Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hira da dariya irin ta abokai da sallama ta shiga tana zama a kasan carpet tace.

"barka da zuwa Daddy ina kwana" kallonta Alhaji Ashraf yayi yana cewa.

"lafiya kalau Baby fatan kin tashi lafiya"?

"Eh Daddy ina lafiya".

"Masha Allah Baby lokaci yayi an kusa tafiya d'aki ko? Muma kwanan nan zamu girma zamu fara tara jikanu" ya fad'a yana juyawa ya kalli Alhaji Tajuddeen wanda shi kuma Nabilah yake kallo yace "amma dai abokina ni za'a baiwa wali ko"? Juyo da kallonsa kan Alhaji Ashraf yayi yana jinjina kai yace "eh me zai hana insha Allahu fatana dai Allah ya sanya alkhairi cikin lamarin ya shige mana gaba".

"Amin, Baby me kike so na kawo miki a matsayina na uba wacce kyautar kike so nayi miki wacce bazaki manta da ita ba"? Alhaji Ashraf ya tambaye ta daidai ta d'ago suka had'a ido lokaci guda zuciyar kowannan su ta buga da mugun 'karfi da sauri Nabilah ta d'auke idanunta tare da d'an dafe'kirji a hankali ta runtse ido tana cewa.

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un me yake faruwa haka"?.

Shima Alhaji Ashraf a nata 6angaren wani irin abu yaji da yanayi me wuyar fassara haka kawai yaji wani abu ya soki zuciyarsa wanda baisan ko menene kuma baisan me hakan yake nufi ba sai sabon kallo da zuba ido dayai mata batare daya ankara ba hankalin Alhaji Tajuddeen baya kansu yana ga TV baisan me suke ko a wanne hali suke ba tunda magana suke a tsakanin su shi bai shafeshi saida yaji sunyi shiru sannan ya juyo yana cewa.

"Uba da 'ya harkun gama maganar ne naji kunyi shiru"?.

Sauke numfashi Alhaji Ashraf yayi da'kyar cikin son fisge abinda yake neman hanshi sukuni ya samu ya janye idonsa daga kan Nabilah yana d'an girgiza kai yace "eh mun gama saidai bata fad'a min kyautar dazan bata ba amma ni nasan abinda zan bata wanda ya dace da ita zan kawo mata gifts guda biyu wanda ba wanda yayi zato" ya karasa maganar da murmushi akan fuskarsa da fara'a Alhaji Tajuddeen yace "alhamdulillah Allah ya baka iko abokina"

"Amin insha Allahu zan cika alkawari ai nina d'auka"..

"Ok Nabilah tashi kije dama kiran kenan Ashraf ne yake son ganinki aiki ya hanashi samun lokaci ya jima baku had'u ba shiyasa da Mamin ki tace kina barci nace ta taso ki jeki" to Nabilah tace tana mi'kewa ta fita haka nan taji lokaci d'aya jikinta ya mutu kamar wanda akai mata allurar kasala ko wacce rashin lafiya ke shirin kamata hatta yanayin kuzarinta da tafiyar jikinta ta sauya bata tsaya a parlor ba ta kama hanyar shiga part d'inta Hajiya Fatima data fito tana waya ganin inda ta nufa yasa ta kalli dinning yadda yake haka yake da alama Nabilah ko kallon wurin batai ba dakatar da ita tayi da cewa.

"Nabilah ina zuwa kizo kiyi breakfast man zaki koma bedroom".

Juyowa Nabilah tai muryarta a sanyaye ba kamar koda yaushe ba tace "ina zuwa Mami brush zan yi yanzu zan dawo" ok kawai Hajiya Fatima tace tana samu guri a d'aya daga cikin kyawawan manyan white and blue cushions d'in dake zagaye a parlon tana sake danna kiran Hajiya Zainab qawarta.

