garin Gombe zamu tattara mu koma,wannan na kauye Kuma za a rufeshi sai in munzo ganin dangi muzo kauye,farin ciki ya kamani nace Alhmdllh Ai Haka ake son taimako ayi maka abinda zaka rike kanka da Yan uwa ba Wai a ebi kudi a baka ba,gaskiya naji dadi, Daddy ne ya katse Mana hirar daya fito yace jeki ki Kira Aliyu Ina son ganinsa.

Mikewa nayi sai Dana fito nasan na Masa laifi sai na hango Saddiqa anci kwalliya tayi kyau nace Dan je ki Ki fadawa Ice Daddy na nemansa,Saddiqa ta kalleni tare da furta Ni fa Dr who ne yake nemana,oh baza kije ba kenan to ko soyayya kuke ne? A'a ko daya munfi dai shiri da shi kawai Ni ai yafi karfi na,Yana dai birgeni sabo da faraarsa,muna Haka sai ga Dr who ya fito Yana sauri da key a hannunsa ya dau wanka da Alama fita zaiyi,Yana karasowa inda muke ya zubawa Saddiqa rankwashi tayi Kara ahhh tana dafe wajen.

Yace ba Kya ji Ina Aiken nawa kinzo Nan kina surutu,Baki ta turo tace to ai Zan kawo maka aiken, Aunty Fadila ce ta aikeni, Miko min to sako na Kuma bazan kaiki ba na fasa,
Magiya ta fara masa tana shagwaba,Yar kallo na Zama Baki bude Ina kallonsu kawai, sai wani irin kallo yake Mata Wanda da Alama na so ne, Jakarta ta bude ta Miko Masa wani Abu a leda Wanda ban San mene ba,Follow me ya furta Yana cewa bye Auntynmu yanzu Zan dawo nace ok a dawo lfy,ita kuwa Saddiqa da gudu tabi bayansa ta shige gaban motarsa suna ta faman dariya su suka San irin hirar da sukeyi.

Sadiya na Samu zata wuce nace Dan Allah zo na aikeki,ta girmeni nesa ba kusa ba Amma gadarata ai matar Ice yayanta ne don Haka Kanwata ce itama tunda kanwar Mijina ce,Kai tsaye nace jeki part din Mijina kice yaje Daddy Yana kiransa,ta kulu sosai ranta ya baci Wanda na tabbatar da ace da ne da sai ta min dukan tsiya Amma sai tace ki kalleni Fadila dan kina auren yayana kice Zaki aikeni kina kanwar Kanwata,Amma dai kinsan ke Kanwata ce tunda Ni matar yayanki ce Dole ki bani girmana,kije kawai wlh ko na fada Masa abinda kika ce kuma kin San Halinsa.

Hmm ta kalleni tace to ba a haifeki ba yarinya banza a banza ke kin Isa idan shi kina juyashi mu wlh munfi karfinki taja tsaki tayi gaba abinta tana Jin kida a ranta,Raina ya baci Bayan Ni na tsokani fadan banyi niyyar zuwa wajen Danbature ba Amma yanzu na dauki hanyar zuwa part dinsa, Yana samansa su Ya Salman suna Palo na gaidasu nace Ina Danbaturena? Sama Musa ya nuna min nace Ina zuwa na haura samansa Ina fushi kamar Zan fashe na Shiga tare da Sallama,Yana jikin mirror Yana fesa turare yana kallona ta mudubi yaji sanyi a ransa na ganina sabo da jiya yayi missing dina Amma sai ya share,
Ina kwana na gaidashi ina fushi ya amsa ganin Ina fushi yayi tunanin wani Abu ya faru da kulawa yace lfy?

