Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a
dakinsu. Ina shiga na Tsugunna ina sauraron shi ya
kalleni cikin nutsuwa ya ce mini,
Rabi kina sanin saura kwana nawa ne bakinmu kuwa?"
Na zuba mishi 1do ina kallon shi, na ce, To
52

mene ne?"
"Ban taba ji kin ce mini komai ba."
Na kalle shi na ce mishi, "Ni yanzu ai ba biki
ne a gabana ba, muhimmin abu a wurina shi ne in san
asalina, in san waye mahaifina. Sannan ma ni yanzu
auren naka baya gabaná, don na gane matsala zai
zamo mini mai girma, saboda haka na ce zan ga baba
in roke shi in ya zo daurin auren ni ya bai wa Yaya
Junaidu kai ya ba ka Rahama ko kuma.."
Da sauri Yaya Almu ya shiga cewa, "Ba ki da
kai Rabi, ke ba ki da hankali, to in baki sani ba ma
yau in gaya miki ke da Junaidu babu aure a
tsakaninku."
Na yi turus ina kallon Yaya Almu, yayin da shi
kuma ya riga ya fusata da jin cewar zan bukaci a
canza mini shi. Na ce mishi, "Yaya Almu...
Bana so kar ki gaya mini komai, je ki ki
bukaci baba ya eanza miki ni, ni ba na bukatar canji a
kan ki ke nake so, ba kuma zan bukaci a canza mini
ke ba. Ni tun kina 'yar jaririyar ki na ke son ki ban
kuma taba dainawa ba. Je ki ki bukaci canji a kaina,
in ba ki yi haka ba ai ba zan gane irin kiyayyar da
kike yi mini ba."
Na soma yi mishi kuka, saboda ganin irin
fadan da yake ta yi mini. Na ce, Kana sona tun ina
yar mitsitsiya, amma kake rerawa Aina'u wakoki a
gabana? Ko ba ina nan a gidan nan ba kuke musayar
Wasiku a tsakanin ku? Ko ban sha ganin wasikunta a
53

dakin nan ba? Ba ka sha jaddada mini irin son da kake
yi mata ba? Don me ba zan nemi canji a kan ka ba?
Shi na taba jin shi yana ambaton sunan wata budurwa
ne? Kai ne kake son Aina'u kake son Uwale, na ga
abin da Aina'u ta yi mini a kan sonka da take yi, ita
ma 'yar uwata kenan saura Uwale, ita kunma ban san
wanda za ta yi mini ba, in mun gamu.
Cikin nutsuwa ya soma yi mini magana,
"In kin ji ina yi wa wata maka Rabi tsokánarki
kawai nake yi, don in lura da kishinki a kaina, ba zan
yi mik musun kina ganin wasikunta anan ba, amma
zan yi miki musu idan kika ce kin taba ganin
wasikuna a dakin ku. Maganar Uwale kuwa ba ni da
wata Uwalen da ta wuce ki Rabi, ni ke ce Uwalena in
kin yarda da wannan bayani da na yi miki to ina so ki
kwantar da hankalinki ki toshe kunnenki ki daina
sauraron duk wani zance da wani zai gaya miki kina
nufin in ni zan rude ki Umma ma za ta rude ki? Har
Baba ma ya yi miki hakan?
Na yi maza na ce mishi, 'A'a.
"To ji ki ki shirya maza ki zo mu fita ki yi mini
rakiya."
Na yi shiru kawai na mike na fita. Na zo na
samu Umma zaune a feionta na zauna rnima kusa da
ita na kalleta na dan yi murmushi, don ta san a cikin
kwanciyar hankali nake. Ta sake kallona cikin
nutşuwa ta ce, 'Mene ne Adawiyya?
Na ce, 'Ba komai Umma so dai kawai nake yi
54

