Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rokeni ta tare da danta mai shan
nono wai watanninshi goma ne kawai bai son a raba ta
da shi, ni kuam sai na ji ban son ya sha nonon nata
tana gidan nan, don kar a haramta mishi auren
ya'yanku, don ba a san abin da gobec za ta haifar ba."
Na ce mishi, "To baba in ta zo din sai ka karbi
yaron ka ba ni shi zan yaye mata shi."
Baba ya yi ta murna yana sanya mini albarka.
Ummana ta sake shafa hannuna ta kar jadada
laushin jikina kafin ta ce mini, "To kin ji yanda aka yi
na mallaki dukiya cikin gadon su Alhaji, baba ne ya yi
mini kyauta."
Na yi ajiyar zuciya mai karfi kafin na ce mata.
"Umma."
Ta ce, "Mene ne Adawiyyah?"
Na ce, "Lallai Baba gadon alheri ya yi wurin
mahaifinshi, tun da ni kar han taba jin labarin
mutumin kirki irin shi ba."
Umma ta ce, "Uhum! Me kika sani game da
baba tun da ba zama da shi kika yi ba?" Na sake ce
mata, "Umma." Ta ce mini,
"Ina jinki Adawiyyah ke nake sauraro"
Na ce,To shi wanna Amarya ta zo da shi shi ne ya zo ya zama yaya
119

Almu ko kuwa da ta zo nan gidan ma ta haifi.wani?
Umma ta ce, "Wannan ne kuma ba zan iya
amsa miki yanzu ba, don in na biye miki sai in kwana
idona biyu."
Na sake matsawa jikinta na kwantar da kaina a
gadon bayanta sosai na cc mata, "Lallai kin yi
gwagwarmaya da Umma Karama, Umma."
Ta ce, "Ba kadan ba ai shi ya sa duk abin da
take yi yanzu kallonta kawai nake yi na san ba zai
yiwu ta maimaita abin da ta yi a baya ba."
Na ce, "Haka ne gashi kuam kin yi sa'a baba
yana matukar Sonki shi ya sa. ma da kiak tayata yi
mishi laifi ya yi fushi da ke matsanancin fushi fiye da
wanda ya yi da ita." Umma ta yi dariya ta ce, "Mu yi
barci Adawiyya." Na ce to Umma, amma dai gaya
mini yaushe ne kika haife ni? Ta ce, 'Ba yau ba." Na
ce to gaya mini abu daya kin sake haihuwa bayan
wancan haihuwar da kika yi? Ta yi maza ta ce na sake
mana. Na ce to me kika haifa? Ta cc Rabi'atu. Na yi
murmushi na kara nutsuwa cikin raina dadi ya
kamani. Nan da nan barci mai dadi ya dauke ni.
Washe gari kuwa farkawa na yi na ga haske
vana kashe mini ido na tabbatar ba lokacin gari ya
waye ba, na.yi maza na dauki agogona na duba karfe
goma ne na safe. Da iya kacin karfina na shiga
Cwalawa Umma kira, amma ba ta amsa ba, sai baba
Talatu ce ta shigo tana murmushi.
"Kin farka ne uwar dakina? Za a shirya miki
120

ruwan Wanka ne?
Na ce mata, 'Eh."
Na yi maza na yi waje, don ganin me Umma
take yi. Tana zaune a falonta tare da su Anti Aina'u,
lissatin kudi suke mata, ita kuma tanan tare da jakarta
alamar tana shirin ba su. Na juya żan koma in da na
fito ta kalieni ta ce mini,
"Kin gaishe su ne?"
Na ce, "Bari in wanke bakina tukunna."
Na shiga wankana ban sake fitowa ba sai da na
tabbatar sun fita. Sannan na fito cikin kwalliya mai
matukar kyau na zo na zauna kusa da ita na fara
gaishe ta. Ta kalleni a lalacc ta ce, 'Ai ba zan yi wata
magana da ke ba yau, sai bayan kin je kin gaida su
Aina'u, kin dawo."
Sai kuwa kawai ta ja tsaki alamar dai ta ji
takaicin kin gaishe su da na yi. Na fita waje don in je
in gaida su Aina'u, dama duk wani wanda yake cikin
gidan na san in ba hakan na yi ba ba shiryawa za mu
yi da Umma ba. Ina fita na ga wani abin da ban san da
shi ba. Mutanc suke ta shiga motoci ana ta fita da su,
ga alama kuma tafiyar ba ta kusa. ba ce, don sai jefa
jakunkunan ya'yansu suke yi a bayan motocin.
SAnnan gaba dayansu janma'ar da na sani ne wato
yan'uwa ko kuma abokan arziki na kusa.
ina cikin kallon na su sai na ga Anti Rahma ta
fito da saurinta ta sha kwalliya tana rungume da
Jakarta, sai wani irin kamshi take yi. Na kalleta cikin
121

