Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ambaliya a fuskarta idonta ya kumbura yayi jawur zama Hajiya Fatima tai a gefen gadon tana ta'ba jikinta jin wani irin mugun zafi kamar wuta yasa a firgice ta sake kallon fuskarta tana cewa.

"Nabilah".

Bata iya amsa mata ba saboda yadda muryarta tai nauyi sakamakon magana data daina yi sam a karo na biyu ta sake kiranta wannan karon runtse ido tayi da qarfi tana fashewa da ba'kin kukan damuwa wanda hatta Hajiya Fatima saida taji hawaye yana tarar mata a ido da sauri ta d'ago Nabilan tana tashinta zaune ta rungume ta cike da tausayi irin na uwa da d'a itama ta fara zubar da hawaye wacce irin kaddara ce wannan ta same su Allah ya kawo musu karshen ta............

D'agowa Hajiya Fatima tai tana goge mata hawayen fuskarta cikin lallahi tace "Nabilah kefa musulma ce kiyi ha'kuri ki dau'ki kaddarar ki kiyi kokarin cinye jarrabawar ki nasani wannan yaron ya cutar dake ya cutar damu yasa yaso 6ata mana suna a gari da yake bamu da alhakinsa Allah ya karemu daga sharrin sa dan Allah Nabilah kodan haka kiyi hakuri ki d'aure duk yadda kike ji a zuciyarki ki zama mai dangana a duk lokacin da wani abu ya sameki kamar irin wannan lokacin ki nuna kwarin gwiwa ki zama me jajircewa akan komai karki d'orawa kanki wata damuwa ki nutsu ki dawo cikin hankalin ki kinji Allah yana tare dake yasan komai zai musanya miki da mafi alkairi".

Nabilah tana shasshe'kar kuka tace "Mami damuwa ta yaya Sultan ne meyasa zaiyi min haka ina son sa amma kaddara tasa zargi ya shiga tsakanin mu har yana cewa shida aurena har abada Allah ya rufa asiri ya auri mazinaciya irina kiji fa Mami wai ni yake Kira da wannan sunan"? Nabilah ta fad'a cikin 'kunar rai tana sake fashewa da kukan ba'kin cikin tuna kalmar zina daya ambata a kanta.

Kai Hajiya Fatima ta girgiza tana cewa "na sani Nabilah Allah ne sheda ya san komai insha Allahu Sultan zai gane gaskiya zai gane yayi kuskure a lokacin dazai dawo yayi dana sani ke kuma sannan kinyi masa nisa domin wallahi Nabilah Nima ko yanzu Sultan ya dawo yace ya amince zai aureki bazan amince ba domin koda ya aureki hankalinsa bazai kwanta dake ba kullum yana cikin zarginki kawai kiyi hakuri Allah ya fito miki da wani na gari wanda ya fishi kyan hali wanda zai rikeki da mutumci yasan kimar mu" kai Nabilah ta d'aga cikin dauriya tace "insha Allahu Mami daga yau zan cire Yaya Sultan daga cikin zuciya koda ace hakan da zanyi zai zama silar rashin samun farin cikina Kuma bazan ta'ba waiwayarsa ba a cikin rayuwa".

"Yauwa Nabilah haka nake son ji Allah yayi miki albarka zan tayaki da addu'a in yarda ya yarda saikin samu mijin aure nagari san kowa 'kin wanda ya rasa ki cire damuwar komai ki manta dashi".

"Insha Allahu Mami zanyi kokarin hakan" Nabilah ta karasa maganar tana d'an yin murmushi kad'an wanda rabonta dashi harta manta mi'kewa Hajiya Fatima tai tana cewa "bari na kawo miko abinci me zafi kici domin wannan ya huce miki" ta fad'a tana mi'kewa ta fita shiru Nabilah tai zuwa wani lokaci ta dau'ki wayarta ta bud'e tare da binciko numbern Sultan ta zuba mata ido kamar shi take kallo daga baya taja tsaki tana yin blocking d'insa sannan ta aje wayar tana mi'kewa yuuu taji hajijiya na d'ibanta da sauri ta koma ta zauna tana dafe kan daya sara mata tun tana ganin duhu har idonta ya washe sannan ta sake mi'kewa tana nufar hanyar toilet domin tayo brush...................

✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë🌺


13~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Khaidinah.


See you tomorrow morning be with me at always my lover's.

DUTSE NEW WORLD 🌏 sabuwar duniya kuzo kuyi kallo dad'i yana Jigawa garin ilmi garin addini zaman lafiya Jigawa state.


TYPING 📲Wed, Jan7/24 11:34am YUSRAH MUSA ABUBAKAR✨🤘.


💕MÏÑÏSTËR ÄSHRÄF💕


WHATSAPP NO:+234 8160983083
yusrahmusa65@gmail.com


ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫 home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan haka taken mu yake.

💦Fatima Zarah Elham
Little Zarahn Aunty.

••• •••
Official
By=== === === ===
✍️ YÚSRÃHMS CE.


14~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Muttaqinah.


💦Yüsëëñ Sïr Äl-ämëëñ çë💦
PG___15&16
Ganin kusan sati guda Sultan bai le'kota ba yasa Hajiya Salmah d'aga waya ta kirashi cewa yazo yanzu tana son ganinsa batai minti sha biyar da kiransa ba yazo tana zaune zama yayi yana kallon fuskarta da babu walwala ta mugun had'e rai tace.

"Sultan Alhaji ne ya hanaka zuwa inda nake kamar yadda ya hanasu Rasheedat ko kuma ra'ayin kanka ne yasa baka zo ba yau kwana kusan sha biyar"?.

Kaiya girgiza yana cewa "a'a Umma ba shibane kawai aikine yayi min yawa shiyasa ban shigo ba kiyi hakuri ba wani abu bane".

Jin abinda yace yasa Hajiya Salmah ta sauke ajiyar zuciya tana cewa "au aina d'auka ko akan Nabilan ne ya dakatar dakai daga zuwa guna yanzu a wanne mataki kuke kai dashi fatan maganar auren ta rushe"?.

"Ai Umma ki kwantar da hankalinki babu wannan maganar a yanzu yayi lallahin duniya yayi fad'a amma nace bazan aureta ba ni yanzu bana sonta Kuma bazan 'kara sonta ba".

D'adi ne ya cika Hajiya Salmah harda sakin murmushi tana cewa "yauwa Sultan sakyau abinda nake son ji kenan kada ka kuskura ka tausaya mata ko mutuwa zatai ba asibiti aka kaita ba ko pharmacy ne akanta kar kaje dubata karka tausaya Mata kome zasuyi ko suce maka ka share su hatta Alhaji karka saurare shi kana kallo akan haka ya sake ni ko? to wallahi matukar ka auri yarinyar nan Nabilah saina tsine maka kaji dai na fad'a maka".

"Karki damu Umma nifa na daina sonta babu ruwana da ita yanzu meye had'ina ita dahar zanje inda take maganar Abba zai tilasta ni a'a domin yayi min fad'a harya gaji ban saurare Shiba balle naje d'in kinga kuwa ai mun raba hanya yanzu harya ha'kura ya daina cemin komai".

Kai Hajiya Salmah ta jinjina tana cije lips tace "yauwa d'an albarka kaga yanzu ka rabu da mangoro ka huta da 'kuda da ka'ki ganewa kullum ina fad'a maka amma sonta ya rufe maka ido sai yanzu da kanka ya gwaro da bango ka gane gaskiyar ita 'yar iska ce ka rabu da ita ta ruwan sanyi yanzu abinda nake so dakai zan kira 'kawata Hajiya Suwaiba zamuyi magana akan 'yarta Hajeer jiya ma tazo gurina ta gaisar dani nasan zaku dace kuma yarinya ce kyakkyawa kana ganinta zakaji tayi maka zan sanar da Hajiya Suwaiban duk yadda mukai saika shirya kaje ka ganota ko"?.

Kaiya d'aga yana cewa "ok shikenan Umma ba damuwa yadda kukai dasu ina jira kisa Aunty Atikah suje su kar'bo min lefe na daga gidan can Kuma koda jan baki ta d'auka bazan yarda ba saita biyani".

