Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace yayi sauri don harda masa matar shi tayi musu,(oh doc Nameer kai da Masa dai 5&6 ne Na ga alama,lol),

Waya ne a kunnan shi yana magana da Mama sai ji yayi kamar daga sama an bangade shi, Wanda saida wayan kunnan nashi ta fadi kasa,

Juyowan da zai yi don ganin waye haka ya sanya ta hardewa tayi taga taga za ta fadi da sauri ya riko waist in ta tare da manna ta a kirjin shi yana bin ta da kallon mamaki, domin daga ganin yanda gashin kanta ya rufe mata fuska ya tabbatar mishi da ita ce ya gani wannan ranar a zaune,

Jin bata kai kasa bane ya sanya ta sakin dariya cikin siririyar muryan ta tare da sanya hannu ta bude gashin kan nata in da nan take kyakkyawan fuskan ta ya bayyana,

Ya salam doc Nameer ya furta yana me zuba mata eyes ko blinking baya yi,ita din ma shi take kallo kafin can kamar Wanda aka tsikara ta fito da tongue in ta tare da lashe mishi kumatu sai kuma ta sanya dariya tare da daka tsalle,

Maganar Nurse Kareematu da ya ji a bayan su ne ya sanya shi dawowa daga Dan guntun sumar da yayi because he was totally shocked da abunda Nadeeya tayi mishi,

Go get her shine abunda Nurse Kareematu tace in da Sam Nadeeya ta ki sake Nameer daga ganin ta xaka San a tsorace take da Kareematun,domin zan iya ce wa she was so free with Nameer lokaci daya,duk da fitowa take ba,and daga ganin yanayin ta za ka san she is so depressed and scared saidai wannan childish behavior in nata da Nameer zan iya kiran shi watakil wai silan haduwar su,

Da kyar da sidin goshi aka ja Nadeeya zuwa dakin ta kuka take tana fadin ita bara ta je ba,ana yi mata injection me zafi bata so,shi dai doc Nameer Na tsaye cak har aka wuce da ita dakin ta tana mika mishi hannu idanun ta cike taf da hawaye....
[6/21, 8:37 PM] My Best Best ❤️: 😭😔UBANA NE KO KISHIYA TA💔💔

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEY BEE)

.......

My group link

https://chat.whatsapp.com/JYJvskgTzZICC4ksRfiMlK

In har kin san ba comment bane zai shigo da ke to don Allah kiyi zaman ki,haka zalika maza kar su shigo mun cikin group domin Na mata ne zallah🙏🏻,

Ga masu son tallata musu hajar su contact me via:

08100046388

...........
Page fifteen

***********

Da kyar da sidin goshi suka samu suka sanya wa Nadeeya chain a hannun ta domin duka ta shiga kai musu ta ko ta ina, inda ta kai wa sis Kareematu wata hambara saida ta fasa mata baki sai ga jini, haka sauran workers in da suka kawo ta duk saida ta laka da musu duka saida aka mata aluran bacci kafin aka samu hankali ya kwanta,

Cike da bacin rai Kareematu ta fito daga dakin,domin kashedi Bashir ya mata kan ko me Nadeeya za ta mata be yarda ta buge ta ba in ba haka ba SEN uban su zai ci daga shi har ita,

Nameer Na nan tsaye har kareeamtu ta zo ta wuce shi,kafin ya dawo hayyacin shi,waye wannan yarinyar,me yasa ta rike shi haka,sannan wani irin injection ne suke mata Wanda take kira akwai zafi bata so,duk sune tambayoyin da ke ringing a cikin brain in shi,ganin wuce war Kareematu ne ya sanya ya bi bayan ta,domin babu me amsa mi shi wannan tambayoyin sai ita,


Da sallama ya tare ta,ganin shi ne ya sanya ta juyo a wulakance tare da kallon shi tana wani harare harare,

Sannu sister shine abunda ya fadi mata ko a jikin shi da irin kallon wulakancin da take bin shi da shi,

A yangance kamar wata yarinya karama tace hmmmm Na miji ke nan,in ce ni da kai Na,na biyo ka har office in ka amman kayi mun diban Albarka yanzu miye kake so daga guri na,ta kare tana hararan shi,

