Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Alhaji mai kyau ne, gashi dama
na riga na saba da aiki na kuam iya girkin ko da yake
baba Rabi tana cewa wai bai war girkin ne da ni, don
komai na yi mai dadi ne. Kullum zan gama girkina da
wuri in na gama in kai wa kowa na shi, na su Alhaji a
dauka a kai sashin yaya babba, don a can suke
haduwa su ci. Nima in je mu ci da matan gida bayan
na kai wa su baba na su. Muna gama cin abincin, zan
dawo in zo in juye ruwan wankana in yi, in yi
kwalliya saboda Alhaji ya hanani zama hira a cikinsu,
In ji shi wai duk sun haife ni bai yarda in rinka wani
hira da su ba, tun da dai sun ce mu ci abinci tare, to
muna gamawa in kwashe kwanuka in tashi. Hakan
nan kullum na gama girki in yi wanka don bai son
warin hayaki, na ce mishi to. Wadannan abubuwa.
biyu sai suka kara tsananta bakin jini na a wurinsu,
wai ba na zama a cikinsu na dauki kaina daban, gani
nake tamkar na fi su, bayan ni din ba komai ba ce in
ban da daure mini gindi da baba ya yi, ya fifitani akan
kowa, ya sa nake raina mutanc. Kuma wai'ni na cika
son miji fitina ce da ni, ba na barin shi ya huta kullum
ina makale da shi, don fitina ma wai kullum sai na yi
wanka da daddare. Kan wadannan maganganun na su
sai na rinka kin yin wankan dare, nan abin ya rinka
hadani rikici da Alhaji har rannan ya kai ni kara wurin
baba.
Na je wurin baban hira kamar yanda na saba yi
87

kullum, don ban taba fasa zuwa mishi hira ba. Kullum
zani mu yi hirar mu ni da shi da Baba Rabi, shi ma
Alhaji yana yin tashi hirar wurin yayanshi sai dai bai
dadewa in ya dawo ya dade yana jirana ban dawo ba,
in na shiga ya yi ta mita yana fadin zai dauki matakin
hanani barci a duk ranar da na je na dade wurin hirar
tun da ban san ya kamata ba.
Ina zaune muna hira da baba ita kuwa Baba
Rabi tana sude kwanon romon kaji da na kawo musu,
ta lashe hannunta ta mutstsuke su tare tana cewa,
To Alhamdulillahi Allah ka yi wa Bello
albarka ka yalwata mishi arzikinshi ka bashi ikon ciyar da jama'a."
Baba ya yi murmushi ya ce, 'Ita kuma mai girkawar fa?"
Baba Rabi ta ce, 'In Bello ya yi albarka ai ta yi"
Ya yi maza ya ce, 'A'a ban yarda ba, rinka yi mata tata addu'ar daban."
Ta yi dariya ta ce, 'To Allah ya wadata ta da hakuri ta zame mishi uwar iyali."
Ya ce, To amin." Ya kalleni cikin nutsuwa ya
ce mini, "Mijinki ya kawo mini maganarki ko da yake
bai gaya mini laifin da kika yi mjshin ba, nima kuma
ban tambaye shi ba, amma ya ce mini ba. kya jin
maganar shi kin fi jin tsoron matan gida akan gudun
bacin ranshi, haka ne?"
Na soma yin kuka. Baba Rabi ta ce, "Tana
88