Murmushi Hajiya Salmah tai cikin jin dad'i domin tasan tunda yace ba damuwa bazai bata matsala ba kuma dama idan ta fad'i magana baya musa mata sai akan neman aurensa da Nabilah ne yaso bujire mata kaita jinjina tana cewa "karka damu lefe yana nan tun kusan kwana ashirin nasa an kar'bo min yana gurina na kaishi gidan Hajiya Falmata danaga ka daina xuwa inda nake ma na d'auka ko dalilin karbo akwatunan da nasa akai ne Alhaji yaji labari ya kiraka yayi maka zagin tsamar nama" kaiya girgiza yana mi'kewa yace...

"A'a inaga baisan kun kar'bo ba kamar yadda nima ban sani ba kuma suma maybe basu nuna ba da ace ya sani da yanxu ya Kira ni akan hakan bari na koma Umma saina dawo duk yadda kukai da wancan yarinyar zanzo jibi sai naji komai" dad'i daya gama cika Hajiya Salmah ji take kamar ta tashi ta taka rawa tace.

"To Sultan Allah yayi maka albarka na tabbata bazan yi maka xa6en tumun dare ba zakaji dad'i matukar dad'in zama da Hajeer ba ruwanta yarinya bata da hayaniya ba kamar wancan fitsararriyar yarinyar ba Mai idon ganin gari".

"Ok Umma na tafi" ya fad'a yana aje mata kud'i mi'kewa tai tana masa rakiya har harabar gida kafin ta dawo murna da farin ciki ya gama cikata jikinta har 6ari yake ta kira Hajiya Suwaiba tana ce mata gobe zata shigo anguwarsu akan maganar Hajeer da Sultan.

Husnah bata gari tun bayan lafawar hayaniyar abinda Sir Ahmad yayiwa Nabilah ta tafi Abuja gidan 'kanin babanta kusan watan biyu tai kafin ta dawo duk tsawon wannan lokacin saurayin ta Suraj bai ta'ba kiranta ba idan ta kira layinsa baya tafiya dalilin haka yasa bata karasa hutunta ba ta dawo Dutse a ranar data dawo ta dau'ki aron wayar Hajiya Sadiya ta saka numbar sa ta kirashi abin mamaki sai taji kiran ya shiga amma ba'a dauka ba harta katse sake kira tai nan no answer a karo na uku zata Kira sai Kuma taji shi ya Kira d'agawa tai tana karawa a kunne tare dayin sallama daga can 6angaren Suraj yace.

"Dawa nake magana"?.

Sauke numfashi Husnah tai tana cewa "baka gane niba nice fa ko murya baka dauka ba"?.

"Eh taya zan dau murya bayan bansan wacece ba"?.

"To Husnah ce" ta fad'a haushi yana d'an rufeta shiru yayi tsam ya bai ce komai ba d'auke wayar tai domin ta d'auka ko network ne ya katse kiran ganin bai katse ba tace "wai baka jina"? Nan ma shiru yayi bai bata amsa ba saida ta sake magana yace "Ina zuwa bani minti biyu" yana fad'in haka ya katse wayar mamaki ne ya kama Husnah har tana bin secreen d'in wayar da kallo to meya faru ya taji yanayin sa ya sauya tasan ba haka suke ba meyasa yau yayi Mata haka dama ya daina kiranta yau ma dan itace ta gwada zama Tai tana jiran Kiran nasa amma a banza harta gaji ta sake kira bai d'auka ba katsewa tai ta saika tura kira sai taji a rufe kanta ne ya d'aure ta kasa fahimtar inda ya dosa bari ta bari zuwa jimawa ta sake gwadawa.

Har dare Husnah tana zuba ido taga kiran Suraj amma shiru da'kyar tai barci gari ya waye ba labari iya damuwa ta shiga haka ta zama kamar mara lafiya wani tunani ne yazo mata kawai tunda tasan gidansu taje ta sameshi tana shirin tafiya ta fito waje bata dau'ki mota ba domin a yanayin nan da nake ciki bazata iya driving ba gara tahau napep taje ta dawo kamar a mafarki tana bud'e kofar gate ta fito taga Suraj tsaye a jikin motarsa fuskarsa a had'e karasawa tai tana kallon sa da mamaki tace.

