Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ace ubanmu ne daya za a daukeki a baiwa wani
ina kallo ba?"
Na ce "Kai Yaya Almu mu bar maganar nan
kawai, tana sawa gabana yana faduwa, zuciyata tana
harbawa da sauri."
Ya yi maza ya ce "Uhm to gara mu bar ta, bari
mu yi wata me sunan wannan abincin da za ki yi
mana? Na cc mishi "Stuffed chickcn onc" Na yi mishi
lakabi da "one" din ne don zan iya yi maka su kala-
kala don haka ran da zan sake yi maka wani zance
maka stuffed chicken No 2, don in bambance maka
su, ya saki wani irin lallausan murmushi ya ce ai na
yarda da ke Rabi na san ke gwanar girki ce na kuma
san za ki iya tattalin mijinki za ki iya tarairayarshi ki
reneshi in na zauna na yi tunani na tuna tsananin
kwadayina game da shimfidata sai in ga to ina ma dai
ke ce wacce zan rinka shimfidewar? Kin sanni ina son
mace mai sura irin taki, ina son komai naki Rabi ina
Son duk wani yanayi naki in da za ki yarda da
shawarar da na kawo da kin yi mamakina da kin ga
irin tarairayar da na yiwa shagwabarki."
Na yi ajiyar zuciya mai karfi na ce Yaya
Almu ka yi hakuri ka san ban saba yin irin wannan
maganar da kai ba."
Ya cc "Gaskiya ne Rabi gaskiya ne, to koya
36

mun girki in mutum zai yi stuffed chickcn one, me za1
bukata? Na soma yi mishi bayani cikin sauri don ban
son ya sake kawo wancan hirar tashi na ce mishi
dankwalcliyar kaza katuwa kamar wannan ya ce na
ganta, na ce to ga nama cikin cup madaidaici, butter
cokali shi da na ture wadannan gefe na sake jawo
wani hadin na shiga nuna mishi na ce sai kuma
wannan naman saniya cup daya da Rabi ferarreen
dankalin turawan da aka yanyanka shima cup daya
madaidaici ga butter cokali takwas, murmushi biredi
cup daya, kwat guda biyar sai albasa guda biyu suma.
Ya ce To amma Rabi wannan irin girki naki
ba zai saki kiba ba?"
Na yi murmushi na ce "Ai kuma na iya abincin
rage kibar iri-iri."
Ya cefo mu yi magana gaskiya Rabi kin san
ba zai yiwu ina kallon alheri da idona kuru-kuru in
barshi ya wuceni ba, ni fa gaskiya na fi so ki zama
matata ni bana son yin kanwar da ke in kima bukatar
yayu ga su Zubairu nan ga su Junaidu da su Kabiru ke
har su Hamza da su Musa sun gimeki ki yi dasu, ni ki
bar ni kawia in zama mijinki uban 'ya'yanki, ki haifar
musu masu yawa, ki yi musu tarbiyya su zama
mutanen kirki na cc a'a.ba za a yi haka ba kai, dai ka je
ka auri Uwalenka, nima in auri Mustaphan wurin
Itinmu yallabai dama ni ina son shi don ina sha'awar
tebarshi tana ba ni sha' awa ka sanni ina cikin maie
masu girmama teba da ganin darajarta be zan iya
37

zama da wanda ba shi da ita ba.
Nan da nan na ga Yaya Almu ya tsuke fuska
alamar zuciyarshi ta so su shi kuwa na yi maza na
koma kan aikina na kamashi gadan-gadan na dauko
turmin karfen da na riga na wanke na kife don ya
bushe shi da tabaryarshi na zuba naman nan na soma
dakashi tare da ferarren dankalin nan sai da ya yi
laushi tukuna na kwasheshi cikin wani kwanon silba
mai dan fadi na juyre murmushen biredi akai da
kayan yaji da yankakken albasa na sa kwai da ruwa
cokalin cin abinci guda biyu na cakudasu da kyau
sannan a dauko dankwaleliyar kazar nan da ba a cire
komai a jikinta ba sai kai da kafafuwa na yi ta cusa
kwababben naman nan a cikinta sai da na cikata tam
ta yi matukar yin nauyi sannan na kawo zaren lilo na
daurcta da kyau Yaya Almu yana bayani ta hanyar
rike mun ita sannan na kawo blucband na yi ta
mulketa da shi kafin na bude 0ven na sakata a ciki ta
soma gasuwa na ce m1shi minti arba'in da biyar za ta
yi a wannan wutar don haka bari in yi wannan hadin
ka gani ya ce mun to.
Na dora wancan naman cup daya na yi mishi
hadin farfesu mai ruwa sosai na zuba kayan hadi su
kayan kamshi shima na rufe sannan na koma na sake
shiryawa Baba abincin darenshi na ka'ida tawon
laushi miyar yauki na tuka mishi tuwon alkama miyar
busasshiyar kubewa, na dawo kan kazar nan na ce wa
Yaya Almu ai ka ga bayan minti arba'in da biyar din
38