nema ne ta zama sakarya tana nema ta biye waa
kazantarsu, kwanannan ba ka ga ba ta wanka ba?
Saboda suna cewa son miji ne yake sata wnakan
dare."
Baba ya ce, 'Ashsha! To ina ruwanki da su
Zuwaira? Mijinki kuwa ai shi kika sani abin da ya ke
so kuma shi ne abin yin ki, ki kuma guji bacin ranshi,
tun da shi ma yana kiyaye kan shi, ya kode a jikinki
kar kuam in sake jin ya ce mini ba kya jin maganarshi,
yanzun nan ma ki tashi ki je ki yi wanka, kar kuma ki
dawo mini hirar sai gobe da safe, don nima kwanciya
zan yi in ban da sakaran namiji wa zai yarda da mace
tana dankon kazanta? Me mijinki ya rage miki da ba
za ki yi mishi yanda yake so ba?
Na dawo dakina na yi yanda Baba ya ce mini.
Na gama shafa ina kokarin sanya sabbin kayan da na
fito da su, sai ga Alhaji ya shigo cikin murmushi ya
ce, To sa kayan me kuam za ki yi yanzu da daddaren
nan?" Ban kula shi ba, zan ci gaba da sanya rigata ya
yi maza ya kulle kofa ya iso gare ni.
A wannan lokacin ne na samu kaina cikin wan
yanayi na rashin jin dadi, kowanne lokaci ina kwance
ba ni da kuzari ga barci komai ban iya har salla ma.
Kowanne loakci Alhajis a cikin nata yake.
'Wai ke me ya same ki ne?
Kullum tambayar shi kenan In ce mishi ban
sani ba, ba na dai jin dadi kawai. Ya kalleni cikins
nutsuwa ya ce, To ko dai kina yawan tunawa da Baba
89

ne tun da dai ni ban ga alamar rashin lafiya a tare da
ke ba, kin ga yanda kika kara kyau kike wani sheki
kuwa?" Na ce mishi ba na zaton tuanwa da Baba ne
tun da dai ai ban taba ma mantawa da shi ba, kullum
ina yi mishi addu'a. Ya ce, To bari nan da kwana biyuu
in bai daina yi miki ba zan san abin da zan yi a kai, ni
in banda tsoron su Baba ma ai da asibiti na kai ki. To
sai su ce mene ne dalilin zuwa asibitin?" Na ce haka ne.
Sati biyu bayan wannan lokacin ya dawo gida
ya zo ya same ni na yi kuka har idanuwana sun
kumbura ko abincin dare rannan ban fito na dora ba.
"Lafiya dai na same ki a haka?"
Ina kuka na ce mishi, "Wani abu ne yake yi mini motsi a ciki."
"A ciki?" Da sauri ya yi tambayar na ce mishi,
Eh." Ya nemi wuri ya zauna ya dora hannu a
cikin nawa yana kokarin jin motsin da na gaya
mishin, sai kuwa ya ji. Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce,
"Anya kuwa ba ciki ne da ke ba kuwa Zuwaira? Kin
ga fa tun da kika yi al'adar nan sau daya ba ki sake ba.
Sannan gashi yanzu cikinki yana motsi ina ji mutum
ne don in ciwo ne ai ba zai yiwu ki yi kiba haka ba."
Na zuba masa ido ina kallon shi, ya ce, "Ko
kuam bari in je in gayawa Baba in ji abin da za ta ce."
Na yi maza na ce mishi, "A'a kar ka gaya mata
bari in je in dora girkina, murhu biyu zan yi yanzu zan
gama." Ya ce mini, To yi sauri don akwai wani

90

labarin da nake son baki, amma sai kin yi wanka kin
shafa jan bakinki tukunna."
Kwana uku ne kawai bayan nan na gane ashe
dama su Baba da Baba Rabi sun san ciki ne da ni,
shiru dai kawai suka yi suna kallona. Wanki na zo
karba wurin Baba Rabi, kamar yanda na saba yi in zan
yi nawa in hada da nata. Sai ta ce mini wai a'a ita ta
yafe wankin nan, yanzu in ji da kaina kawai za ta
rinka yin kayanta, in ya so in Allah ya sauke ni lafiya
na gama jego na yi mata.
Daga ni har Alhaji kunya ce ta kama mu shi
kam mikewa ya yi ya bar dakin, ya bar ni ina mutsu-
mutsu. Baba kuwa ya yi ta yi mata fada, yana fadin.
Wannan wane irin girma ne, ba dama ki ce
mata kin hutar da ita wankin kawai sai kin tsaya yi
musu bayanin dalilinki."
Ban san lissafin ciki ba, gani dai kawai na yi
baba ya tara lodin itace a bayan kicin, har sai da ya
kere tsawon kicin din.
Rannan ina hira ni da Baba da Baba Rabi,
Alhaji ya shigo ya tsugunna ya gaishe su. Dabarar da.
ya gano kenan wai in ganshi zai wuce daki, baba ya
kalleshi ya ce mishi, "In watan nan ya kare Zuwaira
za ta dawo dakin uwarta don kar haihųwa ta zo mata
cikin dare ba ta sani ba."
Alhaji ya sunkuyar da kai kasa ya yi shiru ya
ki amsawa. Ya sake tambayar shi, "To ko za a bar
maka ita ne tukunna?"
91

