Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauya ta fara hada ja,alamun dake nuna inda zata samu sarari kuka ma zatayi

"Mun gama magana da mariya zata bani bintu,ina ganin kamar diyata take tunda dan uwana ya hanani ita din 'yaruwatace mace zatafi fuskantata,har daki nasa an gyara mata an zuba furniture da nayo order dinsu daga turkey,an mata dinkin dukka kayan da zata saka,na siya mata foam zan canza mata ecole duka a nan,na ajjiye mata driver personal,na gama komai cikin satinnnan nake shirin zuwa Nigeria na daukota,shine yanzun ta kirani take gayamin wai abbanta ya hana,kakarsu tace ba zasu bada ita ba" ta qarashe maganar da alama abun ya sosa mata rai sosai.

Kyawawan idanunsa ya lumshe yana jin ciwon abun shima,bawai kuma ciwon hanasu bintu bane,tunda ko ba komai,duk da auty mariya masu wadatane sosai suma din amma basu kama qafar ama ba,ama nada son yara da riritasu,cikin gidan kaf banda sultana baiga wanda baya cin moriyar ama din ba wajen kyauta da jan mutum a jiki,ya sani bintu din zata samu gata da kulawar da babu lallai ta samu a gidan mahaifinta. Bacin ransa na ganin damuwa me tarin yawa saman fuskar ama din,inda yana da hali da ya samar mata wannan abun da zai wanke wannan baqincikin da takeji a duk sanda ta nemi riqon diya cikin diyoyin 'yan uwanta bata samu ba.

Matsowa yayi sosai ya kama hannunta ya riqe cikin nasa,cikin tausasa murya ya soma magana

"Kiyi haquri ama,daga yau kiyi haquri kibar musu diyoyinsu daga yau,ni na miki alqawarin in sha Allah duk sanda nayi aure zanyi addu'ar Allah yayita bani diyoyi mata,zan fara addu'a tun yanxu,sannan na miki alqawarin ko diyoyi mata nawa na haifa naki ne har sai kince kin gani da riqon 'ya'ya mata". Wani qawataccen murmushi da ya bayyana kyau da sauran quruciyarta ta saki bs tare da ta sani ba

"Maina,ta yaya zan gaji da riqon diyoyinku koda taron arfa zaku haifa?,ai saidai naci gaba da addu'ar Allah yaci gaba da baku masu albarka ya kuma hore mana abinda za'a kula dasu" daya hannun nata itama ta dora saman nasa

"Na gode sosai,daga yau in sha Allah na haqura,zan kuma jirayi jikokina komai tsahon lokaci kafin zuwansu" Murmushin shima yadan saki yana jin dadin yadda maganarsa ta faranta mata.

Agogo ya duba sannan ya miqe yana cewa

"Zanje na karbo dinkunana ama"

"Allah ya tsare,kada ka jima kaga bakajin dadi"

"In sha Allah......Key din mota daya zaki bani aro"

"Ya kamata kayi zuciya kayi motar kanka mana" ama din ta fada tana dan murmushi hadi da miqa hannu ta dauko key din motar da dazu goumar ya ara ya fita da ita ta miqa masa

"Akwai lokaci ama,karatu,yanzun inayin mota ko banaso sai ta sanyani yawo,ko banyi ba su sultan zasu sakani"

"Wannan karatu,Allah yasa a gamashi lafiya" ya amsa mata da ameen yana kaiwa qofa.

Sai da yahau titi sosai sannan ya tuna ya cewa bibi zai dawo,don haka ya ciro wayarsa yayi kiranta

"Bibi na wuce amma yanzu zan dawo"

"To yayi,idan kana dawowa ka tahomin da tsiren yahaya,na kwana biyu banci ba" dariya tadan subuce masa

"Kicemin kawai kwadayinki ne ya tashi" dariya tadan saki itama

"Idanma shidinne ai kaine ka koyamin ko?,nidai a kawomin"

"To in sha Allah" ya fada yana murmushi,sai ya katse wayar ya ajjiye a kusa dashi,ya dora hannuwansa duka saman sityarin yana fidda qotutuwar ajiyar zuciya idanunsa bisa titi

"Kowa yabar gida gida ya barshi" ya fadi yana furzar da iska daga bakinsa.

