Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwan su
ba, saboda dai ni din ni ce uwarta. To irin rayuwar da
ni na yi irinta ita ma Adawiyyah za ta yi?"
Yaya Junaidu ya kalleta cikin nutsuwa ya ce
mata, 'Eh Umma za ta yi rayuwar gwagwarmaya da
kwaramni'ya irin wacce kike cewa kina jiye mata
tsoro, sai dai kar ki manta kin yi rayuwar
gwagwarmayar ne a karkashin shugabancin mutum
mai adalci, mutumin da ya san karamci da amana,
wanda ya sadaukar da rayuwarshi don samarwa
kasa da shi ingantacciyar rayuwa, ba kuma sai na
gaya miki ba kin fi sanin cewar bai hada ki da kowa
ba a zaman da kika yi da shi, balle ya fifita wani a kan
ki. To ki yi wa Adawiyyah addu'a ita ma ta samu irin
na kin, amma ba ki, rinka gudar mata ba. Na sha cin
cewa Umma ina yi wa 'yanmata nasiha da cewar lallai
ne su zamo masu godiya bisa alherin mazajensu."
Umma ta yi shiru ta sunkuyar da kanta kasa
lana sauraron shi da ya yi shiru, sai ta ce mishi, "Na
19

gode Junaidu." Suma suka yi mata sallama suka fita
suka tafi na dan bi su da kallo. Sai da na ga sun bace.
Sannan na matsa kusa da ita na ce mata;
"Umma." Ta dago ta kalleni. Na ce mata,
"Wai me ya kawo Wadannan abubuwan
Umma?"
Ta yi shiru tana kallona. Na ce,, "Kuma ga
wasu maganganun ban mamaki da na ji Yaya Junaidu
yana yi a gaban Baba da ban san me suke nufi ba.
Anya Umma ba kya yi mini wani boye-boye kuwa ko
wani kunu-kunu..."
Kan in karasa sai kawai na ji ta kife ni da wani
irin mari, sai da na dungura a kasa.
Tsoro gami da mamaki suka taru suka
lullubeni. Yau kawai sau biyu Umma ta maren, mari
kuma ba na wasa ba. A tsawon zamana da ita kuma
kafin yau hakan bai taba faruwa ba. Lamo na yi na
kwanta a kasa ina sauraron abin da zai biyo baya, ko
za ta rufc ni da duka ne? Shiru ban ji wanr motsi ba,
don haka na lallaba nan ja jikina na shige cikin daki
na hau gado na kwanta, na bar ta nan zaune a kan
kujera kuka take ta yi a zuciyata na ce "Watakila dai
da ma dan kadan kike jira."
Yanda Umma ta kwana a zaune tana kuka haka
nima na kwana a kwance idona biyu. Al'amurán
wunin ranar na ke tunawa, tun daga ji dana yi baba
yana anbaton hadani aure da Yaya Almu ko da yake
dai ban samu wanda ya amsa cewar ya tayani jin
20

wannan zancen ba. 1o amma kuma al'amura musu
yawa sun biyo bayan hakan, masu tsanani da kuma na
ban mamaki.
Gari na wayewa na y1 komai da na saba a
dakin tun daga wanka,, da alwala da sallah. Na yi
kwalliyata ta hanyar gyaran jikina na kuma shafe shi
da turaren Humra. Sannan na sanya doguwar rigata na
yane kaina na fito don in gaida Umma. A falo inda ta
kwana a zaune kasa kallon fuskarta na yi, saboda
kunburin idanuwanta.
Ina gama gaishcta na shuri takalmana na fita
ba ta kirani ba, watakila ta yi zaton za ni gaida
mutanen gidan nc, ko kuma wurin Baba, tun da yana
nan, ni kuam dakinsu Yaya Almu na nufa za ni wurin
Yaya Junaidu, don na gane akwai wani abu muhimmis
a tsakanina da shi. Sai da na ji ya amsa sallamar da na
yi kafin na tura kofa na shiga dakin na su, yana
kwance akan katifa yayin da Yaya Almu yake zaune
kan kujera guda daya da ke dakin. Na durkusa na
gaishe shi, yana amsawa cikin nutsuwa sosai watakila
shi ma ya gane giFmamawar da nake yi mishi ya karu.
Ya zuba mini ido cikin yanayin kulawa sosai kafin ya
ce mini,
"Me ya fito da ke yanzu a sanyin nan kuma da
sassafe?"
Na ce mishi, "Yaya Junaidu wurinka na zo,
don na gane akwai wani abu mai girma a tsakanina da
kai nan gane kana da wani muhimmanci mai karfi a
21