nutsuwa na ce, 'Anti wadannan fa ina za su?" Ta ce za
Su jere. Na ce tun yau? Ta ce eh to a wurinki kam tun
yau mana, amma ni kams da na san har Lagos za a tafi
nawa jeren ai na san ba a yi sauri ba. Na sake kailonta
na ce Lagos kuma za a kai ki? An yi wa Y aya Junaidu
transfer ne? Ta saki wani lallausan murmushi ta ce
'Lah ashe baki da labarin ajiye aikin Junaidu ai shi
baba ya zaba ya zama shugaban kamfanoninshi. Ai
can Lagos za mu zauna a wannan sabon gidan na baba
da ke unguwar My one.'
Na ce, "Anti Rahma wane irin so baba yaké yi
wa yaya Junaidu haka?" Ta kalleni ta kyalkyale da
dariya ta ce, 'Ai fa kamn ni kin ga tafiyata." Ta wuce
ta barni a tsayc ina bin ta da kallo a zuciyata kuwa
cewa na yi, kai to ko dai ma yaya Junaidun ne dan
baba na cikinshi, shugabancin kamfanoninshi da ya
bashi ai yana nufin ya dauki duk dukiyarshi a hannun
shi ne ga shi kuarn darna an co aure bai halarta ba
tsakanina da shi, kuam shi yaya Almiu ya tabbata
kenan shi ne wannan da da Umma Amarya ta zo da shi.
Na wuce na gama gaida mutanen gida. Ina
fitowa yaya Almu na fara gani ya yi adon karanan
kaya, ya yi kyau har bai yiwuwa in yi ta,kwatantashi.
Yana ganina ya yafuto ni na isa gare shi ya kalleni
cikin nutsuwa ya ce, "Ke kam kin yi sa'a, kunya ta
anini baki da ita, gaba daya 'yanmata sun yi sammako
sun bar gida, ke kuwa kian nan kina yawo cikin
122

mutanen da suka zo bikinki"
Na ce, 'Aa ni kadai ce a gida da za a yi bikina
kai fa?" Ya yi murmushi ya.cc, 'Ai ni ma yanz zan
bar gidan in je yawon bankwana da samartaka in za ki
zo mu tafi.
Na ce, Aa ba inda za ni zan zauna wurin Umma mu yi hirarmu mai dadi.
To shi kenan."
Ya yi maza ya juya ya bar wurin, in duba abin
da ya kore shi cikin sauri haka sai kawai na hango
jerin motoci suna shigowa gidanmu Kawayen Umma
ne ina jin sun shirya isowa tare ne don Kila sune masu
tafiya jere na. Na yi maza na bi bayan yaya Almu na
je na bude motar da na ganshi a ciki Ya yi maza ya
juya kan motar, don barin gidan. Sai ga Hajiya Hauwa
tana shigowa wai maimakon ta yi maza ta wuce tunda
yaya Almu ya kauce mata, sai kawai na ga ta ja ta
tsaya tana tambayarshi.
"Kai Lamido ina za ka kai yarinyar nan? Da ita
fa yau za ni gida, don ban riga na gama shirya maka
ita ba."
Yaya Almu ya yi magana a hankali, "Bari in
fita in gaida Hajiya, don ga dukkan alamu ita ce
Surukar tawa."
Ya fito ya je ya gaisheta cikin girmamawa.
Sannan na ji shi yana ce mata, 'A'a dauko baba kawai
za mu." Ta yi dariya ta ce, 'Alhaji Bello zai hada
iyayenshi aure ai.dole zama ya gagareshi, yana
123

