Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga ihu yama tsukeken bakinta cafka, cikin salon mugunta yahau tsotsan lebbenta, tuni tara fita hayyacinta, saida yaga ta tsumu sannan ya turewa iya karfin sa yanai kai mata mugun kallo, jajir fuskan ta yayi tsabar azaba, kuka ta fashe dashi dan ba karamin tsorata tayi dashi ba.
Cikin wata kasalalliyar murya yace "did you enjoy it?.
Harara takai mai, banxa dan iskaa" bata karasa ba ya wanke fuskar ta da lafiyayyar mari da saida taga wuta ya wulka,
Dan kara tasaki ahankali hade da dafe kunci ta da tunda uwarta ta haihefa babu namiji daya taba mata haka, kallonsa kawai take afirgice, da gudu ta fada toilet tana tsuga kuka, ko amarfiki batayi tunanin Rmd dinta xai iya mugunta haka ba, asalima batazo gidan dan yana harassing dinta ba tazo ne kawai yasota amma shi yanai bata kallon yar iskan budurwar shi, kuka kawai take tana sumbatu sai yau taga ranar Mamuda da komin rashin Mutunci da takemai bai taba tanka taba, shine yau kalma biyu kacal sun caza mata mari.

Baibi bayanta ba banda Murmushi daya keyi, duk da a mugunta yayi kissing dinta he really enjoys it, ficewa yayi daga dakin ya koma dakinsa, tsaye yaga Mardiyya tanai kai komo a tsakiyan dakin, tana ganinsa ta karaso garesa, "Sweetie ka dade.." Ta fadi, bai amsa taba yakai bakinsa cikin nata, suka fara kissing juna passionately.


***
Bayan kwana Uku

Tun randa hakan ta faru Batul tahau wasan boya dashi, Duk wata hanya da zata tsada ta dashi bata bi, koda wasa bata zaman dakinta gudun karya shigo ya farmata, ako yaushe gurin Mardiyya take makalewa danta lura ko kallonta bayayi idan suna tare, shi dinma yayi busy, aiyuka sosai ke gabansa, wuni yake a office dinsa na gidan yana danne danne computers sa, ganin haka yasa Batul sakin jikinta da kare zagewa akan ita princess ce.
Da yamma likis, zaune take dakin Mardiyya tanai karambani gyarawa kayan shafanta dake kan dressin mirror zama, Mardiyya na kan gado kwance tana latsar wayarta, jifa jifa kuma suma juna magana.
Roban ban kitso Batul ta daga tana fadin "Sister Mardy kinga wannan ya kare"
Dagowa Mardiyya tayi tace "tun jiya nace Altine ta wulla trash, ashe bata dauka ba"
Gefe Batul ta ajiye robon tace "ni gobe saloon nake son zuwa"
"Ba matsala, Allah ya kaimu goben sai muje"
Dadi sosai Batul taji, turowar kofar dakin ya katse mata hanzari, shigowa yayi rike da wasu takardu a hannusa, nan take jiki Batul yahau bari, matsawa jikin bango tayi ta lafe, ko kallonta bai ba ya karasa gurin Mardiyya da tuni ta mike zaune.
"Diyyah, ga wannnan kije office kimin compiling dinsu cikin data base na marketing department" ya fadi yana mika mata papers din
Karba tayi tana fadin "right away" mikewa tsaye tayi da azama tana cewa batul "princess ina zuwa, duty calls" sannan ta fice ya mara mata baya.

