Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai a kawoni Gidan ka, bakaman lefeba kuma bani da kayan sawa amma ita ai gatacen tana sanya wanda takeso..

Ustaz Yayi jim sai macewa Yayi yawwa kin tunoman ina zuwa ga cefane cen kitashi kimana sanwa...

Khadija Tace" taya ina Amarya zan shiga kiching tin yau, Wallahi bazan iyaba, kuma ka samoman abinda zanci tinda banda lafiya, ga rashin sutura ga rashin kulawa ,wannan wane irin Aure ne?

Ustaz yayi banza da ita zuciyar shi na azalzala shi, ta yama bayyi bincike ba zai bari Aysha nasanya tsadaddun kaya, koda yake hidima taman yawa, a'fusace ya isa d'akin Aysha ya isketa zaune ta canza wanka tasanya Atamfa blue nd white ta kashe d'auri tayi mahaukacin kyau, fuskarta sai shining take dan Aunty Maryam harda mayuka masu tsada ta saima ta, ga d'akin ta sai kamshi yake, zaune take tana cin kaza gefenta Rufaida yoghurt ne, kazar tasha gashi sa tiriri take, hannunta da yasha jan lalle ga mai kon man kazar daya mamayeshi sosai yamata kyau, hannun hagunta rike da wayar ta tana daddanawa.

Ustaz ya had'iye yawu tare da zama kusa da ita Yace aisyha wai wannan wace irin rayuwace kika daukarwa kanki?
Wake baki kudi?
Wake sayamaki kaji?
Shin Aysha waya canzaki? daga ta kwarai kika dawo ta banza marar jin maganar Mijin ta? ke kinson hakkina dake kanki kuwa ?kinson hakkina yafi na Uwar ki dana Uban ki....

A fusace ta tashi tsaye idonta yakawo kwallah Tace" wai miye nai maka? miyasa bana shiga har karka amma kai kullum burinka ka k'ureni? yaushe rabon da ka Zauna kaman maganar arziki?kullum maseefa !wai Ustaz miyasa kana da ilimi amma kake aiki na jahilan mutane, wannan wane irin aure ne ? Wallahi Wallahi baccin darajar Yarana da yanzu nabar wannan gantalallan auran naka da bai karaman komiba sai bakin ciki da takaici, dakake maganar sutura ai'kason wanda suke sona suke son ganin farin cikina sukaman, shekarar mu biyar da kai amma baka tab'aman kaya ba, kace na lefe na sun isa,sune kullum nike fama dasu tamkar uniform, gasunan a'kod'e ta k'amar in maka magana kace ka tsareman ci da sha niga jakka acici ko? Allah ya kawoman sauyi a'rayuwa ya bani yan Uwan dasuka zameman jigo suke son farin cikina, amma baka ganin k'ok'arin su,nason baccin su da a'yanzu ina nan a wulak'ance a idonka dana dangin ka dana Amaryar ka, sun tallafi rayuwata data yarana sun wadatani dakomi amma zakazo kana k'ok'arin cima Iyayena mutunci,harda kiransu tsurara ba Abba balle Umma a ganina duk kan wanda zai d'auki Y'ar shi ya baka ita kamayar da k'ofa ka rufe da ita ba Abun wulakan'tawa bane, amma kai USTAZ tinda na Aureka baka tab'a ganin mutuncin Iyayena ba, baka taba darajasu ba, baka tab'a d'aukar Abun goma kace gashi kaimasu ba, baka tab'a cewa shirya kije ki gaido Umma ba kasancewar ita kad'ai garan, tinda sunbaka ni shikenan Ni ka keso ni ka d'auka, su kuma ko oho,yan Uwan ka ka had'ani dasu baka tab'a zuwa ka furtamasu gaskiya kai ke baka barina fitaba, kullum suna goran taman ne akan na mallake d'an Uwan su, kana tinanin hakkina kadai da suke d'auka Allah zai barka?


