Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai na musu Allah yasa ta shigi jikinsu suka ce a maidani sun daina aikata laifuffuka,sun gane kurensu, Alhmdllh muje gida to Allah ya shiryesu in Allah ya yarda kinfi karfinsu, Ameen Inshallah na Furta,cak ya daukeni tare da sani a gaban mota muka bar wajen,motsi kadan Yana kallona Yana Babu dai matsala ko?karki boye min komai pls,wlh kaji na rantse ko duka ko Hannuna Basu rike ba.
Murmushi yayi tare da shafa fuskata karki Kara Shiga motar Wanda Baki sani ba matukar bani na turo Driver ba,yanzu Driver zai na kaiki ya dakko ki kawai bazan Bari kiyi tukin mota da kanki ba hankalina bazai kwanta ba idan kika fita ke daya.

Na matsu ma ki Gama schl din Nan a huta,To masters fa nufinka bazanyi ba?baza kiyi masters ba baza kiyi aiki ba hakan ya Isa kawai,me kike nema ko mene Zan Miki har danginki to me zakiyi da kudin,burina yanzu kawai ki haifo min yara,Nima Haka na matsu na ganni da katon cikina,dariya mukayi gaba daya yace Allah zai kawo ne kinji.
Allah yasa na furta.

Soyayya da Shakuwa me karfi ce ta kullu tsakanin Dr who da Saddiqa,Duk shaye shayensa ya daina har neman matansa ya daina gaba daya sabo da Saddiqa tace Bata sonsa tunda Yana shaye shaye da neman Mata,Haka Yan uwan Alhaji da Dangin matansa kowa yace ta fito da miji Haka mazan su fito da Matan aure zai musu komai ya dau nauyi,yaransa ma Haka sabo da Haka kusan mutum goma Sha ne suka Nemo ma abota zaman rayuwarsu Matan da suka kawo Wanda Basu da aiki ko Sanaa Daddy ya samo musu,har gida an bawa wasu komai randandan,Dr who kuwa ya tsantsala gidansa,Aliyu kuwa sai kokari yake Yana tausar Daddy kan ya dawo da matansa yace bazai iya Zama dasu ba zai auri dattijuwa ta gari.

Yasan Yana son Matansa musamman Mum Amma dukkansu Babu ta kirki zuciya kuma Bata da Kashi Kar yazo ya dawo dasu dukiya tasa su canja halayensu again,yaso ace Asiya Bata aikata Haka ba da zai iya Zama da ita sabo da kyawawan halayenta Amma yanzu ko ya dawo da ita hankalinsa bazai kwanta ba,daga sanda ta caka Masa wuka gaba daya digon sonta a ransa babu, bare Kuma Mum,Karimatu kuwa ko ta shiryu sai ta cuceshi matukar ta dawo hannunsa, Kudi makudai ya fitar ko waccensu Million biyar biyar ya Sa musu a accnt su ja jari dasu,sai gida dankarere ko waccensu guda daya a state dinsu ya Bata,Aunty Maryam Kuma bazai iya siya Mata a turai ba zata kwashi kudi sai ya tura Mata kudaden gidan dai dai dana Su Asiya, Danbature yaje har wajenta ya sanar Mata komai ya nuna Mata kudinta tunda wayarta na hannunsa,Kuka da Nadama Sunyi ba adadi,Daddy ganin da farko ya zalinci Asiya da yawa da kansa yaje wajenta ya nemi yafiyarta again shima ya yafe Mata ya Bata kudin da takardarta saki daya da Kuma takardar gida Allah ya hadata da rabonta.

Kowa baiji Dadi ba Amma sun cancanci hakan,,sannan Kuma ya Zama darasi akansu Nan gaba idan sun auri wani sai su kiyaye sannan ya Zama Izina ga Wanda yaji labarin.
Bikin da za ayi Daddy yace Amare da angwaye Sunyi yawa kawai aure za a daura a Kai amare ba wani biki da Kade Kade da za ayi,yayin da su Ya Salman ma an Sa bikinsu saura wata biyu ayi sai Murna nakeyi zanje nayi sati guda,Mum Kuma waadinta ya kusa karewa saura sati daya ta fito daga Prison.

