Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abokanshi basu ankaraba sai zaman jira ake.

Haka yakaita har dakinta yafita ya rufe gidan gam ya kashe wayarshi yadawo ciki ya zauna yana murmushi yace dama wannan taron duk gulmace da bidi'a.


Aysha tace wai mikake nufi? kana nufin bazaka bu��e k'awayena da yan uwana su shigoba?

Ustaz yace eh gaskiya kiyi hakuri matata baza aman bidi'ar nan ba agida ke nikeso kadai ingani akusa dani.

Rai bace ta yaye lifayar jikinta sosai surar jikinta ya bayyana lace ne mai kyau ajikinta pink color dinki riga da siket sunkamata tsam, kasancewarta mai jikin kiba madai-daiciya ko ina nata acike Masha Allah tace to wallahi baka isaba wato dan kasameni yau shine zaka nunaan baka bukatar yan uwana ko?

Yau nefa kawai saikace bazaka bude ba.

Ustaz ya zubamata jajayen idanuwanshi yace eh gaskiya bazan bude ba saboda duk bidi'a ce wannan taron azo azigeki kiki yimin biyayya..

Aysha idonta ya kawo kwallah tace Dan Allah Honey.

Ustaz yayi dariya yatashi yasaki labule dakin yayi duhu sosao yace abunda yasanya kikaga nasaki labulan nan ina matukar jin kunyar fadamaki magana ido da ido.

Yakarasa wajenta tare da tallabota, akunne ya radamata miji na bukatar kasancewa da matarshi halaliyarshi....A��]
{
1/13/22, 09:55 - Buhainat: ��c��c��c��c��c��c��c��c
MATAR USTAZ
��c��c��c��c��c��c��c��c
NA UMMY AYSHA
��T���1��_/Q9��_/Q&2��_/Q0��_/Q

""" AYSHA ta zaro ido tare da tureshi ta'ce" karka soma, karma ka fara Wallahi,an'fad'ama ni Jakace da zaka Hayayyak'eman yanzu da rana, harda wani sakin labule, to Wallahi maza ka bu��e get ga yacen ana bugawa ayimin hidima kamar yanda akewa kowace mace.

Ido a limshe USTAZ ke binta da kallo, dan shi harga Allah baida bukatar wannan Bidi'a matarshi kawai ya keso, in'kuma taro a'keso a'mai a'bari sai ta Haihu kawai.

Aysha ta'ce"magana fa nike ma.

USTAZ ya'ce" ba matsala".

Aysha ta'ce" kamar ya ba matsala?

USTAZ ya'ce" ba cewa ki kai a'barsu su gaji su koma ba?

Bakin CIKI ya sa AYSHA fin'cike jikinta ta fad'a kan Gado ta fashe da kuka, wato tin yau dan ya sameta zai gwadamata baya da bukatar kowa nata kenan ko, ba komi Rayuwa ce.

Sosai a'ke buga gidan kamar za a'b'allashi Amma USTAZ yayi banza da su, saima shiga yayi toilet yayi wanka ya sanyo jallabiya ya fito, ya'ce" tashi kiyi Sallah zanje masallaci in dawo.

Aysha ta sha reshi! Amma a'ranta murna take ai dole in yaje fita su shigo, tana ganin ya fito farin ciki ya kamata harda lallabawa ta koma wajen window tana lekenshi, zuciyarta ce ta kusa bugawa ganin USTAZ da dogon tsani yayi wani D'an korid'o na gidan ya tattaka ya haye katangar, yayi zamanshi da ram cike da kuzari ya sake sab'ar Tsanin ya mayar dashi ta waje ya hau ya dire, tare da kwantar da Tsanin yayi Masallacin.

