Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daya ne? To me zai yi wa wata mace
a duniya wanda bai yi miki shi ba?"
Kullum baba ke rarrashina, hirarmu ta koma
hirar bada hakuri. Gaba daya na zube na rasa girmana
da hasken fatata, saboda tsananin bacin rai, abu daya
dai dana rike shi ne ban yarda na daina kwalliya ba,
kullum a cikinta nake.
Rannan bayan fitar Alhaji daga dakina, sai na
dauki buta na shiga wanka, saboda al'ada na gama ga
zaton Karama wani abu muka, ba ta sani ba ni tun
zuwanta babu wani abu tsakanina da shi, da yake ta zo
gidan da girmanta, don ta kai shekaru sha biyar. Ashe
dama ita ake ta son bashi, Baba Rabi ta hana su, kuma
suka ki aurar da ita, shi nema dalilin da ya sa ta yi ta
shige mini tana maida dakina wurin hirarta, don ta
Tinka sa ido kan mu'amallata da mijina. Na fito daga
bandaki sai na same ta tsaye kan hanya na yi kokarin
kauce mata wurin wucewa, amma ina shige ta sai na ji
tasa hannu ta jawo mini zanin da na ruhu da shi.
"Ke ba kya ganin mutane ne kike ture su,
saboda rashin hankali?" Tuni na riga na zo wuya da
ita, saboda irin cin kashin da take kawo mini, don
haka ina juyowa na dauke ta da mari. Ta yi maza ta
103

cakume ni da dambe, don dama abin da take so mu yi
kenan, a ganinta tana da abin da za ta dauka a jikina,
saboda ganin ta fini girma, ga ta kuam da masu mara
mata baya sai sai dai sabanin hakan ne ya faru, don
duka sosai na yi mata, kafin a kai ga raba mu ba a
dauki lokaci mai tsawo bayan yin damben namu
matan gida suka cika a dakinta aka ce wai ta yi bari a
dalilin dukan da na yi mata, sai cewa suke yi,
A'a dama da gangan ta yi ai dama ba ta yi
karin komai ba illa cikin dama so take ta yi sanadin
shi, ita ba ta haifa ba, kuma ba za ta bar mai haihuwa
ta haifa ba."
Aka yi ta wanko jini daga dakin Karama wai
duk jinin barin nc. Haka Alhaji ya dawo saboda kiran
da aka yi mishi, aka yi mishi bayanin abin da ya faru.
Ban taba yin nadama ba irin na ranar na yi ta dana
sanin kulata da na yi, ban san za ta yi bari ba da ban
kulata ba, dana yi tafiyata kawai na bar mata zanin
nawa da ta rike.
Ina zaunc gaban Baba ina ta kuka, shi kuwa sai
caccaka tokar kaskon shi yake yi da wani tsinke yana
wasa da shi, bai kalleni ba. Zuwa can sai ya kallcni ya
ce mini, "Kin dai san ya zame miki dole ki koyi zama
da mutanen .nan tun da dai kin san zan barki a
cikinsu."
Rannan ko barci ban yi ba, saboda tunanin
al'amurana. Baba Rbai ce ta rasu na shiga cikin
wannan halin, to ran da aka ce babu baba fa? Wannan
104