Ajiyar zuciya na relief ta sauke, gadon ta karasa da niyya zama taji ya banko kofar ya shigo, atsorace ta daskarewa agurin, karasowa gabanta yayi yanai mata shuumin kallon sanna yakai hannusa bisa fuskarta, "princess baki iya gaisuwa ba ?
Daburcewa tayi, tahau fadin "ina kwana my Prince" baki na rawa ta karashe maganar.
"Ina kwana by this time" ya fadi hade da janyota jikinsa, kame jikinta tayi tsam dan bataso irin kallon dayake mata.
"Princess" ya kira sunanta cikin wata kasalalliyar murya daya kashe mata jiki, kallonsa tayi tanai kokarin jan baya, yayi saurin tarota, boobs dinta dake neman fasowa daga cikin yar karamar riganta yake kalla, da sauri tayi azaman sa hannu ta tokare, cire hannun yayi yace "bakya so na kalli abuna".
Gutun tsaki taja cikin kaguwa da kallon dayake mata,
"Ni kike ma tsaki ? Ya tambayeta
Banza tayi dashi hade da dauke kai, matse ta gam yayi yahau kissing ko ina na fuska ta, kokarin karkato da kanta yayi dan kissing lips dinta, fir taki yadda dan ba karamin haushi yake bata ba, murmushi mugunta ya saki yakaima boobs dinta wani irin raruma data saki karamar ihu, bata ankara ba sai ganin tayi yana latsar boobs din hade da kokarin cire mata riga.
Hannusa tayi saurin rikewa, "Dan Allah kayi hakuri, banaso"
Bai kulata ba saima kara cigaba da abunda yake, kuka ta fashe, "Dn Allah kabari, akwai aure akaina"
Sakin ta yayi yanai mata mugun kallo, sanna ya shako wuyanta, "yaushe kikai aure, wa kika aura?
Cike da karaji da zare idanuwan sa da suka sauya launi zuwa ja yake maganar.
Akideme Batul ke kallonsa ba tare da kwakwaran motsi ba, ita kanta batasan ya ankai tace akwai aure akanta ba.
Baki na rawa tace "bansani ba, nadai san ina da aure, dan Allah kabari"
Fuska daure yace "Ni zaki rainawa wayo, gayamin wa kika aure, waye mijin"
Shuru tayi banda matsar kwalla da take, shakar da yayi ma wuyarta ma ya isheta.
"Yau zaki san baa raina min wayo" fizgo ta yayi suka fada toilet dake dakin,, duk ta furgici tarasa uwar mai xai mata, bowl mai fadin dake cikin jacuzzi ya kunna ruwan sanyi ciki sannan ya kashe bayan ya cika.
Kallonta yayi yace "yau dolene ki gayamin waye mijinki" wuyarta ya damko gashin kanta ya zubo dan tuni hular kanta ya fice, kallo yalwan gashi yayi ya dauke kai, tuni Batul ta rikice atunaninta wanka xai mata sai kuma taga ya tsugunar da ita hade da tura kanta cikin ruwar, ihu ta saki bayan ya ciro kanta daka cikin ruwan
"Waye mijinki" ya fadi fuska ba annuri.
Iya galabaita Batul takai, ga ruwan bai dan banxa sanyi, tsabar mugunta sai kanta yayi sakanni yake fidda ta.
"Nakasa numfashi, dan Allah karka kashe ni" ta fada, numfashi sama sama, ido jajir.
Tambayar ta ya kuma yi, tayi shuru ba amsa kara danna kanta yayi cikin ruwan sannan ya fiddo ta.
Kuka sosai ta fashe dashi "kayi hakuri, nakasa tuna waye mijin"
Murmushin mugunta ya saki, ya kuma danna fuska ta ciki, kusan sai hudu yayi bata da niyya gayamai waye mijinta, cikin fusata ya ture ta, tsantsin ruwan dake gurin ya kwasheta ta fadi kasa, atake bakinta ya fashe, jini yahau zulala, ko kallonta bai yiba yayi hanyar ficewa sai kuma ya dawo ya damki wiyanta,
"na baki nan da 24 hours idan baki gayamin waye mijinki ba, abunda yafi wannan zan miki" take yatsu kafarta yayi ya fice afusace.
"Innalilahi wa inna'laihi rajun" kadai Batul ke ambata, cike muryar kuka mai tsuma zuciya, agabadaya jikin ta radadi yake mata, kanta wani irin azababban ciwo yake mata, kuka kadai take tana dana sanin kawo kanta gidan Rmd dayake barazanar kasheta, da yanxu tana gidan Mamuda bawan Allah hankalinta kwace ba tare da yayi gigin taba lafiyar jikinta ba, sai yanxu ta tabbarta kauyanta shine birninta, talaucinta shine kwaciyar hankalin ta, ina amfanin an wadata ta da komai amma
ba kwashiyar hankali.
24 hours daya bata kadai ya kara firgita ta, mikewa tayi tsaye dakyar tana fadin "gidannan ba gidan zamana bane, mundin na kara kwana daya saidai afita da gawata" fitowa tayi daga dakin tayi hanyar stairs ba tare data leka ko dakinta ba, gudu gudu sauri sauri ta fice waje ba tare da kowa ya ganta ba, tsakanin cikin gidan da gate ba karamin nisa ne dashi ba haka ta taka ta karasa, securities hudu sanye da uniform tagani, harda mata biyu cikin su, ko kallonsu batai ba tahau kokarin bude gate din, kallota sukayi sukace
"Baa fita saida izinin Oga
"Ni ba yar gidan nan bace, ku bani guri" tafadi tana harara su.
Damko hannuta mata biyun sukayi suna fadin "oga yace karmu bari ki fita"
Hankali batul atashe tahau masu magiyan su barta, ko kallonta basui ba suka cicibeta zuwa cikin gidan, direct inda suka hango Rmd tsaye suka kaita, wani wawam mari ya tsakar mata afuska, yace "My princess baa fita a gidan nan sai da izinina" .
"Ba fita xanyi" ta fadi, fuska jajir ko ganin haske batayi sosai tsabar azaba.
Cema security din yayi su kaita up stairs inda dakinta yake, sannan ya kalleta yace "23 hours 30 minute remaining...."
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
Rubutawa
Xarah Bukar