Kuka Aysha tasa kamar zata shid'e cikin karaji ta'ce" shikenan na Auri bala'i, mai kulle Malam, ya aylah kabani juriya da huakuri, wayyo Allah Musty iyayen ka sun cucemu da yanzu muna nan a inuwa d'aya cike da farin ciki, tasha kuka sosai kana ta Hakura ta tashi ta warware kayan jikinta ta fad'a toilet tayi wanka, ta:sanya riga marar nawie tayi Sallah hade da Azkhar, tana gamawa ta fara tinanin Rayuwa, jin ana isha tayi abunta tare da fesa tirare ta lallaba ta haye gado dan kanta ke masifar ciwo, kwanciyar ta keda wuya bacci yayi gaba da ita.

Ustaz Sai da ya gama Sallah ya gan-gara bakin titi ya hau machine yayo masu sayayya kaji da sauran kayan makulashe, yana dawowa aka saukeshi nesa da gidan shi ya duba yaga ba kowa kana ya aza Tsanin shi ya hau, ya kuma d'auka tsanin ya jefa ta ciki kana yabi akai ya sauka, ya k'arasa wajen get din gidan ya dinga jin hayaniya ta yam mata kala-kala ,A'ranshi ya'ce" ga yanan mu munyi ibadar mu sukam suna nan suna jira, inama am'fani shiyasa kullum zamuyi Addu'a sai mun Bude da Allah ya tsaremu da Biddi'a kullu yaumu,Dan Bidi'a Wuta ce zallah,yayi tsaki ya shige d'akin tare da Rufewa .
Bayan ya gama komi ya k'arasa wajen Aisha da ganan naja kofar na fito.

Da Asuba USTAZ rungume da Aisha kanshi a'kasa yana bata Hakuri da lallashi, batace mai komi ba sai kasa datai da kanta itama tana jin nawin shi kwatan kwacin yanda yake jin nata, cikin kuka ta'c"e ko kabari sai an'gama taro.?

Ustaz ya'ce kiyi Hakuri zamuyi walimar Sunna ne, kuma am'fison ka Tara da iyalinka ina fatan kin fahimceni..?

Bayan watanni goma Aysha ta sumbulo Yaron ta mai suna Usman,(sunan Maifinta kenan)yaron tamkar balarabe saboda kyau, ya had'a da kyan USTAZ dana Aysha, bayan sungama wanka USTAZ yayi sabon Aboki mai Shari'a, ya share Mujaheed saboda yacika matsamai akan ga abunda ya dace.


WAYE MAI SHARI'A.


MAI SHARI'A mutum ne da bayason yaga wani ya fishi, a'cikin kasuwa ko kad'an, ada bayason USTAZ kwata-kwata ganin yanda yake da customers bakamar shiba, ga USTAZ attajirine na mutunci,dan kaf yan gidan su ba wanda ya kaishi Arziki, Mai Shari'a ya fara shishigemai saida yaga yasamu k'arbuwa kana ya fara jefomai ma'anonishin,ganin USTAZ duk abunda ya fadamai yake d'auka ya samu damar nunama USTAZ duk sadda Namiji ya kasance yana sakar ma iyalinshi ku��i tana facaka to Mace akwaita da wayo, zataita ta rasu taje tagi na wata babba masana'anta ta yanda zakaga in kace tayi ba zataji nawi tace batayi b,a saboda ba abun Hannunka take jiraba, tana da nata na kanta.

Sosai maganarshi ta samu muhalli a'zuciyar USTAZ dan bayan auransu ba laifi duk abunda Aysha ke so yana mata.

Mai shari'a ya'cema "USTAZ ka ganni nan ba abunda bandashi na kayan ABINCI a'gidana, shiyasa ko biyar bana bama Hajara, na yarda duk abunda ta keso taman waya zan kawomata ko biki zata na kashe mata biki, saboda haramun ne, duk abunda nai niyya zan'bata ada takai daga baya na fahimci in'kaba da D'ari biyar fatan wanda kaba yamaido maka Dubu, kaga akwai bidi'a anan ko ba haka ba?

Ustaz yace kwarai ko A'bokina Wallahi inajin dadin zama dakai sosai saboda ina k'aruwa.

