Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dariya SEN yayi yace ohhh Afzaal fitina ko Nima nayi missing in ka yaro Na,saidai abubuwa marasa dadi sun faru bayan tafiyan ka,domin Nadeeya hauka ne tuburan ya kamata yanzu haka ma Na kira doc bashir ya tafi da ita,

Oh good Ashe abun babba ne,ai ya wuce yanda kake zato,kai to Allah bata lafiya,ni dai yaushe xan dawo don Na fara gajiya da zaman USA??

Numfashi SEN ya sauke sannan yace not now son ka cigaba da zama har sai wannan kuran ta lafa tukun Na,zan sanya manager yayi maka transfer in 5mil make sure to take care of yourself bye,be jira amsan sa ba yayi ending in call in,

Kallon Kabiru yayi da ke cin abinci yace kai ka ji mun yaro ana ba guri yana ya kwanta wai dawowa yake son yayi,

Dariya Kabiru ya sheke da shi sannan yace ka ji Dan nema to ya dawo yayi me ana tsaka da wannan halin,oho fa ni kan zan shiga ciki Na huta mayi waya kawai,in ka fita kace da Sa'eed duk Wanda ya zo nema Na ace Na sha magani Na kwanta,kai kawai Kabiru ya gyada masa don ya cika shinkafa a bakin sa,

............Kaduna State

44 barrack hospital ,

Zaune yake shi kadai a cikin office in sa,sanye yake cikin white and black dress,shiru yayi tare da kura wa guri guda ido alamun he is lost in thought,

Ko karan bude kofan da shigowa doctor Mujaheed be ji ba,sai da ya taba shi tare da cewa Helllooooo wai tunanin me kake yi ne haka har baka ji shigowa ta ba,

Dago idanun shi yai masha Allah Na furta domin mutum ne me cikan halitta da haiba kyakkyawa dashi bara a kira shi fari ba haka zalika bara ace da shi baki ba,yana da long nose ba wai can ba kai in fact dai he damn cute and handsome,(domin duk creation in ubangiji banu munana),

Kallon Abokin Na shi yayi for some seconds sannan yace wlhy Mujaheed ya tabbata mutanan nan transfer za su mun hakan ma wai within 2 weeks,Doctor NAMEER ABDALLAH ya kare cike da bacin rai,

Numfashi Mujaheed ya sauke sannan yace ikon Allah kuma ina suka aika ka,

Dan guntun tsaki ya ja sannan yace wai Bauchi fa wata Teaching hospital nan aka jefa ni........

Aradun Allah Na gaji🤪,

Don girman Allah Arin ga yi ana kankaro mutunci gurin yin sharing and commenting🙏🏻,

Ina mika godia Gare ku masoyan littafin nan da kuma ni Na gode sosai Allah saka da Alkhairi,

Sai kun ji ni gobe in Allah yayi muna cikin masu rai da lfy,

Ina yi wa kowa fatan Alkhairi🙏🏻❤️
😭😔UBANA NE KO KISHI TA💔💔

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEY BEE)

.........

My what's app group l

https://chat.whatsapp.com/JYJvskgTzZICC4ksRfiMlK

Ina maraba da duk me son shiga wannan group in saidai in har kin San ba sharhi zaki nayi ba toh don Allah kiyi zaman ki kar ki shiga,haka ma Na miji Na roke ku da sunan Allah kar Na mijin da ya yi joining group in nan domin akwai matan aure a ciki,Na mata ne xallah🙏🏻

Ga masu son a tallata musu hajojin su kuwa suna iya tuntuba ta ta wannan layin:

08100046388

...........
Page five

**********

Dan guntun tsaki ya ja sannan ya ce wai Bauchi fa wata teaching hospital nan aka je fa ni,

Murmushi Mujaheed yayi sannan yace but Bauchi is a very nice city mutumi Na domin I have been there twice or thrice haka nan,duk da ba wata girma can Gare ta kamar nan ba and nan mun fi su yawancin abubuwa,but am very sure za kayi enjoying zaman ka a can,domin sun iya
masa sosai,and ka ga kuma kai kana son masa,saidai fa mutanna Bauchi akwai Dan banzan rowa ya kare yana dariya,

Saisa ake musu kirari da yan Bauchi naman keya,ya kare yana Kara dariyan shakiyanci,