®NWA

xarahbukar.wordpress.com

56 - 60

Zazzab'i mai zafin gaske ta kwana dashi ba tare da runtsawar kirki ba, har kusan 11 tana lullub'e cikin bargo bata sauko breakfast ba.

Turo kofar dakin Mardiyya tayi hade da sallamA, can ta hango ta dunk'ule karshen gado tana freezing, karasawa bakin gado tayi da axama ta yane bargon.
"Princess baki da lafiya".
Hannu takai bisa jikinta, zafi rau taji tayi azaman cire hannun.
kuka Batul ta fashe dashi ta riko hannuta, "Sister Mardy dan Allah ki temakeni nabar gidan"
"Haba princes keda bakya cikin hankalinki taya zaki ce haka, kiyi haukari har memories dinki ya dawo nayi alkawarin maida ki masarautar ki dakaina"
Kuka sosai Ta kuma fashewa dashii, tayi dana sanin ce masu tayi loosing memories gashi tana son barin gidan sunki yadda, lallashi da ban baki Mardiyya tahau bata, dakyar tabar kuka bayan Mardiyya ta ce mata zata kaita asibiti, dadi taji aranta tafara tunanin yadda zata tsere daga can.

Zaune yake parlour yana sipping coffe dake rike hannusa cikin mug, Tv dake kunne yake kallan labaran duniya. Cikin takun sauri mai dauke da tashin hankali ta sauko, dayan daga cikin kujerar ta nufa lalubar mukullin motar ta data cilla gurin.
"sweetie princess bata jin dadi, zan kaita asibiti" ta fadi tanai cigaba da laluban ta, ganin mukulli tayi ta juyo tana fadin,
"barin dauko ta" taku daya biyu tayi da niyyan haurawa saman taji ya kira sunan ta, tsayawa tayi tanai kallonsa, bai kalleta taba, fuskar sa na bisa Tv yace "babu asibitin da zakuje"
"Sweetie dan Allah ka bari muje, she needs a Doctor"
"Diyyah" ya kira sunanta a tsawace, kallonta yayi fuska daure.
"naje baza kuba, koma ki zauna"

Tuni Mardiyya ta tsorata, ya rikide mata ainihin Mr Rasheed din data sani, "Adalilin Mene (Ummi Jay) zai mata tsawa" ta fadi axuciyanta, jiki ba laka ta taka kujerar dayake zaune ta zauna gefe dashi adan rukube.

Wayarsa ya fiddo ya kira Doctor Ramalurv sukayi magana sannan ya katse.

