Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bilkisu tace "har gidan ki kuma to waye ya kawota kodai Alhaji Tajuddeen d'in ne suka zo tare to amma me zasu zo yi gurin ki ma ko tare da Alhaji Ashraf d'in suke"? Kai Hajiya Sadiya ta girgiza tana cewa "a'a ba tare suke ba tab Alhaji Ashraf ne zaizo gidana inda nake amma kema dai fad'a kike saboda dad'in zance ko? Hum ni bama wannan ba kinsan abinda ya bani tsoro ina kallonta naji gabana ya fad'i yanayi na ya sauya zuciyata tahau bugawa da qarfi da sauri shiyasa ma na Kira ki me hakan yake nufi dan kawai naga yarinyar zanji haka"?.

Shiru Hajiya Bilkisu tai zuwa wani lokaci tayi dariya cike da tsokana tace ''kodai kin fad'a tarkon son mahaifin ta ne professor Alhaji Tajuddeen idan ba haka ba meyasa xakice dan kawai kin ganta sai hankalin ki ya tashi haba Hajiya Sadiya kina da son d'orawa kanki damuwa dan Allah ki sassauta wannan abun tsabar son da kikewa minister Ashraf ne shiyasa idan kika ga makusancinsa sai kiji gabadaya kin nemi nutsuwarki kin rasa tunda kinga Daddyn Nabilan da kike magana a kanta abokin Alhaji Ashraf d'in ne sosai ba'a ganin tsakaninsu Kuma ance aminta ce mai qarfi tun suna matasa har zuwa d'agowarsu amma kinga ta inda suka bambanta shi Alhaji Tajuddeen yayi aure domin ga zahiri nan kinga 'yarsa a gabanki sa6anin Alhaji Ashraf da bai ta'ba furtawa mace kalmar soba shiyasa ma kike matukar shan wahalar sa domin baisan yadda zafin so yake ba bai ta'ba yinsa yaji yadda ake ji ba dan haka kullum nake gargad'inki ki ri'ka masa uziri kinji qawar kina binsa a sannu harya fahimci menene so ya fuskance ki".

Sauke ajiyar zuciya Hajiya Sadiya tai cikin jin d'an sassauci sakamakon wannan maganar da hajiya Bilkisu tai Mata tace "kwarai haka ne kin fad'i gaskiya qawata nagode sosai da nuna kokarin ki gareni".

"Ok karki damu zan Kira ki yanxu akwai abinda nake yi saboda ina son jibi zanje Dubai na saro kaya ne".

"To shikenan na gode Bilkisu" Hajiya Sadiya ta fad'a tana kashe Kiran tare da manna wayar a 'kirjinta tace "kai alhamdulillah har naji dad'i wallahi da ina neman rud'a kaina a banza bari na koma kar Husnah taga na barsu bayan taxo da ba'kuwa" aje wayar tayi tana fita har lokacin suna zaune inda ta barsu suna hira da dariya sosai babu wata matsala suna cikin nishad'i zama tai batare da tace musu 'kala ba kawai ta d'ora kafa d'aya kan d'aya tana kallon Nabilah a fisge idan taga kamar Nabilan xata ganta sai tai saurin d'auke kanta har kusan magriba sannan ta mi'ke zata tafi gida Hajiya Sadiya ta bata kayan kwalliya da doguwar riga me tsada harda handbag domin kayan sana'ar ta kenan godiya Nabilah tayi mata Husnah tayi Mata rakiya zuwa harabar gidan inda tayi parking da motarta bayan sunyi sallama ta wuce gida.

Hajiya Fatima tana parlor a zaune Nabilah ta shigo tare da zama tana aje ledar hannunta tace "barka da gida Mami na" kallonta Hajiya Fatima tai tana cewa "yauwa kin dawo"? Kai Nabilah ta d'aga tana mi'kewa tace "eh Mami ga tsaraba ma ta bani doguwar riga da kayan kwalliya harda handbag".

"Ok an gode mata kije ki aje kayan ki dawo dama Daddyn ki yana nemanki tun d'azu yayi tunanin kin dawo nace a'a".

"Ok bari na dawo yana gida ne"?.

"Eh ya dawo yana part d'insa".

