Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»Ώ*_Bismillahir rahmanir rahim_*

πŸƒπŸ½β€β™€οΈ *_GUDUN ƘADDARA_*πŸƒπŸ½β€β™€οΈ

*H U G U M A*

PAGE 01


*_Da sunan Allah me rahama me jin qai,dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangijin talikai,tsira da aminci su tabbata ga shugaban halitta annabi muhammadu S A W_

_wannan karon labarin namu zai sauka ne a qasar nijer,duk inda akaga kuskure ko gyara sai ayi haquri,domin ni banigerian ceπŸ˜‚_


*_N I J E R maraΙ—i_*



Tun daga taku me nisan tazara tsakaninka da ainihin layin,amma kuma kana iya jin tashin sautin gangar kidan data karade kusan kowacce shiyya ta unguwar.

Lokacin da ka cimma nasarar isowa layin kuwa,taron dandazon samari ne da 'yammata 'yan bana bakwai,wadanda rayuwa da kuma duniya ke musu dadi suke cashewa,wasu cikin ainihin tsakiyar filin da aka bari domin bawa masu sha'awar taka rawar da kyau,wasu kuma daga bayan fage suke takawa suna kuma rausayawa. Kowannensu cikin shigar dake nuna zallar wayewa da kuma sukunin rayuwa yake. Kusan fiye da rabinsu kyawawan BUZAYE ne,wadanda aka fi sani da ABZINAWA,jefi jefi kuma kana iya hangen masu surkin launin fata,wanda wasunsu suka kasance barebarin nijer zabarmawa da sauran yarukan da qasar nijer din ta hada.

A hankali kyakkyawar motar fara qal qirar Yaris ke gangarowa. A kallon farko idan ka yiwa motar,yanayin yadda take gangarowa kadai zai iya sanyawa kayi zaton man fetur din dake taimakawa wajen motsawarta ne yake Shirin qarewa. Saidai kuma sam ba hakan bane.

Kyakkyawan farin matashin ba'abzinen dake zaune cikin motar ne ua zabi ya tuqa motar a haka,farin buzun saurayin da tashin farko kuma kai tsaye zaka kirashi da BALARABE zalla babu mix. Fuskarsa a dinke take tsaf,yana kuma wani irin tuqi kamar wanda jinin sarauta ke zagayawa a gangar jikinsa zuwa ruhinsa. Duka duka shekarun haihuwarsa ba zasu wuce ashirin da hudu zuwa da biyar ba. Amma wani irin lafiyayyen kwarjini dake shimfide akan fuskarsa zai sanya ka dauka wani babban mutum ne dake da wani muqami na mulki ko sarauta.

Tunda ya jiyo sautin kidan daga nesa ranshi ya soma baci,idan akwai abinda ya tsana cikin dabi'ar qasarsu yake da ikon da zai iya sauyawa to wannan tana daya daga ciki. Yaja tsaki har baisan adadinsa ba. Wannan hanyar itace hanya mafi sauqi a gareshi da zai isa unguwarsu,to amma yanayin yadda suka toshe layin yasan zaiyi wahala ya samu ya wuce cikin sauqi ko dadin rai.

Wani siririn tsakin ya sake ja,yadan cije jajayen lips dinsa na qasa yana cusa yatsunsa cikin lallausa kuma cikakkiyar sumarsa ta asalin buzaye,ya qara hannu daya kan guda dayan da yake tuqin akai,ya soma gangarawa da motar gefe don ya samu gurin parking.

Ya gwammace yabar motar a nan guraren,idan yaje ya karbo aiken daga wajen babbo din,sai ya dawo ya dauki motar ya wuce.

Kashe motar yayi,sannan ya zare key din,ya miqa hannunsa ya dauki wata baqar leda sannan ya buda motar ya zura qafafunsa dake sanye cikin boots din da wandon kakin sojin dake jikinsa shi kadai ya isa ya gaya maka waye shi?.