Mintuna arba'in ya qarasa shagon telan nasa,ya samu kayan a kammale cikin babbar jakar ledar dake dauke da tambarin shagon. Ya qarasa gurin biyan kudi yayi musu transfer na balance dinsu

"Yallabai ka duba mana" auwalu tela ya fada yana dan murmushi. Daukan ledar maina yayi

"A'a,basai na duba ba a hanya nake"

"To godiya mukeyi,sai mun sake ganinka" ya fada yana masa rakiya har bakin motar.

Sanda yake dawowa cikin shagon muzammilu ya tareshi

"Da alama kudi ka samu jikin sarmayin nan naga ka kasa zaune" dariya Auwalu ya saki

"Ah na samu alhmdlh,kowanne kaya saida ya qaramun kudi akan ainihin kudin dinkin kuma yana sane,na jima banga matashi da kudi basu dameshi ba irin maina mayak'i" idanu muzammilu ya buda

"Kai......kada kacemin family din MAYAK'I ne?" Kai auwalu da ya jawo wasu kaya zai yanka ya kada masa

"Qwarai kuwa"

"Amma gaskiya baka hadu ba,kuma kai banza ne,tsakani har ga Allah mutum irin wannan yazo wajen nan koni ka kasa gayawa na yagi wani abu?,yo aiko kudin cefani na sati na samu gurinsa ina laifi" harara auwalu ya jefa masa

"Hauka nake na gaya maka ku zubar mana da mutunci?,irin wadannan basason roqo basason wargi,kai bakaga yanayin fuskarsa ba?, baya wasa,ni ban taba ganin dariyarsa ba,yana dai murmushi sa'i sa'i"

"Ba komai,zamu hade nan gaba"

"Kai ka jiyo" ya amsa masa yana zare tip na awo daga wuyansa.

A nutse yaci gaba da tuqinsa tamkar bashi da wajen zuwa. Haka kawai weather din maradi din yau take masa dadi,sanyi sanyin nan dake nuna an fara bankwana da zafi. Sannu sannu har ya isa gurin yahaya.

Gurin gashin nama ne na gargajiya sosai,mutum biyu bibi keson namansu yahaya ko yahuza. Ba ruwanta da wajen wani BBQ ko gashin engine da sauransu,takance ita tafi gane wannan,shi yasa koda cikin gida masu aiki sukace zasu gasa mata ba kasafai take ci ba,saidai ta aiko nan din ko wajen yahuza a siya mata.

Yana ganinsa ya iso gaban motar tun kafin ya fito.

"Yallabai,hala bibi tayo aike" fuskarsa adan sake ya gyada masa kai

"Saqo ta bayar takanas"

"Kayya,kuma ba'a zo da wuri ba yau,yanzu na gama hada kaya komai ya qare wallahi" ya fada cikin rashin jin dadi yana kallon bayansa

"Babu komai,Allah ya qara albarkar kasuwa" maina din ya amsa yana laluba canjin aljihunsa ya miqa masa.

Hannu bibbiyu yasa ya karba yana godiya,yana matuqar jin dadin zuwan maina gurin,koda bai siya komai ba zai cikaka da alkhairi ya barka a wajen kana godiya,yana tsaye har motar maina din tabar wajen.

Har ya dauki hanyar gida yaga bai kamata ya shigarwa bibi din haka ba,ya tabbatar ta sanya rai tunda har ta bashi sautu,don haka ya juya akalar motarsa zuwa wajen yahuza dake bakin police station.

A hankali yake gangarowa saman babban titin da ya kasance daya daga cikin manyan titunan na garin maradi din. Titine dake dauke da manyan hotels eatery da guest houses parks da sauransu. Wannan dalilin ya sanya baka rabashi da wucewar manyan motoci masu matuqar tsada da daraja saboda gurin na kai kawon baqi daga gurare daban daban,yayan masu kudi masu buqatar hutawa da sauransu,dalili kenan da ya sanya aka qirqiri police station a gurin saboda samar da tsaro da kuma wanzar da zaman lafiya.

Daga gefe ya tsaida motarsa,ya saka hannu yana dage glass din motar yana duban glass din yana jiran ya gama rufewa ya fita a motar.

Kamar gilmawar walqiya motar tazo ta gotashi,idanunsa kuma sukayi masa kyakkyawan daukan wata sura cikin motar da tafi kama da SULTANA.