Dan karamin saki ya ja a ranshi yake fadi ji wannan kamar ce mata aka yi wani abun nake da bukata daga gurin ta,

Ka yi shiru ko baka da abun fadi nayi wuce wa ta,ta kare tana adduar Allah sa inviting in ta dakin shi ko in ce gidan sa zai yi,

Tambaya daman zan miki game da patient in dazu,wani irin tukukin bakin ciki ne ya tokare ta a kirji,wato shi ta Nadeeya ma yake ba ita ba,to wai ita me ta rasa ne da bare lura da ita ba,kyau ne ko diri bata da shi,in yayi zafi ne fa yace ta Dan fi shi a shekaru and miye a ciki ai age is just a number,ga yanda Bashir ke rawan kafa akan ta tana masa yar hali amman shi a karan banza za ta bashi jikin ta yana mata bura uba,

Tsaki ta ja sannan tace da shi ina ruwan ka da ita,ko ina ruwan ka da injection in da ake mata,patient in ka ce for your on information stay away from Nadeeya domin Doc Bashir ke handling case in ta,beside in kana da bukatar tayin da nayi maka har yanzu kofa a bude take za ka iya nema ta,Allah ya mun tsari shine abunda ya ce tare da barin gurin,

Kai tsaye motar shi ya nufa,gida direct ya wuce,takalman shi kawai ya iya cire wa tare da fadawa kan gado,

Goshin shi ya dafe tare da lumshe idanun shi,fuskan ta ke masa gizo yana kallon dariyar da take mishi,ya salam daman ita ce Nadeeya RILWANU Audu Waziri in,but ta ma fi kyau a fili Ashe akan kallon da ya mata a video in ta da ke treading ,

Shafo kumatun shi da ta lasa yayi kawai sai ya saki murmushi,lalle hauka bata yi ba,in ba hauka ba ai ko kudi za a bai wa Nadeeya ta yi mishi abunda ta yi masa he is very sure bara ta iya ba,zai iya ce wa this is the first time da wata mace ta taba shi bayan rasuwar Noor in shi,haka kawai ya tsinci kan shi cikin tunanin wani irin Alura ce haka suke mata da take cewa bata so,karan shigowar kira ne ya katse shi daga tunanin da yake yi,

Daukan wayan yayi tare da Mike wa don ganin Habeeb ne,nan ko ya hau shi da mitan wai ya shanya shi since an gama abinci,hakuri ya bashi tare da ce da shi gashi nan akan hanyan shi yanzu zai iso,

Be dauki tsahon lokaci ba ya isa gidan Habeeb kasan cewar basu da wata nisa,

Gaisuwa suka yi da matar shi Muhibbah sannan ta shige ciki don basu guri,

Suna cin abinci ne Doc Nameer ke ba wa Doc Habeeb labarin abunda ya faru saidai be sanar da shi kan Nadeeyar ta lashe me kumatu ba,

Saida ya kurbi ruwa sannan yace wlhy nayi mamakin da ta fito ma,domin ni tun da aka kawo ta ban taba sanya ta a idona ba,boye ta Bashir yake yi kamar wata Amarya,

Wlhy nima abunda Na gani ke nan,and ni wlhh Na kasa nutsuwa sam wai miye ma silan haukan nata ne,

Wa ni wlhy Nameer ban sani ba domin ko case file in ta ban taba gani ba,hasali ma da aka kawo ta Bashir cewa yayi shi zai yi handling case in kowa yayi staying away from her,saisa ma ko fitowa shan fresh air ba barin ta yake tana yi ba,beside kai miye Na daga hankalin ka abeg mu ci abinci kar yayi sanyi,

Daga haka Nameer be kuma cewa komai ba,Amman deep down ya dauki niyan in sha Allah ya je asibiti gobe zai tuntubi Bashir da maganar,in da zai yarda ma da ya bar mishi case in nata,haka suka gama cin abinci sai yaba girkin matan yake ,a gidan suka wuni har dare suna hira kafin yace zai koma gidan shi,dubu ashirin ya bai wa Muhibba kyauta wai a siya wa baby Fadeel pampers,godia tayi mishi sannan Habeeb ya rako shi har mota ya koma gida,