Tana cikin wayar Nabilah ta dawo ta sauya har kayan jikinta zuwa wasu kayan kanti 'kanana masu kyau tasa qaramin talhat bule black Hajiya Fatima na zaune tazo ta wuce ta karasa dinning tare da zama ta fara bubbud'a dishes dake gurin ganin akwai faten wake da bushasshan kifi yasa tayi serving d'insa ta zauna ta fara ci Hajiya Fatima tana gefe can nesa da ita amma duk abinda takeyi hankalinta nakai sai taga kamar bata cikin walwala akwai wani abu dake damunta so take yi ta gama wayar nan ta tambaye ta.

POV ALHAJI ASHRAF
Tunda ya dawo gida ya rasa me yake masa dad'i daya rufe ido Nabilah kadai yake gani da sauri zai bud'e a zabure yana maimaita innalillahi wa Inna ilaihi raji'un wannan wanne irin abun kunya ne wai meke damuna ne meyasa daga ganin Nabilah zanji hankali ya tashi me ya jawo hakan? Ya tambayi zuciyarshi amma baida amsa shiru yayi cikin rashin sanin madafa yanzu wazai tunkara da wannan tambayar wazai tara ya fad'a masa abinda yaji ya same shi a lokaci d'aya mene fassarar hakan maganar gaskiya yana son sani shidai ya sani bai d'au Nabilah matsayin komai ba sai 'yarsa bayan haka bayajin akwai wani abu game dashi a kanta amma ya kasa yarda da iya wannan hujjar daya samu tabbas akwai dalili, to kodai na fad'a son 'yar abokina batare dana ankara ba? Yaji zuciyarsa ta sharta masa haka wanda a razane ya bud'e idonsa dake rufe yana mi'kewa tsaya ya goya hannunsa a baya ya soma zaga parlon daga nan yayi can a fili ya soma cewa.

"Wacce irin 'kaddara ce wannan na rasa wacce zuciya ta zata kamu da ciwon so sai 'yar abokina? Subahanallahi wannan abun kunyar har ina Allah kasa ba haka zuciyata take raya min ba" ya fad'a yana cike hular dake kansa gashinsa ya ji'ke shakaf da zufa tsabar rashin nutsuwar da yake ciki d'ora hannunsa biyu tayi tun daga kan goshinsa har zuwa fuskarsa ya shafa yana sau'ke zazzafan numfashi me kama da zafin wuta tabbas yau ya shiga matsala da yasan idan yaga Nabilah wani abu zai gifta a zuciyarsa daya ha'kura da 'kara ganinta har karshen rayuwarsa baisan wanne irin tsautsayi ne ya fad'a masa ba a yau wacce irin damuwa ce take tunkaro shi taya zai samu mafita Alhaji Tajuddeen shine abokin shawarar sa baiga ta yadda za'ai yaje masa da wannan maganar ba a yanzu haka yana ji a ransa zai iya aure sa6anin da can daya sa a ransa cewa ba lallai yayi ba abun tambayar anan shine wanne dalilin ne yasa lokaci guda yaji hankalinsa ya karkata ga yayi auren bayan da ba haka yake ba ko maganar mace baiso ayi masa tun shekaru ashirin da biyar daya wuce lokacin da Alhaji Tajuddeen ya auri Hajiya Fatima yayita matsa masa shima ya nemi mace yayi aure yace masa a'a ba yanzu ba da haka har abun ya shige tun yana yi masa tayin auren harya kyale shi abun ya zama jiki da haka yau d'aya yaji son abun yazo masa humm wannan abun mamaki ne.............

