Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

princess ki gayamin gaskia matan Baba nawa ?
Kallon rainin wayo tayi tace " Allah ya sauwake ka zama yayana, mugu kawai, kuma babu ruwanka dako matan Baba nawa"
"Dan Allah ki gayamin badan hali naba" ya fadi amairace.
Kallonsa tayi taga lailai ba wasa tattare dashi, saidai tambayar tai mata bambarakwai.
Tace "matan Baba daya, itace Maihaifiyata Hajjo"
Hannuta ya riko, kaman zaiyi kuka yace "princess ke kanwata ce ta jini, baban mu daya dake"
Kallon rashin fahimta tamai, gabadaya yasata duhu.
Yacigaba "apart from Hajjo wace mace ce kika sani arayuwar Baba ?
Shuru tayi tanai tunani tasan dai babu ko wace mace daga Hajjo sai ita, can dai ta tuna da wani abu tace "akwai mace daya mai sunana, saidai bansanta, Baban bai taba xancen taba, abakin Hajjo nima nasanta, idan nayi laifin takance halin ku daya da mai sunanki, wataran na tambayi Baba wace ce mai sunana, cewa kadai yayi baya fatan nasanta".
Kur yayi mata da ido, yace "Ci gaba"
"Shikenan abunda nasani"
"Plz princess try to remember wani abu
Bata rai tayi hade da dauke kai, tace "ni ba princess bace kadai na kirana da hakan".
Juyo da fuskar ta yayi yace "to mi you're a princess, sunan Momcy gareki kinsan bazan iya fadin sunan kiba".
Gabanta ne ya fadi adalilin kamshi gaskia data fara ganowa cikin xancen sa, sau da dama takan ga kamarsu da Baba saidai bata taba kawo komai aranta ba, kallon sa take tana son tuno wani abu, azubure ta mike tana fadin "OmG".
mikewa yayi hade da riko ta, tuni jikinta yahau rawa.
Cikin muryar kuka tace "you're right, kai yayana ne, what am not sure shine ba Mom ta haifeka ba, i tink Hajjo ta haifeka"
Sabon rudani ya shiga, yasan dai Mom ce uwarsa, yace "miyasa kika ce haka
"Hajjo once told me bani ce yarta ta fari ba, tacemin akwai yayana saidai ya b'ata baa gansa ba" ta fadi cikin kuka, rungumota yayi yanai lallashin ta, abunda dama yake son sanin wato su sibling ne, it doesnt matter ko wace ta haifesa, abu daya yasani shine Mom ce amatsayin mahaifiyar sa.
Kuka sosai take cike da tashin hankalin ya haramta gareta, sai yanxu tagane ashe tun asalin soyyayar jini ce ta hadasu take ta shirme da haukan son shi.
"Princess" taji tlya kira sunanta cikin wata kasalalliyar voice.
Kasa amsa mai tayi, tajanye jikinta gefe, kusa da Inna ta zauna hade da daura kai kan cinyarta tanai kara sautin kukan.
Tausayin su sosai Inna taji, ita kanta sharar kwalla take, matsowo yayi daf da ita yace "Baba suna kauye, gobe ki shirya sai muje can, ai kinsan garin ko ?
Girziza kai tayi alamun a'a bata san garin ba, asalima ma ko sunan kauyan bata sani ba, Jigawa state dai tasan kauyan yake, tun bayan da tana karama suka bar garin bata kara zuwa ba, alokacin ganin take idan taje kauyen yar kauye zata zama, su Hajjo da hassan ke zuwa ita kuma ta zauna gida tare ba baba dasu Hussaini, sai wataran kuma Baba yaje shi daya.
Baiyi Mamaki da rashin sanin kauyan taba, yasan xaa rini balle alokacin kanta na hayaki ba yanxu data saduda ba.
"Gobe zamu koma gida kinji?
Mak'e kafada tayi "nikam bazan bika gidan matar nan ba"
Yasan Mom dinsa take nufi, saidai bazai barta a zaria ba, yace "kiyi hakuri muje, banason barayin nan na dazu su cafke ki"
Tsoro sosai taji dan tuni ta manta dasu, tace "gidan Baba xaka kaini"
"Ba kowa agidan, sabon gidan Mardiyya xan kaiki ki zauna"
Fir taki yadda, saida Inna tasa Baki bayan ya zayyane mata abunda ya faru dazu Sanna ta amince zata bishi.

