Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gobe saita kaisu gidan su cousin dinta Rmd, karfin hali kawai tayi ta amsa masu da naam, ranta duk ajagule ta rasa mafita.

Kallon ta Baba yayi, yanayinta ya nuna ba lapia ba, yace "fatima mike damunki ?
Kuka ta fashe dashi "Baba nikam na gaji da talaunci nan, wai yaushe zakayi kudine, miyasa ma na fado cikin zuria ka" sosai tafashe da mugun kuka, kollanta Baba kadai yayi yana murmushi bayau mace tasaba cin zarafin saba, saidai kalaman fatima ba karamin fama mai ciwo daya dade da samun waraka azuciyar saba.
Ran mamuda kam ya gama bacci hannu ya daga da niyyan sharara mata mari, baba yarike hannusa "dukan mace bai kamace kama, karka kuskura" Acewar Baba.
Harara Batul ta kaimai ta ruga gida aguje, baba ya rike hannusa suka fice zuciyarsa na tafarfasa.

Gam Hajjo ta capke ta data shigo, dan kuwa duk abunda tace taji ta, kaman an aikota tahau Batul da dukam tsiya, banda ihu da kuka ba abunda take,
"Kafin ki kashe ubanki ni xam kashe ki" hajjo ke fadi cikin kunin rai tana mai kara kai mata naushi, saida tayi mata lillis sanan ta barta tana fadin "yar banxa yarinya, kasheki xanyi na huta da bakin cikin ki, nagode wa Allah daya azurtani da kannanki dayau kin kasheni abanza"
Kuka sosai Batul take, tana jawa bawan Allah mamuda Allah ya isa, aganinta tunda yaxo hajjo ke kirbanta, dan kuwa rannan abinci taki zubamai hajjo ta mata lilis yauma ba, wani mugun tsanan shi take ji aranta, ayyada zuciyarta ke tafasa inda zataga Rmd binshi kawai zatayi tabar masu gidan, dan kuwa shine kadai gatan ta yanxu.
"Oh ni fatima ina Xan Ganshi,.." Ta karasa magana cikin matsananci kuka, atunanin ta a zuciya ta fadi not knowing afili tafada, jim muryar Hajjo tayi akanta rike da ludayin miya, tana cewa , idan na fasa maki baki zaki ganshi da kyau"
Ba shiri ta mike da azama tayi cikin bayi da gudu tana kuka.
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: ๐Ÿ’– *INA ZAN GANSHI*๐Ÿ’–
Rubutawa
Xarah Bukar