A nutse ya amsa mishi, 'Eh."
Baba ya ce, "To me za ta yi maka?"
Baba Rabi tana dariya ta ce, "Ka ji mini malamn
shi da matarshi ka tambayeshi me za ta yi mishi?"
Ya ce, To kar in ji na gaya maka kar ka yarda ka matsa mata.
A haka muka yi zamanmu ni da Alhaji, komai
a nutse yake aiwatar da shi, nima kuam na riga na
fahimci mijina bai samun wata matsala a tare da ni,
don haka hankalinshi a kwance yake, gashi bai ganin
girman cikin nawa don gaba daya yaki fitowa.
Wannan dalili ya sa ko na nemi bijire mishi, bai
daukan atakure nake, sai ya dauki matakin yin
rarrashi da bada hakuri.
Rannan cikin dare tun yunkurin da na yi na
baro mishi shinniidar shi in dawo tawa in kwanta.
Bayana ya amsa gaba daya wani irin kidimammen
ciwo ya kamani hankalin Alhaji ya yi mummunan
tashi, don gani yake tamkar shi ya jawo mini ciwon ya
yi yunkurin zuwa kiran Baba Rabi, ya kasa saboda
tsoron kar su gane an yi wani abu ne ya sa ciwon ya
tashi. Nima a tsoracen nake don haka na ce mishi ya
barta kawai, na yi ta fama in mirgina nan, in mirigina
can. Shi kuwa sai faman kamo ni yake yi, .yana ta
kuak tare da yi mini alkawarin daga yau ba zai sake
kula ni ba.
Zuwa can dare ya yi nisa sosai, na rude, na
kidime na yi zaton mutuwa zan yi. Na kalleshi cikin
92

rawar jiki da rawar murya na ce mishi, 'Wani abu zai fasa jikina ya fito."
Da sauri ya sake ni ya yi waje da gudu kiran
Baba Rabi. Ya tafi kafin su dawo har abin da ke son
fitowa ya fito. Na yunkuro ina kokawa don in ga ko
mene ne saboda ban yi zaton haihuwa na yi ba, sai ga
su sun shigo daidai yaron yana atishawa. Nan dan ya
kyanyara kuka. Baba tana salati tana fadin,
'Ai haihu ta yi ga yaro nan, ga yaro. "
Ta sa hannu ta dauke shi. Nan da na aka taso
matan gida aka fito da ni daga dakina aka'kái hi dakin
Baba. Bayan an hura wuta a dakin na hau gado na
kwanta, gani nake tamkar ba haihuwar na yi ba, sai
zazzaro ido na ke yi ina kallon mutane. Ina jin matan
yayan Alhaji suna cewa ai da an bar ni a dakina
kawai, don su ba su ga amfanin daukonin ba. Wata
ma har tana cewa kin ga yaron kuwa kafin a wanke
shi ai duk jikinshi kazanta ne, ba su rabu da juna ba
har ta haihu. Ni dai na yi lamo na rufe idona kamar
ina barci, nan kuwa ba barcin nake yi ba. Cikin
zuciyata dai tsoro nake ji kar ita ma baba Rabi ta gane hakan ta yi muni fada.
Farin ciki wurin Baba bai misaltuwa, sai kawai
da kawowa yake yi, sau goma ya shigo gidan nan sau
goma zai tambaya Zuwaira kalau ko? A ce mishi
kalau dinta. Ya ce to shi wannan mutumin su? A ce
mishi shi ma kalau din shi. Ni kam ko kałon yaron
ban yi ma saboda kunya, sai dai na ji baba Rabi tana
93