Ke da kata -da kata, na'ce! Sarkin kilbibi, ni zaki fad'ama magana? miye kika nema kika rasa? akwai ranar da zaki nemi lomar abinci ki rasa? ko-ko tsirara na barki, zancen yawo kuma ba Allah Yace mu killaceku ba a Gidajen mu, ko an'fad'amaki sunana Dayyus ne? to ba haka nike ba, wato ke ga marok'iya, burinki in'kwashe tattalin ar'zikina in kai Gidan ku, bayan Allah ya basu garadan da zasu nema, hadda katon dake tsinkaman mari, kana abu na karshe Wallahi Wallahi wani dan Uwanki ya k'ara zuwa Gidan nan daniyar baki wani abu kega Mamauliya saina kaishi kotu, saboda ban ragegi da komi ba, Ashe shagalar dake dacin kaji yasanya kika faraman duk iskancin da kike'man yanzu,To in'hakane kam ina am'fanin wannan shagalaswa,an:baki Kaji kinci kinkoshi kin kwanta, baki tausayama talakkan da zai kwana baisamu koda k'anzo ya ciba, kinsha Madara kin kwanta wani talakan ko ruwan ko-ko bai samuba, kin kauga babu babba asarar data wuce wannan Wallahi, ga kinan sai cika kike kinaa tumbatsa, ni nason da yanzu zaki mutu sai kinsha ruwan bulali wajen walakiri,saboda in'kikayi nan bayan mu shake yake da yan gudun Hijira wayan da suke da buk'ata, aini banga am'fani cin da��in da zai sanya in'shagaltuba Wallahi, kuma kinji na fad'amaki musamman wannan kafcecen gardin, ya k'ara shigoman gida batare da sanina ba Wallahi Allah ya isa ban yafeba,katon banza huhulahu, inacen ina neman Abun da zan rufama kaina Asiri daku amma k'ato nanan rungume dake da sunan Yayanki ya sakaki a'kirjinshi yana jin Dad'i shiga tsohon dan bariki marar ilimi mahaukacin banza, kuma kiyi maza ki kwasoman kayan ba zakisa ba Wallahi kinji na rantsemaki, bani wayar nan itama.

Sosai Aysha ke kuka iya cin mutunci a'yau USTAZ yamata, yama Y'an Uwanta masu sonta masu k'aunar ta,jin ya'ce zai kwace wayarta yasanya ta tura wayar cikin pant dinta, .
Afusace ustyaz yayi kanta ya'ce au ke gani kike nan bak'on wajenane da bazan iya sanya hannuna ba? da karfi ya nemi murd'emata hannu data tare da wurin wani gigitaccen ihu su kaji da yasasu juyawa baki d'aya .....A��]
{
1/13/22, 09:55 - Buhainat: 3��_/Q8��_/Q&3��_/Q9��_/Q


Usman ne tsaye sai ihu yake ganin an murd'ema uwarshi hannu, tsawa Ustaz ya daka mai ya'ce" miyasa bakaje school ba? wato kunaso ku zauna gida kuyi koyi da shed'anin halin uwarku ko?

Aysha ta'ce wallahi tallahi ni ba shed'aniya bace, kai bance karsu zauna suyi koyi da bakin halinka ba saini zaka zakace zasuyi koyi da nawa, yaro bashi lafiya taya zanturasu makaranta, baka nemi jin ba a'siba sai yanke hukunci..

USTAZ ya d'auketa da mari har'saida ta fad'i. yayi kanta tare da shakota ya'ce" ina mijinki kike wato ai'nafin gayaman magana?..
Aysha ta'ce" ashe miji, sai dai jahilin miji, inba jahili bane kai taya inka karanta kasani zaka mareni..

Kan ta rufe baki USTAZ ya saketa ta fad'i akan stef din dake wurin, take goshin ta ya fashe .
Ganin haka baisa USTAZ ya saurara mata ba, saima binta da yayi cikin zafin zuciya, yace" wakika gayama magana? bani hakuri dan ubanki.