shi ne abin da ya zo cikin raina tausayin kaina ya
kamani ba ni da kowa sai Baba in na rasa shi ina zan
tsoma raina?
A wannan lokacin na shiga kunci mai tsanani
gaba daya dangin Alhaji sun ce sarnun wurina ya yi
yawa, ni ce bakuwa macce ma ba a san dangina ba,
amma har na samu kwarin gwiwar dukan 'yarsu, in
hukunci da aka yi mini bayana. Bayan a wannan
lokacin Alhaji fushi yake yi da ni,, baya ko kallon inda
nake bai kuma cin abincina. Karama ta sake sani a
gaba fiye da kowanne lokaci na yi ta kakkauce mata
musamman da yake an sake cewa tana da ciki, shi
kuwa Alhaji sai faman kai kawo yake yi, ga matarshi
tana da ciki za ta haifar mishi dan dana kasa haifar
mishi. SAi da na kai ma ko girki na dora a kicin sai
Karama. ta kwarawa muruhun ruwa, saboda neman
magana sai dai in je sashin baba in yi girki, don ina
tsoron kar in bar girkin a ce na bar mutanen gida da
yunwa.
Ina zaune a dakina cikin dare sai ga Alhaji ya
shigo a fusace yana yi mini kashedi, ba zai lamunci
abin da nake yi ba, dan an gaya mishi cewa ina neman
in sake yin dambe da Karama, don na gane ciki nc da
ita, wai har, yana cewa shi ya so bai so a fadi tana da
cikin ba, don kar in sani. Na ce mishi haka ne. Ban
sake wata magana ba na ja bakina na yi shiru, ina
kallonshi yana ta maganganunshi bar ya yi ya gaji ya
gama ya kwanta ya yi barcinshi. Gari na wayewa na je
105

na gama yi wa Baba aikinshi na shirya mishi abin
karyawa na. kai mishi. Ina zaune a gcfc ina kallonshi
har ya garna karyawarshi sai na kalleshi cikin cikin
ladabi na ce mishi,
'Baba."
Ya ce, 'Mene ne Zuwaira?"
Na ce mishi, 'Lokacin da Babana ya ce mini
zai kawo ni wurinka ya gaya mini cewar ka san komai
gamc da shi, in na bukaci sanin inda dangina suke za
ka gaya mini?"
Ya daga ido ya kalleni cikin nutsuwa ya ce
mini, "Kina bukatar su ne a yanzu?"
Na yi maza na ce mishi, 'Eh baba." Hawaye
suka zubo mishi sharrr! Daga idanunshi ya ce, Baki
bukaci saninsu a lokacin da zan iya kai ki ba, kin
bukaci sanin su ne a lokacin da karfina ya kare, gaba
daya bazan iya kai ki wurinsu ba, ba kuma ba zan
wakilta wani don ya yi mini wannan aikin ba, amma
ko ni na dade da gane kian bukatarsu don inda a
cikinsu kike to da wadannan abubuwan ba su same ki
ba, don kuwa dangine da ke masu yawan gaske."
Fadin da Baba ya yi cewar dangi ne da ni masu
yawa, amma gani nan ni kadai ban san kowa ba, kuma
ba a tausayina kan hakar kullum sai an yi mini gorin
dangi, ya sa na yi ta yi masa kuka. Cikin sanyin jiki ya
ce mini,
"Hakuri za ki yi Zuwaira ni din nan da kike
ganina ni danginki ne nine kuma uwarki, nine ubanki
106

Zan kuma tsaya miki matsayin hakan a kowanne
lokaci matsalar kawai ita ce zan iya barinki a kowanne
lokaci." Yana fadin haka ya mike tsaye ya fita yana
doddogara sandarshi, saboda rashin karfi ya je ya tura
Kofar baba Rabi ya bude ya shigo yana gyara dakin.
Na bi bayanshi na karbi tsintsiyar na ce mishi, "Bari
in gyara maka Baba."
Bai bari ba, tare muka yi aikin. Sai da muka
gama ya ce mini,.'Dawo nan ki zauna kafin in ga abin
da zan iya yi miki in Allah ya yarda ba zan tafi in
barki cikin wannan halin ba, zan san abin da zan yi a
kai."
Na dawo dakin Baba Rabi na zauna kusa da
Baba, ya kafa mini dokar kar ya sake ganina a wancan
sashin kar in salke tambayar Alhaji komai, komai nake
so in gaya mishi ko gaishe shi bai yarda in rinka yi ba,
babu ruwana da shi. Na ce mishi to Baba. Girki ma
namu mu biyu nake yi n kuma aka kawo mishi na
seshin Albaji sai ya ce a bai wa almajirai shi ya riga
ya koshi, in shiga wurinshi in yi hira in na ji barci in
shiga dakin Baba Rabi in kwanta. A wannan lokacin
babu abin da nake.yi irin tunaninta.
Alhaji ya dawo daga tafiyar da ya yi ta kwana
biyu ya same ni anan ya shiga wurin Baba ya tambaye
shi wai ko ya yi wani laifi ne ya sa ya ce mini in dawo
nan? Ya ce mishi, "Ba ka yi komai ba na nishadi ne
kawai na karbeta tun da dama sanda na ba ka 1ta ai ba
kar ka ce kana sonta ba, hasalima ko ganintä ba ka
107