yawan cewa wannan da da karanbani yake wai shi
kuma da malam yake kama. Wannan al'amari ya yi
mata dadi, don duk wanda ya zo barka in ta mika
mishi yaron sai ta gaya mishi gashi nan karambana ya
tsallake iyayen shi kaf bai dauko su ba sai ya dauko
mini mijina gata daya, sai a yi dariya a ce to baba ai
shi ne mijin na asali. Ta ce a'a, a'a mijin kazanta dai
ko.
Alhaji ya kan yi kokarin shigowa wurina a
dakin Baba Rabi da Asuba lokacin da takan zauna
gaban wuta wai kar ta rika mutuwa, sai turoni dan ya
tafasa tukunna. A duk lokacin ya shigo zubawa yaron
indo yake yi yana kallonshi.
"Dan miko mini shi nan."
In ce mishi, 'A'a idan baba Rabi ta shigo ta same ka fa?"
Sai ya dan yi waiwaye ko zai ganta tana zuwa
in bai hangota ba sai ya yi maza ya dauke shi ya dan
jujjuyashi ya maida shi ya kwantar, sai ya kallen ya ce
mini, "A gadona zan rinka kwanciya da shi mu bar ki
a na ki gadon, don kar ki zo ki danne shi garin wannan
wawan kwanciyar na ki."
In ce mishi, 'Ai ma kafin in dawo ya girma Baba Rabi ta kar6e shi."
Ya zaro ido yana kallona.
"Wai nan wankan bangali kike yi ne?"
In ce, 'Eh mana.
Ya ce, Kai ba yarda zan yi ba, na san abin da

94

Zan yi ai lokacin da zan bukaci dawowarki ya yi."
Ranar suna Baba ya radawa yaro suna Aliyu,
takwaran Babana kenan. Ni kaina cikin zuciyata na yi
murna. Tun da aka yi suna kullum aka yi mishi wanka
aka sanya mishi kayan shi wurin baba ake kai shi ya
yi ta barci, har sai ya farka Sannan a dawo da shi a ce
in ba shi nono.
Satinmu uku rannan aka tashi baya kama nono
ya sha, cikin shi ya kumbura, har ya haura kan
kirjinshi sai nishi yake yi daidai, alamar dai baya
cikin hayyacinshi. Hankalin su Baba ya yi matukar
tashi su jika wannan su bashi, su jika wancan su ba
shi. Ni kam ina kwance har ma barci ya daukeni.
Tashina aka yi daga barci na ji Baba Rabi tana
fadin magana cikin kuka.
"Dama zuwa ka yi mu ganka ka koma?"
Na shiga dube-dube don jin maganar tata da
kuma hakurin da ako ta ba ta. Lokacin ne na hango
yaron shimfide a tsakar daki a Rasa an nade shi cikin
zaninta, baba ya zo ya tsaya a bakin kofa ya ce mata,
"Miko mini shi nan."
Ta mika mishi shi suka tafi, ita kuma ta kara
tsananta kukan da take yi Shi kan shi Alhaji kasa
hadiye damuwar shi ya yi kan rasuwar yaron, har na ji
baba yana ce mishi, "Sai ka yi hakuri wannan sai an je
can za'a more shi, haihuwa kuma ai soma ta kuka yi."
Ni kam na hadiye babu wanda ya gane
damuwata, sai dai kuam na shiga wahala ga ciwon
95