Zumudin kwanannan zai fara ganin kanne." Ta yi
wucewarta, muma muak sa kai muka fita muka hau
hanya. Yaya Almu yana cewa,
"Kina jin abin da ta ce?"
Ban amsa ba ya yi ajiyar zuciya ya ce, Kowa
sha'awar da yake yi mini kenan nima kuma ina yi wa
kaina wannan sha'awar 'ya'ya nake so Rabi ke fa?"
Na ce, 'Uhum ni ba.su damen ba."
Nan da nan ya fusata yana fadin, "Ai ke ba ki
da hankali ke kam sai dai a yi ta yi miki addu'a,
mutum mai hankali ya ce wai haihuwa ba ta dame shi
ba? Ko da yake ma ai ba ki da wani abin mamaki tun
da kin yi mini abin da yafi wannan a gabana ina
kallonki kina kallona kika ce za ki bukaci baba ya
canza miki ni da Junaidu."
Ya ja wani mummmunan tsakin da ya firgita
ni, don kuwa na yi zaton kifa mini mari zai yi bayan
ya gamna tsakin.
Mun dauko su baba muna dawowa shi da
Urmma Amarya suna bayan mota ni da yaya Almu a
gaba, na ce, 'Ai kuwa baba babu wanda zai yi zaton
zuwan ka a yau." Ya ce, eh uwata zumuncin aurenki
ne ya dawo da ni gida, iyayena za su sake haduwa
wuri daya zan sake zama dan gata daga ranar da zi
daura aurenku ni din kuma ba maraya ba ne, ga ku
wuri daya kun hadu sai kawai in yi ta fata da kuam
sauraron isowar kannena, dan haka kuna hade wuri
daya zan gaya muku ban yarda da tsarin iyali ba."
124

Kalaman Baba suka san ya ni jin kunya, nan
take kuma suka sanyaya mini jiki, wato ba yaya Alimu
kadai ne yake bukatar ganinan ina ta haihuwa ba, har
da baba, tuni na san ra'ayin Umma ne wannan.
Muna kawo su baba muka bar gidan, don ya
riga ya cika da jama'a tamkar ba sai rana ita yau ne
daurin auren ba.
Wuni muka yi muna zaga wuraren shakatawa
na ban sha'awa, mafi yawancin hirar yaya Almu a
ranar magana ce kan muhimmancin haihuwa da
darajar ya'ya a wurin iyaye. A duk lokacin da ya kalle
ni kuwa sai ya jadada fadin, "Hakuri kawai za ki yi
Rabi don 'ya'ya da yawa nake bukatar ki haifo mana,
Ummanmu ta samu, Umma Karama ta samu, Umma
Amarya ma." Haka na zuba mishi ido kawai na
kallonshi ban iya cewa komai ba.
Har dare ba mu dawo ba. Hajiya kuwa sau
biyu tana yi mishi waya, "Kai Lamido kafa kawo mîi
yarinyar nan haka."
Ya ce mata, "To ga mu nan zuwa."
Sai wajen karfe goman dare ya ajiye ni a kofar gidanta.
Kwanaki shidan da na yi a gidan Hajlya
auwa sune suka tsareni daga sanir abin da ya rinka
faruwa a gidanmu, na dai san kawai ana sha'ani mai
yawa, don ko ita ma can take wuni, sai dare take
dawowa, in za ta tafi ne dai za ta fara mini jike-
jikenta ta ce wai in yi maza in shanye su kafin ta
125