Tsaki Doc Nameer ya kuma ja sannan yace ni ina ruwana da Rowan su sai kace karamin yaro kawai daga zuwa Na gari sai Na hau roko haba dallah,

Ni fa ba fa kyan garin ko kyan mutannan garin bane a gaba na, duk abunda ke garin ni bana so Na fi son a bar Ni cikin family Na,

Hannun shi Mujaheed ya dafa sannan yace haba mana Nameer sai kace ba Na miji ba duk wani maaikaci ai ya kamata ya zama a cikin Jinin jikin shi yi masa transfer, don Allah kar ka bar Dan wannan abun ya Dame ka ka ji,

Hmmm Mujaheed bara ka gane bane wlhy duk abun da zai sanya ni nisa da Angel to wlhy Na tsani wannan abun with passion, ko kadan bana son nisa da ita,and sanin kan ka ne babu yanda za a yi Mama ta bari Na tafi da ita har Bauchi ni fa shine damuwan da nake yi,

Zama Mujaheed ya gyara sannan yace haka ne kam Mama ba bari za tayi ku tafi ba kam amman be faithful my friend in sha Allah komai zai zo maka da sauki am very sure sai ka bani labarin irin dadin da Bauchi ta maka domin garin akwai dadin zama,

Dan kallon shi Nameer yayi sannan yace ni kam dai ko yar bauchin nan kake son Kara ta biyu ne Na ga yanda kake backing up in garin nan bil hakki,

Dariya me Dan sauti Mujaheed yayi sannan yace kai mutumi na, shi din ma dariyan yayi kafin yace in tayi tsami ma ji ai,

Duk shiru suka Dan yi kowa Na dan danna wayar sa kafin can Doc Nameer ya dauko tare da cewa yauwa ni kam friend ka ga wani video kuwa dake ta trending daga jiya zuwa yau,

Hmm wlhy Na gani Nameer abun ya matukar daure mun kai wlhy ohhh duniya wlhy ina tsoron wannan rayuwan yanzu tsaban dibewan Albarka ai ubanka ko Dan giya ne bara ka fito bainan nasi kana masa irin wannan zagin karan dagin ba,balle ace mutum me tsoron Allah me dattaku irin SEN ace wai yau yar shi kwaya daya tilo ta fito cikin media ta masa zagin fitan hankali sabida bat ta kunya,daman tsiyan ka nuna wa yaro kana mugun son shi ke nan nan zaka ga yana fallin iskanci ya kare cike da Jin haushi,

Goshi Nameer ya dafe sannan yace dadi Na da kai ke nan Mujaheed yanke hukunci ba tare da kasan cikkkaken me ke faruwa ba,

Ka san me ya mata ne tayi masa hakan?a yanda aka ce akwai shakuwa da soyayya me karfi a tsakanin ta da shi meya sa for all past years in da suka yi spending together bata taba masa hakan ba sai yanzu dole akwai wani abu a kasa,

Miye a kasan iskanci ne fa irin Na yaran masu kudi wai su suna koyi da dabiar yahudawa,domin ita kanta Nadeeyan an ce bata cika zama a nan gida Nigeria ba sai da ta kammala karatun ta tsaf da aikin ma an dauka a can turan za ta yi,wlhy Nameer ba komai bane fa kawai iskanci ne fa da samun guri,Amman ace mutum kamar Audu Waziri wlhy duk duniya an sheda mutum ne me son aluma da kuma tausayin talakawa,ni in ba don yar sa bace sai nace tayi ne don ta bata masa siyasan sa,

Da ido kawai yake bin Mujaheed domin shi fa haka yake magana ce da shi har ta Allah tsine mamaki yake me ya Hana shi karantan Mass com ko wani law sai kuma ya kare da karatun malamin jinya,

Kayi shiru kana kallo na ko kai goyon bayan yarinya kake yi ne ya kare yana tsare shi da ido Wanda hakan ya baiwa Doc Nameer dariya,

Dan darawa yayi sannan yace ba ka da dama wlhy Mujaheed ni a ina Na san ta da har zan bi bayan ka,kawai dai ina magana ne daga abunda nayi tunani,yau da ace kamar daga waje ne wani ya shigo yayi masa irin wannan zagin sai muce daga magauta ne don ba a so ya ci,amman fa yar sa ce ta cikin sa,

