Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne damuwa taba Bilkisu please mi'ko min wayata dan Allah kar zuciyata tayi bindiga" zaro ido Hajiya Bilkisu tai tana cewa.

"Subahanallahi bindiga kuma 'kawata me yayi zafi haka"? Ta fad'a tana karewa yanayin da Hajiya Sadiyan take kallo ganin bata ko motsa ba yasa taci gaba "kinga Hajiya Sadiya dan Allah ki kawar da wannan abu samun lafiyarki a yanxu shine damuwata indai kika mayar da hankalinki kika samu sau'ki ni Kuma nayi miki alkawarin zan taya ki mu had'a karfi da karfe mu shawo kan Alhaji Ashraf ya aureki" jin abinda Hajiya Bilkisu take fad'a yasa da sauri ta kalleta alamar da gaske kike tace "dan Allah Bilkisu bansan wasa kar kisa na saki jiki Kuma baki biya min bu'kata taba kin tabbata zaki taya ni na samo kan Alhaji Ashraf"? Kai Hajiya Bilkisu ta d'aga mata cike da 'kwarin gwiwa da son 'karfafa mata zuciya tace "kwarai Sadiya nayi miki wannan alkawarin insha Allahu zaki auri Alhaji Ashraf ki zauna dashi kuyi rayuwa kamar yadda kike fata amma zan taimake kine kawai idan naga yanzu kin d'auke hankalin ki akansa ki kama shan magani ki samu lafiya bayan kin gama warwarewa saimu d'aura d'amarar neman ta yadda za'ayi mu samu ki shawo kansa ya tattare hankalin sa da nutsuwarsa ya fuskance ki ya soki sannan ya aureki humm 'kawata bake ba koni zanso ace na samu miji irin Alhaji Ashraf na aura wazaiyi sake da irinsu banga lefin kiba kome kikai akan Alhaji Ashraf saidai na sake zugaki 'kawar kada ki sake ki rabu dashi ki kasance me dauriya da yi masa naci a koda yaushe karki gajiya domin ni nagano dalilin da yasa kike shan wuya ba komai bane bari na fad'a miki gaskiya bawai dan ya wulakanta ki ko yasa kiji babu dad'i yake yi miki haka ba a'a saboda Alhaji Ashraf har yanzu shi d'alibi ne a 6angaren soyayya baisan komai ba tunda bai ta'ba yiba amma ke kin santa kin ta'ba yi kuma kinsan dad'inta to kamata yayi kiyi amfani da 'kwarewarki ki nuna masa hanya ki koyar dashi yadda zai koyi sonki ta ruwa sanyi cikin batare da kin furta masa kalmar so ba nina fad'a miki kina zaune zaki ganshi yazo miki har gida sannan ya nemi alfarmar ki ya furta miki so ya 'kas'kantar dakai ya baki ha'kurin Abubuwan da suka faru 'karshen wasan ya aureki shikenan fa burinki ya cika batare da 6acin rai ko hayaniya ba har aji kanku haba Sadi wise kamar mara wayo ya akai kofar tunanin ki ta toshe ne"? Hajiya Bilkisu ta karasa maganar tana kallon yadda lokaci guda Hajiya Sadiyan ta tashi zaune da kanta daga kawancen da take kamar ba me jinya ba haka ta ware har saida ta baiwa Hajiya Bilkisu mamaki ganin ta dau'ki kofin tea d'in ta fara shayasa ta bud'e cooler tana had'a mata abinci kafin ta gama, maimakon ta sauke kofin sai taga ta qara mi'ka mata tana cewa.

"Zuba min wani".

Murmushi Hajiya Bilkisu tai cike da jin dad'i da mamakin ganin yadda ta wartsake kamar me ciwon 'karya kafin ta kar'bi kofin ta sake zuba mata wani ta bata shima bata rage ba sai kofin ta dire sannan taja plate d'in abinci gabanta shima tad'an ci ba lefi kafin ta yagi tissue ta goge bakinta tare ta rufe ido ta bud'e had'e da sauke ajiyar zuciya tana kallon Hajiya Bilkisu tace.