Dawowa daga duniyar tunanin dayai zurfi a ciki yayi sakamakon jin qarar doorbell shiru yayi yana kallon kofar kamar me nazarin wani abu baije ya bud'e ba kuma bai daina kallon kofar ba an danna doorbell d'in yafi sau goma kafin ya baro inda yake yana dawowa ainishin parlon ya samu kujera ya zauna yana d'ora kafa d'aya kan d'aya tare da d'aukar remote ya danne kofar ta bud'e idonsa har lokacin yana kan wajen jira yake yaga waye zai shigo tsintar zuciyarshi yayi da fatan inama ace Nabilah zai gani,,,,, kamar a mafarki yaga Hajiya Sadiya ta shigo da sallama taci wanka ta d'au make-up kamar budurwa me 'kananan shekaru tasa ba'kin glass da wani d'an karamin mayafi handbag d'inta tana ma'kale a kafad'arta tayi kwalliyar 'kure maki babu ta inda ta ragu kallonsa kadai ya saukar mata da wata irin ni'ima da dad'i a cikin ranta tunda take a rayuwarta zata iya kirga shogowarta gidan Alhaji Ashraf baifi sau nawa ba shima da dalili sannan ba ita kad'ai bace a taron mutane ta 6angaren siyasa suke shigowa yaune kad'ai tayi wannan kasadar duk da batasan wacce irin tarba zaiyi mata ba Hajiya Bilkisu ta kirata a waya tace ta jirata tazo su taho tare abun zaifi mata sau'ki amma bata iya jiran minti biyar ba ta 'kagu kawai ta d'auko motarta ta taho...........

"Lafiya meya kawo ki gida na a wannan lokacin Sadiya"? Taji Alhaji Ashraf ya gefo Mata tambaya fuska babu annuri saboda yanayin da yake ciki, da mamaki Hajiya Sadiya ta kalleshi wato yana nan a yadda ta sanshi bai canza ba kenan tunda taji yayi mata irin wannan tambayar maimakon ya fara bata gurin zama ya kawo mata abun sha sai yace lafiya meya kawota gidansa? humm unbelievable.......

"Sadiya magana nake meya faru ya akai kika xo min gida batare da neman izini naba so kike ki jawo min matsala ne kinsan fa ba mace a gidan nan yawan ganinki da mutune suke zaisa su fara zargin kamar wani abu muke aikatawa please dan Allah d'aga yau karki sake zuwa gidan nan ki bari ko menene idan na fita saiki fad'a min ko kije office d'ina Ina ganin hakan zaifi dacewa yanzu a misali kin shigo idanun mutane yana kai sannan anga kin dad'e daga baya aga kin fita dole ne a zargi wani mutunci yafi komai shiyasa nake ro'kon ki da Allah karki sake zuwa inda nake kin gane"?.

Tunda ya fara magana Hajiya Sadiya ke kallonshi har ya gama kafin ta sake murmushi tana kashe ido tare da rausaya kai ta sake gyara d'aurin kwali ta dawo dashi gaban goshi duk tana kallon ta yayi tunanin juyawa zatai ta fita sai kawai yaga ta sake kama kujera ta zauna dis kamar a nata gidan harda yaye mayafin da take lullu'be dashi duk da bame girma bane medium ne da kadan ya zo mata rabin bayanta hannunta yad'au lalle jiki ma yad'au mai kud'i yayi kuka a kayan jikinta cikin kissa da launa harshe da karairaya tace.

"Haba my Ash meyasa koda yaushe idan muka had'u dakai baka da aiki sai kushe ni kana min gargad'i da kasan yadda na damu dakai nake shan wahala akan sonka da bakao wasu abubuwan ba haba Ashraf karka manta tun yaushe nake dakon sonka nake maka biyayya sau da kafa dan kawai ka amince ka aureni amma abun yaci tura please ka fad'a min mene aibu na mene abinda kake so nayi wanda xaisa hankalinka ya karkata zuwa gareni wallahi nayi maka alkawari idan ka aureni zan ri'ke gaskiya da amana ni tsakani da Allah nake son ka badan dukiyarka ko matsayin da kake kaiba ya kamata ka soni koda rabin wanda nake maka ne kaji dan Allah" ta karasa maganar a marairaice kamar zata fasa ihun takaicin sa ganin yadda ya tsume fuska ya had'e rai tasan yauma ba lallai ne tayi nasara ba domin ance labarin zuciya a tambayi fuska ko bai fad'a mata ba a iya yanayin da take gani akan fuskarsa ya isheta sheda sauke numfashi tai tana sake d'agowa ta zuba masa ido wanda tasa yaja dogon tsaki yana cewa.