Yau ranar Jumaa yau Kuma aka daura auren Angwaye da Amare su goma Sha hudu ciki harda Dr who da Saddiqa ranar Kuma aka Kai Amare Ni Ina bangaren Saddiqa komai nata nice a kai,Haka Kuma Karimatu da Asiya sunzo aanyi komai dasu.
Washe gari gida Shuru duk ba Dadi an kwashe mutanen gidan,ga Baki ma sun tattara zasu tafi,yaran saura kadan sai Yan aiki,Daddy kuwa tunda ya Tara Angwaye da Amare ya musu Nasiha ya damkawa Danbature Amanar kula da sauran kannensu aka kaishi airport ya Shiga jirgi sai kasar waje.

Yayin da mu Kuma Muke zuba soyayyarmu ta gani ta fada,Suma Amare da angwaye ana ta Jin Dadi,Saddiqa Daren farkonta Kuka ta dinga yi da safe,Bayan tayi wanka tasa hijab ta fito daga gidan tana kuka,lokacin Dr who Yana wanka ta fito tana dingishi tana kuka,har ta Shiga taxi tace a kaita Tasha Wai Kauyensu zata koma,da kyar aka sameta a Tasha har ta shige katuwar Bus zata tafi garinsu Allah yasa Dr who ya gigice ya kirani a waya ya sanar min nace aje Tasha kawai,Dani da Danbature muka tafi wasu tashar shima Dr ya tafi wata Allah yasa Danbature ya hangota a cikin mota tana zare Ido kamar kace kyat ta zura da gudu,Dariya dai Kam mun shata,Allah yasa tana Jin tsoron Danbature yasa ta fito tana kuka,tana ganin Dr yazo wajen ta buya a bayana,Da kyar muke danne dariyarmu.

Bayan an sata a motar Dr who, Danbature ya jashi gefe ya dinga dariya har sai da Dr ya dinga fushi Yana masifa,Ice Yana rike ciki yace Kai baka da hankali kayi zaton irin Yan iskan matanka ne na da? Wlh duk yanda akayi wahala ka Bata,zaka kashe musu yarinya,dariya Shima Dr yayi tare da cewa to wlh Ni na manta Bata taba yi ba,Amma Zan Kira Doctor ta dubata,yarinya ta tona min asiri,Ice Yana dariya yace Kai ka jawo ka nuna Mata Kai ka Saba da mata Dole tazo Tasha ta nemi hanyar kauyensu,dariya sukayi gaba daya dama ko yaushe kamar frnds Haka suke,Ni dai Ina mota Ina ta lallashin Saddiqa tace wlh indai na Kuma Jin zafi Ni dai gwara ya sakeni bazan iya ba,idan nasan haka auren yake bazan yiba gida Zan gudu.

Da kyar na lallasheta,Shi Kuma Ice yace Wa Dr ka kyaleta tayi kamar 2wks ta huta sannan ka sake,Wani ihu Dr ya saki kamar an watsa Masa ruwan zafi yace sannu mugu,wlh ko Kai na tabbatar ko 3days da kyar zaka bar matakarka sai Ni zaka hadawa mugunta wato Ni na mutu ko? Inda yanzu Allah ya shiryeni kasan Ni bani da juriya ga yarinyar Nan Yar Shila ban taba Jin irinta ba kace Dan mugunta na barta 2wks,Ice yace to kayi abinda kaga dama Kuma wlh baza mu Kuma zuwa Nemo maka ita ba kasan dai yanzu Tasha tazo ko?to next time daji zata Shiga,Kai Malam bafa Zan karbi shawararka ba ato ka sani ma.

Ice Yana dariya ya min magana nazo mu wuce Ina zuwa ya rungumeni a bainar jama'a ko kunya yayi kissing dina a kumatu,Dr Who yace kw gani ko abinda kakeyi Ni Kuma za acuceni to bazan dauki shawararka ba,dariya mukayi gaba daya kowanne suka ja motarsu muka tafi.

