Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafiya yana dawowa, na
san abin da yake nema. To gara in kai mishi ke da
kaina duk da mun yi shekaru ba mu ji duriyar jutna ba,
in dai yana nan zai rike mini ke, in kuma baya nan zan
bai wa iyalinshi in ya so in roke su su kai mini ko
wurin dangina. Akwai bayanin komai a ajiye in kumna
ma na same shi to shi ya san komai, don na taba bashi
labarin kaina saboda lura da halin shi da na yi.
Mun yi wannan hirar da kwana biyu ne kawai
baba ya kwanta biyu ne baba ya kwanta jinya mai
tsanani, daga ni har shi hankalinmu ya yi matukar
tashi, ni ina damuwar rashin lafiyarshi, shi kuwa yana
damuwar bai samu kai ni Wurin amininshi ba.

Kwanaki kusan talatin yana kwance ni ke yi
mishi komai, sai ko makwabtan da ke shigowa suna
taimako na da abubuwan da na kasa. Rannan sai Baba
ya dan samu sauki har ya fita ya bi salalr jami yana
dawowa ya kalleni ya coe, "In har saukin nan nawa ya
kai gobe da safe, to kamar yanzu a gobe insha Allahu.
kina Katagun zan je in kai ki ba zan sake wani bata
lokaci ba."
To haka aka yi gari yana wayewa daga fitowa
daga sallar Asuba Baba ya tasa ni a gaba da dan kullin
kayana a kaina muka je muka shiga mota zuwa
Katagun. Wajen Azahar muka isa.
70

Duk da tsawon shckarun da suka yi ba su sadu
ba, ga kuma halin rashin lafiya. Kai tsaye Baba ya kai
mu gidan bai zauna ba, yana daga tsaye tamkar bai
gaji ba ya tura wani yaro cikin gidan ya ce, "Ka shiga
nan gidan ka ce wai ana sallama da mallam Mai
Hadisi."
Nan da nan sai ga yaran nan ya fito tare da
wani kyakkyawan dattijo Rakkarfa gaba daya
kasunbar shi ta yi furfura da ganinshi ka ga ma'abocin
tsabta irin ta addini. Yana ganin Babana ya buda baki
nuna alamar mamaki da sauri ya zo ya rumgume shi
yana fadin,
"Malam Ali ashe mafarkin da nake yi da kai na
rabon saduwa ne? Ai ni har na tara yara na yi musu
bayaninka na gaya musu watakila za ka zo ne a
bayana, ashe, ashe za mu sake ganin juna ne. To kaa
shigo."
Ya rike hannun Baba suka shiga ciki; nima na
bi bayanshi zuwa dakin da aka sauki babana. Baba da
kan shi ya dama mana fura. Nan da nan 'ya'yanshi
magidanta suka yi ta shigowa suna gaida baba, shi
kuwa yana gaya musu Gashi nan wanda nake baku
labarinshi shekaran jiya nake gaya muku kar ya zo
bayana ku ce ba ku san shi ba,"
Nan da nan sai gashi an kewaye mu da kayan
Sauka iri-iri su kuwa su Baba suna hira. Zuwa can sai
baba ya kalleni ya ce,Wannan yar yarinyar dai
Saratu ce ta haifar mana ita, ko da ban sani ba."
71

Babana ya yi murmushi bayan ya kara kallona
ya ce mishi, 'Eh. "
Baba ya ce, 'To ina Saratun take?"
Babana ya ce, "Bana shekarunta biyar tana
kwance a kasa."
Maganar ta yi matukar girgiza baba. Nan da
nan ya shiga yi mata addu'o'i iri-iri na neman rahama.
Da aka natsa sai Babana ya ce mishi, "Malam nauyi fa
na zo zan dora maka sai ka yi hakuri."
Baba ya ce, 'Nauyi wane iri Malam Ali?"
Babana yay gama yi mishi bayanin halin da
yake ciki. Da ya gama sai ya ce mishi, 'Shi ya sa na
dauko Zuwaira na kawo maka ita ka saka ta cikin
Iyalinka ta zauna ka reneta tare da su, in har ka yarda
ka karbi wannan amana da nan kawo maka to ni zan
koma gida, cikin farin ciki in je in saurari isowar
lokacina cikin kwanciyar hankali."
Baba ya kalli Babana cikin sanyin jiki ya ce
mishi, "To in ban da abin ka małam Ali wannan irin
amana da ka kawo mini ni kwana nawa zan kara
bayanka in biyo ka? Daga ni har kai ai daya muke a
bakin gaba muke, don haka ina ganin tunda ka amince
ka kuma, samu iko ka kawo mini ita amana, to bisa
yardarka nima bari in bai wa yara ita in sun yi yawan
rai sai su rayu tare, don haka in ka yarda zan bai wa
Bello aurenta.
Babana ya kalleshi ya ce, "Ta ka ce fa ikonta
yana hannunka duk abin da ka hukunta a kanta daidai
72