nono, gashi a yanzu ruwan zafin da ake kwara mini
safe da yamma kona ni yake yi, ba na son wankan ba
abin da nake so irin a ce an gama wankan nan, gashi
kuam sai na jiwo magana cewar wai ai arba'in biyu
zan yi, hankalina ya yi mummunan tashi da jin hakan.
Rannan Alhaji ya dawo daga kasuwa da
yamma ya shigo wurina ya zuba mii ido yana kallona cikin tausayi.
"Daga gobe dai za ki huta da wahalar wankan
nan tun da gobe ne arba'in din."
Na kalle shi cikin nutsuwa na ce mishi, "Ai
arba'in biyu, aka ce zan yi." Ya sake kallona ya ce,
Har da babu yaron ma Zuwaira ba za a tausaya mniki
ba? Kin fa rame." Ban tanka mishi ba ya juya ya fita.
Ban san me ya faru ba, ko kuma me ya yi? Illa
dai kawai na ji baba yana cewa Baba Rabi, "Ke Rabi.
ki baiwa yaron nan matarshi ki bar wankan nan haka,
watakila wani rabon ne mai tsanani ya kori wancan
kin ga ya gama zagaye-zagayen shi ban kulashi ba, to
jiya ya fito fili ya yi mini magana ya ce a yi hakuri a
bar wankan haka."
Baba Rabi ta ce, "To ai ba bta gasu ba."
Ya ce, "Eh maida mishi da ita in ta sake wata
haihuwar kya hada gaba daya ki. gasata da kyau,
anma yanzu yana ganin babu dan ai ba zai iya hakuri
ba."
Kememe baba Rabi ta yi ta ce ba za ta maida
ni ban gama wanka ba, ai in na zo wata haihuwar sai
96

in rinka kumburi, jikina ya danyace. Ya ce, "To babu
laifi Rabi rike ta ku zauna."
Alhaji ya maida dakin Baba Rabi ya zama nan
ne wurin zaman shi yana fitowa daga sallar Asuba na
zai zo ya zauna in an ce in fito a yi mini wanka ya
ringa tsaki kénan yana cewa, "Ke ba za ki rinka yi
mata kuka a wurin wankan nan ba, don ta san wahala
kike sha?" In yi kamar ban ji shi ba. Da daddare ma in
ya fito daga wurin yawonshi nan zai zo ya zauna suna
hira shi da ita, tun tana amsa hirar har ta koma
gyangyadi sai jifa-jifa ne za ta rinka amsa abin da
yake gaya mata, ni kuwa in yi ta barcina.
Rannan ina jin baba yana cewa mata, Ai
maganinki kenan duk inda kika dan zauna ki kama
gyangyadi, saboda ba kya samun barci ga tashin
Asuba, wannan dogon hirar da Bello yake yi miki ai
ke ma ma kin san abin da take nufi da matarshi take
dakinshi kina ganin shi ne a dakinki da daddare?".
A hakan sai da ta yi mini wankan wata biyu
safe da yamma. Sannan ta sa aka gyara mini dakina
fes aka wanke mini kwanukana da tasoshina aka sake
jere daki ya yi ras. Da Alhaji ya shigo mata hira da
daddare ranar ta ce mishi "Ba ni wuri barci zan yi
gobe war haka in ka dawo za ka samu matarka a
dakinka."
To haka aka yi na dawo dakina ina tare da
mijina muna zaune lafiya, babu wanda ya taba sjin
tsakanin mu akan wani sabani. Yana matukar sona,
97

yana matukar kyautata mini kowane lokaci idon shia
kaina yake, ga iyayenmu da ke matukar sona suke
kaf-kaf da al'amurana. Sai dai shiru babu ciki, babu
alamar shi. A wannan lokakcin ko atishawa mai karfi
na yi sai Baba Rabi ta ce ai ina jin juna biyu ne da ita,
saboda tsananin matsuwarta da son ta ganni da ciki.
Nan da nan sai ga ta ta shiga yi mini jike-iiken
sauwowi, wai maganin haihuwa. Shi kuwa Baba sai
ya ce mata, "Da kin yi hakuri ita haihuwar nan inta
tashi zuwa ai za ta zo da can saiwa aka ba ta?
Alhaji da kan shi ya soma matsuwa da son
ganin na haihu, dan kankani abu ne zai faru sai ka ji
yana cewa da yanzu yana nan da an yaye shi, ga shi
har yanzu shiru me ya faru ne? In yi shiru kawai in
sunkuyar da kaina ina sauraron shi, sai kuam ya ce,
na ganin har da raba shimiida da kike sawa muna yi
daga yanzu ba zan sake yarda ba."
Yayin da Alhaj! yake wadannan maganganun a
daki su kuma matan tsakar gida cewa suke yi ai ita
mace in ta cika mannewa miji ma haihuwa gagararta
take yi. Da na gaji da irin fitinarshi sai na ce mishi da
ka dan rinka barina ina hutwa, saboda ga abin da su
yaya suke lada. Ya ce, 'Rabu da su ba su san komai
ba, kar ki rinka zama a wurin hirarsu." In ce mishi to.
A wannan lokacin ne Alhaji ya zama saurayi
sosai, ya kuma hada karfinshi wuri daya ya murje ya
yi kumari, kwarjininshi ya soma bayyana sosa1, kyan
Sar ya kara fitowa, gashi ya Soma samun barka sosai,
98

