Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

munafukar ke shiga gurin ta,ko bayan Ku akwai Wanda ya San pin in shiga dakin,


Cikin zabura Kareematu tace yallabai wlhy na tuna akwai wata kawata a asibitin Nurse Zaituna rannan ita na baiwa abincin Nadeeya ta kai Mata bayan kwana biyu kuma shine aka neme ta aka Rasa, yarinya ta babu lafiya ya Sanya through out ban zo aiki ba,

Mikewa Jabiru yayi tare da kwada wa Kareematu mari me zafi da kara sanann yace shegiya dan uban ki duk kin san da haka kika tsaya bata mana lokaci a ina zan samo Zaituna ko miye sunan ta,

Idanu cike da kwalla tace tana cikin asibiti ita ma maaikaciya ce a can,

Daga haka be kuma ce musu komai ba ya Sanya Kai tare da bada umarnin a maida su cell,tare da daukan wayar Shi ya shiga Kiran layin Alh Kabiru,


**********Sen Rilwanu


Zaune yake a parlor ya zuba uban tagumi,kayan cima ta alfarma ce a gaban Shi Amaman sam ya kasa cin ko Abu daya,past days in nan Yana nan kawai ya Rasa me ke masa dadi a duniya,ya Sanya ya Hana kowa zuwa ganin Shi Banda Alh Kabiru sai Salis kawai yake iya gani,


Tunani yake toh wai shin Ina Nadeeya take ne ya shiga uku yarinyar nan in har bakin ta ya Bude Yana wani hali shike nan tashi ta kare muddum asirin Shi ya tonu Zaman garin Bauchi sai ta gagare Shi,wata yawu me daci ya hadiye da kyar tare da lumshe idanu,abun haushin wannan masifa ta Fado mishi ba time in haduwar kungiyar su ba,he is very sure da zai ga Odugwu da matsalan Shi ta kare domin sam babu wani effort da su Jabirun nan ke making,abun haushin kuwa shine ba a ganin Odugwu in ba ranar haduwa ba gashi shi sam Allah be bashi juriya ba yana shiga cikin matsala take nuna masa,


Fadowar da ya ji anyi a jikin Shi ana kuka ne ya sanya Shi zabura daga tunanin da ya fada tare da bin Afzaal dake kuka hawaye biyu biyu Akan kirjin Shi,

Da sauri ya Ciro Shi sanann ya bi Shi da kallon mamaki Yana Kai Afzaal uban me ya same Ka zaka zo kana irin wannan kukan,


Cikin kuka sosai har da shesheka yace Daddy Ashe Ashe,Ashe me Sen ya Fadi xuciyar Shi na bugawa,


Cikin kuka yace daddy Ashe Nadeeya ta ta mutu shine aka boye mun ba a a fada mun ba,Banda yau da jiki na ya Bani ba lafiya ba nace gwara na dawo na gani,


Be Kai ga karasawa ba Sen ya dauke Shi da Mari Tasssss kake ji,da sauri ya dafe kumatun Shi tare da mikewa,

Shima mikewar Sen yayi sannan yace Dan uban Ka ina Ka ji labarin Nadeeya ta mutu,shege me bakin Yan wuta.........




Assalamu alaikum🥰👏🏻


Ina fatan mun wuni lafiya ubangiji ya sa haka,


Alhamdulilah jiki Yana ta sauki na gode sosai da adduo'in Ku masu Kira masu turo mun sakon ni ubangiji ya Saka da alkhairi,Allah kuma ya bar kauna,


Ina me Baku hakurin jina shiru da kukai kwana biyu,Amman yanxu Alhamdulilah da sauki za kuna ji na akai akai in sha Allah,


Ina yi wa kowa fatan Alkhairi❤️

Sai zuwa gobe in me kowa me komai ya Sanya mun Kai.
[6/21, 8:37 PM] My Best Best ❤️: 😭😔UBANA NE KO KISHIYA TA 💔💔

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEYBEE)

.......

