Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sumarta da sam bata kitsuwa damar warewa.

Takalmi zuwa socks dinta ta salube suma ta wurgar,ta zare rigarta da wandon duka,ba abinda ya rage mata sai vest dinta data kawo har cinya da kuma wandonta da ya tsaya iya gwiwa.

Fridge ta bude ta dauki madararta me sanyi ta fasa ta fara sha sannan ta wuce dakinta bayan ta kalli agogo ta kuma qiyasce mintunan da suka rage da za'a dameta da batun tafiya islamiyya. Islamiyyar da ayau ta haqqaqe ko dambun namanta za'a yi yau din ba zataje ba,don haddarta ta jiya da shekaran jiya duka babu wadda tayi. Ba abinda ta tsana irin a bata haddar,a duk sanda malamin ya shigo ita kuma nata karsashin ya qare,ta gwammace ta nade cikin hijabi ta hau baccin qarya,ciwon kai ciwon ciki duka nata ne,tun malamin na tunanin hakanne da gaske har ya fahimci akwai lauje cikin nadi,duk wata hikima da hukunci ba wanda baiyi mata ba amma sam ba abinda ta sauya. Batason karatun shi ya sanya ta sakawa ranta bata ganewa wannan yasa bata ganewar.

Cak ta tsaya sanda ta tura qofar dakin nata tana bin dakin nata da kallo. Taku biyu baya tayi tana mutstsuke fararen idanunta tana sake kallon kowacce kusurwa ta dakin da kyau.

Sakin labulen tayi sannan ta bude dukka siririyar muryarta ta soma kwarara sunan

"Tanja!......tanja!......tanja!" Tamkar wadda sukayi kacibus da mutuwa.

Kusan lokaci daya suka saki dukkan abinda sukeyi din suka durfafi dakin da wani mugun sassarfa. Daga tanjan da aka kira har bibi da ba'a ambaci sunanta ba a rude suke matuqa da kiran tanja da sultana keyi babu qaqqautawa. Zuciyarsa a tsinke da tunanin mugun abu ya sameta.

Birki suka ja dukkansu suna kallonta,ta yaye zanin gadonta gaba daya ta kuma wargaza kayan closet dinta gaba daya

"Ina nini na tanja?,ina games dina?,waye ya shigo ya sacemin kayana?" Ta fada idanunta na rau rau da hawaye,zallar tashin hankali ya bayyana saman fuskarta

"Yanzu fisabilillahi saboda wannan ya sanya kika dinga qwalawa tanja kira?,dukka falukan gidan nan sai da suka amsa?" Bibi ta fada tana tsuke idonta akan fuskar sultana,tana ganin wani tashin hankali da muraran kan fuskarta,kai kace an sace mata wasu abubuwa masu matuqar muhimmanci ne ga rayuwarta. A wajentan masu matuqar muhimmanci ne,domin ninin na daya daga cikin abubuwan da tafi so cikin abubuwan data mallaka,hakanan games dinta suna a mazaunin manyan abokai cikin rayuwarta.

Duk yadda take da surutu rawar kai da tarin tarkacen qawaye hakan bai hanata qin shiga shirgin kowa tare da ware kanta haka kurum idan taso cikin dakinta. Zata iya kashe awanni ita daya,rungume da nini dinta da kuma games dinta.

Kai kawai bibi ta girgiza ta juya tana barin dakin

"Waye ya daukemin nini na?" Sultana ta fada muryarta na rawa tana shirin fara sakin kuka. Itakam bibi ma bata waiwayo ba,sai tanja dake qoqarin kintsa dakin ta amsata

"Mainasara ne sultana"

"Maina?" Ta furta cikin cika da batsewa tana jin masifa fal zuciyarta. Da gaske dai rayuwartata yakeson shigar mata,qarfi da yaji yakeson shiga abinda take ganin bai shefeshi ba tunda tuni ya zare kansa daga sahun mutanen dake qaunarta har zuciyarsu

"Wai shin me yayi ruwansa da kayana tanja?" Ta jefawa tanja tambayar cikin kaushi da zallar bacin rai

"Karatu mana sultana?,maina yana miki sha'awar karatu ne"

"To bazanyi ba,nace bazanyi ba,wani banzan maina bai isa ya takuramin ba bayan shi din ba ubana bane" ta fada cikin tafasar zuciya.
*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

PAGE 07


Maganganun sai suka kwancewa tanja kai,koda cikin mafarki tayi mafarkin sulatan zata iya gayawa maina hakan lallai zata daukarwa ranta cewa gundumemiyar qarya ce mawai shaidan ya wassafa mata a mafarki don yayi wasa da tunaninta. Maina da sultanan da suka zama wani kyakkyawan madubi da kowanne uba zai kalla game da diyarsa?,yau itace ke furta masa hakan?.