"Na gode sosai 'kawata tabbas ke aminiya ta gari ce wacce mutum zai dau'ki dukkan yardarsa ya baki wallahi kafin kiyi min wannan maganar jikina a mace yake fiye da yadda kike tunani ko tashi bana jin zan iya yi amma ki duba kina fad'a min magana me dad'i wacce idan nabi zan samu abinda nake so cikin sau'ki lokaci guda naji wani irin 'karfi yana tunkaro ni tabbas ke amana ce Bilkisu duk ranar da nayi rashinki a rayuwa nayi babbar asara, insha Allahu abinda kika fad'a min dashi zanyi amfani naga cewa na juyo da hankalin Alhaji Ashraf kaina domin harga Allah ina son sa kuma har cikin zuciyata badan kud'in sa ko mu'kamin saba a'a nidai kawai nayi nisa idona ya riga ya rufe akansa tun ranar dana fara had'uwa dashi ban sake samun sukuni da kwanciyar hankali ba saboda jarabtuwa da sonsa daya same ni, amma shi sam baya gani meyasa Bilkisu ki fad'a min ko akwai wata da zanbi"?.

Gyara zama Hajiya Bilkisu tai tana cewa "akwai dalili shi baisan meye soba baisan ya yakeba bai ta'ba yiba sannan rana tsaka kice dole saiya soki kin ta'ba ganin inda malami bai koyawa d'alibi karatu ba kuma ya ri'ka tilasta shi akan dole sai yayi karatun zai yuwu"?.

Kai Hajiya Sadiya ta girgiza jiki a sanyaye tace "gaskiya bazai ta'ba yuwuwa ba taya ba'a koya maka ba sannan ace dole saikayi hakan da kamar wuya akwai 'kamshin 'yar damuwa a lamarin amma yanzu dai na fahimta inda matsalar take daga nine kuma zan gyara zan tsaya tsayin daka na ri'ka shawo kansa ina bashi kulawa ta masa magana me dad'i ina 'kan-'kan da kaina daga haka idan naga na samu kar6uwa sai nayi amfani da wannan damar na fara bayyana masa abinda nake so na nuna masa a zahirance aurensa nake so da burin yi indai nabi hanyoyin da kika fad'a min na tabbata zan dace zan riski nasara zan kai matakin da nake son zuwa".

Kai Hajiya Bilkisu ta jinjina tana cewa "Kwarai Hajiya Sadiya zaki kai labari na tabbata zaki nasara indai kikai amfani da shawarar dana baki".

"Ok shikenan Bilkisu na gode lallai kece irin 'kawar daya dace ayi 'kawance da ita bari nayi wanka yanzu ko jikina zai qarasa warwarewa ina zuwa" mi'kewa tai tana hawa stairs yayin da Hajiya Bilkisu ta sake sabon zama tana aje mayafinta itama ta d'ebi abinci ta d'auko drink sannan ta dawo ta zauna, duk abinda suke fad'a da irin hirar da suke Husnah tana sauraron su hankalin ta ya tashi da jin abinda Hajiya Sadiyan take so waye kumà Alhaji Ashraf a ina yake meyasa Hajiya Sadiya duk shawarar da aka bata bazata tsaya tayi nazari akai ba? dafe kai tayi tare da fad'in innalillahi wa Inna ilaihi raji'un Allah ka ganar da bayin nan naka kasa su dawo kan hanya Momy meyasa zaki min haka meyasa bazaki fuskance niba ki kankaro min martaba ta taya za'ai wanda yake sona da aure zai ganni da daraja wash Allah" ta fad'a tana sake dafe saitin inda zuciyarta take bugawa jikinta a sanyaye sosai ta juya tana komawa bedroom ta rasa me yake mata dad'i tayi nan tayi can karshe sai ji tayi hawaye yana zuba mata a ido kawai ta fad'a kan bed tana ruf da ciki ta soma kuka ko zuciyarta zata samu sassauci da sanyi daga zafin ba'kin ciki da 6acin ran da Hajiya Sadiya take jefata.