Shuru ne ya ratsa sakanin su, kowa da abunda yake sakawa a zuciyarsa, bayan minti sha biyar Doctor Ramalurv ta karaso gidan, gaisawa sukayi ya mike rakata dakin Batul.

Kwance take tanai jiran shigowar Mardiyya, ganinsa ya banko kofar dakin yasa ta razane
"Shigo Dr" yace da Ramalurv da take biye dashi abaya.
Saurin rufe idanu tayi kaman mai bAcci amma tuni yasan ba baccin take ba, taba jikinta da aune aune Doctor tayi sannan tA rubuta mata magungunan bukata ta mika mai takarda, tana fadin "Mura ya haddasa mata zazzabi, for now dole ta kiyaye amfani da ruwan sanyi"
"Okay" ya fadi hade da godiya, bai karbi takarda ba yace ta baiya mardiyya dake kasa taje ta siyo, sallama sukayi ta sauka kasa.

Mardiyya bata kawo komai aranta ba ta amshi takardar ta fice zuwa pharmacy da azama.

Jin alamun shuru yasa Batul bude idanu, karaf sukayi ido hudu dashi, tsaye yake yana kallon ta hannuwansa biyu bisa kirjinsa yayi folding.
Murya can kasa yace "princess ya jikin ki ?
Karashe magana yayi hade da zama kan gadon, fuskokin su na fuskantar juna. Janye jikinta tayi gefe tana kara lullubewa, ba karamin shayinsa take yi ba, sai kace bashi yajaza mata zazzabin ba.
"Da sauki" ta amsa mai cikin murya kaman zatayi kuka.
Hannu yasa ya cire bargon, yarage daka ita sai karamin nitie dake jikinta, saurin takurewa tayi gurin guda hade da kawar dakai gefe, tsoron ta daya karya dawo mata da batun tambayarsa, adiriganta awanni sha hudu suka rage ta bashi amsa, saidai har yanxu batasan abunda zata fadi maiba.
"Tashi kiyi wanka" yace ita
Raurau tayi da idanu "Sanyi nake ji"
Cikin zafin nama ya mike hade da sunkutar ta zuwa toilet, kuka ta fashe dashi tanai rokansa, atunanin ta abunda yay mata jiya zai sake, dire ta yayi, yahada warm toilet cikin jacuzzi.
Kallanta yayi yace
"Baza ki shiga ba saina turaka ciki"
"Zan shiga" ta fadi hade da rabawa ta gabansa, taba ruwan tayi taji da dumi sannan ta kalle sa "dan Allah ka fita"
Harara yakai mata "kina gamawa make sure kizo down stairs breakfast"
Kai da girgiza alaman eh, ya juya ya fice daga dakin.

Yunin ranar yar gata ta zama daga shi har Mardiyya lallbata suke, duk abu da takeso shi sukeyi, kokarin kame kanta kadai take gudu kar gata yayi yawa tafara wuce gona da iri, atleast Rasheed ya kyaleta bai kuma mata batun komai, opportunity kadai take nema ta fice tabar gidan saidai ta lura babu daman hakan saboda tight security na gidan, babban tashin hankali shine idan ta koma gida mai zata ce da Mamuda da Inna, dan kuwa karyarta takare, asalima karya ce ta sanya ta cikin ukubar da take ciki ayanxu.

Washe gari, guraran biyu na ranar taga anata dafe dafe da gyaran ko ina na gidan,
Mardiyya sai up and down take tana aikace aikace sai kusan 5 taga sun kammala.
Mamaki kecin ta, tarasa wanda zata tambaya what the occasion is all about, tana daga parlour ta k'wallawa Altine, da azama tazo hade da dukawa kasa.
"Altine yimin tausa" ta fadi.
"Toh ranki shi dade" Altine ta fada tana washe baki, tausar tahau yi mata cikin kwarewa da hazaka.
Tambayar ta takeso yi amma ta kasa, dakyar dai tasamu courage din tambayar ta ko bakine zasu zo.
Kara washe Baki Altine tayi tace "Momy ce xata dawo, mahaifiyar mai gidan"
Ware idanu Batul tayi, gabanta na dukan Uku uku, fatan ta daya Allah yasa matar mai saukin kaice, indai ta biyo danta a mugunta lailai kuwa kashin ta ya bushe.



