Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *ADANDI*




*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*® FAUZAH*









*_Idan kinason ci gabada karanta wannan lbrn ki tuntubeni ta wannan number a WhatsApp_*
*_09013718241_*



*_Dont read this book if you are not married, Mature content contained in it, Reader discretion is advised, You read at your own risk._*


🅿 *1*


*_Bazanci gaba dasa number ba course masu fita dashi Allah ya isa kuma ban yafe ba duk wacce ta fitarmin da buk saboda bake kadai kika biya ba faqat_*


Da mugun gudu motar me qirar Ferrari ta shigo makarantar Adon Bayero University wadda suke Kira da new set birki ta taka da sauri tare da furta “ya Salam na bigeshi wlh na bigeshi rahama" tana fadin haka ta balle murfin motar ta fito da sauri wata kyakkyawar budurwa ce chocolate color wadda da gani babu tambaya kasan tanaji da kanta kuma tana tashen rashin kunya duba da yanayin shigarta.




Riga da wando ne farin jeans da jar riga three quarter ta hade gashinta na fulanin asali ta daure a baya ta dora wata hula me kamar nadin gammo a kanta tsakiyar kanta a waje ta zuba zobunan gold qafa da hanu sai daukar ido takeyi kamar walqiya duk wani lafiyayyen namiji idan yaganta a yanda take sai yaji yarr a jikinsa yanda take takawa duwaiwakanta na juyawa hips dinta yana daukan hankalin maza duk inda kyau yake Samha takai a kirata kyakkyawa.




Da dan sassarfarta ta qarasa ta tsuguna gaban kyakkyawan farin saurayin takai hanunta zata kamoshi ya kuwa daga hanu ya dauketa da wani lafiyayyen mari ta dafe gurin da sauri ta dago ta dubeshi bakinta yana rawa kafin tayi mgn ya sake dauketa da mari yace “ke wacce irin yar iska ce ki rinqa yiwa makaranta shigar isa saboda rashin tarbiyya dubeki waike kin waye jahila daqiqiya dake saboda kunfi qarfin kowa shiya aka kyaleku kuke abinda kukeso to wlh ba commusioner ko gwamna ne ubanki zan iya bi dake da abinda kike taqama dashi banza shashasha ballagaza kawai dubi shigarki waike qaramar yar iska mtssss"



Yaja tsaki tare da miqewa ya dingisa qafarsa dake zubar jini ya nufi wani teather dake kusa da gurin, wasu hawaye ne masu zafi suka zubowa Samha a idonta tunda take baa taba marinta ba ba marin ne yayi mata ciwo ba irin kalaman batancin daya fada Mata sune sukafi komai zafafa zuciyarta fitowa qawarta Rahmah tayi ta kamo hanunta tace “kinyi mugun bani kunya Samha kamar ki ki tsaya wannan qazamin dalubin ya mareki duk jin izzarki da isarki ni wlh tsoroma naji kar wannan daskararren hanun nasa yaji miki ciwo" ta fada tana shafa kuncin qawar tata.
Kawar dakai tayi ta furzar da wata iska me zafi ta taka a hankali zuwa inda motarta take ta zagaya wajen me zaman banza ta zauna tare da cillawa Ramsy key din taja suka qarasa.



Har Ramsy tayi parking Samha batasan sunzo ba sanya hanu Rams tayi ta janye mata tagumin tace “ki manta kawai mu ya tabo wlh Idan yayi wasa sai munsa anyi withdraw nasa a skull dinnan.
“Wayeshi a makarantar nan da baisan wace ni ba wayeshi da baisan matsayi na ba meye taqamarsa a school dinnan Rams meye taqamar guy dinnan daya jizgani haka?"



Bude mata motar Rams tayi tana riqe da jakarta tace “ki manta kawai dole ya girbi abinda ya shuka Samha...." Daga mata hanu tayi suka jero matasan dake gurin suka taso su uku suka rungume suna fadin Allah ya taimaki uwar dakin mu yaufa da haduwa a club.