ne."
Baba ya mike ya kama hannuna ya ce, "Mu je
Zuwaira in kai ki wurin uwarki."
Na mikc muka shiga cikin gidan mai sassa da
yawa ya ratsa ya kai ni na shi sashin. Matarshi tana ta
faman aikinta cikin nutsuwa tana ganinshi ta mike
tsaye tana gyara yafenta ta yi murmushi ta ce, "Kana
labarinshi ashe yana kan hanya."
Ya ce mata, 'Eh Rabi sai, dai ya kawo mana
aiki amana kin kuwa san in banda girman darajar shi a
wurina babu abin da zai sa in karbe ta a wannan
kurarren lokacin, don haka me kika gani cikin yaran
in zan bai wa wani aurenta, wa ya kamata in ba?"
Ta dan yi shiru cikin tunani, kafin daga baya ta
ce, "To ka bai wa Bello mana, duk da dai akwai na
gaba da shi."
Ya ce, "To mun yi daidai nima dama shi na fada, shi zan bai wa."
Ya juya cikin sauri ya fita ya bar ni a wurinta.
Nan da nan ta maida ni 'yar gida ta hanyar dauko mini
wannan wancan, ci wannan, karasa wannan, abin da
take fadi kenan.
Washe gari da hantsi sai kawai aka shiga gida
ana raba goro da dabino. Ana fadin an daura auren
Bello da bakuwar yarinyar, Gaba daya gida ya dauka
ikon Allah, dama ashe matar Bello ce ta zo.
Baba Rabi ta yi maza ta sanya ni a lungun
dakinta. Bayan ta kawo sababbin tufafi ta bani na
73

Sanya ta lullube ni ta ce, "Yi zamanki anan kar ki bari
kowa ya ga fuskarki." Na ce mata to.
Na wuni anan a lullube, sai dai bini-bini zata
zo ta kawo mini wani abin da zan ci. Ta ce mini maza
cinye kar mutane su ganki, in ce to, ba tare da na san
abin da hakan ke nufi ba. Kan ka ce me ye wannan sai
ga gida ya cika da jama'a masu zuwa murnar Bello ya
yi mata. Da daddare bayan jama'a masu tafi ne baba
Rabi ta tasani a gaba ta kai ni dakin da Babana yake ta
tsugunna daga bakin kofa ta gaishe shi ta juya. Ni
kuwa na shiga ciki na zauna a kusa da shi. Ya kalleni
cikin murmushi duk da kaduwar sanyin da yake yi ya ce,
"Ashe gidanki na kawo ki?"
Ban kula wannan magarfar ba, saboda
hankalina ya tashi da ganin yana rawar sanyi. Baan ga
wuta a dakin. Na cc mishi, "Baba ciwonka yau ma zai
tashi ne?"
Ya ce, 'Ai babu komai tun da na riga na kawob
ki inda ya kamata in kawo ki, ke dai ki zama mai
hakuri da bin na gaba da ke, musamman mijinki."
Dan zaman da na yi a wurin nan baba bai yi shiru ba
nasiha yake ta yi mini har aka zo aka tafi da ni cikin
gida.
Halin da na samu babana a ciki ya sa ban iya
Tuntsawa ba, ina ta tunanin jikin na shi inda a gida
muke da ina tare da shi ina dan bashi uwa yana sha,
don jika bakin shi. Yanzu kuwa babu hali an kankane
74