My what's app group link

https://chat.whatsapp.com/FKZuWu1yj7VJ9L6izLqLhA

Don Allah in har kin San ba karanta book ina da commenting bane zai kawo ki toh yi Zaman ki ba sai kin yi joining ba,haka zalika maza should stay away from my group domin na Mata ne xallah🙏🏻,

Ga masu son a tallata musu hajojin su should contact me via:

08100046388

..........
Page thirty

*********


Doc Nameer*****

Habeeb wai ina Ka Sanya wayan Ka ne tun dazu I have been calling u Baka dauka,

Yi hakuri doc Handsome na shiga wanka ne,me ke faruwa ko Ka Kira Ka ji lafiyar Ajiyar Ka ne,

Murmushi Nameer yayi kafin yace I trust you gee na san tana nan lafiya,kasan me ya faru,

AA sai Ka fada Habeeb yace Yana goge ruwan jikin Shi da towel tare da Zama a kujeran gaban mirror,

As expected kasan yanzu Yan sanda suka bar gida na,

Idanu Habeeb ya zaro tare da fadin Yan sanda kuma na me toh,

Wlhy ina asibiti suka daga ni wai suna son su yi searching in gida na,wai Bashir ya sanar da su Yana zargin ni na sace ta,Saida sun yi late daman jiki na ya Bani za a yi haka Wanda ya tsane Ka toh zai iya yin komai don ya ga bayan Ka, gudun haka ya sanya nace da Kai Zan maida ta gidan Ka don nasan Bashir ba Bari na zai yi na huta ba,

Dariya Habeeb ya Sanya tare da fadin gaskia I salute you my friend kana da brain ni ban taba tunanin abunda ya Sanya ka dawo da ita nan ba,na dau kana gudun zama daga Kai sai ita ne gudun samun matsala,ya kare Yana dariya,

Zan zage Ka Habeeb dan iskanci ko ni na kawo jaraba duniya AI na tausaya mata balle kai kan ka shaida ne ni bana bin Mata,

Jiki da Jini aboki na an Dade ba a Hadu ba,ya kare Yana dariyar tsokana,tsaki Nameer ya ja sannan yace Ka ji da Shi dallah ni lemme shower in zo mu karasa magana domin yanda aka Fara zargi na din nan gwara as soon as possible in dauke ta mu bar garin nan gudun fada wa matsala,thank god yau Allah ya taimake ni,toh shike nan sai Ka iso Nima lemme pray da haka ya kashe wayar tashi,

Kai Nameer ya girgiza da ya shiga dakin nashi ya ga komai Yana nan fes kamar ba bincike aka Shigo aka yi ba,Yan iska ashe mara sa kunyar karya ne, da haka ya kwabe ya shige wanka Yana mamakin me yayi wa Bashir ne da ya tsane Shi har haka,


*********Police command

Rai a matukar bace oga Jabiru ya Shigo cikin police command in,Kai tsaye office in Shi ya wuce tare da bada umurnin a Shigo mishi da doc Bashir,

Jiki na rawa Bashir ya Shigo office in ganin yanda fuskan Jabiru ke a turbune nan take jikin Shi ya bashi ba a dace ba,cikin dauriya yace ranka ya Dade kun same ta,

Mikewa Jabiru yayi sanann yace a gidan uwar Ka muka same ta,ni zaka bata wa lokaci Kai ya kare cike da tsawa,

Nan take ya rude cike da rawar murya yace sorry yallabai kuskure aka samu,ba gidan doc Nameer nake son cewa ba,

Da kallon mamaki yake bin Bashir in kafin yace toh gidan wa kake son cewa,

Yauwa yallabai bayan dogon nazari da na kuma yi na gano Shi Sen da kanshi ya sace ta Dan kawai ya Sanya mu a damuwa ya kuma bata maka lokaci ya Sanya shi cewa mu ne muka dauke ta,Amman am very sure da za Ku je gidan Shi za Ku ganta,that man is very evil aswear to almighty God Yana samun pleasure a yayin da yake azabtar da wasu Kai ne Baka san Shi ba,