Allah Na tuba duk da ance sanin mutum sai Allah amman ya ci ace ta san halin uban ta ciki da waje,kai ni fa sai sa Sam bana son politics kila ma hadin baki suka yi da yar ta shi tayi masa hakan domin ya samu sympathy in mutane a kuma Kara ganin kima tausayi da kuma mutuncin shi,ka zo ka tsaya kana kare shi kamar muna court room ya kare tare da mikewa,

Mujaheed in ma mikewan yayi sannan yace ai daman politics in ko hakan ne da Sen ya ban mamaki wlhy,kar wani abun da Dan Adam zai yi ya baka mamaki Mujaheed domin yanda ka ga mutum ka bar shi kawai,fatan mu dai shine Allah yasa muyi kyakkyawan karshe ya kare tare da fita daga cikin office in,da Ameen Mujaheed in ya amsa sannna ya bi bayan sa yana me yi masa wani hiran daban,

Nadeeya.......

Ba ita ta farka ba sai karfe 10 Na safiya sakamakon Aluran baccin da doctor Bashir ya shigo ya tsikara mata,

A hankali ta fara bude idanun ta Wanda sun riga da sun kumbura tsaban kukan da ta ke ci kwana 3 da suka wuce,a hankali ta ji kanta Na juyawa Wanda ta sanya hannu tare da dafe kan tana kokorin bude idanun ta Tas ta samu ta sanya wani abu a cikin cikin ta domin ba karamin yunwa take ji ba,don rabon ta da cin abinci tun shekaran jiya,

Hamdala take yi wa ubangiji a ranta da ya kubutar da ita SEN be sanya an mata komai ba domin har ga Allah ta tsorata time in da doctor Bashir suka zo daukan ta, ganin she is still alive ne ya sanya ta fara bin damin da take jiki da kallo,

Mamaki take yaushe aka kawo ta cikin dakin nan ina ne ma nan gidan waye and be take yi,ko dai ya sanya an kawo ta nan ne don ya ji dadin kashe ta,

Mamaki ne ya kamata tare da bude baki sakamakon ganin uniform sanye a jikin ta,Wanda harda no a jikin rigan domin ita ce no 354,

Hasbunallahu wa ni imal wakil,shine kalman da take Nana ta wa,in har ta canka daidai nan dai asibiti aka kawo ta ,saidai no in da ke jikin ta ne bata san Na miye ba,a hankali ta sauko daga kan gadon duk da ba wani karfi bane a jikin ta ta fara bin dakin da kallo, Sam brain in ta yaki responding balle ta samu ta fahimce inda aka kawo ta,saida idanun ta suka sauka akan chains in da ke jikin gadon,

A mugun tsorace tayi baya tare da furta kalman Na shiga uku ni Nadeeya kar dai abunda nake tunani ne,kar dai gidan mahaukata wannan mugun ya sanya aka kawo ni,shike nan Na kade shine kalman da take fadi tana kuka,

Ganin in ta zauna kuka ba inda zai kai ta domin burin ta be wuce ta ga ta tona wa SEN asiri ba,tana son duk duniya su san shi wani irin mutum ne,Amman abune me matukar wahala,

Kamar Wanda aka zabura tayi saurin mikewa domin bara ta zauna da hankalin ta a maida ta mahaukaciya ba,

Tunanin guduwa ne ya fado mata a rai, da za ta samu ta gudu daga kasar nan ma baki daya ta koma can wata kasan ta faro rayuwar ta daga farko yanda SEN bare ma San yanda take ba,

Da Sauri ta nufi bakin kofan saidai duk yanda ta so ta samu ta fice kasawa tayi,tayi kuka kamar ranta zai fita ta kuma ja wa SEN Allah ya isa ya fi 10 basket, nan kasa ta kwanta looking so very helpless tun tana kuka,bar tayi shiru tana tunanin mafitan da za ta samar wa kan ta,

..............Kaduna

Shigowan shi ke nan parlor in hajiyar sa,bakin shi dauke da sallama,da gudu gudu sauri sauri wata yar cute baby Wanda bara ta wuce 2 and the half years ba ta nufo shi tana ware hannaye,ta fadi ta mike tana fadin Papeee daga ganin yanda take masa kasan murna take da zuwan shi,