in tambaye ki ni waye ma ya haifi Yaya Junaidu?
Babu wata damuwa ta ce mini,
"A'a yau kuma ba ki san uban Junaidu ba?"
Na ce, "Eh Umma gani nake kamar ba hakan ba ne mantawa na yi."
To Alhajin Tudu ne wan Alhaji, wanda suke
uwa daya, uba daya amma akwai mace a tsakaninsu
ita ce yaya Lami, mahaifiyar Aina'u. Wannan dogon
bayanin da na jaddada miki ya gamsar da ke?"
Na ce mata, "Eh Umma."
Na dan sake kallonta na ce mata, "To nima
Baban Tudun ne ya haife ni? Ta girgiza kai nuna
alamar a'a. Ta sake kallona cikin murmushi tare da
sansanyar ajiyar zuciya. Sannan ta sake kallona cikin
nutsu wa ta ce, "In Alhajin Tudu ne ya haife ki da wani
wanda ya isa ya ce ke ba 'ya ba ce a gidan nan?"
Nan da nan na ga kuma ch haka ne. Na sake
kallonta na ce, "To Umma gaya mini abu daya ni 'yar
ki ce?" Ta yi maza ta ce mini,
"Kwarai da gaske."
Na sake cewa, "Ke kika haife ni?". Ta zuba
mini ido cikin nutsuwa ta ce,
"Kina tantamar hakan ne?"
Na ce mata, 'A'a. To amma Umma...."
Ta ce mini, "Ke nake sauraro."
Na ce,"Nuna mini nankarwar ki."
Ta yi maza ta ce, 'Yanzu kuwa."
Ta sa hannu ta kwaye shimin da ke jikinta..
55

Gasu nan rada-rada, kwance a kasan cikinta, har zuwa
gefen cinyoyinta. Cikin zuciyata na ce tabbas wannan
nankarwar da kan samu ne ta dalili haihuwar da ba ta
halittar ba, Dadi ya kamani cikin zuciya na tabbata
Ummana ita ce ta haifen. Na kalleta na yi murmushi
na ce,
Umma."
Ta tayani murmushin ta ce, 'Mene ne
Adawiyyah?"
"Ni tun da dai ke kika haifen to magana ta kare
komai mam zai biyo baya to ina ganin shi din mai
sauki ne, zan iya hakuri in aka ce ba baba ne ya haifen
ba, amma ba zan iya yin hakurin akan ki ba."
Umma ta sa hannu ta jawo ni jikinta, na
kwantar da kaina a gefen kafadarta cikin murya mai
sanyi na ce mata, Ina jin mamakin abubuwa da suke
fitowa kwanan nan a kaina Umma, na yi iyakacin
tunanina na kasa gano dalili a ce wai aure ya haramta
tsakanina da yaya Junaidu, ya kuma halarta tsakanina
da yaya Almu. Wannan ba abin mamaki ba ne?"
Ta yi maza ta bata rai ta ce, 'Eh abin mamaki
ne sai ki je ki.yi ta bincike kina jiwo abin mamaki iri-
iri."
Na ce, Ba bincike ba ne Umma..."
Ta ce, To wannan magana ta ishen haka."
"To Umma." Na ja bakina na yi shiru.
Shirin biki na sosai da sosai Umma ke yi. In
tsaya kwatanta lamarin ma bata lokaci ne, a kowanne
56

lokaci cikin biki take, a kowane lokaci kuma a kan fita
take, saboda al'amuran da ta ke gudanarwa ita da
kawayenta guda biyu wadanda suke sune na hannun
damarta, suka tafi Dubai, don sayayyar kayan dakin
amare, wato Hajiya Hauwa da kuma Hajiya Furera.
Ina kwance ni kadai a dakinta, saboda tafiyar
tasu sai na ji kadaici ya dame ni na tashi na jawo
suwaita na dora kan doguwar rigar da ke jikina na fito
waje ina tafiya ni kadai nufina in isa wurin baba
maigadi in zauna in taya shi hira, sai na hango yaya
Junaidu yana tsaye jikin kofar motarshi da ke bude
hankalinshi kuma ya tafi wajen kallon wani abin da ke
zaune cikin motar. Da sauri na nufi wurin nashi, don
ganin mene ne? Ina isa wurin na gaishe shi ya dago
kai ya kalle ni cikin murmushi ya ce da ni,
"Adawiyyah kin fito ne?"
Na ce mishi, "Eh."
To kun gaisa da Rahama ne?"
Lokacin ne na lura ashe ita ce a cikin motar ita
yake yi wa wannan karkacewar da na ganshi yana yi.
Daga inda nake tsaye na ce mata, Sannu Anti
Rahma." Ta amsa cikin wata irin muryar da ban taba
sanin tana da ita ba. A zuciyata na ce a'a har yaya
Junaidu da aka girma a gabanshi sai,an yi mai wannan
kashe muryar? Na dan yi murmushi, Yaya Junaidu ya
kalleni ya taya ni murmushin ya ce, 'Ai yan matan
dukansu tuni suka watstsake suka shiga hidimar bakin
su in da za ki leka dakin baki yanzu da za ki samu
57

Alna'u da Basira suma samarinsu sun zo. Kabiru da
Rashida kuwa tun safe suka bar gidan nan, Mustapha
ne shi kadai ga shi can a bayan motarshi yana zaune
ko za ki je mishi hira ne?"
Na yi kamar in ce mishi to, sai kuma na ji ina
Son komawa wurin mu. Na ce mishi, 'A'a Yaya
Junaidu." Na yi ma Anti Rahma sai da safe na juya na
koma wurinmu. Ina shiga sashin Umma na ji jikina ya
bani an shigo wurin. Na ja na tsaya ina kallon kofar
falonta da ke rufe kamar yanda na bar shi. Shiga
sashin Ummana ba komai ba ne, don wuri ne na
mutane ko tana nan ko ba ta nan. To amma wannan
karon sai na ji kamar ba irin shigar da aka saba yi ba
ne. Ina cikin wannan tsayuwar na hangi inuwar wani
ta bayan dakinta. Da gudu na fita ina ihun barawo!
Barawo!! Da iyakacin karfina.
Gaba daya samarin gidan manya da yara dama
duk wani wanda yake cikin gidan aka firfito. Yaya
Almu ya bai wa Baba maigadi umarnin rufe get kar a
bar kowa ya shiga ko ya fita.
"Barawo ki ka ce Adawiyya?" Yaya, Junaidu
ya tambayan jikina yana bari na ce mishi, "Eh a sashin
Umma na gan shi."
Shi da Yaya Almu da yaya Harnza suka taso ni
a gaba saura kuma suka ce su tsaya a nan, don kar
wani ya ce zai zo ya fita, tun da katangar gidanmu dai
babu mai iya tsallake ta. Muka isa sashin Umma na ja
na tsaya daga nesa na nuna musu ta inda na hango
58

inuwar suka je suka duba suka dawo, suka ce babu
kowa.
"Anya ba tsorata kawai kika yi ba Adawiyyah?"
Yaya Almu ay ce, "An shigo ga alamar kafa a nan,"
Gaba daya suka sake zubawa wurin ido. A
hankali suka rinka bin takun suna dubc-dube zuwa
can yaya Junaidu ya ce, Zo nan Mustapha ba a yi
wani abu a wurin nan ba? Da sauri ni da yaya Hamza
muka karasa wurin na su, yaya Almu ya kalli Hamza
ya ce mishi, "Yi gudu ka kira mallam tare da baba
maigadi, su Musa kuam su tsaya a get kar su bar kowa ya fita ko waye shi"
Su baba maigadi da maiam suka iso.
'Malam ba a yi tono a wurin nan ba?" Yaya
Almu ya tambaye shi. Ya ce, Eh to da alama dai kam
an yi."
Baba maigadi ya co, Eh to ai da akwai baki a
gidan shekaran jiya kun tafi kai Hajiyá airport su
kuma aka shigo da su."
Yaya Junaidu ya kalle shi ya ce, 'Amma shi ne
ka yi shiru ba ka fada ba'?" Ya kara rage murya ya ce,
'Ai na gane an saba kawo irin su, su gama, kwanakinsu
su fita, ita kuam Hajiya nan ba mai yarda a rinka
kawo mata irin wadannan laburan ba ne."
Yaya Almu ya nemo shebur ya shiga kwashe
kasar wurin. Tuno sosai aka yi aka tarar da wata
59