nan na sake rage wuta ta yi kasa sosai na tsawon minti
talatin ya ce Eh na gani na ce to yanzu komai ya
kammala bari in cirota ta gani na ciro kazar ta yi shar
gwamin sha'awa sai wani kamshi ke tashi daga cikinta
na juye farfesu a kanta cikin kwanon dana sanyata mai
kyau na' kawo murfi na rufe. Yaya Almu ya ce bari in
kai mana wannan ke kya taho da sauran. Na ce mishi
to.
Na shiga falon, na samu Baba yana tambayar
Yaya Almu kai ka yi sallar Magariba kuwa Lamido?"
Ya ce "Eh Baba itama mai girkin ai ta yi balle
ni na bi ku sallah ana idarwa ne dai na fito ban tsayya
ba." Na isa wurin ajiye abinci na ajiye kwanukan da
na zo da su kamshi ya gauraya ko ina Baba ya kalleni
cikin murmushi ya ceUwata in kina mun irin
wannan liyafar a za ki sa in fasa yin bikinki a bana ba
kuwa?"
An zauna gaba daya ana cin abincin rana cikin
raha, Baba ya sakc cewa da can duk tsawon lokacui
uwata ta iya irin wadannan girke-girken amma ba ta
ciyar da danta da su ba ta boye abinta sai ta je gidan
mijinta ta yi ta shirya mishi gara, miji ya fi uba ne
uwata?
Na kalleshi cikin ladabi na ce mishi "A'a Baba,
ya yi maza ya ce "A'a ya fi miji ya fi uba daraja uwata
don kuwa shi ta dalilin biyayyar da ki ka yi mishi ne
za ki shiga aljanna, uwarki ba ta taba gaya miki haka
ba?"

39

Na ce Ta taba." Ya ce "Yauwa to ita ai mai
girmama aurenta ne."
Na idar da sallar isha'i, bayan na yi wanka sai
na zauna na yi kwalliya bayan na gama shafe jikina,
na gyarashi yanda ya kamata, doguwar riga har kasa
na sanya na wani yadin material bluc, Umma ce ta zo
mun da yadin daga Dubai tsawon rigar ta sanya har ba
a iya hangen siket dinta dake jikina, wuyan rigar an yi
adon zare dan kadan na daura dankwalin a kaina
sannan nakawo sarka da 'yan kunne bluc da warwaro
da zobe mahadinsu na sanya, farin zaren da aka ratsa
da blue wajen yiwa wuyan rigar ado ya sa na yi
amfani da farin gyale dan siriri sosai na sanya farin
takalmi da jaka na kara fesa wani turen na yi matukar
yin kyau na fito na shiga dakin Baba inda duk aka
hadu ana ta hira na je na zauna kusa da Baba a kasa
sai dai ban tsoma baki cikin hirar tasu ba, ian dai ji ne
kawai don ta yi mun kama da hirar manya da suka
gama ne yaya Junaidu ya yi wa Baba sallama ya ce
mishi za su tafi, za su bi Jirgin karfe goma.
Baba ya yi musu addu'a, suka yiwa Umma
Amarya sallama suka fita. Yaya Almu ya ce mun zo
mu je ki rakani mu kaisu airport mu dawo.
Baba ya kalleshi ya ce "Kai Lamido ba ka ce
gobe kana case a court ba ne, ya ce eh zan yi
Sammako in tafi ya ce to shi kenan ke uwata tashi ki
rakashi, na bi bayan Yaya Almu wanda shima ya sha
kwalliya cikin farin boyel.
40

