Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasa a fridge ba sai kinzo ki gani da kanki yaso kin dawo kun gaisa har yace zai jira ki taso sai kuma akai kiransa a waya shine suka fita tare da Daddyn naki".

Murmushi Nabilah tai tana d'agowa kalle ta domin tunda taji tace Daddyn ta tasan wa take nufi aje wayar tai cikin zumud'i ta mi'ke tana zuwa ta d'auko kyakkyawar ledar dake she'kin tabuntaka balle kumà abinda yake ciki ta dawo tana zama har lokacin da murmushi akan fuskarta ganin kayayyakin da suke ciki yasa ta sake fad'ad'a murmushin ta cikin walwala tace.

"Wai Mami kina nufin Daddy Ash yazo gidan nan yau? Wayyo gashi bana nan".

Zaro ido Hajiya Fatima tai tana kallon ta da mamaki tace "Daddy Ash kuma Nabilah abokin uban naki guda kike kira da Ash"? Dariya Nabilah tai tana cewa "to Mami ba sunan shi bane"?.

"A'a ba sunan shi bane tunda ba Ashraf kika ce ba shi kuma sunansa kenan".

"Ai Mami da Ash da Ashraf duk d'aya ne".

"A gurinki ba amma ba d'aya bane tunda shifa ba yaro bane da saurayi ne saiki kirashi da hakan amma ubanki guda"?.

"To Mami bakiji akace dakai wasa da baban wani gara kayi da naka ba shiyasa nayi hakan".

"Au haba kenan yanzu zaki iya kiran naki tsohon da Daddy Taj ko? Tunda ai shima Tajuddeen yake".

Hhhh dariya Nabilah tai tana fiffito da kayan zallar chocolates ne kala kala sai yogurts da ice cream da tsadaddun biscuits humm Hajiya Fatima bata bud'a taga mene a ciki ba amma tasan za'a rina kallon Nabilah wacce ta 6are wata babbar chocolate tana sha tayi ta d'an girgiza kai tana cewa "wai mutum ya girma shekara ashirin da yan kai amma saboda babu qani yasa suke shagwa'ba ki yanzu irin wannan kayan za'ki haka kamar 'yar yaye"? Dariya Nabilah tai tana mi'ko mata guda d'aya tace "Mami kema gashi ki sha wadannan chocolates d'in na dabam ne bana yara bane" kai Hajiya Fatima ta girgiza "a'a nikam bazan sha zaki ba kema da kike wadansu abubuwan ganin ba wani sai kene da kina da qani ko qanwa baza kiyi wani abun ba koda kud'i" murmushi Nabilah tai tana hade kayayyakin ta mayar dasu cikin ledar tace.

"Shiyasa ya Sultan yake cewa wai Daddy's dina sune suka 6ata ni dashan abubuwa shiyasa ban damu da abinci ba shikam bazai yarda da wannan shaye shayen kayan za'kin ba dole ya koya min cin abinci".

Jin abinda Nabilan tace yasa Hajiya Fatima cews "oh nina manta ma d'azu da safe kunyi sa6ani kina tafiya school sai gashi ya shigo gidan yana neman ki nace masa kin tafiya makaranta shima a lokacin hospital zai tafi dana fad'a masa haka sai kawai ya juya ya fita ban sani ba ko yaje"?.

Kai Nabilah ta girgiza tana cewa "A yau ya Sultan yazo gidan nan Mami"? ta fad'a da surprise a fuskarta domin jiya da sukai waya ya fad'a mata zaiyi tafiya yau da safe ya akai kuma ya fasa d'an shiru tayi cikin nazari zuwa wani lokaci ta d'ago tana kallon Hajiya Fatima kamar zatai magana sai kuma ta fasa tana mi'kewa ta shige part d'inta ta d'auko hijab ta dawo parlon da mamaki Hajiya Fatima tace "Nabilah ina zuwa haka daga dawowar ki a school ko hutawa baki yiba balle kici abinci"? Kai Nabilah ta girgiza "no Mami na 'koshi zanje gidansu Daddy Mukhtar ne naji Yaya Sultan ya fasa tafiyar".

"Amma me yasa bazaki kirashi a waya ba dole sai kinje kinsan ba jininku ne ya had'u da yaran gidan ba musamman Rasheedat harda ita kanta matar gidan Hajiya Salmahn to me zakije kiyo".