Mai Shari'a yayi Murmushin samun nasara ya'ce" to Wallahi Hajara ko waya ban barta da itaba mai kyau, saboda ba damar in'koma gidana in fiddo waya ina chart da customer d'ina da suke siye ko nike siye, sai gaka tana ��aukar ta-ta itama tana abunda ta keso tana huraman hanci, kaga kenan biyayyar da a'kace sumana a'matsayinmu na tsama dasu bazasuyi ba ko?..

Ustaz yace wannan gaskiyane Wallahi, kuma ni kaina haka Aysha keman, duk abunda nayi sai tayi maka mancin shi, in rasa wake tire ta.

Mai shari'a ya'ce" yawwa Aboki ka gane kenan, to ba kowa ke tire suba sai wannan K'awayen nasu da kuma makwabtansu dake shigar marece, daka fito a'fada ana baje sirrin ka sai kafito ai'tamaka daukar wawa .

USTAZ yace A'uzubillahi wai dama haka matan suke? ka son ni ba ruwa na da wannan binciken, kuma bana shiga shirgin su.

Mai shari'a ya'ce" ai sun mafi haka, in'kanason samun kan matarka kai ka��ai to ka rabata da kowa sai wanda ya dace, kar'ka bayar da k'ofar da za a'dinga shiga gidanka koda yaushe tinda dai ba a'bariki bane.

Sosai USTAZ yai na am da shawarar Mai Shari'a yamai godiya ya tashi.

Wanann Hudubobin su suka zauna daram a'zuciyar USTAZ, dama tin farko sai a'hankali dan Aysha nada Hakuri ne shiyasa baka ganewa, USTAZ yazo gida ya fara tsiro da abubuwa masu wuyar sha'ani ,tin Aysha na daurewa har ta fara mayar da martani tana nunamai gajiyawar ta, ga fita baya bari sai yaga dama, ya k'arbi wayarta ya bata wata lalata ta,tayi Hakuri ta shareshi ya rabata da kowa nata sai matan A'bokai, ba k'aramin damuwa Aysha ke ciki ba ko fara'a USTAZ bata gani sai bukatarshi ya tashi, a'haka har ta haifi Sadeeq ganin halin k'uncin da take ya sanya ta fara kula wata sst Maryam makwabciyar su, a'sace suke k'awance har Maryam ta son wani a'bun nata, daga nan Aysha ta bukaci ta naso tamata Allura planing dan ta dan huta, dan bata bukatar haihuwa a'yanzu, itama Maryam ta goyi da bayanta ta mata, a'haka rayuwar taita juyawa USTAZ yazama wawan karfi da yaji ko abu Aysha tamai sai ya fad'ama mai Shari'a, daga karshe Mai Shari'a ya fara jan USTAZ gidan Yayar shi da niyyar sunzo gaishe ta, tin USTAZ baya sakewa har ya fara daga baya yaizo ya kecema Mai Shari'a Aysha ta fara gudunshi A'shimfid'a, ba damar ya neme ta sai fushi da zuciya. MAI SHARI'A ya'ce" shawarar da zan baka ka k'ara aure kawai, kason mace in'tana ita kadai ba k'aramin iskanci take ma mutum ba, gani ma suke su Hakuri suke damu Wallahi, ni kaina na fad'ama nakusa AURAN nan nan da wata biyu in huta.

USTAZ yayi shuru yace Anya Aure mafitane kuwa.?

Mai shari'a yace yo ai dan cika Sunna, muna fama da geme kamar na Masara amma ace matan mu d'aya ai'kaga ba girma.

Nan nefa Mai Shari'a yay ta tusama USTAZ son Aure daga baya yabashi shawarar nai man khadija yar Aunty Mai Shari'a, amma da sharad'in sai ta k'arasa shekarata ta karshe da baifi watan niba.