"Suraj kazo ashe amma baka kirani na fito ba meya faru ne kwana da yawa shiru har naje Abuja na dawo baka ta'ba kirana ba na Kira wayarka ya'ki tafiya sai jiya nasa numbar a wayar Momy na sannan na samu ta shiga fatan lafiya ko"?.

Wani kallo yayi mata kamar bazai yi magana ba sai kuma ya gyara tsaiwarsa yana hard'e hannu a 'kirji yace.

"Tambaya ta kike abinda ya faru na daina Kiran ki na daina zuwa inda kike oh ke harkin manta abinda kikai min kenan"?.

Da sabon mamaki Husnah tace "ni kuma me nayi maka Suraj".?.

"Au baki san me kikai min ba"?.

"Gaskiya ban sani ba ko Kuma na manta".

"Ok to kafin na fad'a miki lefin ki Ina so zan sanar dake neman auren ki da nake yi na fasa bazan aure kiba na ha'kura dake" yana rufe baki Husnah ta zaro ido waje cikin firgici da tashin hankali tace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un meya faru wanne lefi nayi maka dan Allah kayi ha'kuri" kaiya girgiza Mata yana cewa "Husnah dazan iya ha'kura dana ha'kura to amma maganar gaskiya idan ma na aureki zargine zai rika shiga tsakani na dake tun daga ranar dana ganki kinje hotel 'kawarki Nabilah ta fito da gudu tana kuka ko kwali babu a kanta tun daga nan na yankewa zuciya ta shawarar rabuwa dake Husnah ina son ki amma gaskiya bazan iya aurenki ba na ha'kura dake inai miki fatan alkairi Allah ya baiwa kowa rabonsa kiyi ha'kuri" yana fad'in haka ya juya yana shiga motarsa yabar gurin 'kamewa Husnah tai a tsaye tana d'ora hannu aka kamar zata fasa ihu cikin tashin hankali tace.

"Na shiga uku ni Husnah wannan wanne irin bala'i ne ya same mu lokaci guda nida Nabilah innalillahi wa inna ilaihi raji'un dama a ranar Suraj ya bibiye ni batare dana sani ba? Shiru tai cikin tarin damuwa da tunani har tad'au tsawon lokaci a haka daga baya ta sauke numfashi tana jin yadda 'kirjinta yake mata zafi saboda abinda ya faru yanzu tsakanin su tace.

"Ya Allah ya ubangiji kana gani kaine shedata kasan abinda dake 6oye a zuciyata ha'ki'ka ina matukar son Suraj amma na rasashi a lokacin daka sake jarraba ta da tsananin soyayya sa ya mujibud Dua ya mai amsa addu'a ina ro'kon ka bani wani wanda ya fisa ya mai kyauta ya mahalicci Allah ka bani miji na gari wanda zanyi alfahari dashi Suraj kuma kasa rabuwar mu itace mafi alkairi Allah ka bani juriyar rashinsa a rayuwata ka mantar dani ruwan tsirarsa na rungumi 'kaddarata a duk yadda tazo min" ta karasa maganar tana d'agowa ta kalli gabanta inda photon tayar motarsa take ta dad'e tana kallon gurin kamar me tunanin wani abu daga baya ta jinjina Kai cike da takaici da mamaki tana juyawa ta koma gida dan kada Hajiya Sadiya ta ganta kota fahimci tana da matsala kawai tabi ta kofar bayan ta shige part d'inta cire hijab d'in tai ta shiga toilet tayo alwala ta shimfid'a sallaya tayi sallah da addu'a ta sake ro'kon Allah ya bata karfin zuciya da juriya sannan ta mi'ke tana d'aukar towel ta shiga wanka da niyyar tana fitowa kwanciya zatai.