Be Kai ga hade lips in Shi ba ya ji saukan Mari tassss,tsaban bacin Rai har idanun Jabiru yayi jawur,

Cikin Ihu yace out of my office nonsense,na ga alama Kai ma brain in Ka ya Fara tabuwa daman an fada mun zaka ce Shi ne ya sace yar sa,Banda hauka taya babban mutum kamar Sen zai sace yar Shi ya daura muku Akan me me zai yi gaining in yayi haka, stupid an Jima ma cewa za Ka yi ita ce ta boye Kan ta ko kuma ni ne nan na sace ta na boye,and I promise you yau sai Ka sha bugun da tunda uwar Ka ta yafe Ka ba a taba maka irin Shi tunda Ka bata mun lokaci sai na fanshe a jikin Ka fice mun a office Wawa kawai ya kare har Yana kumfan Baki,

Sim sim doc Bashir ya ja kafar Shi tare da barin office in Shi wlhy ya gaji ya gaji sosai da irin wannan bakar hukuban da suke ci a hannun wannan mugun Dan sandan da be son darajar bayin Allah ba(ni ko nace Kai kan Ka ba sanin darajar Kan Ka kayi ba,domin duk wanda zai je ya kwanta da matar wani ko yayi kokarin daukan ran wanni ko ya hofantar da lamuran iyalan Shi toh tabbas be san darajar Kan Shi ba balle har wani ya San darajar Shi),


*******Doc Nameer

Saida ya Bari Rana tayi sanyi sanna ya shirya cikin kananun Kaya tare da nufan gidan Habeeb bayan ya hado su tarkacen kayan Wasa da madaran Yara,sai ya siyo ice cream don ya san Nadeeya na so saidai be San ko za ta iya sha ba domin har yanzu jikin nata dai babu wani ci gaba,ko ruwa in Baka yi da gaske ba dawo maka da Shi take in Ka bata,tana nan kwance sai an daga sai an kwantar da tube Ake samun abinci yake shiga jikin ta,Shi ya Rasa wannan mutuwar jiki da ta samu na ba gyara babu dalili,duk wani necessary gwaje gwaje yayi ya gano babu wani matsala tattare da kashin ta ko jijiyan ta Banda brain in ta da ya tabu sakamakon aluran da aka yi ta Dura Mata,to sam ya kasa gane miye ke damun ta da ya haddasa Mata halin da take jiki,

A nutse yake driving Yana sauraran wakar Bunna boy ft Ed Sheeran (for my hands),Yana bin wakan a hankali a haka har ya iso gidan Habeeb in yayi horn aka Bude masa gate ya shiga da motar Shi,

A tsakar gida ya tarar da Habeeb suna Wasa da dan babyn Shi da ba wai ya gama koyan tafiya bane,sai abun ya bashi shaawa nan take ya ji Yana missing little Hanan in Shi,wannan matsalan Nadeeyar ne duk ta dauke mishi hankali kwana biyu be Kira ya ji lafiyar ta ba,

Parking yayi tare da fitowa,gaisawa suka yi da Habeeb in sanann yace da gate man in Shi ya fito da kayan da ke cikin motar Nameer in ya Shigo da su parlor,

Karban babyn yayi sannan suka shigo,na san ko na ce Ka zauna Ka sha ruwa ba yarda za Ka yi ba in ba Ka ga Nadeeya ba mu je suna jiki da Muhibba,

Murmushi kawai Nameer yayi sanan suka nufi dakin tarar wa suka yi Muhibba na fesa wa Nadeeya turare alamu sun gwada wanka ta Gama Mata,

Da kallo kawai Nameer yake bin ta ganin yanda take kwance tana bacci hankali kwance sai tayi masa kyau domin har simple kwalliya Muhibba ke Mata time to time a cewar ta mace ce AI don jinya ta Gama ta bara a Kula da ita ba,