katuwar kwarya. Yana daga kwaryar sai ga dan
kunkuru mai rai a kife. Gaba daya wuri ya dauki
salati. Ni kam kuka na kama yi. Ya sa hannu ya dauko
dan kunkurun wanda ni tsoro ya hanai kare mishi
kallo, balle in ga abin da ake cewa an rataya mishi.
Malam ya karbi dan kunkuru shi da baba maigadi
suka tafi bayan sun jaddada muhimmancin a yi shiru
kar a tada maganar.
Yaya Junaidu ya kalleni ya ce, "Mu je can ki
kwana a wurin mu. Ita ma baba Talatun da take tayaki
kwana ta kwana a wurin su kawai a rufe nan din."
Na ce mishi, "To."
A dakin su Yaya Almu ina kan katifarsu su
kuwa hirarsu suke yi a kan kujera. Farkawa kawai na
yi cikin dare na ga ni kadai ce a dakin, amma ban
tsorata ba don gaba daya wannan sashin nan samari
ne. Ina kwance idona biyu ina tunanín abin da ya faru
sashin Umma.
"Yau me ake nufi da wannan abin da aka yi? A
kashe ta ko a yi mata me? Aurena da yaya Almu ne
kawai ya jawo hakan ko kuwa dama can ana yi sani ne
kawai ban yi ba?"
Hawaye suka suka yi ta zubowa a idona,
saboda tausayinta da ya kamani, abin da na sani shi ne
Umma zaune take zuciya daya da kowa, amma kuma
ita ake zargi wai mai magani ce ta mallake baba, sai
yanda ta yi da shi. Ina cikin haka na ji kamar ana
magana a waje. Da sauri na.tashi na sanya suwaitar da
60

hular sanyina na fita. Wurin baba maigadi na nufa,
don can na hango mutane a tsaye. Wasu mutane ne su
uku sai zazzare 1do suke yi, alamar rashin gaskiya, shi
kuwa baba maigadi yana zaune hankalinshi a kwance.
"Ba zan bude gidan ba, sai gari ya waye yau
ma,"
Umma Karama ta iso wurin tare da wani
alamar kiranta ya je yi, ganina a tsaye ya sata ta yi
wani iri alamar rashin jin dadi.
"Maigadi ka ce ba za ka bude musu ba? Bayan
ni na ce ka bude musu?"
Ya ce, 'Ki yi hakuri Hajiya Lamido ne ya ce
kar a bude sai gari ya waye tukunna.
Ta daka mishi tsawa, 'Na ce ka bude musu da
umanina da na Lamido wanne ne gaba?"
Yaya Almu ya fito daga dakin baba maigadi,
ashe dama yana ciki ya ce mata.
"Ki yi hakuri Umma ba umarnina ba ne,
umamin baba ne ya ce kar wanda ya shigo mishi gida
bayan karfe goma, kar kuma a bar kowa ya fito bayan
wannan lokacin. Yanzu karfe biyun dare ne an zo ana
cewa a bude mishi gida kuam su wadannan mutane
Idan gari ya waye zan hada su da hukuma nc, don su
amsa tambayoyi kan abin da suka shigo mana gida
babu izinin mu, suka keta mana haddin gidan. Bayan
haka suna cikin gidan nan dazu aka yi ihun barayi,
duk wani wanda yake cikin gidan nan ya fito, amma
Su ban gan su ba, don haka ban yarda da su ba."
61

Umma ta soma fadin maganganu. Ya ce mata,
"Ke uwata ce Umma, don haka na roke ki ki yi hakuri
ba zan yi komai don cin mutuncinki ba, abin da kike
tunani a kaina kuma ba haka ba ne, ni na kowane a
gidan nan duk wanda yake ciki nawa ne, ba ni da wani
bangare in kin ga ana yi miki wani abu wanda bai yi
miki daidai ba gaya mini na yi alkawarin zan yi miki
maganin abin ko waye mai yi mikin, kai ko baba ne ki
gaya mini, don shi mai karbar nasihar na kasa da shi
ne."
Yaya Kabiru ya fito da moto ya zo ya tsaya.
"Su shiga mu tafi."
Da sauri ta ce, "Ina?"
Yaya Almu ya ce, Police Station za'a kai su,
don su yi bayani."
Jikin Umma ya yi matukar yin sanyi ta kira
yaya Almu yabi bayanta suka tafi. Nima na koma daki
na kwanta, sai dai ba barci na yi ba, har gari ya karasa
wayewa, idona biyu. Sai da gari ya waye na fito bayan
na gama komai na kimtsa sashin Ummana na nufa don
in ga abin da ake ciki. Yaya Almu na samu a wurin
ko'ina a bude yake gaba daya kayan sashin Umma an.
yi waje da shi. Cikin nutsuwa ya kalleni ya ce mini,
"Kin karya ne?"
Na ce mishi, "Eh."
To ki koma can, nan ba ki ga ana aiki ba?"
Na koma na je na gaida Umma Karama, na
kuma tafi dakinsu Baba Talatu na hau gadon ta na
62