ยฎNWA

xarahbukar.wordpress.com

36 - 40

K'ashe gari da k'arfinta ta tashi, fuskar ta dauke da murmushi dan kuwa tayi alwashin daina zubda tsad'addan hawayen ta kan matsiyacin nan, ranar kin dillanci kadai take jira.
Kayan jinkinta ta cire ta dauro zanin wanka ta fito tsakar gidan, bayin ta leka taga babu ruwan balle famfo sai bukitin k"arfe marar hannu dake ajiye, tsaki taja aranta tanai tir da talauci, kofar Inna kulu ta nufa ta tsaya, babu ko gaisuwa tace "Tsohuwa xanyi wanka".
Daka cikin k'uryar dakin Inna tace.
"nazo na mike ne ?
Mikewa tayi hade da sunkutan redionta ta fito tana kara maimaita abunda ta fadi.
Cike da tsiwa Batul ke kollanta, "ruwa zaki ban nayi wanka"
Yar tsugunno dake gurin Inna ta dasa mazaunin ta akai sannan tace "ayyo ainan babu ruwa, waje zaki je akwai burtsatsan unguwa saiki dibo"
Kallon rainin Batul takai mata, tayama xata fita waje diban ruwan kamar wata buduwar k'auye, agidama Hassan ke jamata ruwa a rijiya balle kuma nan daba zama taxo ba.
"Ba girma na bane, saidai jikanki ya fita ya debo min"
"Toh saiki jirasa yaxo" Inna ta fadi cikin ko ta kula da kallon da take mana.
"Ina ya fita da safan nan" Batul ta tambaya .
Banxa da ita Inna tayi, saima redio data kunna jin labaran karfe takwas. Tsayuwar mintinu ashiri Bayul tayi, Inna bata tanka taba, wanka kadai takeson yi danji dadin jikinta, ganin tsayuwar ba amfani yasan ta komai daki tasanya hijb ta fito, bokitin dake bayin ta dauka ta fice waje.
Sai yanxu ta karewa unguwar kallo, jama'an cikin ta ba abun kallo akara bane, gaba da gidansu kadan butsatsan yake, mutane kusan ashirin data ganin bisa layi yasata jan mugun tsaki, itakam bada ita zaai haukar nan ba, dole nema subarta ta diba dan ita ba kalar subace. Karasawa tayi tanai ma kowa kallon wulakanci, su dinma ita suke kallo, dire bokitinta kusa da wanda tagani yana diba, jira kaidai take ya cire tasanata, yana cirewa kuwa ta sanya, murmushi tayi ya kusa cika babu wanda ya tanka ta, saima kallon ta da kadai suke, kadan ya rage ya cika, wata yarinya dake can baya ta karaso tasa hannu tayi wurgi da bokitin ruwan ya kelaye gurin.
"Ke kin isa, wa kika fi gashin tsuliya anan dahar zaki raina mana wayo kizo ki ganmu alayi dan iskanci shine zakiyi babakere" yarinya mai suna Dija ke magana cikin karaji da zare idanu.
Murtukewa Batul tayi, ta nunata da yatsa, "ke bakauyiya, ki kiyaye ne, kinsa dawa kike magana kuwa "
"Nasani mana, da mutum nake bada dabba ba, layi kuwa sai kinbi tunda ba ubanki ya kafa famfam ba" kallon sama da kasa Dija ke mata ayayinda take maganar.
Dariya yan gurin su kwashe dashi, daya dake gurin tace "kalle tafa damu da ita banga bammaci ba, sai felekan tsiya harda wani ansan dawa take magana, kaji ja'iri, mukam nan saidai kici na jaki"
Ruwan ne ya cinye Batul tayi tsit, tayi underestimating dinsu, batayi expecting zasuyi magana ba yadda tayi masu kallon yan primitive society, cike da kunya tadau bokitin ta koma baya ta tsaya, dariya kuwa basu fasa ba, ignoring kadai Batul tayi har layi yaxo kanta, bisa kai ta aza ta koma gida cike da tausayin kanta. Wanka ta shiga sharp shrp ta fito, sauri take tana da lecture by 10.
Kwalliya sosai tayi cikin atamfa riga da skirt ta fito ta riske Inna hartai wanka tana zauna bisa tabarma tana shan shayi da buredi da fried kwai, mamaki karara tayi yaushe Inna ta debo ruwan waima yaushe ta kunna murhu aza ruwan zafi da soya kwai, gadai murhu babu alamun an taba, tsaye tayi kan Inna, "kudin mota, xan wuce makaranta"
Cikin fara'ar Inna ta kalleta tace "mijinki zaki tambaya bani ba, kuma ai kyaci abinci kafin ki fiti ko".
Kaman jiran take tace toh xan ci" wazai ga kwai da biredi ya kyale, dama yunwa takeji ba kadan.
"Gashi" inna ta fadi hade da mika mata bakar leda
Budewa tayi da azama, saidai abunda tagani yasata yamutse fuska, taliyar hausa ce danya da manja da kulli gishiri da yaji, "Tsohuwa miye wannan"
"Abincin ki mana, dare da rana, ga murhu can ki dafa asawake, ga langar samira xan ara miki tunda baki kawo tukunya daga gidan kuba"
Kuka ne ya rage Batul batai ba, daurewa kadai tayi ta ajiye ledar ba tare datace uffan ba, tunanin kawai take ta tashi ta gudu ne ko yaya, toh idan ta gudu taje ina, shi wanda take muradin so baima san da zaman taba, fuskar sama ba sani tayi ba, ance he is rich & simple, amm toh ina zata ganshi, burinta daya taga tazama matar mai kudi ba matar matsiyaci ba.