kaina, duk da ban san fa inda ya fito ba.
A hankali ya ce mini, "Amma ina fata ba abin
da kika zo tambaya kenan yanzu ko?"
Na ce mishi, "Eh Yaya Junaidu zuwa na yi in
tambayeka ka gaya mini gaskiya ka ji Baba ya ambaci
sunana a wurin nan jiya?"
A nutse ya ce mini, "Na ji ya ambaci sunanki
Adawiyya mene ne?"
So nake ka gaya mini dawa ka ji ya ce zai
hada ni?"
Cikin nutsuwa ya ce mini, "Da Mustapha ne."
Na sake kallonshi na tambayc shi, 'Wane ne
Mustaphan?"
Kan Yaya Junaidu ya amsa mini sai na ji Yaya
Almu ya ce mini, "Mustaphan wurin aikin ku, ko ba
sunan yallabai din office din ku kenan ba? Ai kin san
na gaya miki cewar bayan kin gama aikin nan zuwan
yallabai din ku biyu ya zo wurin baba, saboda an ce
mishi ba zai yiwu ya zo ya kiraki ba sai ya nemi izini.
To shi ne daga baya ya turo iyaycnshi."
Sanin da na yi an yi wadannan abubuwa da
Yaya Almu ya fada duka ya sa na kidime nan da nan
na shiga kokarin tunanin sunan yallabai na asali. Ina
cikin haka Yaya Junaidu ya ce mini,
"Saurare ni Adawiyyah."
Na juya gare shi na maida hankalina wurin
sauraron abin da zai gaya mini. Ya ce, Ki nutsu ki
zama mai hankali, kin ji motsin wata yarinya a gidan
22

nan tun da aka yi maganar nan?"
Na ce mishi, "A'a."
T kina nufin su duk sun gamsu da abin da aka
yi musu ne?"
Ban amsa ba, sunkuyar da kaina kasa kawai na yi.
Ya ce, To ina tabbatar miki biyayya kawai
suka yi, don haka ki tafi ke ma ki nutsu ki zauna
wurin daya ki kudurwa ranki yi wa Baba biyayyar da
tafi ta su yawa."
Na ce mishi, 'To." Na mike zan fita da ni,
"Daga nan kar ki je ko'ina ki wuce wurin Umman ki kawai."
"Zan je in gaida Baba tukunna." Na ce da shi.
"Baba yana Lagos yanzu Adawiyya sai da
muka ga tashin shi a filin jirgi ni da Mustapha. Sannan
muka biyo hanya muka dawo muka yi sallar Asuba a
gidan nan Ya dauki Umma Amarya sun tafi ya bar
Umma Karama, duk da da ita ya kamata ya koma ta
karasa kwanakinta da ba ta gama ba, saboda bai huce
ba kan laifinta da ta yi mishi ita ma Umma ya tafi bai
yi mata sallama ba, saboda ran shi ya baci da abin da.
ta yi mishin, ko ni da Mustapha mun ji ana bude get
din gida ne muka fita da sauri muka gan su za su tafi
shi ne muka yi mishi rakiya, don haka ki nutsu ki
shiga hankalinki kar ki bari shi ma ya yi fushi da ke."
To yaya Junaidu." Na ce da shi.
A falon Umma na same ta zaune kan sallayarta
23