Yau Monday yaune Kuma Mum za a saketa waadinta ya cika,murna wurin Ice da Dr ba a magana,Meena kanwarsu sosai yanzu muke shiri da ita watarana ma sai tayi sati guda a gidanmu tana girmamani sai abinda nace takeyi komai sai tayi Shawara Dani,idan tana gidansu kuwa kullum sai munyi waya munyi Hira.
Ice da kansa yaje ya dakkota gidansa,lokacin na shirya girke girken tarbar Mum,Dr na gidanmu tare da Saddiqa,Meena na Nan da wasu kannen nasu duk sunzo ganin Mum Suma Ana ta shagali,sun Ware speaker suna ta rawa iri iri musamman Meena.
Mum dake wuri me kyau aka sata ba sosai ta lalace ba,suna zuwa Murna ta kacame Ana ta Mata sannu,Sai Murna take yi itama,Bata ko zauna ba nace Mum muje kiyi wanka,yanda nake rawar kafa ko uwatace sai Haka,ta Dade tana darzar jikinta kayan data cire kaf a Dust bin muka zuba su,Dama kayanta na gidan Daddy an kwaso Mata, har da sababbi Ice sun dinka Mata latest masu tsadar gaske,cikin danyen lace ta hade Kai kowa ya kalli Mum yasan ta hadu ta ko Ina Bata tsufa.

Abinci muka baje aka ci aka Sha sannan muka taru kowa yayi Alwala mukayi nafila rakaa biyu na Godiya ga uban giji.
Mum wani Sona takeyi tana Masifar ji Dani,Haka Saddiqa ma duk da cewar Saddiqa Bata da walwala yanzu tana tsorace da Dr who,Mum tunda taga Haka ta gane Saddiqa dai duk surutunta da iyayinta Babu tasan Lallai Dr baya daga Mata kafa.
Bedroom din da muka bawa Mum taja Saddiqa tana tambayarta Kuna zaune lfy dai ko? Sai ko Saddiqa ta rushe da uban kuka ta kife kanta saman bed tana ta yi,Tambayar duniya Kuma taki fadar komai tace lfy suke.

Mum tace to yanzu Saddiqa Haka Zaki kula da Mijin naki,bakya koyi da Fadila,mijinki fa kin San sanadiyarki ya shiryu maimako ki daure ya Dore a Haka shine kike Haka,ko so kike ya koma harkarsa ta da can? So kike ko ya Miki kishiya,Ido fal da hawaye ta Dago tace Ni Dan Allah ya auri wata Ni na bar Mata shi wlh har ga Allah Mum bazan iya ba,dariya Mum tayi Lallai ba karamar azaba Dr yake bawa Saddiqa ba mace da kanta tace a Mata kishiya tun batayi 2wks ba.
Me yake Miki Saddiqa karki ji kunyata ki fada min zanyi maganin abin,Ni kunyarki nake ji sai dai na fadawa Aunty Fadila ta fada Miki,Nima kamar Mamanki ce ki fada min sai na hanaki komawa gidansa,Saddiqa na Jin Haka murna ta kamata tace To....ahm...uhmm....ta Sosa goshinta tace...Uhmmm...umm..Kinga dai..shine Nan dai....ta rumtse Ido tace Abu yake ta yi tun dare har wajen Asuba kawai Dan Hutawa akeyi kadan,Kuma da safe ma kafin ya fita Office,Haka da Rana zai dawo,ya koma Office,da yamma ma,Babu hutu Kuma duk naji ciwo yaki Bari na warke ta Karasa tana Hawaye.
Mum itama ta jinjina Maganar tace to baza ki koma ba muna Nan dake sai kin warke ki barni dashi,Saddiqa sai Murna take yi,Mum tace ai da tuntuni ki gudo gidan Ice kin sanar Masa,Tab Mum yafa Gama Raina Ice Wasa sukeyi ranar ma dariya suka dinga yi,Kuma Mijin Fadilan ne yace idan na sake fita daga gidan Mijina ba izninsa sai yasa Dr ya min abinda mutuwa kawai zanyi shi yasa ko kofar gida ban Kuma fita ba,rannan ma da kawayena suka zo ko rakasu banyi ba.