Babu abunda zai ce da Muhibba ko Habeeb saidai fatan Allah ya Sanya su Gama da duniya lafiya domin tabbas Yan uwan rufin asiri ne su,

Tun Ranar da ya sanar musu Nadeeya na gurin Shi Muhibba ta dauke ta kamar yar uwa komai bata kyashin yi Mata,saisa at times Akan ce dadin Zama sai bare domin yanda take kula da ita ko uwar ta sai haka,bayi da bakin gode musu wlhy,

Lah ya Nameer Ka zo ne ta Fadi tana murmushi,

Shi din ma murmushin yayi sannan yace eh wlhy mommyn Fadeel ya dawainiya kuma,na gode sosai ubangiji ya Miki Albarka sanann ya biya ki da Aljannah,

Murmushi tayi domin a rayuwa tana Jin dadin adduo'in nan da Nameer ke Mata kullum,tana matukar respecting in Shi don duk friends in Habeeb zata iya ce wa babu Wanda Jinin su ya zo daya kamar Nameer in kallon babban yaya take mishi,and ba kowa ne za Ka yi mishi abu yayi appreciating har ya San kayi masa ba,akwai dadi duk kankantar abunda mutun xai yi maka Ka gode Ka kuma nuna Jin dadin Ka,shima dai gaba ya samu karfin gwiwa,

Ameen ya rabil Alameen Ka Shigo mutuniyar tayi bacci,

Eh wlhy haka nake gani, ubangiji dai ya Baku ladan jinya,ita kuma Allah ya bata lafiya,Ameen duk suka amsa,sannan suka fito daga dakin,

Nan parlor suka baje ta kawo musu abinci suka shiga ci suna hira irin nasu na abokai a nan ne yake sanar wa Habeeb Yana so in sha Allah tunda gobe Saturday babu aiki Yana ga gwara ya dauki Nadeeya ya tafi da ita Kaduna daman tunda ya zo be je ba,

Nan take kuwa ran Habeeb ya Baci Akan meyasa zai ce haka,gani yake Yana takura su ko kuma su din sun gaza bara su iya Kula da ita ba,

AA wlhy ko daya Ka fahimce ni ba daidai ba,gani nayi yanda aka Fara binciken nan toh ban san iya yanda zai tsaya ba gwara in dauke ta tayi nisa da garin nan gudun Kar in Sanya Ku a wata matsalar,

Da kyar ya samu Habeeb in ya fahimce Shi be bar gidan ba sai dare bayan yace da Muhibba ta shirya ta da wuri don Allah don asubanci yake so suyi,

Da haka ya koma gida,Saida ya kuma wanka sabida Yana yi na zafi kafin ya gabatar da sallahn Isha sannan ya dauki waya ya Kira Mama,

Idar wan ta ke nan itama tana lazumi kiran nashi ya Shigo,ajiyar zuciya me karfi ta sauke domin yau Kusan kwana uku ba suyi magana ba duk hankalin ta ya tashi addua kawai take Allah ya Sanya Yana lafiya domin ko sun Kira basa samun Shi,

Da sauri ta dauka tare da sallama,amsawa yayi sannan yace ina wuni Mama,

Baba na ba zan amsa ba Ka ga yanda Ka daga mana hankali kuwa ina Ka shiga ne haba baba na,AI ko sako Ka turo in ma busy kake in dai san kana cikin koshi lafiya,ta kare kamar za ta sa kuka,

Numfashi ya sauke sannan yace kiyi hakuri hajiya mama wlhy ana ta dan rikici ne a gurin aikin na mu,

Subhanallahi ina fatan dai ba da Kai Ake rikicin ba dai ko,

Dan dariya yayi sanna yace haba mama ni kan AI bana rikici da kowa ba da ni bane,

Toh Alhamdulilah ina fatan kana lafiya sanan kuma kana cin abinci,ni wlhy duk hankali na ba a kwance yake da garin da Baka san kowa nan ba,ta kare tana jimami,