Nufan ta yayi da sauri yana dariya domin yanda take gudun tana talle yan tiny legs in ta abun dariya ne,

Daukan ta cak yayi tare da juyi da ita sannan ya rungume ta tsam a kirjin shi yana Jin kaunar yarinyar ta shi har cikin Jinin shi,

Lallausan suman kanta ya shafa sannan yace my Angel wa ya bar miki suman ki a bude??,

Mama ne ta fadi cike da gwarance,mama ce ta bar mun kan Angel ita a bude haka,kai ta daga mishi tana dariya tare da tsale a kan jikin shi,

Lalle Haanan wato ni za ki yi wa Shari don kin ga Papan ki ko,ai ko zai ta fi ya bar Ni da ke a cikin gidan nan wata yar kyakkyawan dattijiyar mata ta fadi tana fitowa daga cikin kitchen,

Fuskan ta ta boye a kirjin shi tana dariya domin yarinyar ba dai wayo ba,

Shi kan shi Nameer dariyar yake domin drama in Mama da Haanan Sam baya kare wa,domin mama maida ta take kamar wata babbar mata tayi ta tsokana ta tana kiran ta Tsohuwa,

Dan risina wa yayi tare da cewa an wuni lafiya Mama, cike da faraar ta ta amsa shi da Alhamdulillah my son ya gurin aiki kuma,

Kai ya dan Sosa sannan yace wlhy mama gurin aiki ba dadi don maganar ma da nake miki yanzu sun yi mun transfer zuwa garin Bauchi,

Kai mama ta jijiga irin Na nuna alhini sannan tace ayya Abu be yi dadi ba Sam wlhy Amman ya aka iya toh,haka xa muyi hakuri ka tafi,gashi ni ba kowa Na sani a garin Bauchi ba,Amman ba komai Ubangiji ya sanya hakan shi yafi zama Alkhairi,

Ameen thuma Ameen Mama hope dai babu wata matsalan,aa Sam babu matsala Babana Allah yayi maka Albarka ta kare ka a duk inda kake,Ameen ya Allah mama ta,ya kare yana jan yatsan kafan Angel,

Kuma yaushe ne tafiyar taka ,wlhy mama within 2 weeks suka ce,

Kai da wuri haka,toh Tsohuwa sai ki Bini a sannu don papa dai Bauchi zai tafi ya bar Ni daga ni sai ke,

Dariya ya sanya sannan yace aa mama da Angel ita zan tafi,hararan wasa tayi masa sannan tace ka ma isa,ai tun da kaki Kara auran nan to ba yanda za ka da ita,

Ace magana kullum mun yi tayi ke nan haba Baba Na yau margayiya shekarun ta biyu da rabi da rasuwa da ya ci ace ka Kara aure wlhy ko don yarinyar nan kar ta taso babu uwa a tattare da ita,

Numfashi me zafi ya furxar,domin har Ila yau in aka yi maganar mutuwar RA'ISAAH ji yake kamar jiya ta bar shi s doran duniyar nan shi kadai da little Hanaan in shi,

Nan take idanun shi suka kafa a hankali yace kiyi hakuri mama wlhy ba wai naki jin maganar ki bane ko auran ne bana son karawa, wlhy mama tunda Ra'isaa ta rasu ta tafi da duk wata soyayya ta,bata raye Amman har yanzu bugun zuciya ta tata ce bana Jin akwai wata macen da zan kalla har ta burge ni balle har Na ji shaawar auran ta ,ya kare kamar zai yi kuka,

Numfashi Mama ta sauke tana me tsananin Jin tausayin Nameer in domin ita kanta sheda ce ba karamar kauna yake wa margayiya ba,

Shike nan my son Na fahimce ka Allah ubangiji ya cigaba da yi wa Ra'isaa rahma ya sanya ta huta in namu ya zo ya sanya mu cika da imani,

Ameen thuma Ameen ya amsa tare da mikewa ya shimfida Haanan da already tayi bacci akan sofa yace Mama bari na Dan shiga Na rintsa zuwa la'asar zan tashi, toh son abincin fa,bara ka bari ka ci abinci ba ka ji dadin kwanciya,aa mama abincin nan zai n tashi ya kare tare da shigewa daki,da kallon tausayi mama ta bishi domin ta san ba wani baccin da yake ji kawai hiran margayiya da aka yi ne ya tado mishi inda yake Mai kaikayi,


