Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakai dan haka d'aga muji abinda zaice Ina daidai dashi" Hajiya Salmah ta karasa maganar harda zaro ido waje tana harare harare kamar Alhaji Mukhtar d'in ne a wajen.

D'agawa Sultan yayi yana daidaita muryarsa yace "hello Daddy ina yini"?.

Alhaji Mukhtar bai amsa masa ba domin ina yinin da yace sai ya sake fusata shi murya a kausashe yace "Sultan duk inda kake duk abinda kake komai muhimmancin sa ka katse shi yanzu kazo Ina neman ka a gida karka kuskura ka 6ata min lokaci" yana fad'in haka ya kashe Kiran dafe Kai Sultan yai yana cewa.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Umma kinga abunda nake gudu ko shiyasa tun farko nace ku kyale na had'a wani lefen akai karki kar'bo akwatunan nan zai tada fitina gashi tun ba'a je ko'ina ba ni bansan yadda zanyi da rayuwata idan Abba yad'au fushi yana ji baya gani baya saukowa da wuri".

Ta'be baki Hajiya Salmah tai tana kallon sa da yadda lokaci guda ya susuce ya fita daga nutsuwar sa tace "oh akan wannan d'an abun shine har ka tada hankalinka? Hummn Sultan karka damu bakasan wace niba ganina kawai kake haka matsayin Umman ka idan na fito maka a kalata zaka sha mamaki dan haka tashi kaje karkasa tunanin komai a ranka kaje ka fuskance shi ka tsayar da idanuwanka cikin nashi Ina me tabbatar maka idan kayi haka zakai masa kwarjini zai rasa abunda zaice maka karshen wasan zakaji yace tashi ka tafi".

Da mamaki Sultan yace "Allah Umma"?.

Cikin yardar da taiwa kanta cewa hakan ne mafita da bashi 'kwarin gwiwa tace "kwarai kuwa jeka gwada Ina jiranka nan da bayan sallar isha" Kai Sultan ya d'aga yana sauke ajiyar zuciya yace "to amma Umma.....................

Kiran Alhaji Mukhtar daya sake shigowa wayarsa shine ya hana ya fad'a Mata abinda yake son fad'a da sauri ya mi'ke ko sai an jima baice mata ba yayi waje yad'au mota da mugun gudu ya nufi gida yana yin parking daidai Alhaji Mukhtar ya gaji da kiransa ya fito harabar gida ya tsaya a jikin mota kawai ya zubawa kofar gate ido yana jira yaji motsin Sultan d'in amma shiru sai yanzu.

Ko daidaita parking Sultan baiyi ba ya fita daga motar yazo inda Alhaji Mukhtar yake tsaye saidai ya kasa d'agowa ya tsayar da idanun nasa cikin nasa kamar yadda Hajiya Salmah tace masa bazai iya ba domin mahaifin sane yayi masa kwarjini kallonsa sosai Alhaji Mukhtar ya tsaya yi kamar me tunani daga baya ya jinjina kai yana jin kamar ya rufeshi da duka ya daure dai yakai zuciyarsa nesa saidai kana jin muryarsa kasan a fusace yake juyawa yayi yana bud'e murfin mota yace.

"Tashi ka shiga akwai inda zamuje".

Mi'kewa Sultan yayi da'kyar kamar mara lafiya ya zagaya d'ayan site d'in ya shiga Alhaji Mukhtar ya tada mota suka bar gidan tambayoyi ne sosai aran Sultan to yanzu ina zasuje meyasa ya d'auko shi a motarsa.......................

Tunanin sane ya katse jin ya tsayar da motar yana horn da sauri ya d'ago yana kallon gurin daidai me gadi ya bud'e kofa sun shiga fad'uwa gaban Sultan yahau yi bayan Alhaji Mukhtar ya parker da mota sun fito me suka zo yi a gidan su Nabilah kuma? Kai akwai wani abu da yake faruwa Allah yasa ba aure zaice an d'aura musu ba tabdijan daya shiga uku ya zaiyi da Hajeer me zai cewa Hajiya Salmah bazai iya fuskantar ta ba tuna hakan yasa ya zabura har saida Alhaji Mukhtar ya kalleshi amma ba kallon rahma ba kallo ne me cike dam da tsantsan fushi.