na durkusa a gefenta duk da tsoron da nake ji na kar ta
sake marina. Na ce mata, 'Umma baba ya taff" Ta
gyada kai nuna alamar ta sani. Hawaye suka zubo
shar! Daga idanuna loakcin da na buda baki na ce
mata, 'Saboda ni ya yi fushi da ke?" Ta dan saki
fuskarta ta shafa fatiha ta miko hannu tana share mini
hawaye a hankali ta ce, "Ba saboda ke ba ne
Adawiyya laifi na yi mishi."
Na sake kallon Umma cikin nutsuwa a kumna
tsoracc na ce mata, 'Umma." Ta zuba mini ido tana
kallona cikin sauraro ni kuma ina tsoro fadin
maganar, don ina tsoron marin da ta gane yi mini, ban
sani ba ko ta gane haka ne sai ta miko mini hannunta
alamar wai in kara matsawa jikinta, cikin sauri na yi
hakan ta kwantar da kaina akan cinyarta ba tare da ta
yi mini komai ba, nima kuma ban sake yin wata
magana ba. Har baba Talatu ta shigo tana tambayar
me za a shirya mata na abin karyawa?
Wajcn karfc goma da rabi ne yaya Junaidu ya
shigo ya gaida Umma, ya kuam shaida mata cewar za
su bi bayan Baba za su je su bashi hakuri kan fushin
da ya yi. Ta ce mishi yana da kyau hakan kai da
wayc? Ya ce dukkan mu ni da Zubairu da Kabiru da
Mustapha. Ta ce to ku gaishe shi.
Bayan fitarshi su Yaya Kabiru duk suka shigo
suka yi mata sallama, yaya Almu ne ya shigo a karshe
yana ganina a zaune ya ce, Ya ya haka ba za ki shirya
ba?" Na ce, 'Ai ban da ni." Ya ya maza ya ce, "Haba
24

Rabi shirya mana mu je ki yi mini rakiya." Na ce
mishi to.
Kasancewar wurin Baba za a je ya sa na yi
kwalliyar atamfa fara super ce tana da dan adon
furanni bakake jefi-jefi. Takalmin da na yi amfani da
shi shi ma baki da fari ne hakan nan jakar hannuna sai
na yafa farin gyaie na yi matukar yin kyau, sai daukan
ido nake yi, ga kuma kamshina na kowanne lokaci.
Na yi wa Umma sallama na fito na hangi yaya Almu
yana fitowa daga wurin Umma karama lokacin ne na
tuna yau ko gaisheta ban je na yi ba. Na same su a
waje dukkansu sun shirya dukkansu kwalliyar ta zarce
suka yi babu kuma wanda bai sanya hula ba a cikin
su, sun yi matukar yin kyau, amma zan iya cewa yaya
Almu daban yake kasancewar shi mai yawan amfani
da fararen tufafi, saboda ganin shi a cikin su bai
hanawa ka yi ta ganin kyan kwalliyar tashi ya yi kyau.
Yaya Junaidu da yaya Zubairu ne a gaba, yaya
Zubairu yana tuki, yaya Kabiru yana santar bayan
direba sai yaya Almu a tsakiya ni kuma ina gefen shi
ta jikin kofa. Ana tafiya suna hirarsu mafi yawancin
magangarta su akan aure ne da halaiyar mata na
tsananin kishi da rashin hakuri. Yaya Zubeairu yana ba
Su labrin abin da Umma Karama ta. yi wa Baba da
yanda ita da kanta ta nemi ya ba ta saki da kuma ya ce
ya ba ta sakin ta rude tana ta faman kuka.
To wannan wane irin abu ne naka? Yaya
Kabiru ya ce,
25

Eh ai su haka suke suna son abu suke nuna
wai ba su son shi a dole su ga masu jan aji.
Su ka dan yi dariya cikin jinjina lamarin, shi
kam Yaya Junaidu tsaki ya yi ya ce, "Ni fa ko dokin
auren nan ba na yi saboda na san wani nauyi ne kawai
zai hau kan mutum kuma ko daga kallon irin yadda
al'amura suke tafiya ma ai kai ka san su baba hakuri
kawai suke yi."
Yaya Almu ya karkato ya sunkuyar da
bakinshi ta wurin kunnena ya ce, "Ki ji mun Junaidu
wai baya dokin aure, saboda sai an yi hakuri da mace
ake iya zama da ita, shi ke nan yake jin haka ni kam
dokin nake yi ina zumudis cikin raina a kowanne
lokaci kuma kallon agogo nake yi ina ganin tafiyar
lokaci, ina kirga sauran awowin da suka rage a kawo
mini Uwale, kin san irin son da nake yi mata kuwa?"
Na girgiza kai nuna alamar ban sani ba.
Ya ce, "Uhm! To ko yau din nan sai da na
ganta wajen sau hudu, amma har yanzu ban gaji da
ganin nata ba, ji nake tamkar a bar mu mu biyu kawai
a daki mu yi ta maganarmu mai dadi in kuma na ji ina
ra'ayi in dan shafe ta in ji dadi."
Na ce, "To ai kai da zamanka ka yi a gidansu
kawai ba ka yiwo wannan tafiyar ba." Ya yi maza ya
ce. 'Eh kuwa to sai dai kuma na riga ai na fito, amma
dai bari kawai ba zan yarda a kwana ba yau din nan za
mu dawo, don in je in ganta da daddare." Ya dago ido
ya kalli Yaya Zubairu da ke ta faman tuki ya ce mishi,
26