Ko kafin tanja ta sauke tunaninta sultanan ta fice a dakin a gaggauce.

A falo taja tunga,don dama bibi take nema kuma ta ganta. Da jiqaqqun idanunta da suka gaza boye hawayen da taketa son shanyewa ta dubi bibi,don duk yadda taso ta shanye bacin ran maina amma ta kasa,saboda zuciyarta ta gaya mata nini dinta da games dinta sun tafi kenan,tafi kowa sanin shi din kaifi daya ne,kuma ya aikatashi zaiyi shi ne gaba gadi,babu kuma sauyi ko canji a hukuncinsa

"Bibi ki gaya masa ya dawomin da kayana" ajjiye cup din hannunta bibi tayi,daga tsayen da take ta maida dubanta kanta

"Zai dawo miki dasu,amma saifa idan kin maida kai ga karatunki,na tabbatar idan yaga hakan ko bakice ba zai dawo miki da kayanki gaba daya koda kuwa ba'a ce masa ba"

"ni kawai ki gaya masa ya dawomin da kayana tunda dai ba shine ya siyamin ba" tayi maganar da alamun kuka yana son balle mata.

"Ai sai kije ki karbo da kanki" bibi din ta fada cikin gatse. Bibin na direwa sultana tayi hanyar falon cikin dakiyar zuciya,cikin zuciyar tata tana fadin

"Aiba ubana bane,ba kuma mala'ikan mutuwa bane da zanji tsoronsa".

Kaman ko yaushe,ma'abocin rashin son hayaniya ne da kebe kansa guri guda a mafi yawancin lokuta. A yanzun ma hakan take. Shi daya ne a farfajiyar gidan,yana sanye da wata lallausar shirt da trouser dukkansu royal blue ne da dan ratsin blue din kadan a jikinsu. Ma'abocin karance karance ne sosai,yana daya daga cikin hobby dinsa. Ko yanzun ma littafin wani shahararren marubuci ne a hannun nasa dan qasar faransa.

Idanunta a kansa tun daga nesa ta tsareshi dasu,sannu a hankali take qara kusanci a tsakaninsu. Wani irin kwarjininsa ke dukan zuciyarta yana neman cire mata dukka wani qwarin gwiwa da ta fito da ita,saita ta lumshe zuciyarta na sake bata qwarin gwiwar tunkarar nasa ta kuma zazzage masa dukka bacin ranta da abinda ke cikin zuciyarta.

Maimakon ci gaba da samun qwarin gwiwar isa gareshi din,a duk sanda tayi taku daya sai qarfin gwiwarta ya ragu da wani kaso me yawa. S hankali ta tsaya cak kamar wadda aka yiwa burki sanda take dab da isa gareshi,kwarjininsa gaba daya ya gama cikata,tayi imanin tayi kadan ta isa inda yake din duk da confidence din da ta fito da shi a dazu,wannan baqincikin ya sanyata juyawa da sassarfa me hade da gudu tana komawa sassan bibin.

Sam baisan da tsaiwarta a wajen ba,don shi din mutum ne da bai fiya mai da hankali da idanu akan abinda bai shafeshi ba,yaji motsi da taku duka lokaci daya,ya daga shanyayyun idanunsa yana bin hanyar da kallo. Baici nasarar ganinta ba,saidai yaga shigewar mutum sashen bibi,sai ya dauke kansa ya maida ga abinda yakeyi.

Da kallo bibi dake zaune cikin lafiyayyun kujerun falon ta bita. Ta sake baki kawai sanda ta zube saman daya daga cikin kujerun tana sakin qarfaffan kuka

"Oh.....oh ni maryamu,yau naga abinda ya isheni"

"Alla......Allah sai ya dawomin dasu,Allah bibi kiyi masa magana" abinda sultana din ke maimaitawa kenan cikin kuka. Ta tafasa sauke bibi bata sake cewa da ita ba sai maida kanta da tayi ga abinda takeyi,saboda tayi imanin zata bata bakinta ne kawai,don babu abinda zatace da sultana da zai sanyata tayi shuru.