Aysha juyi kawai take dan kanta wani irin mahaukacin ciwo ya d'auka, cikin lokaci komi yakoma mata duhu-duhu.
Ustaz da yaji tayi shuru ya kalli hannunta ��aya dake saman step ya taka da mugun karfi take ta saki ihu mai furgitarwa tashid'e..

Usman ya saki kuka tare da rugawa yana rike USTAZ ya'ce dan Allah Abbah ka daina, Uncle Auwal yace mana Babu kyau ana dukan babba..


Wani irin mari USTAZ yamai cikin zafin zuciyarshi, ya dauki yaron ya wurwura ya maka da kujera, cikin gigicewa Usman ya tashi a'rikece yana kuka yafita da gufun bala'i ya fada gidan Aunty Maryam, ya isketa tana rufe d'aki alamun fita zatai, cikin kuka yace" Abbah ne ya kashe Ummy.

Maryam ta saki jikkar ta! ta zaro ido tace mene ?
Kai miyasamu Ummy naku ne.?

Usman ya k'asa magana sai nunamata hanya yake, da gudu maryam taja hannunshi suka fita suka fad'a gidan USTAZ, karcet marya6m data gigice tace ina take?

Da gudu Usman yayi wurin AYSHA yana kuka! Maryam ta saki salati tayi wurin Aysha ta tallabota taji tayi jigif,tayi nawie sosai ta d'aga hannunta taji ya saki sosai,kuka ta fashe dashi tare da cewa kar kimin haka mana k'awata dan Allah. iya binciken Maryam nason ganin taga lumfashin AYSHA ya dawo amma ina, ko motsi bata yiba.

Cikin kuka Maryam tace" Usman mi akaima Ummy ku?
. Usman ya taka k'afarshi da karfi yace "haka-haka yamata,sai tayi haka! ya nuna yanda abun yafaru, kuka Maryam ta sake sawa tare da lalubar wayarta tafara neman layin Abdul, dan tin sadda akai case din waya tayi save,bugu biyu ya d'auka cikin Sallama! cikin kuka Maryam ta amsa tace AYSHA AYSHA gatanan .

Abdul ya'ce" wacece bangane ba? wace AYSHA?

Maryam ta sake sakin sabon kuka tace ni makwabciyar'tace suna na Maryam Aysha kanwarka mijinta ya raunatata....

Azabure Abdul ya mike illahirin jikinshi na rawa, cikin rawar murya yace" kuna ina? kuna ina yanzu..?

Maryam tace' gamunan d'akinta dan Allah a'taimakamana a'kaita Asibiti.

Abdul bai tsaya bata am'saba yayiwa Saif waya tare da cewa kai kana ina?


Saif yace" ganinan na fito zanga wani.

Abdul yace maza muhad'e gidan Aysha akwai matsala Wallahi, ya kashe waya.

Jikin saif rawa ya d'auka tare da fadin ya rabbil a'lamina ka kawo karshen AURAN nan, ya yiwa driver ban'shi magana suka juya sunata jiniya! tare suka isa kofar gidan AYSHA da Abdul .
USTAZ na jin jiniyar motoci ya saurara tare da cewa subhanallahi batamaji a'binda na fad'amata ba kenan, yau kam kotu zata rabamu da wannan d'an iskan, a'fusace ya fito daga palon Khadija yana uban waye ke man jiniya,kan ya rufe baki suka turo kai suka shigo, Saif yamai wani kallo shikuma Abdul ko inda yake bai kallaba saima rugawa da yayi sashen Aysha, Saif ya cema guard dinahiy kar abari kowa ya fita, har sai na bada dama .
Sukace ok sir tare da saramai.

Tsawa Ustaz yadakamai tare da cewa fita daga gidan nan Wallahi kan in kaika kotu.