•• •• ••Bayan kwana biyu Hajiya Suwaiba ta kira Hajeer part d'inta har cikin bedroom kamar wani ne zai jisu tayi kasa-kasa da murya tana kallonta tace "Hajeer kinji maganar da mukai da qawata Hajiya Salmah shekaran jiya tazo akan tana son ki auri d'anta Sultan na amsa Mata zaki aureshi duk da ban nemi yardarki ko shawarar kiba na amince saboda Hajeer mutanen nan akwai kud'i ke kinsan da haka tunda tare da 'kanwarsa kike karatu a Poly ina so ki aureshi domin muma mu samu mu zama masu wani abu dukiyar mu ta sake ninkuwa mu zama kowa ya sanmu kamar su nasan zaki bani had'in kai dan Allah Hajeer karki bani kunya ki amince mu kwashi rabon mu kinji"?.

Kai Hajeer ta d'aga tana cewa "bana jin sonsa a raina amma tunda kince yana da kud'i na amince zan aureshi saboda ni daman ba matar talaka bace me aurena saiya shirya wallahi nikam sai Alhaji wanda zan ri'ka wankar nera a gurin sa zan yarda na aureshi ne dan naci kud'insa Ina gama d'iban rabona zan d'aga masa hankali na tada masa bala'i na hana shi jin dad'i da walwala ta 6ata tsakanin sa da mahaifiyar tasa da 'yan uwansa Kuma dole ya sakeni nazo na auri za6in raina domin ni Amaan nake so shi d'an manyan mutane ne babu abinda Sultan ya isa ya nuna masa".

Kai Hajiya Suwaiba ta d'aga tana cewa "Yauwa Hajeer 'yar albarka kenan ashe harkin gano inda na dosa ni kaina bana son auren ku da yaron nan yayi nisa dan Hajiya Salmah d'in ta matsa ne nima nasan waye Amaan nasan mahaifansa ba 'kananan mutane bane idan shi kika aura na tabbata cikin shekara d'aya sai mun zama millionaire a gidan nan dan haka Dan Allah hajeer abinda nake so dake kisa tunanin ki guri daya ki nutsu kiyi kokari kisan duk wani sirri nasa da dukiyoyinsa da kadarorinsa ki zage ki d'ebo mana rabon mu tunda Hajiya Salmah tana sonki kiyi amfani da wannan damar ki tsula mata tsiya son ranki duk abinda zaki mata bazata ga lefinki ba kome zaki bazata ji haushinki ba dan haka zanje gobe na sameta nace kin amince duk abinda mukai zan sanar dake" "ok Mama ina jira" Hajeer ta fad'a tana mi'kewa ta fita da kallo Hajiya Suwaiba ta bita tana murmushi cikin jin dad'i tasan sukam kwanan nan kakarsu zata yanke sa'ka indai ta samu ta lalla6a Hajiya Salmah tayi Mata shigo-shigo ba zurfi ayi auren ta gane kurenta.

***Alhamdulillah yanzu jikin Nabilah ya karasa warwarewa ta dawo daidai kamar yadda take da jikinta kamar bata ta'ba rashin lafiya ko wani abun damuwa ya sameta ba a kwanan baya ta mayar da hankalinta guri d'aya ta cire Sultan daga shafin rayuwarta tunda taga tunawa dashi baida wani amfani saidai ya cutar mata zuciya babu inda take zuwa daga gida sai islamiyyah lokaci zuwa lokaci tana shiryawa taje gurin Husnah ta wuni.

Kwance take a bedroom d'inta da waya a hannunta tana chatting bayan tayi sallar isha Hajiya Fatima ta shigo da sallama aje wayar Nabilah tai tana tashi zaune da murmushi akan fuskarta ta zauna kallonta Hajiya Fatima tai jikinta babu 'karfi a sanyaye tace "har yanzu baki barci ba ashe"? Kai Nabilah ta d'aga tana duban yanayin ta tace "eh Mami banyi amma lafiya naganki wani iri"? "Eh lafiya kizo Daddyn yana nemanki".