Zaman kusan awa biyu tayi gurin Mamuda bai zoba, yunwa na nema illata ta, mikewa tayi tahau aza murhu, abunda bata taba yiba saidai Hajjo tayi, ba karamin wahala tasha ba sannan wutan ya kama, karamar bokiti datagani tadau ta debo ruwa ciki tahau kikirkiri din daura taliyar.
Bayan ta sauke, ko tayi batama Inna ba tahau ci. Sai bayan Sallah azahar Rasheed ya shigo gidan, tana ganin sa tahau surfa masifan yaja mata bataje makaranta ba, gaisawa da Inna yayi kafin ya zaune yace mata "banda halin ciyar dake da biya miki na makaranta, hakuri xakiyi idan Allah ya hore nan gaba kyaje, rayuwa saida manaji, ina abinci na ?
Ya gama soka mata kibiya azuciya, daskerwa tayi tana sauraran sa sannan tace "duk inda kudi suke dole ka nemo su, uwarka ma tayi kadan ta hanani zuwa balle kai karan kadan miya, abinci kuma ban dafa dakai ba"
Kallonta kawai yake bai ce uffan ba, aransa fadi yake bakisan uwata ba dole kice haka, duk randa kika shigo hannuta zaki gane ruwan ba sa'a kwando bane.
Masifa sosai da fitsara tayi tamai, wata zuciyar nace mata toh idan kinje makarata kicewa su Billy mene, ai da kunya ma, kila ma sun gama yada ta aduniya, hakura kadai zatayi tayi da batun makaratta kafin tasan abunyi nan gaba.



****
Sati biyu zani bata canxa ba, halin Batul sai wanda ya karu, akullum Rasheed xaije gidan amma maganar arziki bata hadasu, iya kaci susha hira da Inna da dare ya koma gida, dadi sosai Batul takeji aganinta a kekensa yake kwana waje ita ta kame a daki, wanka da cin abinci duk bayayi agidan, atunaninta tsoronta ya hanasa sakat.
Ta bangaran Inna kuwa ta rasa daga ina ake kawo mata abinci mai rai da lafiya, saida taga tanaci amma ita an barta da manja da yaji, ba abunda ya shafe ta, opportunity kadai take jira ta fece.

Yau ya jima a gidan suna hira da Inna, sai kusan tara yamata sallama, rai bace yabar gida, yafara gajiya da cin mutunci Batula, sakinta zaiyi ya shafawa kansa lapia tunda ba sonta yake ba. Inyaso taje can ta karata da karyar ta, shidai Rmd ya mata nisa saidai ta nemi wani can daban.


Agajiye likis ya dawo gida bayan ya tsaftace jikinsa, Mom ya tarar tsaye tsakiyar palon tana kai komo, kafin yakai ga isa gareta ta tunkaro sa, cike damuwa tace "my boy daga ina kake by this tym
Agogon hannusa ya kalla, goma dayan mintinu amma ji yadda take interrogating dinsa kaman karamin yaro ,rabawa gefenta yayi ya zauna kan kujera,
"Ancemin kwanan biyu bakaje office ba, idan kasa wasa asset dinmu xai iya dropping" ta fada tana kai mazaunin ta dayan kujerar dake gefensa.
Takaici ne ya cikasa, matan biyun duk sun dauramai zafi, ya dawo gida bai tsira ba, Mom dinsa mai kudi amma sai shegen son kudi alway seeking for more, dayar can kuma talaka but desperate to be rich by all mean, kodayake baima san inda ta dosa ba, karyata kadai ya isheshi bugun zuciya.
Nisawa yayi yace " Mom gayamin make tsakanin ki da Hajiya safara"
Gabanta ne ya fadi, wace irin tambaye ce wannan, ta fadi aranta, afili tace "babu komai, kawata ce tun muna yammata, miyasa ka tambaya ?.
Kawar da tambayar yayi dacewa, "na yadda xan aure Mardiyya"
Dariya mai dauke da farin ciki tayi, "ka fara sonta kenan ?
Kai y girgiza, "a'a, xan bata chance ne, you once said kwarya tabi kwarya, shiyaaa nayi deciding auranta"
Dadin sosai Mom taji, atleast xata huta da threat din Hajiya safara, saidai wani hanzari ba gudu ba, zusa katsina ya kamata, amma da wana ido zata dubi kawu Habibu, kusan shekarau sama da ashiri ta yayesu a ababin rayuwar ta, saukin abun ma My boy yakan kai masu ziyara. Mikewa Rasheed yanai mata Sai da safe, bai jira cewarta ba yayi gaba, tuni ya gano ta lula duniyar tunanin dabai san ta miye ba.