Dan murmushi yayi sanann yace hajiya mama ke nan toh ki kwantar da hankalin ki in sha Allah gobe a Kaduna Zan kwana asubanci ma Zan yi da yardar Allah kafin 10 ina gida, breakfast in ki ma Zan ci,

Cike da murna domin ita kanta tayi missing Dan nata tace da gaske kake Babana,Bani son zolaya fa,

Shima dariyar yayi sanann yace da gaske nake mama gobe Zan zo ba ma ni kadai zan zo ba,

Kai dawa ye ta tambaya,mama labarin da tsaho ki Bari sai na iso Zan Miki bayani za ki fi gane wa,

Toh shike nan ubangiji ya kawo Ku lafiya Allah ya tsare hanya,

Ameen thuma ameen Mama tah ina angel take,

Ka ganta can ta gama fitina ta na dake ta na hurga ta gado tayi bacci,

Haba mama nawa angel take da za a Mata dukan da har sai tai bacci ya kare kamar zai yi kuka,

Gidan Ku Baba na yarinya tayi mun bar na bazan buge ta ba,Ka fita a idona da wannan kwalafucin da kake Akan yarinyar nan fa,

Baki ya turo kamar karamin yaro sanan yace shike nan kiyi hakuri sai da safe,

Dariya ta Sanya sannan tace au don nayi fada shine zaka kashe wayar taka ko,

AA mama ba don haka bane fa,Allah ya shirye Ka Baba na da haka suka shiga hira irin ta " da uwa Wanda daga gani za Ka gane akwai tsantsan shakuwa da soyayya me karfi a tsakanin su,Saida suka yi Kusan 1 kafin suka yi sallama ya ya kwanta Yana Jin kamar ya janyo gobe tayi ya ganshi a gida,saidai wani gefen zuciyar Shi na tambayan Shi me zai ce da mama in ta ganshi da Nadeeya, inda ya samu kwanciyar hankali ya San Mahaifiyar tashi akwai saukin Hali da fahimta he is sure za ta fahimce Shi,da haka ya kwanta bacci me dadi ya dauke Shi,


Ko da ya tashi sallan asuba be koma bacci ba,kayan Shi ya hada Wanda ya san zai bukata Saida ya Gama sannan ya fada wanka,bayan ya fito ne ya shiga Kitchen cikin sauri yayi frying egg da plantain sannan ya hada tea ya fito,a nutse yake cin abinci don in yace zai Bari sai ya Isa ya ci abinci zai jigata,domin daga Bauchi zuwa Kaduna ba karamin tafiya bane,

Around 6:30 ya gama hada koman Shi ya zuba a mota,Saida ya rufe ko ina na gidan sannan ya fito ya shiga motar nashi,

Saida ya biya inda yake Siyan masa ya siyo don yayi alkwarin Kai wa mama,sannan ya biya Jifatu siyayya yayi musu sosai wa mama Nadeeya da kuma angel inshi sannan ya dau hanyar gidan Habeeb,

Da isar Shi kuwa ya tarar da Muhibba ta gama shirya Nadeeya cikin dogon Riga,dauko ta yayi zai shimfida Leda tace da Shi AI ta Sanya Mata pampers Kar ya damu har su Isa bara ta yi komai ba don ba wani ruwa sosai ta bata ba,

Godia sosai yayi musu inda a karshe ya dauki kyautar 100k ya baiwa Muhibba sam taki karba Akan ita fa ya wuci haka don Allah ta kula da Nadeeya,da kyar ta karba bayan yace da ita AI ance gaida me gaida Ka ko bare amsa ba,godia tayi mishi sosai don har da kwallan ta,sabida ba karya ta Fara shakuwa da Nadeeyar duk da ba magana take ba,