taba yi ba na daura maka aure da ita, don haka in na
karbeta ai ban yi laifi mai yawa ba ko?
An yi wata biyu Alhaji yana ncman sañin
laifinshi, baba yana cewa bai yi komai ba. Rannan ya
ganshi ya zo zai shiga dakin da nake wai zai yi
magana da ni don ya ga na ki kula shi. Baba ya yi
maza ya dakatar da shi ya ce mishi, 'Kai Bello na
haramta maka shiga dakin nan in kuwa ka yarda na
ganka a ciki to ranka zai 6aci:"
Zamana a wurin Baba sai na samu nutsuwa
hankalina ya kwanta, na yi kiba, na yi kyau, na maida
jikina. Kullum sai ya yi aike kasuwa an sayo mana
nama na gasa mana in ya ga manshanu ko wani abu
zai kare ya yi maza ya bada kudi a sayo mana. Komai
Alhaji ya kawo mana sai ya ce, 'A'a kaiwa iyalinka
kawai, ita wannan na sauke maka nauyinta ni kuam na
yafe maka ba sai ka yi ta wahala da ni ba."
Hankalin Alhaji ya yi mummunan tashi, ganin
irin matakin da baba ya dauka a kan shi. Kowannc
lokaci zai sa shi a gaba yana bashi hakuri, fare da
tambayarshi.
"Baba ita Zuwaira ta ce na yi mata wani abu ne?"
Baba ya ce, 'A'a me ka yi mata? Ai ba ka yi
mata komai ba, dan gata wanda yake cikin dangi ai
shi ake yi wa laifi, amma ba irin ta ba."
Tun Alhaji yana bai wa Baba hakuri yana
rokonshi ya maidani, don gudun 6acin ra baban har
108

ya koma yi yake yi, don yana Son komawar nawa ya
kuma matsa yana son ganina a dakinshi. Baba ya ce,
ina ai an yi wannan zaman an gama in kuskure ya yi
ya sa ya bashi ni, to yana neman gafara,
Rannan na je gaishe shi da safe, sai ya kalleni
cikin nutsuwa ya ce mini, "Na yi niyya zan kai ki
kasarku wurin danginki tun da na ji karfin jikina,
amma ina so kafin mu tafi in sani in munje za ki biyo
ni ne mu dawo tare bayan kin ga danginki ko kuwa za
ki yi zanmanki ne a cikin su? Don in san irin shirin da
zan yi miki."
Na yi kamar in, cewa Baba zan yi zamana ne a
cikin su sai na kasa gaya mishi hakan, don na san irin
son da yake yi mini. Sai na rage murya cikin ladabi na
ce mishi, "Baba ai ni taka ce ba zai yiwu in zartarwa
kaina da wani hukunci ba, sai abin da ka zartar mini."
Ya yi matukar jin dadin abin da na gaya mishi,
ya ce mini, To ni in hukuncina ne ai ba zan rabaki da
Bello ba Zuwaira, ai duk wannan abin da ke fruwa
kuriciya ne da kuma halin zama na yau da gobe,
saboda haka kai ki kawai zan yi ki gan su in dawo da
ke."
Jikina a sanyaye na ce mishi, "To Baba." Duk
da dai ni kam da ba haka na so in ji ya ce ba.
Ya yi ta shiri babu abin da bai shirya ba na
dukiya da zai rike a hannunshi. Alhaji ya gane abin da
Baba yake nufi ya tasa shi a gaba da roko da ban
hakuri, gashi ya hana shi shiga dakin da nake, ni
109