"Sadiya tashi ki fice min daga nan kuma daga yau karki sake kuskuren zuwa gida na kome zaki fad'a min ki bari mu had'u a waje kin gane"?.

Mi'kewa Hajiya Sadiya tai tana gyara mayafinta tad'au handbag d'inta tare da kalonsa shima ita yake kallo fuska babu walwala tace "shikenan Ashraf kayi hakuri zan tafi amma dan Allah kafin na tafi Ina so zan ro'keka wata alfarma"?.

"Alfarmar me"?.

"Zan tafi saidai ina so dan Allah kayi min wani taimako please Ashraf dan Allah ka ri'ka bani lokacinka muna magana kaji tausayi na da kasan irin gararin da zuciyata ta shiga a dalilin sonka da bazaka sake min shariya a rayuwa ba yau shekara nawa ina binka ka aureni amma ka'ki meyasa me na gaza dame mata suka fini ka kalle ni dakyau ka gani babu nakasa a jikina" ta fad'a tana juya masa jikinta kawar dakai yayi jin yadda jikinsa yake neman shiga halin da bai ta'ba jiba wani irin abu yana yawo a jikinsa baisan feeling ba tunda bai ta'ba aure ba baisan me ya jawo masa jin hakan ba baisan sha'awa ba dan haka bai fahimci me yake damunsa a yanzun ba saidai ita Hajiya Sadiyan ta gane Kuma ta sani iya idonsa ta kalle ta saki murmushi tana jinjina kai a ranta tana jin yadda ya shiga yanayin nan inama ace yau ta aureshi da sun more rayuwa saita gwada masa dad'in da aure yake dashi saita susutar masa da 'kwa'kwalwa da hautsina masa lissafi ya gane cewa 'kin auren dayai shekaru masu yawa da suka wuce ba 'karamar asara yayi ba bai jiyar da kansa dad'i ba.................

"Sadiya fita anan".

Taji saukar muryar sa da sauri ta dawo cikin hayyacinta tana kallonsa tare da sake yin wata girgiza tace "ya ka ganni nasan na had'u koba haka ba"?.

Bai kalleta ba yaja tsuka yana d'aga mata hannu ganin tana neman jawo masa bala'i cikin son ta bar masa gida yace "shikenan naji jeki kawai".

"Naje kuma ka amince kenan zaka aure ni"?.

"A'a".

"Meyasa"?.

"Saboda bana jin hakan a raina".

"Dan Allah Ashraf kar muyi haka dakai zaka ji hakan a ran naka ni na yarda zan aureka na zauna dakai koda ace baka sona indai ka amince min"?.

"No ban amince ba dan haka ki 'kyale ni naji da damuwar dake damuna".

Da mamaki Hajiya Sadiya tace "haba Ashraf wacce damuwa ce kai kuma zata dameka a rayuwa kaiba d'aba ba jika ba amma mezai dameka"?.

"Babu ruwanki da abinda yake damu na kije kawai".

Kaita jinjina tana cewa "shikenan tunda kace ba ruwana amma nikam a ganina yanzu mun zama d'aya ko"?.

"A'a ke haka kike tunani"?.

"Eh haka na gani ma ba nake tunani ba".

"Yayi miki kyau pls ki tafi dan Allah" ya fad'a yana dafe kansa da yaji lokaci guda ya harbu da ciwo qureshi da kallo Hajiya Sadiya tai tana cewa "meyasa ka damu na tafi ne daka bari mun gama maganar zan tafi ai dakaina nazo kuma da kaina zan tafi idan lokacin tafiyar tawa yayi"?.

"Me kike nufi"?.

Kau dakai tayi tana cewa "ba yanxu zan tafi ba sai xuwa jimawa" tana rufe baki ya d'ago yana kallon ta kamar zaiyi magana sai kuma ya jinjina kai yana tashi taje kofar parlor tare da bud'ewa sannan ya juyo da hannu ya nuna mata hanyar fita da mamaki fal a ranta ta zaro ido tana kallon sa 'kara had'e rai yayi yana cewa.