Dariya Mum tayi tace in Banda shirmenki ta Ina Ice zai ganki? Baki ta bude tace yace Na'ura ce dashi Yana daga gida zai ganni,Mum da kanta ta Kira Dr suka Sa labile daga ita sai shi,ta dinga Masa fada,tana bashi shawarwari nasu na manya karshe tace Saddiqa a Nan Zata zauna sai tayi sati guda na gyara musu yarsu sannan ta koma,Dr who kawai sai ya Kama kwalla yace shi wlh ba Wanda zai rabashi da Matarsa,Ni kake fadawa Haka? To Mum sabo da Allah Ina ruwanki a nan,so kike kawai Ni ki rabani da matata,Duk abinda zaka ce kace baza ta koma ba sai na gyara ta,Kai nakewa gata ai shashashan banza.

Ice ne ya shugo shima yace Saddiqa baza ta koma ba,cikin fushi Dr ya Suri key din mota ya bar gidan,Ina kiransa Amma yace Fadila baza ku Kara ganina a gidanku ba Tunda bakwa kaunata ya fice a fusace,ganin yayi fushi yasa jikin Saddiqa yayi sanyi ta fashe da kuka ta mike tace Mum Ni Dan Allah Zan bishi mu tafi Kinga yayi fushi,Mum a ranta tace yarinya me biyayya Bata son mijinta yayi fushi Nan take ta tuna da zaman aurenta a gidan Daddy su basuyi Masa Haka ba sai zaluntarsa da sukayi a hankali ta goge kwallar nadamarta.

Zamanmu lfy mukeyi a gidan bana taba gajiyawa da yiwa Mum Hidima,Saddiqa yau kwananta hudu a gidanmu ta Kara haske kyau da kiba,gata dama ta waye tana daukan wanka ni da Mum muna Kara wayar Mata da Kai da yanda zata kula da kalar mijinta Dr,Meena ma Kullum a gida wurin Mum take yini sai dare Driver ke maidata gida watarana ma a gidanmu take kwana tare da Mum.
Mum tayi fresh da ita sai dai kullum cikin nadamar zaman aurenta takeyi mijinta na sonta Babu asiri ba komai sabo da Allah Amma ta zalunceshi tir da halayenta a da.
Soyayya kuwa tsakanina da DanBature sai abinda yayi gaba,kullum kunya yake ba ni gaban Mum da Saddiqa baya kunyar uban kowa zai ta rungumeni Yana min kiss sai Ina yi ina boye Masa,Mum kuwa baturiyace ko a jikinta farin ciki ma takeyi sabo da su aladarsu Haka sukeyi wannan abin farin ciki ne, Saddiqa kuwa kallo take Sha tana Kara daukan darasi tace itama tana komawa zata dinga yiwa Mijinta ta rike abinta,tana ta koyan girke girke,ga novels na tura Mata a waya tana ta karantawa sabo da ta Kara koyon yanda ake rike me gida.
Dr who kuwa tunda yayi yaji Bai dawo ba Amma ya kasa daurewa da rashin masoyiyarsa Dole yau muna zaune muna Dinner sai gashi ya shigo.

