Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanshi na kallon gefe haka yake cinikin dan duk karya taka Shari'ar Allah, Yan Mata da dama na sonshi saboda dukiyar da Allah ya mashi da kuma kyan da Allah ya bashi dan farine sol gashi da yalwar galgasa, musamman sajen da yayi wa kyakyawar fuskar shi 'k'awanya ga geme dai-dai na Malamin sunna ya aje... Duk budurun su bai tab'a kallon suba balle ya tanka, da tafiya tai tafiya ya samu Yaran Unguwar su guda biyu ya kawosu shagon nashi, ya koyar dasu yanda ake Kasuwanci, sai Mace sama da Ashirin ta shigo ba ima sani ba yana cen yana karatun shi ko lazimi, kullum idon shi a'lumshe kamar sabon makaho, dan duk karya bude ya kalli Haram, dan Yace kasuwa matattalar sharrice.

Wata rana suna zaune da Abokin shi Mujahid Dan Allah Yayi USTAZ da son farantama Abokin shi sai dariya yake kamar bashi ba" Yace wai da gaske ka'ke mujahid?"

Wanda aka kira da Mujahid ya kwashe da dariya "Yace Wallahi da gaske nike" kai ma ka jaraba ka gani, ka ganni nan cema ta nai ni dan
Gwamna ne, wawuyar har'ta yarda yanzu jira take int'uramata kudi zata kitso.

USTAZ ya kwashe da dariya Yace kai Allah ya shirya man kai Abokina, ko nace karka yi da mutane baka bari sai kayi .
Sallama sukaji daga bayan su cikin wata tattausar murya mai da��in a'mo, USTAZ baison sadda yajuyo gaba dayan shiba harda ta shi tsaye ya kure wata budurwa da bazata wuce Y'ar shekara 17 ba da ido, halshen shi yamai nawi a'wajen magana yakasa koda amsa mata Sallama.

Yarinyar ta 'bata fuska tace yadin Hijjob nikeso Ash ko zan'samu?

USTAZ bai cemata komi ba sai kanshi daya kada mata.

"Tace aban yadi hudu."

Ya karbi kudin tare da mikama Ahmad Yaron shi Yace ya kamata. ya koma kujerar daya ke ya zauna tare da dafe kanshi.

Mujahid ya dan rankafo da kanshi "yace miya faru Abokina ko kana ciki ne?

Da sauri Abdullahi ya d'aga kanshi danshi bai iya boye Abun da ranshi ke soba,gashi da gaggawa.

Mujahid "Yace ta kwana Gidan sauki kasanya a'ranka kamar anyi an'gama, yau zata had'u da Mazan fama, Abun da ban taba jiba kace kana son wata yau ka furta kai kanka ai'kason akwai kura wallahi.

Abdullahi baice kami ba ya dukar da kanshi kasa .
Mujaheed "Yace mai amma dai baka )�arbi kud'in ta ba ko?

Abdullahi yasakar mai harara Yace kawai dan nace ina sonta sai inki kar�a hakkina ,miye a'lakar soyayya da kasuwanci .

Mujahid yayi tsaki Yace ai kaji, kai matsalar ka kenan Abdullah, baka iya hada ala kar ku��i da komi, maimakon ka k'ara mata kala biyu ka hadama ta da kudin ta kabata. ai Wallahi da sai tafi ganin mutun cinmu ta tsaya..

Abdullahi ya ��agamai hannu Yace daka ta dan Allah, abar soyayya haba, yo haka kawai hakki nane fa, kuma nema nike ba dare ba rana, sai kuma in'bata in ni nayi niyya ai zanba ta..

Ran mujahid ya �aci "Yace to na fasa bin nata kai ka bita, dan bazan iya da wannan Matsolanci naka ba, inama anfani ya kara sa yana ficcewa daga shagon baki ��aya.

Abdullahi naji nawin ya mike ya bita ya naji yana gani aka gama mata ta fita ta barshi zaune sun'kuye da kai.