To be Continued.........
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
Rubutawa
Xarah Bukar

®NWA

xarahbukar.wordpress.com

61 - 62


K'arfe shida motar Mom ta diran agidan, ajiyar zuciya mai dauke da relief ta sauke tana shakar sanyayyiyar iskar dake bazama a farfajiyan gidan. Cikin takun takama ta k'arasa takawa bakin kofar parlour gidan cike da mamakin Altine batazo tarbar taba
Turo kofar palon tayi ta kusa ciki kai batare da tayi sallama ba.
"Altine" ta kira sunanta ganin ta duk'e tanai ma Batul tausa, duk atunanin Mom mardiyya ke kwance gurin, ganin Mardiyya na sauko wa daga stairs fuska dauke da fara'ar yasa ta karasa shiga cikin palon.
"Sannu da zuwa Mom" Mardiyya ta fadi
Yauwa" Mom ta amsa cikin k'aguwa da ganin waye hakinci kan kujerar palon gidanta.
"Bak'uwa mukayi" Ta fadi tanai kallon Batul dake kokarin mikewa zauna tana sosa idanu, dan tuni bacci ya kwashe ta jin surutu yasata farkawa.
Ido hudu sukayi tayi azaman mikewa tsaye adan firgice.
"Ina wuni, sannu da zuwa" ta fada murya sarke, gabanta na faduwa sakamakon gane Mom da tayi wace ce ta k'irata da almajira a fountain Mansion.
Kallon wulakanci Mom ke mata, aranta tanai fadin "wanne ne karo na uku da take ganin yarinyar nan, amma miya kawo ta gidan nan"
Afili tace "wace ke, daga ina, gurin wa kika zo" atare ta jeho mata tambayoyin, fuska ba annuri.
Caraf Mardiyya ta amshe dacewa " tayi loosing memories dinta, abu daya mukasani game da ita shine she is a princess"
Murmushin dabai kai zuci ba ba Mom tayi, tace "Princess my foot, dayake baku da hankali wannan tayi kaman da princess, she looks more like a Gold digger"
Shuru Batul tayi kaman ruwa ya cinyeta, fisgo ta Mom tayi da karfin gaske ta rike ta kam, cikin karaji da zare idanu tace
"Nawa kikeso nabaki ki fita daga rayuwar mu, kinsan dai nasanki, duk wani cunning moves dinki bazai yi aiki akai naba"
Fashewa da kuka Batul tayi dan ba karamin riko tayi mata ba, ita ba kudi takeso ba asalima idan zaa bude mata gate fecewa zatayi, saidai mamaki take yadda Mom ta ganeta so easily, dan ko ranar dinner ba wani kallon k'urilla tayi mata ba. Matsowa Mardiyya tayi ta cire hannun ta daga mugun riko datai mata, tace "plz Mom kiyi hakuri ki barta, bata da isheshen lapia, ina kika santa ?
Nisawa Mom tayi.
"bansanta ba, all i know is saita bar gidan nan yanxu" ta fadi hade da kara riko hannuta, janta tayi bakin kofar palon hade da hankada ta waje ta fada jikinsa dayake kokarin shigowa.
"Mom"ya kira sunanta cike da baccun rai, yasan zaa rina yasa yaketa sauri danya iso gidan unfortunately traffic jam ya tsayar shi.
"For goodness sake Mom mai tayi miki daga zuwanki? Ya fadi yanai rike da ita suka shigo ciki, kuka sosai Batul take, taga samu taga rashin da tuni ta ware.
Dogon surutune bazata iya ba, balle akan matsiyaciyar yarinyar nan, abu daya tasani shine bazata bari ta zauna mata gida ba, kallonsu tayi tana girgiza kai, aranta tana fadin bazai yuyuba, almajira da danta over her dead body" batace uffan ba ta wuce dakinta dake nan kasan, hand bag dinta ta dire tadau wayarta ta kira Hajiya Safara, sun jima suna magana sannan ta katse cike da tsananin baci rai.