Danbaturena ya kwashe da dariya tunda yaga Dr,Mum ta daki Ice a baya Ina ruwanka sashi to Babban banza,Saddiqa Kam sanyi taji a ranta tana Allah yasa ya huce, Bayan Ice da Mum ta duka na Shiga Sosa Masa Ina dariya nace sannu, Dr Bai kula kowa ba Mum kawai ya gaisar ya dauki Saddiqa cak ya zauna a kujerarta ta Dinning sannan ya daurata saman cinyarsa ya fara cin abincinta Yana Bata,Dani da Saddiqa kadai ne kunya ta kamamu kamar zamu nutse Amma Mum da yaranta ko a jikinsu sabo da dabiarsu ta turawa kenan ba kunya ba Kara wannan a jininsu yake.
Ana Gama cin abinci yace Mum mu tafi gida yau ko? Mum tace saifa tayi 1wk wlh kaji na rantse,Ok Mum to ai dai zata rakani mota ko? Ae rako ban hanata ba Amma 3mnt na Bata ta dawo gida nasan ba mutunci gareka ba,dariya mukayi Baki daya,Saddiqa ta mike ta rakashi mota,suna zuwa ya far kalallameta da dadin Baki cewar ta Shiga mota suyi a ciki sharp sharp zaiyi ya tafi Yana cikin wani Hali a matse yake,yanda taga yanayinsa taso ta yarda Amma sai Mum ta danno Kira ta shigo gida,Dole Haka ta bashi hakuri ta tafi ciki,shima ya dawo,Mum tace ka tafi mana ya Naga ka dawo,Baki ya turo gaba yace bazan tafi ba Nima anan Zan kwana na fasa,Nayi mamakin nacin Dr haka, da kyar Mum ta koreshi ya tafi ya sake cewa bazai Kuma zuwa ba gidan har abada,Saddiqa harda kukan tausayin mijinta.

Mum Kuma tace ko me zata yi sai ta Gama gyaran da take mana.
Kwana Nan Kuma yawan zazzabin dare nakeyi,kullum da dare da kyar muke yin bacci da zazzabin nake kwana sosai sai Asuba nake samun lfy.








AsmaBaffa
[9/4, 10:26 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕






86-90








Official







By
AsmaBaffa




Ina matukar Godiya da jinjina muku...
Maman Nusy,Aisha h kunji,Hassana Danja,Mr Mubarak,Ummu sadeeq, Aeesha A Salim,Maman Ameer,Ishkee,Maman Fati,Aishatu Musa gidalo,Deexu,oum Naufal.



Page naku ne
Aisha Humairah,Fancy Honey,Maman Yuseef,Hafsat, Oums Zara and Wasila.








Da sauri na kwaci kaina Ina harararsa da Wasa nace idan aka Kama mu fa? Wai ya akayi alkalin Nan yayi Saurin yanke hukunci haka Kuma yayi me sauki nayi mamaki fa,Murmushi ya saki tare da cewa aiki nane kin San kasar Nan sai da kudi sannan yasan Daddy shi yasa ya saukaka lamarin Amma da har Nanee sai tayi prison wlh bazai daga kafa ba.
Numfashi naja nace Kai duniya Wai Nanee guda,karki ga laifinta Mum ce da laifi ita tasa Daddy koma me ya aikata,ita Kuma Nanee zuciyarta ta fara bushewa da nasan hakan zata faru wlh gidansu Zan Bari ta tafi kawai gashi abin ya girmama, yanzu wanne Namiji ne zai iya Zama da macen da tayi yunkurin kasheshi? Ko ya hakura bazai saki jiki da ita ba,yanzu ban San wanne hukunci Daddy zai dauka ba da nine gaba daya sakin su zanyi.

Kadan na dukesa a kirji baka da kirki kawai yayi hakuri Kar ya sakesu,ka tafi gida kawai sai Gobe,kin ma Isa yarinya tare zamu tafi,nifa bazan bika ba,kwana na nawa rabona dake Dan Allah kizo mu tafi,Hajiyarmu tana Nan Ina so muyi Hira da uwata Ni bazan bika ba,takura min yayi Dole sai na bishi Ni kuwa na sakar Masa kukan shagwaba ba shiri yace ya hakura Amma shima a nan zai kwana gobe sai mu tafi gaba daya. Farin ciki ya kamani nace na gode na gudu ciki na barshi a Nan Yana kirana Amma naki zuwa,yace hmm zaki bayani.