"Me kike jira"?.

Gira ta d'auke batare da tace komai ba ta fara takowa da wata karairaya tana karkad'a jiki tazo zata fita kamar zata rungume shi da sauri ya matsa mata gefe amma duk da haka saida ta gogi jikinsa lumshe ido tai tare da sauke sansanyar ajiyar zuciya jin yadda ta shiga wani irin shauki ta juyo tana kallon sa tace.

"Ashraf ina son ka kuma insha Allahu saina aure ka kaine mafarki na gobe zan zo office d'inka zamu karasa maganar mu dan Allah so nake dana dawo daga Russia muyi aure amma bazan tafi ba saina tabbatar da an gama komai tsakanin mu ka huta lafiya" tana fad'in haka ta juya cikin taku ta fice zuwa inda tai parking da motarta tsaye Alhaji Ashraf yayi a gurin kamar me tunani yayi shiru zuciyarsa na sake dawo masa da abinda ya yake tunani d'azu kawai kallon Nabilah yake a idon zuciyarsa lokacin data d'ago suka had'a ido innalillahi wa Inna ilaihi raji'un lahaula wala quwwata illah billahil aliyul azim ya Allah ya ubangiji na ka cire min yarinyar nan daga raina wanne irin abun kunya ne wannan yake tunkaro ni me hakan yake nufi meyasa kullum da nake ganinta ban ta'ba jin wani abu game da ita ba sai yau"? Shiru yayi tsam yana sauke numfashi cikin d'umamamman yanayi wanda yake jinsa kamar yana gaban wuta ko gidan buredi zuwa wani lokaci ya sauke zazzafan numfashi yana mayar da kofar parlon ya rufe tare da juyawa bai tsaya a parlon ba ya wuce bedroom domin yayi wanka ko ya d'anji dad'in jikinsa saidai yadda yake ji a ransa dole bazai iya barci ba sai yaje yaga Nabilah koda ace zai samu nutsuwa a ransa da yayi tunanin bata kyautar da yake nufin bata sai ranar d'aurin auren ta amma yanzu dole ya dau'ki d'aya cikin biyu yakai mata kodan ya samu ganin nata.

••Washe gari tun safe Nabilah take kiran Husnah tazo ta taya ta had'a wasu abubuwan tace mata Momynta ta aiketa gidan Hajiya Bilkisu kuma daga can zata je d'an masara gurin wata 'yar uwarsu amma nan da la'asar zata dawo insha Allahu zata zo a gurin ta ma zata kwana jin haka yasa Nabilah farin ciki domin a rayuwa tana matukar son Husnah har batasan yadda zata kwatanta ba tunda suka gama waya ta fara tanadar mata abinda idan taxo zata tarbeta dashi.

Tun bayan sallar la'asar take zuba ido amma babu alamar Husnah gashi ta kira wayarta network ya hana ta shiga tashi tai tana d'an zaga bedroom d'in ko zata samu ta shiga ba zato taga kira ya shigo wayar tata da ba'kuwar number duk zaton ta ma Husnan ce saidai me tana d'agawa taji muryar namiji mamaki ne ya kamata tunda taji ba Sultan bane har d'auke wayar tayi daga kunnenta ta zubawa numbar ido bata ganeta ba maidawa kunnen tayi tana cewa.

"Hello".

Daga can 6angaren taji ance "Emm ya kike Nebilah"? Jin muryar da batai zato ba yasa da sauri ta sake cire wayar a kunnenta tana kallon secreen d'in cike da mamaki taya akai Sir Ahmad ya samu numbern ta harya kirata a Ina ya samu ta tabbata Husnah bazata bashi ba to waye ya bashi? Katse mata tunani yayi da cewa "fatan kin gane me magana"? Shiru Nabilah tai ranta in yayi dubu ya 6aci cigaba Sir Ahmad yayi "idan baki d'au murya ba Sir Ahmad ne Ina son zamuyi magana dan Allah ki fito yanzu zaki koma minti goma yayi yawa" yana rufe baki Nabilah ta zaro ido tana cewa.