Zuciyar saif a hassale jiyake kamar ya shake USTAZ, cikin sauri yayi sashen Aysha USTAZ ma yabi bayanshi yana baka jina! Wallahi bazakaga iyalina ba, baka fita? ko kallonshi Saif baiba ya afka d'akin ya iske Abdul kamar mace ya rungume AYSHA yana kuka matuk'a shida Aunty Maryam, jikin Saif har wani huci yake yayi wajen Aysha yaga jini duk ya b'atamata goshi, ihu ya saki ya tallabota baki d'aya a kirjinshi, yana Auta! Auta!! Auta!! mi akai makiiiiiii? ya k'arasa cikin karaji.

Da sauri Aunty Maryam tace ka sauketa da alama hannunta akwai karaya kajifanyana lilo. suduka suka kai kallonsu akan hannunta salati suka saki USTAZ ma kanshi saida gabanshi ya fad'i , Saif ya ajeta ya d'aga hannunshi sama ya kwarara wani ar'nan ihun da yasanya sadeeq watsowa da gudu, Saif yace mi kai mata?uban waye ya karyaman k'anwa...?

Usman ya taso yana kuka ganin Abdul da Aunty Maryam nayi, ga uwarshi a'mmata d'aukar sabon jariri, Usman yace Uncle haka-haka ya gwadamasu kamar yanda yagwadama Aunty Maryam..

Jikin USTAZ ya kama rawa ganin yanda kirjin Saif ke tashi kamar na budurwa.

Bai dawo duniyar tinanin ba yaji an'mai wata kafurar shakar da yasa yafara ganin garara-garara, kuka Saif ya fashe dashi kamar Amarya murya a"sheke yace mitai maka? mitaimaka ,ka kasheta, kwara in kasheka Wallahi da zuciyata ta buga, ba uba ba k'anwa, ya kaima USTAZ dukan da yasa shi furta ya Subhanallahi, walhamdu lillah,i la'ilaha illah .

Saif ya k'ara shakar USTAZ shaka ta mutunci , ya fara kai mai duka,tare da cimamiyo hannunshi ya fara k'ok'arin k'aryawa , USTAZ sai tsala ihu yake yana kiran kubrah kubrah .
Abdul ya dakama Saif tsawa tare da cewa taya zaka biyema wanda hukunci ya hau kanshi kota bala'i,kazo mukaita mufarajin yah lafiyar ta take...

Fusata ya sanya Saif d'aukar bindigar shi ya fara sakin harsashe a saman POP dake d'akin, yaran suka rikice da kuka da gudu Abdul yayi kanshi dan yason bakar zuciyar Saif, rungumoshi yayi baki ��aya ya fara cewa kayi hakuri ba tada wayanda suka fimu a'yanzu, in ka hau dokin zuciyar da zai fitar da kai hayyacinka zamu iya rasata abanza, kwara muyi gaggawar kaita Asibiti yanzu...

Bai rufe baki ba khadija ta shigo da gudu tana zare ido tayi kan Ustaz dake zaune yana maida numfashi" tace kai tashi anshigo gidan nan da rana."

Tsawa Saif ya dakamata ya fizge jikinshi daga na Abdul ya fita waje, tare da dakko wani kwafcecen kulki ya shigo gidan,gadan-gadan yayi kan USTAZ ya sakamai kulkin nan cikin hamitta tare da tankwarashi da karfi, ihu USTAZ yake ba )�a)�)�autawa, amma ko ajikin Saif,saida yaji hannun USTAZ yayi )�ara kana ya saki yacire belt dinshi yafara zubamasu da gashi har Khadijah, sosai USTAZ ke kuka kamar yaro.

Abdul ya samu da kyal ya cicci�i AYSHA ya fita da ita yasa a'mota Aunty Maryam ta shiga sukayi Asibitin su, dan ya son bakar zuciyar ysaif bazai fito ba sai yayi b'arna.

Saif gani yake duk launin azabar da ya kema USTAZ baiba, ya dakama khadija tsawa tare da cewa ficce dan ubanki..

Ai a'guje ta fita tana waiwaye, jikinta sai rawa yake, D'aki ta ta shige ta rufe ta lalubo wayarta.