"To tsaya na aje kayan naje" ta fad'a tana d'auka ta shiga part d'inta tana ajewa ta fito ganin bataga Hajiya Fatiman ba yasa ta shige part d'in Daddyn nata a zaune ta samesu da sallama ta shiga tana zama tare da gaisar da Alhaji Tajuddeen amsawa yayi yana kallonta tare da sauke numfashi saboda tunani ta Ina zai fara yi mata maganar da Alhaji Ashraf ya fad'a masa taya zaice ta daina mu'amala da Husnah ta ruwan sanyi batare da 6ata ran dukkan su biyun ba? sake kallonta yayi yana cewa.

"Nabilah a ina kuka had'u da wancan yarinyar Husnah Sahah ko a school d'in"?.

Nabilah tayi mamakin jin tambayar da Alhaji Tajuddeen d'in yayi mata batai tunanin abinda zai fad'a ba kenan to meyasa ya tambaye ta? Kaita d'aga tana cewa "eh Daddy a school muka had'u da ita".

"Shekara nawa da had'uwar ku"?.

"Tun farkon shigata school d'in muka had'u muke 'kawance da ita har yau kuma ina jin dad'in zama da ita domin tana da hankali".

Sake sauke ajiyar zuciya yayi a karo na biyu yana cewa "da akwai sha'kuwa a tsakanin ku"?.

"Eh Daddy sosai ma ni bayan ita bani da wata 'kawar na yarda ita kamar yadda itama ta yarda dani nasan bazata ta'ba cin amanata ba har abada".

"Ok Masha Allah shikenan tashi kije Allah ya tashe mu lafiya" Amin Nabilah ta fad'a da fara'a a fuskarta duk da batasan me tambayar da Alhaji Tajuddeen ya mata ba ta mi'ke tana fita Hajiya Fatima ta kalleshi tana cewa "amma Alhaji meyasa baka fad'a mata wata magana ba ka bari ta tafi taji kana cewa masha Allah me hakan yake nufi ko ka fasa hanasu mu'amalar"? Kai ya jinjina yana cewa "eh gaskiya Fatima bazan iyaba ba dan komai ba na gani Nabilah tace min sun dad'e tare kuma ki tuna shekaru uku baya da suka wuce xuwa yau yanzu da nake miki wannan maganar ki gani kin ta'ba ganin wani hali mara kyau Wanda Nabilah ta koya ko tayi wanda ya sa6a hankali ta'ba yi kece zan tambaya domin kin fini zama tare da ita"?.

Kai Hajiya Fatima ta girgiza tana cewa "a'a ban ta'ba ganin wani abu sa6anin hankali ba gaskiya bata ta'ba zuwa da wani sabon al'amari gidan nan da sunan a gurin 'kawa ta koya ba".

"Ok to kin gani saboda haka hanata mu'amala da yarinyar akwai damuwa me yawa dun riga sun sha'ku sun saba rana tsaka nace ta rabu da ita ba wani hujja abun xai mata barazana sannan zata nemi dalilin hanata kawance da yarinyar nace mata me? Bani da bakin magana tunda kika ga har Allah ya kawo mu yanzu bakiga ta koyar da ita wata mummunar d'abi'a ba to insha Allahu inada tabbacin babu wani abu dazai faru kawai kibar maganar ya wuce shi kuma Ashraf nasan yadda zanyi dashi" kai Hajiya Fatima ta d'aga tana cewa "to shikenan Allah yasa alkhairi tsakaninsu Allah yasa su cigaba da amfanar da junansu Allah yasa tarayyarsu tayi amfani koda a gaba ne" amin Alhaji Tajuddeen yace tare da mi'kewa ya shiga bedroom cewar zaiyi wanka mi'kewa Hajiya Fatima tao tana bin bayansa ta had'a masa ruwan.


MRS ÃL'ÅMÉÉÑ ÁHMÃD CË.

Rayuwar daba Annabi SAW ba rayuwa ba dakai na fake rasulullah ban fake da kowa.
💓Na kirayi sunan Allah mamallaki me mulkin dukkan halittu marashin mataimaki auwalu akhiru zahiru bad'inu ya madaukaki ka karan dubun basira badan halina ba.


Tnks for ur supports 🔥 nagode sosai masoya we will meet again sai mun sake had'uwa be with me at always my lover's.

4~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil khaifina.