"To ai Mami ba gurin ta zanje ko gurin yaran gidan ba ni gurin ya Sultan zanje".

"Ok gurin Sultan d'in da zakije inace a gidan yake kuma d'anta ne ko asibitin doctor Sambon zaki bishi"? Hajiya Fatima ta fad'a tana qare mata kallo jiran amsa kai Nabilah ta girgiza tana cewa "a'a ba hospital zan bishi ba asalin gidansu zanje ba dad'ewa zanyi ba yanzu zan dawo".

"Humm Nabilah kenan ni harna rasa bakin magana wai da gaske ke a zuciyar ki son Sultan kike bayan kina kallon irin zaman da mahaifiyar sa Hajiya Salmah keyi damu ga fitsara gurin 'ya'yanta amma ke duk hakan yayi miki a haka kike son kije gidan matsayin surukarta bayan kinsan har gobe bata goyon bayan Sultan akan neman aurenki da yake yi haba Nabilah ina kika Kai tunanin ki ya kamata ki tsaya guri d'aya kiyi nazarin abinda kike son aikataw....................

Bata karasa maganar ba akai kiranta a waya dan haka ta mi'ke tana shiga part d'inta domin ta amsa kiran a nutse ba kamar tana parlon ba shiru Nabilah tai bayan wucewar Hajiya Fatima ta fad'a cikin tunani ta sani har gobe Hajiya Salmah bata son ala'kar ta da d'anta Sultan amma tunda ba Sultan d'in ne ya 'kita ba itama bazata watsa masa qasa a ido ba zata aureshi kodan samun farin cikin su ita dashi ai tasan duk tsiya ba gida d'aya zai zauna da Hajiya Salmahn ba balle yawan fitina ta ri'ka tashi, sauke numfashi tana mi'kewa ta dau'ki ledar chocolates da key d'in motarta ta shige part d'inta domin ta samu tayi taga magriba tayi gara taje tayi sallah yau yadda take jinta a gajiyen nan barci zatai da wuri ko jikin nata ta samu ya daina ciwon inta tashi.

***
Da dare har tayi shirin barci ta kwanta ko wayarta bata kashe ba tunanin ko Sultan zai kira kwanciyar ta da mintuna kad'an har barcin ya fara fisgarta kiran Sultan ya shigo da sauri ta bud'e ido tana tashi zaune ta d'auka ganin numbar wanda take tunani yasa saida taiwa secreen d'in wayar kiss kamar Sultan d'in take gani kafin ta d'aga tare da fara ido tana kashe murya tace.

"Hello ya Sultan barka da dare".

Shima a nasa 6angaren yana bedroom d'insa a kwance ya lullu'ba da bargo yana rungume da pillow ya sake gyara kwanciyarsa sosai yana murmushi yace.

"Ya kike Baby na"?.

"Ina lafiya ya Sultan ashe bakai barci ba naga goma ta kusa"?.

"Eh taya kike tunanin zan iya yin barci bayan a yau ban sanya ki cikin idanuwan da zasu barcin ba tunda safe na wuni da kewar ki gashi ban samu na dawo gida da wuri ba dana dawo daga hospital Ina sauri bayan nayi wanka da sallah ko tsayawa cin abinci banyi ba domin kar dare yayi na samu nazo gurinki sai kuma nayi ba'kon bazata abokina Sameer ne yazo min ziyara tun daga Miyetti shiyasa ban samu nazo ba amma ya kike fatan kin wuni lafiya"?.

Kaita d'aga kamar yana ganinta tace "lafiya kalau gaskiya nayi kewarka ya Sultan" ta fad'a a shagwa'be domin ba lefi ta riga data saba bata magana d'aya biyu saita saka shagwa'ba a ciki.

"Nima nayi kewar ki Baby gashi yanzu idanuwa na suna son ganinki ba hali shiyasa nake fatan da naje Indian nan na dawo zanyiwa Daddy magana kawai a d'aura min aure dake ki dawo kusa dani sai hankali na yafi kwanciya dama kullum cikin kishi da fargaba nake kwana da'kyar nake iya barci idan na tuna kullum sai kin fita waje kinje school samari suna ganinki suna kalle mun ke kada wani banzan yaji kinyi masa ya tareki da maganar so ko ya biyoki gidan ku hummm wallahi saina 6alla masa 'kafa na zubar masa da ha'kora" .