kuwa ina ganinshi sai in kule ciki ba halin ya yi mini
magana.
Ana gobe za mu yi sammmako mu tafi, da
yamma sai ga liman yana sallama da baba a waje. Kai
tsaye baba ya ce mishi ya shigo. Ya shigo sashin shi.
Na yi musu shimfida suka zauna na durkusa na gaishe
shi. Sannan na koma daki.
Liman ya kalli Baba ya ce mishi, "Haba malam
Mustapha wane irin laifi ne yaron nan ya yi maka
haka da aka rike mishi matarshi wata da watanni ka
hana shi ita. Sannan yanzu wai kana shirin maida ita
can wani wuri."
Baba ya gyara zama ya kwashe labarina duka
ya bashi, bai rage mishi komai ba. Sannan ya ce, To
tun ina raye ma kenan ta shiga wannan hali, to in ba
na nan fa ya ya za ta yi?"
Liman ya jinjina al'amarin ya ce, "To babu
komai al'amarin duka ba namu ba ne, ka yi hakuri ka
bar mishi ita kar ka raba su ai fushin zuciya ba na ka
ba nc, kai addu'a ce kawai ya' dace ka yi ta yi ita din
yana da kyau ta san danginta, amma ba a irin wannan
tafiyar ba, in ka maida ita dakinta aka zauna lafiya sai
ka sa mijinta ya kai ta."
Ina jin baba ya amsawa Liman ya janye tafiyar
na yi ta kuka, shi kuwa Liman ya yi ta yi mishi
godiya, ya mike zai tafi yana jaddada mishi, "Ka
mayar mishi da matarshi yana." Yana cewa to.
Da daddare Alhaji ya dawo yana murna, don
110

liman ya yi mishi bayanin yanda suka yi. Ya zo wurin
Baba yana tambayar to yaushe zan dawo dakina? Ko
kallon shi baab bai yi ba ya ce mishi, 'Sai ran da
matarka ta haihu tukunna ba za ta koma a tsokane ta a
yi dambe danginku su ce ta zubar da ciki ba, tun da ita
na ta cikin a tafin hannu yake baya tashi kifewa sai an
yi dambe da ita. To ku je in dai lissafin na ku irin
nawa ne ai cikin ya yi wata bakwai, yanzu in ma bai fi
ba, tun da ko zaman Zuwaira a nan wata hudu ne har
da kwanaki."
Maganar in koma dakina ya zama wani babban
al'amari. Abin da Alhaji yake ganin ai zancen ya kare
tun da har gashi an fasa maida ni, kuma an yarda za a
maida ni dakina. Rannan dai ya gaji ya samu Baba a
dakinshi muna tare, gasa mana naman rago nake yi a
kan tire yana tayani jujjuyawa yana cewa saura nan
din, nan bai gama gasuwa ba. In ce mishi to in juya.
Alhaji ya shigo ya gaishe shi ya ci gaba da tsuguno,
shi kuwa baba ya yi kamar bai ganshi ba. Sai da ya
gaji ya ce, "Baba ina so ne in roke ka ka yi hakuri ka
yafe mini laifin da na yi ka bar Zuwaira ta koma
dakinta, kar ka ce sai Karama ta haihu, ni ban san
ranar haihuwar ta ba, tun da jiya na tambaycta lissafin
cikin kama-kame kawai take yi."
Baba ya ce, 'Ai ya." Ya ci gaba da sauraron shi
sai da ya ji ya gama duk bayanin da zai yi Sannan ya
dauko mishi dogon tarihi tun farkon gamuwarshi da
Babana, mu'amallar da ta hada su, da dadéwar da suka
111