Tun tsaiwar motar taja hankalin mutane da yawa dake wajen,baisan me ya sanya ba,motar ba mallakinsa bace,amma a duk lokacin da ya shiga motar sai take qara masa kwarjini me yawa,abu daya da baiso yadda take sanyawa idanu ke yawa a kansa,wannan ya sanya ba kasafai ma ya fiya hawa din ba,saidai idan aiken gaggawa ne bobbo ko tati sukayi masa,kamar dai wannan aiken.

Da kyau ya hade fuskarsa ba yana ci gaba da ratsa taron,wanda kusan maza sunfi yawa a ciki,zuciyarsa na baci a duk sanda yaga wata mace a cikinsu. Wannan wacce irin lalacewa ce?,qarfi da yaji suna daukan kansu kamar suna france?,baisan wacce irin dabi'ar banza ce wannan da har yau suka kasa dainata ba.

Sake kame jikinsa yayi da kyau lokacin da yake niyyar ratsawa ta sararin da aka bawa masu sha'awar raqashewa da kyau. Duk yadda yaso ya dauke idanuwansa daga kan yarinyar dake tsaye tsakiyar filin tana taka rawa cikin wani irin salo na qwarewa da kuma gwaninta,karya jiki tako ina,kama daga qugunta har zuwa qirjinta da ko irga dangi bata farayi ba,amma tabbas tana kan hanya. Qafafunta da take kadawa tayi gaba ta dawo tayi baya kamar wadda ake matsawa remote control.

Wata mummunar faduwa gabansa yayi,tun daga cikin qwaqwalwarsa zuwa kunnuwansa yaji wani irin sauti kamar an qwala masa farantin silver

"SULTANA!" ya kirayi sunanta cikin wani irin zallar fushi da ya cukuda da tsananin mamaki.

Ko kadan bata fahimci da tsaiwarsa a wajen bama bare ta jiyo kiran da yayi matan. A hankali daya cikin 'yammatan dake tsaye daga gefe,wanda tun ratsowarsa gurin yayi matuqar tafiya da hankalinsu ta matsa daura da ita kadan tana tabota. Sai data daddaki bayanta kusan sau uku sannan ta waiwayo,saidai maimakon idanunta su sauka akan wadda ke tabata din,basu zame ko ina ba sai cikin idanunsa.

Iyakar razana da firgita ta jita har tsakiyar hantarta,to amma ita din nuna tsoro ko razani saman fuskarta ba al'adarta bace,wannan ya sanya ta juya abinta,saidai kuma ta fara lissafin ta yadda zata zame tabar wajen tun kafin ya yarfata.

Ta karanto tunaninsa kuwa a dai dai,sanda yake taku cikin tsananin zafi don ya cimmata tayi amfani da wannan damar ta kurda ta cikin mutane ta fice. Sama ko qasa sultana tayi masa batan dabo. Cikin zafi yaja da baya ya kutsa ta gefen mutanen cikin sassarfa yana fita daga taron,burinsa shine kawai ya cimmata. WAI YAUSHE TA KOMA HAKA?,YA AKAYI TA SAUYA GABA DAYA?,DABI'UNTA SUKE KOMAWA MASU BAN TSORO?. Wannan tambayar itace ta dinga masa rakiya tana kuma ingizashi da sassarfa,har zuwa lokacin da ya dangane da katafaren gate din gidan nasu.

Cikin wani irin zafi ya tura qaramar qofar dake maqale da gate din gidan,a take ta bude ta kuma hadu da bango ta bada sautin BUM!. Farar buzuwar dake tsaye cikin parking space na gidan ta waiwayo wadda shekarunta ba zasu haura arba'in da hudu zuwa arba'in da biyar ba.