Bayan sati biyu Abdullahi yayi wata mahaukaciyar rama idon shi ya koma kamar kwan-kwala'to, sunyi mai luhu-luhu ba K'aramar azabatar dashi son Yarinyar da ganin farko da yamata yaji ta shiga ranshi ba.
Ganin zai hallaka kanshi a banza ya yanke shawarar zuwa shagon mujahid dan yabashi shawara .

Bayan ya dawo Sallah yayi tsinke shagon Mujahid tare da cewa shikenan sai kaman yajin a ko?

Mujahid dake waya ya datse wayar ya d'ago yazu bama Abdullah harara Yace Wallahi USTAZ baka da kirki,kanason abu amma baka jin zaka iya kyautar ban girma.

USTAZ yabata fuska "Yace kai ni fa duk ba wannan ba! bakaga yanda na koma ba, Wallahi ko abinci bana iyaci dan Allah Abokina ka taima kaman ka tayani neman Baiwar Allah nan.

Mujahid ya kalleshi take yaji tausayinshi yakamashi!!" Yace karka damu an'jima ka shirya zaka raka ni wajen wani Abokina bayan mangari ba..

Ustaz Yace haba nace kayi hakuri mana, ya ina maka magana Yarinya kana man magana Abokin ka, ko bakayi hak'urin bane?.

Mujahid Yace ya wuce kaidai ka shirya in kuma baka zuwa ba matsala.
Abdullahi ya tashi yana fad'in ba damuwa Allah yakaimu. ya koma shagonshi

Bayan mangariba USTAZ yayi shigar shi ta yau da kullum farar jallabiya da hular shi ta'bani kaji hadith, ya hau mashine d'in shi dan shi baida ra'ayin mota sosai! yayi Unguwar su Mujahid .
Yana zuwa ya faka kofar Gidan su ya ��akko K'aramar wayar shi yakira Mujahid, bai da gaba sai gashi ya fito da sauri yasha wanka harda babbar riga yasanya,da farin glass yayi kyau sosai.
Mujahid "yace Affuwan Aboki n....

Bai karasa ba yasaki baki yana fad'in wai miyasa ka'ke wulakanta rayuwar ka ne Abokina, Ya Allah ya maka sitira kai kema sai data maimakon aga sam'fari jikinka Amma za agan ka haka kullum da hula kamar ka kifa fo, sai Jallabiya kai ba limamin kwartaye ba..

Ustaz "Yace sub'hanallahi ya kake ai banta shiga ta, bakina kaga da goro ko jikina kaji yana tsami ?duka ba ko ��aya hasalima kayan nan yau na fasasu nafara sawa.

Mujahid "Yace to Wallahi na fasa zuwan, koma gida kaima tinda baka shirya zuwanba.

Ustaz yayi shuru dan haka nan yaji yana son fitar, da Mujahid yasa mai rai"cikin sanyin murya shi Yace shikenan hau muje in'canza kaya.

Mujahid Yace Wallahi harma mota saika dauka, da kudi, koda dubu biyar ne dan ba karamin wuri zamu ba.

Ustaz yace kai a'bar tafiyar haba sai me, yafara ko'karin tada mashine Mujahid Yace ba matsalata bane, matsalar kane dan wajen wadda zata nemo maka Yarinyar da kake So zamu, ka kauga )�aruwar kace.

USTAZ ya jinkira ta yana na zari zuwa cen" Yace muje bakomi. Mujahid ya haye suka komo Gidan su USTAZ, suna zuwa suka isa har palon su Mujahid ya tsaya gaida Hajiyar Ustaz.
Ta amsa cikin farin ciki tare da fadin Mujahid dan Allah ka dinga cema Abokin ka Yayi shiga irin taka, Wallahi ni ban'ma gane yana canza kaya koda yaushe Jallabiya kuma fara kamar gawa, ko ��an canji babu.