kwanta. Na kwanta muna hira da ita ta ce mini, "Au
dama can haka ake zaune in ba a binne wannan ba yau
gobe za a binne wancan. Na da bai yi komai ba, ai na
yanzu ma ba zai yi ba."
Na ce, 'Haka ne."
Muka yi hirarmu. Ban fitò ba sai da yaya Almu
ya aiko ya ce a kira ni. Na same shi a motarshi cikin
kwalliya sosai, ga kamshin shi mai dadin ji.
"Shigo mana unguwa,za ki raka ni." Na yi
maza na shiga, saboda ina nson tambayarshi labarin
mutnaen nan.
Muna tafiya muna hira na ce mishi, "Yauwa yaya Almu."
Ya ce, 'Na'am Uwale."
Na yi maza na ce mishi, "Kai! Kai!! Yaya
Almu gaskiya ba na son wannan sunan ko baba ma
Uwata yake kirana ba Uwale ba."
"To, to shi kenan Adawiyya."
Na ce, "Yauwa. To mutanen nan nake son jin yanda ká yi da su."
Bai kalleni ba, ya ce, "Ina ruwanki da
maganarsu? Saura kuam ki ce za ki gayawa Umma
abin da ya faru, don ke baki da wayo ba ki san abin da
za ki rinka yi kina kwantar mata da hankali ba, kin dại
san ba dabarar ki ba ce yasa kika ga wadannan
nutanen za su iya yin abin su su gama babu wanda ya
gansu, musamman da yake kin fito ne aka shiga, don
ba a yi zaton komawarki a wannan lokacin ba, to
63

kuma da sun bari kin yi barci ma da za su shiga Su yi
abin su, su gama babu mai ganinsu, amma saboda
Umma ba ta da alhakinsu ita tana zaune da komai
zuciya daya shi ya sa duk abin da ake yi babu wanda
ya taba samunta. Ai kin ji Baba maigadi ya ce irin
wadannan bakin sun saba zuwa ko?
Na ce mishi, "Eh."
To kar ki yi mata maganar na kuam san su
Junaidu ba za su yi mata ba, yanzu dai za mu je ne ki
zabar mata kayan da za su dace da wurin nata, don na
sa an fitar da komai a mayar mata da sababbi."
Na ce mishi, "To."
Muna tafiya yana jaddada mini dole ne in
zama mai hakuri kan al'amu masu yawa in gani in ki
ji in ki gani, ko a gabana a ka yi abu in ba a ce in
ganni ba sai in kawar da idona.
"Da na ki da wanda ba naki ba, duk ki maida
shi naki. Yanzu kamar Umma kina iya gane nata da
wanda ba nata ba? Babu wani wanda bai da alaka mai
karfi tsakaninshi da Umma Karama, saboda ita
kanwar Baba ce, amma hakan ya hana su son Umma?
Bai hanan su ba ko ba su sonta kuwa dole su hadiye
su maida ita abokiyar mu'amallar su, saboda halinta,
masu kin Umma na wajen gidan ne sune masu cewa
wai abin da ya sa in ka zauna a gidan dole ka so ta, ko
ka rinka jin maganarta wai asiri take yi a gishin miyar
gidan ko?"
Ya waiwayo ya dan kalleni cikin murmushi ya
64