Suna shiga parlor Alhaji Tajuddeen yana tsaye shima tun akan abinda Hajiya Salmah tazo tayi yana damunsa ganinsu tare da kuma yanayin da yake ganowa a tare da Alhaji Mukhtar da sauri yace "lafiya na ganku a haka Mukhtar"? Daidai sun karaso Alhaji Mukhtar ya jinjina kai yana cewa "eh lafiya yaya magana zamuyi" ya fad'a kafin ya juya inda Sultan yake ba zato Sultan yaji an kifeshi da mari kafin ya samu damar d'agowa Alhaji Mukhtar ya sake d'auke shi da wani mari" da mamaki Alhaji Tajuddeen yace.

"Subahanallahi Mukhtar me kake yi haka".

Alhaji Mukhtar baiyi magana ba sai rigar Sultan daya ri'ko yaci kwalarshi ransa na 'kuna ya hankad'o shi gaban Alhaji Tajuddeen cikin tsawa yace "dur'kusa ka bashi ha'kuri".

Da sabon mamaki Alhaji Tajuddeen yace "wai Mukhtar lafiyar kalau kuwa"?.

"Eh Yaya ina lafiya kuma a hayyacina nake kawai Sultan da Salmah sun kaini bango ne yau sai yadda Allah yayi nida Sultan ne zaiga fushi na wanda bai ta'ba gani ba bai Kuma San Ina dashi ba yanzu ya baka ha'kuri".

Da alamun tambaya Alhaji Tajuddeen yace "To ha'kurin me kake so ya bani yayi min wani abu ne"?..

"Kwarai ai shi yasan abinda yayi maka dan haka ya baka ha'kuri da farko kafin na fad'i abinda nake son fad'a" mayar da hankalinsa kan Sultan yayi yana cewa "ka bashi ha'kuri ko sai nayi shot dakai anan".

Da sauri Sultan ya durkusa har yana bugewa da kujera ya dafa kafafun Alhaji Tajuddeen yana cewa "dan Allah Daddy kayi hakuri dan Allah ka yafe min".

Kai Alhaji Tajuddeen ya girgiza yana cewa "ni babu abinda kai min Sultan tashi kaje" yana rufe baki Sultan ya mi'ke tsaye yana shirin ficewa daga parlon da sauri Alhaji Mukhtar ya mayar dashi qasa yana cewa "wallahi yaya Tajo saiya baka ha'kuri Kuma sai kace ka yafe masa idan ba haka ba ni bazan yafe masa ba".

"Haba Mukhtar ni meyayi min dan Allah ka rabu dashi".

"Yayi maka Yaya amma tunda lokaci ya wuce basai an dawo da baya ba kowa ya tuna bara baiji dad'in bana ba kawai ni ya baka ha'kuri ina ji shine zan gamsu".

"Idan ya bani ha'kurin shikenan ina komai ya wuce"?.

"Eh to banace ba amma dai ya fara baka ha'kurin naji".

"Ok sultan bani ha'kuri" Alhaji Tajuddeen ya fad'a da murmushin rigima irinta Alhaji Mukhtar a fuskarsa.

Kan Sultan a sunkuye yace "kayi hakuri Daddy dan Allah ka yafe min".

"Na yafe ka Sultan Allah ya yafe mana baki d'ayan mu, kallon Alhaji Mukhtar yayi yana cewa "ya bani ha'kurin shikenan ya wuce"?.

Kai Alhaji Mukhtar ya girgiza yana cewa "ya kusa wucewa dai abu na gaba da zakai ni kuma na yafeka shine kaje duk inda Hajiya Salmah takai akwatunan nan ka dawo min dasu gidan nan kafin ranka yai mummunan 6aci ni zaka mayar 'karamin mutum ka biyewa mahaifiyar ka tana d'ora ka akan gur6atacciyar hanya baza kasan kayi babban rashin Nabilah ba a rayuwar ka sai ranar daka gane gaskiya lokacin da ni kuma bazan saurareka ba".