"Kai Zubairu wannan irin tafiya da kake yi ni
fa sauri nake yi, don ba kwana zan yi ba, zan dawo in
tafi tadi."
Yaya Kabiru ya ce, To mu sauke ka mana ka
bi ta nan." Ya nuna mishi hanyar daji wai ya yi yanke.
Gaba daya suka kwashe da dariya, suka ci gaba da
zAncensu shi ma ya juyo wurina hannunshi ya miko-
yana taba makalallen dankunnen kunnena na asalin
azurfa, ya ce, "Rabi kenan ke kam kin iya kwalliya
har dan kunnen nan ma fari ne da ratsin baki ga abin
wuyan shi ma." Ya mika hannu zai ciro abin wuyan
daga cikin gyalena wai ya kara gani, karo, na farko da
na ji ba na son hakan na yi maza na hana shi. Cikin
hanzari ya daga hannun nashi daga jikina yana cewa,
"Uh! Gara in yi maza in koyi daina taba jikinki
kar wata rana Uwa ta ganni, don na san kishi za ta yi,
daga ganinta. To wannan fa na gamu da daidai da ni
ni kishi-kishi ya ya kenan?" Ya zuba mini ido yana
kallona cikin sauraro ban tanka mishi ba.
Ke kin san kishin Uwa kuwa?" Ya sake
tambayata, ,nima na sake yin kamar ba da ni yake
maganar ba, ya dan yi murmushi ya ce, "To ko da
yake dai babu komai tun da ina son ta kin san shi
namiji kan matar da yake so kamar bawa yake." A
Zuciyata na ce, kai ne dai hakan.
"Ai ni babu abin da Uwa za ta yi mini in ce
bana dokin aurenta, ko in rinka maganganu irin na
Junaidu ji shi ji abin da yake fadi." Lokacin ne na

27

Jiwo hirar da Yaya Junaidu yake yi na wani abokin sh
da wai saboda halaiyar matar shi, shi din ya daina
Zuwa gidansu. Yaya Almu ya kalleni ya ce, "Ni doon
irin su Junaidu sun daina zuwa gidana ni da Uwale ina
ruwana? Ban da kawai mu rufe kofa mu yi ta
sha'aninmu." Na kalle shi kawai cikin zuciyata na ce,
'Ai kai kam sai addu'a don ka riga ka tafi."
Jirgin sha biyu da rabi muka hau, don haka a
gida muka yi sallar Azahar. Bayan mun idar ne muak
sami Baba a falo shi da Umma Amarya, ta sha
kwalliya riga da siket wai Umma ta sanya tamkar
wata 'yar yarinya.
Baba yana cin abincin da Umma Amarya ta
gama shirya mishi a gaban shi ya kalle mu ya ce,
"Wannan wane irin zuwa kuka yi babu sanarwa, babu
komai ko kuma kin zo ne don ku cinye mini abin
dadin da Amaryata ta shirya mini?"
Gaba daya aka dan yi murmushi, sai yaya
Junaidu ya ce mishi, "Baba mun zo ne don mu baka
hakuri kan laifin..... " Kan ya karasa baba ya katse
shi.
"Kar wanda ya ce zai yi mini wata magana ko
ya ce zai ba ni hakuri, ba zan saurare shi ba tun da dai
ita uwarku ta ga abin da ya dace ta rinka yi mini
kenan, to mu je zubawa ni da ita."
Gaba daya aka sake shiga wata nutsuwar ni
kam kuka a kama yi. Yaya Zubairu ya kara rage
murya ya ce, "Baba, Umma kuwa mai gudun Bacin.
28