GIDAN ALHAJI MUKHTAR
Zaune Hajiya Salmah take ta cika tayi dam kamar ta fashe yayin da wasu mata su hud'u suke bubbud'e akwatunan da suke gabanta sunata sam barka babu wanda ya lura da yanayin ta daidai wata mata ta bud'o kofa ta shigo da sallama ganin abinda yake faruwa yasa ta tsaya durus tare da kallon Hajiya Salmah wacce ta kusa yin bindiga tace.

"Tofa wannan kuma daga ina ko lefen Rasheedat ne aka kawo kuma ko a gayyato mu musa albarka gaskiya Hajiya Salmah baki min daidai ba"? Ta karasa maganar tana shigowa kallonsu tai duk babu wacce ta sani da ido taiwa Hajiya Salmah magana mi'kewa tai suna shiga part d'inta cikin za'kuwa Hajiya Suwaiba tace.

"Me yake faruwa ne Hajiya naga wadancan matan suna duba kaya kuma ke kina zaune kin saka su gaba kina cin magani lafiya dai"? Cije baki Hajiya Salmah tai cike da takaici tace "hummm Ina lafiya Suwaiba Sultan ya gama mugun raina min hankali wai kayan lefe yake had'awa a part d'insa amma bai ta'ba nuna min ba ya had'e kai da ubansa suna komai tare sai d'azu kawai ina zaune kamar a mafarki naga wadancan matsiyar 'yan uwan nasu sun zo shi kuma Alhaji ko kunya baiji ba shine me d'auko akwati daga bedroom d'in Sultan yana kawo musu wai na tambaya daga Ina zuwa ina kinsan me yace" ta fad'a tana goge idonta da yake neman cika da hawaye kafin taja wani irin mugun tsakin tsanar da taiwa Nabilah da mahaifiyar ta tace amsar daya bani wai "lefen Sultan za'a kai gidansu wancan tsinanniyar yarinyar Nabilah kuma kona shirya ko ban shirya ba d'aurin aure ranar juma'a ta sama babu fashi kiji wata masifa da yake neman d'ora min".

Zaro ido waje Hajiya Suwaiba tai tana cewa "auren Sultan kuma? Nima fa abinda ya kawo ni gurin ki kenan da kikace kina so ya auri Hajeer shine nazo muyi magana sai kuma na samu wannan tsiyar yanzu ya za'ai kenan"?.

"Humm ya za'ai kuwa ni yanzu ban isa hana Alhaji abinda yayi niyya ba saidai wallahi bazan kalli wannan yarinyar matsayin surukata matar d'ana ba bana sonta dole ya qara aure ko yana so ko baya wallahi tallahi saiya auri wacce nake so saidai akan haka ko mene zai faru ya faru".

Kai Hajiya Suwaiba ta jinjina cikin zuga da son zuciyar aso 'yarta a aureta dan su samu dukiya tace "kwarai Hajiya karki ta'ba yarda da wannan lamarin tabd'ijan to bari kiji kwanan baya da idona naga yarinyar da Sultan d'in zai aura wani murgujejen Alhaji ba'ki mummuna me jan ido ya sauketa a mota sun shiga hotel tare hannunsu ri'ke dana juna da nazo gida ina jimami a lokacin Hajeer ta dawo daga islamiyya nake fad'a sai tace ai wannan 'karami na gani bansan komai ba har video akai mata ba kaya ana d'orawa a internet tsakani da Allah zan fad'a miki gaskiya Sultan bai dace da yarinyar nan ba domin muguwar 'yar iska ce mutum indai namiji ne babu kalar wanda bata mu'amala dashi a gari duk ansan da haka saboda ku kun dangance su kuma ana ganin d'anku ne zai aureta shiyasa ake 6oye muku amma ance har asibiti take zuwa wannan yarinyar anayi mata d'inki tana zubar da ciki".