Dad'i sosai ya kama USTAZ zai auri Yarinya da tafi Aysha biyayya, daga nan ne duk abunda ya shafi mai Shari'a sai USTAZ ya rike wuta Aysha taje, ita duk batason mike faruwa ba, taje gidan Aunty mai shari'a bila adadin dan ko ciwon kai tai sai USTAZ yace taje ta gano Aunty Abokin shi batada lafiya, haka zata kwasa kafa taje ta dawo ko mafalkin da USTAZ yayi na Auran shi da khadija ne, shiyasa ya tashi cikin farin ciki wannan kenan.

Da safe USTAZ yayi wankan shi yayi kyau matuka, dan ko bakomi Aysha tayi K'ok'ari ta nan taraba shi da duk wata jallabiya inba sawar dare ba, yafito zai tafi kasuwa fuskarshi a'daure Aysha tace ya maganar fitar da zanyi jiya banje ba?..

Ya mikomata D'ari biyar ya ficce, har ya kai k'ofa yace gidan mai shari'a zaki kiyi kamar awa biyu, sannan kije cen inda zaki ko ina kiyi minti goma kidawo kinji na fadamaki, kuma zan'biya wajen Abdur-rahman din inji miyasa ya baki wayar ,yasa kai yakama gabanshi.
Yana fita Aunty Maryam ta fado tace nasamu Abdul din, kuma na fad'amai yanda mukai," yace ba matsala". Aysha ta mata godiya Aunty Maryam tace bari in tafi na fad'ama mai gida na zai mai magana an'jima har kasuwa zai iskeshi.
Da sauri Aysha tace ba matsala nagode da k'ok'ari.
Aunty Maryam tace bakomi ta fita.

USTAZ na fita yayi tsinke gidan su Aysha, ko Umma bai karasa ya gaida ba yatsaya A,
D'akin su Abdul ya tambayeshi "fuska a'daure Abdul yace eh ni na bata, saboda baka barinta zuwa kuma mahaifiyarmu na kewarta, shiyasan ya na kaimata tawa kamin in saimata sabuwa...

Kan USTAZ a'kasa yace to mafi Mishkila ya tada motarshi yayi gaba. .
Abdul ya'ce" na tsaneka wallahi amma nakusa kwatarma kanwata yanci Wallahi, bari dai ayi auran nan kagani da wani banzan gemanka kamar gashin ��iyar baby...

Bayan sati biyu Aysha kwance tana mura kanta yayi zafi matuka dan mura na bata wahala sosai, USTAZ ya fado gidan yayi tsaye kanta tare da cewa Dan Allah tashi kije gidan Aunty Mai shari'a ki gano ta, ulcer ta ta tashi, kuma kimata murna d'iyarta ta kammala makaranta.

AYSHA ta dago jajayen idanuwanta ta'ce" Wallahi USTAZ bazan iyaba kaina naman ciwo sosai, kason mura nike ka zoman ma da maganin kuwa?.

Rai a'bace ya da kamata tsawa tare da cewa wallahi sai kinje, ni zaki maida mutumin banza mutumin wofi, in masu magana zakije kana kiceman bazaki ba, tashi Dan Allah Malama, da daddare zan dawo miki dashi...

Aysha ta tashi tana kallonahi ta'ce" wai minaima ka kwana biyu duk ka canza, komi zanyi sai kwatsa da hantara..

Ustaz ya'ce halin banzarkine dakika koya shike had'ani dake, kin cika k'orafi ga rainuwa dan Allah kitashi nace...

Aysha batace komiba sai tashi da tayi ta d'auki dogon hijjob inta ta sanya, tare da safa tace bazan iya sanya nikaf ba saboda numfashina saita baki nike.

Ustaz yace naji ta shi ki tafi..