ranka ce, ko wani ta hango zai bata ma hankalinta
tashi yake yi."
Ya ce, Eh, amma kuma tafi kowa yi mini abu
cikin gadara ina abin da ya shigar da ita cikin
maganata ni da matata, ita auro mini ita? Ko ba
kwanan nan ne ta yi mini irin wannan abin ba na ce
mata kar ta sake shi ne yanzu ma ta sake? Saboda ta
raina ni, to hana ta tafiyar da kuka yi ni zan bar mata
gidan na shekara guda ko daurin auren ku ba zani ba,
su Yayan Tudu sa daura."
Kukan da nake yi ya tsananta sosai, na ce,
"Baba ka yi hakuri." Ya kalleni cikin bacin rai ya ce,
Haba Uwata a ce har yanzu ni ban wuce Umman ku
ta dauko hijabinta ta ce za ta bar mini gida ba, saboda
wani abin bacin ran da na mata ba?
Na ce, "Ka yi hakuri Baba ta san ta yi maka
laifi, ta ce mini ta yi maka laifi." Ya zuba mini ido ya
ce, Ta gaya miki?" Na yi maza na ce mishi,
'Eh Baba, ta ce mini ta yi maka laifi na kuma
San ba ta ji dadin abin da ta yin ba."
Ya ce, 'A'a ta ji dadin hakan da ta yi Uwata
tana sane da abin da take in ba haka ba ai kwanan nan
ne na ce mata kar ta sake yin hakan, ta ce ba za te sake ba."
Yaya Almu ya dan gyara zama ya ce, Baba ba
1a kwanan nan ba ne tun Rabi tana da shekaru hudu ne
abin ya faru."
Baba ya ce, 'Af! To yaushe ne? Yaushe ne aka
29

naifi Uwata? Ba kwanan nan ba ne aka haifeta, anan
gidan ne fa aka yi renonta. Aurena kuwa da ita uwar
taku ai ba na shekaru arba'in ne daidai, amma saboda
rikicin auren da ba a daura ba ta fito za ta tafi ana ba
ta hakuri, babu kuma abin da yafi komai kona mini
zuciya irin 'wuce ni da ta yi ina tsaye ai na fito ne don
ta ganni ta koma, amma ta wuce ba ta fasa ba, wato
bari ta nuna mini ni din me?
Yaya Kabiru ya ce, Ka yi hakuri Baba, Umma
ba za ta fadi haka ba ta dai yi maka ba daidai ba in
mun je gida kuma za mu gaya mata duk da ta sani ta
san ta yi maka laifi, kuma na san ta fi mu rashin jinn
dadi."
Baba ya dan yi shiru jimawa kadan ya ce,
"Abin da take gadara da shi kenan ta san komai ta yi
ba za ku bar ni in yi mata abin da ya dace da ita ba, ai
ya dace ta shekara ba ta ganni ba, in Maryam ta gama
kwanakinta ita Hajiya Karama ta zo ita kuwa ta yi ta
zamanta anan."
Yaya Junaidu ya sake gyara zama cikin
nutsuwa ya kalle shi ya ce mishi, "Baba ka taba ce
mana ba a biyewa mata."
Baba ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya ne
Junaidu ba a biye musu ku yi, ta hakuri da su, don
kuwa su din manyansu da yaran su halinsu duk daya
ne, yanzu ka duba ka gani irin gudun bacin ran
yarinyar nan da nake yi, amma ko a jiknta, ita in tayi
nishadi sai ta bata mini."
30