shi. Ina nan a kwance na ji baba ya shigo yana salati.
Yana karawa da sauri baba Rabi ta tashi tana taya shi
salatin tare da tambayarshi.
"Ya ya dai malam?"
Ya ce mata, 'Malam Aliyu ya cika, wa'adi ya cika."
Kalmar ya cika din da ya yi amfani da ita da
kuam fadan da Baba Rabi ta yi mini na in komamn in
kwanta ya sa ban gane rasuwa ya yi ba. Sai da gari ya
waye na yi kuka har na gaji baba Rabi tana ta
rarrashina, amma ina, ko da nake yarinya a lokacin
mai shekaru bakwai na riga na gane mutuwa, saboda
yawan labarinta da babana yake ba ni, gashi kuma na
riga na shaku da shi, shi kadai na sani, shi kadai nake
mu'amalla da shi. in banda jiya da na shigo cikin
sababbin mutanen da suka karbe ni hannu bibbiyu har
na ji zuciyata ta dan samu nutsuwa a tare da su.
Jama'a masu yawan gaske ne suka yi jana'izar
Baba, tamkar ba bako ba, aka yi zaman makoki na
kwanaki uku aka gama.
Washe gari bayan an idar da sallar Asuba, ina
zaune ina karanta addu'o'in da baba Rabi ta ce in rinka
yi wa iyayena, sai na ga wani ya shigo, bayan na amsa
mishi sallamar shi ya nemi wuri ya zauna cikin
nutsuwa muak gaisa da shi, ya yi mini ta'aziyya. Ban
damu da kallonshi ba, don dama samarin gidan sun yi
ta shigowa suna gaishe ni, sai dai shi wannan
dabi'arshi daban take da ta sauran. Nutsuwar shi ma
75

daban take, hakan nan kalaman da yake yi mni na
kwantar da hankali ne.
"Baba Rabi ba ta gaya miki Baba ya cika yana
kalmar shahada ba?"
A hankali na ce mishi, Ta gaya mini."
To kar ki sake bakin ciki, kar ki sake kuak rinka yi
mishi addu'a kawai. Cikawa da kalmar shahada
alamar samun rahama ce, dama kuma mun san nan ba
matabbata ba ce, hanya ce kawai ta wucewa zuwa
inda muak dosa, ko ba haka ba?
Na ce mishi, "Haka ne."
Ya sake kallona cikin nutsuwa ya cc mini, "Miko mini maburgin can na kan dankin Baba, hannunki zai kai?"
Na yi maza na ce mishi, Eh." Na mike na
dauko mishi ya yi kamar za karba, sai kuma ya ce,
Ko kuma maida shi ki yi zamanki kin taba kada miya kurwa"
Na ce mishi, Eh a gida ni nake mana da baba
bai da lafiya." Sai ya ce mini ga yanda zan yi, ga
yanda zan yi. Ban damu da kallon da ya rinka yi mini
ba, hakan nan ban kula jana da magana da yake ta yi
ba, ban fahimci komai a game da shi ba, sai da ya ce
mini,
"Wai an daura miki aure da wani Bello ko?"
Na dan sunkuyar da kaina kasa nuna alamar
kunya. Ya ce, "Kin taba ganinshi?" Na girgiza kaina a
hankali tare da cewa, "A'a."
76

Ya rage murya a hankali ya ce mini, "To nine
Bello da aka daura miki aure da shi." Ina jin haka na
yi wuf na koma lungun da baba Rabi ta nuna mini na
jawo katon zanin da ta ba ni na lullube kaina. Ban san
yanda aka yi ya fita ba.
An dauki lokaci mai tsawo Alhaji yána mini
gizo ba na gane shi. Dukkansu gaisuwa daya nake yi
musu, sai shi ne yake ce mini, "Ke wannan mijinki ne
Zuwairiya rinka kallona kian gane ni." Ina jin ya fadi
haka sai in ruga in shige lungun da ke kusa in buya.
Ina gane Alhaji shi kenan sai na shaida kowa na gane
wannan shi ne yaya Babba, wannan shi ne yaya
Barau, ga yayan Tudu, sune maza manya da ke gaba
da shi, sauran matane sai kuam kannen Alhaji. Baba
ya'ya ne da shi sosai matr yawancinsu mata sunna
gidajen aurensu.
Dana watstsake a gidan nan 'yar gida sosai na
zama ba mai cewa ni daban ce a cikin gidan. Wasa
sosai nake yi da yaran gidan sa'o'ina. Baba kuwa har
kayan wasa yake sai mini, su tallen miya, su tandun
tuya, su gadon 'yar bebi. Komai na kayan wasa babu
abin da ba ni da shi. Da daddare kuma in ya dawo zai
kirani dakinshi mu yi dumi tare ya kuam ba ni abin
tsarabar da ya zo mini da shi. Na yi sabo mai tsananin
yawa da Baba, hira sosai yake yi mini, ya kuma yi ta
tambayana abubuwa ina gaya mishi.
Rannan na je gaishe shi da safe da ya kalleni
sai ya ce mini, Kina lissafi kuwa Zuwaira yau fa
77