TYPING 📲Thu, Jan 2/25. 3:13pm YUSRAH MUSA ABUBAKAR🤘💓💯.



💕MINISTER ASHRAF💕


ÀÑÑÙRÌ WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan haka taken mu yake.


×××××××××××××××××××××××××××××
++++++++++++++++++++++
*******************


STORY WRITTEN ND EDITING


°°°°°°°°BY°°°°°°°°


✍️ Yusrah Musa Abubakar YUSEEN SIR ÄL'ÄMËËÑ ÄHMÄD ÇË.


YMA DUTSE NEW WORLD🌏 sabuwar duniya kuzo kuyi kallo dad'i yana Jigawa garin ilmi garin addini zaman lafiya Jigawa.


5~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil D'a'inah.


WhatsApp no:234 816 098 3083.
yusrahmusaabubakar65@gmail.com


¶~¶~¶~¶~¶~¶~¶~¶~

©®YMA DUTSE


BISMILLLAHIR RAHMANUR RAHIM.


💦Yüsëëñ Sïr Äl-ämëëñ çë💦
PG_____05&06
Washe gari ba school Nabilah a bedroom ta wuni bata fito ba tana karatun exam kanta yad'au zafi domin ko kiran ta da Sultan yayi sama-sama sukai magana akan yadda hidimar graduate d'inta zai kasance da abinda zatayi yace zuwa jimawa zai kawo mata d'inkin dayai mata da sauran abubawan da zata bu'kata kafin ta aje wayar taci gaba da karatun ta bata fito part d'inta ba sai bayan sallar magriba sannan ta d'auko hijab ta fito tana bud'e kofa Sultan ma ya bud'o kofar parlor tsaye sukai suna kallon juna daga baya kowa ya rufe karasowa Nabilah tare da zama tana kallonsa kafin tace.

"Yaya Sultan yau meye sirrin"?.

"Sirrin me"? Ya tambaya cikin mamaki yana kallon ta shima murmushi tai tana tagumi kamar me tunani kuma har lokacin bata daina kallonsa ba tace "gani nayi kayi kyau sosai yau kamar ango wallahi".

Jin abinda tace yasa ya murmusa yana cewa "kin fad'a daidai ai dama angon ne saura wata d'aya fa auren namu haka d'azu Daddy ya fad'a min yace fatan na fara shiri nace masa na gama komai balle ke" dariya Nabilah tai cikin farin ciki tace "au wai kai harsun fad'a maka lokacin bikin amma ni ban sani ba"?.

"Eh idan kin sani me zakiyi"?.

"Amma ko bazan yi komai ba ai zan gayyaci 'kawaye na ko"?.

"To daga gayyatar 'kawayen naki ina shikenan komai saidai a miki"?.

"Me za'ai min"?.

"Kema kin sani".

"Ni ban sani ba kawai ka fad'a min".

"Da gaske baki sani ba"?.

"Kwarai ban sani ba".

"Ok shikenan zan fad'a miki amma ba yanzu ba sai nan gaba".

"Gaba kamar yaushe"?.

"Kamar lokacin da kika bu'kata fad'a min abubuwan da kike so ayi a bikin mu wanne irin tsari zakiyi sannan wanne kalar kaya da make-up zaki d'auka"?.

"Humm ai Yaya Sultan na d'auko buri da yawa nifa a bikin nan so nake mu gwangwaje Ina so ka kama mana moderling event center sannan ga gyaran jiki da wedding gown Ina son guda biyar saboda sati zamu d'auka ana biki tunda kaga bayan ni Daddy da Mami na basu da wani d'an da za'ai shagali dole ne a gyagije sosai ko"?.

D'agowa yayi yana kallon ta kamar me kallon mirror sai kuma yayi murmushi yana jinjina kai yace "as you wish duk abinda kike so shi za'ai miki madam".

Cike da murna Nabilah tace "da gaske zakai min duk abinda na lissafa maka"?.

"Eh Nabilah kinfi karfin komai a gurina nifa Nabilah koda raina akace na bayar madadin ki zan bada ina yi miki so a zuciyata wanda bazan iya kwatanta girman saba kawai saidai nace ina son ki".