Ina kumbura nace Wai Sadiya ce kanwarka na aiketa tace baza ta zo ba,yanzu kamar Ni ban Isa da kannanka ba ko ba komai ai sai su bani girmana na matar yayansu Amma sai ta ci min mutunci.
Ido ya tsura min Yana kallona ya ganni yarinyata yana dariyar tsokanata yace Lallai ai da kin sani kin mareta ace kamar matata kannen miji na Mata rashin kunya,zanyi maganinta,ganin Yana zuba Murmushi nace to muje kayi Mata a gabana Naga kana min Dariya ko nufinka ban Isa dasu ba,da sauri ya tsaida dariyarsa yace Ni na Isa muje,nace Kuma Daddy Yana nemanka ma kaje yace, alright muje kawai,kaci abinci kuwa? Kai ya daga min munci da ya Salman.
Tare muka fito dashi mun jera,yace Wa Su Musa Bari na dawo zanje wurin Daddy,ok suka ce Muka fita, muna tafiya a nutse yace Jiya da wa kika yi waya na kiraki busy sai lokacin na tuna ban boye Masa ba nace wani ne ya dameni Bari mu zauna Zan fada maka abinda yake cewa,Nan danan kishi ya kamashi ya daure muka tafi har inda Sadiya take,tana ganinmu ta firgita tsoro ya kamata tasan Halinsa idan ya fara dukan mutum baya tsayawa.
Jikinta rawa kawai yakeyi,kallonta yayi fuska ba Rahma tare da Furta Baki da kunya ko ke har Fadila zata aikeki kice baza kije ba,kina Kanwata? ai Dole ace da Mijin iya Baba cewata.
Wlh daga yau idan ta aikeku kuka ce baza kije ba sai nayi maganinki,To Yaya Ice kamar wannan zata aikeni Dan kawai tana matarka sai ta aiki kamata,Akan me Ni wlh gaskiya Zan fada idan zata aikeni sau dubu bazan je ba karma kaga laifin.....Tasssss......kake ji ya kwasheta da mari,Manyan kaya yasa ba belt na Mika Masa charger dake Hannuna ya karba kuwa,zata gudu na rike rigarta ya kamata Kam a hannunsa ya Shiga shauda Mata bulala da mugun karfi sosai tana ihu tare da bada hakuri tana Yaya Wlh zanje Dan Allah kayi hakuri.
Saida yasan ta daku yace oya Bata hakuri,da sauri tace Kiyi hakuri Fadila,nace na hakura Amma karki sake wlh duk ranar da kika sake ko fada min bakar magana sai na fada Masa,Kyaleta Honey ta tafi, bace min anan ya furta da tsawa tuni Sadiya tayi gaba tana Hawaye.

Karo taci da Daddy ya fito yace ke Kuma lfy,Ya Aliyu ne ya dukeni akan Matarsa ta aikeni nace bazan je ba na girmeta shine ta fada Masa,Tunaninta Daddy zai bi bayanta sai taji yace Good ai ya kyauta Marasa tarbiya yanzu Matar Ice ai yayarki ce tunda tana auren yayanki ai Dole ki girmama ta.

Ni kuwa murna nayi an tare min fada,muna tare dashi zaune a kujerun garden Ina tayashi lissafina wasu kudade masu yawa na Company nasa, sai ga Meena wacce suke uwa daya uba daya taci wanka cikin matsatsun kana Nan Kaya.
Da hannu na yafitota tazo kuwa tace gani Fadila, Ice yace Dan ubanki saarki ce ba ko Aunty ma sai Fadila,sorry tace,nace ki canja sutura Meena Kinga maza baligai suna zirga zirga a gidan Nan zasu ce babu tarbiya a gidan Nan, to kawai tace tana hararata ban San tanayi bama Ashe Danbature ya gani sai ji nayi kawai ya kwasheta da Mari,ga lokacin Daddy da Abbu zasu wuce ta wurin.

Daddy Yana karasowa yace lfy wlh Aliyu zanyi maganinka sai dukar min Yara kakeyi,kazo ku tafi gidanku a Haka zaka koya musu tarbiya,Daddy kana gani Fadila suke wa rashin kunya akan ta fada musu gaskiya, tace tasa matsatsun Kaya maza na sintiri ko Ina taje ta cire shine zata harareta.

Uhm kinyi gaskiya Fadila irin wannan shike jawo mazan gida,Yan aiki,suke yiwa Yara fyade,sai kaga Wanda ka aminta dashi ya lalata maka yarinya,Abbu yace hakane Amma ke Fadila nasan halinki tun a gida akwai iya kinibibi da samun waje in kika ga kin samu karbuwa to in Banda Shagwaba da Jaye Jaye ba abinda kika iya ki kiyaye karki jawo dangin Miji su tsaneki kina hada su fada da Dan uwansu da iyaye ganin kina da fada wajen me gida da dangi,Daddy ya katseshi da ba Maganar fada bace wlh gaskiya Fadila ta fada.

Shuru nayi har suka tafi na mike Nima nace Bari naje wurin Hajiyarmu ta shirya mu tafi gidan namu,ki Hado kayanki gida zamu koma Baki daya,fuska na bata yanzu baza mu kwana a gida ba zuwa gobe idan su Abbu suka tafi sai mu koma Baki daya.