ce, "Nima ki zo mini da irin wannan gishin Rabi. Na
taya shi murmushin kawai a zuciyata na ce, ashe shi
ma ana fada yana ji. Yana kallon hanya bai kalleni ba,
ya ci gaba da magana.
"Da kike ganina na fiki sanin Umma, na fiki
sanin sirrinta, domin nine na santa tana ganiyar
kuruciyarta, na san ta tun loakcin da kishi yake yi
mata zafi, na santa a lokacin da ake yi mata abu ranta
ya baci ta yi.fushi, ba yanzu ba da komai aka yi mata
take kawar da ido akan shi, in da tana da dabi'a ta bin
masu binne-binnen nan fo da nati kowa sanin hakan.
Na kuam gayawa Umma Karama ban boye mnata ba
cewar inda Umma tana yin irin abin da ake yi mata, to
da an yi nasara a kan ta. To amma ba ta yi, don haka
babu abin da zai faru da ita, sai alheri; don shi ta sani
take kuma yi."
Cikin kwanaki biyu kacal aka yi wa sashin
Umma gyara na ban sha'awa, harabar wurinta gaba
daya tiles ne masu tsadar gaske, sun yi matukar
kawata wurin babu sauran a y1 mata biso a wurinta.
Gaba daya furannin wurin babu Su, sai yan kadan da
aka kawata wurin da su ta hanyar aj1yewa kawai,
amma ba shuka ba. Hatta labulayenta sabbbi ne farare
Sol, marasa nauyi. Sai kuma aka bi, bayan su da masu
ruwan sararin sama. Kayan fafon gaba daya irin
kalarshi kenan, bai yiwu ma in tsaya kkwatanta kyan da
wurn Ummana ya yi. Sai da aka gama gyara komai.
Sannan yaya Almu ya rufe shi. Ni kuwa na

65
koma da kwana a dakinmu tare da su Aina'u ko ba
komai dai na lura da gani har su mun ji jiki a damben
da aka yi, don kuwa a yanzu ba sa yi mini irin kama-
karyar da suka saba yi mini. Na kuma lura na gane
Aina'u ba karamin son yaya Almu take yi ba, duk da
zirga-zirgar saurayinta a wurinta ta kasa kawar da kai
daga al'amarinshi, ko wayata ce ta yi motsi sai ta kasa
kunne ta ji dawa nake magana? Ni kuwa dana ganetaa
in tana wuri ya yi mini magana sai in sake mu yi ta
hirarmu mai dadi, ina kyalkyalewa da dariya, sabanin
in a gaban shi na ke sakin baki da nake yi in yi ta gaya
mishi maganganu masu dadin ji, in kashe murya in yi
ta gaya mishi irin son shi da nake yi da darajojin da
yake da su wadanda suka bambanta shi da sauran
maza. Ya sa babu dama ya yi minti talatin bai yi mini
waya ba, sai dai in wani aiki yake yi, bai sani ba ni
don in kular da Anti Aina'u mai nuna kishi a fili nake
yin hakan.
Rannan Ummana za ta dawo tun safe yaya
Almu ya bude wurinta. Baba Talatu ta shiga ta gama
gyara komai nima ina tayata, muka gama na faffesa
turararruka kala daban-daban. Sannan ya sake rufewa
Nima na je na yi wanka, muka yi shiri ni da shi muka
tafi dauko su a airport cikin motar da ake dauko baba.
Umma tana zaune a falonta bayan sun gama
cin abinci, sun huta an maida kawayenta gida ta kuam
gama gaisawa da jama'a ta kalle ni cikin murmushin
dake kara bayyanar da farin cikinta ta ce mini,
66

Wannan dai aikin Babangida ne?"
Na ce mata, "Eh Umm."
Kamar in gaya mata abin da ya faru wanda ya
yi dalilin da aka yi mata aikin. Sai kuma na tuna
kashedin da ya ba ni na cewar ba wai zai 6oye
maganar ba ne, don yana son a cutar da ita, shi mai
yin komai ne wajen ganin ya kareta daga kowacce irin
cuta, sanin darajar Umma wurin yaya Almu ya sa
nima na kame bakina, na yi shiru, na bar ta ta yi ta
farin cikinta.
Rannan muna kwance a kan gadon Umma da
daddare, ko wurin yaya Almu ban yarda na je ba,
saboda dokin dawowar Ummana, hira mai dadi muke
yi. Maganganun da suka shafe mu muke yi cikin hirar
ta mu ce Umma ta yi mirii maganar da ta sanya ni yi
mata tambaya. Bayan ta kai karshen zancen nata,
cikin nutsuwa na ce mata,
"Umma!"
A hankali ta ce mini, "Mene ne ya faru Adawiyya?"
Na ce mata, "Kin taba gaya .mini cewar ke din
baki hada komai ba da baba a mu'amalla ta zumunci,
amma kuma gashi a yau kina ba ni labarin gadon da
kika ci a gidan su Baba."
Ta miko hannu tana shafa hannuna, dana
shagala kan wuyanta ta ce, "Kai Adawiyyah wane irin
taushi jikinki ya yi haka?"
Na ce mata, Yaya Almu ne ya canza mini
67