Idanu ta kafeshi dashi sosai sanda yake takowa cikin gidan,ba ita kadai ba,hatta baaba leko me gadin qofar gidan shi da hamidan dake da alhakin gyara da baiwa tsirran da suka qawata harabar gidan ruwa suma binsa sukayi da kallo. Dukkaninsu ya dauki hankulansu,saboda sanin da sukayi masa. Mutum ne da fushinsa bai fiya zuwa da sauqi ba,hakanan yana da wata irin zuciya wadda a duk sanda ta motsa sai kowa cikik gidan yaji a jikinsa. Duk da cewa ba kasafai yake irin wannan fushin ba,amma abu ne da kusan kowa na cikin gidan baya da burin gani a tattare da shi.

Har ta bude baki zatayi magana sai ta fasa,taja wani dogon tsaki tana dauke kanta daga gareshi. Ko ba'a gaya mata ba tasan shi da waye,yanzun nan ta wuce ta gabanta da wani mugun gudun data tabbatar ba lafiya ba.

"A kirawoshi ne hajiya?" Driver hamidou ya fada yana karya murya,saboda ya sani,ita daya ce tal a gidan zatayi furuci qwaya daya da zai dakatar dashi,duk kuwa irin girman fushin da ua debo. Yanayin fushin da ya shigo dashi din kuma ya bayyana muraran ba me sauqi bane,yasan kuma sahun wace ya biyo,ba zaiso kuma a taba lafiyarta ba,don akwai jituwa me yawa a tsakaninsu.

Harara ta watsa masa da fararen idanunta kamar zata cinyeshi danye

"Ban sakaka ba sarkin kankanba"

"Allah ya huci zuciyarki" ya fada yana bude mata motar. Fararen qafafunta ta zura ta shige abinta,cikin ranta tana addu'ar

"Allah yasa ya kakkaryata kowa ya huta" ta fada tana sake jan tsakin me matuqar zurfi da qarfi.

"Maina....." Muryar dattijuwar ya ratsa kunnensa sanda yake shiga qawataccen falo din da zafi zafinsa. Waiwayowa yayi yana riqe da labulen. Kallo daya tayi masa ta fahimci akwai wani irin fushi da damuwa narke cikin idanu da kuma fuskarsa

"Ina sultana?" Ya tambayi dattijuwar

"Tana dakinta a kwance bata jin dadi,ko islamiyya bata samu zuwa b......" Bai jira ta qarasa fadi masa dogon bayanin data debo ba ya wuce da sassarfa zuwa corridor din da zai sadashi da dakunan nasu.

Sosai ta sake laqewa a blanket tana jan tsaki qasa qasa,duk maganganunsu cikin kunnuwanta ne,ita sam wannan ba mainanta bane,tafiyarsa da dawowarsa a can aka canza mata shi. Tabbas tasan yaa maina da zafi akan kowa amma banda ita,ita din shalelensa ce,wadda baya barinta tayi kuka,babu wanda kuma ya isa ya tabata,koda kuwa rana ce bare ruwan sama,koda quda inda yana da iko bashi bari ya sauka a jikinta bare kuma sauro da ta manta da wanzuwar rayuwarsa cikin duniya.

Tana dire wannan tunanin taji an buda qofar da qarfi,qarar sautin qofar ya saukar mata har tsakiyar 'ya'yan hanjinta,ta runtse ido ta kuma damqe bargon da take ciki,tsoro yana mamayarta,amma tattaurar zuciyarta na bata qwarin gwiwa.

"Ke!" Ya kirata cikin kaushi da sautin sunan da bai taba kiranta da shi ba.

Duk a tsorace take amma hakan bai hanata murguda baki cikin duhun blanket din ba,tare da ayyanawa zuciyarta ko zai shekara yana kiranta da ke ba zata taba amsa masa ba. Ta fuskanci ya sauya halayya da dabi'a gaba daya,ita kam ba zata yarda yayi mata yadda ya saba yiwa su lamira ba.

"Sultana!" Ya sake kiranta karo na biyu,fushinsa da bacin ransa suna ninkuwa,saboda yayi imanin tana jinsa.

Dakakkiyar sautin muryarsa data fita tamkar yana sansanin atisaye ya sanyata bankada blanket din ta fiddo kanta ba tare data shirya ba.