Kuka sosai tayi cikin kujerar kamar wadda aka yiwa mutuwa,irin kukan data jima batayishi ba,har ranta bibi kejin kukan amma tayi banza da ita,saboda ita kanta ta tabbatar dauke kayan shine maslaha. Tanja ce ta dinga fama hade da jelar lallashin sultanar amma babu abinda ya canza. Zuwa wani lokaci tayi shuru,shurun da ya tabbatar tayi bacci.

Blanket tanja ta dauko tana jan qafafunta ta gyara mata kwanciya,zuwa yanzu sultanar tayi girman da ba zata dauketa ba,ba kamar shekarun baya ba da idan ta gama rigimarta kamar haka tayi bacci tanja din ke daukarta ta kaita dakinta ta kwantar da ita.

Wannan abun da ya farun ya sanyata tsirar fushi da kowa cikin gidan,gefe daya kuma ta sake fakewa da wannan ta aske zuwa islamiyya. Hatta bibi batasan bata zuwa din ba,tanja kawai tasan da hakan,ita dinma kuma bata gayawa kowa ba,saidai tanata qoqarin lallabata da hikima da dabara akan batun zuwan.

Cikin kafiya da taurin kanta tayi kunnen uwar shegu da tanja din,duk da hakan tanjan bata fasa hilatarta ba.

Kwanaki uku kenan ya karanci kowanne yaro na fita islamiyya amma banda ita. Tun a kwanan farko yaso yiwa tufkar hanci,amma sai ya fasa ya zuba idanu yaga iya gudun ruwanta. A iya nata hasashen da gajeren tunanin tana tunanin kamar ya fita sabgarta ne,hakan ya sanya baya gane duk wani motsi nata kenan.

*_L A H A D I_*


Kimanin qarfe uku na yammacin ranar lahadin,ranar da kowanne yaro na gidan ke tafiya tahfeez,tun sha biyun rana sai qarfe biyar da rabi na yammaci suke dawowa cikin gidan.

Dai dai lokacin da sultana ke cikin dakinta,tayi game yau din har ta godewa Allah cikin wata wayarta da uncle inoussa ya taba bata gift na birthday dinta. Shekara guda kenan wayar na ajjiye bata taba amfani da ita ba,sai a yanzu da maina ya talautata ya kwashe mata dukka abokan debe kewarta.

Qishirwa ce ta dameta,ta bude fridge dinta babu ruwa,madararta ma sauran kadan ta qare. A kwanakin ta sha madarar sosai zaman da takeyi a dakin na awanni har batasan adadin guda nawa ta sha ba. Maida murfin fridge din tayi ta rufe,ta sauke lausasan siraran yatsunta qasa ta miqe tana daure gashinta dake da tarin yawa tsaho da santsi,baqi sidik da shi na asalin buzaye.

Cikin takatsantsan take takowa zuwa falon don kada suyi kacibus da bibi,taji dadi sosai data fuskanci babu kowa cikin falon,wannan ya sanya kanta tsaye taci gaba da takawa zuwa ga babban freezer dake girke a wata kusurwa ta musamman dake cikin falon.

Cikin nutsuwa jerin gwanon motocin ke kutso kai cikin tafkekiyar harabar farko ta gidan,wadda a nan aka tanadi wani tsararren parking lot da aka gina shi bisa tsari da kuma dacewa.

Lafiyayyun motoci ne da suke lashe manyan maqudan kudaden da kai zaiyi ciwo wajen lissafin yawansu. Kowacce mota kuma mallakin hamshaqin attajirin dan kasuwa ne wato MUHAMAT MUHAMMAT MAYAK'I. Dan kasuwar da sunansa yayi wani irin fice yayi tambari ya kuma shahara cikin qasar NIJER dama nigeria din gaba daya.

A nutse suka gama tsaiwa,mota ta qarshe a cikinsu seat din gaba suka bude. Wani farin matashi me tsaho da kuma kauri ya fito ya dawo set din baya ya bude murfin motar.