Bayan kwana biyu ba inda yake zuwa sai office, da wuri yau ya shirya ya fice office, aiki sosai ya wuni yana yi, charles ne ya shigo yace Mardiyya keson ganinsa it urgent, izini ya mai data shigo, sanna ya fice.

Da sallama ta shigo, hannun ta rike da files, amsawa yayi yanai sakar mata murmushi, karfin gwiwa ta samu ta karasa ta hade da mika mai, bai karba ba ya mata nuni da ta ajiye,
"Ki zauna mana" ya fada ganin tana shirin fita.
Akunyace ta zauna, yace "Momcy bata gaya maki good news ba ?.
Sunne kai tayi danta gane inda xancen ya dosa,
"Ya preparation"
Nisawa tayi, dakyar tace "babu wani shiri, am sure kaima you aint interested da wani grand Preparations".
Murmushi yayi yana cigaba da kallonta, duk lokacin nan yarasa miyasa bai gano good side of her ba sai yanxu, koda yake Batula ta sanya shi gano hakan, sau da dama akance yaran masu kudi basu da tarbiyya ashe ba duka aka taru aka zama daya ba, guntun tsaki yaja aranshi, bai taba cin karo da bad girl irin Batula ba, wani mugun tsanar ta yakeji aranshi.
"Marfiyya inason auran nan yaxama grand weedding, wanda kowa a duniya saiya san ni Rmd nayi aure".
Tsuru tayi tana kallonsa, ita mamaki ma yabata all of a sudden ya yadda da auranta kuma big wedding yakeso, kodayake itama hakan takeso, halinsa yasa ta kama kanta.
Hira sosai sukayi kaman masoyan asali, tun tana kame kanta harta saki jiki tana dariya.



*Katsina*


Wedding Bells ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: ๐Ÿ’– *INA ZAN GANSHI*๐Ÿ’–
Rubutawa
Xarah Bukar

ยฎNWA

xarahbukar.wordpress.com

41 - 45


Katsina..

K'arfe sha biyu na rana direban Mom yayi horn gaban kataferan gate din gidan Kawu Habibu, bude gate mai gadi yayi da azama kansancewar ubangidansa ya sheda mai zuwa su.
Parking yayi ya fito ya bude mata kofar b'angaranta, cikin isa ta fito tanai karewa gidan saman kallo sannan ta taka zuwa tangameman palon.
Ajiyar zuciya kawu Habibu ya sauke, tun shigowarsu yake tsaye bakin window benan yanai kallonta, hali da bazai canza ba abunda kadai ya furta sannan ya juyo saukowa.
Hajiya Suwaiba matar sa ta fito daga kitchen, kicibis tayi da ita tanai ma palon mugun kallo, "hajiya Fati harkin karaso ashe, sannu da zuwa" Hajiya Suwaiba ta fada cik'e da fara'a.
Ayatsine tace "sauri nake kice wa Kawu na iso"
Gyaran murya kawu Habibu yayi yana saukowa.
Kunya ne ya kamata batayi tunanin zai jita ba, mazewa tayi tace "Kawu ashe kana kusa, ina wuni".
"Lapia lau Fatima",ya amsa hade da zama kan kujera, itama zaman tayi, hajiya Suwaiba ta koma kitchen nema mata abun sha.
Gaisuwa sukayi mai tsawo kafin Mom ta gabatar da abun da ya kawo ta, Jinjina kai kawu yayi, yasan tabbas rana irin tayau zataxo, matar da bata daukesu abakin komai ba shine yau ta tako taxo dan danta xaiyi aure, ashe dai komai nada ranarsa.
Nisawa yayi yace "naji dadi matika, Abdulrasheed zaiyi aure, naso ace na hadashi da diyata Hafsat saidai hakan bai yuyu ba".
"Gaskia ne" Mom ta fadi tana murmushi dabai kai zuci ba, yaushe ma zata yadda Hafsat ta auri Rasheed, mai kawu yake dashi ma, mutumin da rabin dunkiyar sama Ubanta ne basa, dan lecturing da yakeyi nawa yasamu, shima dai xance kawai yage, bazata yuyuba, Mardiyya ce daidai da Boy dinta.