Hira suka sha sosai da Mama,ya so ta bai wa Angel ta ce da shi tayi bacci saidai Amrah, mamaki yayi wai har yanzu ba ta tafi ba,mama za ta bata ya ce aa ta bari zai kira ta da kan shi, da haka ya kwanta bacci abun shi,

Washe gari sassafe a asibiti yayi mishi,direct in da ake aje files ya nufa domin shi fa ya kasa yarda Nadeeya hauka tayi, don maganar gaskia yanda ya gan ta babu Wanda zai ce mahaukaciya ce,zai fi ma yarda da maganar jefan da aka ce anyi mata,ya sanya yake son ganin case file in ta domin ya San matakin haukan nata,

Saidai kaf ya gama bincike cikin gurin Amman babu case file in Nadeeya,mamaki ne ya kama shi domin a iya sanin shi ba a karban patient ba tare da an rubuta case report in shi ba, ganin dai babu Na tan ya sanya shi fitowa tare da nufan office in doc bashir,

Gaishe shi yayi,ya amsa shi a dakile sannan yace da shi lafiya,uhmm daman Na zo ne game da case in number 354,

Da sauri Bashir ya mike tare da fadin and what about her,aa actually Nothing kawai dai if you don't mind ina son ganin case file in ta ne,because the why she is isolated haka Na san ita kanta she will be depressed,

Rai Bashir ya bata sannan yace ina kace if I will not mind toh I will mind in fact I want to advise you to stay away from her domin ni ke handling in case In ta,and about her isolation mahiafin ta ne ya bukaci hakan so I think we are done babu ruwan ka da ita carry on with your work and stay away daga abunda be shafe ka ba,

Ran Nameer ya sosu sosai da abunda Bashir ya fada mishi and right through his eyes ya gano akwai abunda yake boye wa,domin Habeb ya sanar da shi harda pin code aka sanya a kofar shiga inda Nadeeyan take,in har babu abunda yake boye wa miya sa ba a barin ta tana fito wa kamar sauran majinyatan,

Saidai ya hadiye bacin ran tare da yin murmushi yace well tunda kace haka daman I was just been concerned ne,and at least hospital daya muke aiki so duty Na ne nayi making sure duk wasu patients Na lafiya, tunda ka ce I should stay away ba damuwa zan yi yanda kake so,Amman kafin nan I want to know wani irin injection kuke mata ne,ko in ce wani irin treatment kuke mata Na ganin recovery in ta don tayi complaining ana yi mata alura me zafi,

Tashi Bashir yayi yace yo ga iskanci ganin ido Na,kila Dan sanda ne kai ko kuma lawyer me kariya right halan a court room muke,sabida tsaban ka raina ni,za ka zo har office ina kana mun irin wannan tambayoyin rai nin wayon,

Murmushi Nameer yayi sannan yace ko daya kawai dai ina carrying out duty Na ne,rai bace doc bashir yace carrying out duty ko kuma munafurci, daman ni can Na ga take taken ka munafuki ne kai,toh wlhy ba dai wa ni za ka yi wa munafurci ba yo har sai ka kama maganar mahaukaciya ,

I don't see any reason da zan tsaya explaining kai Na a gurin ka tunda ba uban ta bane kai,one thing da nake so da kai shine ka bar mun office ina right away kafin ka gama bata mun rai,

Kai kawai Nameer ya girgiza domin in ya canka daidai doc bashir yana kan Jin haushin shi ne akan abunda ya faru kwanaki,

I never thought magana ta za ta bata maka rai I was just being concerned ne but since ran ka ya baci am sorry and as u said babu ruwana so daga yanzu I am stepping back daga abunda be shafe ni ba,daga haka ya fice daga office in ran shi a bace,

Da de yafi maka bakin munafuki masu hana ruwa gudu tunda kaine ubana shine za ta zo kai kafi kowa son sauke duty,to Allah ya tsine uban me duty din ma,doc bashir ke ta sababi ko in ce kokarin kare kan shi,shi dai Nameer be kula shi ba office in shi kai tsaye ya wuce ran shi nayi masa zafi domin karara ya ga rashin gaskia a idanun Bashir Amman yayi masa irin wannan diban Albarkan,