Sallama suka yi da Habeeb bayan ya sanar da Shi in sha Allah bare wuce week in nan ba zai dawo gudun Kar a zarge Shi,shima ya kuma mishi godia sannan ya shige motar sa,adduar Allah ya kiyaye hanya suka yi mishi tare da daga mishi hannu har ya fice daga gidan,

Cikin kwanciyar hankali ya dauki hanya Saisa ya zabi tafiyar samako domin gujewa idon sani KO kuma road safety suke ne ko yan sanda 🤣,da haka ya dauki hanya Yana tafe Yana duba halin da yar mutane ke ciki,sai muce Doc Nameer Allah ya kiyaye hanya,


*********Sen Rilwanu

Bugun kofar dakin Shi ne ya farkar da Shi daga baccin safen da yake yi,da kyar ya samu ya tashi ya nufi kofar domin ya sha maganin bacci jiya kafin ya kwantan,

Bude kofar ya ga Falmata ce durgusawa tai tare da gaishe shi,da hannu ya amsa ta,a ladabce tace da Shi ranka ya Dade kayi bakuwa,

Bakuwa ya maimata da mamaki,eh Waye shine abunda ya tambaye ta,

Yallabai Hajiya ce,idanu ya zaro yace hajiya fa kika ce eh tace da Shi a nutse,be koma cewa komai ba ya fada daki cikin sauri ya wanke Baki tare da wanke fuska ya xura milk jallabiya tare da feshe turaruka ya dauko carbi yana dan ja a nutse ya fito da murmushi Kan fuskar Shi,

A zaune ya tarar da yar dattijiwar matar da ke tsananin kama da Shi,sanye da hijabin ta har kasa tana jan nata carbin,

A gaban ta ya zube tare da fadin sannu da zuwa Hajiya Ashe kina tafe,

Kallon Shi tayi tsaf daga Sama har kasa saidai sam yaki barin su hada idanu da ita,

Kai ta girgiza sannan tace Abul bait wai me ke damun Ka ne,

Cikin saukar da murya yace hajiya magauta sun sako ni gaba na rasa yanda zanyi,

Anya kuwa Abul bait Anya,sai kuma ta girgiza Kai,tare da gyara zama,

Mikewa yayi tare da fadin Bari na sanya a kawo Miki abinci na san Baki karya ba kika taho,

Dawo Ka zauan ba abinci ne gaba na ba,magana nake son muyi ta fahimtar juna,

Ba musu kuwa ya dawo tare da zaunawa Kusa da ita,duk iskancin Sen Yana mugun shakka da tsoron Mahaifiyar shi (Hajiya Rakiba),


Abul bait,naaam hajiya ya amsa ta,na tambaye Ka miye damuwar Ka Amman kace Dani magauta sun Saka Ka gaba,na Rasa gane wani irin abu ke bibiyar Ka Ka duba fa ace tun mutuwar Mahaifiyar Nadeeya ace har yau shekaru Kusan 25 baka kuma aure ba,

In anyi magana kace mun komai yar lokaci ne,sannan ace yarinyar nan jarabawa ta fada Mata ni Banda nasani ya and kace da ni babu abunda kake boye mun,

Ina yawan mugayen mafarkai da Kai Wanda na Rasa gane dalilin haka,Ka ji tsoron Allah Ka fada mun in har akwai abunda kake boye wa duk duniyar nan Baka da kamata ni ce uwar Ka ni ce uban Ka,don haka Ka sanar da ni miye kake boye mun,

Kan Shi ya kwantar a cinyar ta sai ya Sanya kuka,hajiya mutane sun Saka ni gaba kaina aka Fara siyasa an samu wasu mugayen da suka jefi yarinyar nan hauka tuburan tayi hajiya bata komai sai auna mun zagi,

Kallon Shi kawai Hajiya ke yi kafin tace Ka tabbatar babu abunda kayi wa yarinyar nan Baka zalunce ta ta ko ina ba,