Shike Nan tunda kina so iya gobe Dole mu koma gida yaushe rabona dake sai ja min Rai kikeyi sabo da kin San Ina sonki da yawa,Murmushi nayi tare da Furta nimafa Ina sonka ka sani ma cikin Sigar rada rada Wanda hakan da nayi har cikin jininsa Wanda yasa ya fisgoni na Fado jikinsa ya rungumeni a jikinsa Yana cewa I love you tare da kissing dina Ni kaina Me too na iya furtawa Ina kissing nasa kamar zamu cinye bakunan junanmu har wani sauti kisses din suke fitarwa Wanda na kusa ma sai yasan Ana tsotse tsotse kamar mayunwacin jariri na tsotsar Nonon uwarsa , janye jikina nayi Zan bar wajen ya rike min hannu tare da cewa pls Help me muje Part dina nasan me yake nufi, nace kasan fa Hajiyarmu tana jirana fa,zuciyarsa ta tunzura matuka da Jan ran da nake Masa,ya kalleni sosai yace daga yau bazan Kara tambayarki ba Inshallah Kuma Zaki zo ne kema,Dariya ya bani ma nace to ai Ni Zan nemeka in ma baka zo ba Ni zanzo ai,Zaki gani Ni kadai Zan koma kwana tunanina Wasa yake yace jeki na mike na tafi ban San gwada Ni yayi ba.
Tuni nayiwa yan aikina waya sun shirya abinci da gyaran ko Ina na gidan namu nace Anjima Zan zo da Yan uwana ai kuwa gida yasha gyara.

1:30pm munyi sallah mukayi wanka mota biyar akayi kusan gaba daya Yan gidan su Ice har kaka Hajjo,Ya Salman,Musa da Hajiyarmu motarsu daban,Abbu da Daddy suna tasu,Ni da Angon nawa motarmu daya yanda mukayi wankan kamar Ango ka rantse party zamuje na biki.
Tun daga unguwar kowa ya Zama Dan kallo kamar Yan kauye,Daddy Mashaallah kawai yake cewa tsarin gidan kawai ya gigita kowa duk zaga Duniyarsu sai da gidan ya firgitasu sabo da kyau da gani an narka dukiya ba kadan ba.
Basu Gama Shan mamaki ba sai da muka Shiga ciki tuni Mata an fara daukan selfie kyas..kyas,ko Ina kamshi da sanyi,Basu ko zauna ba sai da suka zagaye gidan ko Ina Ice Yana nuna musu, Hajiyarmu harda kukan murna yarta ce a wannan gida Haka,Abbu kuwa tare dasu Ya Salman kasa magana sukayi,Bayan an nutsu Daddy da Abbu suka dinga zuba Albarka da Addua sannan nasa Yan aiki aka kawo abinci iri iri Wanda shi kanshi Ice yayi mamakina dana tsara hakan Kuma yaji Dadi na Kara birgeshi,a Nan akayi lunch kowa yaci ya koshi Ana murna Hira da farin ciki.
Sai wuraren Magrib Daddy yace su taso a koma gida gaba daya,Abbu yace to Fadila mu munyi Sallama dake ki zauna dakin mijinki gobe mijinki ya siya Mana ticket na jirgi 9am zamu tafi sai kinzo ganin gida Kuma.

Fuska na hade nace haba dai ai tare zamu tafi mu kwana in kun tafi sai na dawo gobe,muna hada Ido da Danbature ya gasa min uwar Harara, Hajiyarmu ta bude Baki tace bakya Jin magana ko? ko Haka kika ga Mata nayi? Shuru nayi shi kuwa Ice Dadi yaji harda min gwalo, Daddy ka gani ko? Me ya faru ya tambaya nace gwalo yake min Yana tsokanata,Dariya akayi Baki daya yace kyaleshi idan kika je ganin gida sai kinyi 2wks, gwalo Nima na Masa na rama nace Allah kaimu kowa ya ce Ameen.
Har mota na rakasu mukayi sallama,Ya Salman yace baza kiyi kuka ba zamu tafi,Dariya nayi Ina jikin motarsu nace Ina tare da Danbaturena na nunashi da yatsa yana wurin Hajiyarmu da Abbu suna ta magana ban San me suke cewa ba,Hannu Musa ya Miko min muka tafa yace na tuna sanda yarinyar Nan take barka Mana kuka kullum sai mune muke zuwa mu zauna tare da ita,ga Abbu yace ba gidansa ba,sai tace shike Nan mutuwa zanyi ya Salman ya gwada muryata muka shekewa da dariya na zura Hannuna ta glass na mintsini Musa a wuya,yayi Kara kadan,Ice Yana kallonmu Yana magana da Abbu,Bayan sun Gama suka tafi driver yaja mota Ina daga musu hannu.