Jikina ya yi sanyi na yi zaton ko da ni baba
yake maganar. Na yi maza na kalle shi na ce, Ni
Baba?"
Ya ce, "Uwar ki dai ke kam me za ki yi ki bata
mini rai uwata?" Na dan sake kallon shi na ce, "Baba
yanzu ka ce auren ku shekaru arba'in kuma kana ce
mata yarinya? "
Ya ce, Yarinya ce uwata na mafi ganin
kuruciyar ta kan kowa, don kuwa an daura man aure
ne tana da shekaru bakwai. Wani irin aure da mutunci
da amana ya bani, amma wai kullum aka dan yi wani
abu sai ta zaro gyale wai ita za ta bar ni a ce ba ta ci
mutuncina ba?"
Na ce, 'Gaskiya Baba ba ta kyauta ba ka yi
hakuri."
Ya ce, 'To ya ya zan yi? Ya wuce."
Muka shiga hira sosai. Baba ya ce, "Za ku tafi
ne ko kuwa kwana za ku yi?" Na yi maza na ce, "Ni
dai kwana zan yi Baba."
Yaya Zubairu ya ce, "Mu zamu koma don mun
fito dukanmu ba mu bar kowa ba a gidan."
Baba ya yi maza ya kalle shi ya ce, "Abin da
nake yawan tunawa kenan, dukan ku za ku bar gidan
ko da yake dai ga wasu samarin nan su Hamza, amma
me kuke ganí?"
Yaya Kabiru ya ce, "Za su iya yin komai baba
a1 shi Hamza da Musa masu tsayawa ne kan al'amura
za su daidaita komai."
31

Ana waunan maganar yaya Almu ya yi mini
magana a hankali, "Ki dai san wannan zuwan na ki
rakiya kika yi mini, don haka ba wani kwanan da za ki
yi tafiya za mu yi, don ni ba zan kwana ba zan je gida
in je tadi, zan kuma gayawa Baba."
Na yi maza na ce, "A'a ina ruwana?" Baba ya
kalleni ya ce, "Mene ne Uwata?"
Na ce, "Baba Yaya Almu ne wai ba zan kwana
ba."
Ya ce, 'A'a a kan me? Shi ma ya kwana mana
in yana so, mene ne na sai ya sa ki kin tafi? Ai ni ma
ina son kwanan na ki sai mu yi hira ko?
Na ce, "Eh Baba."
Jin da na yi Baba ya co yana son kwanan ya sa
na yi niyyar yi mishi girki, don ya kara jin dadi. Ana
idar da sallar La'asar na shiga kicin na samu Umma
Amarya a ciki na shiga tayata aikin da take shirin yi.
Muna 'yar hira sai ga Yaya Almu ya iso kofar kicin
din.
"Rabi zo mana." Ban kalle shi ba, na ce, Girki
zan yi wa Baba."
Umma tana jin haka ta fice daga ciki, shi kuma
ya shigo, "Ke yarinyar nan kina so ki raina ni fa
kwanan nan in kinra ki ki ce ba za ki zo ba?"
Na ce, 'A'a to mene ne in na fadi haka kai da
kake murnar za ka samu matar da za ta raba ka da
yan'uwa duka? Ai har da haka zai kara sawa in
kwana, don in gayawa baba komai da komai, in yana
32

da abin yi tun wuri ya yi."
Yaya Almu ya zuba mini ido ya ce, "Ke ki ce
za ki zauna ne don ki kulla mini sharri, yaushe na
gaya miki haka? ta uwa ma wannan salihar yarinyar
yaushe za ta ce za ta raba ni da ku?"
Na ce, Ai ba ita ce mai raba kan ba, ra'ayin ka
ne hakan kana samun mata za ka rabu da 'yan'uwa."
Yay ce, "Tabdijam! To ai gara da na biyo ki
kicin din nan kin ga ai na ji irin kullalliyar da kike
neman ki kulla mini."
Na yi shiru na soma shirye-shiryen girkin da
zan yi ina harhada kayayyakin da zan yi amfani da su
ya matso kusa.da ni a hankali ya rada mini.
"Da gaske aure nake so Rabi, kamar in yi ya
ya? Yanzu na riga na girma son mace na ke kamar
me? Da kuma ba ta damen ba, don ni ko 'yan mata a
ban cika yi ba sai dai kawaye, amma a dan tsakanin
nan ni ka ina a tsorace da kaina nake, shi ya sa kusan
kullum ki ke ganina ina Azumi."
Na ce, "Uh! Yana da kyau."
Na ci gaba da aikina, shi kuma ya kara
matsowa jikina.
"In ban da sha'anin kima Rabi ai da na yi miki
wata magana."
Na ce, "Kamar wacce iri kenan?"
Ya ce, "A'a na gane kamar kin tsorata sosai
kan cewar da kika ce kin ji kamar baba ya yi na cewar
Zai hadani da ke aure.
33