A hanya muna dawowa ya dan wiawayo kadan
ya kalleni ya ce mun "Ina son ki fa Rabi kin san ai ba
zai yiwu in yi ta yi miki haka-haka ba, ko? Na ce "E
to haka ne amma ai ka san ni kuma da wuya in yarda
ka san mene ne so?"
Da sauri ya tambayeni don me? Ina da shekaru
talatin a duniya ki ce mun ban san so ba? N acc to
kwanan nan ka gama son Aina'u har kana zama kana
rera mata wakoki kana siffantata da siffofin ban
mamaki kace wai kai a haka kake ganinta a irin son da
na san kana yi mata, ni na dauka in ba a baka ita ba
suma za ka yi ta yi sai na ga ka shanye kemadagas ko
a jikinka sai ka koma son Uwalen da aka ce za baka
ko yau da safen nan akan sonta ka ke shi ne nima
yanzu za ka ce kana sona?
Ya ce "E ai ina sonki din ne."
Na ce "To kar ka sake gaya min haka abin da
na sani shi ne kai wana ne ubanmu daya don haka ni
ban taba yin wani tunani game da kai ba, yallabai
kadai nake so shi ne yake bani sha'awa tebarshi kuma
tana burgeni tun ba in naga ta turo cikin babbar rigar
nan tashi ba."
Yaya Almu ya buge mun bakina da karfi da
bayan hannunshi na sa hannu na taba labban nawa na
ga jini don haka da karfi na rinka kurma mishi ihu har
muka iso gida ban yi shiru ba yana tsayawa na bude
kofa na fito ban saurari maganar da yake yi mun na
nufi falon Baba ina ihu ga shi na yi sa'a labban nawa
41

sun kukkubura shi kadai na smau a ciki na durkusa
gabanshi ina ihu ya zubawa bakin na wa ido yana
kallo. "Yi hakuri uwata ai kin wuce irin wannan
kukan mai karfi yi shiru ki gaya mun me ya fasa miki
bakin naki haka?"
Na bar kuka na ce mishi Yaya Almu da kanshi
ya lcka ya kirashi ya shigo, ya kalleshi ya ce me ta yi
maka haka? Ya ce rashin kunya ne da ita Baba ba zaka gane rashin kunyarta ba sai na ce maka Baba daga
shekaran jiya zuwa yau sau biyu Umma ta bugeta.
Fuskar Baba ta yamutsc alamar ranshi ya baci
da jin bayanin na Yaya ALmu ya kalleshi cikin 6acin
rai ya ce lallai ne ka gaya mun abinda ta yi maka mai
tsananni wadda ya sa ka yi mata wannan abin bayan ta
yi kwalliyarta mai kyau dubi abinda ka yi, na ce ka
duba waiwaya ka gani me ta yi maka?
Yaya Almu bai boye ba ya ce maganar
mutumin wurin Antinsu take yi mun. Baba ya kalleni
cikin nutsuwa ya cc me yasa haka uwata? Na kalli
Baba cikin nustuwa na ce Baba dama ana aure
tsakaninw ad akanwa ne? Ya yi maza ya ce Babu na
cc a to to shi Baba sai ya rinka yi mun wata magana
na ce mishi ni da shi ai kaine ka haifemu, ya ki. Baba
ya ce to kai me ya sa ka ki Lamido? Yaya Almu ya
sake maida bayanir shawarar daya bayar, Baba ya yi
murmushi ya ce to amma uwata ai ina ganin kamar
lallai Lamido yana sonki tunda har zai iya kawo
wannan shawarar a tsakaninku ban ga abinda zai sa ki
42