Tamkar an sanya wuta an jashi haka yaji haka yayi fit ya fita a motar,daidai sanda motar ke sanya hancinta zuwa cikin katafaren hotel din dake girke a wajen,karkatawar da motar kuma tayi ya bashi damar ganin sultana din sosai zaune daga back set tana dariya.

Wani mugun bugawa zuciyarsa tayi har sai da yaji kaman zai fadi. Bai qara koda second guda ba ya soma tattakawa cikin sassarfa yana dosar gate din. Kanshi tsaye ba tare da ya tsaya kulawa da security dake bakin gate din ba ya cinna kai ciki. Daidai sanda motar ta kammala tsaiwa qofofin motar suka bude wadanda ke ciki suka fito.

'yaran 'yammata ne kamarta su biyu sai matasan samari su uku harda driver din.

Sanye take da wani tsadadden trouser da ya zauna daidai jikinta kamar yadda rigar tayi masifar dacewa da qirar jikinta,qafafunta saye cikin wani arnen Boot da aka siyeshi da CFA me tarin yawa. Kanta babu koda qyalle bare dan kwali,gashinta me matuqar tsaho da santsi an masa wani irin gyara da idan ka kalleta zaka rantse batasan zoka kasheni da yaren hausa ko buzanci ba,don gaba daya ta koma kamar wata balarabiya daga qasar qatar ko oman ko wadda ta fito daga qasar hindu. Iya kyau tako ina ita kanta tasan a yau ta yishi,tun sanda aka gama shiryata,su lamira da sauran friends dinta kuma suka tabbatar da hakan ta hanyar kodata.

Batasan ya akayi ba,ta sama ne ta qasa ne oho,saiji tayi an finciki hannunta. Sanda ta waiwayo taga shine sai da taji tamkar jinin jikinta ne tsaf ya qone,wata mahaukaciyar razana tayi,amma cikin qasa da minti guda wannan zuciyar ta yunquro ta kuma fara haska mata tarin tozarci da asarar da zaya janyo mata matuqar bata jajirce ba. Wannan ya sanya ta turje sanda yake qoqarin riqeta da kyau ya kuma janyeta daga cikin gurin.

"Ka sakeni mana,me nayi maka?" Ta fada tana bata fuska da turo baki gaba cikin tsiwa da rashin kunya.

Yana waiwayowa abu na farko da ya fara yi sauke mata wani zazzafan mari da tunda ya soma dora hannunsa saman fuskarta bai taba mata irinsa ba. Marin da ya sanya ta gigice gaba daya ta kuma tabbatar da cewa ashe a baya qaryar jin zafin marinsa takeyi,yanzunne ta tabbatar da ainihin abinda ake nufi da mari,yanzu ne kuma ta gasgata gaskiyar zafin da yake dashi na gasken gaske. Mari na biyu daya qara mata shine ya cisge duk wata kafiya tata da taurin kanta,bakin cewa ya saketa ta koma ya mutu murus. Ya janyeta da zafi zafi tana gurdewa saboda tsinin takalman qafarta,bai kuma saketa ba ako ina sai cikin motar sa,ya maida murafun ya rufe ya murza key ya kulleta.

Hannayensa ya zuba duka cikin aljihun wandonsa yana kallonta sanda take rusa kuka yana kuma furzar da wata zazzafar iska. Shi kadai yasan me zuciyarsa ke raya masa a kanta. Sultana a hotel?,tafiyarsa har ta sake sanyata ta kuma lalacewa haka?,me bibi takeyi?,aikin me aba yakeyi?,haka ake gata?,sudin haka akayi musu?. Qafa ya saka cikin zafin rai yadan daki gaban motar sai ya juya yana nufar wajen yahuza wanda baisan ma yazo ba,cikin ransa yana rantsuwa da Allah yau kam za'a kawo qarshen komai,duk da ama taja kunnuwansa akan sabgar sultana din,amma yanzun an fara kaiwa shingen da idan basu tsaya ba zasuyi kuka dukkaninsu da idanunsu,tunda zuwa yanzun ta fara kaiwa shekarun girma,shekara goma sha uku nan da shekaru biyu budurwa za'a yi kiranta.