Haka ta tashi tana hada hanya ta fita, tayi tafiya mai dan tsayi kana ta iso dan gaban makaranta su Usman ne, da tazo ta dade tana buga kofar kana aka bud'e, wata budurwace doguwa fara ta bude suka zubama juna ido, hakanan Aysha taji gabanta ya fadi suka gaisa ta wuce ciki wajen Aunty, suka gaisa kamar kullum suna fira sama-sama budurwan nan tazo ta kwanta, tare da lumshe ido ,Aysha ta cema Aunty ina khadija yan makaranta.?
Aunty tai murmushi tare da nuna budurwar ta'ce gata anan ..

Ido Aysha ta zaro tace kai masha Allah She budurwace, nifa nasanya yarin yace lallai Aunty kunga jiya kunga yau.

Aunty tai murmushi ta'ce" aiko da dama mutane cewa suke waini na haifeta .

Aysha tace dan baki da jikin k'iba shiyasa.

Aunty ta'ce" hakane Aysha dama inaso in maki wata magana inba damuwa naga kamar bakisani ba .

Sosai gaban aysha ya Fadi tace miyafaru Aunty?.. Aunty tace to ba komi bane ba dama mijinki ne zai Auri khadija, tin tana gab dashiga ss3 yakawo kudin auran shi, da goro akasa rana yanzu dai bikin sati ukku ya rage dan Allah kiyi hakuri ku zauna lafiya..A��]
{

Naira dari ukku ne duk mai so na zafce dari duba da yanayin da ake ciki mai so yabada 200 ya kirayi wannan number.

07038423451

Last free page
1/13/22, 09:55 - Buhainat: ��c��c��c��c��c��c��c��c
AURAN USTAZ
��c��c��c��c��c��c��c��c
NA UMMY AYSHA
��T���2��_/Q1��_/Q&2��_/Q2��_/Q

"""Aysha tayi shuru zuwa wani d'an lokaci Hasbunallalu wani imal wakim take am'bata aranta zuwa cen ta d'ago fuskarta cike da fara'a kamar koda wane lokaci ta'ce" bakomi Aunty Allah ya had'a kawunan mu ya bamu zaman lafiya."

Fuskar Aunty fal da fara'a ta'ce" Ameen naji Dad'i kwarai da gaske.."

Aysha ta'ce" ba komi bari in'tashi zan biya in d'auki su Usman a makaranta.

Aunty ta'ce" ba komi ki gaida Gida". khadija tashi ki rakata. ta'ce da khadijar dake kwance ta lumshe ido.

Fuska ba Sukuni Khadija ta taso suka fito ba wanda ya'ce" da kowa komi, har suka isa get Khadija ta juya Aysha ma ta koma .

La'ilaha illah anta Subhanaka inni kuntu mina zalimin! shine kalmar da Aysha ta fara fad'a lokacin da ta fito jikinta ya fara d'auka Rawa ko ta ina, Ashe dama tsantsar so zai iya juyewa ya zama k'iyayya, ni USTAZ zaiwa haka duk Hakurin da nike da baud'ad'an halinshi, yanzu a'matakin iliminshi shine zaizo neman Aure ba tare da sani naba, hmmm A dai-dai wannan lokacin ya kanata in dawo Aysha ta- ta da Wallahi, ya kamata duk wani tsantsar iskanci da zayyi zanzubamai ido inga iya gudun ruwan shi,ta tashi taci gaba da tafiya harta isa makaranta su Usman, ganin akwai sauran lokaci dan karatu suke kawai ta wuce gidan ta, har zata bud'e gidan kuma ta fasa ta fada gidan Aunty Maryam .

Aunty Maryam na zaune taga Aysha murna ta kamata! ta'ce" yau kece agidana?

Aysha ta'ce" ai'kuwa magana nikeso muyi dake ta fahimta, shape-shape ta fad'ama Aunty Maryam abunda ya faru yanzu." Dogon salati Maryam ta sanya sai ga hawaye shar a fuskar ta, dan harga Allah sosai take son Aysha so bana wasa ba, cikin kuka ta'ce Aysha abunda USTAZ ya zab'ama Rayuwar shi kenan?