Mujahid "Yace yanzu ma Abin da ya maidomu kenan, dan wata Yarinya ya gani yana so kuma yanzu zamuje wajen ta, da haka zaya nace mudawo ya canza.

Hajiya ta rike baki tare da fadin Alhamdulillah USTAZ yakusa Aure muhuta, Allah yabashi wadda zatai hak'uri da halinshi.
Mujahid yace Amin tare da tashi yabi Ustaz ��akin shi.

Yana zuwa ya iske USTAZ ya sanya wata bakar Jallabiya data haska farar fatarshi, sai dogon wando shima baki ya ��auki hularshi yasan ya.

Mujahid ya shekamai harara tare da fadin Wallahi baka isaba, haba saika ce kwarto, kai in'bama ita kasaba bakajin dad'i.

Ustaz yayi shuru baice komiba.

Mujahid ya k'arasa wajen wadrobe d'in Yace "Masha Allah ganin kaya wane guda ��ari, Wadrobe din mai shidda ce cike take gam da kaya, sai gefe guda kuma duk Jallabiya ne, haka Mujahid yaza �omai wata dakekiyar Wagambari Ash color, tasha aikin hannu mai masifar kyau, nan ya fiddo mai ita, ba yanda Ustaz ya iya haka yasan ya kayan Mujahid ya mikomai takalman suma yasanya, Masha Allah itace kalmar data fito daga bakin Ustaz d'in da kanshi" Yace " Abokina babu Abun da zance da Ubangiji na sai godiya"gaskiya Alhamdulillah.

Mujahid da yaketa zubama Ustaz photo batare da yasani ba ya kallai "Yace kai ke neman kashe kanka, ko laraba suna surka kaya amma kai kullum da jallabiya kamar wanda a'kaima shayi..

Ustaz yaka��a kai yayi murmushi.

Mujahid ya ��akko tiraran USTAZ ya fesamai sosai ajiki, ya zaro key din jeeb din motar USTAZ yace to muje.

USTAZ yabiyo shi yana gyara babbar rigar data maseefar dace da kyakyawan jikinshi, suna sakkowa gabaki dayan k'annan shi suka saki ihu!! da gudu suka tashi suka Makal kaleshi suna murna" Bilkisu Tace" ku tsaya in'maku photo mana, dan Allah ya'ya Abdallah ka tsaya in maku?.

USTAZ yadakamasu tsawa tare da fadin miye haka? zaku wani kan kameni kamar ba man yaba, karfa kuga Uwar mu ��aya uban mu ��aya kuce zaku dinga Abun da bashi bane, wannan bai dace ba.

Take suka sha jinin jikinsu suka fara neman matsawa.

Hajiya data shagala da kallon d'an nata "tace kai tsaya ai'maku kaji nace, ai shi Photo ana yinshi ne dan tarihi dan haka ka tsaya nace Umarni na baka ba shawara ba, nima bari in'yaso amamu.

Abdallah ya sunkuyar da kanshi Yace kiyu hakuri, kuta so.
Cikin murna suka tashi suka jera cikin natsuwa Mujahid ya dinga hask����������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������������asu harsuka gama suka fita...

Suna fara tafiyar mujahid yami komai hannu "Yace bani nan, ya fad'a yana daure fuska".

USTAZ ya zaro 5k yabashi "Mujahid yafita yashiga Jifatu ya yo sayayya kayan zaki da yason Mace naso ya dawo ya aje.

USTAZ kad'an-kad'an Yace subhanallah dan zuciyar shi mugun duka take.

Sunje wata Unguwa mai suna Dutsin safe saman low-cos suka tsaya. Mujahid ya ��aga wayar shi Yace nazo wajen gidan ruwan dakika fadaman

Ba aji'maba wata Budurwa ta bud'e wata ma dai-dai ciyar kofa ta fito, tasha bakar Hijjob dinta har kasa, ta k'araso wajen motar, da sauri Mujahid ya fito yana fad'in Ranki ya da��e.

Nan suka gaisa Mujahid ya kwan-kwasa glass din yacema USTAZ fito mana.