Koda yaje yadan samu layi,ba mutum ne shi me take doka ba,duk da akwai sanayya tsakaninsa da yahuza ta regular customer da business owner amma sai yabi layi kaman kowa. Saman kujerar roba dake wajen ya zauna,saidai sam bashi da walwala ko sukuni,saboda wani irin zafi da zuciyarsa take masa.
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

PAGE 21

______________________________

*_KUSAN FA MU DUK TA GEFEN DA QAMSHI YAKE MUNA WAJEN😄😄,AHTO,KU MATSO KU GA WANI ABU*_👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

_ADVERT👇👇_

MKBEES PERFUMERY
_(GIDAN KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_


_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE,
_KAI DAKA FESA KAJI DADI NAKUSA DA KAIMA YAJI DADI.TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA KAYAYYAKIN_KAMSHI MASU SANYA NUTSUWA DA KWANCIYAR HANKALI

_*KU GARZAYO MKBEES PERFUMERY
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN CHADI DA SUDAN AKWAI OIL PERFUMES,AIR FRESHNER, CARPET SPRAY DA TURARUKAN MOPPING DANA WANKA DANA GADO,LABULE DA KUJERU , BANDAKI DA DRAWER .

_AKWAI TURAREN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DAHANA TSAMIN GASHI DA KUMA LAUSHI. AKWAI HODAR HAMMATA ME TAIMAKAWA WAJEN HANA WARI DA TSAMI ACIKIN LOKACIN ZAFIN NAN,AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYEN DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN MKBEES PERFUMERY.
KO BAKU SIYA KAYA BA KUYI SAVING NUMBER DINTA KUFADA MATA TAYI SAVING NAKU DOMIN KOYON DUBARUN KASUWANCI KYAUTA A STATUS DINTA.

_NAMBAR WAYAR SU: 07011113951,07032456061.
INSTAGRAM :Mkbees_perfumery.
_YOUR NUMBER ONE PLUG FOR KOMAI KAMSHI A TRIAL WILL CONVINCE YOU.
_______________________________




Kuka takeyi sosai tana murza fuskarta dake mata wani irin mahaukacin radadi,baya ga zafin marin babu abinda yake zuciyarta illa asarar zuwa birthday din dake tunkarota tunda tayi amanna zuwa yanxu sha'ani yayi nisa,kuma dukka su lamira aminata da yasmine suna ciki.

Yaushe ma yazo garin bayan kwanansa nawa duka da tafiya?. Me yasa bashi da aiki sai marinta?,abinda wani halitta be taba yi mata ba sai shi?.

Wata irin mahaukaciyar qiyayyarsa da tsana me qarfi ta sauko mata sanda taga fuskarta a jikin mirror,ta hada wani mugun ja,shatin dogayen yatsunsa kwance akan fuskarta.

"Wallahi daga yau ba zaka sake marina ba,bakaci bulus ba" ta fada a fili cikin muryar kuka

"Tome zaki masa ki rama?" Ta tambayi kanta da kanta.

Gilmawar wani dan sanda ta bakin motar yana nufar can wajen yahuza saita zame mata tamkar amsar tambayar ta,cikin sauri ta koma bakin window din,akwai sauran space da bai qarasa rufewa ba don haka ta saka kanta ta wajen ta fara sharara ihu tana kallon saitin policestation din.

"ku taimakeni!,wayyo Allah,don Allah wani ya taimakeni!!" Ta fadi tana kallon gate din policestation. Shuru ba kowa ta wajen,abun da ya tabbatar mata sai tayi da gaske,kuma tana buqatar tayi komai da sauri kafin maina ya cimmata,don haka sai ta qara bude dukka muryarta da qarfi tana fadin

"Ku taimakeni a taimakeni wayyo Allah wani ya taimakeni!!!,ku taimakeni don Allah SATO NI yayi!" Maganarta ta qarshe tayi dai dai da dawowar police din dake riqe da wata qaramar baqar leda,da alama wani abun ya siyo.

'yan sanda ne tsayayyu da sukasan abinda sukeyi cikin kulawa da haqqin kowa,ba batun cin hanci ko rashawa burinsu dai kawai aikin da hidimtawa zuwa ga qasarsu NIJER. Da sassarfa ya nufo gurin,sai sultana din ta qara bude murya da kyau tana sake sakin ihun neman taimako

"Ke!,menene?"

"Me motarnan ne ya satoni"ta fadi cikin kukan baqinciki ya bata mata ranar gaba daya.

"Sata?" Bai gama jiran amsarta ba ya waiwaya yana qwala kiran inoussa da idrissa. Cikin qasa da second biyar sai gasu sun iso,fitowar tasu da tsaiwarsu a wajen suna cigiyar waye mamallakin motar ya fara jan hankulan jama'a ta wajen.