"Hope bata ji miki ciwo ba" ya fadi yana k'arewa jikinta kallo, kai ta daka mai bata bar kukan ba, yace "kiyi shuru banaso kuka, very soon zaki bar gidannan kinji"
"Okay" ta fada araunane.
Nufasa Mardiyya tayi tace
"Sweetie kodai na kaita gidan Umma ta zauna"..
Kallan baki da hankali yayi mata, yadda ya tsani Hajiya Safara ko makiyinsa bazai kai gidan ba, balle ma Batul, dukda ba sonta yake ba taci albarkacin mahaifinta.
"babu inda zata" ya fada atakaice, janta yayi suka haura sama, Mardiyya ta bisu da kallo zuciyar ta na zayyano mata abubuwa iri iri.
Da dare kowa daban yaci abunci adakinsa, daka ga su hudun kasan basa cikin walwala, kowa da abunda yake sakawa aransa.

Da safe Mom ce tafara zama dinning yin breakfast sannan Mardiyya da Rasheed suka sauko, gaida ta sukayi ta amsa da fara'arta tamkar ba abunda ya faru, "My Boy kayi resuming work ?
"Not yet" ya fada fuska ba yabo ba fallasa.
"Allah kaimu" .
"Amin" ya amsa agajarce. Serving dinsa Mardiyya tayi suka fara ci atsanake. Altine ta karaso rike da plate ta dibi abincin xata wuce, Mom ta dakatar da ita da cewa "ke, ina zakije da abincin nan?"
Altine tace "Aunty princess xan kaiwa"?
Takaici ne ya cikata, kalmar princess da suke ambata yana mugun kona mata rai, "ajiye ki wuce aikinki" ta fadi.
Ajiyewa altine tayi tabar gurin.
Mikewa yayi hade da daukan abincinsa yabar gurin batare daya kallesu ba yahaura sama.
Tsaki Mom taja hade da dangwarar da spoon din hannuta, kallon Mardiyya tayi da itama kallonta take, tace "ban taba ganin shasha kamar kiba, da wayewar ki da komai kalli yadda mijinki ke tashi zaune kam shegia yarinyar can amma ko aji kinki"
Galala Mardiya tayi tana kollanta tace "ni banga wani abu acikiba, shi yayi causing accident dinta so kinga dole ya damu da ita"
Harara takai mata, "jiya daya ke rungume da ita duk damuwar ce komi ?
Shuru Mardiyya tayi tana gasgata xancen.
Mom tacigaba, "dole musa hannu tare musan yadda tabar gidan nan"
Ware idanu tayi.
"Mi yayi zafi haka, plz mom ki bari tayi regaining memories dinta, nidai ba hannuna ciki, dama keda Umma kun saba kulle kullen ku nidai bada niba".
Gwab'e mata baki Mom tayi tamike tana cewa "wawiyar yarinya"
Turo baki Mardiyya tayi tanai gunguni, itadai bata ga wani abu tattare da princess ba da akeson barin ta gidan, asalima tausayi take bata.

Tsaye take tsakiyar dakin tanai kaiwa da komowa jikinta sanye da yar figiyar rigar bacci, sak'a da warwara na abunda zata fada mai take, shawara daya ta yanke na fadi mai gaskiyar wace ce ita, idan har ta fadi hakan kadai xaisa yabarta tabar gidan asauwake.
Turo kofar dakin ne yasata ta dan firgita, shigowa yayi fuska murtuke.
Jiki na rawa ta tadau zani ta daura tana fadin "ina kwana".
Bai amsa ba ya mika mana plate din hannusa,
"bana jin yunwa" ta fadi araunane bata da niyyan amsa, mugun kallo ya kai mata ba shiri ta amsa hade da matsawa lungun gado ta zauna..
Zama yayi kan Sofan dakin hade da shigidewa, fuskarsa na kallon sama.