**

Washe gari dakyar Batul ta yadda suka shiga mota, kukan rabuwa da Inna take sosai, lallashi sosai suka hau bata da sharadin zaina kawota ganin Inna.
Sun kama hanya titi tace ya tsaya, ba masu ya tsaya ta fito daga motan, daga can nesa da teburan sa ta tsaya tare da tura yaro ya kira mata shi, Ganinta yayi tsaye yayi azaman ajiye biredin dake hannusa ya nufota, sallama tamai hade da bashi hakurin tafiyar tazo a tsaitsaye, sosai Nafiu yaji ba dadi haka dai sukai sallama bayan ya bata numbar wayarsa akan cewan zata kirasa.
Duk akan idonsa, saidai ya tausaya mata da karewa Nafiu kallo, koshi da yake a Mamuda yafi sa kimtsi da wadata, dawowa motar tayi ta zauna hade da dauke kai gefe.
Yace "kinyi sabon Prince ashe ?
Kallan sa tayi hade da daure fuska "Naf'iu mijina na, the only prince da nake dashi kaine, my brother my prince"
Dariya yayi yace to miye na daurewa prince fuska.
"Ai dole na harrare ka, idan na tuna dukan da kamin i feel like slapping you"
"Bismilla" yafadi hade matso mata da fuska.
Hararar sa tayi.
"kasan dai bazan iya ba, amma zan gayawa Babana duk muguntan da kamin"
Kumatunta yaja yace.
"zaki sha wani dukan kenan"
Ture baki tayi tace "nifa ba ruwana dakai, kadaina min magana"
Toh princess you wish is my command" ya fadi.
Shuru duk sukayi kowa da abunda yake tsakawa game da haramtar Junan su, tsaki suka ja atare hade da kallon juna.
"miye" suka fadi atare.
"Bansani ba" Batul ta fadi adan tsiwace, kallon side mirrro tayi kaman xatayi kuka, ba karamin tausayawa kanta take ba, wani irin so da kaunar sa ke shigar ta, saidai kokarin yakacesa take a zuciyanta.
Haka suka karaso gidan ya fito hade da zagayawa gurinta.
"Fito" yace da ita ganin bata da alamu saukowa.
"Nifa bazan fito ba, kamanta agidan nan ka wulakantani ko tausayina baka jiba ka sakeni, nayi alkawrin bazan kara taka kafata cikin sa ba".
"Koh" ya fadi hade da kashe mata idanuwa.
Dauke kai tayi.
Cikin azama yasa hannu ya cicibota yana fadin "tunda bazaki takama daukar ki xanyi"
Ihu tayi
"Dan Allah ka sauke ni, wasa nake"
Bai kula taba ya direta apalo, Mardiyya ce ta fito daga daki fuskar ta dauke da fara'a tana fadin "Sweetie sannu da zuwa"
Yauwa" ya amsa mata.
Kallon Batul tayi tace "welcom back sister inlaw"
Dariya Batul tayi, wai ita inlaw, gaida ta tayi cikin girmamawa hade da jajan yaushe rabo, dakinta taja ta suka shiga suna hira.
Tuni dama yafita dauko mata kayanta, shigowo dasu yayi ya shigar mata dashi dakin.