Danbaturena ya karaso inda nake yace to Allah ya kawo mu yau gaki gani daga Ni sai ke,Zaki San wa kika yiwa,dama na taraki da yawa,Bari naje gidan su Ayman dama yayi min sabuwar budurwa zamuje na ganta idan tayi min na karo Miki ita na huce takaicin mace daya sai Hawan jini kike sani.
Tsoro naji tunanina da gaske yakeyi sabo da yace dama zaiyi maganina, cumb ya zaro karami a aljihunsa ya sake taje gashinsa a gabana sannan ya Shiga Mota tare da janta cike da salon kwarewa ya tafi abinsa ya barni Nan tsaye.

Kishi ya turnukeni katsam sai ga wayar mutumin dake kirana ya Kira,da sauri na daga cike da balai nace dalla Malam ka daina kirana nafi karfinka me zanyi da Kai fasiki aikin banza kawai Kai dakikin Ina ne jahili,dabba,asararre anyi asarar haihuwa wlh matsiyacin banza duk yanda akayi a baya a goye aka zo dakai gidan ubanka Dan shege ne Kai ba ta halak aka sameka ba,marar zuciya Wanda Kare ya dauke.
Murmushi me Sauti ya saki yace kin jawowa kanki wlh sai na nuna Miki iyakarki, zuciyata Kuma ba Kare bane kadai ya dauke harda Zaki da damisa ne suka dauketa.
Tsaki naja tare da kashe wayata Baki daya na koma ciki abina tuni masu aiki sun gyara kitchen da ko Ina da Baki suka Bata.
Saman bed kawai na kwanta Ina tunanin Danbaturena ko da gaske wajen wata ya tafi,a fili nace kan uba ai wlh sai dai ya sakeni kawai Ina bazai yuwu ba.









AsmaBaffa
[9/4, 10:26 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕









96-100







Official







By
AsmaBaffa








FINAL









WANNAN PAGE NA DUKKAN MASOYA ASMABAFFA NE MAKARANTA NOVELS DINA.

WANDA BAN SAMU DAMAR BAKU PAGE BA KUYI HAKURI KUYI MIN AFWA INSHALLAH NAN GABA ZAN BAKU.








Muna kwance cikin dare zazzabi me zafi ya rufeni da kyar nake motsi,jikina zafi zau,sai Nishi nakeyi da rawar sanyi,karkawar da nakeyi itace tayi sanadin tashin Danbature daga baccinsa me Dadi, jikina ya taba yaji zafi zau kamar Zan Kama da wuta yace Innalillahi wannan zazzabi gwara kawai ya dawo jikina na huta Akan ya taba min lafiyar Beauty na,kullum sai yazo ya Hana min ke sakewa,duk da Ina cikin cuta naji dadi da sanyin kalamansa Wanda har ban San Ma nayi Dan dariya ba kadan,kayan jikina ya cire min kaf ya Shiga toilet ya ebo ruwa shi ba me sanyi ba baza Kuma ace me zafi ba,da towel ya Shiga goge min jiki na kamar yanda ya Saba min kullum,Magani nace ko zaka bani Paracetamol?

A'a Mahaukaci ne Ni na sani ko ciki kika samu na Baki magani bada sanin doctor ba ya zube,to Bari kiji gobe dole muje asibiti ko kina so ko ba Kya so,Shagwaba na fara Masa Ni Allura zasu yi min,Bari kiji ko bana nan karki sake Kisha magani sai dole Munje asibiti, zafin jikin nawa ya ragu sosai ya maida komai toilet ya dawo ya kwantar Dani saman jikinsa ya lullubemu Baki daya Yana shafa gashina tare da bayana Yana min sannu,duk ya damu sosai sai lallabani yakeyi,nace karka ji zafi kaima ka Shiga blanket Kuma ba a sanyi Danma da ac.
Ai Ina Jin halin da kikeji Nima Zazzabin ya kamani shi yasa na shige tare da ke,kin San kuwa irin son da nake miki,wlh da gaske akan ciwo ya kamaki gwara ya shigeni,kamar Zan dauke Miki ya dawo kaina Haka nake ji Allah ya Baki lfy kinji Yar balarabiyata,Ameen na Furta zuciyata fari Kal sai naji Ciwon ma duk ya gudu sabo da dadin kalamansa.