Muna zaune a dakin da aka bawa Hajiyarmu muna Hira wayata ta Shiga ruri na duba Naga sabuwar Number na kirana,banyi niyyar dagawa ba Hajiyarmu tace ki daga mana Dole na daga naji wata Muryar Namiji Yana amsa sallamata,waye pls? Wani masoyinki ne Wanda ya Dade cikin matsanancin kaunarki,Malam wrong number ne Ni Ina da aure, Hmm ai na sani ba kece Fadila ba matar Ice? Nace ae itace,to nafi Ice sonki a sannu sai kin zamo matata Nan da kankanin lokaci zanyi sanadiyar mutuwar aurenki Ni kuma na aureki,Wlh Fadila da gaske kaunarki nake tun farkon ganina dake.
To Ni Kuma bana sonka bana kaunarka wlh ka kiyayeni Dan Babu Wanda nake so ko zanso a duniya sama da Ice,kafin yayi magana na datse wayata na kasheta Baki daya.

Hajiyarmu ta kalleni lfy Fadila? Waye Haka? Wlh ban sanshi ba,kiyi ta Addua to Allah kiyaye sannan ki sanarwa mijinki da wuri Kar ya hada Miki sharrin da za a kasa warwarewa,boyewa mazaje shi ke jawowa a samu babbar matsala ki sanar Masa da wuri.
Hajiyarmu duniya ce ta lalace yanzu da yawa ba tsoron Allah wasu ma su basa harkar nemen Mata sai da masu aure,wasu Matan Kuma basa neman maza sai Sunyi aure yanzu zamanin Nan Allah ne kadai yasan yaran da ake haifarwa wasu mazan suna rikesu a matsayin nasu Wanda Kuma ba nasu bane,
Hajiyarmu tace Ke Kam Fadila kinyi Dace Allah ya taimakeki da samun Miji irin wannan,ki daure ki kula dashi sosai ki Masa biyayya,mijine na gari Aliyu, ki Zama me hakuri da juriya,ki rike addininki, munga rayuwa munji abinda bamu taba sani ba a duniya kamar a film rayuwar wannan gida wlh munyi darasi sosai,naso ace anzo da Anty Amarya itama ta koyi darasi mu hadu mu Kara gyara halayenmu Dan muma muna da laifuka da dama Wanda inshallah zamu gyara mun koyi darasin rayuwa.
Farin ciki ya kamani nace Allah yasa Hajiyarmu,Ameen tace sannan ta Miko min katuwar Leda na kayan gyaran jiki ta fada min yanda zanyi Amfani dasu.

Nace Hajiyarmu Bari naje wajen su Ya Salman muyi Hira sai na dawo,to sai kin dawo ai su Salman sun samu ci gaba ta sanadin aikin da mijinki ya samo musu Murmushi nayi tare da furta ai na gani tun a jikinsu sunyi kyau da Zama Yan gayu ga daukan wanka Haka Ana ta kamshi,jeki kyaji komai daga bakinsu.
Ina Fitowa na Samu Abbu a part din Daddy suna Hira na Shiga wajensu da ladabi na zauna kusa da Abbu nace Abbu zuwa fa nayi na ganka na tafi,dariya sukayi har Daddy, Abbu ya furta jeki gobe zamu hadu.
Allah ya kaimu nace na fita zuwa bangaren Su Ya Salman suna part din Ice, Ina zuwa na samesu tare da Ice suna ta Hira harma da wasu samarin na gidan da Kuma wani Babban abokin Ice wato Alamin,Dr who ma Yana cikinsu Ana Shan hira.
Da sallama na Shiga suka amsa min na tsallake kowa na Shiga tsakiyar Ya Salman da Ya Musa na zauna dama su kadai ne 3seater.
Kawai sai Naga Danbature ya wani hade rai,kamar ban gani ba na shareshi na riko hannun ya Salman nace Ya Salman kuzo muje muyi Hira Mana ko tunawa Dani bakwa yi ai to yau sai mun kwana muna Hira,Dr who yace to anji masu yayye ba inda zasu duk abinda ma Zaki fada musu ki Adana su sai gobe,Ya Salman yayi Murmushi yace tashi ki tafi Ni bana Jin Hira yau,bare Kuma Ni da zanyi waya da sweetyna yanzu bamu da time naki sai gobe.