............Doc Bashir

Tsaye yake da waya a kunne alamun waya yake yi hakan ma da mutum me mahimmanci,ranka ya Dade tana nan a cikin koshin lafiya duk wani abun bukata da kace duk mun sanya mata, yanzu haka ma bacci take yi,

Ban ji abunda aka ce daga can bangaran ba sai ji nayi Bashir Na cewa aa ranka ya Dade ba a riga an fara ba,

Sorry ranka ya dade,injections in ne bamu da shi a nan Amman Na aika yana kan hanya gobe ko jibi za mu fara mata in sha Allah ka kwantar da hankalin ka yanda kake so haka zai faru ,Dan dariya yayi sannan yace godia nake ranka ya Dade Allah Kara girma......

Ayi mun afuwa da typing errors pls am trying all my best ban yi edit ba kuma typing in dare ne and keyboard ina yana bani matsala wlhy,

Masoyana ina Jin dadin irin karfin gwiwan da kuke bani,Allah saka muku da Aljannah,

Sai kun jinu gobe in sha Allah,

Ina yi wa kowa fatan Alkhairi.
😭😔UBANA NE KO KISHIYA TA💔💔

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEY BEE)

.........

My what's app group link

https://chat.whatsapp.com/JYJvskgTzZICC4ksRfiMlK

Kofa a bude take kowa Na iya joining Amman,in har kin gan ba sharhi bane zai kawo ki don Allah to ki yi zaman ki ba sai kin shigo ba,and don Allah wannan group in mata ne xallah domin akwai matan aure a ciki,maza Na hada ku da Allah stay far away from this group please🙏🏻,

Gama su son a tallata musu hajojin su kofa a bude take har yanzu za su iya mun magana ta wannan layin:

08100046388

...........
Page Six

********** A week later,

Nadeeyah na hango kwance a kuryan gado ta zuba wa guri daya ido alamun tunani take yi,

Hawaye ne ke zubowa daga cikin idanun ta,domin yau kimanin sati daya ke nan da kawo ta dakin nan aka rufe ta,bata cika ganin mutane ba sai doc bashir yakan shigo ya duba lafiyar ta a ce war sa wai tana da ciwon hauka,Wanda ta Riga da ta san sam ita lafiyar ta klau,sai sister kareematu da ke shigo mata da abinci Wanda sai ma an tambaye ta me take so ta ci,

SEN ya zo gurin ta har kusan sau hudu Amman sam taki ma ta bashi daman ganin nata domin toilet ta shiga ta rufe kan ta a ciki,in akwai hallitan da ta fi tsana a doran kasa toh bayan SEN ne,

Shiru kawai tayi tana juyayin yanda rayuwar ta ta kife lokaci guda,ace wai for all people yau ita ce Nadeeya Rilwanu Audu Waziri ke kwance a kan gadon asibiti da sunan wai ta haukace,ga shi wani abun haushin ta sha attempting guduwa saidai sam kasawa take because shi kanshi dakin da take ciki akwai security pin code Na bude shi da rufe shi,Wanda har Ila yau bata san miye pin in ba,

Jin alamun bude kofa ne tare da Dan magananganun mutane ya sanya ta gane dakin ake kokarin shigowa,kila doc Kareematu ce ta kawo mata abinci,

Yau dai by all means sai ta bi bayan ta a boye ta ga numbers in da take dannawa kofar ya bude,ko tayi mata Alkawarin kudi in har ta taimaka mata ta gudu domin ta ga alama ita mata ce me kwadayi da son abun duniya,

Saidai fuskan SEN da doctor Bashir da ta gani ne ya sanya ta ji ranta ya kuma baci,da sauri tayi kokarin mikewa don shigewa toilet coz ita dai bata ga amfanin zama tayi magana da wannan mara tsoran Allahn ba,

Cike da raunanan murya ta ji ya kira sunan ta princess,bata dago ba haka zalika bata ce da shi uffan ba,

A hankali ya taka tare da nufar inda take ya kamo hannun ta tare da cewa am sorry my love jiya ban samu Na zo ba wlhy kina rai Na meeting ne ya rike ni,

Dago da kanta tayi tare da watsa masa wata irin kallon tsana,sannan tace can you pls take off your hands a jiki Na,I told you to stop touching me da wannan hands in naka ko ka manta ne,