Sauke ajiyar zuciya Nabilah tai itama cikin tsananin son da take masa tace "Yauwa Yaya Sultan nagode da nuna kaunar ka gareni na sani samun wanda zai soni kamar yadda ka 'kaunace ni zaiyi wuya ka nuna min gata ka bani duk abinda nake so a rayuwa fatana Allah ya barmu tare" da sauri Sultan ya d'aga hannu sama harda shafawa yace "Amin Nabilah wallahi wannan addu'ar taki bakiji yadda ta sanya min nutsuwa da sanyi a zuciyata ba burina naga ranar dazan bud'e ido na ganki a gidana matsayin matata".

"Insha Allahu Yaya Sultan kamar yaune zakaga lokaci yazo".

"Ai Nabilah gani nake yanzu kamar lokacin baya gudu".

"Yana gudu man kawai dai kaine baka ganin hakan".

"To meyasa ni nake ganin baya gudun"?.

"Saboda ka 'kagu kaga ranar bikin mu shine dalilin dayasa koda lokacin yana gudu kai baza kaji yana gudun ba".

"Haka ne zan tafi domin jiya nazo gidan bakya nan sai iya Mami tace min kinje anguwa gurin 'kawarki".

"Eh naje gurin wannan 'kawar tawa wacce kwanan baya nace muje Yalwawa ka d'auko ta naje gurin tane jiya da safe na dawo bayan magriba".

"Ok muje ki taka min" ya fad'a yana mi'kewa itama mi'kewar tayi suna fita tare har jikin mota ta rakashi anan ma sun dad'e suna hira kamar bazasu rabu da juna ba kafin da'kyar sukai sallama amma duk da haka saida taga tashin motarsa me gadi ya bud'e masa gate ya fita sannan ta juya tana komawa ciki ganin har lokacin babu alamar Hajiya Fatima kawai taje dinning table d'ebi abinda take so ta koma part d'inta balle jiyan Alhaji Ashraf bayan dawowar su ya taho mata da kayan chocolates masu yawa shi take sha shiyasa ma bata fito ta nemi abincin ba.

*** ***Humm tun ranar da zasu gama exam d'in final suka fara shigulgula da kid'a-kid'e kamar a gidan DJ wadanda basa rawa ma ranar saida suka girgiza balle wanda ya saba abun ba'a magana 'yan mata ansha lalle an dau kwalliya kamar ranar zasuyi partyn da sun tsara zasu kama Hall daga baya sai sukace suyi abubuwan su kawai a cikin makaranta yafi suna fitowa daga d'akin exam suka saki ihun murna musamman samari abubawa iri iri tun ranar suka sha kid'a-kid'e kafin washe gari kowa yasha wanka ala tsine uwar me 'karya haka ranar suka taru suka sake gwangwajewa.

Duk abinda suke Sir Ahmad hankalin sa yana kan Nabilah tun data shigo school d'in ya kafeta da ido duk wani motsi da zatai yana binta da kallo saida ya bari lokacin tashi ya kusa ya mi'ke ya yana zuwa inda take tsaye tare da Husnah da sauran 'kawayen su tana ganinsa saida taji gabanta ya fad'i ta rasa meyasa batasan koda hangoshi daga nesa balle yazo inda take ko yayi mata magana saidai tuna daga yau shikenan ba sake ganinta zaiyi ba kuma dama shima state d'insa xai koma yasa kawai ta share batun tabar 6acin ran daya taso mata karta 6ata ranar farin cikinta da damuwa...................


"Nabilah Sir Tajuddeen happy graduation".

Taji muryar Sir Ahmad d'an kallonsa tayi a fisge tace "na gode" tana fad'in haka ta ri'ke hannun Husnah tana janta alamar subar gurin su sake shiga cikin d'alibai ya dakatar da ita.

"Nabilah ina so zamuyi magana ko minti biyar ne domin maybe daga yau baza mu sake had'uwa dake ba" jin abinda yace yasa taji wani sanyi da dad'i ya rufe ta tasan kila gobe ko jibi zai ware hakan yasa ta saki hannun Husnah tana cewa "bari na dawo" ta fad'a suna wucewa da harara Husnah ta raka bayan Sir Ahmad domin ta matukar tsanarsa musamman wannan takurar da yake yiwa Nabilah yana mugun 'kona mata rai.