Saida ya sha ruwan sanyi sannan ya dan ji sassaucin zafin da zuciyar ta shi ke mishi, zama yayi tare da kura wa kofa idanu haka kawai ka bi ka takura kan ka akan Nadeeya ina ruwan ka da ita the best thing is to stay away from her shine abunda zuciyar shi ke fada mishi,

Saidai wata zuciyar Na sanar masa kamar yarinya tana cikin wani hali hali Na neman taimako and he will forever hold himself responsible yana da hali be taimaka mata ba,

To a taya zai ma taimake ta shi da be ma San takamammiyar abunda ke damun ta ba,ya dauka zai ga case file in ta ne,but daga abunda Bashir ya fada mishi ya gano tabbas akwai abunda suke boyewa shi da Kareematu to miye ne wannan abun,shine abunda yayi ta matsawa ranshi ya sani.....



Wlhy Na so ya fi haka saidai ina fama da ciwon hakori, Wanda yayi mun causing in ciwon kai,a sanya ni a addu'a don Allah,sannan ayi mun afuwa don nasan bara a rasa typing error ba wlhy da kyar Na samu nayi page in nan,

Ina wa kowa fatan Alkhairi.
[6/21, 8:37 PM] My Best Best ❤️: 😭😔UBANA NE KO KISHIYA TA💔💔

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEYBEE)

......

My group link

https://chat.whatsapp.com/JYJvskgTzZICC4ksRfiMlK

In har kin san ba karanta book ina da comment bane zai kawo ki to pls kar ki shigo,don ko kin shiga zan yi waje da ke,haka zalika maza should stay far away from my group please🙏🏻,

Ga masu son a tallata musu hajojin su kuwa contact me via:

08100046388

...........
Page seventeen

************

Tun daga wannan ranar doc Nameer ya maida isolated room gurin hiran daran shi, domin a kwana ukun nan baya missing kullum sai ya je gurin Nadeeya ,

Haka zai bari sai kowa ya tafi sannan ya bi dare ya dawo kamar wani barawo, and baya taba zuwa mata hannu haka ice cream dai wajibi ne sai ya kawo mata, sai ya hada mata da wani kayan dadin,

Tun tana duka da masa ihu in ya zo har ta gane shi ,tana ganin shi sai ta hau murmushi tana mika mishi hannu ta san ya kawo mata kayan dadi,a haka zai lallace a gurin ta tayi ta masa shirme yana biye ta har sai ya ga bacci ya dauke ta tukuna,ya Na son ya ga an gyara mata gashin ta an yanke mata nails in ta saida baya son yayi mata da kanshi don ba muharramar sa bace be son yana taba ta any how and be San ko tana da aure ko Alkwarin wani akan ta ba tunda ba ganin case file in ta yayi ba,saisa baya son tana shige masa jiki,

A matukar rude Kareematu ta shigo office in Bashir inda ta same shi ya tasa wata karamar nurse sai matse ta yake,

Tsaki ta ja kamar halcen ta zai tsinke sannan tace kai dai wlhy anyi Dan iska wlhy ka ji kunya wani irin maita ne wannan mutun ace jaraba ta fi karfin shi,

Da sauri yarinya ta sauka akan table in office in tare da Saurin ficewa shi ko tashi yayi tare da gyara zaman wandon shi sannan yace Malama uban me ya kawo ki office ina ba tare da neman excuse ba,

Yo kace haka ai Dan iska tunda Na kama ka da mace wlhy ka ji kunya in banda iskanci da kana tambaya ta me ya kawo ni office in ka ne,sabida yanzu ka ga karamar yarinya shine duk ka wani bi ka rude ta kare tana Galla masa mugun harara,

Look Kareematu daka ta mun and ya zamo karo Na karshe da zaki zage ni,jiki ne Kin ce bara ki sake bani naki ba,toh ai ba ke kadai bace me shi Na ga duk matan duniya da shi aka haife su,don haka ki jiga naki ki shanye sannna ki cire ido akan abunda zan yi domin ba ruwan ki,

Ba shakka Bashir ai ka fada mun komai an sha magoro an shanye dadin an yarda ba,toh wlhh baka isa ba,