"Daddy yake nema na"? Ta fad'a tana zaro ido duk da batasan dalilin kiran ba kai Hajiya Fatima ta jinjina tana cewa "eh yana parlonsa magana zakuyi kiyi sauri" jin abinda tace yasa Nabilah mi'kewa tana d'aukar hijab din'ta tabi bayanta tana tafe zuciyarta na mata sa'ke-sa'ken Allah yasa ba wani abu ne ya sake faruwa ba kodai Sultan ne ya ha'kura yace ya dawo yanzu zai aureta? Ta tambayi zuciyarta lokaci guda taji jikinta yayi sanyi 'kirjinta yahau bugawa da'kyar ta iya d'aga kafarta ta shiga cikin parlon da sallama Alhaji Tajuddeen yana zaune Hajiya Fatima tana gefen sa karasawa Nabilah tai tana zama a kasan carpet a hankali cikin nutsuwa tace.

"Barka da dare Daddy fatan ka dawo lafiya"?.

Kallonta yayi yana jinjina kai yace "lafiya kalau na dawo Nabilah ya jikin naki yanzu kina jin d'an wani sauyi ne har yanzu"?.

Kaita girgiza tana cewa "a'a Daddy na samu sau'ki babu inda yake min ciwo babu abinda yake damu na".

"Ok Allah ya rufa asiri Allah ya 'kara sau'ki haka ake so" ya fad'a tare da yin shiru yayi tsam ya zuba mata ido kawai bai sake cewa komai ba itama Nabilan shiru tai amma dai haka nan jikinta ya bata kamar da matsala saidai bata da bakin da zatai tambayar tunda bai bata izini ba saidai idan shine ya fad'a koma dai menene tana fatan ya kasance alkhairi ne.........................

Katse mata tunanin da takeyi yayi da cewa "Nabilah" ba zato taji ya kira sunanta daidaita kanta tayi tana cewa "na'am Daddy".

Sake kallonta sosai Alhaji Tajuddeen yayi kamar ya'ki fad'a saboda bazai a yadda xata dauki maganar ba saidai ya zama dole ya fad'a kodan samum masalaha a tsakanin juna.

"Nabilah tambaya zanyi miki ki bani amsa ta gaskiya bana son jeka ka dawo kinji"? Kaita d'aga jikinta yana sake yin sanyi yana saki harta ankara ta fara zarguwa da wasu abubuwan da'kyar muryarta ta fara rawa tace "to Daddy".

"Ok am Nabilah tambayarki zanyi bayan rabuwarku da Sultan kin sake samun saurayi ne ko a'a"?.

Batai tunanin abinda zai tambaye taba kenan ta d'auka wani abune dabam sai taji sa6anin yadda zuciyarta take sharta mata har batasan lokacin data d'ago take kallon Alhaji Tajuddeen ido da ido ba tsabar fargabar meyasa yayi mata irin wannan tambayar kuma a daidai wannan lokacin tabbas akwai wata a 'kasa kodai wani ne yazo yayi magana dashi akan yana sonta shiyasa yake tambayarta tana da saurayi....................

"Nabilah".

A firgice ta dawo cikin nutsuwar ta tana cewa "na'am Daddy" da mamaki ya 'kureta da kallo yana duban wani irin yanayi data shiga daga lokacin da yace mata tana da saurayi yace "baki bani amsata ba kina dashi I mean kin samu wani ko a'a ki fad'a min ni mahaifin kine bayan ni babu wanda zaki iya tara da damuwarki kin gane" kaita d'aga ta kasa magana a yanzu yaci gaba "ok Ina sauraron ki kina dashi"? Runtse ido tai hawaye yana cikasu amma saboda kada su gani ransu ya 6aci ko suji ba dad'i yasa ta d'aure ta mayar dasu bata bari sun fito ba ta sake sunkuyar da kanta qasa sosai tana girgiza kai murya can ciki tace.

"A'a Daddy bani dashi".

"Ok shikenan na fahimta dama Alhaji Ashraf ne ya sameni da wata magana tun jiya amma na kasa na tareki na fad'a miki saida muka gama yanke shawara a tsakani na da mahaifiyar ki sannan yanzu nace ta kira min ke Nabilah kin sani cewa aure baya haramta akan kowa sai wanda kuka sha nono d'aya ko? Ya fad'a yana kallonta kaita d'aga zuciyarta na sake tsinkewa taji ya d'ora da cewa.