Dafe 'kirji Hajiya Salmah tai tana cewa "dan Allah da gaske kike Suwaiba? Na shiga uku aiko wallahi Sultan bazai auri Nabilah koda ace nima zanyi asarar nawa auren saina wargaje bikin nan bari naje gurin wadancan matsiyatan suma su tashi su barmin gida na rantse da Allah bazasu kai wadancan akwatunan ba tashi muje" mi'kewa sukai suna fita daidai sun gama gyara komai suna shirin fita Hajiya Salmah ta dakatar dasu.

"Tsaya Labara ku dawo da akwatunan nan baza akai suba".

Da mamaki Labara tace "akan wanne dalili ne baza akai ba"? A masife Hajiya Salmah tace "akan haka nayi ra'ayi ina wanda zaku kaiwa d'ana ne nice nake da iko dashi to na hana zaku iya aje min ku bar min gida kin gane"? Da sabon mamaki Labara tace "mu aje mu bar miki gida saboda gidan kine"?.

"Kwarai baki 'karya ba gida nane tunda gidan mijina da 'ya'ya ne dan Alhaji yana d'an uwanki baki Isa kice zaki min gadara ba domin nike da iko da komai nasa baki da wani hakki akansa.

D'aga mata hannu Laraba tai tana cewa "kinga Salmah ki iya bakin ki a kaina kin gane ked'in banza ked'in wofi shashashar banza bulkumar asara uban waye yake miki gadara da dukiya ke kud'i na dama alhamdulillah masha Allah ubangiji ya bamu babu abinda zamu zo gurin wani so'ko'ko mu tambaya balle ayi mana gori da haka ki kama kanki kar kiga gidanki nazo kice zaki kawo min raini wallahi tallahi saina baki mamaki na nuna miki isar 'yar uwa tafi ta mace idan shekara d'ari kikai tare da Mukhtar kece kika haifa masa duniya daga ranar da yace kije ya sake ki dole kibar gidan nan niko Ina da gurin zama ko yanzu nazo gidan nan Kuma kedai banza a banza baki Isa kiyi komai akai ba".

Tada jijiyar wuya Hajiya Salmah tai tana cewa "a'a ki iya bakin ki wallahi kada ki kuskura ki fad'a min magana yanzu za'ai d'an karamin ya'ki a gidan nan dan wallahil azim kome zaki yau akwatunan nan bazasu fice daga wannan gidan ba".

Wani banzan kallo Laraba tai mata tana sakin dariya tace "zamu fita dashi zuwa gidan yayana Alhaji Tajuddeen idan isa ke 'yar iskar kanki ce dan Allah kizo ki tareni ko ki hana fita dashi zan nuna miki cewa kura ba farkar kare bace zaki gane kin min rashin kunya bari Alhaji Mukhtar d'in ya dawo gidan ai Ina nan har gobe sai an yita ta kare kinsan wace ni bana d'aukar raini" juyawa tai tana kallon Hajiya Hindu da Saudat wadanda suka sake baki suna mata kallon ikon Allah tace "muje Hajiya idan mun kai ta nan zamu dawo kowa ba gidansa zai wuce ba saina tabbatarwa da Alhaji Mukhtar wannan abinda ya faru muje" tana fad'in haka suka fara fita da akwatunan zuwa harabar gida Hajiya Salmah tana tsaye ba'kin ciki ya gama cika mata ciki har suka gama d'ebewa tana jin tashi motoci guda da bud'e gate da ficewar wata iriyar zazafar ba'kar ajiyar zuciya ta sau'ke tare da zama jagwaf akan kujera tana dafe kanta da hannu biyu jin juwa na d'ibanta zama kusa da ita Hajiya Suwaiba tai tana dafe kafad'arta tace.

"Hajiya karki damu ki daina damun kanki kar kiji komai bata Isa maganganun da suka fad'a miki suyi tasiri ba dan wallahi nima zan taya ki ya'ki da fad'a na ganin cewa Sultan bai auri wannan yarinyar ba naga alamar wadannan dangin mijin naki basu da mutunci ki dage idan sun dawo shima Alhaji Mukhtar d'in ya dawo kada ki bari su samu ke6ancewa ta fad'a mata karya da gaskiya ki tsaya ayi komai a gabanki karta jawo auren ki ya mutu dan naga wannan matar da kukai musayar yawu da ita har wani zaro harshe take ko mayya ce oho".