Be ce da ita komai ba ya juya tare da kokarin barin office in Sai kuma ya juyo in kin gama surutan da iska kina iya fitowa ki rufe mun kofa,domin Na ga sabon likitan nan an sha wanka yau kya iya zuwa ya rage miki zafi don Na ga kamar a matse kike,

Bura uba Bashir ni kake wa bura uba duk Dan Na kama ka da mace,ka mun laifi sannan ka fi ni baki,Amana ta fa ka ci bura uba shine kake watsa mun magana son ranka,ta kare tana girgiza, shi dai be ce da ita komai ba,yana kokarin fita

Ai ka fita Amman ka fin ka bi shegiyar yarinyar ta ka ina so ka biya dakin Nadeeya ka ga halin da take ciki,domin am very sure in har ka ganta sha'awar kan ta sai ta dauke maka domin ka san waye uban ta sarai wlhy ba yarda zai yi ba,

Da mugun hanzari ya nufo ta yana fadin Na shiga uku Kareematu me kika yi wa Nadeeyan,hannun shi ta doke sannan tace ka ji mun Dan iska me kuwa zan mata ni ma abunda nake son in tambaye ka ke nan,domin ai kai ka ganta Na karshe jiya har ka jona mata shocking, halin da ake ciki yanzu dai,ai be jira karasa Jin ta ba ya nufi dakin Nadeeya a 360 zuciyar shi Na tsanan ta bugawa,yana adduar Allah sa ba wani abun ya same ta ba,to ko dai mutuwa tayi, Na shiga uku shine abunda ya fadi a fili tare da shiga cikin dakin,

A kwance ya same ta idanun ta a bude sai hawaye ke fita,zuwa yayi har gaban ta tare da tsunguna wa yace Nadeeya me ke damun ki,Jin shiru ya sanya shi cewa lfy don't you want to talk,

Nan ma shiru,hankalin shi ba karamin kadawa yayi ba ganin ko motsi bata yi,ga magana ma bata yi,ganin haka ne ya sanya ya dauko alura sanin ko ma iskanci take yi in ta ga aluran tana tsorata tayi ta buge buge Amman har ya tsikara mata ko tari bata yi ba,

Na shiga uku shine abun da ya fadi a bayyane ganin ko hannun ta bata iya daga wa,nan take cikin shi ya murde sai ya ji wani irin zawo Na kokarin zubo mishi, da sauri ya fada toilet in ta ganin zai iya yi a jikin shi, yana zawo yana hawayen tausayin kanshi domin ya San wlhy SEN ya ji labarin nan sai ya kashe shi, a haka ga fito jiki ba kwari ya bar dakin,

Kai tsaye office in shi ya koma tare da kiran Kareematu, da tagumi a fuskan shi ta same shi,dariya ta so yi ganin lokaci daya inda ya ficicike,

Hope ka ganta ko Bashir ka ga abunda nake ta fada maka,Na shiga uku Kareematu shine abunda yace kamar zai yi kuka,wai don Allah me kika mata ne,

Bura uba na rantse Bashir zan ci uban ka in ka kuma ce wa Na yi wa yarinyar nan wani abu,ni sau nawa ma Na taba mata Alura kai ke da in charge in komai nata,don haka am sure kai ne kayi mata wani abun,ka ga tun wuri baran kira uban ta in sanar masa kafin ka kashe musu yarinya a rufe mu da asibitin mu,Ashe bayan san kudi har kisa za ka iya yi,

Zufa ne ya wanke masa fuska cikin muryan tausayi yace Na rantse da Allah Kareematu ban yi wa yarinyar nan komai ba,ni miye hadi Na ko in ce miye riba ta in Na kashe ta ko Na nakasa ta,wlhy babu ruwana da ita,ni ban mata komai ba,don Allah kar ki kira SEN wlhy mutumin nan ba ganewa zai yi ba ki tsaya mu nemi mafita,

Mu nema ko ka nema ni miye nawa,and da kake cewa kar mu sanar wa uban ta,to uban wa kake so mu sanar wa,ai dole kuwa ya ji sabida ya san me zai yi,don hka ni yanzun nan zan Kira shi ba sai anjima ba,

Na shiga uku kareema in kina wa Allah ki rufa mun asiri sai kace ba masoyiya ta abar kauna ta ba,Kareematu Bashir in ki ne fa,