Tattaunawa sukayi da kawu, sannan ta gayamai sun riga sun tsayar da rana sati daya kacal, farin ciki sosai Kawu yayi, yanaji da Rasheed tamkar dansa, halin uwarsa kadai yasa yake maintaining distance. Sun dade suna magana daga bisani Mom ta masu sallama ta kamo hanyar Kd.
Gidan Hajia Safara ta nufa, nanma sun dade suna tattauna yadda buki zata kasance, daga bisani ta mike zata wuce suka hadu da Abban Mardiyya ya shigo, gaisawa sukayi da Mom yana zolayarta ya shirye shirye, dariyar kawai tayi bata amsa baima ta wuce waje Hajiya safara ta rakata bakin motar ta. Murmushi Abban Mardiya ya saki aransa yana fadin "ku gama shirin bukin ku kafin nima nawa buki yaxo" darawa yayi ya karasa wuce warsa ciki.


***
Bikin ya kusanto gadan gadan, kwana biyu kadai ya rage, pre-wedding picture kusan ashirin suka dauka da differnt photographers, sunyi matukar kyau, matured style sukayi wanda bai sabawa addinin musulunci ba, Duk inda ka shiga xancen kadai ke ruruwa, Iv din bukin da picx sai yawo suke a social media, daga masu murna sai masu ihu ganinsa, wasu dan shishigi ma har watapp name dinsu Rmd suka maida.

Tun bayan datayi sallar azahar Batul take jin jikinta amace, gabadaya ta rasa make mata dadi, shi matsiyacin can kusan sati bata gansa ba, hajjo da Baba da yan kannanta ne suka fado mata arai tahau lalubar wayarta da tunga aka kawota bata bi takan shiba, dauka tayi taga yaki kunnuwa, tsaki taja sanin cewa rashin caji yahana ta kunnu, gashi kuma gidan ko wuta babu balle soket.
Fitowa tayi tadau bokiti tace, "Inna na fita dibo ruwa"
"Kar dai ki dade"Inna tafada daga cikin daki.
Dire bokitin tayi ahankali bakin karga sannan ta fito tsakayir unguwar dubawa tayi ko zata samu masu cajin haya, wayam babu ko alamun su, wani gidan siminti tagani can gaba dasu da wutar lantarki awaje, da azama ta taka ta shiga gida, Kwakwasawa tayi, yarinya mai suna Hafsat Rano ta bude,
"ina wuni, dan Allah caji nakeso asamin, ga gidan mu can" Batul ta fada tana mata nuni da gidansu.
Shigo, amma maman mu ta fita" acewar Hafsat.
Godiya Batul tayi ta shiga ciki, yammata biyu zaune tagani kusa da socket suna cajin wayoyinsu suna chating, kaman munafuka ta gaidasu sanna ta sakala nata cajin, gefe guda taja ta zauna hade da tagumi.
Dariya daya cikin yammatan mai suna Baby nurse tayi tana fadin "nashige su mistakely na tura pre wedding picx din Rmd da matarsa group, yaukam nasan dole xarah ta cireni".
Dayar mai suna Dija Waziri tace "maiya kaiki kinsan dai Xarah bata bari aturo abunda bai shafi littafi ba, turomin hoton Iv dinsu, zakije Dinner din ?.
Ihu murna Baby Nurse tayi tace "invited or no invited we must be there,".
shewa sukayi hade da tafawa, (ni xarah nace gayyar sode)