USTAZ ya bude yafito yana tafiyar shi cikin natsuwa ya iso wa jensu, kanshi a'kasa, yayi tsaye.

Mujahid yace ka d'ago kan mana USTAZ.

Ustaz ya gilgiza kanshi tare da cewa hakama Masha Allah

Mujahid yace A'isha baki gaida Abokina ba!

Ta d'ago kyakyawar fuskarta, ta zubama USTAZ da kanshi ke kasa Ido" Tace ina wuni ya kasuwa?

Da sauri USTAZ ya d'ago fuskar shi dan bazai taba mantawa da wannan muryar ba a'karo na biyu cikin tarihin rayuwar shi ba.

Ya amsa yana kallon A'isha" Yace dama nan kike ?

"Tace eh"
Yayi shuru baice komiba dan baison mizai furta ba.

Mujahid Yace toni na sauke nawa saura naka! yajuya zai koma mota da sauri USTAZ da dukkan jikinshi ke rawa ya jawo rigar Mujahid yana gil-gizamai kai alamun roko karya tafi," Mujahid ya kwabe hannunshi ya shige motar yana dariya.

Aisha duk ta lura da Abun da yake yi dan illahirin Hakinshi mujahid ya fad'a ma ta, dan ranar data bar shagon Mujahid ya ta reta ya samu yashawo kanta harta Amince tabashi number wayar ta, daga lokacin ya fad'a mata Abun da Abokin shi yace. Tace ta Amince ya fadamata Abokin shi USTAZ ne saita bayar da gudun muwar ta, Tace Babu matsala ta yarda tana son shi. shiyasa Mujahid ma bai tsaya sauraran shi ba yayi gaba .

Aisha tayi gyaran murya tace sannu USTAZ ka kasa cewa komi.

Ustaz da jikinshi ya sake ��aukar rawa yace am... am..dad..da..ma ke ke nike jira yafa��a cikin ina ina.

Aisha ta bushe da dariya tace hala kai sabon shigane USTAZ ?

USTAZ da bai fahimce taba yace aa sanyi nikeji kawai ,da sauri Yace As'tagfurullahul zakisa inyi karya..

Aisha ta sake kwashewa da dariya!! USTAZ ya ��ago idonshi yana kallon ta, kyakyawace ajin farko, farace sol ga dogon hanci idonta manyane sai ��an karamin bakinta da jajayen lips d'in ta sukai mai 'kawanya in'tai dariya zakaga wushiryar ta mai kyau gata ma abociyar fara'a aganin farko zaka ganta kamar tana da fa��a, amma inka zauna da ita zaka fahimci bata da matsalar rayuwa .

Ustaz yace dama nace ina Sonki ?

Aisha tasaki baki tana kallon shi wai dama nace ina sonki ta maimaita a'ranta.

Tace to Nagode zanshiga gida.

Ustaz yace to bakice komi ba, kuma in Baban ki na nan kifa��a mai gobe iyayena zasu zo..

A'isha ta zaro ido tace suzo a'yimi?

Ustaz Yace to nidai ba wasa ya ka woni ba gaskiya, Auran ki zanyi nan da wata daya ko sati biyu..A��]
{


"JUMARE" KI KIYAYENI WALLAHI ���j���j���j

Zance nafasa littafin sai inga yazakiyi���j



Sakwanni sunzoman daga )�annena Amina da Amina sun ceman ana zagina to ku kuka sani masai don Jumare tace kuzageni bakomi zamu hadu kotu gobe daku
1/13/22, 09:07 - Buhainat: ��c��c��c��c��c��c��c��c
AURAN USTAZ
��c��c��c��c��c��c��c��c
NA UMMY AYSHA
��T���7��_/Q8��_/Q


""""Wata irin dariya t'akama Aisha jin abunda yace, take ta maida USTAZ mahaukaci tai ta mishi dariya," duk yabi ya diririce yama rasa ina zai sa kanshi,dan gani yake kila yasaki layi shiyasa take mai haka.