shekara guda ne tun da muka rabu da dan'uwana
malam Aliyu?"
Na yi shiru cikin jimami, hawaye suka soma
zuba a idona. Lokaci mai tsawo ya dauka yana ba ni
labarin halin rayuwa ya yi mini hirar mu'amallarshi da
babana.
'Mahaifinki mutum ne mai son gaskiya wanda
bai son nuku-nuku ko kunbiya-kunbiya kan wani
lamari, ko nawa zai samu cikin har ka yana hango
rashin gaskiya a ciki za ka ji ya ce ba ya so. Ki zama
mai gaskiya ke ma kin ji ko?"
Na ce, To Baba."
Ranar da daddare da Alhaji ya dawo ya kirani
na je na same shi a bayan rumbu yana tsaye ya kalli
tandun tuyan masan wasan da ke hannuna ya kalleni
cikin nutsuwa ya ce mini, "Sai yaushe kike ganin za ki
daina wasan nan Zuwairiyya? Yau fa shekara guda ne
da auren mu ko kin manta ne?" Ban amsa mishi ba.
Badi iwar haka kuma ina ganin kamar zan bukaci
baba ya ba ni ke."
Kullum ya dawo zai nuna rashin dadin shi
game. da wasannin da ya kan samu ina cikin yara,
kowanne lokaci sai ya gaya mini "Wadannan
yayyanki ne, amma kina wasa da su, maimakon ki
tsame kan ki daga cikin su, ki kama girmanki, ba ki
girme su ba a shekaru, amma kin fi su daraja, saboda
ke matar kanin Babansu ce."
Da irin wadannan kalaman na shi na fita
78

harkar wasanni na koma zama tare da baba Rabi, ina
koyon aikin gida, tare da ita. A wannan lokacin komai
na aikin gida ni na ke yi, Baba Rabi kan yi mini gyara
ne kawai ta hanyar ba ni umarni mafi yawancin lokaci
na kan yi aikin ne tana tare da mijinta suna hirarsu.
Mace mai matukar karamci. Na dade kwarai a gidan
kafin na ngane ba ita ce mahaifiyar Alhaji ba. Ta yi
matukar kokari wajen sabar da ni yin mu'amalla da
shi, ta hanyar aikena wurinshi da take yi kai mishi, ko
dauko mishi, maimakon da da sai ya ritsani ne a wani
wuri yake gaya mini abin da yake son gaya mini.
Rannan Baba Rabi da Baba suna hira ina jin
sus ni kuwa ina dakin dahuwa tankadan tuwon dare
nake yi. Lokacin nan kuwa shekaruna tara ne, sai naji
ta tana ce mishi.
"Anya Malam ba ka ga kamar Bello zai bukaci
a bashi matarshi da wuri ba kuwa?"
Ya ce, Na gani mana ja'iri bashi ita ne kawai
ba zan yi ba, sai ta yi sha uku ta mori kuruciyarta
tukunna."
Da sauri baba Rabi ta ce, "Tabdijan! Ai kuwa
dai abin da ba zai yiwu ba, kenan shekarun shi nawa
ne yanzu? Yan'uwanshi suna kamar shi ai matansu
sun tare musu, bana fa shekarunshi ashirin ne.
Baba ya ce, 'Eh ba mancewa na yi ba."
To shi ne za ka tsare mishis ita har shekaru hudu? Ai
kai ma gara ka san ba zai yiwu ba, don kuwa zirga-
zirgar nan tashi ta tsakanin nan a kanta ne babu abin.
79