kasuwa ta bude mishi ta ko'ina, duk abin da ya taba
sai ka ga alheri ne ke ta faman shigowa fiyc da yanda
aka yi zato. Ni kaina yanzu ne ya dacc a ce na zama
budurwa shekaruna goma sha bakwai ne, na yi kyau
har ba a magana, na riga na san dadin mijina yanzu ne
na kara fahimtar auren sosai, in muka shiga daki ni da
Alhaji mu kadai mu ka san abin da ke faruwa, shi
kuwa Alhaji dama zani ce ta tadda mujemu don haka
da rana ma barin kasuwa yake yi ya taho gida duk
lokacin da zai shigo kuwa ba zai shigo haka ba, sai ya
riko wani abu ya ce "Raba ki kaiwa su Baba da
mutanen gida ke ma ki dauki naki."
A wannan lokacin dakin Baba da Baba Rabi
bai rabuwa da naman kaji soyayyu a ajiye hakan ai
hanawa kullum ya zo da wadanda za a yi musu
farfesu, ga zuma a ajiye, ga yaji da manshanu. Kullum
Baba Rabi ta gama cin abincinta in tana lashe yatsa za
ta ce, "Ubangiji ka yalwatawa Bello arzikinshi don ay ciyar da jama'a."
Muna cikin wannan hali ne kawai baba Rabi ta
kamu da zazzabi ko a jikina ban damu ba, don ta saba
yin rashin lafiya irin wannan tana warkewa, don haka
na dauki matakin kulawa da ita kawai, kamar yanda
na saba. Na kai mata ruwan wankanta na riketa na ka
ta ta yi na rikota na dawo da ita dakinta. Bayan ta
yiwo alwala muka dawo daki ta kwanta, na gyara
mata ruhuwa na je na kawo mata gaurwáshin wuta na
Zauna 1na dama mata furarta ina shirin ba ta sai na ji ta
99

kama shakuwa mai karfi, da sauri na dago ta ganin
halin da take ciki ya sa na yi maza na maida ita na je
kira Baba muka shigo tare na sake dagota na
rumgumeta ya zuba mata ido yana kallonta hawaye
suka zubo sharrr! Daga idanuwanshi. A hankali ya ce,
"Ashe haka za mu yi da ke ke ma Rabi? To Ubangiji
ya baki sa'ar tafiya, sai na zo."
Yana fadin haka ya soma shafa mata ruwa,
yana salati yana nanatawa, har ita ma ta kama yi.
Zuwa can sai ta yi shiru.
Baba ya yi ajiyar zuciya mai karfi, ya yi
kalmomin godiya ga Ubangiji da nemar mata rahama
ya kalleni ya ce mini, "Shi kenan Zuwaira Rabi ma
tabi bayan yan'uwanta su duka ukun sun tafi sun bar ni. "
Rasuwar Baba Rabi a gidan nan ba karamin
al'amari ba ne a gidan nan. A wurina dai rasuwarta ita
ce ta sankar da ni yanda dacin mutuwar mahaifiya
take. Ko kwana arba'in da matuwarta ba a yi ba aka
ware ni a gidan, ba ma shiga harkata, babu mai
magana da ni. Maganganu iri-iris suke yi ta fitowa
ciki har da haihuwar da na yi ni kadai a daki ban kira
su ba. A ka'ida kuma wai uwar gidan yaya babba ake
kira in ana nakuda sai kuma ta kira sauran matan da ta
zaba su zo su kewaye mai nakudar, ita Baba Rabi a
kan je ne kawai a gaya mata an yi haihuwar amma ni
da mijina ba mu yi haka ba. Wasu suka ce to in dai ma
namiji ne ai alkawarinshi ragagge ne muna nan da ku
100