dawo. Tana isowa kuma za ta tasani a gaba da wasu
kwayoyi ta yi ta sani ina hadiyesu, kamar zakara, tana
kuma kara gaya mini kyan su har tana fadin
Wai wadannan da kike gani kwanan nan za
ki fara nemansu da kan ki in kika gane amfaninsu
daga London na zo da su, saboda ke saura in kin je ya
yi miki tabara ya ce sai kun ci amarci kafin ki fara
haihuwa kull Kika yarda ai kina jegonki kina cin
amarci, ina ganin kin dauki wani lokaci mai tsawo,
ban ji wani bayani ba da kaina zan zo har Kadunan in
same ki, kin san halina sari, don angwayen yanzu
dabararsu kenan, wai a ce amarci kafin a fara haihuwa
to ni ba yarda zan yiba in ma ita Hajiya Zuwairiya ta
yi miku shiru ni ba kyaleku zan yi ba."
Sai ana gobe daurin aure ne aka shirya dawo
da ni gida. Ina jin Hajiya tana yi wa Ummana waya
tana cewa, To uwar angwaye motoci muke so a turo
su zo su dauke mu za mu kawo amarya wurin saka
lalle. Umma tace bazan turo ba in motocin gidanku
ba za su dauko ku ba, ki eike amaryar kar a saka mata
lallen. Hajiya Hauwa ta kyalkyale da dariya ta ajiye
wayarta lokacin ne na gane ita Umma ta tsaya
matsayin uwar angwaye ne kenan, 1yayen amare suna
da yawa, tunda nima Hajiya ce tawa uwar.
Maganar da Umma ta yi bai hana abokan yaya
Almu yin jeri gwanon motocin su a kofar gidan
Hajiya Hauwa ba, dama kuma gidan nata a cike vake
don mafiyawancin kawayen nasu nan suke taruwa
126

kafin su hadu su tafi gidanmu.
Na sha kwalliya sosai, an yi mini gyaran jiki
na ban mamaki, an kuma kawata jikin nawa da adon
lalle mai kyan gani, ga wasu kaya na alfarma da
Hajiya ta sanya mini. Sannan ta dauko mayafi ta
lullube ni ta kuma wuce gaba tana rike da lullubin
nawa ta yadda babu mai iya ganin komai nawa. Ta
wuce muka shiga ni da ita mota, muna baya direba shi
kadai a gaba ya ja muka bi.bayan sauran motocin da
aka basu umarnin su fara tafiya. Sannan wasu suka
biyo bayanmu. A haka har muka isa gida. Wajen karfe
tara na dare aka saka mana lalle gaba dayanmu a wuri
daya aka hadamu aka sanya mana. Muka kuma kwana
wuri daya.
Washe gari da safe ta ko'ina dirin mutane kake
ji alamar dai gidan a cike kwarai yake. Gaba dayanmu
mu shidan muna nan a dakin kowacce ta shiga cikin
nutsuwar ta ni dai babu abin da ya tsaya mini a rai irin
kewar rabuwarmu, shi kenan zaman tae ya kare, sai
kuma zumunci abin da kullum Ummana take gaya
mini kenan.
Ina cikin wannan tunanin sai ga Hajiya ta
shigo cikin wata irin kwalliya ta kasaita tasa katon
mayfinta ta rufe ni ta yi waje.da ni. Sashin Ummana ta
ki ni a wani daki da babu kowa a cikin shi muka
shiga ta ce, "Shiga ki yi wanka ki fito ki shirya, don
mu karbi Fatiha tare." Na fito daga wanka hajiya ta
tasani a gaba tana shafa mini mai tana dariyar abin da
127

ke faruwa a falon Umma, inda wasu suke tambayar
ina uwar Zubairu? Ta yi maza ta ce, "Gani nan." Suka
gaya mata abin da suke nema, ta sa aka yi musu. Ba ta
zauna ba sai ga wasu sun iso.
"ewar Junaidu muke nema."
Ta ce musu, "Ni ce."
Nan suma suka kama bayani. Hajiya ta gyada
kai a hankali ta ce, 'In kika gama wannan bikin
mijinki ne zai ji jiki da ke, mu duk gudu za mu yi mu
bar mishi ke."
Kwalliyar amarci sosai Hajiya ta yi mini.
Karfe goma sha daya daidai aka fara daurin
auren ina kwance a jikinta ina sauraron abin da ke
faruwa cikin zuciyata ina cewa, yau ne zan tabbatar
tsakanin ni da yaya Almnu wake da baba a matsayin
mahaifi? Gaba daya sai da aka yi daurin auren guda
biyar gaba daya kuma mutane daban-daban ne suka
bayar ko suka karba. Sannan sai na ji ana cewa,
"Ina wakiyar Rabi'atu da wakilin Mustapha,
mai bayarwa da mai karba kenan" Sai na ji ana cewa,
To ya yi gasu nan sun zauna, Alhaji Bello Mustapha,
uban 'yar gaba daya, uban angwaye da amaren duka
shi ne da kanshi zai bayar da auren Rabi'atu yayin da
aminishi Alhajin Malle żai karbarwa Mustapha auren."
Ina jin haka na ce shi kenan na rasa baba a
matsayin mahaifi na san babu yanda za a yi baba ya
haifen. Sannan ya zauna ya bayar da aurena a gaban
128