Shagwaba na fara yiwa ya Salman dama munfi shiri dashi nace pls Ya Salman tare da daura kaina saman kafadarsa,kefa bakya Jin magana bazan iya surutu yanzu ba na gaji ki tafi kiyi bacci sai gobe Kinga ma kusan goman dare ta wuce.
Mikewa nayi ganin Danbature sai fushi yakeyi Bai ce komai ba nasan da wata a kasa na fita da sauri Ina jinsa yace Bari naje na karbo sako wurin Daddy, basu gane ba suka ce sai ka dawo,ya biyo bayana,lokacin nabi ta Bayan corido lungu Ina jiyowa nayi arba dashi na Danji tsoro sabo da wurin akwai duhu kadan Kuma ban San Yana Bina ba,Fisgo Ni yayi da karfi na Fado jikinsa fuskar sa ba Rahma yace kina so mu Bata,me nayi Kuma na tambaya? Akan me Zaki Shiga tsakiyarsu maza ne fa,sannan Baki wani saurareni ba Ni da nake mijinki Zaki je ki daura kanki a kafadar Ya Salman,ba gwara kizo Ni ki daura kanki a jikina ba Amma ko kulani bakiyi ba dan na barki ki kwana anan wlh kika sake tafiya gida zamuyi yanzu.

Baki bude nake kallonsa nace Haba Danbature kasan fa yanda muke dasu Yan uwanane na jini muharramai na,na sani to Ni bana son Haka na fada Miki ma ki sani Ina da kishi,ai dai Yan uwana na ne kuma a Nan dai bazan daina ba sabo da na shaku dasu sai dai kayi ta fushinka.
Haka kika ce? ah to me zance maka Ni ba Wanda zai rabani da Yan uwana ehe,Ido ya zura min kawai yaga yanda nake Masa tsiwa Good ya furta ya juya ya tafi a fusace.
Nima na tafi Ina mita su maza in kana binsu komai kayi ace kayi laifi Haka kawai Ni bazan dauki Haka ba Yan uwa ma sai anyi kishi dasu mene na laifi a Nan fisabilillah.

Ina zuwa wanka nayi tare da Shirin bacci,Hajiyarmu tuni tayi bacci abinta gefenta na kwanta Bayan nayi Shirin bacci na,Number din dazu ce ake ta kirana da ita na daga nace Malam ka daina damuna na gaji wlh bana soka kiyaye na kashe wayar, Ashe lokacin Danbature ya kirani yaji number busy.
Sai Bayan 20mnt ya sake Kira lokacin nayi bacci ya dinga Kira ina bacci sai ya kule naki daga wayarsa.
Dama gashi da Saurin fushi watarana sai ya tunzira ya fara fushi,wasu da dama Haka suke Ana musu biyayya kullum Amma Rana daya idan aka samu matsala to fa babu Uzuri ba a tuna halayen mutum a baya da abin ki rkin da kayi sai laifinka za a kalla na lokacin da kayi.

Washe gari da safe suna tare dasu Salman can aka Kai musu kayan Kari iri iri,Ni kuwa da wuri naje na gaida Daddy tare da Abbuna mukayi Hira Da Abbu sosai ya Kara min Nasiha sosai yace Fadila hakika Ni kaina na koyi darasi dangane dake da Kuma gidan Nan kiyi hakuri farko bamu rikeki da Amana ba munyi tunanin takura Miki da Nuna kyama shi zai jawo kiyi aure koma waye bamu damu ba matukar zakiyi aure ba ruwanmu da ki auri na gari ko ma waye kawai ace kinyi Aure Wanda da yawa iyaye na Hausawa Haka suke kawai ayi aure koma waye

Please Login or Register in order to submit comment