da ya ke so irin ay shigo ya ganta ita kadai, don ma ita
yarinyar ba mai dabara ba ce gudunshi take yi."
Baba ya ce, 'Gaga ta yi ta gudunshi, tausayinta
nake ji shi ya sa nake ganin inda mun dace mun raye
to zan barta ta yi sha uku tukunna ta dan yi kwari ta
kuma yi wayo."
To shekara guda bayan wannan lokacin Baba
da kanshi ya bai wa Alhaji umarnin gina mini inda
zan zauna, saboda ya fito da maitarshi fili a kaina, ko
da dai ba magana ya yi ba.
Ina jin baban yana gayawa Baba Rabi, "Ja'irin
yaro yau dai na yi maganinshi na gaya mishi ya gina
mata inda za ta zauna ban kuma yarda ya bai wa wani
aikin ba, ya yi da kan shi. Bayan haka kuma babban
daki nake so ya yi mata, inda za ta sake ita da
ya'yanta"
Baba Rabi ta ce, To me ya sa ka yi mishi irin wannan tsananin Malam?"
"Don ya kai badi bai gama ba, kin ga kuam
nan da watánni kadan ruwa zai sauka da alama ba zai
je ko'ina ba uwa zai sauka kan ya gama ta kara kwari."
Tausayin Alhaji ya kamatá ta yi ta fadin magana, shị kuwa ko a jikin shi.
"Ginin nan fa kai kake bayarwa a yi. Sannan
shi ga kasuwar da yake zuwa, yaushe ya je ya dawo
ya zo ya yi aikin nan?" Duk bayanan da take yi Baba
baya tankawa, sai dai ta yi ta gama ta yi shiru.
80

Ba a dauki wani lokacin da ya wuce sati biyu
ba rannan da daddare sai Alhaji ya zo ya cewa Baba
Rabi a gayawa Baba in ya yarda yana son fara aikin
nan. Ta ce mi shi to. An bashi izinin farawa kuwa ya
kama ranar da ya shata ginin, rannan Baba Rabi ba
karamin fada ta yi mishi ba, akan me zai shata daki
biyu? Wato ciki da falo, ana gane mishi wahalar aiki
yana karawa kan shi. Baba ya yi murmushi ya ce.
'Dadina da ke ba kya iya ganin abu ki yi shiru,
ai ba a kwacewa yaro garma, yi abin ka Bello ai kana
da lokaci mai tsawo na yin aikin, ni dai na yi maka
alkawari kana gama gininka zan ba ka matarka."
Alhaji ya ce mishi, 'To baba."
A haka Alhaji ya kama aikin nan. Ya kan kama
aiki ne da sassafe daga fitowarshi daga sallar Asuba in
rana ta yi kuwa sai ya bari ya yi wanka, ya tafi
kasuwa. A haka cikin watanni biyu sai gashi har ya yi
rufe, ya yi shafe da dabe, har ya sa rumfa a kofar
dakin, ga kuam dabe ko'ina, ga kuam wurin
kewayawar shi can gefe shi kadai. Ya kuma kawayata
wwrin da shafen farar kasa.
Rannan da daddare Baba Rabi da Baba sunan
hira ta ce mishi, 'Ni mallam ba ka ga yaron nan ya
gama aikin da ka bashi ba ne, ban ji ka ce komai ba?"
Baba ya ce, 'Eh na gani ya yi kokari."
Ta yi dariya ta ce, "In mutum ya yi dace yana
da zuciya ai ya more, babu wani abin takaicin da zai
dame shi, don haka sai ka cika mishi alfawarin da ka
81