****
Kwance take tana tunanin yadda rayuwarta ta kasance, su Baba kadai take son gani, ga Nafiu ya isheta zai turo abunda bai sani ba tuni aure ya fice mata arai.
Jin kaman Mardiyya na amai a toilet yasata mikewa hade da karasawa bakin kofar, "Sister Mardy lapia kuwa ?
Ido jajir ta kalli fuskar ta ta madubi, dakyar tace "babu komai, ki duba wardrobe dina daga gefe ki mikomin wani magani a kwali"
Okay" Batul ta fadi hade da dauko mata maganin, mika mata tayi ta kofar data bude ta miko hannu ta amsa.
Komawa gadon Batul tayi ta zauna ba tare data kawo komai aranta ba, "bari dai na leko yayana" ta fadi aranta, mikewa tayi ta nufa dakinsa hade da kwankwasawa, izini yayi mata ta shigo, zaune yake kan gado yana danna laptop din gabansa, jikinsa sanye da rigar bacci wando da riga mai kauri.
"Prince kunyi wayar da Baba ? Ta fadi hade da zama gefensa suna fuskartar juna.
Matsar da laptop din yayi gefe hade da dubanta, yace "kazamar, kowa na shirin bacci da sanya nitie, amma ke amtafa ce jikin ki"..
"Ina ruwanka toh, nidai gayamin koka kirasa"
"Layin Baba baya shiga"
Bata rai tayi, cikin turo baki tace
"Ni wlh na matsu nabar gidan nan"
Daga girasa yayi sama yace "kin daina sona huh ?
Dariya tayi
"Dama ai banasonka, yauwa kama tunamin, bani wayarka na kira saurayina"
"Mai shayin?
"Eh shi, kuma haka nake son abuna ehee" karasa maganar tayi cikin juya idanu.
Wayar ya mika mata, tuni ta rike numbar sa, sawa tayi hade da dailling, bugu daya ya dauka, nan suka fara hira cikin raha da annashuwa.
Kallonta yake kaman yayi hauka tsabar tsananin kishinta dayake ji, saidai dole ya kama kan sa danta haramta gareshi, jan laptop dinsa yayi yacigaba da harkar gabansa.
Mardiyya ce ta shigo dakin, jikinta sanye da nitie, ganin su zauna kan gadon yasata zauna gaban dressing mirror hade da dauka comb dake gurin tana tazar gashin kanta da batayi niyya ba.
Gama wayar tayi ta ajiye gefe tana fadin "Nafiu akwai kirki, My prince yaushe zaka kaini Zaria naje gaida Mamansa"
Bata rai yayi, bai dago ba yace "ba rana".
"Kama isa" ta fadin hade kaimai mitsini a hannu.
Daure fuska yayi ya kalleta, "kika mitsini " karashe maganar yayi hade da kawar da laptop din gefe,
Murguda baki tayi
"Eh din, ko zaka dakeni ne"
"Ba duka ba zagi" ya fadi hade da janyota, jakwulkuli yahau yi mata tana dariya tana fadin "dan Allah ka bari, Sister Mardy kinga shiko"
Murmushi Mardy tayi tana kallon su ta mirror, inama ace ita yake ma wasa haka da taji dadi.
Dakyar Batul ta mike tana dariya, tana fadin "Allah kuwa gobe saina rama"
Saurin sa hannu yayi zai rikota tuni ta fice daga dakin tanai ma Mardiyya Good nyt.
Dariya sosai yake, Mardiyya ta mike tahau gadon ta kwanta, "good nite" tace dashi.
"Nyt dear" ya fadi hade da tsayar da dariyan ya cigaba da danna dannan sa.
Yaken dayafi kuka ciwo tayi, hade da jan bargo ta rufe jikinta, tunani take, bawai sex dinne ya dame taba, asalima bata da karfin tab'uka komai, i dont care habit dayake nuna mata ke mugun sanyaya mata jiki, farkon auran yanai kokarin kulata amma yanxu duk ya wani birkice mata.