Murmushi tayi na qarfin hali karo na farko data farayin danasanin shigar isar da takeyiwa makarantar tasu ta hanyar yin gudun wucce sa'a tare da buge duk wanda tsautsayi ya fada kansa.
Wasu yan matane su uku suka taso bayan matasan mazan sun gama shafeta daga sama har qasa dayan yayi kissing boobs dinta suma yammatan rungumeta sukayi suma murmushin yaqen tayi musu ta wuccesu ta nufi Hall din da zasuyu lecture ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.



Shigowa sukayi suka zauna kusa da ita dukkansu fuskarsu dauke da damuwa da alamun Rams ta qyasa musu abinda ya faru Surayya ce ta ruqo hanunta tace “kiyi cooling mind dinki Samha babu wanda ya isa ya takaki a cikin mkrntar nan mu kyaleshi wlh saiya gane kurensa sai yasan ya tabo click din masifa da bala'i" Nadiyya ce ta cafe tace “kecema kika ba damu Samha da kinbi takan dan iska kin markadeshi kamar greater aida baiyi mana wannan cin mutuncin ba" Rams ce ta cafe zaren zancen da cewa “ni nama rasa me zance tun dazun wlh ni tun ranar dana ganshi naga yanda yake taqama da kyau da isa gaba daya naji na tsaneshi" Zainab da tunda aka fara mgnr take kallonsu tayi qwafa tace “uhm kune baku sanshi ba bakuda lbrnsa a haka jin kansa yake saboda yana da kai sosai Abdullah kenan duk faculty of law shayinsa sukeyi asalinsa dan sarautar Katsina ne amma da ganinsa a wahale suke sarautar ma wlh" dukkansu suka kwashe da dariya amma banda Samha data dora hanunta a kanta tace “oh sheet!"



Tsayawa sukayi suka zuba mata ido takart ta dauka ta fito da bututun shisher ta miqawa Rams da sauri ta karba ta dauki magic could ta kunna Mata a ciki ta zuba mata flavor din ta miqa mata ta sanya a bakinta ta zuqa ta fesar tana sauke ajiyar zuciya zuqarts biyu tayi jifa da ita ta dafe kanta tace “tention din kaina yafi qarfin wannan bude Jakarta ta kumayi ta dauko wasu qananun qwayoyi ta watsa a bakinta tabi dasu da ruwan ever din dake hanunta daidai lkcn malamin nasu ya shigo duk faculty of educational psychology ana tsoron malamin amma banda wannan click din sai ya kasance shine ma yake tsoronsu saboda tsagerancinsu dadinta daya shugabar tasu wato Samha tana gane darasin nasa sosai wanda ya sani bawai donta gane din take zama ba kawai brain dinta ce me saurin ganewa batare data nemi shawararta ba gyaran murya yayi yace “yau zamuyi lecture ne akan clinical psychology..."



Iyakar abinda Samha taji kenan harya gama ya fita kanta yana kife saman dext tana baccin qwaya sosai lamarin yarinyar yake bashi mamaki bata missing attending lectures amma kullum cikin maye take indai lkcn lecture dinsa ne ance talauci shine yake sanya lalacewar tarbiyya da shaye shaye to kuwa idan har gaskene da Samha Sa'ad Dandoki batayi ba saboda talaucin ma gudunsu yake saboda yasan uwarsa zaici harda ubansa a wannan family din.





*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*



*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*




🅿 *3*





Dagowa yayi fuskarsa daure tamau wanda hakan yasa gabanta faduwa be amsa Mata ba bai kuma daina kallonta bai cikin kallon dake nuna asalin qyamarka da abinda kake kallo, daqyar ta iya tattara yawun bakinta tace “in dama nazone saboda na baka hqr akan abinda ya faru jiya wlh tun jiya na kasa samun nutsuwar zuciya inason idan nayiwa mutun laifi na bashi hqr ya nunamin yafiyarsa gareni nasani tsakanin Allah da bawansa akwai yafiya da gafara Amma tsakanin bawa da bawa Allah baya shiga harsai sun yafewa pls don Allah kace ka yafemin Abdul"