Hannun USTAZ zugi kawai yake !cikin kuka yace kamin lamani malam Saifullahi dan Allah, ha)�i)�a banson na yimata hakaba, nason shai��ani ne ya karyata dan ya ha��ani daku.

Saif ya kasa magana sai idonshi da keta sake rinewa yanayin jajawur! jin abinda USTAZ Ya'ce'' yasashi sake fita da mugun sauri yayi magana da yaran shi ya kar�o wani abu ya dawo, cikin sauri ya samu kujera ya zauna tare da jawo USTAZ kamar kayan wanki gabanshi, ihu USTAZ ya saya jin hannunyahi na shirin ficcewa.

Saif ya kama fuskar USTAZ tare da fiddo wata aska baishafa ruwa bai shafa mai sabulu ba ya sanya askar nan da karfi ya fara shi��e ma USTAZ geme,ihu USTAZ yasa yana fa��in lahh karka yankeman mutuncina, da kamalata, da Sunna ta.

Saif bai saurari USTAZ ba saida ya tabbatar yamai kwal, fuskar nan tayi fari fari kamar ta ��iyar baby.

Ustaz ya shafo fuskarshi yaji salaf ya fashe da kuka ya'ce" shine zaka mayar man da fuska haka kamar bayan sabulun wanka.

Cikin murya Basawa Saif ya'ce" Wallahi Wallahi na�Yara ganin wannan ko ��a��d'ar fuskar taka irinta jemage da gashi sainaci uwar ubanka, saina ma mugun duka, na halbarmaka k'afa Azzalumi makiri mai takama da ustazanci kana zalinci, ayau sai naci kutumar bura ubanka Wallahi, ga takadda maza sakar man k'anwa dan baka ba ita har abada.....
1/13/22, 09:55 - Buhainat: 4��_/Q0��_/Q&4��_/Q1��_/Q

Ustaz ya gwalo ido ya'ce" a'zahirin gaskiya komi zakayi bazan saketa ba, dan babu tsarin saki a lamarina, komi kau mace zataman,tinda na Aure ta niketa hakuri da ita, dan Aisha bata da D'a'a,sai ka'zo ka bata babbar waya ka ida lalata mata rayuwa, kai tsaye zance tayi tace batayi,kai kanka akwai sakayya mai, girma tsakaninmu dakai wallahi dan bakin gwalgwado ina mata a'dalci, ina bata abinci Available, ga store na nan ka duba akwai garin masara, akwai Doya, akwai mai, akwai shinkafa, taliya makaroni indomyi, babu abunda bandashi, kaje kagani !nan kuma bayan mu in kabi akwai wayan da suke ciyar da kansu, mazajen su sun gudu, sun kyalesu da yara,ko tanan basai ta k'ara gode man ba, yaushe rabon da asamu nagartattun maza a'wannan zamanin irina, masu tsayawa bin dokar Allah, jibi taf keken. Mahallin da k'anwarka take ciki,ban:tsaya duba da kabarin daza a'sataba bayan mutuwar ta ba, na keta hakkin shara'a na wangala wannan taf keken palon,kaga ni kaina na sab'ama Allah, dan da shari'a zanyi wallahi Akurki, zan ginamata, dan ya kasance kullum zuciyar ta a'raunane take, ta k'ara k'aimi wajen ibada, kar ta shagala da duniya....



Afusace Saif ya kaima hannun USTAZ mai rauni duka! Ihu USTAZ ya saki sosai dan jin kamar an b'allamai hannu.

Sosai Saif ke huci yace" kama mayar dani dan iska abokin wasan ka ko? shiyasa har'kake fada'man magana, wawa jahili kawai,gidan ka da ko tsokar nama mutum bayasawa bakin shi saboda mak'un a'sara irin naka, shine kake ganin har wani burgewa kake, ka takura matarka kamar ba saida ka kusa hauka aka baka ba,ko abanza ka sameta?da haka kake? kaida ko sitira baka iya sawa saida ta koyama, amma dayake kai dan a'kuyane kasameta ka rabata da kowa saima wulakanci da yake biyo baya ko? to dan kanka duniyace, kuma Wallahi tallahi saika bata takardarta.