"A gaida hajjaju don Allah" yahuza ya fadi yana miqawa maina ledar naman

"Zataji" ya amsa da sauri don yana burin ya isa gida kan sanda aba ke dawowa.

Da mamaki yake kallon motar tun kafin ya qaraso yadda 'yan sanda suka baibayeta

"Duk yadda akayi me motar yana ta nan baiyi nisa ba,ku bincika" gabansa ya tsinke dajin abinda suke fadi,ko wani abu ya faru da sultana dake cikin motar,wannan ya sanya ya qarasa da sassarfa yana fadin

"Gani,nine me motar" yadda dukka aka zuba masa idanu yasa yasha jinin jikinsa

"Kaine me motar?"

"Eh" ya gyada kai

"Satar mutane da ranar Allah kuma don rashin kunya ka daukota ka aje cikin jama'a kusa da hukuma saboda ka maida polisawa shashashai?......idrissa,karba maqulli ku sakata a ciki shima ku shigo dashi yayi bayani". Gaba daya kansa ya qulle,baima fahimci komai da suke fada ba. Ta gefen sultana kuma sai taji hakan baiyi mata ba,ba ciki taso a shiga ba,a nata plan din zasu budeta ne ta fita,ita kuma sai ta samu ta koma gurin birthday din,sauran kome zai faru idan sunje gida wannan wani abune na daban.

A nutse kuma cikin zallar mamakin daga inda batun satar mutane ya bulla ya shiga motar ya kunnata ya kuma gyara tsaiwarta ya gangara da ita cikin police station din.

Su suka nuna masa inda zai ajeta ya ajjiye din kuma ya fito yana bin bayansu zuwa cikin station din.

Gurin zama yayi musu a gurin da ake daukan statement,har a lokacin tunaninta gaba daya yana wajen birthday din burinta daya suce ta tashi tayi tafiyarta ta samu cikakkiyar damar zuwa ayi sha'anin da ita

"Kikace satoki yayi daga ina?" DPO ya jefawa sultana tambayar yana kallonta. Da sauri tana kuma sharbe hawaye ta gyada kai

"Satoni yayi zaiyimin FYA'DE" Ta fada da confidence tare da nuna tsoro zalla saman fuskarta.

Wani mugun duka zuciyarsa tayi,irin dukan da bata taba yi masa irinta ba iyakacin tsahon rayuwarsa.

"Sultana!?" Ya kirayeta da wata madaukakiyar tsawa fuskarta cakude da wasu al'amura masu nauyi da suka hada da razani da kuma firgici me yawan gaske

"fermez-la(shut up)" shima dan sandan ya dakawa maina tsawa cikin nuna bacin rai qarara

"Bude mata ido zakayi ka hanata fadin gaskiya?, idan har kai me gaskiya ne ka bari ta gama jawabinta sai kayi naka" ya fadi yana muzurai idanunsa akan maina,kamar yadda shima maina din ya kafeshi da nasa idanun,maqoshinsa yana sama da qasa,idanunsa kuma sauya launi a hankali a hankali,saboda wata muguwar suya da kalmar FYA'DE ZAIYIMIN din data fada ke yi masa.

"Kin sanshi dama kenan?" DPO ya sake tambayarta yana maida hankalinsa kanta. Ga tarin mamakin maina saita girgiza kai da sauri

"Ni bansanshi ba,bansan wayeshi ba,ban taba ganinsa ba sai yau,a hanya ya ganni ya satoni,yanata qoqarin min fyade din......."

"Sultana!" Ya kuma kiran sunanta jin tana sake yunqurin dangantashi da kalmar fyade

"vas-tu te taire ?(zakayi shuru ko kuwa?" Dan sanda da tasa budaddiyar muryar me kauri data lullube ta maina ya fada yana tashi kaman tsaye kaman zai rufeshi da duka,kasancewar ko a girme ya girme masa.

Zuciyar 'yan maza ta motsa,ya mance sam sam wai a gaban hukuma yake, idanunsa rufe ya soma zazzagawa dan sandan masifa

"Ta yaya zaka zauna yarinya qarama ta dinga tsara maka qarya abinda bai faru ba ehhh?"