"To kamar yadda nace miki haka to hakance ta faru a kanki kinsan Alhaji Ashraf abokina ne na gaskiya tun tasowarmu komai tare muke yi ba'a ganin tsakanin mu muna yiwa juna wata irin yarda da so da sha'kuwa kamar na uwa da d'anta kema sheda ce domin tunda kika taso kike gani na muta tare da Ashraf ya riga ya zama d'an uwana ya wuce matsayin amini balle aboki ina matukar ji dashi a rayuwa sannan babu abinda zai nema a gurina na hana shi ko menene shi koda ace zan rasa rayuwata wanjen ganin ya samu farin ciki zan iya hakan Ashraf mutum ne na 'kwarai na ha'ki'ka wanda mutum zai dau'ki amana ya bashi wallahi na tabbata bazai taba cutar da wani nawa ba bani d'in bama,,, shiru yayi yana jinjina kai tare da d'an dafe goshinsa ya shafa fuska yana sauke nannauyan numfashi a karo na babu adadi ya zubawa Nabilah ido wacce jikinta yake rawa tun kafin ya gama fad'ar abinda yake fad'a addu'a kawai take karantawa a zuciyarta tana fatan Allah yasa ba cewa zaiyi Alhaji Ashraf ya samo mata mijin aure ba bataso ta qara yin aikin baban giwa so take a barta ta nutsu sosai hankalinta ya dawo jikinta ta samu mijin 'kwarai mai kyakkyawan halaye abin kwatance ta aura ba miji mai ba'kar zuciya ba......................

"Nabilah".

Alhaji Tajuddeen ya kira sunanta "na'am Daddy".

"Ke musulma ce kuma kin yarda da kowacce 'kaddara ce data sameki me kyau ko akasin ta sannan duk abinda kikaga ya sameki dama bazai kuskure miki ba abinda Kuma daya kuskure miki dama bazai sameki ba na sani zakisha mamakin maganar dazan fad'a miki zakiga tamkar ba a gaske bane mafarki ne saboda nauyin maganar saidai ya zama dole na fad'a miki domin komai a kanki ne, Nabilah jiya bayan na fita office Alhaji Ashraf yaje ya sameni yayi min magana a kanki cewa kina da saurayi ne yanxu nace ban sani ba saina tambaye ki shine yace to idan na tambaye ki kince babu kowa shi yana SONKI😳 zai aureki idan harkin amince🙊" Alhaji Tajuddeen ya karasa maganar yana kallonta sosai domin yaga yanayinta ya zata kasance idan taji abinda Alhaji Ashraf yake so a gurinta, aiko cin karo yayi da wani irin ba'kin mummunan tashin hankali a fuskarta wata iriyar ba'kar kakkarwa jikinta ya d'auka lokaci guda ta susuce idanuwanta suka daina gani sai hawaye masu gumin zafi dake zuba mata tana Kuma girgiza kai tare da dafe saitin zuciyarta da take jin kamar tai tsalle ta fito waje tsabar tsananin harbawar da take na firgicin data tsinci kanta mi'kewa tai da'kyar tana kallon fuskar Alhaji Tajuddeen wanda shima har lokacin ita yake kallo baki ta bud'a zatai magana ta kasa sai wani mayan kukan tsantsan razani daya taso mata a gigice ta fashe da kuka tana ficewa daga parlon da gudu ko takalminta bata tsaya d'auka ba tana shiga bedroom ta fad'a kan gado tana sake fashewa da sabon kukan damuwa da d'imuwa tare da danna kanta cikin bargo ta hanyar son hanawa kanta wadataccen numfashi me kyau ko zata samu wata 'yar salama a rayuwarta me cike da jarrabawa da 'kalubake daga wannan yakau sai wannan.

Bayan fitar Nabilah jiki a sanyaye cike da damuwa Hajiya Fatima ta kalli Alhaji Tajuddeen wanda ya dafe kansa tana cewa "ka gani ko Alhaji dama tunda kazo da zancen nan na fad'a maka Nabilah kanta bazai

Please Login or Register in order to submit comment