ki yarda ba, na ce msihi a'a baba ni na fi so ace Yaya
Almu dani dukanmu 'ya'yanka ne bana so ka rasa
kowa a cikinmu bana so ace ba kai,, ka haifi Yaya
Almu ba haka nan zan yi bakin ciki in har aka ce mun
ba kaine mahaifina ba nan da nan na soma yi mishi
kuka baba ya shigå rarrashina har na yi shiru na share
hawyaena na kalleshi cikin nustuwa, bayan fitar Yaya
Almu na ce mishi Baba waye Mustaphan da aka ce z
aka baiw ani? Ya zuba mun ido ya ce Lamido ne na
sake buda baki cikin karfin hali na ce mishi Baba su
waye suka haifeni? Da gudu hawaye suka rinka zuba
daga idona, Baba ya sake kallona ya ce mini,
"Kina tuhumar umarki ne?
Na yi maza na ce mishi, 'A'a."
To don me ni za ki yi mini wannan tambayar
kin taba ji an ce miki ga dan'uwanki ya zo?
Na yi maza na ce mishi, 'A'a Baba."
"To don me shi Lamido ba za ki hada shi da su
Junaidu ba, me ya fi su? Me ye bambancin shi da su?
Da Lamido da Junaidu da su Zubairu duk daya ne kar
ki damu kan ki da cewar shi yaya yake, muhimmin
abin shi ne ke tawa ce wani muhimmin abin kuma shi
ne Ummanki ce uwarki al'amarinki mai girma ne a
wurina, don haka jna fata za ki kar6i mijin da na zabar
miki da hannu bibiyu in dai ba ba kya son shi ba ne."
Na durkusa gabanshi na ce mishi, "Zan bi
umarninka da hannu bibiyu Baba ko da ba Yaya Almu
ka zaba mini ba, balle Yaya Aimu sanin halin shi da
43

alherinshi da na yi ne ya sa na ke tsoro kar a ce shi ma
ba na ka ba ne?"
Ya ce, "To kar ki ji komai ni kowa nawa ne."
Na ce mishi, "To Baba."
Shigowar Umma Amarya ya katse hirarmu don
kuwa dare ya yi nisa hakán nan shigowa ta yi da shirin kwanciya.
Washe gari kuma fitowa na yi ban ga Yaya
Almu ba. Wajen karfe goma na shiga falon Baba,
saboda na yi barcin safe, na gaishe shi na zauna nan
muna karyawa. Ya ce mini, 'Ai Lamido ya zo zai
tashe ki wai ku tafi na ce mishi ai ko don dukan da ya
yi miki jiya ba zan barki ki bishi ba kin ga kuma har
yanzu labban naki a kumbure suke, ki rinka kiyayyye
maganar da za ki rinka gaya mishi, kin ji ko?"
Na ce mishi, 'To Baba."
Da La'asar sakaliya sai ga Yaya Almu ya dawo
alamar dai yana-fitoa daga kotu, arport ya je ya dawo
Lagos. Na kalle shi na yi murmushi, Baba ya taya ni
murmushin, shi kuwa ya kule.
"Ai dariya ma kike yi mini?"
Baba ya ce, Za ta yi mana ai ba ka da
jarumtaka ne na dauka fushin da ka yi da safe ba za ka
dawo ba sai kwanaki bakwai din da nan diba sun
cika."
Yaya Almu ya sunkuya ya ce, 'Baba sauran
yan matan fa suna can suna ta shirye-shiryensu."
Baba ya ce, 'Haka ne to gobe in Allah ya kai
44

mu sai ku tafi tare."
Hankalina a kwance yake lokacin da na dawo
gida, ba ni da wata damuwa cikin raina, sabdoa tsoron
da nake ji din an kawar mini da shi, ni ce dai yar baba
ta asali ta cikinshi shi kenan bukatata ta biya. Yaya
Almu kuwa na san shi ne mijin da ya dace da ni, zabin
da Baba ya yi mini din zabi ne na tsananin kauna
zaton da nake ji cewar shi din uba daya mu ke shi ya
hana ni yi wa kaina sha'awarshi, ko a hakan kuma ina
kishin kalaman shi kan matar da zai aura. A yanzu
kuwa son shi nake yi da iyakacin raina, illa iyaka dai
na ki yarda in nuna mishi hakan.
A falon Umma muka fara sauka mun same ta
da baki sosai, kawayanta ne da na dade da sanin su a
duk lokacin da hidima ta taso mata, kuma sune farkon
masu zuwa kan lamarin nata, don kuwa aminanta ne
na kut da kut.
'Ashe bikin Adawiyya ya tashi? Abin da sabbin
shigowa falon suke gaya mata kenan.
"To wai ni Furera Adawiyya ce kawai za a yi bikin ta
ne?
"Har da su Junaidu fa cikin masu aure nan.
"Amma bakwa ambaton kowa sai Adawiyyah."
Umma ce mai, gayawa wata kawar tata haka.
Ta ce, 'A'a to wannan ai ke ya shafa mu kam ai auran
yar mu muka sani za mu yi bikin 'yar fari kuma yar
auta."
Gaba daya suka kwashe da dariya.
45