Cak ya tsaida dubansa akan fuskarta,kamannin nafeesa suna kai kawo saman fuskarta. Wani abu yaji ya ratsa zuciyarsa fushi da kuma tsananin takaicin abinda ya ganta tana yi ya sake tasirantuwa cikin ransa

"Uban waye ya kaiki rawa cikin tsakiyar maza?" Duk da tasan da wannan tambayar zata biyo baya,amma hakan bai hana gabanta sake tsananta faduwa ba,saboda ta sani,sun sha gwagwarmaya da bibi akan wannan

"Ni?,rawa kuma?,a kwance ka sameni fa yaa maina,ni ba inda na fita" ta furta maganar tana nuna kanta da kanta da yatsanta.

Mamaki hade da zallar bacin rai suka saukar masa,shi da sam baya daukan wargi ko qanqani,yau sai gashi yarinyar da ya baiwa shekara kusan goma sha biyar na neman raina masa wayo,yarinyar da yayi yaqinin inda rabonta a jikinsa yake yanzu haka ita din diyarsa ce. Ya tabbatar kaf fadin gidan ba wanda ya isa yayi masa rainin wayo me kama da wannan,hakan yana nufin sassauci da kulawar da yake nuna mata sun fara gaya mata cewa zata iyayin komai ba komai bane?!.

Bata ankara ba sai ji tayi ya fusgo qafafunta,sai gata tana Shirin direwa daga saman gadon zuwa qasa,abinda yayi matuqar razana ta ta saki wata razananniyar qara. Qarar data sanya bibi sakin matajin da take taje doguwar sumarta da har yanzu ke da tsananin tsaho,duk da tarin shekaru ba abinda ya canza daga gareta sai furfurar data jirkita ainihin baqinta. Kai tsaye dakin ta banka gabanta yana wani irin faduwa. Tun sanda ya shiga dakin taji zuciyarta bata kwanta Mata da hakan ba,to amma mu'amalarsa da sultana din ya sanya taji ta dan nutsu ta wani sashen kuma.

Dab da bakin gadon yayi mata burki,ya qara taku biyu zuwa gabanta hadi da jawo stool ya zauna yana dubanta da rinannun idanunsa

"Bariki kikeso ki fara?" Ya jefa mata tambayar fuskarsa na wani irin hucin da shi kansa yasan fushin dake cikin zuciya da gangar jikinsa ya banbanta da na ko yaushe,jinin NAFEESA CE FA?,shine abinda ke amsa kuwwa cikin kwanyarsa.

Cikin tauri da dakewar zuciya tace

"Ni me nayi?" Haushi da takaici suka sake turnuqeshi,ido cikin ido sukayi da ita,amma yanzun shi take tambayar wai me tayi?. Tana masa magana kuma cikin confidence da soyewar zuciya

"Ki gayamin me ya kaiki nan wajen?"

"Ni fa ba abinda naje,ba a kwance ka samenib......." Bai barta ta qarasa ba ya sauke mata mari saman fuskarta,abinda yayi matuqar razanata,ya kuma razana bibi dake shigowa ta fado dakin da mugun sauri kamar zata kifa.

Wani irin kuka da gigitacciyar qara sultana din ta saki tana riqe bibi data qaraso gurin. Tallafe sultana din tayi tana fadin.........


*ZAFAFA BIYAR FAMILY*πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚

πŸ”₯ *me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba*

*_ZAFAFA BIYAR_*❀‍πŸ”₯πŸ”₯❀‍πŸ”₯πŸ”₯❀‍πŸ”₯πŸ”₯


❀‍πŸ”₯ *_SABUWAR SHEKARA_*

❀‍πŸ”₯ *_SABON TSARI_*

❀‍πŸ”₯ *_SABBIN LABARAI_*


❀‍πŸ”₯ *_TSUMAMMIYAR SOYAYYA_*

❀‍πŸ”₯ *_CAKWAKIYA_*

❀‍πŸ”₯ *_LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO_*

❀‍πŸ”₯ *_SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA_*

❀‍πŸ”₯ *LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_*

*_KWANTAR DA ZUCIYA_*

*_CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA_*

*QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA*


*KWANKWASON JIMINA* _ME WUYAR TABAWA_ (miss xoxo)