Kasa cin abinci tayi tanai jujjuya spoon din hannuta, so take ta gayamai amma tana tsoro, dakyar tasamu courage ta mike tadau mayafi ta karasa gabansa ta zauna.
"Dan Allah kayi hakuri ka barni na tafi "
Yana jinta bai tanka ba saima runtse ido da yayi kaman mai bacci.
Taci gaba, "niba yar kowa bace agarin nan, asalima karya nayi dana ce ni jinin sarauta ce".
Ko motsi Rasheed bai yiba banda kasa kunne dayayi yana sauraranta.
Bata boye komai na rayuwarta taba ta kwashe ta fadi mai sannan ta hada da cewa "ina son mijina dan Allah ka barni na tafi na nemin gafarsa" Karasa magana tayi cikin shesheka, shuru ne ya ratsa sakanin su na mintina biyar sannan ya bude ido yanai mata kallon mamaki.
"Princess yaushe kika iso nan, kukan mi kike, kiin gama cin abinci ? Ya fadi murya kasa kasa kaman wanda ya farka daga bacci.

Gabanta ne ya fadi, badai baiji abunda tace ba, murya sarkake tace, "ban gama bama"
Mugun kallon yakai mata, cikin tsawa yace "zaki tashi anan ko saina mare ki"
Tsum ta mike, tanason tambayarsa ko yaji amma tana tsoro ganin yadda ya daure fuska.

Mikewa yayi ya fice daga dakin tanai binsan da kallon bakin ciki da takaici, ajiye plate din tayi gefe tana rusa kuka.

Office dinsa na cikin gidan ya nufa ya zaune hade dafe kansa, maganar zuci yake. what next, tunda tayi confessing, shidai ba sonta yake ba balle ya cigaba da zama da ita. K'wafa yayi yana yana neman mafita, chance daya zai bata tayi proving kanta, idan har batayi ba he has no choice daya wuce ya rabu da ita for good.
Kusan awa hudu ya kwashe gurin yana sake sake, daga can palon kasa yafara jiyo hayaniya kamar ya share sai kuma yafasa sakamakon muryar Mom daya jiyo tana tsine tsine.

Fitowa yayi da azama ya iske yan sanda kusan goma tsaye a Parlour Mom na yi masu bayani cikin daga murya, Mardiyya na tsaye gefe tana sauraran ta.
"Make faruwa ne" ya fadi yana kallon Mom,
"Sata akamin acikin gidannan"
Kallon ta yake ya kasa gasgata xancen, miyasa tunda baai sata ba sai yanxu daga zuwanta.
"Miye aka dauka"
"Sabon Gold earring dana zo dashi is missing" cikin huci ta karashe maganar, kallon yan sanda tayi tace "kuyi searching ko ina na gidan including the rooms"
"Toh hajiya" suka fadi atare hade da fara dube dube.
Murya kasa kasa yace "Mom miyasa baki gayamin an miki sata ba zakiyi alerting police"
Harara takai mai,
"Nayi laifi saika dakeni"
Matsawa tayi can gefe batare data tsaya saurarasan ba, Mardiyya ce ta matso garesa tace "cikin mudai ba barawo, i tink ko Mom tayi misplacing earring din wani gurin".
Shuru kawai yayi baice komai ba, yasan drama ne kawai Mom take babu wani Gold dinta da aka sace.

"Muje sama, kuyi checking duka dakunan" Mum ta fadi tanai masu jagoran hawan saman, da azama yabi bayansu yana fadin "mom dan Allah ki bari, i will get you a new one"
Banza tayi dashi suka karasa hawa, direct dakin da Batul take suka fantsama ciki, ran Rasheed ya baci matuka, dadin abun ma bata dakin tana toilet tana wanka, bakin kofar toilet din yaja tsaya gudun karta fito su ganta.

"Lungu lungun da sako ku tabbata kun duba, cox i dont trust her" Mom ke magana ayayinda yan sanda sai biincike da bude bude suke, itadai Mardiyya kallon su take cike da haushi, dan kuwa bazata bari ama dakinta iskancin nan ma.

Daga pilo daya daga cikin yan sanda yayi saiga dankareriyar earing na gold shumfide gurin , dauka yayi yana fadin "hajiya wanan ne?
Kwarai kuwa shine" ta fada hade da dafe kirjin cike da mamaki"
Ta kuma cewa "Dpo tana wanka,

Please Login or Register in order to submit comment