yi na bashi matarshi da zarar ya gama aikin da ka bashi."
Baba ya ce,"Yanzu da damunar nan yaushe
zan yi hidimar biki? Ai kuma sai da kaka."
Baba Rabi ta ce, "Malam jiya ne fa aka yi
ruwan farko. Habá malam kar ka yi wa yaron nan
haka ka yi hakuri." Tana fadin haka ta kama kuka.
Baba Rabi ta tasa baba a gaba ya yi bikina a
tsakiyar damuna, saboda mita kowanne lokaci,
damunar nan ba ta hana babu komai ba, hidima sosai
ya yi har da yanka saniya ya gayyaci 'yan'uwa da
abokan arziki sosai, duk da ni kadai ce za a yi bikin
nawa, sauranyan matan da da za a hada mu da su
gidajen mazansu sun ce su a yi musu hakuri sai kaka,
ba za su yi biki da tsululun damuna ba.
Hidima sosai baba ya yi tamkar dai bai taba
aurar da wata ya ba sai a kaina. Dattawa abokanshi
suka yi ta- zuwa mishi murna, shi kuwa sai cewa yake
yi, "Ba na shekaru hudu kenan da kwanciyar malam
Ali nima yawan rai ne ya sa na gani ban yi zaton
hakan ba, gashi lokaci ya yi zan dankata ga mijinta ko
da dai shekaru goma shadaya ne da ita. Cikin zuciyata
tausayinta nake ji ba ta yi kwari ba, amma dai na
sauke nauyin dake kaina."
Su kuwa sai sukan ce mishi malam wannan
yar taka ma ai babu mai cewa shekarunta kenan, in ba
ka fadi ba, saurin girma ne da ita.
Daki biyun nan tam baba ya cika mini su da
82

kaya. Gado biyu ya yi mini, a lokacin nan kuwa gado
biyu sai 'yar gata sosai. Aka yi mini jeren tasa mai
Kadangare, a kanta daya-daya kantar kuam jeren
kwanuka. Abin dai gwanin sha'awa.
A haka aka kaini dakina hankalina akwance
ban san yaya auren yake ba. Na yi zaton canza mini
daki kawai aka yi aka kai ni kayatacce. Haka nan
ganin shigowar Alhaji bai tayar mini da hankali ba,
saboda ya riga ya yi dabarar da ya ja hankalina zuwa
gare shi. Sannan bayanin da baba Rabi ta yi mini
kenan cewar canza mini daki kawai aka yi, amma
gani ga ta ga kuma babana, don haka kar in damu. Na
ce mata to. Kasa hakuri da ni da Alhai ya yi ne ya
firgitani na tsorata kwai da shi na rinka gudun dakin,
ian zuwa wurin Baba Rabi muna kwana tare. Tun tana
cewa hau gado ki yi kwanciyarki ja'irin yaro kawai,
wanda bai san bin al'amaria hakali ba, har ta gaji da
kanta take korata ta ce ke tafi dakin ki bana son
sakarci. Da ta fara korata sai na koma kwana cikin
yaran gida sa'o'i na, ita da Alhaji su kwana suna
nemana, sai da safe su ganni ba su san ta inda na fito ba.
Rannan ban san tunanin da ta yi ba sai ga ta ta
shigo tana haska fuskokin mu da yar fitilarta tasa
hannu ta kamo ni ta fito da ni su kuwa yaran ta bi su
da sanda ta kwakkwada musu, wai gobe ma su sake
barina na kwana a cikin su. Na dawo kwana a dakina
kamar abin arziki, Alhaji ya fita harkata, gashi kuma
83
kullum zai kawo mini abuuwa masu dadi iri-iri zai
kuma zauna yana yi mini hira mai dadi, in ma na ce
mishi zan je wurin yara mu yi tatsuniya sai ya ce mini,
ai shi yafi su iya tatsuniya, in zauna ya yi mini. In na
ce to bari in kira su ya yi mana tare sai ya ce wai a'a ni
kadai zai yi wa su in suka zo tatsuniyar za ta bace. In
ce mishih to ya zaunar da ni ya yi ta yi mini
tatsuniyoyi masu dadi a duk lokacin da ya yi mini
guda biyu zai ce nima, in yi mishi, sai kuma in yi mishin.
Irin wannan mua'amallar sai ta sa na sake sakin
jiki da shi, sai dai bai, a je ko'ina ba ya sake tsoratani
na koma guduwa, ina buya a bayan rumbu a yi ta
nemana ba a gannina. Rannan da daddare baba ya fito
daga waje, rannan neman ya yi tsananí, shi ma da kan
shi ya fito. Walkiya ce ta haskani ya ganni tsugunne a
tsakanin rumbu ya tsaya yana kallona ya ce mini,
"Zo nan Zuwaira."
Na fara kuka ya ce, "Ki yi hakuri ki fito nan ni
kam ai ba zan ganki in mayar mishi da ke ba, ita ma
Rabi da take yin hakan son rai ne ya sa ta take yin
shi." Ya shige da ni đakin shi yana fadin, "Wannan
fitina ai tana da yawa duk dai laifina ne da na biye
mata na bada ke inda na ki yarda ai da kina nan zaune
cikin rufin a sirinki, hau gadon can ki kwanta."
Na yi maza na yi hakan, shi ma ya bau na shi
gadon ya kwanta. Bayan ya gyara wutar kaskon shi,
saboda saukar ruwan sama, har dakin ay yi sanyi yana
84
kwance yana fadin,
Ai wauta na yi na ba su ke da ban bayar ba da
wanda ya isa ya yi mini wannan shakiyancin ban ci
mutuncinshi ba?"
Kwana da kwanaki kowa ya san a dakin Baba
nake kwana, babu wanda ya yi magana, saboda tsoro.
Rannan dai baba Rabi ta zo ta mishi, "Ni malam
wannan yarinyar ba za ta dakinta ba ne?"
Ya yi maza ya ce mata, "Eh ba za ta ba."
Ta ce,To ai sai ta yi ta zama tun da ita daban ce da
kowa, ita ba za ta iya hakuri da al'amarin mijinta ba,
tun da tana da daurin gindin da za ta rinka, tona mishi
asiri sauran matan da suke rufe kofa da nasu mazan
me ya same su? Haka kawai za ta maida yaro ya zame
mata abin tsoro kamar wani dodo."
Baba ya ce, Dodo ne mana tun da bai da hakuri."
Tun daga rannan kullum baba Rabi za ta sani a gaba tana yi mini nasiha.
"Haba Zuwaira ba za ki yi hakuri ki dauki
lalurar mijinki ba? Yaro yana sonki kamar ya ya,
amma kina ta faman wahalar da shi? Ina amfanin
wannan abin da kike yi? Ina amfanin a ce in zai taba
ki gabanshi ya ringa faduwa kenan, saboda ya san za
ki yi mishi kwakwazo a cikin jama'a? Mutanc suna ji
sun san halin da yake ciki ke ba za ki rufá mishi asiri
ba ne? To ba na so kar in sake ji ai ke matar rufin
asirin shi ce, kar ki yarda a rinka jin tsakaninki da
85