'yan'uwanshi da abokashi bai wakilta wani ya ce ya yi
mishi hakan ba. Hawayc suka zubo mini sharr! Ana
shafa Fatiha Hajiya Hauwa ta kalleni ciki nutsuwa ta
ce, "Yau din nan ranar farin cikin uwarki ne. Ban
yarda ta ga hawayenki ba, ta kuma ga bakin ciki iri-
iri, don haka taimaketa ta girbi alhcrin hakurinta,
koma me ke cikinki watstsake mu yi shagalin bikin
tare, hankalinmu kuma a kwance."
Kalaman Hajiya suka kara fahimtar da ni cewa
bai kamata in bari tUauna ta san halin da nake ciki ba
a yanzu. Ana ta hidimar biki ta ko'ina sai tashin kida
kake ji amare suna can a tsakar gida suna ta faman
cashewa, angwaye da abokansu suna ta yi musu kari.
Ni kam ina daki kwance a jikin Hajiya sai kukan
sharbe nake yi, babu abin da ke kai kawo cikin
zuciyata sai tambayar wane ne mahaifna? Shin yana
raye a duniya ko ya mutu? Shin da gaske Umman ce
ta haifen ko kuwa ma ni din 'yar tsintuwa ce, tun
dama gashi wasu na yi mini łakabin shegiya. To in
kuwa ni shegiya ce ai na tabbatar ba Ummana ce za ta
yi wannan cikin shegen ba, na san darajarta ta. wuce
hakan. Sau. biyu ana aikowa wai a fito da amarya ta yi
rawa, sai kawayen Umma da ke falo su ce a'a a je a
gaya musu .wannan amaryar ba mai rawa ba ce, ba ta
iya ba.
Da daddare misalin karfe takwas aka fara
tafiya kasaitacciyar liyafar da baba ya shirya, don taya
shi murnar auren 'ya'yanshi da ya yi. Ni kam ko
129

goggoron da amare ke sanyawa ban saka ba, katon
gyale kawai Hajiya Hauwa ta miko mini na yi lullubi
da shi, hakan nan da abokan yaya Almu suka nemi a
ba su ni in tafi tare da ango kamar yanda aka yi wa
sauran angwayen, hakuri hajiya Hauwa ta ba su ta ce
musu su je za ta kawo musu ta su amaryar.
Wurin liyafar ya kai ya kawo ko iyakacin abin
da baba ya kashewa liyafar shi kadai ya kashe ya isa a
ce ya kashe kudi. An yi matukar kawata wurin, abin
ba a magana. Angwaye da amarensu suna kan high
table ni kam ina zaune tsakanin kawayen Ummana
Hajiya Hauwa da Hajiya Furera don su suka zo da ni
daga inda muke zaune, ina kallon kowa ina hango
Umma farin cikinta a bayyane yake, shi ma Baba
haka. Na zuba mishi ido ina kallonshi cikin zuciyata
na ce, wannan wane irin mutanne mai iya maida dan
wani ya zama na shi? Ina cikin wannan tunanin aka
fara bude taro da addu'a aka yi ta gabatar da abubuwa
iri-iri kamar yanda aka tsara su. Zuwa can sai aka
nemi mutum daya a cikin angwaye ya wakilce su ya
yi jawabi. Yaya Junaidu ne ya yi hakan. Da ya gama.
ya zauna sai aka,nemi wata daga cikin amare ma ta
tashi ta yi magana a madadinsu. Ban 6ata lokaci ba na
mike cikin lullubina har kasa hawaye suna zuba a
idona na bude jawabin nawa da doguwar addu'ar da ta
sanya gaba daya mutanen wurin suka shiga cikin
nutsuwarsu. Na yi wa Annabin Rahama salati. Sannan
na yi sallama ga 'yan'uwa Musulmi, wanda gaba daya
130