Dagowa yayi sanann yace haba hajiya ke fa kin fi kowa sanin halina,

Yo wani sanin Hali Dan mutun da Ka Haifa ne Baka Haifi halin Shi ba,AI kana iya canzawa a KO wani lokaci amamn da mamamki ace Nadeeya ke maka irin wannan diban albarkan da na gani a video,

Wlhy hajiya sa hannun magauta ne,

Kayi mun shiru in sanya hannu ne Miya Sanya Baka kawo ta gurina ba sanin Kan Ka ne Ubana babban malami ne kafin ya mutu duk garin Azare har nan cikin garin Bauchi babu Wanda be san da Zaman Shi ba,

Kawunan Ka wani irin ayoyi da adduo'in karya sanmu ne Basu San Shi ba Amman Ka dauke ta Ka Mika ta asibiti,tunda ga rannan nasan tabbas akwai wani Abu a kasa KO ba haka bane,ta kare tana tsare Shi da idanu don son karantar Shi,

Idanu yayi saurin saukewa domin wani yarrr yake ji a duk lokacin da ta tsare Shi da idanu har rawa jikin Shi ke yi at times,

Cikin kwantar da Kai yace wlhy hajiya Bani son daga Miki hankali ne na ga ba isashen lafiya gare ki ba,and Kabiru ne ya bada shawaran a Kai ta asibitin domin likita yace kwakwalwan ta ya dan tabu dole akwai bukatan ayi na asibitin kafin a yi na gidan,Jira nake in an Gama daman sai na kawo ta gurin ki,sai kuma aka yi rashin dace an bita can asibitin an sace ta yanzu haka case in na gurin Yan sanda suna bincike akai,

A Ka sace ta salati hajiya ta Sanya tare da tafa hannuwa wanann masifa har ina,Anya Abul bait ba wani Sabon Allah kake yi ba shine ya tashi kama Ka ta wanann hanyan,

Cikin sauri yace wlhy hajiya Bana aika ta komai ina sallah ina azumi ina zakka ina sadaka ina kyauta,ina sauke farali sannan Ina kyautata muamala ta da mutane da makota na uwa uba kuma ina Miki biyayya ke dai kawai in jarabawa ta samu mutum,

Dan shiru hajiya tayi sannan tace ina fatan dai kana gujewa haramun domin cin haram kadai Kan iya wargaxa ma lamuran rayuwar Ka,


Da sauri yace Allah ya mana tsari da haram hajiya Bana cin ta Bana kusantar ta kuma Bana kaunar me taammali da haramun,

Shiru suka Dan yi Basu ce komai ba sannan can tace ko dai za Ka hakura da neman wannan takaran ne haka kawai Bani da good feelings Akan takaran nan naka Abul bait,Ka dube Ka duk Ka Rasa nutsuwa yarinyar nan ba ma mu san halin da take ciki ba duk Akan neman duniya wani irin arziki da dadi ne Allah be azurta Ka da Shi ba,

Kirjin Shi ne ya buga,a taya zai ma Fara Aje takaran nan bayan abubuwa da yawa da ya Rasa sabida Shi,AI ina bare ma taba yuwa ba,

Kayi shiru ina yi maka magana,

Zama ya gyara sanann yace hajiya Nima da zan so ajewar tunda hankalin ki be kwanta da Shi ba,Amman kuma mutane zaki duba gabada hopes in su na ga Allah na gare ni don alummah ta nake son yi,domin kawo cigaba Amman in Baki so zan hakura,

Dan tsaki tayi sanann tace ubangiji ya shige mana gaba Ka dai dage da azkar yanda kace an sako Ka gaban nan Nima Zan na taya Ka,sannan Ka ji tsoron Allah a duk yanda kake in kayi Abu kana tunanin bazan sani ba Allah zai sani kuma Yana gani domin Shi ya yayi mu duka,Allah ya gani na Baka tarbiya da ilimi daidai iyawa ta,

Haka ne hajiya ina Kan ji wlhy ayi ta taya mu da addua in sha

Please Login or Register in order to submit comment