mijinki kin ji ko?" In yi ta kuka don na san karshen
maganar tata, dai maida ni za ta sake yi.
Shekaru biyu kacal da zaman mu sai na yi
wani irin girma na bam mamaki, babu mai cewa
shekaru goma sha uku ne kaca da ni a duniya. Na yi
kyau, na yi fari, ga mijina jarumi kowanne lokaci a
cikin sai mini kayan ado yake; man shafawa kuwa
bana shafa bude da kwabo, sai mai gurguwa shi ma
sai ya kwaba mini shi da zaitun da habbatus-sauda ga
turaruka na almiski nima kuma gani da tsafta kullum
zan yi kitso in yi lalle, kafa da hannu gwanin sha'awa.
Tun a lokacin nan na soma samun matsala tsakanina
da matan yayyen Alhaji, wadanda suka yi matukar
sanya ido kan al'amarina da mjina in ji su wai bai yin
kormai sai da yardata da magana ta kai kunnen baba
Rabi sai ta ce da su,
"Ku ma ku je ku yi wa na ku mazan haka ai ba
hana nku a ka yi ba; yarinyar da aka rena a gabanku
shi' ne har kun fara maganarta in ban da abin da alkunya? "
Rannan Alhaji ya dawo da yamma muna daki
tare da shi, ina kwance a jikin shi don ya riga ya sabar
mini da irin wadannan abubuwan. Ya kalle ni ya ce mini,
"Ni fa Zuwaira ina son fita daga girkin gidan
nan, ba na son shi in na fita za ki iya daukar dawainiyar mu ko?"
Na ce mishi, "To."
86

Ina soma yin girki na soma shirya wa su Baba
gara kullum cefanen

Please Login or Register in order to submit comment