zai yi mata kishiya sai kuam mu ga tsiya, tun da tana
zauni ita kadai ba ta kama mu ba, ai kishiya ba za ta
zo ta cc mana ta san da mu mu yarda ba. A wannan
lokacin ne na gane Baba Rabi ta tare mini abubuwa da
yawa a gidan nan.
Ni kam ina jin su ba na kuam ta tasu, na maida
hankalina wurin baba, wanda ya rasa lafiya tun bayan
mutuwar matarshi kowanne lokaci ina tare da shi, ina
yi mishi hidimominshi ko in taya shi hira ko shi
Alhaji a wannan lokacin nan wurin nashi yake hira.
Koda baba ya watstsake nan wurin shi muka
mayar da hira da safe da daddare, nima na maida kicin
din baba Rabi wurin aikina, saboda yafi kusa da
wurinshi ina aikina muna hirarmu, don fito mishi da
shimfida nake yi a inuwar bishiyar da ke nan sashin,
sai na zama in ba Alhaji ne ya dawo ba ba na zuwa
sashin da nake, saboda ba na wani jituwa da wadanda
muke taren. Kullum dai baba ya kan gaya mini,
"Kar ki yarda ki tanka musu duk abin da za su
yi miki nan in da kike ganinsu babu wacce ba ta
haifcki ba, in ban da Bilki." In ce mishi to Baba.
Ana cikin haka ne aka wayi gari daurin aure da
safe a gida, ashe wai kanin Baba mai binshi ne ya bai
wa Alhaji auren yarshi bisa hujjar wai ni din ba mai
haihuwa ba ce. Ran Baba ya yi matukar baci da jan
maganar tasu ya ce da ba shi auren kawai aka yi aka
yi shiru da ban ji takaici ba, amma a ce Zuwaira ba ta
haihuwa? Ai ta haifu ba a bar mata ba ne. Yana
101

maganar cikin hawaye ya kalleni ya ce mini,
"Kar in ji kar in ganni, kar ki yarda in ji kin yi
wa miinki wata magana, wannan auren da kike gani
an dade ana son bashi Rabi ta yi uwa ta yi makarbiya
ta ki yarda, don haka ki yi hakuri ki daure ki bai wa
mara da kunya." Na ce mishi to baba.
Umarnin da baba ya bani na in zuba ido shi na
bi na yi matukar kokarina wajen cire auren daga
raina, duk da tsananin kishin da ke damuna babu halin
in ga ya shiga dakinta sai in rinka ganin tamkar shi
kenan abin da yake yi mini ita ma shi yake yi mata,
bisa wannan dalili sai zafin kishi ya ringaye ni, na
shiga yi mishi rowar kaina, na bijirewa duk wani
rarrashi nashi, gashi kuma dama mutancn gida gaba
daya suna tarc da amarya ne, ita yar dangi ce ko ba
haka ba ma dama sun riga sun kosa su ga an yi mini
ita. Sai na zama ba ni da wani abokin mu'amalla mai
dadi sai baba. Bisa wannan al'amari sai Karama ta yi
amfani da abin da ta gani na juyawar Alhaji wurinta
de goyon bayanta da takc da shi wurin dangi duk ta ki
yarda ta marawa kokarina na ganin mu zauna lafiya.
Ana cikin haka sai aka ce wai tana da ciki, gaba daya
gida ya dauka matar Bello juna biyu ne da ita, ko
bako ne ya zo sai an gaya mishi, in aka gani a wurin
ma an fi tsananta bayanin.
Rannan ina zaunc gaban Baba kuka nake yi,
Kuka kuwa ba na wasa ba, saboda na fara gajiya da
ganin abin da nake gani. Rarrarshina yake yi yana ba
102

ni hakuri. Da ya ga na yi shiru sai ya kalleni ya ce
mini,
"Ashe ba ki da hakuri ban sani ba? Ai ita
rayuwa babu abin da ya dace da ita irin hakuri. Ashe
ba za ki iya zuba ido ki kalli Bello da mutanen nan ba
ko da na shekara

Please Login or Register in order to submit comment