Ta fada tana durqusa gwiwarta a qasa, ajiyar zuciya yayi cike da mamakin yarinyar saukowa yayi daga saman motar da yake ya juya zaibar gurin saboda mugun haushinta da tsanarta yakeji ya tsani mace mara kamun kai wadda batasan ita halitta ce mai daraja abar kawwamewa da alkintawa ba Amma tazo tana sarayar da qimarta da mutuncinta tana tallan surarta da kyawunta.
Har yayi nisa da ita ta daga murya da sauri tace “na roqeka badon niba don darajar Annabi Muhammad (S.A.W) kacemin wani abu Abdul"




Murmushin takaici yayi yace “kije ki qara ilimi akan wanene Annabi Muhammad wanne saqo yazowa da duniya sannan wanne dokoki ya shimfidawa matan musulmi tukunna kafin ki hadani dashi" memakon taji ciwon mgnrsa sai kawai tayi murmushi tace “na gde da hakanma " kafin ta gama rufe bakinta har yayi mata nisa bayansa tabi da kallo tana murmushin jin dadi tare da qarfafawa kanta gwiwa.



A kasalance ta nufi faculty dinsu tana shiga samarin sukayo Mata cahhh suna tafi suna kiran sai Samha Allah dai ya biya Uwar dakinmu kina bada kala Hajiya aci gaba da bada wuta" murmushi tayi kawai ta nemi guri ta zauna wannan karon ta saurari lecture sosai musamman da malamin yake bayani akan alamomin kamuwa da son wani abu da kuma na qiyayya sai taji kamar don ita yake lesson din basu fito ba sai 12:30pm dake course din three credit ne suna fitowa suka nufi capteriar wani restaurant suka shiga sukayi order ta abin da suke buqata suka faraci daga idon da zatayi ta hangeshi shida abokansa a zaune a wani table dake nesa dasu kadan Ja'afar Nasir Khamal Mansur saishi na biyar ajiye cokalin hanunta tayi ta dora hanunta akan hannayenta tana qare masa kallo ta cikin glass din dake idonta saida suka gama Rams tayi mata mgn tajita shiru juyawar da zatayi taga Abdul din ta zubawa ido duk da akwai glass a idonta takaici ne ya kama Rams ta jijjigata sannan ta dawo hayyacinta ta miqe ta cire kudi a aljihun Jakarta Rams tace “namu da nasu Menson"




Tana fadin haka ta fara takawa zata fita daidai lkcn daya dago suka hada ido duk da nata a cikin glass yake, tsaki yaja tare da ajiye cokalin hanunsa Ja'afar ya kalleshi yace “yada tsaki haka?" Sake daure fuska yayi yace “na tsani mace ballagaza a rayuwata yarinyar nan tana daya daga cikin mutanen da da zaa bani dama zan kasheta saboda batada wani amfani sai yada fasadi da sabon Allah a doron duniya bata boye fasiqancinta a fili take fito dashi" dariya dukkansu sukayi sukace “Samha Sa'ad Dandoki kenan" Ja'afar ne yaci gaba da cewa “yanda yarinyar nan take burgeni bata shiga abinda babu ruwanta sannan batada hayaniya dadin dadawa qwaruwa ce ta wajen karatu sannan tanada naci akan duk abinda tasa a gabanta bata da girman kai ga wanda yayi mu'amala da ita amma tana da kwarjini, yar gatace sosai ta gaban kwatance ita kadai iyayenta suka haifa mahaifiyarta Shuwa'arab ce babanta kuma Bakatsine ne suna sonta fiye da duk hangenka Abdul tunda ta taso a rayuwarta batasan fada ba balle duka batasan babu ba komai takeso shi take samu ciki harda karatu anan B.U.K itace ta dage sai tayi karatu anan kamar yanda kaima ka dagewa mai martaba saida ya qyaleka ya turoka kake basaja Abdul Samha tantiriya ce ta gaban misali zata kashe ko nawane wajen holewa da rayuwar nishadi Daddynta yana Abuja da Mamynta ita kuma gdanta yana nan Janguza siya matashi Daddynta yayi kawai saboda tayi zaman karatunta anan Samha bata less kuma bata zina kamar yanda kowa yake tunani barta da lashe² da tabe²nta click dinsu yan lesbian ne kuma mazinata ne amma banda ita saboda alqawarin data yiwa mahaifinta zatayi komai amma banda shiga qungiyar asiri banda zina banda less kuma banda shan Alcohol bayan wannan har hodar iblis wani lkcn tana shaqa aminiyarta Rams itace take bani wannan lbrn sama da shekara daya kenan dana nuna inason rayuwa da ita sannan ta gargadeni koda wasa kada na furta mata kalmar so saboda abune me sauqi taci mutuncin mutum akan so kullum furucinta daya ne abune me wuya ta bada so amma idan taba dashi bata qwacewa wannan shine kadan daga cikin tarihinta saboda na lura kai baka sani ba"