Sauraran su Batul take amma tarasa inda xancen su ya dosa, kalmar Rmd kadai hankalinta yafi karkata akai, kasa daurewa tayi ta kunna wayarta, gashi kuma bata watsapp balle su turo mata hoton, karfin hali tayi tace "sis dan Allah turonin picx din Rmd ta Bluetooth".
Kallon banza Baby nurse takai mata, abun mamaki wai ta bluetooth, har yanxu ana yayin sane ta fadi aranta.
Cikin rawar jiki Dija waziri ta kunna Bluetooth tahau tura mata, godiya sosai Batul tayi bata tsaya jiran wayar ta cika ba ta cire ta koma gida, dakinta ta shige da gudu batare data tsaya sauraran Inna dake magana ba.
Addua takeyi wayar na bisa kirjinta, so take ta kalli pic din amma tana tsoro karya zamana Rmd da take muradin samu bai hadu ba, dakyar dai tasamu courage ta kalli pic din, kur tayi tana kallon kyakyawan fuskar sa mai dauke da murmushi, saidai kuma kaman taso tasan fuskar wani guri, a iya tunanin ta bata gano ba, sanin ya mata nisa inama zata ganshi, wani irin sonshi da begansa ne ya mamaye zuciya ta, ware idanu tayi adaidai lokacin da suka sauka a fuska Mardiyya, tsaf tagane ta kwanaki sun hadu a ostrich bakery, last tym da taganta ba karamin burgeta tayi ba amma yau duk sai taji wani irin haushi da kishinta....dafe kai tayi tana fadin innalilahi wa inna'ilaihi rajun, Mamuda ka cuceni,, adalilinka wata ta maye gurbin wanda nake muradi arayuwata, Allah ya isa tsakanin dakai, na tsane ka, banza matsiyaci dan tasha" kuka sosai ne ya kufce mata, su baba da hajjo da tayi niyan kira fasawa tayi, wurga wayan tayi gefe cike dajin haushin su, koma miya faru sune suka caza mata.



******

Buki Budiri ya kankama๐Ÿ’ƒ, duk wata shagali na bukin hausa, turawa dana India gabadaya an kwatanta, duk fadin duniya zancen su ake, BBc, cnn, aljazeera, channels, nta tashoshi da dama ka kune hirar auran Rmd Da Mardiyyah ke wanzuwa, manyan mutane ,yayan sarakuna da gwamnoni duk sun hallara ranar daurin auren su.
Karfe 3 na rana aka mika amaryan gidansu Rmd nan inda suke zama da Mom, Hajiya safara baki yaki ruhuwa sai murna take yarta tayi goshi, guraran 8pm aka fara shirin tafiya haddaddiyar Dinner da xaa ayi a fountain Mansion...ni xarah nace bara na leka Batula nasan za ayi african time kafin afara.


**
"Yaunxu Batula baza ki bar kukan nan ba, abu yakici yaki cinye wa tun shekaranjiya kina abu daya" Inna ta fada tana tsaye bakin kofar dakin.
cikin shesheka tace "Inna dan Allah kice wa Mamudu ya dawo ya sakeni, bana sonshi, ki taimaka ya sakeni na auri wanda naso" karasa maganar tayi cikin kuka mai tsuma zuciya.
Ba karamin tausayin ta Inna taji ba, karasa shiga dakin tayi ta zauna gefen ta tana fadin "karki damu very soon xai sakeki,
"Dagaske Inna" ta fada in cool voice.
Kai kadai Inna ta taga mata alamu eh, hankalinta na kan fuskar wayar Batul, hoton Rmd din ke kan screen saver ta wanda tuni tayi croping ta cire fuskar Mardiyya, "kaico yarinya kishe ke dawainiya dake," inna tace aranta
Lallashi sosai Inna tahau yi mata amma kamar zugata take kara sautin kukan ta take.
Tamkar an tsigare ta mikewa tayi tana zara idanu sannan ta janyo ghana must go din ta, budewa tayi tadau yar dubu daya rak data mallaka arayuwarta sannan tadau jan gyale ta yafa bisa kodaddiyar goriyar atamfa dake jikinta, "Ina xaki adaran nan" Inna ta fadi tana kallonta.
Cikin saurin tace "bazan dade ba" ficewa tayi da azama ba tare da ta jira cewarta ba.
Sauke numfashi Inna tayi ta mike tsaye tana kai komo adakin, yazamata dole tama Rasheed magana, lokaci yayi dazai fito ya nuna mata shine wanda takeso tun kafin ciwon zuciya ya kamata, yadda taga Batul na kuka ta yadda cewa lailai tayi sanyi kuma ta saduda, dakinta ta nufa tahau lalubar wayarta dan kiran Rasheed.