kayan shafa."
Ta yi murmushi ta ce, "Bari yau in dan baki
labari na dan kadan tun da kin girma kin yi hankall.
kwanaki kadan ne kuanm suka rage mana za ki tafi
gidan mijinki bai kamata a ce ba ki san komai a kan
al'amarinki ba, ko da yake dai mijin da za ki aura ya
san komai a kana, babu wanda ya san sirrina irin shi,
shi ya sa nake kara son aurenku don kuwa mutumin
da ,nake so fiye da kowane Alhaji zai bai wa ke
wannan alheri da Alhaji ya yi mini ya kara bayyanar
mini da muhimmancina a wurin shi.
Na ce, "Haka ne Umma, to ba ni labarin na ki
in ji?"
Ta ce, 'Yanzu kuwa." Tana yin gyaran murya
ta ce mini to.
Ni dai ko ban gaya miki bab kin san sunana
Zuwairiya, hakan nan na sha gaya miki cewar ni din
ban taba sanin mahaifiyata ba, ina dai kawai na san
ina matukar kama da ita, abin da babana ya gaya mini
kenan mahaifiyata mai hakuri ce kwarai. Na sha jin
shi yana jaddada hakurin nata a lokuta daban-daban.
Babana ya yi abota ne da mahaifinsu Alhaji
suka yi mu'amalla a kan harkar dukiya na dan lokaci
kadan, sai suka rabu, saboda dama abotar ta su a kan
harkar sana'a ce garin su ba daya ba ne. An yi hakan
ne kumna shekaru masu yawa katin a haife ni, amma
har na yi wayo baba yana bani labarin amana irin ta
mallam Mai Hadisi, samun irinta wurin mutanen
68

wannan zamani da wuya
Bayan rasuwar mahaifiyata baba bai sake aure
ba, na sha jin aminanshi suna ce mishi mallam Aliyu
ina amfanin wannan zaman nan ka a haka? Shi kuwa
ya kan yi murmushi ya ce inda sauran auren sai wani
dalili ya sa yi. Mafi yawancin sanin da na yi wa baba
na yi mishi ne a kwanakin da lafiya ta yi mishi
karanci, watakila saboda yawan shekaru, watakila
kuma saboda kusantowar wa'adi.
A irin hirarrakin da ya kan yi mini ne a wancan
lokacin ya sanar da ni nufin shi na kaini wurin malam
Mai Hadisi ya bayar da amanata a gare shi, sąboda ya
san shi din zai rike ni kamar 'yar cikin shi, koma fiye
da hakan; don bai taba ganin mai amana irin ta shi ba.
A irin soyayyar da na san Babana yana yi mini nan
kuma ji shi yana cewa zai bada rikona a wani wuri sai
na tsorata na yi ta kuka ina rokon shi ya bar ni in
zauna tare da shi: Ya kalleni cikin tausayawa ya ce
"Ki yi hakuri kamar yanda nima na yi, ina jin
tsoron kar in mutu in bar ki a nan ba ni da wasu
'yan'uwa a kusa tun da ni ba mutumin nan kusa ba ne.
Sannan ba zan 1ya bada,amanar ki wurin kowa ba in
ba shi ba, don ko na yi hakan hankalina ba kwanciya
zai yi ba. Mai Hadisi shi ne kadai mutumin da na bai
wa ajiyar dukiyata a lokacin da zan tafi kasarzmu na je
na dawo na same ta ko kwanceta bai yi ba, balle ya
taba bayan na je na yi shekaru uku maimakon watsa
shidan da na ce mishi zan yi, sauran wadanda na bai
69


wa ajiyar duk sun cinye, wasu ma cewa su y1 ban ba
su komai ba.
A yanzu na riga na tsorata da rashin lafiyar nan
don na san halin ciwon da ke

Please Login or Register in order to submit comment