Ajiyar zuciya yayi tare da yarfe hanu yace “wannan ba abinda ya shafeni bane amma wlh qaryane akayi maka wannan yarinyar tasan maza wlh bazata rinqa wannan tantirancin a banza ba" nan ya kwashe duk yanda sukayi da ita tun daga jiya har kawo yau ya sanar dasu.
Wata uwar ashar Nasir ya saki yace “Abdul kanada lucky a rayuwarka tunda har Samha ta bigeka a mota ta tsaya kuma harta qara binka domin baka hqr da kanta yawanci saidai ta tura yaranta subawa mutum hqr wannan shine tsarinta" wani kallon banza ya watsa musu yace “ku dama a gurinku saa ce tunda halinku daya nikuwa a gurina asara ce banga wani abun burgewa ba don wannan karuwar yarinyar ta shigo rayuwata shine har na zama me sa'a?" Khamal ne ya cafe da cewa “yess ni ta kulani ma mana aida naji dadi Samha fa ake fada maka babbar yarinya yar ministan kudi ce fah su qasar takeyi dasu tunda tazo skull dinnan bata tabayi session biyu da mota daya ba kuma naji wasu ma sunce bata taba maimata sutura ba"




Miqewa yayi batare da yabasu amsa ba don ya gaji da shaqar kayan takaicin nan nasu suma miqewa sukayi suka bisa suka fita daga capteriar suka nufi Department dinsu suka fara daukar darasi.
A bangaren Samha kuwa rayuwa ta fara sauya mata duk abinda take daukansa me sauqi a baya yanzu shine yake bata wuya abinda take dauka jin dadi yanzu ta fahimci ba shine jin dadi ba asalin jin dadi yana tattare da samun soyayyar abinda kakeso gskyr Dr Zaks da yace babu abinda yakai soyayya dadi kasancewa da abinda kakeso yafi komai dadi da sanya farin ciki itama shaida ce saboda yanda takejin dadi da nishadi hadi da farin ciki Idan ta hangi Abdullah ko daga nesa ne.




Ta mayar da gurin zamansa yana nazari gurin zamanta takan zauna ita kadai a gurin ta dauki handbook tana dubawa wanda a zahiri bawai karatun takeyi ba kawai kallonsa takeyi lokuta da dama takan gwada yi masa mgn amma yakan shareta kamar bayajin me take cewa hakan yana damunta amma bata taba nuna masa ba itadai kullum burinta shine ya fahimci halin da take ciki ko ya tausaya Mata.