Ina iliminshi ?
Ina bin Dokar Allah daya ke?
Mikikai mai da tsantsar so ya riked'e ya koma zalinci da k'untatawa?

Aysha ta'ce" oho" kila duk cikin ilimin nashi ne, Wallahi Aunty Maryam ni na son sai da tsantsar so ake kishi, azahirin gaskiya ban ma USTAZ wannan ham'shakin son balle inyi kishi na hauka a'kanshi, kuma Wallahi tallabi ni Aysha nayi Al'kawarin duk wuya duk rintsi bazan yiwa USTAZ wannan maganar ba ,kinga sati ukku ya rage ko? to ya dad'e ina kwance bai shigo yace in gyara zai wuce da wata ba. ta fada cikin hargagi.

Aunty maryam ta'ce" kiyi hakuri Aysha! fatana ki ��aukeni kamar yanda na d'aukeki, Wallahi tsakanina da Allah nike sonki, kana zanyi am'fani da dukiyar da Allah yaman zamuyi a'bunda ran mu ke so a'bikin nan, ta yanda babu shegen daya isa yakawo maki raini shikuma ki zubamai ido kiga iya gudun ruwan shi kinji?

AYSHA ta'ce" baki da matsala da wannan yanzuma wayata zan fiddo in fara am'fani da ita.

Aunty Maryam ta'ce" ai layin ki zaki sanya akai ko"?

Aysha ta'ce eh shine.

Maryam ta'ce to zanyi miki transfer credit yanzu in yaso saiki kira Umma kiji ta-ta shawara ko?

Aysha ta'ce" haba ki barshi Wallahi ba damuwa nagode hakama ".

Maryam ta b'ata fuska ta'ce" miyasa kikeman haka ne dan Allah? ko dai baki yarda da ni bane?

Aysha ta'ce aa wallahi ba haka bane! kawai kinson yau da gobe sai Allah, amma shikenan Nagode. sukai sallama ta fita! tana fita su Usman na dawowa ta kamasu suka shige gida shape-shape ta masu wanka ta zubamasu sakwara Doya da miyar a'gushi da tayi, sai kamshi take miyar ko nama babu dan USTAZ yace yawan cin nama cuwul wuta yake kawowa, bayan sungama sukai Sallahma tayi masu bitar k'aratu kana ta kaisu suka fitsari ta kwantar dasu, tare da tofesu da Addu'a ta fita har lokacin USTAZ bai shigoba abunda bayayi tayi wankanta fess ta fesa turarukanta da Aunty Maryam ta bata ta koma d'akinta tare da dakko wayar data cika da charger ta sanya layin ta ta kunna cikin lokacin wayar ta bude rass da ita tamakar sabuwa farin ciki marar musultuwa ya kama Aysha, ganin ta yau da babbar waya, shekara biyar kenan rabon ta da waya sai k'arama! k'arama ma saida hakkin a'shana malatsinta ke am'fani.

Tana kunna wa message ya fara shigo wa, ciki kuwa harda na transfer da Aunty Maryam ta Mata na D'ari biyar, da��i yakama Aysha ta lalubo Number Umma ta kira, bugu biyu Umma ta d'auka cike da farin ciki! ta'ce Auta kece A gari inji maki bak'o?

Aysha tai Dariya ta'ce Wallahi kuwa Umma! nan suka gaisa suka fara firar duniya anan Aysha ke sakoma umma zancen bikin Ustaz da bata saniba.

Umma tayi mamaki matuk'a amma bata nuna ba, sai cewa tai haba yo miye a'bunda yake maki shizai mata in ya kawota, kuma ke ai'kwara da akai, a'nan ne zai fahimci wacece ke, da kuma irin Hakurin da kike dashi, karki wani damu nason kishi wajibine kuma halittace, amma sai kiyi Hakuri ki danne kinji Auta ta? ina mazajena.?