Can cikin makaranta suka shiga inda ya kasance shiru ba kowa suka sami gurin zama suka zauna Nabilah harda d'ora kafa d'aya kan d'aya ta fuskance shi tunda tasan duk tsiya daga yau shikenan ko a tunani bazata tuna Sir Ahmad ba domin tunanin sa zai ri'ka dawo mata da takurar dayai mata...............

"Nabilah".

"Na'am Sir Ahmad".

Kaiya jinjina yana kallon ta yadda tayi kyau ta tsaru yace "Nabilah na fad'a"? D'agowa tai tana masa kallon mamaki da alamun tambaya tace "me"? Da ido ya nuna Mata kwalliyar jikinta yana cewa "kin yi kyau sosai yau har bansan yadda xan kwatanta miki ba" jin abinda yace yasa cike da jin haushi Nabilah taja tsaki a ranta amma a fili ba yabo ba fallasa tace "tnks" ta fad'a tana sake kawar dakai daga kallon da yake mata.

Gyara zama yayi yana cewa "Nabilah kinsan meyasa na kiraki ina so ne nayi miki tambaya ta karshe daga yau shikenan na sani idan har ba kin amince ba basake had'uwa zamuyi dake ba har abada please Nabilah dan Allah ki amince min ki yarda ki soni ki aureni wallahi ina sonki so na gaskiya da aure ba yaudara ba" yana rufe baki Nabilah ta soma girgiza kai tana cewa.

"A'a Sir Ahmad dan Allah nima kayi ha'kuri ka fahimce ni ina da wanda nake so kuma shi zan aura".

"No Nabilah zuciyata bazata iya ha'kuri dake ba ina matukar sonki ki fahimta please Baby Nabilah Kinga I love you bana jin dad'in wannan shariyar da kike min idan jan aji ne dajan rai na gama jawuwa ki fad'a min kalmar so Nabilah".

"Dan Allah Sir Ahmad ka gane gaskiya nake fad'a maka domin bazan yaudare kaba ina da wanda zan aura".

"Ki rabu dashi Nabilah ki bar batun sa ki 'kyale shi kingan ni nan zan baki komai da kike bukata da jiyar dake dad'i da kud'i masu yawa ki rabu da wancan ki aure ni pls" ya karasa maganar yana shirin ri'ke hannunta a zabure ta mi'ke ganin yana neman d'ora mata hau ta matsa baya ranta a 'bace tace.

"Wai me kake yi haka na fad'a maka da wanda nake so amma ka'ki ganewa ko ana so dole ne wannan wacce irin rayuwa ce dan Allah ka rabu dani ka 'kyale ni haba" tana fad'in haka ta juya fuuuu tabar gurin.

Da kallo ya bita tare da kad'a kai yana sakin wani irin murmushin takaici kafin ya mi'ke yana tafe shi kad'ai yana magana da zuciyarsa har tuntu'be yake yi "meyasa zaki min haka Nabilah ina son ki meyasa kika kasa fahimta waye wanda zaki aura a ina yake dole na nemoshi dole nayi magana dashi ko yana so ko baya so saiya barmin ke ta halin tsiya da masifar da zata sameshi idan har bai bar min keba to shima bazai ta'ba auren kiba saina wulakanta ki na 6ata al'amarin saina sa ki kuka da ba'kin ciki ba keba hatta danginki sai sun shiga tashin hankali zan rabaki da abinda kike tunkaro dashi a jikin ki sai naga karshen 'karya" dariya yayi shi kad'ai yana jinjina ya koma ainishin inda ake shagalin amma babu alamar Nabilah maybe tana baro gurinsa ta fita a school d'in ta'be baki yana d'aga waya ya kira wata budurwa da kamar minti biyar tazo cikin 'kaguwa yace.

"Nazzi yaya kin samo min"?.

Murmushi tai tana d'aga kai tare da mi'ka masa wayarta tace "eh na samo maka amma da'kyar a gurin wata student 'yar classmates d'insu ce saida na bata kud'i masu yawa kafin itama ta shiga cikin lad'iban ta nemo min" kaiya jinjina yana amsar wayar ya zubawa numbar wayar Nabilah ido kamar ita yake kallo daga baya ya d'auko tasa wayar ya dau'ki numbar yayi saved sannan ya mi'ka mata yana cewa.