yi ba su sadu ba; amma duk da haka ya yanke
shawarar zabenshi a matsayin mutumin da ya dace ya
bai wa amanar'yarshi da dalilin da ya sa shi kuma ya
zabe shi ya bashi aurena, amma kuma akan idonshi ga
abin da yake fruwa. Ya lissafawa Alhaji tas din abin
da aka rinka yi mini wanda ni ban ma san ya sani ba,
da ya gama sai ya ce mishi,
"Wani ciki ne da ita? Matarka ba ta taba yin
cikin ka gani ba, shi ne ba za ka lura ka gane ba, daga
karya kawai?"
Ni kaina ban taba zaton cikin karya Karama ke
yi ba, sai a wannan lokacin.
Alhaji ya ce, To ka yi hakuri baba ka barta ta
dawo dakinta yau."
Baba ya yi maza ya ce, 'A'a ba za ta shiga
wannan kurar ba sai an samu okaci an gyara tukunna
in na nutsa zan samu musu gyara mata in ba su su yi."
A haka ya mike ya tafi.
Kwana biyar bayan nan sai ya dawo ya samu
Baba ya ce mishi, "Yaushe ne komawar tata?" Baba
ya ce ai har yanzu bai samu gyara mini dakin ba.
Alhaji ya ce mishi, "Na gyara Baba kullum cikin dare
nake bude dakin in shiga in yi ta gyarawa sai Asuba ta
ksua in fito, to jiya har kayanta na bayar a wanke
saboda kura, nan dawo da su yanzu ka tura ka gani
komai tsab yake cikin tsabtarshi"
Baba ya yi murmushi ya ce, "Lallai kana so
matarka ta dawo, to za ta dawo sai ka yi ta hakuri ka
112

hada su dukansu ku zauna lafiya."
Bayan fitar shi ne baban ya kalleni ya ce mini,
"To yaushe za ki koma dakin ki Zuwaira." Na cc sai
karshen wata. Ya yi maza ya ce, 'A'a kul na ji kin yi
wannan maganar yanzu dai yau ki kara lallenki ki
tusashi ya yi sheki da safe sai ki je wurin Bilki ta yi
miki kitso tun da dama ita ke yi miki da daddare kuwa
sai in kirata in sata ta raka ki dakin ki, nima in ji dadi,
don dama a kan dole na ke rike da ke tun da na san ba
ni da 'yancin rike mishi matarshi. Ke matarshi ce yana
kuam son ki fiye da komai, don haka ko bayan raina
na yi miki umarnin ki yi hakuri da shi, ki kuma
ragewa kan ki kishin da ke damunki." Na ce mishi to.
Washe gari ko fita Alhaji bai yi ba ya makale a
dakin baba watakila gani yake tamkar in ya fitan wani
dalili zai sa baban ya fasa maida ni dakin nawa.
Da daddare na yi wanka na yi kwalliyata cikin
sabuwar atamfar da ya saya mini na ci abincina ni
kadai, don dama ya fitar da ni cikin cin abincin
taraiya. Yaya Bilki ta zo kamar yanda ya yi mata
umami ta rakani dakina.
Ranan na samu Alhaji cikin doki da zumudin
samuna tamkar dai a ce ranar ne ya fara sanina. Zan
iya cewa kusana wannan lokacin ne muka yi
amarcinmu da Alhaji, don a farkon aurenmu shiriritar
kuruciya ta hana ni in sakar mishi komai nawa ya
morewa aurenshi.
Rannan ina zaune wurin baba da hantsi muna
113

hira atishawa nake ta yi, sai ya kalleni ya ce mini, Wa
ya sani ma ko wani rabo ne ya tunkaro ya sa Bello ya
nacewa komawarki a lokacin nan Na yi murmushi
na ce mishi, "Ba komai baba.
Ya ce, To ki yi hakuri ko wata ta zo ta haihu
sai ki tuna kin haifa kafin ita, kar kuna ki yarda ki
dagawa mijinki hankali, kar kuma ki lura da abin da
na yi mishi a kan ki ki ce z8 ki wulakanta shi, ki
girmama shi, ki guji bacin ranshi, ki sani baki da
wanda yafi shi. Ban kuma bashi ki ba sai da na san
cewa shi ne wanda zai iya rike mini amanarka, ko
bayana kin ji ko ba ki ji ba?" Na ce mishi na ji baba.
Alhaji ya yi juyin duniya ya zauna da Karama
lafiya abin ya gagara, saboda ba yanda take so ya yi
mini yake yi ba. Gaba daya hankalinta ya tashi, ita da
take sa ran za a maidani wurin dangina hakan bai
yiwu bas, gashi kuma ba zato ba tsammani na dawoo
dakina. Hankalin mijina kuma ya dawo gare ni,
lokacin ne ta ganc a wancan lokacin ni ce na
taimaketa ita da mukarrabanta, har suka samu suka
sha gabana a wurinshi, yanzu kuwa na sa hannu biyu
na karbe shi na kuma janye daga jin takaicin aurenshi,
na yi niyya zan kyautata zamana da shi ne kawai, don
na riga na kara sanin ba ni da kowa sai shi in kuma
baya tare da ni to ba karamm tozarta zan yi ba wurn
'yan'uwanshi, masu son ganin iyakata. Babu yanda ba
a yi ba a hadani da shi abin' ya gagara, kullum ya
shigo dakina na san yanda zan yi in watstsakar da shi
114