D'agowa Hajiya Salmah tai tana cewa "ai wallahi Suwaiba ko baki fad'a ba bazan kyale suba domin Nima ba kanwar lasa bace nafi karfin dukkan su hud'un zasu dawo su same ni" cikin zuga Hajiya Suwaiba tace "tabbas karki yarda ki nuna musu tsantsan fushin ki karki yarda ni bari dama yana shigowa ko tare dasu ko shi kadai kawai ki fashe masa da kuka sannan ki 'kuga musu sharri a gurin kice haka kawai suka saka ki gaba sukai miki tas ta uwa ta uba babu lefin tsaye bana zaune ni bari na tafi karsu dawo su sameni hayaniya ta tashi nasan zasu iya yimin sharrin nice na zuga ki tunda naga ba 'yan arziki bane" ta fad'a tana mi'kewa tayi mata sallama har harabar gida ta rakata suka sake sabuwar tsewa tana sake 'kulla mata abubuwa daga baya ta shiga motarta tabar gidan Hajiya Salmah kuma ta koma ciki tsaye tay a parlor ta kasa zama tayi nan tayi can gabadaya zufa ce ke tsattsafo mata a jiki har mamaki ne ya kamata meyasa take zufa sai kace mara gaskiya shiru tai cikin dagulewar lissafi jira take Rasheedat ta taso daga school ta aiketa gashi Amrat tana bedroom bata jin dad'i huuuuuuhh ta sau'ke ajiyar zuciya tare da nufar kofar part d'in su Amrat danta gano yaya jikin nata ta tashi ko har yanzun tana kwance.

***✍️✍️✍️Duk abinda ya faru a gidan Alhaji Mukhtar saida Laraba ta mayarwa Alhaji Tajuddeen komai domin ta fahimci kamar har yanxu Hajiya Salmah bata sauko ta sauya halinta ba badan dai Sultan ya riga ya gama gidansa ba tare zai zauna da mahaifiyar saba da tace a fasa auren Nabilah dashi domin maganar gaskiya ta hango wata irin 'kiyayya da Hajiya Salmah takewa Nabilah tunda har aka zo wannan lokacin bata daina ba tofa baxata daina d'in ba da ace zasu yarda toda data basu shawara kawai Nabilah tayi ha'kuri da Sultan ta auri wani duniya tana da fad'i ba dole sai ta auri Sultan ta zauna dashi ne zata iya rayuwa ba a'a duk gidan wanda Allah ya kaita zatai rayuwar farin ciki me cike da 'yanci bata da yadda zatai ta hana auren amma xatayi ta addu'a idan har babu alkhairi tsakanin Nabilah da Sultan Allah ya rana abun ta ruwan sanyi idan kuma 'kaddarar Nabilah ce auren Sultan nan ma tana ro'kon Allah yasa ta iya cinye jarrabawar ta.

Har bayan sallar isha suna gidan Hajiya Fatima suna ta hira anan Laraba ta kira Alhaji Mukhtar yaxo ya dauke su ya mayar dasu gida ya dad'e acan gidan Laraban suna zance da mijinta bai bai ankara har lokacin ya fita sai kusan karfe sha d'aya ya dawo gida Hajiya Salmah harta gaji da zaman jiransa a palor ta koma bedroom barci ma ya fara d'aukarta kamar a mafarki yaji tsayawar motarsa wani irin wuntsulowa tai daga kan bed tayo kasa da sauri ta mi'ke jiki na 6ari ta suri hijab ta fita a bedroom d'in hijab d'in na hannunta bata samu damar sakawa ba saida ta kusa shiga part d'in sa sannan tasa tare da banka kofa ta shiga ko arzikin sallama babu yana zaune bayan ya cire kaya sai ganinta yayi ta fad'o masa cikin bedroom tana huci baiyi mamaki ba tunda Laraba tayi masa bayani yasan komai kawai ya shareta ko d'agowa baiyi ya kalleta ba balle tasa ran zaiyi mata magana ganin haka yasa tace.