*TSUTSAR NAMA* _ITAMA NAMA CE_ (Billynabdul)

*AMEENATU* (Mamuhghee)

*GUDUN K'ADDARA* _GUZURIN TARAS DA ITA_ (Huguma)


*_KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI_*

*_Biya naki ta wadannan lambobin domin ki zamo cikin ZAFAFA FAMILY HOUSE_*

*TSARIN SHINE KAMAR HAKA*


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*THANKS FOR CHOOSING US*πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚πŸ«‚
*_GUDUN KADDARA_*


*HUGUMA*


PAGE 02


Wani irin kuka da gigitacciyar qara sultana din ta saki tana riqe bibi data qaraso gurin. Tallafe sultana din tayi tana fadin

"Ashsha,ashsha,haba maina,me ya hadaku da zafi har haka?kai da nace maka baka ta lafiya?" Ta qarashe maganar idanunta saman fuskar sulatana da tayi jazur. Har cikin tsakiyar ranta takeji kamar ana fusgarta,saboda yadda zallar madarar zafin marin ya ratsata yadda ya kamata. Kai tsaye zata iya cewa ta manta da wani abu mai suna mari bare yadda zafi da radadinsa yake,sai gashi yau ya zama mutum na farko da ya tuna mata da wannan

"Ta gaya miki yaushe tabar dakin nan ta tafi gurin raye raye a tsakiyar maza ba tare da saninki ba" abinda ya furta kenan yana nunata da yatsa,ya sauke hannun ya juya yana fita a dakin cikin tsananin qunar rai.

Fuskar sulatana din bibi ke shafawa tana qoqarin rarrashinta,saidai ko a jikinta wai an mintsini kakkausa,kuka take sakewa kamar wadda aka yanki naman jikinta

"Wallahi radadi fuskata takeyi bibi,Allah bazan yarda ba,bazan yafe masa ba" sosai maganar ta daki zuciyar bibi din,tabi sultana da kallo wadda ruwan hawaye ya dade da gama jiqa mata fuska

"Sultana,mainanki ne fa?"

"Shi din bibi,mugu azzalumi,kawai don naji ana kida na tsaya rawa sai ya biyoni ya mareni?,me nayi masa?" Sosai jikin bibi ta mutu,bata taba tsammanin akwai ranar da zata zo da wani sabani me kama da wannan zai gilma tsakanin maina da sultana ba,sultanar da ko ita ba kasafai yake bari tana yi mata fada ba,bare duk da batasan yaushe ne lokaci na qarshe da aka daketa din ba. Sultana din da bata cin abinci ba tare da maina ba,bata iya bacci ba tare da maina ba,komai ma na rayuwarta maina ne,yau rana tsaka kamar wadanda aka yiwa farraqu suke neman sauya halayya ita da shi gaba daya

"Amma dai sultana sau nawa ina jan kunnenki akan zuwa wannan gurin?,saboda gujewa rana irin wannan?,ranar da maina din zai san kina zuwa?"

"Wallahi bai isa ya takuramin ba,shi waye ya takura masa?,kawai don yaga ina masa biyayya?,ai ba tsoronsa nakeji ba" ido da baki gaba daya bibi ta bude tana kallon sultana din. Mainan da ya zamewa kowa dodo cikin gidan?,koda a boye basu iya hirarsa bare a zahiri irin haka amma ita take sake masa magana?.

"Anya sultana?,me yake cikin kanki?,kina girma kina cin qasa?"

"Ki rabu dani tunda goyon bayansa kikeyi kema" ta fada tana ture hannun bibi dake cinyarta,sai kawai ta nufi toilet dinta ta shige ta maida qofar ta kulle,ta zauna a toilet seat taci gaba da rera kukanta kamar wadda sautin yakewa dadi.