"Na fito kuma"?.

"Eh ki fito".

Cikin fargaba tace "me zanyi maka idan na fito d'in wacce irin magana ce zaka fad'a min bazata fad'u ta waya ba"?.

Kaiya jinjina mata kamar tana kallon shi yace "eh dole sai gani gaki zaki fi fahimta ta sosai" kaita girgiza tana cewa "gaskiya kayi hakuri Sir Ahmad bazan iya fitowa ba idan zaka fad'a min ka fad'a idan bazaka fad'a ba ka rabu dani" jin zata kashe wayar yace.

"Nabilah please dan girman Allah ki fito yanzu zaki koma wallahi ba wani abu bane kawai Ina so muyi sallama ne zan bar na yanki state namu zan koma so nake na sake ganinki koda sau d'aya ne ganin 'karshe kuma na miki fatan alkairi tunda naji ance aure zaki dan Allah Nabilah ki fito" shiru tai jin ya hadata da girman Allah yasa babu yadda ta iya bari taje tunda tafiya zaiyi tasan duk tsiya daga yau shikenan mi'kewa tai ta dau'ki hijab din'ta tana fita can nesa da gidansu ta ganoshi yana tsaye a jikin motarsa karasawa tai fuskarta a mugun had'e dan kada yaga wata kofa dazai samu damar fad'a mata maganar banza tana zuwa taja ta tsaya a dake bayan tayi masa sallama amsawa yayi yana murmushi ya kalleta yadda tayi kyau yace.

"Shigo muje" shine abinda taji yace yana nuna mata motarsa wani irin kallo tai masa tana cewa "na shiga muje zuwa ina kenan"?.

"Wani wuri zaki rakani yanzu zan dawo dake ina so zan baki gifts ne na aurenki to bansan wanne zaifi miki kyau ba kizo muje ki za'ba da kanki saina dawo dake maganar kuma ko a hanya mayi" kaita girgiza tana cewa "ni bazan je ko'ina ba kyauta Kuma nagode idan bazaka fad'a min dalilin kirana dakai min ba zan koma" ta fad'a tana shirin juyawa yace "Nabilah" haushi ne ya rufeta domin ko shine ya rad'a mata sunan iyaci kenan ya iya bud'e murya ya 'kwalla kiran mutum kamar sabon makaho........

"Nabilah dan Allah kizo muje yanzu zan dawo dake ko minti goma bazan ba" tsayawa tai cikin takaici to uban me zaiyi mata mene hadinta dashi mezai nuna mata Ina zata rakashi............

"Please Nabilah muje dan Allah nayi miki alkawari yanzu nan zan dawo dake idan ma bakya bu'kata zansa me napep ya dawo dake" jin abinda yace yasa a fusace ta juyo tana cewa "Sir Ahmad nifa irin wacce ka dauka bace ni ba 'yar iska bace aina gane manufar ka wato na bika ka lalata min rayuwa shine 'kudurinka ko? Humm Allah ya toni asirin ka kuma insha Allahu mugun nufinka saidai ya qare a kanka".

Murmushi Sir Ahmad yai yana girgiza kai ya kalle ta kafin yace "Danual" waige waige ta farayi jin yana kiran sunan wani wato tarko yake neman hada mata zatai magana ganin wani ya fito daga cikin motar yasa kawai jiki ya bata akwai wata 'kullalliyar da Sir Ahmad ya shirya juyawa tai da sauri zata tafi gida sai gani tayi Danual yasha gabanta tare da nuna mata wani abu a hannunsa yace "muje" lokaci guda taji jikinta yayi sanyi ta kasa bud'e baki ta furta masa kalmar cewa bazata jeba wani irin murmushin mugunta Sir Ahmad yayi yana bud'e murfin mota yace "Nabilah shiga mana yanzu kam bazaki musa min ba kome nace miki" ya fad'a yana kallonta babu musu ta tako ta shiga kamar wacce ya rufewa baki da sauri ya rufe motar shima ya shiga Danual ma ya shiga tada motar yayi suka bar wurin sun d'anyi tafiya me nisa Nabilah da taji kanta yana juyawa wayarta ta dauka a 6oye suna gaban mota ita Kuma tana back seat text ta turawa Husnah domin taji inda yace zasuje ta fad'a mata cewa ga abinda Sir Ahmad d'in yayi mata Kuma ta kasa bud'a baki tayi masa magana dan Allah ta biyo bayansu kar ya cutar da ita.