"Alhaji yanxu tsakani da Allah abinda Laraba tai min ta kyauta irin cin mutumcin da tazo har gidana tayi min tayi daidai kenan wallahi badan darajarka ba yau batai kwanan gidan ta sai nasa an rufe min ita akan me zata zo har cikin gidan aure na ta tada min husuma kawai ta gayyato wasu mata 'yan bariki masu wari haya'ki sunzo sun cika min gida to wallahi bazan yarda ba nice na haifi Sultan ba ita ba dan haka bata da iko dashi sai abinda nace ka samu 'yar uwar ka kaja mata kunne ba ruwanta da lamarina zance nane da d'ana baza'ai min dole ba ha'kuri na yazo karshe ta gama kaini bango ka taka mata burki kafin nad'au matakin da kowa bazai ji dad'in saba".

Kamar gunki takewa magana haka Alhaji Mukhtar yai bala'in d'auke kai daga saitin ta ya manna mata hauka wanda taji matukar zafi da ciwon abun ta fad'a masa maimakon yayi magana saiya baiwa iska ajiyarta? Kuka ta fashe dashi tana cewa.

"Gaskiya Alhaji kana da abun mamaki wanne irin son Kaine da rashin adalci wannan ka nuna min dan kawai ita jininka ce ni Kuma barenka ce ka fad'a maka tazo har gida tayi min zagi na tsamar nama har kakanni na saida ta ambato ta saboda batasan inda mutumci yake dama na sani tunda dad'ewa Laraba bata kaunata kuma nafi 'karfin ta haka zata ganni ta barni tunda naga bakin ka d'aya da ita gashi tazo tayi min abinda ranta yake so na fad'a maka kayi banza dani ba matsala ta faru ta 'kare tunda har Allah yasa ka sani nan gaba xan dau'ki doka a hannu na wallahi tallahi duk 'yar matar data sake xuwa gidan nan ta kawo min raini saina 6are mata kai mu zuba ni dasu d'an halak ka fasa" tana gama fad'in haka fuuuuu ta juya kamar zata tashi sama ta fice daga bedroom d'in kai Alhaji Mukhtar ya jinjina cike da tsananin mamakin maganganun rashin arzikin da Hajiya Salmah ta iya tsayawa tserere a kansa kamar zata rufeshi da duka ta fad'a lallai ya jinjinawa rashin hankali irin nata amma yana daidai da zamaninta zaiyi maganin gaba-gaba dai zatai dana sani indai bata canxa halinta ba zai bata mamaki zanyi abinda bata ta'ba tunani ba.


✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë mai tambarin yma dutse new world sabuwar duniya kuzo kuyi kallo dad'i yana Jigawa garin ilmi garin addini zaman lafiya Jigawa.


💃Da anyi kiran Jigawa har wani tunkaro nake yi ana maganar Jigawa har wani canza salo nakeyi Jigawa jiharmu ce abar faharin muce an sanmu akan zaman lafiya ba'a sanmu da rigima.🌹


Tnks for ur supports 🔥 nagode sosai masoya godiya sosai sosai godiya 🌺🥀 ana tare 🤝 insha Allah YÚSRÃHMS CE.

8~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Hamidinah.


Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë 😘
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


TYPING📲 FRI, JAN3/25 8:25pm YUSRAH MUSA ABUBAKAR🤘💓.


💕MINISTER ASHRAF💕


WHATSAPP NO:+234 8160983083
yusrahmusa65@gmail.com


ÀÑÑÙRÌ WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta.


We love our NABI SAW no success without him he's the light of every darkness he's the answer to every question he's the mirror of our life he've no limits ya rasulullah muna sonka fiye darai da iyaye da dukiya.


•••••••••••••••••••••••
•••••••••••••••••••••••••••••••••••
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••


9~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Salihinah.