"Bismillahir rahmanir raheem" shine abinda mutumin ya fada yana sako dogayen qafafunsa yana fita a motar.

Tsayayyen ingarman ba'abzine fari sol sol dashi,giant ma'abocin tsaho da kuma qiba wadda tsahon ya tafi da ita,wannan dalilin ya sanya kai tsaye zaka iya kiranta da murjewar jiki. A duba na farko kawai zaka yi masa kasan cewa yana cikin jerin samarin da suka zuba kyau da kuma qasaita a zamaninsa. Dai dai lokacin maina ya qaraso gurin. Qarasawarsu kusa da junan ta haifar da wani kyakkyawan kallo na kyawawan halittu guda biyu masu dan shigen kamanni da juna. Maina din ruwa biyu ne,wani lokaci kamanninsa sukan juye zuwa na ABA,wani lokaci kuma sai kaga kamar kaga AMA.

Isowar tasa ta fidda murmushi saman fuskar mutumin,bai iya jurewa ba ya miqawa maina din hannu

"Likita bokan turai mainassara" siririn miskilin murmushi ya walqa saman fuskarsa,cikin matuqar girmamawa ya furtawa aba din kalmomin maraba da shiryayyu kuma taqaitattun kalmominsa,sannan ya matsa gaba kadan yana karbar briefcase din aba din daga hannun daya daga cikin yaransa.

"Ka shaidawa bibi isowata" aba ya fada don yasan abinda maina din ke son fara yi kenan.

Kansa tsaye ya tunkari sashen bibi din yana takawa cikin nutsuwar nan tasa data girmewa shekarunsa. Yana bude qofar tana sakin gorar ruwan hannunta,hantar cikinta tayi wani mugun kadawa lokacin da idanunsu suka gauraya waje daya,tsoro ya bayyana sosai cikin idanunta,yau kam tasan ta kade,batasan kuma me qwatarta ba bayan ubangijinta.

Shanyayyun idanunsa ya zube mata yana fara hukuntata da kallonnan nasa da a baya su kadai suna iya fahimtar da ita umarninsa ko haninsa. Ya raineta da irin wannan sigar da ta sanya basai ya furta komai ba take iya gane me din yake nufi. Duk taurin kanta da dakiyarta a yau jikinta ya kasa shanye wannan tsoron daya kwanta saman zuciyarta. Dukka jikinta yadan soma rawa,ya ajjiye briefcase din aba ya goye hannayensa a qirjinsa ba tare da ya dauke idanunsa a kanta ba ya jefa mata tambayar

"Ina islamiyya?,me kikeyi a gida?" Kwata kwata dukka wata amsa ta dauke a bakinta,musamman sanda idanunta suka hangi bibi tsaye daga bayansa baki sake tana mamakin ganin sultana din itama a gida

"Ina islamiyya nace miki!" Ya sake fada cikin tsawa,tsawar tasa data kusa ruguza ragowar nutsuwarta.

Cikin harshensa daya gauraye da hausa faransanci da kuma yaren buzanci yayi sallama a falon,sallamar tasa da tayi dai dai da saukar rahama da wani irin farinciki a zuciyar sultana. Dayan madogarartata ya dawo,bango abun jinginarta,wanda a yanzu tana da yaqinin shine ya maye gurbin matsayin yaa maina din a ranta da zuciyarta,ta tabbatar kuma a yau ta kubuta daga dukkan wani hukunci da muguntar da maina ya tanadi yi mata. Bata qara koda second biyu ba ta qarasa gareshi da hanzarinta. Kaman wadancan shekarun ta tarbeshi,saidai a yanzun ita kanta taji kunyar fadawa jikinsa sai hannunsa data kama,qwayar idanunta dake da wani irin maiqo koda babu hawaye a cikinsu sun sake sheqi saboda qwallar data tara a cikinsu.

*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

PAGE 08


Dukka kafadunta ya dafa yana kallon fuskarta dake tuna masa abubuwa masu tarin yawa da suka shude

"Meye haka?"

"Yaaa maina ne" ta fada tana qarasa tsinkewa da kuka kamar abinda take jira kenan dama.

Tsaf aba ya dinke fuskarsa yana dubansa. Mamaki yana ratsashi shi kansa,dama akwai wani lokaci da har wani zaiji rigima tsakanin maina da sultana?,alaqarsu data zarce ta mahaifi da d'iyarsa?.