"Ok nagode Nazzi muje nayi dropping d'inki a gida saina wuce idan lokaci yayi zan neme ki kece zakiyi min aiki".

Murmushi tai daidai ya bud'e mota ya shiga itama ta shiga d'ayan site d'in tana cewa "amma sakamakon irin wannan aiki ina karbar kud'ad'e fa masu yawa domin kasan aikin sayar darai ne kai kanka sheda ne kasan wace Nabilah kasan mahaifin ta ba 'yar 'kananun mutane bace idan tsautsayi yasa a wajen aikin aka samu akasi bansan wanne hali zan shiga ba".

Kai Sir Ahmad ya d'aga yana cewa "nasan 'yar waye ita shiyasa zan bi ta hikima na 6ata mata rayuwarta kamar yadda ta bakanta raina ta hanyar 'kin amincewa 'kudurina kin gane? karki wani damu ina tare dake babu yadda za'ai su gane zamu had'a baki tare da Danual komai zai kasance a sirrince ina kammala aiki na zamu tattara kayan mu harke mubar Dutse ko koma state namu acan za'ai bikin auren mu ni dake" kaita d'aga masa cikin jin dad'i domin tana mutuwar sonshi amma dalilin Nabilah yasa baya bata lokaci yanzu kuma da yaga Nabilan tayi masa nisa dole ya dawo gurinta.

Nabilah kam 6uya sukai ita da Husnah sai bayan sallar la'asar suka bar school d'in sakamakon Sultan ne yazo d'aukar Nabilah tun a cikin school d'in sukai sallama tana cewa mata sai ranar biki zata zo mata fitarsu ba jimawa Husnan itama ta dau'ki motarta ta nufi gida daidai tayi parking taga Hajiya Sadiya ta fito hankali tashe ranta a 'bace hatta mayafinta yana kafad'arta bata samu nutsuwar yafawa ba da sauri ta nufi parking space idonta a rufe ko ganin Husnah batai ba wacce ta tsaya kamar sanda cike da mamaki tana binta da kallo harta bud'e mota zata shiga Husnah tace.

"Momy".

A firgice Hajiya Sadiya ta juyo tana kallon Husnah da jan idonta domin batai tunanin ita bace bataso ta dawo ta sameta bata fita a gidan ba amma hakan ma bazai hanata fita ba batai magana har Husnah ta rufe murfin motar data fito ta karaso gurin Hajiya Sadiyan ta kalleta sosai kafin tace.

"Momy meya faru ina zuwa yanzu haka magriba tayi naga ranki a 6ace"?.

Shiru Hajiya Sadiya tai ta rasa me zatace mata dan haka kawai tace "eh akwai inda zanje ba zama zanyi ba yanzu zan dawo ki kula kar kije ko'ina" ganin tana shirin shiga mota Husnah tace "Momy dan Allah karki fita yanxu Ina zakije ne a wannan daren"? Husnah ta fad'a ranta duk babu dad'i a fusace Hajiya Sadiya ta juyo tana cewa "gidan mataccen ubanki Sahah Bilal zanje yanzu kin gane inda zanje"? Karasa maganar tana kallon yadda Husnah ta zaro ido jin abinda tace ganin batai magana ba yasa taja dogon tsuka tana shiga motar da 'karfi ta rufe tare da yi mata key ta fita daga rumfar aje motocin ta nufi gate tare dayin horn me gadi ya bud'e ta fita Husnah tana tsaye tana kallo saida taga me gadin ya mayar da gate ya rufe sannan ta sauke wani irin zazzafan numfashi idonta fal da hawaye ta koma gaban motarta tana d'auko handbag d'inta ta cire key d'in motar kafin ta rufe ta shiga gidan cike da tsananin damuwa.