💦Yüsëëñ Sïr Äl-ämëëñ çë💦
PG____09&10
Abu kamar wasa tun Hajiya Salmah tana ganin kamar bada gaske bane abun bazai faru ba har taga a zahiri dai ga bikin nan ya tunkaro sosai har 'yan uwanta na nesa sun fara kiranta a waya suna sanar mata cewa suna nan suna shirye shiryen tahowa damuwa ta gama damunta batai komai ba fuska babu fara'a haka gabadaya ta sauya zaman gidan ko gaisuwar Sultan bata amsawa balle Alhaji Mukhtar tayi masa yaji ta daina zuwa part d'insa Amrat kuwa da taga murna take saida tayi Mata shegen duka harda fasa mata baki Rasheedat ce me sake tunzurata tana zugata cewa har numbar wayar Nabilah ta kar'ba kullum sai sunyi waya itadai Amrat batace komai ba ta bari Allah ya saka Mata sharrin da Rasheedat d'in tayi mata akan haka Alhaji Mukhtar yayi mugun 6ata Mata ranta yayi mata tas har saida taji dama bata daki Amrat ba haka ta d'au fushi da ita kamar abokiyar gabarta ta dawo ba sosai take kulata ba da'kyar take amsa gaisuwarta ba yabo ba fallasa Hajiya Salmah ta zama haka take zaman gidan bata shirin komai balle Rasheedat da take jin kamar ta kama da wuta tsabar ba'kin cikin Sultan ba Hajeer zai aura ba hatta lallen da Amrat tayi lalle da saloon akan haka saida sukai fada karshe suka raba d'akin kwana.

Haka a 6angaren amarya Nabilah ma shiri take sosai kullum suna tare da Husnah tana taya ta wasu abubuwan bata komawa gida sai dare itace ta tayata suka raba invitation card da komai a lokacin bikin ya rage saura kwana goma sha biyar Nabilah tana gidan wata qanwar Mamin ta acan ake mata gyaran jiki me kyau da kayayyaki a 'kan'kanin lokaci duk kamaninta ya sauya ta sake wani irin kyau da haske acan akai kiran me lalle tayi mata ba'ki da ja akai mata saloon batai kitso ba tabar gashinta a sake ta tajeshi yayi kyau ya zuba akan jikinta ba'ki wulik yana she'ki saura sati d'aya d'aurin aure da dare Hajiya Hauwa ta dawo da ita gida domin akwai wasu abubuwan daya kamata su tattauna tsakanin ta da mahaifanta.

°°°°Washe gari Nabilah tana bedroom a kwance har kusan sha biyu na rana bata tashi ba tun bayan sallar asuba data koma barci bata farka ba bud'o kofa Hajiya Fatima tai ganin har lokacin Nabilan barci take yasa ta karaso tana yaye bargon tsaye tai cike da mamaki take kallon Nabilah ganin yadda ta qara kyau da haske kamar ba ita ba gashi ta d'au lalle da saloon duk kamaninta sun 6ace sauke ajiyar zuciya tai tana sake qare mata kallo kafin tad'an girgiza ta tana cewa.

"Nabilah Nabilah ki tashi haka".

Ta fad'a tana sake girgiza ta da'kyar Nabilah ta bud'e ido tana kallon Hajiya Fatima da idonta wanda yake cike da barci tace "Mami lafiya"? Kaita d'aga mata "eh lafiya ki tashi haka rana tayi baki breakfast ba kuma gashi Daddyn ma yazo yana nemanki" tashi zaune Nabilah tai tana cewa "Daddy Ash"? Ri'ke ha6a Hajiya Fatima tai tana kallon Nabilah wacce ta mi'ke tana d'aukar wani siririn mayafi ta yafa a kanta tace "Nabilah dama baki daina cewa Daddy Ash d'in nan ba"? Nabilah dake shirin fita jin tambayar da Hajiya Fatima tayi mata yasa tayi dariya tana cewa "ayya Mami na riga na saba saidai ha'kuri" ta fad'a tana bud'e kofa fita Hajiya Fatima tai ita kuma tabi bayanta.

A parlon Alhaji Tajuddeen ta samesu suna ta

Please Login or Register in order to submit comment