Kallon da yayi masa ya tabbatar kallo ne na tuhuma,sai ya jaye dubansa daga b'arayin da aba din yake

"Ya kwashemin Jeux(games)dina,tablette(tab) harda nounours(teddies) dina gaba daya aba" ta fada hawaye na tsargo mata,da alama sosai da gaske tayi missing teddies din nata.

"assez(ya isa),zauna maza" aba ya fada yana jan hannunta zuwa saman daya daga cikin kujerun falon.

Dukkansu suka zauna,saidai shi maina din yana tsaye harde da hannunsa. A nutse aba ya daga kai ya kalleshi

"asseyez-vous(zauna)" gaba kadan ya matso ya zauna daura da bibi

"Me yasa maina?" Aba ya jefa masa tambayar yana dubansa

"Batason karatu aba,bata iya komai cikin karatunta ba sai tarin shirme,batason makaranta"

"Me yasa sultana?" Aba ya maida duba da tambayarsa a kanta

"Ina zuwa abba Allah,kullum ma,kuma ko yau naje ka tambayi su najma" .

Idonsa ya qanqance yana jin zafi har tsakiyar qirjinsa. A duk sanda tayi qarya sai yaji kamar ya tsinko zuciyarsa,ya raineta saman qin qarya da fadar gaskiya komai dacinta kamar yadda tasa dabi'ar take,amma dare daya ta sauya tamkar wahainiya.

"to amma islamiyya fa?" Aba ya tambayi sultanan yana kallonta.

Shuru tayi kamar yadda falon ya dauki shuru kowa yana jiran amsarta,sai mutsu mutsu data fara da hannayenta da qafafunta tabbacin rashin gaskiya kenan. Haka aba ya gaji da jiran amsarta ya zame hannunsa yana gyara zamansa sosai

"Kina jina sultana?" Kai ta gyada a sanyaye,amma zuciyarta wani zafin haushin ya maina take mata

"Karatu shine mutum kinji?,dukkanmu nan da kike ganin gajiyarsa muke ci kuma darajarsa muke ci,Aliyyu ba matsa miki yayi ba,yana sone yaga kinyi karatu sosai kamar yadda yake shine burin nafissa,Allah baiyi zatayi karatu me zurfi ba ya dauki abarsa" ya qarasa fada alamun suna nuna har yau furta sunan nafisa a bakunansu yana tuna musu da dacin rasata da sukayi

"Zanyi aba" ta fada a sanyaye da kuma zummar katse fadan da aba yake mata a gaban ya maina din

"Allah yayi miki albarka,kije ki gayawa tanja ta rubuta abinda dukka kikeso wanda baki dashi" murmushi ne ya qwacewa sassanyar fuskarta dake lullube da wani irin kyau dake garwaye da sauran quruciya

"Aba,madarata ya kusa qarewa"

"Carton nawa ya rage?,tanja ta rubuta ki kawomin a qaro miki" . Wani wawan tsalle ta buga tana sake riqe hannun aba da kyau,kai kace duka duka shekarunta basu haura uku ba

"Mêrci aba" sai kuma ta saki hannun nasa tana zarcewa ciki da sauri sauri. A duniya tana iya jurewa daina shan komai amma banda madararta wadda ta zame mata kamar jini da hanta,hakan kuma baya rasa nasaba da cewa madarar itace ta zame mata tamkar uwar raino a lokacin da ta rasa dumi da gardin nonon uwa da kowanne yaro ke mararin samu a harshe da cikinsa.

"Aliyyu" aba yayi kiran maina wanda ke zaune cikin amintacciyar nutsuwarsa kansa a qas. A zahiri yana latsa wayarsa ne amma can cikin zuciyarsa cike take da wata irin fargaba. Yayi tsammanin aba din zai zama mutum na farko da zaiyiwa sultana fada kashedi da kuma jan kunne da kakkausar murya,amma kuma sai yaga akasin hakan,bayan yayi mata fadan kuma ya buge da wanke laifinsa ta hanyar bata tukuicin madara,wai shin a haka sukaci gaba da rainonta dama bayan ya gusa daga gidan?.