dakin ne suke amsa sallamar, saboda hankulansu sun
riga sun dawo gareni. Na fara gabatar da godiya cikin
harshen turanci amadadin da sauran amare duka ga
1yayenmu da daukacin jama'a maza da mata, wadanda
suka taimaka wajen ganin komai ya tafi kamar yanda
aka tsara shi. Sannan a karshe na ce, zan sake mika
tawa godiyar ta musamman ga iyayena guda biyu da
na sani a matsayin uwa da uba, wato Umma da baba.
Na ce iyayen da suka rike ni, wani irin riko da ya
shagaltar da ni daga tunanin 'WACE CE NI' sai a yau
din nan na bayar da bayani na yarda na girma
gabansu, ban taba tunanin iyaye ba, saboda tsananin
gatan da suka yi mini.
Na fadi yanda zuciyata ta yi ta kai kawo a
iokacin da baba ya ce zai hadani aure da mutumin da
nake ganin ni da shi duk daya, ma'ana dukkanmu
ya'yanshi. A karshe dai na ture shi gefe na kuma
yardarwa kaina cewar ni ce 'yar baba ta cikinshi, sai a
yau din nan da gaskiya ta bayyana.
Dakin ya rabu biyu wasu suna tausayin
jawabin nawa, wasu kuwa dariya suke yi. Na kalli
Wurin da baba yake zaune na ce mishi, "Godiya mai
yawa gare ka ya kai babana, har abada ni a wurina kai
na mahaifina.
Na koma na zauna. ina zama sankiran da ke
gabatar da abubuwa ya mike cikin ajiyar zuciya mai
karfi ya ce, Wohoho! Ga wani jawabi mai ban tausayi
jama'a kalubalane mu mutane nawa ne suke iya yi wa
131


ya'yan da ba na su ba ne irin rikon da yarinyar nan
take bada labarin an yi mata? Ko ni in ban da ita da
bakinta ta fada da tambayata aka yi in fidda mutum
daya tsakanin ita a angon nata wane ne dan Alhaji
Bello na cikinshi ita zan zaba."
Yana gama maganar cikin raha gaba daya
dakin aka kwashe da dariya, ya tsaya yana kallon
kowa tamkar ba shi ne ya yi abin dariyar ba. Sai da ya
ga an nutsu. Sannan ya sake cewa,
To kalubalenmu mu iyaye. Yanzu kuma za mu
sake neman wata daga cikin amare ta yi mana karatu
Alkur'ani mai girma kafin mu rufe taron da addu'a."
Ganin da na yi amaren ba su motsa ba, ya sa na
sake mikewa na karanto ayoyi goman karshe na cikin
suratul Bakara. Sannan na koma na' zauna. Ban san
me, baba yake radawa Umma ba, na dai hange su ne
yana gaya mata wani abu a kunne, ita kuma ta
sunkuyar da kanta kasa, sai murmushi take yi.
Mun fito daga wurin liyafar bayan an rufe
taron da addu'a Hajiyá Hauwa tana rike da ni za ta
shigar da ni cikin motar da muka zo a ciki, don mu
koma gida. Sai na ji yaya Almu yana ce mata.
"Hajiya kin manta ai nine zan tafi da amarya."
Ta yi maza ta ce, "Haka ne Mustapha omantawa na yi."
Ta yi maza ta juya ta sakani çikin motar da
yake tsaye a cikinta kan in ce komai har ya yi maza ya
shige ciki ya zuge gilasan ta bakake ya rankwafo da
132


kanshi jikina ya ce,Y au iyaycn baba sun sake
haudwa. "
Yana fadin hakan ya saki wani kyakkyawan
murmushi ya ce, Ai kin riga kin yi sallama da Umma,
Baba y8 riga ya sallame mu ya ce kowanne ango yana
da 'yancin tafiya da amäryarshi a yau. Junaidu yanzu
yana hanyar airport ya nufa ya ce jirgin dare zai bi a
gidanshi zai yi angwancinshi, nima ban samu jirgin ba
ne mai zuwa Kaduna yanzu da daddare, amma duk da
haka muna da daki."
Ya dauko dan makullin ya nuna mini. Sai da
na ji gabana ya fadi, ya sake kallona ya yi wani
murmushin ya ce,Y anzu can za mu don ki gyara
mini shimfida."
Na ce, "Haba yaya Aimu auren da aka daura
yau shi ne har za ka fara kira mishi irin wannan maganar?"
Ya bata-rai ya ce, To bari in jira sai badi."
Na ce, 'A'a ba haka nake nufi ba, amma dai ka
san, ina da matsala da Umma, ina son ganinta don ta
gaya mini wance ne mahaifina?"
Ya ce, "Ni ba ni da matsala da ita a kan
wannan tun da ni a sanuna mun riga mu warware. Na
ce ni na bar miki baban, kuma ke ma dazu anan kin yi
magana mai dadı' cewar shi ne mahaifinki na har
abada, to ba shi kenan ba?
Na ce, "A'a yaya Almu."
Ya yi maza ya cc, 'A'a kar mu bata lokaci a
133