daga duk wata damuwa da ya zo da ita, don haka in
yana dakin kowanc lokaci cikin murmushi za ka
ganshi. Ni da Karama kuwa ko kallon inda take ba na
yi in gari ya waye na ce mata ina kwana? Sai kuma
gobe in za ta Wuni tana zage-zagenta kuwa ba zan
kulata ba.
Rannan dai aka wayi gari a kan dole a ka ce
Karama ta yi bari tun da ba a samu an yi dambe da ni
ba, na ki yarda gashi kuma a lissafi ciki ya kai
watanni tara. Jini ya yi ta gudu a tsakar gida ana
kwara ruwa, ana wanke shi. Alhaji ya shigo gidan
fuskarshi a daure alamar dai bai ji dadin 6arin da aka
je aka ce mishi ta yi ba. Yana tsaye a tsakar gidan ya
fara tambayar matar yaya babba wacce dama ita ce
uwar dakinta.
"Ina dan yake?"
Ta yi maza ta soma yi mishi bayani.
"Wane da ake maganar shi, wannan ciki da ya
rididdige ya fadi a hankali ba a sani ba, ashe an dade
da sa mata hannu a kan shi."
Maganar tata ta kara fusata shiga sakin
maganganu. Ina jin haka na yi maza na kulle kofata na
tafi wurin baba na ba su wuri. Ban dawo ba sai da ya
zo can din ya same' ni. Saanan muka dawo tare.
Sati guda bayan nan aka zo aka tattara Karama
aka tafi da ita bisa dalilin wai ansa mata hannu cikin
ta ya lalace, amma ba a kula da ita ba, ba a kuma.
dauki wani mataki ba na yin maganin hakan. Baba ya
115