Na yi maza na kalleshi na ce, Zan tsorata
manan hakan fa yana nufin tsakanin ni da kai akwai
wanda ba baba ne ya haife shi ba."
Hankalin Yaya Almu a kwance ya ce mini, "To
sai me in an yi haka? Ni inda na san wannan kawai
matsalarki ai da sai in ce miki ke ki rike baban kawai
na ki ne, ke kadai tun da kin fi ni tabbacin zama yar
shi ko ba komai ke Umma ce uwarki, yanzun nan ne
kuma baba ya gama cewa tun tana da shekaru bakwai
aka bashi ita, bayan haka ke kadai ce mai kama da ita
a gidan nan. Ni kuwa muan da yawa ni ina kama da
baba, Junaidu yana yi, Zubairu yana yi, Musa yana yi,
kin ga da sai duk ki maida mu 'ya'yan dangi kawai, in
ya so ni sai in zama surukin shi.'
Na ce, 'A'a ai kai ma Umma Amarya ce ta
haifeka."
Ya ce, "Ai wannan ba komai ba ne tun da ita
Umma Amarya ba budurwa ba ce, lokacin da baban
ya aureta."
Sai da plate din hannuna ya subuce kasa ya
tamutse, jin maganar da Yaya Almu ya yi mini. Bai
ku kara kaduwar da na yi ba sai kawai ya sunkuya ya
tsine fasassun tangaran din ya zuba su cikin dosbin
ya tawo ya tsaya kusa da ni, bayan ya wanke
hannunshi.
'Ashe Umma ba ta taba gaya miki ba? Ai ita-
Umma Amarya ta auri Baba ne bayan ta fita takabar
mijints na farko kin ga kenan in dai dan'uwanshi ta
34

aura ta can na samo kamannina da shi, kamar dai su
Junaidu kenan ko ya ya kika gani? Hakan bai yi ba?"
Nan da nan zuciyata ta shiga kai kawo cikin
tunani mai tsananin rudarwa a ce yaya Almu ba dan
Baba ba ne na cikin shi? Kai zan ji tausayin shi in har
hakan ya faru baki ne komai ba rabi nace kai yaya
Almu ace zaune kaima badin Baba bane na cikin shi
zanji tausayin shi in har hakan ya zai sance Baba yana
bakarar da hanziri jarumi mutumin kirki kamar ka
wanda zai yi alfahari dani wanda zai rinka daga ido
yana kallonshi yana ganin shi a matsayin wani alheri
da Ubangiji yayi yarda in kore shi in har zan iya yara
in kore shi daga jikinshi ince kai din ba nashi bane
don komai aurc ya halatta a tsakaninna da kai to na
zamo mai son kaina da yawa in kuwa zane kaina akan
Baba to banayiwa kaina adalci ba don haka muyi
zamanmu kawai ni da kai dukkan mu ya'yan shi ne.
Yaya Almu ya ce "Uhun Rabi ke nan ni a
wurina da ace dukkanmu na shi ne gara a yi in
wannan din, ke tashi ni surukinshi ai ya mallakmu
dukanmu. Ke 'yarshi ta cikinsa wacce matar deb slke
so ya ke girmamawa fiye da kowacce ta haifar rooshi,
ga ki mai kyau, Rabi don kawai kin yi sa'a kin dauko
kyau irin na Umma ke har ma kin so ki fita don kuwa
ke kam ai ko namiji ya yi tsayinki ya more ina jin dai
wurin Baba ki ka samo wannan tsayin naki, ga ki mai
kirki da kuwa kin gaji kirki Rabi kin san yawa kirkin
Umma da laherinta kuwa? Dubi irin shugabancin da
35

take yiwa Baba a gida yanzu ke a ganink ace ke
matata ce, za ki zama mun uwargida a gidana ki y
mun irin shugabancin da ki ka ga Umma ta na yi bai fi
mun

Please Login or Register in order to submit comment