Washe gari fes muka tashi,kafin mu fito har Saddiqa tare da Mum sun shirya Breakfast lafiyayye,Muna ci Ina tsokanar Saddiqa yau zata koma gidan mijinta ita kanta murna takeyi ta Matsu ta koma ta rigada ta Saba da jikin mijinta,sai zumudi takeyi, Muna breakfast kuwa sai ga Dr yazo tafiya da Abarsa Babu Wanda yace komai ta fito da kayanta Wanda Meena ta ebo Mata a gidanta ta fito tayi Mana sallama muka rakasu Mota suka tafi Bayan Mum ta Kara Jan kunnensa.
Mu kuwa Shirin zuwa Hospital mukayi,Shadda muka sa Sea blue iri daya munyi anko,duk Wanda ya kallemu sai ya Kara,Asibitin Dr who katafare mukaje aka dauki fitsarina sukayi gwaji sai gashi an gano ina da ciki na wata biyu da Sati daya,Murna kamar zamuyi ihu musamman Ice,kafin ace me duk ya watsa labarin,shawarwari da Magunguna suka bani muka dawo gida,Mum murna kamar me,Haka Yan uwan Ice da dangina,Daddy kuwa tunda yaji labarin ya dinga murna Yana Mana Addua sannan yace Next month zai dawo zai je daurin auren su Ya Salman.
Kannan su Ice da yayye sai zuwa dubani sukeyi suna Murna.

Attine ma takanas tazo ta yini,sannan take sanar min an kusa bikin Safarau yarta,Ko da na sanarwa Ice cewa yayi ya dauke komai zaiyi kayan daki da komai,sannan ya bawa Attine jari me yawa,munji Dadi har ban San da me Zan saka Masa ba.yanzu dangin Mijina muna zaune lfy suna kawo min ziyara Nima Ina zuwa,yau saura kwana uku bikin Safarau zata auri manager na Company nasu,bikin Rana daya Dana Saad abokin Ice Wanda ya hadamu yayi Mijin karya.naci na fara yi Lallai sai ya barni naje biki nayi kwana biyu,shi Kuma yace muna gari daya bazai iya barina ba sai dai kullum ya kaini ya dakko Ni,fushi nakeyi dashi,da yamma Mum ta fita unguwa gidan kawarta ni kadai ce a gida Ina zaune nasha kyau,sabo da cikin jikina yasa na Kara wani fresh da kiba,Apple nake ci.

Sallamarsa naji tarbar Dana Saba Masa banyi ba yau yasan Akan me nake fushi,kusa Dani ya zaune tare da ajiye ledojin shopping a gaba na,yace ga dinkunanki na karbo Miki,sannan ga wasu kayan Nan,dama fa dinkunan biki ne Kuma kace bazan je ba me zanyi dasu,Ni nace karki je? Kullum Zan kaiki da safe da yamma na dakko ki,rau rau nayi kamar zanyi kuka nace yanzu kamar Attine bazan kwana ba? Sannan Safarau ko yaushe tana hanyar zuwa wajena tare mukayi shirye shiryen bikin Amma ace bazan je na kwana ba.
Mene ne abin kwana pls tunda Zan kaiki me yasa bakya Jin magana ne,da yaron ciki Zan Bari ki tafi unguwar kwana kullum da zazzabi kike kwana fa in kin tafi gidan su wa zai kula dake?
Indai wannan ne Zan kula da kaina ga Attine ma,Kai ya girgiza yace to a dawo lfy ya mike tare da haurawa sama.

Ni dai ko a jikina shiri na fara yi kawai Yana kallona ransa a matukar bace yaje yaci abincinsa na Gama shiri na tsaf na fito nace na shirya,jikina sanyi yayi ganin yanda yake fushi Kar na tafi ba a son ransa ba Allah yasa wani abun ya sameni.
Bedroom na koma na ajiye kayan Dana shirya na dawo Inda yake a Palo na zauna gefensa da sanyayyar muryarta nace na fasa zuwa Allah
ya kaimu ranar Event din sai ka kaini kamar yanda ka tsara.
Tausayina yaji sosai yayi wani Murmushi lafiyayye yace ko kefa Allah ya Miki albarka Ameen nace na kwanta a jikinsa.