Aysha ta'ce" Insha Allah Umma nah, Wallahi ina kewarki matuk'a,sunyi bacci inaso inzo in ganki.

Umma ta'ce" ba matsala duk sadda ya barki ai'kinzo kuma yanzu ga waya zan dinga kiranki, Allah ya d'ora da zumuncinku da Maryam tana da kirki Wallahi, kuma Abdul dama ke taso yaga yasaimaki, kinson ai'kin nan dayake nema da gidan da yake shiya kwashemai duk wani tattalin ar'zikinshi, amma Alhamdulillah an'samu aikin wata ukku kenan...

Sosai AYSHA taji Dad'i ta'ce" umma ki gaidashi da yah Saif soja mazan fama.

Umma tayi dariya ta'ce" zayaji shima ai an'kusa kammalawa, yace;man nan da wata biyu za a'basu office.

Aysha taita tsalle tama manta da wata damuwar ta! sukai sallama takashe .

Nan tashiga app din da littafai suke ta fara karanta wani littafi na UMMY AYSHA MAI SUNA ZAMAN TASHA.
sosai labarin ya d'auki hankalinta sai kwasar dariya take harda kwallah, jin cakwakiyar dake cikin littafin, kwata-kwata ta nemi wata k'aramar damuwa ta rasa, har shad_aya tana karatu kuma ustaz bai shigo ba, ko a'jikinta dan burinta takai karshe kamin ma ya dawo,shad'aya da kwata ya bude get d'in gidan yashigo, Aysha tac'e" kash Wallahi naso inji ya zata fashe tsakanin Modibbo da Tsohuwa hahhha ta saki dariya ita kad'ai, USTAZ na bud'e palo ya murtuke fuska .Aysha ta fito fuskarta fall da fara'a tace Ustaz sannu da zuwa.

Shaye da toka yace yawwa ina yaran?..tace sunyi bacci.

Yace kin gano Aunty d'azu?.. AYSHA tace eh mana.

Ustaz yace kinma yar ta sannu da zuwa?

AYSHA ta'ce" duka dan itama tayoman rakiya har get.

USTAZ ya washe baki ya'ce ai khadijatul kubra akwai hankali da natsuwa uwa uba godiyar Allah..

Aysha tai murmushi tace gaskiya kam naga Alama, Allah ya bata miji nagari.

Ustaz yace Ameen yama baata mai kyakyawar dabi'a dai-dai da tarbiyyar gidansu..

Sosai maganarshi ta mata zafi amma bata nuna ba sai murmushi da tayi tace to Allah yataimaka.

Yace Ameen yawwa gobe kishirya kije gidanku keda yaran, za ad'anyiman gyare-gyare dan har d'akin cen nikeso a'sama tiyil kema za a'maki penti.

Aysha ta'ce kai Masha Allah kace gwan-gwaje mu zakai kenan, to Allah yakaimu ya k'aro azziki mai Al'barka.

Ustaz yace Ameen baki sanin gwan-gwaje wa, sai nan da sati ukku rana mai kamar ta yau, zan zuba kayan a'latu a'gidan masu d'aukar hankali marar godiyar Allah...

Aysha ta daka tsalle ta rungumeshi tare da cewa ina maka murna ya Ustaz.

Ya b'anb'are ta daga jikin shi tare da cewa cikani wanka zanyi, banason damuwa a'dai-dai wannan lokacin da nike cikin farin ciki..

AYSHA ta'ce Allah! to ayi Hakuri takoma ta zauna tare da lumshe idonta .
Washe gari cikin zumud'i Aysha ta shirya itada yara tin shidda na safe , USTAZ ya bata d'ari biyu yace ku hau napep da daddare zanzo d'aukar ku, in an'gama, in'kuma ba a'gamaba kuyi kwanciyarku kawai.

Aysha ta'ce to bamatsala sakhallahu khairan.

Ciki ciki yace Ameen.