ce ai ba ni ce na sa mata hannu ba, sh1 ne tun da ni
kam wa nake dashi da zai yi mini wannan aikin? Sun
yi zaton Allah zai yi ta zarya a kanta, su ma su ja
mishi rai, kamar yanda suka ga baba ya yi mishi, shi
kuwa sai ya yi banza da su.
Rannan ina zaune wurin baba ina gyara mishi
farce, sai ya ce mini, "Ni kuwa wata shawara nake so
mu yi da ke duk da dai na san kishinki yawa ne da
shi"
Na yi murmushi na ce mishi, 'Gaya mini baba."
Na yi zaton zai yi mini maganar dawowar
Karama ne sai na ji ya ce, 'Shekaran jiya Liman ya zo
wurina ya gaya mini cewar 'yarshi za ta fita taka ba
gobc, shi ne nake tunanin ko zan gaya wa mijinki ya
je ya ganta ne? Kin ga yarinya ce karama, bab ia fi
Karama ba. Sannan tana goyon danta na fari, ga
wadannan fitinannun mutanen da kike tare da su ba za
su bar ku ku huta ba ke su tasaki a gaba da fitina, shi
su tasa shi a gaba da karyar ciki. Na ce ko zai aurota
ne? In ya yi sa'a sai ta haihu ke ma in kuka zama ukun
za ki dan samu saukin abubuwa in ba ki shirya da
wata ba, za ki shirya da wata."
Ban yi musu ba na ce mishi to Baba.
Kwana uku ne, kawai bayen nan sai aka yi
daurin auren Alhaji da Maryam, don shi bai je ganinta
ba, da Baba ya gaya mishi kawai sai ya ce ba sai ya je
tadi ba, a sanar da liman kawai a ji abin da zai fadi.
Ana gaya mishi kuwa ya ce gobe a dawo daurin
116 auren.
Labarin auren Alhaji ya zamo kwaram a gidan
nan gaba daya hankula suka tashi, saboda babu wanda
ya yi zaton hakan, su suna jiran ya zo biko ne su
gindaya mishi sharudda, wai har suna cewa ai nimna
ba daga tafiyata ya kidime ba, sai da baba ya shiga ya
fita. Sai kwaram suka suka ji zancen aure. Ranar
kuma da yamma baba ya yi amfani da taron da aka yi
na murmar auren da Alhaji ya kara ya tara gaba daya
ya'yanshi maza da mata, ya kuma aika aka kira mishi
aminanshi da sukai saura ciki har da liman. Gaba daya
sai da aka taru. Sannan ya ce a dauko mishi abin
rubutu, a rubuta. A ka je aka dauko abin rubutu ya
mikawa Yayan Tudu ya ce,
"Dukkan ku ku shaida don shi ne dalilin da ya
sa na tarakun ku zamo shaidu kan cewar ko bayan
raina wannan daki nawa da nake ciki da kuam
fadamar rakena da ke kofar yamma basa cikin abin da
magada za su gada na dukiya na bai wa Zuwaira su,
daga yau su din mallakinta ne, na kuma bata šu ne tun
ina raye, saboda na san ba ta daga cikin wadanda za
su ci gadona, gashi kuam ita din 'yata ce da amana ya
bani."
Ya sake nuna wata saniya da danta tare da
wani bijimi ya ce, "Hakan nan wadancan shanun nats
ne, sanda mahaifinta ya kawo mini ita ya bani
dukiyarta ya ce in rike in loakcin hidimar aurenta ya
zo a yi mata da su, don haka babu komai nawa cikin
117

kudin kayan dakinta da kudinta na yi mata hidima, ni
dai na dauki nauyin ciyar da jama'a ne kawai a
lokacn tun a sannan kuwa na gaywa wasu daga cikin
ku hakan. Bayan an gama bikin ne na gayawa Rabi
cewar ga sauran kudinta da sukai saura sai dai babu
yawa, ta ce mini a sayo mata tunkiya a daure mata. To
da ta yadunc aka sayar da su aka sai mata karsana a
kan idonku ne kuma ta haifi wannan ta yaye shi, ta
kara wannan. Na roke ku kar ku zalunccta a bayana,
ita ma yar uwarku ce don ba ta da kowa sai ku."
Daga Karama har masu tsaya mata babu wanda
ya furta wani abu kan wannan kyauta da baba ya yi
mini, don sun riga sun ga abin da ya firgita su. In da
da nc kuwa kafin auren Alhaji baba ya yi mini
wannan kyautar da sun ce ya yi bambanci tsakanin
matan danshi a wannan lokacin kokarinsu bai wuce
Karama ta dawo katin tarewar amarya ba, wacce aka
dibar mata kwana bakwai kacal. Shi kuma Alhaji ya
ce ta yi zamanta tukunna sai amarya ta zo ya ga
kamun ludayin zamana da ita kunna, don yana son
gane waye mai fitina a tsakanina zaman. Baba ne ya
ce a'a kar ya yi haka ya barta ta dawo dakinta shi dai
kawai ya zama tsayayye kan lamarin gidanshi. Ya ce
mishi to.
Karama ta dawo da kwana biyu. Ita ma amarya
ta iso ta kuwa iso cikin matsananciyar gata, ita ma dai
kam mai dangin ce. Da yamma kafin zuwan nata baba
ya kirani ya ce mini, "Wani alheri nake so ki yi mini."
118

Na ce mishi, To baba." Ya kalleni cikin
nutsuwa ya ce mini,
"Hakuri za ki yi ki dauki nauyin da yake kan
ki duk da ke din kin yi wa hakan kuruciya, ita wannan
amaryar liman ya

Please Login or Register in order to submit comment