***


Sosai ran Mom ya bacci da rashin kamota dasu Roze basuyi ba, masifa sosai take zazzaga masu sunai bata hakuri, katse wayan tayi tanai kai komo adakin, ta tabbata My boy dinta ne ya dauke ta a motar, Amma ina ya kaita, tambayar da tama kanta, har gidan Baba ta tura basa nan sun tafi kauye, dole tadau mataki kafin Baban ya dawo.
Dabarar kirar Mardiyya ce ta fado mata, yarinyar tsokuwa ce, tasan tana iya gayamata ko suna tare da princess, wayar ta danna tahau dialling numbar ta.
Kowa ya tashi banda Batul dake kwance tana bacci, karar wayar Mardiyya dake kusa da itane ta farkar da ita, daukar wayar tayi taga number ce ba suna, ajiye wayar tayi ta cigaba da baccin ta, kusan sau biyar wayar na ruri, cike da haushi tace bari tacewa mai kira bata kusa, dauka tayi hade da dasawa akuune.
"Hello, mai wayar bata kusa" ta fadi tanai hamma.
Daga can bangarean Mom tace "wake magana".
Zuciya daya batul tace "fatima ce kanwar mijinta, xan gayamata kun bugo"
Sosai Mom taji dadin haka, faduwa tazo daidai da zama, tace "Batul ce ?
Ware idanu Batul tayi sakamakon dago muryar mom da tayi.
Baki na rawa tace "itace" mugun tsoron Mom take.
"Yar banxa yarinya, ki bude kunnen ki dakyau ki saurari abunda xance"..
Cike da kidema Batul ta tashi zaune.
Mom tacigaba "naso rabaki da d'ana hakan bai yuyyba, dayake ke mayya ce koh ?
Girgiza kai kawai Batul tayi, tuni hawaye yafara wanke mata fuska.
"Na baki nan da kwana biyar kiyi convincing Rasheed ya daura miki aure dakoma waye, idan ma baki da mashishini xan turo mai gyaramin mota na ya kwashe ki"
Kuka sosai Batul ta fashe dashi, cikin rawar murya tace "Mom dan Allah kiyi hakuri, baxan iya aure yanxu ba"
Daga murya Mom tayi cikin kuluwa tace "wato kina jiran Ubanki ya dawo ya fada miki akwai aure tsakanin ku ko, to baki isa ba, aure kuma dole ya daure miki in 5 day if not, har can kauyen da ubanki da uwarki Ikilima suke zan tura amasu yanga rago, harma da kannanki hassan da Hussaini, Make sure kuma Rasheed karya san abunda na fadi maki" katse wayan Mom tayi..
Gabanta ne ya fadi tsoro, da firgici suka dabaibaye mata zuciya, cilli tayi da wayan ayayinda kukan ta ya tsanan ta yankan rago kadai take maimaitawa azuciyar ta, sai kuma inda Mom ke fadin akwai aure tsakanin su.
shin dama akwai aure tsakanin su ? Amma miyasa Mom zata mai karyan Ubansa ubanane, kodai kanin baba ne Ubansa, duk azuciya take fadin hakan cikin tsananin gigita da tashin hankali.
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
Rubutawa
Xarah Bukar