*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*




*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk_*




🅿 *2*



Yana fita Rams ta tasheta tace “tashi muje hostel mu kwanta Zeee inajin feeling dinki sosai wlh" itadai batayi mgn ba saboda kowa yasan Samha yasan miskila ce da ake cewa tafi mahaukaci ban haushi.
Motarta ta shiga ta jirasu suka iso taja suka fice maimakon hostel din fita sukayi daga mkrntar suka nufi cikin unguwar Janguza gaban wani matsakaicin gda sukayi parking ta cilla musu key din tace ku wucce kawai bazan samu zuwa birthday din Najwa ba kice mata banjin dadi" tana fadin haka ta sanya key ta bude gdan ta shiga ta sake bude qofar falon ta shiga ta zube a kujera tanajin kanta na juyawa miqe ta shiga dakinta tayi wanka ta dawo tayi sallah ta kuma shiga kitchen tayi jallop din cous-cous ta dawo ta zauna bata iyacin na kirki ba ta koma dakin ta kwanta duk son Samha da yawo ranar a kwance ta yini tana tufkawa da warwarewa sai sha biyu da rabi na dare qawayen nata suka shigosu hudu zubewa sukayi a falo suna mayar da numfashi, itama ba bacci takeyi ba kawai a kwance take don haka ta miqe ta fito sanye da rigar a jikinta tana fitowa Zainab ta zuba mata ido tana hadiyar yawun kwadayin son kasancewa da Samha yana damunta amma tasan ranta nw zai baci ma don duk inda take tunanin tantiranci Samha ta fita amma bata lesbian ke ko mazan ma ita bada kowanne gara take harka ba lamarinta yana bata mamaki Samha ta qware a video sex chat da call sex amma kullum cika baki takeyi batayin sex bata taba yiba kullum fada musu take Mijinta shine zai fara saninta.




Nadiya da Zainab cikakkun yan lesbian ne Rams kuwa da Samha sunfi qwarewa a harkar maza.
Zamanta ne yasasu kallonta Rams tace “meye ya hanaki bacci Pretty?"kallonsu tayi tana yatsina fuska tace “inajin wani abu yana damun zuciyata game da guy dinnan idan harda gaske ne abinda kuka dade kuna fadamin akan so to bana tantama na rufta Rams na fada tarkon wanda bansan ya zai karbeni ba Rams" kallonta sukayi suka “waye wannan wanne dan sa'arne?" Dago dara²n idanunta tayi tace “Abdullah..." Miqewa sukayi a firgice sukace “Abdullah kuma Samha?" Itama miqewa tayi ta dora hanunta a kanta tace “na shiga ukuna meyasa qaddarata ta hadani dashi yaya zai karbeni wlh tun lkcn da abin ya faru zuciyata ta kasa hutawa da tunaninsa da farko nayi tunanin tausayinsa nakeji sai daga baya na fahimci zuciya tace ta karbi wani baqon saqo me wuyar fassarawa game dashi wlh inajin wani abu yans ratsa jikina game dashi inason mu'amala dashi inason kasancewa dashi pls kubani shawara ya zanyi friends"



Ajiyar zuciya suketa saukewa gurin ya dauki shiru kafin Zainab tayi qarfin halin cewa “kawai Ina ganin kudi zaki sakar masa ki fito masa da ainihin kyawunki da surarki namiji ne kuma inada yaqinin lafiyayye ne dole zaiso kasancewa dake daga haka kawai saiku soma rayuwa dashi...." Saurin daga mata hanu tayi tace “ya isa haka Zainab bakisan so ba Nadiya inajin taki shawarar” ajiyar zuciya tayi tace “ki bishi a hankali kada kiyi gaggawar nuna masa ki rinqa shiga jikinsa a hankali sannan kisan duk wata hanya da zakibi domin siye zuciyarsa"




Juyawa tayi ga Surry tace “kefah?" Numfashi taja tace “ni nama rasa abin cewa kibi shawarar Nady kawai idan da gaske kike sonsa amma banda abinki ma me zakiyi da qazamin guy dinnan ko wanka bai I dauka ba don Allah kada ki zubo mana da ajinmu mana pretty ga guys na masu tafiya da zamani daidai dake zaki biyewa wani alaramma....."