"Au qarya ma takeyi?,wannan marukan na fuskarta duk na meye?,ko ku baku gani ba?" Ya fadi yana tambayar sauran Yan sandan dake wajen

"Gaskiya ne Monsieur(sir),dama duk sanda zasu aikata hakan saisun mammare fuskar yara harda duka na rashin imani" wata police mace dake tsaye a wajen ta fada cikin hasala,da alama itama akwai adawa me qarfi tsakaninta da fyaden

"fermez-la(shut up),kina sanye da kaki amma baki iya banbance tsakanin me gaskiya da me laifi,kuna hukunci da abinda aka baku labari!"

"Zaginmu zakayi?" DPO din dake tsaye a daura dashi ya fada cikin hasala

"Bazan zageku ba amma na raina iyawark......." Baikai qarshen zancan ba DPO din ya zuba masa lafiyayyen mari saman kyakkyawar farar fuskarsa.

Tamkar gilmawar walqiya,tamkar kuma gizo sultanar taga saukar mari kan fuskar maina. Tayi muguwar razanar da har sai data miqe daga saman kujerar da take zaune a kai

"Koma ki zauna,ai tunda kike nan tu es en sécurité,bai isa yayi miki komai ba,mara gaskiya kawai,ba daka mata tsawa da hanata tona maka asiri zakayi ba,défendre kanka zakayi kaima indai kai me gaskiya ne,ka gaya mana a ina ka santa?" Koda yana da nufin masa bayani bayajin zai iya buda bakinsa a yanzu,domin wata irin wuta ce kai kawo tsakanin qirjinsa zuwa bakinsa,wani irin kallo yake jifan DPO din dashi da idanunsa da sukayi jazur kaman an masa kwalli da borkono.

"Wannan bashi da gaskiya,ku sakamin shi a bayan kanta" ya fada cikin bada umarni. Bai hanasu yi kasa komai ba don yasan kowanne motsi zaiyi a wannan lokacin to tabbas zai iya daukan mummunan hukunci akansu gaba daya saidai duk abinda zaya faru ya faru. Takalminsa suka karba agogonsa da wayoyinsa dukka suka kashe. Yana tsaye daga dakin yana kallon yadda suka rufe sultana suna mata sannu hade da sake dubata

"Ki rakata gida aicha" DPO din ya fada

"A'ah zan iya tafiya" ta fada da sauri tana satar kallon inda suka rufe maina

"Idan aka ganni da ku kowa ma zaisan me ya faru,banason mamana ta sani hankalinta zai tashi"

"Shikenan,ku kaita bakin layi" ya fadi yana sanya hularsa gami da miqewa.

A hanya sam batajin me suke cewa sai tunanin abinda ya faru a station din. Ranta ya danyi mata rashin dadi da kulleshin da sukayi,so tayi ace tunda Allah yasa sun rama mata mare maren da tasha a hannunsa su sakeshi hakanma kadai ya isa.

A bakin layin nasu suka ajeta ta taka har zuwa gida da qafarta. Tana shiga farfajiya ta biyu ta sami su lamira. Dukkansu sukayo kanta

"Su zinnira sukace wai yayankine ya tafi dake,sunce kaman yaa maina,amma shi kuma baya nan,ina kikaje har akayi aka gama baki wajen anata cigiyarki?" Kusan a jejjere suka dinga jefa mata tambayar

"Yaaya Samaila na raka wajen budurwarsa(wani dan aminin oncle bashar ne" itace amsar data basu kenan tana wucewa sashen bibi ba tare data tsaya jiran labaran da suka qullo zasu bata ba,don babu abinda labaransu zasu qara mata ta sani sai zallar bacin rai,tunda dai maina din da basusan da zuwansa ba ya bata mata ranar gaba daya.

"Allah ya sakamin" kawai take fadi duk sanda ta tuno burin da taci akan ranar amma ya wargaza komai

"Allah yasa ya sake musu taurin kanshi su sake lallasashi yadda ko ya dawo gida zai barmu mu sarara" ta kuma fadi sanda ta tube kayanta ta shiga wanka.

Wankanta tayi abinta ta shirya tsaf kamar ba abinda ya faru taci gaba da sabgoginta. Duk sanda ta tuna ya maina din yana kulle a station sai taji dariya tazo mata,musamman idan ta tuna zafin kansa tsananin tsaftarsa da qyanqyaminsa,yau ya zaiyi dasu?.

Ba

Please Login or Register in order to submit comment