"Kin fara tsuma mana ita kuwa? Don na san
halin ki." Umma Hauwa'u ce mai wannan maganar.
Irin wadannan kalaman sune suka yi sanadiyar fitata
daga wurin Umma na ce bari in je in gaida Umma
Karama da sauran mutanen da aka wajabta mini
gaishe su a gidan. Sai dai ina shiga sashin Umma
Karama na soma jiwo abin da ya birkitani ya fiddani
cikin hayyacina, ya katse mini farin cikina, ya sani na
Ji tamkar yawo nake yi a sama.
"Wai a kan wannan shegiyar 'yartata. To
shegiya mana wane ne ubanta? Nan gidan ubanta ne?
Shi Lamido dama a mallake yake a hannunta, don
abin da yake mata ya wuce biyayyaya tasan ma bauta
daga kawai na ce ban yarda hadin da ya ce zai yi
tsakanin Lamido da yarta ba, don hakan tamkar
neman mallaka mata komai na shi ne tun da za ta
mallaki Lamido shi kuma kamata ya yi a ce kowa na
shi nc a gidan don haka Aina'u ce ta dace da shi, ita ce
yar dangi ba wannan yarinyar da ba a san asalinta ba.
To ba a san asalinta ba mana, mene ne asalin na su da
Uwarta?"
Rantsuwa mai tsammanin karfi na ji Umma
Karama ta yi kafin ta sake jaddadawa wanda take
magana da shi diu cewar ni şhegiya ce daka kawai tafi karfin Alhaji.
Dafe kirjina na yi da hannu biyu ina fadin, "Na
shiga uku." Na juyo da sauri na fita na nufi dakinmu
zan je in dan kwanta in huta, saboda kai tsaye ba zan
46

iya fuskantar Umma da wannan zancen ba. Ina tafiya
inan kara jaddada mamakina game da hadani aure da
yaya Almu da aka ce za a yi.
Ina shiga dakin mu na wuce Aina'u da Basira,
na fada kan gadonmu na kwanta na dafe kaina, saboda
sarawar da yake yi. Bayan na dan nutsa ne na ji hirar
da suke yi sosai, ashe wai Ummana suke zai shi ya sa
ba su samu damar amsa gaisuwar da na yi musu ba.
"Cikin shiege ina jin ta yi ta haife ta, tun da shi kam
baba ai kowa ya san yaya Aimu dan shi ne." Maganar
Basira ne wannan da ta yi matukar kashe mini jiki.
Tabbas in har za a cire mutum daya tsakanın ni da
yaya Almu a ce wane ne wanda ba baba ne ya haife
shi ba? To ina ganin kamar ni ce za a cire. Son kai ne
kawai ya hana ni yin wannan hukuncin, to amma
kuma zai yiwu a ce ni shegiya ce a ce ba a san asalina
ba? Ina cikin wannan kidmane na ji Aina'u ta fige
zanin gadon da nake kwance a kai tana tambayata.
"Kin shimfida gadon ne da kika zo kika hau
kai?"
Na ce, 'A'a amma ko ban yi shimfida yau ba ai
akwai ranakun da nan ke yi, ban zo na kwanta akai
ba. "
Ta ce, Ke kar ki kawo mini iskanci kin ji?" Ni
uwarki ma yanzu ba girmanta nake gani ba, balle in ji
tsoronta. Kan mu rabu kuma zan nuna mata asirin da
ta yi wa baba da Umma Amarya da su yaya Almu, ni
bai kama ni ba, don haka daina nuna mana wata
47