Kan wannan na vi miki alkawari nan da wata uku zan
kawo ki ki ganta, in ya so lokacin sai ta yi miki
wannan bayanin.
Nan ce, 'To gaskiya ni ban yarda da zuwa wani
wuri ba mu je gida kawai.
Ya sake zuge gilas ya cewa direba shiga ka kai mu gida.
Muna shiga dakin na su al'amura suka sauya,
abin da ban taba tunani ba kwana daki aya da yaya
Almu bai zame mini komai ba an yi hakan yati a
kirga, ban taba ganin ranar da ya dora hannunshi a
jikina ba. Na yi kokarin kwance kaina daga gare shi
na kasa, na kalleshi cikin haki na ce mishi.
Zan yi maka ihu ga su yaya Musa nan a dakin
can su jika."
Da ya dan saurara yana jn maganata yana jin
abin da na fadi. Ya ci gaba da abin da yake yi yana
cewa, "In ihun ya dame su sai su bar wurin, amma ni
kam ai ba ni da matsala, don na dade da sanin cewar
daren farko sau da yawa ba girma da arziki ake yin shi ba. "
Ganin da na yi ya kusa yin galaba a kaina, don
tuni ya riga ya gama zubar da kayan jikina ya sa na
fara rokon shi.
"Kar mu yi dambe da kai yaya Almu, kar ka ce
za ka nuna mini karfi wanka kawai za ka bami in yi
shi ne matsalata, don in ji dadin jikina."
Yana jin haka ya yi maza yay tsallake ya nuii
134

ban daki don shirya mini ruwan wankan. Nima na yi
maza na suri sabon tawul din da ya wurga akan kujera
lokacin muka shigo na daura a kirjina na yi a hankali
na bude kofa na yi waje da gudu. Wurin Ummana na
nufa. Na yi sa'a wurin nata a bude yake daga nesa
kana jiwo kamshin da ke fitowa daga cikin shi, ita
kadai ce a ciki tana zaune gaban madubinta wai
gyaran jikinta take yi. Tana ganina ta saki baki tana
kallona cikin mamaki ta ce,
"A daren nan Adawiyyah ga hadari me ya hana
ki tsaya ki bai wa mijinki hakkinshi?"
Ina jin wannan maganar tata na fashe mata da
kuka na ce, "Umma!"
Ta ce, 'Eh to mene ne Adawiyyah? Nima wurin
mijina nake shirin zuwa me zai hana ke ma ki je wurin
na ki mijin in ya so da safe mun hadu duk wata
magana da kike son mu yi."
Ina kukan na yi mata rantsuwa na oe, "Umma
ba zan taba sauraran yaya AlImu ba. Ba zan taba bashi
hadin kai ba. Ba zai samu abin da yake nema a wurina
ba, har sai ranar da kika yarda kika gaya mini WACE
CE NI?
Umma ta zuba mini ido cikin nutsuwa, kallona
take yi. Wani irin kallon da, ban san me yake nufi ba.
Zuwa can ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ya zama dole in
gaya miki ke wace ce? Tun da an riga an yi iska asiri
kuma ya tonu."
Mu tafi littafi na uku don jin wace ce Rabi'atun
135

tamu?

Na gode.
Ubangiji ya sake sada mu da alheri.

Note:
Kafin úwar Rabi'atu ta gaya mana ita din Wace
Ce? Ke a naki tunanin WACE CE RABI'ATU?
INA SAURARON AMSOSHINKU.
07035586299, 08025078968
Ta ku:
Hafsat C, Sodangi.


136



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa

Please Login or Register in order to submit comment