"Ka maida mata kayanta maina koda ba yau bane,kayi haquri da wautarta,duka canje canjen da kake gani na wani dan lokaci ne,tana girma gaba kadan zata qara hankali ta watsar da komai"

"Sai yaushe kenan aba?shekara ta sha daya cikin ta sha biyu sai yaushe hankalin da girman duka zasu zo?" Ya fadi can qasan ransa,amma a fili sai kawai ya gyada kai.

Daga aba har bibi babu wanda baisan halin maina din ba,farin sani suka yiwa halaye da dabi'arsa tun gidan babu wasu yaran bayan shi da abokan haihuwarsa da ya bawa 'yan shekaru kadan

"Qarasamin da briefcase dina ciki,ka gayawa mammanka na iso yanxu xan qaraso" aba din ya fada.

Tsam ya miqe yasa daya hannun nasa da babu komai a ciki ya dauki jakar. A nutse ya fara tattakawa yana barin qawataccen falon bibi din zuciyarsa a quntace.

Duk yadda yaso ya zabge bacin da ranshi da zuciyarsa tayi amma hakan ya gagara. Yayi zaune a falon ama yana games bisa wayarsa,duk da hakan ba dabi'arsa bace. Cikin masu aikin ama din daya ta ajjiye masa madarar nonon raqumi me kyau da gardi,kasancewar tana daya daga cikin abubuwan da yakeso tun daga quruciya,dayar kuma ta aje masa ruwa. Duk da miskilanci cikin jininsa yake amma sunyi mamakin yadda ya dauki tsahon lokaci bai taba komai a ciki ba. Ama tana sama batasan da zamansa ba don bai qarasa can ba. Bata sauko ba har sai da habee ta shaida mata an kammala komai tazo ta duba kaman yadda aka saba.

Zabgegiyar buzuwa kuma ba'abzinar cikin shadda 'yar mali dinkin boubou take saukowa daga stairs din,daga wuyanta zuwa hannunta dauke suke da warwaraye da sarqa da suka qara mata kyau cikar ado da kuma zati.

Ita dinma bata lura da shi ba sai data kammala saukowa. Shi din shine d'a na fari a wajenta,yana da wani irin kaso me yawa na soyayyar 'ya'yanta qwalli uku dake zuciyarta.

Kallon farko tayi masa tasan ranshi a bace yake. Bacin ransa bashi da dadi sam,tasan wannan,ba kuma kasafai yake nunawa ko bayyanawa ba. Muddin dai kuma cikin gidan aka bata masa rai tasan baya rasa nasaba da bangaren bibi,indai daga sashen bibi ne kuwa ba shakka sultana ce.

Har zatayi magana idanunta ya sauka kan briefcase din mijinta da kyakkyawar luggage dinsa,abinda yasa ta fasa magana akan wancan yanayin nasa

"Aba dinku ya dawo ne?" Ta jefa masa tambayar tana tsareshi da kallo. Gyara zamansa yayi cikin kujerar yana zama sosai,saidai bai kalleta ba don yasan idanunsa kadai zasu gaya mata ranshi a bace yake,indai ta fahimci hakan kuma yasan zaiyi wuya bata fahimci meye silar bacin ransa ba

"Ya dawo,ya shiga wajen bibi su gaisa"

"Shine zaka zube masa kaya a nan?"

"Na shigo ban sameki ba" ya fada shortly

"Me ya hana kasa ayimin magana ko ka haura da kanka?"

"Am sorry" ya fada da harshen turanci.

Idanunta ta dauke daga kansa tana tabe baki. Itakam abun yana mata dadi ta yadda yake fahimtar yadda yarinyar ke neman zama gagarau cikin gidan,kaf yaran gidan babu wanda ake fama da case dinsa irin sultana,ba wanda take shakka cikin gidan bare kuma na waje. Zamanka lafiya kada ka shiga lamarinta,saidai kuma duk da hakan zata iya bugar qirji tace tana cikin jerin sahun mutanen gidan da ko kada idanu da zummar rashin kunya bata iyayi mata bare wani abu na daban. Batasan me yasa ba,amma tafi alaqanta hakan da rashin janta a jiki da kuma rashin shiga shirginta da batayi.

Takawa tayi zuwa kitchen din tanason tabbatar da komai ya kammalu yadda takeso,wanda tana shiga din

Please Login or Register in order to submit comment