gadara, don an riga an yi iska abin kasa ya riga ya
bayyana, mun riga mun gane nan ba gidan ubanki ba
ne cikin she.......... "
Kan ta kai karshen maganar tata ban san yanda
aka yi ba ganí na kawai na yi a tsakar gidanmu muna
cin uban dambe ni da Aina'u. Na kuma san danben ne
ya fito da mu daga dakin na mu. Damben mai tsanani
ne sosai, don kusan su biyu ne a kaina. Yaya Zubairu
ne ya turo kofar wurin namu da saurin shi ya zo ya
raba mu, na kalli Aina'u na ce,
"Karya kike yi ki ce ba kya jin tsoron Umma
don kuwa ko ni zan yi mata maganinki ba kuma ke ba
na gaba da ke ma tafi karfin su.
Ke Adawiyya ku wuce mu je."
Umarnin da yaya Zubairu ya bayar kenan.
Muna fitowa muka gamu da Umma Karama za ta
shigo wurin namu, cikin sauri watakila labarin
damben namu aka kai mata, shi ya sa ta zo da kanta.
Can wurimta yaya Zubairu ya kai mu. Muna shiga
wurinta ta kalle su cikin takaici ta ce musu,
"Ku biyu ita kadai amma ji abin da ta yi
muku? Ji ki Basira, ji fuskar ki tabarya ta kwada miki
ko?"
Ganin yaya Zubairu a bayanta ya sa ta y1 maza
ta yi shiru cikin jin kunya. Sai kuma ta shiga yin tada
wai za ta ji abin da ya hada mu. Aina'u ta ce mata ji
kawai ta yi kawai ta yi na rufe ta da duka. Ta ce, "Eh.
to dole mana samun wuri ne kansa bako ya fi dan gida
48

iko a gida." Ta kalleni ta ce,
"Amma ai kin san su Aina'u ko Sa'a sune sun fi
karfin duka a wurinki, don su nan gidan ubansu ne, ke
kuwa fa kina tambayar uwarki asalinki? "
Ban ji kunyarta ba na ce, Ba na tambaya ba kuma zan
tambaya ba, don girmanta yafi gaban a tuhume ta, na
kuma san inda duk ta samo ni ni 'yar halak ce, don
Umma ba ta yi kama da mai yin halin banza." Ina
maganar ina kuak sai na ji yaya Zubairu ya yi mini tsawa,
"Ke Adawiyyah kar in sake jin kin yi wata
magana."
Ta ce, 'A'a kar ka ce za ka ce mata komai ni
uwarta ce daidai da ni." Tana fadin haka ta figi
gyalenta ta wuce wai wurin Umma za ta.
Yaya Zubairu ya bi bayanta yana cewa, 'Umma
kar ki jc mata wuri ki yi hakuri ki dawo wurin ki." Ba
ta kula shi ba. Da gudu na wuce na tafi wurin Umma
na yi sa'a duk bakin nata sun tafi kan ma in ce zan ce
mata komai sai ga Umma Karama ta shigo. Wadansu
irin maganganu take yi masu tsananin zafi da gore-
gore wai tana rama zagin da na yi mata. Umma tana
jinta ba ta daga ido ta kalleta ba, balle ta buda baki ta
tanka mata, in banda da ta ga za ta nufo falonta na
farko ta shigo inda take zaune ne ta ce mata,
"Kar ki karaso nan, saboda ba na so ranki ya
kara 6aci, in dai kika tsaya anan to za ki yi ki gama
lafiya."
49