Kamar yanda yace Haka ya kaini Dinner abin mamaki Ashe Saad Shi zai auri Safarau,a Company nasu take aiki shine Manager kuma,Lokacin yaso Ni a ransa Amma Allah ya taimakeshi ya Kai zuciyarsa nesa tunda suka hadu da Safarau Kyakyawa itama kusan Muna yanayi da ita ya kamu da sonta gashi yanzu,Munsha shagalin biki lfy mun Gama lfy.

Bayan wata biyu Tunda Saddiqa ta koma dakin mijinta tana zaune lfy tana kula da mijinta suna soyewa yayin da Alamin Wanda ya taba kidnapping dina suke soyayya da Meena kanwar Ice.
Saura kwana biyu bikin Ya Salman,Musa da Mahmood Dan Kawu Salisu.
Wannan karon Bai hanani zuwa ba cikina Yana wata biyar ya fara Fitowa ma Amma Haka naje Gombe a jirgi,shi da Daddy Kuma zasu zo daurin aure,Mum ma zata zo bikin da Meena,Saddiqa da wasu kannensu Sunyi min Kara sunzo, anyi biki lfy an Gama lfy,dama su Abbu sun koma sabon gidansu a birnin Gombe,sannan har kauyenmu naje ganin dangi.
Sai da aka Gama komai Dani sannan na dawo gida,lokacin Kuma tuni su Mum sun Gama Idda.

Nanee saurayinta na farko da suka Sha soyayya tun saurayi da budurwa yanzu shima Hamshakin me kudi ne yarans hudu kacal sabo da baya Haihuwa sosai a Nan birnin Adanawa, Matarsa kwana Nan ta rasu Yana Jin labarin Nanee aurenta ya mutu dama tsohuwar soyayyar tana Nan yazo,itama dake tun farko shine farkon soyayayyarta akansa tasan so,Allah yayi Bata aureshi ba yanzu kuwa Yana zuwa ta Amince ai kuwa ranar wata jumaa aka daura musu aure ta tare,yaranta dake Lagos labari kawai suka ji Sunyi bakin ciki tare da kishin Daddy,sanda Labarin ya iske Danbature shima baiji Dadi ba yaso Bata yi gaggawa ba Daddy ya dawo maybe ya maidasu dakinsu,Koda ya buga Mata waya sai hakuri ta basu kawai.
Bayin Allah Kar kuyi zaton Dan Mace ta Tara Yara gidan miji baza su iya rabuwa da Mijin ba,sannan komai tsufanki matukar kika fito daga gidan miji to da yawa tsofaffin samarinki sai sun dawo,wani dama Allah ya rubuta sai kin aureshi Amma sai kinyi Aure kin fito sannan shi ya aureki kaddara kenan Allah yasa mu Dace.

Karimatu kuwa babanta ya matsa Mata yace da sauran kuruciyarta ta fito da miji cikin zawarawanta ta aura a hakika ita Daddy tafi so ta koma gidansa Amma Shuru Bai ko nuna alamat zai iya maidasu ba,Dole ta yanke Shawara cikin Zawarawanta ta fitar da wani Me kudi Dan majalisar tarayya yayi sai uku ya rike mukamai da dama sannan yanzu ma shine Akan mulki a Maiduguri,Aiko ta aureshi bashi da wata matsala Kuma Yana da Matarsa daya da yaransa 7.
Sai labari muka Kara ji Karimatu ma ta tare a gidan mijinta Daddy Yana can Bai sani ba,ko a waya ba Wanda ya sanar Masa.

Mum kuwa so take ta koma wajen iyayenta can Paris Amma Ice yace wlh baza ta koma yanzu ba,Mum ta Gama Zama cikakkiyar salihar mace Sannan ta koma Islamiyyar Matan aure tana zuwa sosai Bata da aiki sai karatun ilmin islama, muna zaune lfy abinmu Ras,yayin da cikina ke Kara girma.

Cikina ya cika wata takwas Daddy ya dawo Nigeria yayi kiba kuruciyarsa ta kara Fitowa,har gidanmu sai ganinsa mukayi katsam lokacin Mum tana Islamiyya dagani

Please Login or Register in order to submit comment