Babban titin unguwar ta tako tanai sak'a da warwara a zuciyan ta, Iv data gani ya nuna mata a fountain Mansion xaai Dinner saidai kuma batasan gurin ba, amma kuma idan taje ya xatayi, nuna kanta garesa xatati ko miye ?, gigiza kai tayi hakan bazai yuyyba, zataje ne kawai taganshi ido da ido.
Napep data tsada ba wanda ya dauke ta acewarsu gurin district area ne da napep ko achaba basa zuwa, dakyar dai tasamu taxi sukayi ciniki ya kaitaa naira dari shida dan ba karamin nisa ne da inda ya dauke taba, can farkon hanya ya sauketa ta tafara takowa toward the gate, Kasa karasawa tayi bakin gate din, sojijin kusan 20 ke tsaye bakin gate din, sai manyan motoci da suke artawa ciki a guje, daga gurin da take tana jiyo sautin wak'a dake dashi.
Tsuru tsuru tayi, bugun gabanta na tsananta, shahada tayi ta nufa gate din, daya daga cikin soja ya dakatar da ita yana tamvayar ta Iv, ba'a bata ba tace dashi, tuni ya kuma daure fuska, dan kuwa babu mai shiga sai da Iv, dinner din is strictly on invitation.
"Oga dan Allah ka barni na shiga " ta fada amarairace. bai tanka taba saima kallon gefe sa da yake, Mom ke takowa cikin takun kasaita, sanye take cikin tsadaddiyar leshe kanta daure da gele wanda Oshewa beauty suka mata tieing, kallonta Batul tayi aranta tana adduaa Allah sa matar ta barta ta shiga.
Karasowa tayi.
"Julius make sure ku tsaya postion dinku, gasu nan isowa" ta fada tana kallon julius bata ma lura da Batul dake tsaye ba, juyawa tayi zata tafi sai kuma ta juyowa kallon Batul, dauke kai tayi da sauri ta kalli julius tace "miya kawo almajirai gurin nan ?
"Hajiya ayi hajuri, yanxu zata tafi"
Harara takaimai taja tsaki ta wuce.
"Yarinyar kibar gurin nan, kafin nasa a wulla ki titi"
"Dan Allah ka barni na shiga, it very urgent" kuka ta sanya tana magana.
D'ayan soja dake tsaye yace "yunwa take ji, bara atura kodan snack ne abata ta tafi"
Gefe Batul tayi ta tsaya tana sharar kwalla.

Covony na mayan motoci guda ashirin sukayi, motar amarya da ango ne a tsakiya, suka karaso gaban gate din basu shiga ba, duk motocin suka tsaya, Zaune suke a motar babu mai magana tsakanin, jifa jifa ne Mardiyya ke kallonsa ta saki murmushi, shima murmushi yake sakar, gabadaya hankalin sa baya jikin sa, maganar su da Inna a waya kadai ke yawan mai a kai, ita so take ya nunawa Batul kansa, saidai bazai iyaba dan kuwa ba sonta yake kuma bai yadda ta saduda ba, nan gaba tana samu wani oppurtunity halin karyar ta xai dawo, asalima he is planing of sakinta idan Baba ya dawo daga tafiyar kauye da sukayi.
Numfasawa yayi ya jingine kansa cikin seat hade da kawar da kansa gefe yana duban waje da hasken lantarki

Please Login or Register in order to submit comment