Ita Aysha dariya ma yake bata waishi sabon Ango, shiya sanya ya keta cin magani,haka suka k'arasa su Usman sai murna suke zasu wurin Umma, dan tin Sallah raban su da gidan, mai adaidaita na tsayawa suka afka ciki da gudu suna kwalama Umma kira, itama Umma jin haka kar'cet ta taho tana maraba-maraba da yan jikokina, Allah Sarki dama zaku zo maman ku bata fad'aman ba, ta duk'a ta rungumesu tanajin soyayyar yaran da tausayin uwarsu har k'asan ranta, suna haka Aysha ta shigo ta tsaya tana kallonsu idonta fal Hawaye, itama a'guje ta k'araso ta rungume Umma suna Hawaye, suna cikin wannan halin Abdul ya shigo yana kwalama umma kira da mugun karfi .

A'zabure Aysha ta tashi tana lafiya yah Abdul.

Abdul bai tsaya komi ba, ya rungumeta ya'ce" k'anwata sannu da zuwa yau farin ciki a'kan farin ciki,gaki nagani ga kyauta na samu."
Ya karkace ya zaro key din mota yace Umma kinga wannan key din oganmu yabani shi,halak malak da gida anan Malali, Umma bakiga gidan ba, taf ke-ke Wallahi, gashi parta biyu kar'kiso kigani ga million d'aya na al'bashin farkona na wata ukku, kai Umma Dad'ai.

Haba kansuce mi Aysha ta fara taka rawa cike da farin ciki, itama umuma tashi tai tana Alhamdulillah Allah Abun godiya, tabbas ba maraya sai raggo, Allah nagodema dakasa Yarana suka zamamen garkuwa Alhamdulillah.

Fira sosai ta b'arke tsakanin Abdul da Aysha, Umma takwashe labarin komi ta fad'amai .
Abdul yace" Wallahi Wallahi Umma saina kwatarma Aysha yan'cinta cikin k'ank'anan lokaci, banaso kice komi amma bazan ce komi ayanzuba sai Saif ya dawo.

Umma ba tace komi ba dan itama Wallahi lamarin USTAZ ya fara bata haushi , Abdul ya'ce bari inyo cefane Umma ya fita.

Bai wani jima ba sai gashi da ledoji da katon2 din lemuka manya masu kyau da tsada, yashigo dasu yace umma ga kaji nan manyane guda goma a'yimana soye da miya da biyar, biyar kuma a'mana danbu lemuma goma ne, Aysha ta taima su Usman da biyar a'barmana biyar anan, yace Aysha yaushe zaki tafi ?kuma mi kike buk'ata ?yatambayi Aysha cikin kulawa..

Idon AYSHA fal da hawaye ganin yanda yan uwanta ke rititata da Yayan ta tace yaya bakomi.

Abdul ya b'ata fuska ya'ce" aa ko in canzo miki wayar yanzu?

AYSHA ta'ce aa Yaya kabarman wannan kartaga kamar na raina ko Umma?.

Umma tace hakane barmata Abdul ai yanzu a'kafara .
Abdul ya'ce to shikenan Umma mi kuke bukata.?

Nan Umma ta lissafamai ya sake fita ya hau Dalleloyar motarshi yayi kasuwa ya jido kaya nagani na fad'a ya yoma Aysha sayayya kaya sunkai kala ashirin manya masu tsada da wasu zafafan guda biyu duk d'aya dubu tamanin, a'takaice Abdul tin a'ranar saida ya kashe dubu dari biyar kana yayo gida da sayayya niki-niki, yana Sallama yaga Aysha tsaye tana waya da USTAZ yana cewa ke kima kwana, zakiyi sati d'aya dan aiki za ayiman sosai ko d'akinki rusheshi za'ayi.

Aysha harda tsalle ta'ce_"bakomi Allah ya kaimu."

Ustaz yace Amin tare da kashe wayar ! Abdul yaji da��in ganin bata sanya damuwa a'ranta ba, nan ya jata

Please Login or Register in order to submit comment