Baki sake tabar bibi a zaune a wajen,cikin matuqar mutuwar jiki ta dauke kallonta daga bakin qofar toilet din,tasan halin sulatana da tsananin kafiya da kuma taurin kai,duk yadda taso ta fito a yanzun idan ba niyya tayi ba zata bata bakinta ne kawai

"Allah ya kyauta,yayi mana maganin wannan sabuwar matsalar kuma" bibi ta fadi ta yunqura tana miqewa. Sai a sannan taga jakar makarantarta dama doguwar rigar uniform da hijabinta a yashe a qasa. Tasa hannu ta kwashesu ta juya tana barin dakin.

Tsaye tayi gaban mudubin bandakin nata tana kallon fuskarta,sosai fuskar takeyi mata radadi,tasha ji a bakin su lamira cewa yaa maina din yana da zafin hannu,amma bata taba tantancewa ba sai yau,tunda bai taba kai hannunsa fuskarta ba. Hannu ta sanya ta sake shafar kuncin nata da yayi jajur,abinka da farar fata

"Dama haka zafin mari yake?" Ta tambayi kanta da kanta can qasa,saboda iya rayuwarta da kuma wayonta ba zata iya tuna lokacin da aka daketa bama bare a mareta

"Allah ya isa na" ta fada qasa qasa wasu sabbin hawayen suna zubo mata. Da baya da baya ta koma,tayi zamanta saman toilet seat tana ci gaba da fitar da sheshsheqar kuka. A iya marin da yayi mata yau kawai sai takejin wani mugun haushinsa irin wanda bata taba ji ba. Yaa maina din,shalelenta itama shalelensa,ba wanda ke tabuwa a wajen dan uwansa,amma yau sai taji ko fuskarsa bata son kalla.

Da zazzafan ruwa sosai yayi wanka bayan ya gama dukka uzururrukansa na ranar,da dan wuri yaso shigowa gida saboda yanayin sanyi da ya fara busawa,amma kuma daukan karatun da ya tsaya yi a zawiyya yasa lokacin shigowarsa gidan ya dan ja. Yana shiryawa yana bin tsarin dakin nasa da kallo,yaja tsaki lokacin da ya bude wardrobe dinsa yana bin shirin kayan da kallo.

Hannu ya saka ya zaro wata turtle neck sweatshirt me dogon hannu baqa,wadda ta fidda zallar hasken fatarsa da kuma narkakken kyau da yake shimfide a fuskarsa,wanda ke cakude da qyalli da sheqin samartaka.

A nutse ya shirya,idanunsa saman agogon dakin nasa ya dauki wayarsa yana shirin ya fita. Kamar jira wayar keyi ta dauki tsuwwa,sai ya dakata ya maida hankalinsa kanta.

'BIBI NA' shine sunan dake yawo saman screen dinsa. Daga wayar yayi yana ci gaba da shirin fitar.

Muryar Dijama ce, cikin d'ari d'ari da takatsantsan take gaya masa saqon bibi

"Okay" kawai ya fadi a taqaice yana katse kiran. Iska me zafi ya furzar daga bakinsa

"Me ya faru ne bayan tafiya ta?" Ya yiwa kansa da kansa tambayar da shima neman amsarta yakeyi. Gaba daya sauyin halayya da dabi'u yake gani daga yarinyar. Yarinyar da ya bata dukkan wani minti da awa dake cikin rayuwarsa wajen ganin ya raineta rayuwa me kyau,ya bata tarbiyya da tasha banban da ta kowa,ya kuma killaceta fiye da yadda ake killace kowacce diya mace dake jahar maradi,sai gashi tafiyarsa da waiwayo gida da yayi komai ya kwabe ya canza.

Iskar ya sake fesarwa,sai ya soma fita a dakin a gaggauce,can qasan ransa cike da tunani tare da son gano ina matsalar take?.

Zaune ya sameta cikin parlor din nasu,sanye

Please Login or Register in order to submit comment