®NWA

xarahbukar.wordpress.com


*Wannan Shafin nakune TeamBatul, bukin budiri on point* 🤸‍♂🤸‍♂🤸‍♂


74

Kuka take sosai cikin tsananin tashin hankalin da bata tab'a fuskanta arayuwarta ba. Turo kofar dakin yayi yana fadin, "Princess baza ki fito breakfast.." Makale wa kalaman sa sukayi a mak'o shinsa ba tare daya ida ba sakamakon ganin dayay mata.
Sauri goge hawayan fuskanta ta hau yi amma tuni yagani, kasa daurewa tayi da boye damuwar ta karasawa gabansa tayi hade da fadawa jikinsa tanai kuka mai tsuma zuciya.
Cike da tashin hankali ya rike to suka zauna kan gadon,
"Princess mike damunki, waya tab'amin ke" ya fada yanai kokari dago da fuskarta dake boye cikin kirjinsa.
Kuka take tana tuna kashedin da Mom tayi mata, mudin idan tafadi ma Rasheed bazata barta lafiya ba, saurin tsayar da kuka tayi, ahankali ta dago da fuskarta suna fuskantar juna.
Baki na rawa tace "tsoro nake ji"
"Tsoron miye ? Ya fada yana kawar da gashin kanta dake neman tsone mata idanu.
Sabon kuka ta fashe dashi tana fadin,
"Mutanan nan su nake gani a mafarki zasu kamani"
Hannu yakai bayanta yana lallashin ta "Plz dont cry, its just a dream, babu wanda zai kamaki"
Kai kawai ta daga mai, lalashin ta sosai yahau yi saida yaga tabar kuka sannan ya lallabata ta shiga wanka, Parlour ya koma ya cigaba da cin breakfast dinsa akan dinning, tuni Mardiyya ta kammala cin nata abinci, zaune take kan kujerar apalo tana kallon Tv.
Cikin bakar abaya Batul ta fito, bata karasa Dinning ba ta zauna kan kujera hade da gaida Mardiyya.
"princess baza ki ci abinci ba" Mardiyya ta fadi ganin bata da niyya tashi.
Yaken dole Batul tayi, aranta tana fadin ashe da ex kishiyata nake zaune ban sani ba, afili tace "zanci, xuwa anjima"
Kafin mardiyya takai ga bata amsa ya mike daga ina yake zaune yana fadin "Diyyah dauko min abincin ta" karaso yayi ya zauna kusa da Batul.
Abincin Mardiyya ta dauko a plate ta mikemai hade da mango juice cikin glass cup.
"Tnx dear" ya fadi hade da amsa.
Kallon Batul yayi da tuni tafara yamutse fuska, diba yayi a spoon akai bakinta, dauke kai tayi alamun bazata ciba.
"Zan dauko Bulala fah "ya fadi hade da daure fuska.
Tsoron duka taji, ba shiri ta jiyo yanai feeding dinta tanai zuba mai shagwaba, dakyar tasamu ta iya cin rabi tace ta koshi, juice din yabata tasha sanna ta langwab'o jikinsa.
"Prince yaushe zamu je zaria" ta fadi kaman zatai kuka.
Cheeks dinta yadan ja cikin salon wasa yace "kin fiya son yawo, gobe if am less bizy sai muje"
Kare shigewa jikinsa tayi hade dayin Lamo batare data ce uffan ba, runtse idanu tayi tana sak'a da warwaran yadda zatai convincing dinsa.
Shuru dayaji yasa ya dubi Mardiyya da gabadaya hankalinta na kan Tv, yace "Diyya dauko min Car key dina adaki"
Ba musu ta mike ta shiga dakin ta dauko.
Mikewa yayi ahankali hade da kwantar da Batul kan kujerar, amsa key din yayi yace da ita ya tafi office sannan ya fice.
Plate dake gurin ta dauka ta nufi Kitchen ajiyewa, mikewa zaune Batul tayi hade da dafe kanta, duniyar gaban daya tai mata zafi ji take tamkar ta shige karkarshi kasa, jiki sanyaye ta mike tsaye ta fada dakinsa, wani irin sanyayyar kamshi da sanyi ne suka bigi hancinta, kwanciya tayi kan gadon cike da tausayin kanta.
Fitowa Mardiyya tayi daga kitchen ganin Batul bata palon yasa tayi tunanin ko ta shiga dakinta, zuciya daya ta shiga dakinsa da niyya kwanciya ganin Batul kwance kan gado yasa tayi azama juyowa ba tare data karasa shiga ba, Dakinta ta nufa ta zauna kan gado hade da daukar wayarta, dialing nambar Hajiya Safara tayi, ringing daya, biyu ta dauka daga can bangaran.
"Hello, Umma ina Kwana" ta fadi cikin yanayin ba yabo ba fallasa.
"Lafiya lau Mardy, ya kuke, fatan dai shegia matar nan bata tsangwame kiba ? Acewar Hajiya Safara
Takaici ne ya kama Mardiyya tace "plz Umma ki bar fadin haka, kinsan dai maman mijina ce kuma she deserve some respect"
Tsaki Hajiya safara taja.
"Toh uwar son Miji, sai kiyi ai, ya jikin naki ?
"Da sauki, nasha magani"
"Idan kin shirya zuwa Asbiti kimin magana sai muje" acewar Umma.
"Toh Umma" Mardiyya ta fadi, hira kadan suka dan tab'a sannan ta katse.
Ajiyar zuciya ta sauke tana xancen zuci, "am sorry Umma, wannan karan na sab'a maganar ki, kusan shekara daya ina zuwa asibiti ba tare da saninki" tunani tahau yi hawaye na d'isa bisa fuskarta.