Jin abinda Alhaji Mukhtar yake fad'a yasa Alhaji Tajuddeen ya samu hasken abinda yake faruwa tsakanin su kaiya girgiza yana kallon Alhaji Mukhtar wanda fuskarsa ta gama cika ta batse da 6acin rai yace.

"Zaune Mukhtar muyi magana".

Zama Alhaji Mukhtar yayi sannan Alhaji Tajuddeen ya mayar da kallonsa kan Sultan yace "kaima gyara zamanka Sultan kar kafarka yai ciwo" gyara zama Sultan yayi kuma har lokacin ya kasa d'agowa ya kalli Alhaji Tajuddeen saboda kunya..........

Magana Alhaji Tajuddeen ya fara cikin nutsuwa ta sigar da zasu fahimce shi yace "Mukhtar dan Allah kabar Sultan ya auri za'bin ransa karka hanashi kuma kar kayi fushi dashi bakasan me Allah ya rufe ba a cikin wancan auren da yake so kowanne bawa da kalar tasa kaddarar insha Allahu daga yau na warware komai Babu maganar aure tsakanin ka da Nabilah saidai kuyi zumunci Allah ya baiwa kowa abokin zama na gari kai kuma Mukhtar abinda nake so dakai kayi hakuri kar kayi fushi da Sultan duk abinda kaga bai faru ba to Allah ne bai nufa ba ya kamata abun ya tsaya iya haka a fuskanci juna ayi ha'kuri kaji".

Kai Alhaji Mukhtar ya d'aga bawai dan ya ha'kura ba a nasa 6angaren amma dan kada Alhaji Tajuddeen ya fahimci har yanzu bai huce ba kuma bayan ya isa dashi bazaiji dad'i ba yasa ya sassauta fuskarsa yace "shikenan Yaya Allah ya rufa asiri ya wuce Allah ya baiwa Nabilah miji na gari wallahi da ace ina da wani d'an bayan Sultan a gobe sai an d'aura masa aure da Nabilah amma shikenan" ya fad'a yana jan 'kwafar daya kasa danneta sannan ya mi'ke bai sake cewa komai ba ya fita a parlon jikin Sultan ne yayi mugun sanyi amma kunya ta hana yacewa Alhaji Tajuddeen wani abu kawai yaci gaba da zama a gabansa yana jiran yaji me zaice............

"Sultan".

Yaji ya kira sunansa da'kyar ya iya amsa masa cigaba Alhaji Tajuddeen yayi "karka damu kaji nasan ba lefin ka bane bazaka ta'ba yin haka ba Saboda kana da tarbiyya nina sani ba komai tashi kaje sannan duk wani abu da kasan baka yi ba na 6angaren auren ka da wancan yarinyar nima ubane kamar Mukhtar kai min magana zanyi maka komai kaji" da'kyar Sultan yace to kamar me ciwon cinya ya tashi jiki a sa6ule ya fita a parlon murmushi Alhaji Tajuddeen yayi yana jinjina kai ya sani gaskiyar Alhaji Mukhtar bata yabon kaiba Sultan yayi babbar asarar rashin auren Nabilah amma bazai gane hakan yanzu ba sai nan gaba, mi'kewa yayi shima yana fita a gidan domin dama akwai gurin da zaije dalilin maganar da Hajiya Fatima ta fad'a masa ne ya hanashi fita amma tunda yanzu an gama da shafin kuma yaga kiran Alhaji Ashraf maybe yana son ganinsa ne bari yaje ya sameshi..............✍️ YUSRAHMS CE.

#300
Acc: 2410673902
Nm: Yusrah Musa Zenith Bank

Mai son ci gabansa should DM me kayi min magana ta wannan number tawa 👉+234 816 098 3083 Yusrah Musa Abubakar.


Y A
°•°•° U R °•°•°
°•°•°•°•°. S °•°•°•°•°
°•°•°

YMA DUTSE NEW WORLD 🌏
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment