Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ma'aikata tuni suka dam'ke su a gurin tare da sanya musu ankwa jami'in daya ji akan me suke maganar yace.

"Waye d'ayan da kuke magana a kansa"?.

Shiru Danual yayi cike da taurin kai alamar bazai fad'a ba marin da jami'in ya kifa masa har saida bakinsa ya fashe jini na fita cikin tsawa yace "zaka fad'a ko saina tashi kanka da bullet"? Ya fad'a yana d'ora masa bindiga a saman kai tare da d'ana kunamar kamar zai saki a rud'e Danual yace.

"Zan fad'a kayi hakuri zan fada" dan Allah".

Janye bindigar yayi yana mi'kewa yace ina jinka yanxu kayi magana fad'a min".

"Ba laifi na bane wani ne yasaka mu aikin kud'i ya biya mu".

"Waye ya saka ku ina yake"?.

"Yana gidan sa".

"Ina ne gidansa"?.

"Wajen can haka ne gaba da nan".

"Ka tabbata yanzu yana gidansa za'a sameshi"?...

"Eh yana gida jiran mu yake".

"Ok kira mana shi".

D'ago hannu Danual yayi yana nuna musu ankwar da suka d'aura masa yace "bazan iya daukowa ba tana aljihun wando na".

Jin abinda yace yasa jami'in zura hannu a cikin aljihun Danual ya d'auko waya yace "mene securityn"? Fada masa yayi ya rubuta bayan ta bud'e ya fad'a masa number ya kira tana shiga Sir Ahmad ya d'aga yana cewa "hello Danual me kake har yanzu baku taho mun tafi ba"?.

Datse kiran jami'in yayi yana kallon Danual yai qasa da murya yana cewa "ka amsa masa idan ya kira kuma kada ka kuskura ka nuna masa mun kamaku kuna hannun mu kayi masa magana a nutse kai Danual ya d'aga yana cewa to daidai kiran Sir Ahmad ya shiga karawa Danual a saitin bakinshi yayi bayan ya d'aga daga can 6angaren sir Ahmad yace.

"Hello Danual ina jiranku fa a ina kuka tsaya ne harna fito da mota waje kuyi sauri mana".

Kai Danual ya jinjina yana cewa "am kayan namu ne yayi yawa bazamu iya kawowa ba kazo da motar saika d'auke mu" ok kawai Sir Ahmad yace yana katse kiran wayar jami'in ya mayar masa yana kallon sauran 'yan uwansa yana cewa "yanxu abinda zai faru kowa ya samu guri ya 6uya ku kasance cikin shiri amma kada kuyi harbi" amsa masa sukai tare da bazuwa a gurin kowa ya la6e agu me duhu can hasken fitilar motar Sir Ahmad ya tunkaro gurin ganin motocin jami'an tsaro kusan guda uku a gurin yasa jikinsa ya bashi akwai wata matsala karya kwana yayi da sauri ya juya yana baiwa motar giya aguje jami'an suka fara fitowa tare dabin bayansa da gudu suka fara harbin tayar motar tuni iskar tayun suka sace amma bai daina gudu ba har saida yaje ya daki bishiya kan motar ya mokad'e sannan ya tsaya a bisa dolensa cikin azama ya bud'e murfin motar ya fito daidai sun karaso zai zuba da gudu suka ri'ke shi batare da sunce masa komai ba suka saka masa ankwa shima cikin tsaurin rai da karfin hali yace.

"Yalla'bai me nayi muku"?.

Wani irin kallo ya watsa masa yana hankad'a 'keyarsa suka fara tafiya zuwa gurin motocin su yace "ban sani ba ka idan munje zaka ji abinda kai" shiru Sir Ahmad yayi bai iya cewa komai ba sai gabansa daketa dukan d'ari d'ari cike da fargabar ya zaiyi ya kare kansa yanzu hankalinsa bai sake tashi ba saida aka jefa shi cikin mota yaga Danual da Nazzi saidai ba damar yayi musu magana yana ji yana gani aka tafi dasu zuwa bayan kanta aka rufe,, a daren akai Kiran Alhaji Tajuddeen aka sanar dashi an samu wadanda ake zargin da saka hannunsu a sharrin da akaiwa Nabilah kasa nutsuwa Alhaji Tajuddeen yayi a lokacin ji yake bazai iya bari sai gari ya waye ba a take ya tafi Saida yaje yaga Sir Ahmad da Danual da Nazzi ji yayi wani irin 6acin rai ya rufeshi yaso ace anyi musu shegen duka tun a daren amma wani tunani yaxo masa tunda ba'ai bincike ba Bari ya barwa gobe.

Gida ya koma amma bai iya runtsawa ba har nisan dare ya gani tsabar 'kaguwar da yayi gari ya waye asubar fari ya fita masallaci bayan anyi sallah bai dawo gida ba tare da Alhaji Mukhtar da Alhaji Ashraf suka tafi gurin wancan case d'in.

Alhaji Ashraf yafi kowa fusata da tozarcin da sukaiwa Nabilah shine ya bada umarnin a nad'a musu mugun dukan da azaba zata saka su duma wuya ta farfad'o dasu sannan baice a sassauta musu ba ko mutuwa zasuyi kafin azo kan dalilin kama sun da akai.

Danual akwai bala'in tsoro tun dukan bai gama tsara masa jiki ba ganin ana neman hallaka shi ga tsawa da barazana shine ya fara fad'ar gaskiyar aikin da Sir Ahmad ya sashi yayi masa Nazzi ma ta fad'i cewa ba Nabilah bace wacce akai wannan abun da ita itace fuskar Nabilah kawai tasa domin biyanta Sir Ahmad yayi.

Amma abun daya baiwa kowa mamaki da aka tambayi Sir Ahmad sai yayi tsalle ya dire yace sam sharri sukai masa bai bai sasu aiki ba baisan komai ba yin duniya ya furta cewa shine yaiwa Nabilah haka amma ya'ki amsawa yace shi bashi bane an d'auki kusan sati biyu ana yiwa Sir Ahmad tambayoyi da Kuma shedu 'karara hatta Husnah da Nabilah saida suka zo sannan suka fadi abinda ya faru yace ina shifa bai aikata ba abu kamar wasa harya tafi wata guda sir Ahmad yana kan bakarsa shi baisan komai ba karshen wasan da yaga azaba da mutuwa 'kiri-'kiri ana nemam hallaka shi da'kyar aka samu ya bud'e baki ya fad'i gaskiyar lamarin da yadda komai ya faru tun daga ranar daya fara ganinta har zuwa ranar da yazo kofar gidan su Nabilan da sigar yaudara ya d'auketa zaije ya keta mata mutuncinta kuma bata amince ba ta fice a d'akin bayan ya cire mata hijab......................

Yana gamawa ko baki bai rufe ba Alhaji Tajuddeen ya kifa masa mari tare da mi'kewa ya dam'ki wuyansa idonsa jawur ya soma aika masa naushi cikin tsananin 6acin rai ganin xaiyi masa illa yasa da'kyar Alhaji Mukhtar da Alhaji Ashraf suka 6am6are shi jikinsa na sewa yake kokarin 'kwacewa amma basu sake ba domin idan ransa ya 6aci yana da wuyar dawowa daidai kawai janyeshi sukai suna fita dashi daga gurin sir Ahmad kam yana yar6e a kasa ya kasa tashi tsabar nuna da jikinsa yayi da azabar duka sai zuwa akai aka daukeshi ana mayar dashi aka rufe Alhaji Tajuddeen bai bar ofishin ba saida ya tabbatar an gama komai ya yanki takardar sammaci wacce zasu shiga kotu alkali ya yanke musu hukunci sannan suka koma gida.

Ganin irin ba'kar azabar da Sir Ahmad yasha yasa da aka zo gaban alkali gudun abinda zai sake faruwa dashi ana tambayarsa gaskiyar mene abinda ya faru tsakanin sa da Nabilah ya fad'a komai baiyi 'karya ba sannan aka tambayi Nabilah haka ne tace eh Danual da Nazzi ma suka fad'i iya aikin dayasa su sukai masa ya biyasu kud'i me yawa nan ma aka tambayi Sir Ahmad haka ne gaskiyar abinda ya faru yace eh haka ne yayi kuskure amma dan Allah a yafe shi a take Alhaji Tajuddeen yace babu wanda zai yafeshi idan ma yana tunanin Nabilah ce zata yafe masa to yayi hauka dan wallahi baiga dalilin da zaisa Nabilah ta yafewa Sir Ahmad ba dole sai an yanke masa hukunci kowa haka yake cewa tabbas ayi masa hukunci shine daidai yanxu idan aka sakeshi ba'a dau mataki a kansa ba an bashi damar yaje ya sake aikatawa wata budurwar haka ko wani a gefe wanda yaga abinda Sir Ahmad d'in yayi Kuma ba'a d'au mataki ba yaji sha'awa shima ya aikata gara a bashi hukunci daidai da lefinsa bashi ba wani ma saiya kiyaye daga shi har Nazzi da Danual babu wanda aka sake dukka aka kaisu gidan maza su zauna daidai da lefinsu da kuma rubutacciyar takarda me nuni da cewa ba Nabilah ba Sir Ahmad har abada kotu tayi musu iyaka sannan a gaban jama'a kowa da kowa aka wanke Nabilah daga zargin da ake mata na watsi da tarbiyyar da aka bata sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta abinda ta dad'e batai ba wato murmushi a ranar shi tayi ta rungume Alhaji Tajuddeen da kukanta na murna tana yi masa godiya sannan taiwa Husnah godiya itama wacce ta tsaya tsayin daka har saida ta kawo karshen zaluncin da Sir Ahmad yayi mata tun daga wannan ranar shikenan aka rufe babin Sir Ahmad Nabilah ta d'auke hankalinta a gurin ta manta da abinda ya faru tsakanin su gudun ta ri'ka tunawa tana d'orawa kanta damuwa hakan baida amfani.

Duk wannan gwagwarmaya da ake ta kashe case d'in Nabilah Sultan baice 'kala ba kuma koda wasa bata sake ganinsa ba tun daga ranar kamar wanda yabar garin haka yanzu ya dawo babu inda yake zuwa saboda damuwa da d'acin dake cin ransa daga hospital sai gida kullum hatta magana ya daina yi ba sosai ba.

Yauma kamar kullum da yake weekend ne baije ko'ina ba tunda gari ya waye har kusa sha biyu na rana ko breakfast da yake fita yayi yau baije yayi d'in ba yana kwance idonsa na kallon pop d'in d'akin bud'e kofar bedroom d'in akai ana shigowa amma bai d'ago ba balle yasan waye ya shigo.

Tsaye Hajiya Salmah tayi a bakin kofar shiga tana kallon yadda gaba daya yabi ya rame akan abinda ya faru ji tai takaici ya rufeta 'bacin rai ya baibaye mata zuciya karasowa tayi tana zuwa kansa ta tsaya tana cewa "Sultan yau ko breakfast baka fita kayi ba saboda da tunanin wannan tsinanniyar yar iskan yarinyar ko? wai me yake son mayar da kanka akan wata banzar mace mara kamun Kai kana ganin fa yadda ta bayyanar da tsiraicinta ga wani tsinannan idan har ka aureta mene ribarka taya kake zaton zaka manta da haka?.

Ganin har lokacin yayi shiru kuma bai motsa ba yasa Hajiya Salmah fitar da huci me turiri tana jinjina kai a ranta tace "amma gaskiya su Alhaji Tajuddeen sun cuceni babu abinda zance saidai Allah ya isa tsakani na dasu indai dalilin wannan bankad'addiyar yarinyar tasa ka zama haka ni fatana ma Allah yasa kada hawan jini ya kamaka" a fili kuma juyawa tai zata fita daga bedroom d'in ranta a 'bace har takai bakin 'kofa ta dakata batare data juyo ba tace.

"mahaifin ka na nemanka nasan akan maganar wannan 'yar iskan fitsararriyar yarinyar ne Nabilah maybe zaice kayi hakuri ne ka d'au kaddara baza'a fasa ba a rufawa juna asiri hum'um to wallahi bari kaji kada ka yarda ka amince idan kuwa ka yarda sai mun raba hanya dakai wallahi tallahi kaji na rantse ko? Karka amsa zaka aureta domin naji yana cewa "komai ya wuce wai wani anyi bincike an gane sharri aka had'a mata wani saurayi ne lecturern su a school ya biya wasu kud'i aka 6ata mata suna ba ita bace wata arniya ce tasa fuskarta humm ma'karyatan banza duk da haka ni dama dan ka nace ne amma wannan yarinyar Nabilah batai min ba bata cikin kalar 'yan matan da nake so su zama surukai na ka gane muje yanxu ni dama haka nake so kullum fatana Allah ya kawo silar wani tsautsayi ya gifta wanda xai hana yuwuwar auren nan Ashe zanga wannan ranar gashi Allah ya kawo mu burina ya cika dan ko mutuwa zatai bazaka aureta ba wallahi kaji na rantse muje" ta fad'a tana yin gaba mikewa yayi yana saka takalminsa yabi bayanta fuska a had'e babu walwala har suka je parlor inda Alhaji Mukhtar yake zaune su Rasheedat yasa su tashi su bar parlon zasuyi magana saida ya rage su uku ya kalli Sultan yana cewa.

"Abdul-azeez kasan abubuwan da suka faru damu kwanan nan na damuwa da tashin hankali da fituttunun da sukai ta afkuwa wanda yasa gabadaya duniyar ta canza mana cikin 'kanqanin lokaci sakamakon kallon da mutane suka koma yi mana akan Nabilah da wani 6ata garin yaro yaso yi mata sharri kai kasan komai tunda kaima ya baka waya ka kunna ka gani to amma yanxu alhamdulillah domin hausawa sunce ciki indai gaskiya wuka bata huda shi kamar yadda ya faru akan Nabilah batasan komai ba yayi nufin 6ata mata suna ya 6atawa mahaifanta da ma mu da muke family d'aya shi wannan saurayin sunansa Ahmad Samual ya kasance d'an kudu ne ya nemi had'in kan Nabilah ta soshi ta aureshi amma saboda kai ta'ki amincewa hakan datai shi kuma yadau zafi da ita har yayi nufin jefa fitina a tsakanin ku lallai a ranar ya bukaci Nabilah ta fito kofar gida akwai abinda zai fad'a Mata amma kafin taje saida ta Kira kawarta ta fad'a mata cewa tabi bayanta Koda wani abu yaso aikata Mata yayi amfani wata 'yar arna mai suna Nazzi da kuma wani saurayi mai suna Danual ya dau kwafin fuskar Nabilah wannan Nazzi d'in tasa a matsayin Nabilah da ita aka had'a baki akai wannan videos d'in ya biyata kud'i hakika dukkanin mu mun zargi Nabilah a rashin sani wanda a zahiri kuma ba haka abun yake ba sai yanzu da muka gane gaskiya sannan ina fatan kaims Abdul-azeez zaka fahimce ta sannan zaka bar zarginta domin bata san komai ba idan Allah ya kaimu ranar juma'a za'a d'aura muku aure insha Allahu a babban masallaci juma'a"?.

Yana rufe baki Sultan ya girgiza batare daya d'ago fuskarsa ya kalli mahaifin nasa ba yace "a'a Daddy abar maganar nina ha'kura da auren Nabilah na fasa bazan aureta ba zan nemi wata wacce na tabbatar koda bana nan bazata ci amana taba amma Nabilah ba matar da za'a aura a zauna da ita bace domin ta gama zubarwa da kanta mutunci a idanun jama'a koda ace da gasken ba ita bace amma ai idan wasu sun yarda wasu bazasu yarda ba ni a yanzu na cireta a zuciyata na daina sonta bazan ta'ba aureta ba har abada ka gafarce ni idan na 6ata maka Rai Daddy" Sultan ya karasa maganar yana qara had'e girar sama data 'kasa dan a yadda yake ji a ransa ko farfesun sa Alhaji Mukhtar zaiyi a yanzu bazai iya auren Nabilah ya had'a jiki da ita ba bayan ta gama baiwa wani namijin titin kanta to waya sanima koba iya dashi kad'ai take mu'amala ba akansa asirinta ya tonu.

Cike da tsananin mamaki Alhaji Mukhtar ya qure Sultan da kallo yana cewa "Sultan ni kake cewa bazaka iya aurenta ba dama Ina ganinka haka ashe baka da hankali kaima koda ace da gaske ake Nabilah halinta kenan a tunani kai me rufa mata asiri ne ka aureta ban ta'ba kawowa a raina zaka fad'i irin haka ba kayi hauka ne me kake nufi da cewa zata ci amanarka wato abinda mutane suke fad'a ada ya shiga kunnen ka kenan ko? har zaka tsaya fad'i in fad'a dani saboda wani banzan tunaninka to bari kaji indai nine mahaifin ka na isa dakai saika aureta kaji na fada maka tashi kaban gu" Alhaji Mukhtar ya karasa maganar a fusace.

Jin abinda yace yasa da sauri Hajiya Salmah dake gefe tana jijjiga kai ta tsomo baki batare da an bata izinin magana ba tace "to Alhaji ya za'ai Sultan da hankalinsa da tarbiyyar sa yarda ya aure ballagaza jakar mats bayan ga abinda ya faru wallahi Nabilah ta 6ata muku ahli ko zakaji haushi na saina fad'a ashe dama yaudararsa take bayan ta gama wulakanta kanta a titi gurin wani shegen wanin tambad'dd'an d'an iskan saurayi irinta d'an duniya mara asali tsintaccen kan hanya wa yasani ma ko ba iya shi kad'ai take kulawa ba dama can take saba akansa ne asirinta ya tonu gashi abun ba'kin ciki ubanta sananne yanzu ta zubar masa da mutunci ta 6ata masa suna a gari humm bama iya gari ko jiharmu ba a duniya gabadaya zance tunda yace zai yad'a videon wa yasan iya inda abin zai tsaya dan kawai anyi shari'a an kashe case d'in toni a guna bai kasu ba wallahi tallahi Alhaji kome zakai kaji rantsuwa ko? Wallahi Sultan bazai auri Nabilah ba har abada domin shi bai kasance d'an iska kuma fasi'ki kamar taba taje can ta samu irinta mazinaci ta aura..............................................


Tana rufe baki Alhaji Mukhtar ya d'auketa da mari wanda ba ita daya mara ba hatta Sultan saida ya zabura yana matsawa baya ya d'auka shi zai kawowa dukan itakam a gigice ta fara ihu tana tsalle-tsalle da kuka kamar yarinya ta fad'i a kasa harda burgima tana cewa.

"Na shiga uku na lalace Alhaji akan na fad'i gaskiya shine kake neman makanta ni wallahi tallahi kome zatai Sultan bazai auri Nabilah ba idan kuwa ka matsa saiya aureta ni saidai ka sake ni gara nabar maka gidan inyaso saika zauna da Nabilan amma nikam bazan ta'ba kallonta a matsayin surukata ba wallahi Allah ya sauwa'ke saida ta gama tallar kanta a titi sannan za'a takurawa d'ana a cusa masa ita salon ta saka masa cutar data kwasa a gurin tsinannun mazan da take bi".

Tunda Alhaji Mukhtar ya mi'ke ya mareta bai koma ya zauna ba harta gama maganganun ta sannan ya jinjina kai yana cewa "dama ko baki fad'a ba daga yau bazaki sake kwanar mun a gida ba ki tashi ki tattara dukkan abinda kikasan naki ne ki barmin gida na sake ki kai Kuma zan dawo kanka" yana karasa maganar yana nuna Sultan da yatsa cikin fushi kafin ya juya ya fice daga parlon kururuwa Hajiya Salmah keyi tana yage-yage kamar me ciwon hauka Sultan dake zaune jin abinda Alhaji Mukhtar d'in yace ya ta'be baki yana mi'kewa yaje ya dagata yad'au kwalinta ya mayar mata kanta yana kallon yadda hannun Alhaji Mukhtar ya fito d'arr a fuskarta har bedroom ya kaita ya d'ebo mata ruwan zafi tana d'und'uma fuskan nata shi kuma ya fara had'a mata kayanta a cikin akwatuna mi'kewa tai tana saka hijab d'inta ta ja trolley d'aya ta fita dashi zuwa harabar gida Sultan ne ya d'ebo mata sauran ya saka a mota ta shiga ya kaita gidansu acan wurinta ya zauna bai dawo gidan ba saboda haushin marin da Alhaji Mukhtar yayiwa mahaifiyar sa.

Su Rasheedat basu san me yake faruwa ba sun dawo daga anguwa da basuga Hajiya Salmah ba sunyi tunanin ko taje anguwa ne amma ganin shiru yasa abin ya basu mamaki sunyi kiran wayarta ta fad'a musu abinda ya faru d'azu tsakanin su har ya saketa yanzu haka tana gida gobe da safe suzo tana nemansu karaf a kunnen Alhaji Mukhtar ya shigo yaji me Hajiya Salmahn take cewa da sauri ya karaso a fusace ya kar'be wayar ya fasa ta sannan cikin murya me nuni da tsantsan 6acin rai yace musu duk wacce tsautsayi yasa ta kuskura taje inda Hajiya Salmah take sai ya d'au tsattsauran mataki a kanta.

🙇🏻‍♀️AYI HA'KURI YAU TYPING D'IN BA YAWA.

We will meet again nagode.

11~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil 'Kaiminah.

Manzon Allah s.a.w
Kaine me kyau ganinka yafi zama d'an aljannah a kyanka ne akai kyan matan aljannah gabanka kyau yana komawa mummuna ai anta ajamalul kal'ki nabiyur-rahma ya sibgatullahi ni kai min alfarma na ganka ko a barci baban Fad'imah ya shugaba cika mini burin 'kalbina.

YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨✨
🌹🌷🌹🌷🌹🌷🌹🌷🌹🌷🌹🌷🌹🌷


TYPING📲 Tue, Jan6/25 8:24AM
YUSRAH MUSA ABUBAKAR 🤘💯.


💕Minister Ashraf💕


💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫
🕳️Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta haka taken mu yake.


STORY WRITTEN ND EDITING
📝✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë.


12~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Kaidinah.

BISMILLLAHIR RAHMANUR RAHIM 📿.

💦Yüsëëñ Sïr Äl-ämëëñ çë💦
PG____13&14
Bayan lafawar komai Alhaji Ashraf har gida yazo domin yayiwa Alhaji Tajuddeen jajja6in abinda ya faru amma sai yake masa wata magana wacce baiji dad'inta na musamman daya fahimci kamar Sultan ya 'ki amincewa da auren Nabilah har lokacin ya'ki yarda sharrine kallon Alhaji Tajuddeen yayi yana cewa.

"Kayi hakuri dan Allah Tajuddeen abinda ya faru naji kana cewa Sultan ko d'aga wayarka bayayi balle yazo kuyi magana akan Nabilah kardai kace min ya fasa auren ta meyasa ya fasa d'in"?.

Cike da damuwa Alhaji Tajuddeen ya girgiza kai yana cewa "ban sani ko fasawar yayi amma alamun 'karfi yana game 'kiba tunda har kaga take taken sa hakan yake nufi nikam bansan yadda zanyi da wannan al'amarin ba kaina gabadaya ya kulle" ya karasa maganar yana yana dafe Kai cike da takaici dafa kafad'ar shi Alhaji Ashraf yayi cikin rashin jin dad'in ganin irin kaddarar data samu abokin nasa yace. ..

"Subahanallahi Allah ya rufa asiri kayi hakuri Tajuddeen insha Allahu koda ace Sultan ya fasa Nabilah bazata rasa mijin aure ba balle bama fatan ya fasa d'in za'a san yadda za'ai ayi auren ni ka hadani da Sultan d'in ka tura min shi muyi magana dashi ko ka bani number wayarsa nasan abinda zan fad'a masa wanda komai zai wuce" kai Alhaji Tajuddeen ya girgiza yana sauke numfashi yace.

"Sultan yana da taurin kai tunda har yace ya ha'kura bazai dawo ba kome za'ai masa bazan ma 6ata bakina ba kawai ka manta da al'amarin insha Allahu Nabilah zanyi aurenta ko bada Sultan ba muje ka duba ta tana bedroom bata jin dad'i" ya fad'a yana mi'kewa shima mi'kewa Alhaji Ashraf d'in yayi yana cewa.

"Bata da lafiya meyasa baka kaita asibiti ba"?.

"A'a na kaita asibiti kusan sau uku wannan zuwan karshen ma har gado aka bata kwanan ta goma aka bata sallama muka dawo gida abun ne sai a hankali muje ka dubata".

"Ok" Alhaji Ashraf ya fad'a suna shiga bedroom d'in Nabilah a zaune suka sameta ta jingina bayanta da fuskar gadon ta zubawa guri d'aya ido hawaye ya ji'ke mata fuska shakaf girgiza kai Alhaji Ashraf yayi yana d'an sunkuyawa kad'an yace "sannu Nabilah ya jikin naki"? A hankali ta d'aga kai muryarta yana fita da'kyar sakamakon maganar data daina yi yanzu tace "da sau'ki Daddy".

"Allah ya sauwake Nabilah Allah ya baki lafiya".

"Amin" tace tana goge hawayen fuska tata kafin ta zame ta kwanta tare da rufe idonta kawai tayi tsam shiru Alhaji Ashraf yayi yana kallon fuskarta datai jawur ta rame sosai ji yayi wani irin abu ya tsirga masa na 6acin rai ganin irin halin data tsinci kanta juyawa yai yana kallon Alhaji Tajuddeen yace.

"Shikenan Allah ya rufa asiri muje Nabilah Allah ya sauwake in an jima zan turo doctor ya duba ki" kaita d'aga tana cewa "to Daddy nagode" "aha ba damuwa Nabilah Allah ya sauwake muje Tajuddeen" kallon Nabilah Alhaji Tajuddeen yayi ya kalli abincin breakfast d'in da aka kawo mata bataci komai ba harya bud'e baki zaiyi mata magana sai kuma ya kyale ya juya suka fita a bedroom d'in.

Kamar yadda ya fad'a ko awa biyu cikakkiya Nabilah batai ba doctor yaxo ya dubata harda ruwa ya d'aura mata sannan yayi mata allurar zazza'bi da magunguna sannan yace zuwa jimawa zai sake dawowa ya dubata ya fad'awa Hajiya Fatima cewa ta ri'ka zuwa tana dubuwa saboda kar ruwan ya 'kare ba'a cire da wuri ba to tace masa bata ma fita daga d'akin ba ta zauna har saida ruwan ya qare ta cire ta dau'ki d'ayan tasaka mata kafin ta mi'ke tana fita shiru Nabilah tai idanonta a rufe tun d'azu babu abinda take sai aikin tunani da tuna rayuwar su ta baya ita da Sultan bata ta'ba zaton Sultan zai zargeta ba koda ace da gaske ta aikata a tunaninta zai iya yafe mata da wani ne yace Sultan zai mata haka bazata yarda ba saida ya nuna mata taga zahiri da kanta nannauyan numfashi take fitarwa da'kyar ji take kamar an d'ora mata dutsi me nauyi a kirji har hanata numfashi mekyau yake har batasan lokacin da hawaye yake shararo mata ba tun tana tunani har tayi barci.

***Washe gari tana kwance a bedroom kamar yadda take kullum ta rufe dukkan jikinta da bargo d'akin shiru kamar ba halitta a ciki bud'o kofa Hajiya Fatima tai tana shigowa abinda ta fara kallo abincin data kawo mata tun na breakfast bata tashi tayi ba gashi yanzu karfe daya da rabi na rana cike da tsananin damuwa ta karaso tana yaye bargon da Nabilan ta lullu'ba dashi tana kallon ta dama abinda take tunani kenan ba barci take ba sai zazzafan hawaye da suke

Please Login or Register in order to submit comment