Har gaban hotel d'in suka je Saida yai parking ya fito yana bud'e Mata itama ta fito ciki suka shiga tana binsa a baya har suka shiga ciki sosai wani d'aki me shiru juyowa yayi yana kallon ta yasa dariya yana cewa "Nabilah me wayo barka da zuwa dama ba komai zan fad'a miki ba so nake ki taya ni kwana anan yau" yana rufe baki ta zaro ido waje tare da girgiza kai da sauri jikinta na mugun rawa ta soma ja da baya tace.

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un Allah yamin tsari dakai mugun mutum dama rayuwata kake neman lalata min insha Allahu bazaka ta'ba cika burinka a kaina ba nafi karfin ka wulakanta ni domin niba irinka bace niba 'yar iska bace".

Jin abinda take fad'a yasa yayi murmushi yana cire kayan jikinsa dan taga zahiri cewa yau ko zata mutu sai yayi disvirgin d'inta daga shi sai gajeran wando ya sake nufota da karfin gaske yakai mata runguma a susuce ta goce hawaye na zuba a idonta tuntu'be Sir Ahmad ya kwasa domin ya riga da ya kawo karfi sai gashi ya fad'i qasa timm ganin haka yasa da sauri ta bud'e kofa zata fita shima da mugun sauri ya mi'ke yana ri'ke hijab din'ta ya jawota baya tagal-tagal tai zata fad'i ya tareta yana rungumarta ihu ta zunduma cikin tashin hankali daidai ya fisge hijab d'in jikinta daga ita sai doguwar riga a susuce tasa hannunta akan kirjinsa tayi masa wata muguwar hankad'a wacce bai ta'ba tunanin tana da irin wannan karfin ba bazato ya jishi ya yar6u a 'kasa ya fad'i akan hannunsa har qara yayi ganin ya tsaya ri'ke hannun yasa a hargitse cikin azama ta fita da gudu daga d'akin ko tsayawa d'aukar hijab d'in batai ba domin tsoron karya tashi ya sake kamata tana fitowa daga cikin hotel d'in da gudu daidai motar Husnah tayi parking da gudu itama ta bud'e kofa ta fito ko rufewa bata tsaya yiba ta shiga ciki a guje kamar wacce ta zare tana kwalla Kiran Nabilah Nabilah Nabilah kamar an jefo Nabilan haka ta ganta ta fito daga wani guri da gudu ko kallon gabanta batayi batama kula da Husnan ba a gigice tazo zata fice rikota Husnah tai wanda Nabilah ta fasa qara a a razane tace.

"Na shiga uku na lalace dan girman Allah Sir Ahmad karka lalata min rayuwa wayyo Allah ka sakeni" rungume ta Husnah tai tana cewa "ki kwantar da hankalinki Nabilah Allah ya tsare ki nice Husnah na zo ki dawo cikin nutsuwar ki" jin muryar Husnah yasa Nabilah d'agowa daga jikinta tana kallonta sai kawai ta fashe da wani azababbar kukan damuwa tana cewa "shikenan Husnah Sir Ahmad ya cuce ni bazan ta'ba yafe masa ba ya yaudare ni ya kawo ni nan yana neman keta min kimata".

Hankali tashe Husnah take kallon Nabilah wacce ke kuka tace innalillahi wa Inna ilaihi raji'un fatan baiyi miki komai ba Beelat"? Ta fad'a tana qare mata kallo cikin kad'uwa da'kyar ta Nabilah ta iya

Please Login or Register in order to submit comment