Da kyal Aisha ta tsaida dariya ta "tace wato aure nan da sati biyu ko?
Saboda gani d'iyar roba, to gaskiya bazan iya ba, in sauri ka'ke zaka iya zuwa Masallaci a'kwai wayanda ake sanarwa a'naso ayi gaggawar aura dasu. ta juya zata shige gida dan take taji bazata iya zama dashiba lokaci guda yafita ranta, ita da ke karatun novels na hausa tanajin yanda ake zab'ga soyayya shikenan daga zuwanshi yau kawai zai maganar aure.

Cikin sauri USTAZ yabita tare da "fadin dan Allah karki barni mana, ni banson mizancemaki ba, sannan ba iya soyayya nan nai ba, nidai burina ki Amince'man kawai in Aure ki.

Aisha ta juyo a'fusace dan yafara k'uleta "tace haba banayi dan Allah Malam ko dole ne. haka kawai, to bari kaji akwai wanda nike so ya kesona, Wallahi bazanyi AURAN kashe kai ba, kai ga USTAZ baka iya kalamai ba ko? wato kwara kawai ka Aure ni kasani cikin gidan ka katafi ka kyaleni, to gaskiya bazan iya ba ta shige gida..


USTAZ yacire hular kanshi tare da fadin Hasbunallahu wani imal wakim, Hakika akwai Mishikila anan,wato a'she kazama ai'nafin d'an duniya ma yana da rana, toni mizan ce da Aishatu? ya subhanallahi, hakika bazan iya barin kiba malama Aisha, saboda ina wato ai'nafin son yar kakkaura Mace...


Daga bayan'shi yaji an'saki dariya.

"USTAZ "yace sub'hanallahi ya Allah, wanene ke ai'nafin son rikita ni.."

Mujahid yasa ke kwashewa da dariya "yace ash'sha ya USTA, Affuwan, na wato ai'nafin tsorata ka..

USTAZ yayi tsaki tare da "cewa a'zahirin gaskiya baikamata kana tsorata d'an uwanka musulmi ba, dan sarai nason cewa kason hakan Hara'munne, amma ba mishkila na ya'fema...
Mujahid yayi dariya tare da fadin A'bokina sai haka ta faru? hahahaha ya saki dariya, ashe kaga ranar mu kenan,Wallahi ina al'fahari da kalamai na, ni na'son bankai ka kud'i ba, amma wallahi zaka iya zuwa wajen diyar Shugaban K'asa taki kulaka, nikam da bankai ka kyau da ku��i ba tsab zata kulani, harma in naso inyi am'fani da damar in'gasamata Aya a'tafin hannu, saboda Mace na son ka nuna mata kulawa, ka tararraye ta, kanuna'mata babu na d'ayan ta, kazama mai iya rarrashi a'duk sadda kaga zata shiga damuwa, da haka zakaga kaza'ma zakaran gwajin dafi a'wajenta, amma kai kullum kai a'cikin tulu, bama dole ba tak'i Son ka ba, saika wuce muje Allah ya had'aka da Ustaziya yar uwar ka, tinda ita wannan yar soyayya ce..."

USTAZ da idonshi yayi jawur sakamakon kanshi daya fara saramai,saboda ko kad'an bayajin zai iya hakuri da soyayyar Aisha, musamman yanzu daya kara kallonta mikin soyayyar'ta yasake mikewa a'cikin zuciyar shi, bazai taba yarda ya yiwa kanshi babba ilaba ta hanyar rasata ba,bai tsaya komi ba yafad'a gidan da Aisha ta shiga, tare da rafka Sallama..

Mujaheed ya dinga dariya ganin USTAZ yafara zama soko akan So,harda fad'awa gidan mutane.

Ustaz yayi sallama takai goma kana yaji an'ce waye?

Yace Abdullahi bin ABBA Mai Jama'a ne..

Wata Dattijuwa da bazata wuce shekara arba'inba tafito sanye da hijjob inta har kasa.

"Tace daga ina bawan Allah?"

USTAZ da baiji da��in ganin taba,yaso ace mai gidan ne yafito zaifi sakewa kanshi a'kasa "yace dan Allah in'ba damuwa Hajiya mi zai hana mai gidan yafito in'fadamai abunda yakawoni, amma in'nace inyi wato ai'nafin magana dake, hakika na keta dokar musulunci.yafad'a yana kara matsawa cen bakin kofar waje.

Cikin bacin rai matar "tace au USTAZ muka samu to maza makabarta low-cos ka kirashi sai kuyi magana bom ta turo k'ofar da karfi.
USTAZ bai son sadda ya yo waje a'guje ba yana Hasbunallah....A��]
{
1/13/22, 09:07 - Buhainat: ��c��c��c��c��c��c��c��c
AURAN USTAZ
��c��c��c��c��c��c��c��c
NA UMMY AYSHA
��T���9��_/Q&1��_/Q0��_/Q

""Mujaheed ya kwashe da dariya tare da Ce'wa Subhanallahi USTAZ mi ya faru ko jefo ka akai?
USTAZ ya dafe kanshi tare da Ce'wa shikenan in an'ganka USTAZ baza a'taba Son ka ba, ana maka ma kallon wani gara-gara dan kawai munabin k'aidar Addinin mu..

Mujaheed ya'ce Hmm Ruwa ka'ke tsullugudum wallahi,a'wannan zamani Mace Kalamai ta kebi ba wai kyau ko kudi ba, dan haka in'ka shirya yanda zakai yak'i da soyayyar Aisha, zaka iya tsayawa in tsarama ka yanda ya dace, in kuma baka shirya ba to zaka iya sanyo Jallabiya da Cas'baha kullum kazo ita kuma ta koraka
yawwa wuce muje..

USTAZ ya'ce ya Subhanallahi!! hakika na shiga cikin wato ai'nafin shauk'in K'aunar ki ya Aishatu, Insha Allah zan kauce hanya ta ai'nafin ko yan kalamai dan in faran ta ranki,Allah ma shedata ne zanyi hakanne dan faranta ran iyalina. Insha Allahu.

Mujaheed ya'ce kan'ka a'keji Mahaukaci yafa��a Rijiya ya'ce ni wanka na nike." haka suka shiga mota suka tafi." USTAZ ya buga uban tagumi tare da rasa a'bunda ke mai Dad'i dan illahirin kirjinshi ciwo yake mai." a takaice dai kan sukai gida USTAZ ya fara sakin tari ba kak'kautawa."tin Mujaheed na tsokanar shi har ya fuskan'ci abun na gaskene kan ya an'kare USTAZ ya sume mashi a'mota..
Agigice mujaheed ya saki salati tare da gilgiza kan Ustaz amma shuru. bai tsaya komi ba yaja motar da mahaukacin gudu yayi Asibiti da yason suna da family cart cikin gaggawa aka tar'besu, aka fara ba USTAZ taimakon gaggawa sama da awa biyu kana numfashinshi ya dawo suka kaishi D'akin hutu tare da D'aura mai drive.mujaheed ganin an fiddoshi yasanya hankalinshi kwanciya ya D'aga wayarshi tare da kiran Alh Abba ya fad'amai halin da d'anshi yake ciki,abunka ga mai kula alamarin y'ay'anshi cikin lokaci suka karaso kusan su duka hadda kan'nan USTAZ maza da matan. a'gigice suka shugo Mujaheed ya koramasu bayanin akan abunda yasani .

Hajiya asiya ta fashe da kuka tare da fad'in mi yasa za tace batason Abdullah, bayan yana da nagartar da yakamata kowane namiji a'soshi dan su...

Mujaheed yayi shuru dan bazai iya cemata D'anta baison komi ba a'harkar soyayya. Ya nada ilimi Sosai Amma bai da kalamai.

Hajiya Asiya ta'ce dan Allah muje ka kaini gidansu yarinyar yanzu..

Alh abba ya zaro idonshi ya'ce haba Hajiya akan mi zakice zakije gidan mutane yanzu, kiyi Hakuri mana sai zuwa gobe in sha Allah zamu son abun yi..

Ba dan Hajiya ta soba ta koma ta zauna tana kallon Abdallah da lokaci k'ank'ane yayi wani irin mahaukacin kyau. ya k'ara fari ga hancinshi yasake fitowa zarr dashi" Hajiya tace miye ai'bunka Abdallah da har za ace ba a'sonka a'wannan lokacin,samun Namiji kamar ka ma ai ai'kine Wallahi.
Mujaheed ya kalli Hajiya baice komi ba,dan yason ita kanta Hajiya tason D'anta mutum ne mai wani irin rikitacen hali. amma yanzu gashi ba laifinshi take gani ba na yarinyar take gani.

Washe gari Asubar fari USTAZ ya tashi yana salati, ganinshi akan gado ya sashi fad'in ya Allah miyafaru da nine.
Da sauri ya sakko tare da fisge K'arin ruwan." acen gefe yaga mutum lullube bai tsaya bi takan ko waye ba ya zura takalmanshi ya fita, ya tsaya yayi Sallah Masallacin Asibiti yana gamawa ya fita, a'kafa ya dinga tattakawa har yakawo unguwar su Aisha, dan asuba ne ba abun hawa, yana zuwa kofar gidan yaga wani saurayi zai shiga gidan, da gudu USTAZ ya karasa tare da fashewa da kuka yana durk'usawa kasa.

Ad'imauce Saurayin'nan ya fara k'okarin shiga gida dan gani yake ko sharri USTAZ zai jamai shiyasa ya zube gabanshi.
USTAZ ya rikoshi yana fad'in dan Allah ka taimakaman inga Aisha, wallahi mutuwa zanyi in'ban gantaba,dan Allah ka roket a ta soni koda cikon cokali ne. kajifa hannuna kaga jini yake zubarwa, daga asibiti nike ba wandama yason na fito Wallahi," ya k'arasa yana kuka sosai kamar yaro .."

Saurayin yayi shuru tare da cewa to kayi hakuri ka tashi kaga gari ya fara wayewa yanzu bari in'shiga gidan in'kirama Aisha....


Ayi hakuri ba yawa a'tari gobe Insha Allah inada uzuri
1/13/22, 09:53 - Buhainat: ��c��c��c��c��c��c��c��c
AURAN USTAZ
��c��c��c��c��c��c��c��c
NA UMMY AYSHA
1��_/Q1��_/Q&1��_/Q2��_/Q

"""USTAZ ya kad'a kai kamar yaro "ya'ce Dan Allah kar ka barni tsaye."

Saurayin ya ��agamai yatsu biyu tare da shigewa gidan yayi sallama. "Dattijuwar nan ta amsa" yakarasa wajenta tare da cewa Umma ina kwana?.

Umma "ta'ce lafiya lau Abdul ya kuka tashi?

Abdul yace Alhamdulillah .dama Umma wani saurayine yazo nan kofar gidan......
"Ya fada mata komi" ta rike ha�a tare da fa��in anya kuwa Abdul lafiya yake? zuwa gidan su Budurwa da sanyin safiya haka, kamar biyan Bashi..

Abdul yace umma wallahi yaban tausai, bakiga Hannun shiba sai zubar jini yake, da alama da gaskiyarshi da yace daga asibiti yake.

Umma" ta'ce jeka ��akin A'isha ka kirata inji ko ta son shine.
Abdul Ya'ce to. tare da tashi yashiga ��akin A'isha ya isketa zaune tana shafa mai ga jikinta ,"yace AYSHA kizo inji Umma."

YAysha ta taso ta fito har wajen Umma" tace Umma na ina kwana? yanzu dama zan fito in gaisheki ,ya Abdul Ina kwana.
Umma da Ya Abdul suka ce lafiya lau.
Umma _ta'ce A'isha waye kukai dashi zai zo gidan nan kamar yanzu?

A'isha ta zaro manyan fararan idanunta" ta'ce Wallahi Umma bance da kowa ya zoba, sai dai in yah Abdul ya tambayo mana yaji waye.

Umma ta'ce Abdul jeka ji ko waye, ka mace ya shigo kawai, ke Aisha je ki sanyo Hijjob ki fito.

Abdul ya'ce to. ya fito ya iska USTAZ tsaye bakinshi nata motsi a'lamun Azkhar yake. yana jin motsi ya tashi da sauri ya na "fadin alhamd7ulillah malama A'ish.. bai karasa idon shi ya fad'a ga yah Abdul. ustaz ya saukar da kanshi kasa tare da fadin bazata zoba ko?

Abdul "ya'ce kashigo ciki inji umma mu."
Ustaz "ya'ce to muje ka shige gaba.
Abdul yayi murmushi dan ya fahimci USTAZ akwai a'kida, haka suka shiga har bakin Barandar tsakar gidan nasu, USTAZ yayi tsaye tare da cema Abdul ka "fada mata gani nan."

Daga ciki yaji Umma na "fadin shigo mana bawan Allah.."

Ustaz ya sanya kanshi gabanshi na faduwa. sai shafa kanshi da yasha rattali ya koma kwal kamar Gidauniyar sulba yake, yayi sallama yashiga .

Umma ta amsa tana Binshi da kallo kamar ta sonshi, Aisha kam mikewa tsaye tai tana fadin ikon Allah USTAZ dama kaine?

Ustaz ya d'ago ya tsuramata ido yanata kallonta kamar ya tashi ya rungumeta, yamayar da ita cikin shi ya keji, shi ya son Allah ne ya jarabceshi da son Aisha, gashi itace first love dinyshi bai tab'a soyayya da kowa ba hasalima baya kallon matan balle ya fahimci ya suke.

Umma tai gyaran murya. da sauri USTAZ ya sunkuyar da kanshi kasa yana As'tagfurullah na tsare a'bunda ba halaliyata da ido ba, Allah kayafeman..

Umma tayi murmushi dan sai yanzu ta fahimci wanda ya zone jiya" tace muntashi lafiya?.
USTAZ ya zabura tare da fadin ina kwana hajiya, Wallahi mantawa nai aman Affuwa.

Umma "ta'ce bakomi lafiya kake neman Aisha?

USTAZ yashafa kanshi ya'ce am dama..dama ..nazo jiya shine.. amm..hmm ya fara kam- kame .

Umma da yake wayayyar Macace daga ita har y'ayanta "ta ce ok kaine kazo jiya son Aisha kake ne?

Da sauri USTAZ ya k'ada kanshi cikin jin kunya matuka "yace hajiya dan Allah a'man a'fuwa zanyi magana da wancen in maharraminta ne.

Umma tayi murmushi!!"ta'ce to ba damuwa sai dai abunda nikeso in fadama Aisha marainiyace, mahaifinta baida rai tin tana karama ya rasu, kuma akwai wani saurayi da take tare dashi amma har yanzu bai maganar aure ba, yana ma makaranta Zariya, amma muna sanya rai da yagama zasu turl insha Allah,dan haka ina mai baka Hakuri da kajanye tinda a'matsayinka na USTAZ kason neman Aure kan Aure haramunne. tat ashi tashige d'aki tare da cewa Aisha rakashi waje, kaima Abdul in ya nemi karin bayani kai mashi..


Tin sadda ta am'baci akwai wanda keson Aisha ji da ganin USTAZ suka ��auke, ya dukar da kanshi k'asa bai da goba kuma bai ta shiba, hazbunallahi wani imal wakim kawai yake am'bata, tare da k'ok'arin saita kanshi nason yaga ya mike yafita amma zuciyarshi taki

Please Login or Register in order to submit comment