Hajiya Sadiya tana fita daga mopal-base government house ta nufa da mugun gudu burinta kawai ta had'u da Alhaji Ashraf ko hankalinta zai dawo jikinta tsabar tsaron dake gidansa ba'a barta ta shiga ba ba'kin ciki kamar zai kasheta gashi ta kira numbern wayarsa yafi a kirga ta'ki ya d'aga tana tsaye ta jingina a jikin motar ta kifa kanta cike da damuwa da tashin hankali zuwa bayan sallar isha kusan karfi tara taji motoci suna parking da sauri ta juya tana kallon gurin motocin gidan Alhaji Ashraf ne daidai an bud'e kofar babban gate d'in gidan sun fara shiga Hajiya Sadiya ta cije yatsa cike da takaici tasan yau ko mutuwa zatai bazai saurare taba saidai ta barwa gobe, akan idonta suka gama wucewa kafin aka mayar da gate aka rufe runtse ido tai ba zato taji hawaye yana zuba kaita jinjina tare da nufar motarta ta shiga ta koma gida a parlor ta samu Husnah ko iya shiga part d'inta batai ba tunda taga fitar Hajiya Sadiyan ganin ta shigo yasa zubur ta mi'ke tana kallon yanayin rashin walwalar dake kan fuskarta tace.

"Momy ina kika je"?.

Wani irin kallo Hajiya Sadiya tai mata jin tambayar data jefo mata batare data motsa koda lips d'inta ba kuma bata tsaya ba ta wuce part d'inta da kallo Husnah ta bita tana sau'ke ajiyar zuciya itama ta shiga nata part d'in tunda tasan ko tayi uwa yata maye ayau Hajiya Sadiya baxatai mata magana ba saidai gobe idan ta huce........✍️ AYI HA'KURI YAU TYPING D'IN BABU YAWA.


MRS ÃL'ÅMÉÉÑ ÁHMÃD CË.
Mai tambarin yma dutse new world me alfaharin jihata ce ko'ina nake inda zan zarce a cikin Nigeria muke da gada mun taka kan dutse birnin daraja daya batse ga haske🎆 ga adon Dutse 🏞️.

See you tomorrow morning.
We will meet again.
Be with me at always my lover's.


6~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Taibanah.

∆Saleem Musa Abubakar
∆Naja'at Musa Abubakar
∆Fatima Musa Abubakar
∆Aishat Musa Abubakar
∆Abubakar Musa Abubakar.


@YUSRAHMS CE.


TYPING 📲 SUN, JAN3/25 10:18pm YUSRAH MUSA ABUBAKAR.


💕MÏÑÏSTËR ÄSHRÄF💕


ÀÑÑÙRÌ WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan.


WHATSAPP NO:234 816 098 3083.
Yusrahmusa65@gmail.com



STORY WRITTEN ND EDITING
By°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

YMA DUTSE NEW WORLD🌏.


📝✍️WRITER
1_Yarima abdul-maleek
2_Rayuwa biyu
3_Safreeyyah
4_D'an millionaire
5_Royalty
6_Zuciyar Aliyu ce
7_Tajuddeen Aryam
8_Me kamar sarki
9_Husnah ko Badiyat
10_Dama kece
11_Minah-Umer
And now........✍️📝minister Ashraf


7~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Abidinah.


🌺🥀🌹🏵️🌷🌸💐🌻🌹🏵️🌹🥀🌺
Bismilllahir Rahmanur Raheem.


💦Yüsëëñ Sïr Äl-ämëëñ çë💦
PG____07&08
Duk yadda Hajiya Sadiya taso had'uwarta da Alhaji Ashraf bai samu ba har hanya ta nema yadda zata samu ganinsa amma bata samu tayi ba'kin ciki ta shiga damuwa har saida ta d'orawa kanta jinya ta kwanta asibiti kusan kwana goma sha biyar bata samu sau'ki ba karshe da'kyar ta samu tad'an farfad'o aka bata sallama amma tsabar karfin hali tana daga ta d'ago tana kallon Hajiya Bilkisu dake gefe tana had'a mata tea d'in da Husnah ta dafa mata cikin muryar rashin lafiya tace.

"Bilkisu dan Allah bani waya ta a cikin handbag d'ina".

Hajiya Bilkisu batai magana ba saida ta gama had'a mata ta mi'ko mata kar'ba tai tana ajewa a gefe tace tare da girgiza kai da mamaki Hajiya Bilkisu tace "haba Sadiya ya haka kuma baki da lafiya fa ki duba yadda kika koma ke bakya tsoron abinda zai faru a gaba ne taya kike tunanin zaki samu sau'ki bayan kinsa damuwa a ranki"? Yamutsa fuska Hajiya Sadiya tai tare da dafe kanta da yake sarawa numfashinta na fita da hucin zafi tace "ba wannan

Please Login or Register in order to submit comment