Ustaz yace" nacema ko kasheni zakai bazan bataba, ya fad'a yana kuka dan hannunshi mugun zugi yake mai.

Saif ya tashi tsaye yace nabaka nan da sati biyu ka kawomata takardarta dan Aysha bazata dawo gidan nan ba, inba hakaba ni dakaina zan makaka kotu.

Ustaz ya'ce" wallahi bazan bata ba,akan nama! naman banza! masana cinshi sunce yana sanya ciwo, sai in d'auka inba iyalina, inta asara kudin magani kai kanacen bisa table bakasanin mike faruwa, ni kuma inata safa da marwa Asibiti, ana lalikeni a'banza, aini Wallahi duk duniya banda abokin kwarai dake d'orani bisa madai-dai ciyar hanya kamar mai Shari'a, da ba ina sawo naman ba, saida yaban shawara nagane gaskiyane,tinda su zuri'a sarkin fawa ne masana nama kenan, ba gayanan ba yama kanwarka illah har yanzu ko dakwaye bata sake haifaman ba,wanda taci ya tunkushe mata mara jinjiri yaki kwanciya, inka rabamu wazai rufamata asiri ya zauna da juya, iyee? kuma ma baccin nan wallahi ba wanda ya isa in fara noma har in samu al'barkarta kuma wani dan a'kuyan yace zai shiga har yayi k'ok'arin ya dasa tashi, saboda ni ba Addayus bane, ina da kishi matuk'a.


Saif yaji wayarshi na ring yasa hannu ya fitar tare da saka speaker ya'ce," inaji."

Umma cikin kuka tace" saif haka wannan d'an iskan yaron yama yarinyata? ga likita nan yana fad'amana mu yita Addu'a yana ganin kamar Aysha ta bugu sosai, kamar abun zai shafi kwakwal warta, in kam har bai shafaba sai ya sata ciwon mantuwa, kuma zatakai wata shidda kamin ta dawo dai-dai, ta karasa cu6kin kuka! a'fusace Umma tace ka gwarama shege kai, kasa kulki kacima shegen kan'nan nashi mai kama da kwaryar kauye uwa, kaima kanshi muyvun dukan da sai kaga jini ya had'e da kwalwarshi kamin ka kyaleshi, in'yaso yanda Zanyi jinyar ��iyata itama uwarshi tayi jinyarshi haka..

Saif a'jiyar zuciya kawai yake saukewa, jin bala'in da yasamu k'anwar shi, cikin karaji yace ma USTAZ kaji dai ko? kaji da bakin ka ko? Amazhabar ku miye hukuncin wanda yayi kisa.?.

Jikin USTAZ na rawa ga zugin hannun shi ya'ce" a'mai hakuri kawai.

Saif ya dakamai tsawa tare da cewa in'baka ban am'saba Wallahi saina raunata lakkar bayanka, zanbi umarni uwata inma abunda nike so dan ubanka kuma Wallahi ba akomi.

USTAZ ya'ce" a'kasheshi.

Saif yace "wanda ya raunata wani shi miye hukuncinshi.?

Ustaz ya kad'a kai yace" akyaleshi dan Allah tinda aikin shed'an ne, bana mutum ba.

Saif yace Wallahi tallahi zamu jirayi falfad'owar Aysha duk a'bunda sakamako ya bada Wallahi haka kaima zanma, muddum k'anwata ta zama mai mantuwa ko mai tab'in kwalwa Wallahi kan fanka zan mayar dakai, ai'kason kan fanka ko? Karshen wanda baida hankali ko, to Wallahi mahaukaci zan mayar dakai, sai kayi tsirara zaka dinga bin hanya.