"Me za ki yi?" Ta shiga dura ashar. Ana cikin
haka sai ga su yaya Junaidu dukkansu sun shigo ga
alama yaya Zubairu ne ya kira su.
Yaya Almu ya ce, 'Amma Umma wannan abin
ai shi ne abin da ba zai yiwu ba ko? A ce wata zata
tashi ta je wurin wata ba don mu'amular arziki ba sai
don ta je ta ci mutuncin ta, yanda babu mai yi miki
haka. Hakan nan ba zai yiwu ki yi wa wata ba in Rabi
ta yi miki rashin kunya, sai ki gaya mini don ba ki
taba kawo kararta na kyaleta ba."
A fusace Umma Karama ta ce mishi, 'Ai
lokacin ba ta gama da kai ba ne, amma yanzu da ta
fara tura maka ita kuna kwana me za ka iya? Me zan
ce maka jiya da shekaranjiya duk a ina ku ke? Ina ce
kuna can küna holewarku."
Ban san lokacin da yaya Almu ya sulale ya bar
wurin ba, ya bar Umma Karar1a tana ta faman fadin
maganganunta har ta yi ta gaji ta juya ta fita, saboda ta
gaji da zage-zagen da take yi. Ba wanda ya tanka
mata. Bayan fitar ta ne yaya Kabiru ya kalleta cikin
sanyin jiki.ya ce mata,
"Ki kara hakuri Uma." Ta yi murmushi ta ce
To ya ya zan yi? Ina na kula ta muka yi kuma
ai ni ce a kasa, Adawiyya ce ai ta jawo jta ta yi mata
rashin kunya."
Yaya Zubairu ya yi maza ya ce mata, "A'a
Adawiyya ba ta yi mata komai ba, Umma ke dal
kawai ki yi hakuri."
50

"Ba komai." Umma ta ce da shi.
Da daddare rannan ina kwance a bayan Umma
ita ta ce in zo in hau bayanta in kwanta. Ina kwance a
bayan nata tana tambayata.
"Jikinki dumi Adawiyya ko ba kya jin dadi
ne?" Na ce mata na yi kwance cikin ruwa mai zafi ne
Umma.
A hankali ta soma yi mini hira cikin nutsuwa,
"Sai kin zama jaruma kin zama mai hakuri kan zaman
da za ki yi da Babangida, shi kam ba ki da matsala da
shi, don kuwa babu wani wanda zai so ki
kwatankwacin son da Babangida yake yi miki. To
amma, yan'uwanshi su ne matsala."
Na ce mata, "Umma."
"Mene ne?"
"Kin yarda in tambaye ki wani abu?"
"Uh, uh kar ki tambayeni komai yanzu barci ya
kamata mu yi."
Na ce mata, "To." Na kara matsawa jikinta na
jingina kaina da bayanta. Sannan na shiga barci.
Dare ya yi nisa lokacin.da na ji Umma tana
kiran sunana cikin salati da tsoro ta.
"Adawiyya! Adawiyya!!." Na bude idona a
hankali ina kallonta cikin rawar jiki a dalilin tsananin
zazzabin da ke kadani kar! kar!! Kar!!! Na zuba mata
ido ina kallonta cikin yanayin rashin lafiya. A hankal
na bude baki na ce mata,
"Ki yi hakuri Umma dazu na ji tsoron gaya
51

miki ne su Anti Basira sun cijeni da karf."
Umma ta ce, "Cizo?"
Ta shiga salati tana kuka. Yayin da take yaye
ruhuwar tawa, don ganin inda cizon yakc. Nan da nan
ta shiga kuka mai tsanani tana cewa,
"Ya ya zan yi da ke Adawiyya? Ya ya zan yi
da wadannan mutane da suke shirm tosa mini ke a
gaba? Ba ki kuma yi musu komai ba, laifina ne kawvai
ya shafe ki, kiyayyar da suke yi mini ne za su dawo da
ita kan ki."
Ta sa hannu ta dauki wayarta. Y aya Junaidu ta
kira. Har cikin dakin Umma ya shiga, ta nuna mishi
jikin nawa, ya ce, 'A'a wannan al'amari Umma hakuri
fa za ki yi kawai tun da dai an kusa rabuwa ba kuma
zai yiwu ki ce za ki yi wa yara wani abu ba, tun da
dukkansu ya'yanki ne."
Ta ce, "Haka ne."
Cikin daren jiya Junaidu da Umma suka kai ni
asibiti aka yi mini allurai, suka dawo da ni. Kwana
biyu ina jinyar cizon da su Aina'u suka y1 mini, amma
ba wanda ya sani, don yaya Junaidu ya ce kar a
gayawa kowa, a yi shiru kawai.
Rannan yaya Almu ya kirani, na same shi

Please Login or Register in order to submit comment