Kallon da taga Samha tana watsa matane yasata saurin tsuke bakinta Rams ta cafe da cewa ko ki yarda ko karki yarda Abdul ba tsaranki bane ba kuma abin kunya ne a gurinki damu kanmu ace wata cikinmu tanason kucakin yaron nan balle keda kanki meye ma ya burgeki dashi dan Allah meye abin sha'awa a gurin wannan yaron don baikai matsayin dazan kirashi haka kema pretty ki basar kawai ki dauki abin a matsayin raha" daga mata hanu tace “ya isa haka Rams kin sani ba abune me sauqi bayar da soyayya a gurina ba tunda baku tabajin koda wasa na bawa wani ba amma idan na badata bana qwace ta sannan abu qarami shine yake burgeni a mutum harma na mallaka masa abu mafi tsada a rayuwata so Rams jarumtakarsa itace abu na farko daya burgeni don haka nayi alqawarin zanyi juriya da hqrn duk abinda zan fuskanta gareshi har zuwa lkcn da Allah zai cikamin burina ku daina tunanin so irin na sha'awa nake massa aa so irin na aure nakeyi masa”



Tana fadin haka ta miqe ta shige dakinta ta kwanta sun jima a falon suna jinjina girman al'amarin da shugabar tasu ta dauko kafin Nadiya da Zainab su tashi su shiga wani dakin data basu suke kwana ita kuwa Surry saurayinta ne yazo ya dauketa saboda itadai Samha ta yarda ta kawo namiji gdanta amma bata yarda wani ya kawo mata ba.
Rams ce ta shiga dakin Samha ta ganta kwance ta zubawa p.o.p din saman dakin ido dafata tayi tace “ki fahimceni pretty wlh guy dinnan wulaqantaki bashi da mutunci baya shiga harkar mata ko kadan yanada aqidar tsiya abokin man-son nefah duk iskancin Manson tunda suka hadu yayi sanyi damma dasu Ja'afar suna dan janyeshi " tunda ta fara mgnr har ta gama miskilar batace komai ba dole taja bakinta tayi shiru ta koma ta kwanta.




Da safe da wuri Samha ta tashi ta hada tea tasha ta shirya lkcn suma sun tashi duk sun gama shiryawa ita kawai suke jira ta fito cikin takunta na isa ta suka fita lkcn har almajirinta ya wankenta motar, yau a nutse take tuqin ba kamar ko yaushe ba harta shiga makarantar ba iya su Rams ne kadai suke mamaki ba harma da sauran dalubai saboda sanin kansu ne hakan sabon abune a gurinta.
Can nesa da inda tayi parking ta hanqeshi zaune saman wata mota qirar HONDA da wani littafi a hanunsa ta jima a zaune cikin motar ta dora habarta saman sitiyarin motar tana kallonsa yayi mata kyau sosai cikin qananun kaya blue jeans da black shirt me gajeran hanu dantsensa cikakke me cike da gargasa sumarsa tasha gyara da dan siririn sajensa daya qara mawa fuskarsa kyau.





Bude motar tayi batare da tayi tunanin komai ba ta nufi gurinsa rungume da takardunta na karatu sai wayoyinta guda biyu sanye take da qananun kaya riga da wando pencil ta gyara gashinta me yalwar tsayi tayi donunt dashi dan qaramin mayafi ne a kanta ta rufe gashinta dashi wanda da yawan mutane suna dauka gashin kanti ne saboda tsayinsa da baqinsa rigarta armless ce mara nauyi amma ta sauka har zuwa cinyoyinta shigarta kenan tunda ta shigo makarantar shekara biyu kenan tana qarasawa tayi masa sallama cikin siririyar muryarta tace “Assalamu Alaika Barrister Abdullah barka da hutawa"






*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_AD_*



*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*





Jarabawa ce take tunkarosu wadda zata kasance ta qarshen session zasuyi hutu me tsayi hakan ba qaramin damuwa yake sanyata ba saboda ta sani zatayi nisa da masoyinta wanda baimasan tanayi baduk Wanda yake tare da Samha zuwa yanzu yasan ta shiga cakwakiyar

Please Login or Register in order to submit comment