Auzubillahi ya saifillahi, wannan wane irin bakine, da bad'ala,ya ka keman wannan fatan taya zakaiman fatan komawa gilu,kuma shawaraki, ka yimata fatan ALKHAIRI mana shine yafi wannan fadace fadacen...

Saif ya'ce" tabbas na biyema agidan nan yau Wallahi saina halbeka,ya jawo hannun USTAZ keeeeee marar lafiya yafara ja.

Ihu ustaz ke kur'mawa baji bagani, ba salati ba komi sai ihu .saif bai kyaleshiba saida ya fito dashi har wajen motarshi, kana ya watsar dashi ya shiga d'akin AYSHA har bedrom d'inta ya tsaya yana kallon, mima zai tattara !da yaga bazai iyaba kawai ya rufe ko ina ya sako key din aljihu ya fito, tare da shurar ustaz daketa ihu da kafa ya ficce.

Saif na zuwa zai fita yaga sodoji sun zagaye mijin Maryam da bindiga sunce ya k'ara motsi sai sun halbeshi, dan burin shiga gidan yake, yaji ihun ustaz.


Saif yace ku barshi muwuce, suka kyale shi suka hau mota suka wuce suna sakin jiniya. da sauri Najib ya fa��a gidanz cen wajen motar ustaz yaga ustaz zaune kamar murhun gawayi yana kuka, har Najib zai gif tashi ya dawo dan yaga kamar ba USTAZ ba, da sauri ya k'araso ya d'ago fuskar USTAZ ya'ce" lah ashe kaine? miya had'aka kai ko USTAZ da sodoji....?

Cikin kuka USTAZ ya'ce" ka kirawo man Alhajin mu dan Allah, a'taimakaman a'dubaman hannuna, Wallahi ya karyani na shiga ukku ina Ango, kwana biyu kacal an'man babba ilah, Amarya da illah Ango da illah, nashiga ukku ni Angon kubrah, kubrahhhhhh!!!! ya kwalama khadija daketa wayarta hankali kwance k'ira.

Sauran ka��an dariya ta kama Najib ganin fuskar ustaz yanda tayi ba kyan gani, lallai saje ga namiji a'done matuk'a, sai hancishi da yasha duka ya kumbura kamar tattasai, Najib yace kai kodai yan kidnapped ne suka shigo? to kuma ai in'sune tafiya zasuyi da kai,to mi yakai na aski kamar yan 419...

Ustaz ya dakamai tsawa ya'ce" kai bansani ba, duka yaushe na sonka da zankwashi sirrina in'baka, kodan kaga d'azu na fadama? shima dan nason abunda ya shafi aikin kune,maza ka Kira iyayena ko ka duba man hannun.

Dariyar da kecin Najib ya saki ba kakkauta wa,yace"kai dai gakanan an'maidaka mace anma kace sai kayi koyi da zaratan maza, har fad'a ka keman, ina ita matar taka take ?ko ince ina wayar taka?

Ustaz ya tina da wayar na ciki ga khadija saikiranta yake shuru .

Najib ya mike tare da cewa bari a kwankwasamata k'ofar.

Ustaz yace kull karka soma, bazan yar jema kowa ba!yaci gaba da kwala mata kira .
Zuwa cen sai gata ta fito daga ita sai vest da D'an zani.

Ido ustaz ya zaro ganin ta haka,baison sadda yafara k'ok'arin mikewa ba,amma ya kasa, dakyal ya dafa motarshi ya mike tsaye, Najib da baison mike faruwaba saiji yayi USTAZ ya cimimiyeshi yaa da d'emai idanuwa....
1/13/22, 09:55 - Buhainat: 4��_/Q2��_/Q&4��_/Q3��_/Q

Sosai Najib ya rikice da hannu d'aya ya tura USTAZ! take ya fad'i bisa hannunshi ya saki ihu .

Cikin sauke tagwayen numfashi Najib ya'ce" baka da lafiyane da zaka rufeman idona? sai kace marar ha=^...