Murmushi yayi tare da cewa Allah sarki Nadeeyan daddy wlhy mutanan nan da suka miki wannan abun ba zan taba yafe musu ba,

Wow SEN shine abunda ta katse shi da shi wai was all this drama necessary I mean all the tears all the lies all the stories da kayi cooking up, har wai da kan ka ka sanya a kawo ni gidan mahaukata Daddy are u for real,ta kare tana kallon shi,

Daga ni har kai har wannan mugun doctor in mun san I am not mad lafiya ta kalau,me yasa bara ka bar Ni nayi tafiya ta ba,okay kana Jin tsoron zan tona ma asiri ne right ,fine SEN I promise you baran ce wa kowa koami ba I will hold my mouth to my self,all I want from you is my freedom wlhy am sick tired of all this game da kake playing ta kare tana kuka,

Tsunguna wa SEN yayi shima yana hawayen tare da kallon ta,yace haba Nadeeya do u think ina enjoying kallon ki haka ne??God knows irin rashin baccin da nake samu kullum akan ki,

Nadeeya I love you so much ke ce rayuwa ta and duk abun nan da kika ga ina yi sabida ke ne wlhy,

Kallon shi tayi da sauri sannan tace sabida Ni fa kace tana nuna kanta da yatsa,murmushi tayi Wanda ake kira ya fi kuka ciwo sannan tace kana yi dai sabida siyasan ka da kuma mutanan gari,

Daddy in har kana sona kamar yanda kace why not bara ka kawo karshen wannan abun ba,I won't you let me go, Na fada ma I will surely hold my lips,

Kai ya girgiza sannan yace doc ni yana ke ga kamar ciwon nata dada karuwa yake yi kuma kace da ni tana samun sauki,

Stop changing the topic pls ka tsaya muyi magana wlhh ma gaji shine abunda Nadeeya ta fadi tana kuka,hannun ta ta hade guri biyu in a pleading way tana fadin Na roke ka pls SEN set me free I want my freedom, I promise you in Na fito zan tafi can inda bara ka sake gani Na ba don Allah ka ji,

Kai ya girgiza sannan ya kara da wlhy an cece ni sanin kan ki ne Nadeeya bara iya jure zama babu ke ba,ni dai nawa kaddaran ke nan,ba komai akwai Allah in sha Allah zai saka mun akan abunda aka miki,Na sanya ana saukan qurani da sunan ki,sannan ni da Alhaji Kabiru kullum muna tsayuwar dare da sadaka tare da rokan Allah ya baki lafiya,ga Doc bashir ma is trying his best day and night don ya ga kin samu lfy in no time,kar ki damu Nadee dee ta you will be fine in no time zai zamo kamar ba a yi ba,za mu cigaba da rayuwar mu kamar da ko Doctor SEN ya kare yana kallon Bashir,

Da sauri ya daga kai yana fadin yes haka ne,hakuri kawai za ki kara Hajiya Nadeeya domin mu samu mu kawo karshen problem in ki ki koma gida, mutane Na haukan da ya fi naki ma su warke balle naki ai me sauki ne,

Dariya ta kwashe da shi sannan tace wlhy Doc bashir kai ma baka tsoron Allah wai ni kam nawa wannan mugun ya baka ne ka dage lalle sai ka lagaba mun cutar da bani da,1 mil,5mil,10 mil 20 or 50 mil,ta kare tana tsare shi da idanu,

Kame kame ya soma yi yana uhmm ahhmmm wani irin magana ke nan nawa kuwa zai bani bayan kuma aiki Na ne kula da marasa lafiya,

Wani darinyan ta kuma sannan tace it shows akan face in ka baka da gaskiya ka karbi kudin Senator,look doc wlhy I promise u in har ka sake ni Na fita I will double the amount in da ya baka,

Jin hakan ne ya sanya SEN cewa doc ka ji ko wlhy Nadeeya ta,ta tafi shike nan ya tabbatan dai princess ita hauka tayi,ya kare yana share hawaye,baran iya cigaba da zaman dakin nan ba doc mu je ka raka ni akwai abunda nake son fada maka,

Karasowa yayi gurin Nadeeya tare da shafa kanta sannan yace my baby girl ni zan tafi sai jibi in sha

Please Login or Register in order to submit comment