Bai wuce office ba ya nufa gidan Mom, Shingide ya isketa bisa kujera apalo tana shan fruit, Altine na daga gefe tanai mata tausa, gaida ta yayi aladabce.
Bata amsa gaisuwa ba tace "ina fatan dai ka dawo ne da zama".
Murmushi yayi hade da zama, yace "Mom yanxu abunda kikayi kin kyauta"
Gabanta ne ya fadi, tayi yunkuri gyara Zama, atunaninta Batul ta fadi mai threat dinta.
Yacigaba "tunda kika tura thugs su kamota, ta fita hayyacinta da mugayan mafarkai"
Ware idanu tayi tanai mai masa kallon rashin fahimta, dukda ta gano inda xancensa ya dosa.
"Mom dont give me that look, nasan kinsan komai, kece kika turo kattin nan"
Daure fuska tayi tace
"Of course nina tura, nayi hakan ne danna baka ita as surprise, naga ka jima kana nemanta baka ganta ba, idan baka godemin ba ai bazaka zageni ba"
Nisawa yayi yace "thanks Mom, ai bansan you were trying to help me find her ba".
Murmushin dabai kai zuci ba Mom tayi tace "Never mind, nayi hakanne kawai amatsayin she is a daughter to me, kuma kanwarka ta jini, she deserve more from me"
Sosai Rasheed yaji dadi da kulawan Mom, godiya sosai yayi mata, sun jima suna hira daga bisa ya fice zuwa office.

Yunin ranar haka Batul ta kasance jiki sanyaye, bayan ya dawo ko hirar kirki batai dashi ba ta lallaba ta kwanta bayan sallar isha'i, tuni Bacci yayi awo gaba da ita.

***
Washe gari, Da fara'ar Batul ta tashi, karfe sha daya na rana ta shirya da temakon Mardiyya cikin atampa riga da skirt, farin ciki sosai take zataje Zaria gurin inlaws dinta.
Palo ta fito ta iske shi kwance kan kujera, jikinsa sanye da gajerar wando da singlet, wayarsa rike a hannusa yana latsawa, babu alamun shirin zuwa Zaria tattare dashi.
Murtuke fuska tayi ta tsaya gabansa.
"Na shirya fah".
"Sannu da shiri" ya fadi yana cigaba da danna wayar ba tare daya dube taba.
Cize labban ta tayi, idan bata lallaba saba shareta xaiyi, gashi kuma kwana hudu ya rage mata, yazama dole taje ta lallaba Nafiu ya temaka ya aureta.
Tsugunnawa tayi gabansa, hade da kashe murya tace "My prince dan Allah tashi muje" karashe maganar tayi hade da kai hannuta bisa soft hair din kansa tana shafarmai dasu baya.
Ajiye wayar yayi yana dubanta, ba karamin kyau tayi masa ba, murmushin dabaiyi niyya ba ta subuce masa.
"Plz" ta fadi cikin kasalalliyar Murya.
Bata rai yayi yace "nagaji bazan iya tashi ba"
Mikewa tayi da azama hade da riko hannusa dan ya mike tsaye, "plz yayana tashi muje" kaman zatayi kuka ta karashe maganar.
Mikewa yayi yana fadin
"Kin fiya naci"
"Eh din",ta fadi hade da jansa zuwa daki, toilet ta turasa tana fadin "yi wanka, bara na fiddo ma kayan da zaka sa"
Closet dinsa ta nufa ta fiddo mai kananu kaya jean da short sleeve tshirt, rikosu tayi tana shakar kamshin su, ajiyewa zatayi kan gado Mardiyya ta shigo rike da kaskon tiraran wuta.
"Na miye kayan nan" ta fadi tana kallon Batul, fuskar ta dauke da fara'ar.
Ida ajiye kayan tayi tana fadin "Kayan da prince zai sane, shine na fiddo mai"
Dariya Mardiyya tayi hade da ajiye kaskon, kayan ta dauka tana fadin "Sweetie bayasa irin kayan nan, by this time" karasawa tayi closet din hade da maida kayan ta ciro wasu traditional outfit marar nauyi, ajiyemai kayan tayi kan gado hade da kallon Batul da tuni jikinta yayi sanyi, tace
"Thanks sister inlaw, kije parlour ki jira shi, karki damu xanyi making sure bai bata maki lokaci ba"
Kai kadai Batul ta daga, bata iya cewa uffan ba ta fito palo ta zauna kaman zatayi kuka cike da tsananin kishin dake kokarin fasa mata zuciya.
Kara gyara dakin Mardiyya tahau yi, fitowa yayi daure da towel yanai goge jiki, karasawa yayi inda yaga kayan a ajiye, Murmushi yayi, aranshi yana jin dadin yadda tasan taste dinsa,
Duk akan Idon Mardiyya, tasan sarai ya dauka Batul ce ta fiddo mai kayan, batace komai ba, taci gaba da adjusting pilo acikin case dinsa.
Shiryawa yayi tsaf cikin kayan, fita Palo xaiyi Mardiyya tayi saurin bin bayasan tana fadin "Sweetie kayi kyau sosai"..
Murmushi yake cikin jin dadi yace "Thank dear"
Kallo daya tayi masu ta tashi tabar palo, ta fita gurin Motar ta tsaya, wani irin haushi take ji na ba gaira ba
dalili.
Har bakin Motar Mardiyya ta rakosa tanai masu Allah ya kiyaye hanya.
Yaken dole Batul tayi tace "Sister Mardy saimun dawo" hade da fadawa cikin motar.
Amsata Mardiyya tayi fuskarta dauke da Murmushi, saida taga sunja sannan ta koma cikin gidan.