Bai k'arasaba idonshi ya sauka kan Khadija, itama ta kalleshi! karcet tayi d'aki da gudu jikinta na rawa, ta D'ora hannu akanta tana nashiga ukku, miye hadin mutumin nan da USTAZ?.

Najib cikin rawar murya ya cema USTAZ kai wannan yarinyar itace matarka?

Ustaz ko kulashi baiba sai kuka yake jage,-jage da hawaye .
Karcet Najib ya fita daga gidan, bai jima ba ya dawo ya bashi wani abu akwali,yace" ka gwada ka ganema idonka, sauran bayanin ba yan zuba.

Cikin kuka ustaz ya mika hannu ya kar�i abun da aka bashi yasa cikin al'jihunshi, tare da cewa kaiko baka da mutunci kason hannuna tsami kawai yake, amma ka kasa taimaka man matsayinka na likita.

Najib yace" gaskiya ba fannin karaya nike ba, kuma akwai buk'atar atai da yan sanda,sannan akwai aikin da zanyima wata nama makara, amma bari in kamaka in kai ka bakin )�ofar ka, sai ta fito ta shiga dakai.

Ustaz ya ��aga kanshi, ya kamashi ya kaishi,Najib ya ficce yana mamakin ya akai yarin yar nan ta zama matar USTAZ.?

Acikin gidan USTAZ ya dage ya nata buga Kofar sosai kana khadija ta fito a'furgice ta bu��e, ta kalli wajen da taga Najib taga bayanan cikin rawar murya ta'ce" miye ya cemaka?miya fa��amaka? Wallahi sharri yake man.

Ustaz Yace bansaniba, ashe haka kike?bakida hankali bakison ciwon kanki ba? saiki fito haka ?
Yakamata kenan?
Daga kawoki ko kwana biyu baki cikaba amma kifito haka,ya dace, koda kuwa ni kad'aine agidan..
Khadija ta sauke ajiyar zuciya tare da sakar mai harara , ta'ce" yo nida gidan aurena, in ban sakata na walaba ya zanyi, kuma ai laifin kane, da kabani kayan da zansanya ai da hakan bai faruba, ni ku��i ma nikeso kaban a'yiman sayayya .

Ustaz dake zaune ranshi ya �aci da abinda tace yace maza ki ��akkoman waya ta, bakiga abunda yasameni ba?

Khadija ta yamutsa fuska tace naga ka koma yaro,wallahi sai najima duk kaban haushi da akaima kwal ��in nan,ga wani kanka yayi wani tsururu kamar gwangwanin madara Wallahi mtss inama amfani,saje sai ma'a....

Mikikace.?
USTAZ ya am'bata da sauri .
Cikin in ina tace nace saje sai masoyina USTAZ nada,amma ba na yanzu ba, miyasa ka aske abun wasana.

Ustax yace bansaniba maza ��akkoman wayar.

Khadija ta juya ciki tana yatsina fuska ta ��akko mai ta kawomai, ya karba ya lallatsa tare da kangawa da kunne, ya naji an ��aga yasaki kuka yana Hajiya an mayar dani musaki a'taimakaman akawoman mai gyara, an'karyaman hannu an man gudun-gutsun kamar naman rago har cikin ��akina wallahi Hajiya..
Agigice Hajiya ta tashi tsaye ta'ce" kace mine? Abdullahi waye ya karya ka ?kuma mi kai mai?

Ustaz Yace" sai dai kunzo, ya kashe wayar yana yarfe hannu dan sosai yanzu hannunshi ke mai zafi.

A�angaran AYSHA tin bayan tafiyar su hankali tashe ga yaranta da Abdul yasa a'mota ya tafi da su da Aunty Maryam suka kaita Asibiti, ganin tare suke da Maryam aka karbeta aka shiga da ita A&E aka rufu akanta dan sosai kanta ke zubar jini.

Aunty Maryam ta fito taga Abdul rike da

Please Login or Register in order to submit comment