Tsaki ta ja sannan tace kamar ba wa ni ka ga ma yi wa diban Albarka ba sannan yace ka zo kana wani Kareematun ka ce,ai ka je can gidan yari Na San SEN zai sa a kai ka,

Cikin shine ya kuma murdewa yace haba tawan kar ki mun haka,zan tura miki dubu dari da hamsi don Allah kiyi shiru kar ki kira shi Na roke ki,ya kare yana hade hannayen shi,

Harara ta watsa mishi sannan tace dubu dari uku za ka tura mun kafin nayi shiru harda kudin Mari Na don ba banza ka mara ba,

Mamaki yake wai Kareematu ke masa barazana haka ikon Allah, bayi da choice haka a take ya mata transfer in dubu dari ukun,

Dariya tayi ta girgiza kai sannan tace Allah ya shirya ka Bashiru Na bari Na je, Allah kawo maka da sauki,

Da ido ya bita yana me jin haushin ta saidai bayi da choice da ya wuce ya bi ta a sannu domin ya san kwayancin kareema Sam bata da mutunci bata kuma da tsoro,


Kareematu ko tana fita wayan ta ta dauko tare da danna no in SEN, haka kawai ai wlhy Bashir sai Na tona ma asiri, ko ba ni ka mara ba,

Har ya gama ringing ba a dauka ba saida tayi kira sau uku sannan aka dauka,

Gaishe shi tayi cike da girmamawa sannan tace ita daya daga cikin nurses masu kula da diyar shi Nadeeya,yau tun safe take kuka take kiran sunan ka da alamun son ganin ka take yi,ta kare murya cike da biyayya,

Okay I will be on my way shine abunda SEN yace tare da kashe wayan, dan tsallan murna Kareematu tayi kafin ta maida wayan cikin aljuhu tana Jin ranta fesss ko banza ta hadawa Bashir,


...............SEN

Cike da mamaki yake bin wayan da kallo, Kabiru ne yace ya ne Aboki Na lafiya,

Hmmm kabiru bari kawai wlhy kira ne daga asibitin su Nadeeya wai tun safe take ihun kiran suna Na wai tana son gani na,

Ganin ka kuma, wlhy nima abun ya dauran kai Na dau by now bakin ta ya rufu kirif,Amman sai Na ji wani abun daban, kai kan ka fa kasan aikin odugwu kamar yankan wuka ne tunda har ka bada abunda ake so kuma kai kan ka kace mun an karbi sacrifice in ka Odugwu be taba karya alkwari ba,tunda har yace zai yi to wlhy zai yin ne ba fashi ,Amman tashi mu je asibitin Na karasa maganar a hanya,

Nan suka nufi mota sai hospital, kai tsaye office in Bashir suka fada wanda suka tarar ya kifa kanshi a jikin table,

Doc bashir Alh Kabiru ya kira sunan shi, a razane ya dago ganin SEN a tsaye a Kansa shida Kabiru ya sanya ya ji hanjin cikin shi ya kada,saidai yayi kokarin dannewa tare da mikewa, cikin karfin hali yace SEN sannu da zuwa lafiya Na gan ka ga guri ka zauna,

Murmushi SEN yayi sannan yace aa ba sai Na zauna ba Na zo ganin princess ne,

Da sauri yace yallabai an ce ma wani abu Na samun ta ne,babu fa abunda ya faru da ita tana nan cikin koshin lafiya,

Da ido SEN ya kalle shi sannan yace Bashir ni ka ji Na ce akwai abunda ke damun yarinya ta,ko kuma laifi ne in uba ya zo ganin yar sa,

Kai kake masa bayani ma SEN daman ka fada mun yawa magana Bashir ke da shi ,dallah tashi ka kai mu,muna da abun yi,

Jiki babu kwari ya mike tare da yin gaba suna bin bayan shi,SEN ke rada wa Kabiru ya yaga Bashir kamar yana cikin damuwa,yoo ni ina nasan wa Dan iska mu dai je mu gan ta first mu san halin da muke ciki,

Da sallama Bashir ta shiga dakin zuciyar shi Na bugawa uku uku,ji yake kamar ya rufe su a dakin ya ruga

Please Login or Register in order to submit comment