Tuki yake cikin hankalta da kwarewa harya iso Zaria, babu mai magana da junansu, kallonta yayi yaga yadda ta daure fuska, kumatun duk sun kumburo, kiris ya rage ta fashe da kuka, Dariya sosai tabashi, dakewa yayi yace "Princess kinfi kyau when you smile"
Bata kallesa tace
"Babu ruwanka dani"
Dariyar daya kasa barin aransa yahau yi, yace "yayanki kike cewa babu ruwank dashi ?
Ya gama kuleta ba kadan ba, ita tana kokarin boye sonshi aranta, amma shi kallon kanwa ta jini yake mata, bata iya basa amsa ba tace "gidan inlaws dina zaka ajiye ni, daga kwanar gidan Inna sai tasu"
Daure fuska yayi
"Wato kinma san gidan har zuwa kike kenan ?
Kaman zatayi kuka ta dubesa tace "ban taba zuwa ba, Nafiu ya min kwatancen gidan"
Baice uffan ba har suka shigo layin, da hannu tamai nuni da gidan, parking yayi kafin ya karasa gurin, kallon gini yake wanda kiris ya rage ya rushe tsabar tsufan sa.
Maido da dubansa yayi gareta ganin bata da shirin sauka asalima k'asa idanuwanta ke kallo tana zubda hawaye.
"Miye kuma na kuka" ya fadi cikin rashin damuwa da yanayinta.
Kasa magana tayi banda kukan daya sarke ta, sosai takeyi harda shesheka, bai kuma cewa uffan ba banda kafeta da ido dayayi tanai kukan ta.
Dakatar da kukan tayi tahau kokarin bude motar zata fita taji ya riko hannuta, wani irin yanayin taji ta shiga marar mitsaltuwa, juyo da fuskanta tayi suna duban juna cike da so da kauna.
Handkerchief ya cusa mata a hannu yana fadin "ki sharar hawayanki, banaso inlaws dinki su ganki haka"
Janye hannuta tayi tace "thank you"
Yace "In 30 minute xan dawo daukar ki"
Bata iya basa amsa ba ta fice daga motan. Afusace yaja motar yabar gurin, bin kurar daya had"a tayi da kallo.
Bakin kofar gidan ta tsaya hade da sallama cikin sanyayyar Murya, daga ciki aka amsa hade da mata iso.
Wata dattijuwa tagani tsaye tana surfen gero a turmi, daga gefe kuma yar budurwa ke tankade da reraya.
Risinawa tayi tana fadin "Ina wunin ku"
Dattijuwa mai suna Goggo tace "lapia yammata, dadddawa da kuka zaki siya?.
Kafin tayi magana yarinya mai suna Naja'atu tamike tsaye tana fadin "Goggo bara na leka waje ko budurwar Ya Nafiu ta iso" da azama ta rugu waje.
Bata rai Goggo tayi ganin Batul

Please Login or Register in order to submit comment