Hhhhh dariya Nabilah tai tana cewa "kai Yaya Sultan akwai kishi ji yadda kake magana da fad'a Kuma a misali na tambaye ka a bisa tsautsayi saika ganni tare da wani saurayin ina hira dashi ya zaka yi"?.

Jin tambayar datai masa yasa ya zabura har yana cilli da bargon daya lullu'ba ya soma girgiza kai tare da dafe saitin zuciyarsa dake bugawa yace "nooo Nabilah please dan Allah karki kara fad'ar irin haka idan ba so kike zuciyata ta buga ba" zaro ido tai tana cewa.

"kai ya Sultan ya zuciyarka ta buga kuma ni nayi ya? Kasan irin son da nake yi maka kuwa bana jin zan iya rayuwa idan batare dakai ba".

Kaiya jinjina yana sakin murmushin da saida ta jishi a kunnen ta yace "yauwa ko kefa Baby nagode sosai yanzu ki kwanta kiyi barcinki saboda kada ki makara gobe idan Allah ya tashe mu lafiya maybe kafin na wuce hospital zan biyo ta gidan naku ki kula min da kanki".

"Ok ya Sultan goodnight".

"Shikenan mu kwana lafiya Baby".

Sauke ajiyar zuciya tai bayan ya katse Kiran sai yanxu taji wani irin dad'i da iska mai sanyi tana ratsata sakamakon wayar da sukai amma da ta hana kanta sukuni lokaci guda ta koma kamar mara lafiya ita a zatonta ko laifi ma tayi masa domin ta sanshi da zuciya shiyasa duk abinda tasan zai 6ata masa rai bata yinsa ko menene qara gyara kwanciya tai tana sake rungumar pillow da murmushi akan fuskarta ta rufe ido tun tana tunani har barci ya d'auketa.

✨✨✨✨Saboda tasa abun a ranta ko barcin kirki batai ba sai mafarki iri iri har asuba sannan ta tashi duk jikinta ma ciwo yake da'kyar take takawa kamar mara lafiya ta shiga toilet tayo alwala ta fito tana saka kaya da hijab tai sallah bata tashi a gurin ba ta dau'ki al qur'ani ta bud'e ta fara karantawa a bayyane cikin zazza'kar muryarta me dad'in sauraro kafin gari yayi haske saida tayi izu biyar sannan ta rufe tayi addu'a ta shafa ta mi'ke tana mayar dashi inda ta d'auko kafin ta cire hijab d'in da kayan ta d'aura towel ta shiga wanka shaf shaf ta fito sauri take ta ta kammala shirinta sakamakon ta kwana da cewa Sultan zaizo kafin ya wuce asibiti haka ta tsara kwalliya mai kyau ta d'au wankan ala tsine uwar me 'karya hatta takalmin data saka a ranar yasan yau zatai muhimmin ba'ko d'aukar handbag d'inta tayi tana fitowa daga part d'inta tasan ba kowa a parlor yanzu idan ma ta fita sai iya 'yan aiki dan haka part d'in Daddynta ta shiga suna zaune tare da Hajiya Fatima suna zance ta shiga da sallama duk binta suke da kallo cikin mamaki yadda tayi kyau ta fito d'as da ita zama tai bayan ta gaisar dasu Alhaji Tajuddeen dahar lokacin yake kallon d'iyar tasa ya sauke numfashi tare da godewa Allah sannan yace.

"Nabilah yau ko gasar kyau ake yi a makarantar taku ne? Naga kin d'au wanka kamar zakije gano shugaban qasa"?.

Murmushi Nabilah tana kallon Hajiya Fatima dake mata kallon tasan saboda dawa tai wannan wankan tace "a'a Daddy zanyi ba'ko ne" da mamaki Alhaji Tajuddeen ya sake dubanta yana cewa "ba'ko kuma wanne iri Nabilah da wannan sassafen"? "Eh Daddy Yaya Sultan ne zaizo" ta fad'a tana d'agowa ta kallo Hajiya Fatima wacce ta d'an girgiza kai dama tasan sai shi murmushi Alhaji Tajuddeen yayi yana kallon ta yace "Ok yayi kyau Allah ya taimaka"..

"Amin" Nabilah tace tana mi'kewa zata fita tace "na tafi school Daddy da Mami" ta fad'a tana shirin fita dakatar da ita Alhaji Tajuddeen yayi da cewa "amma bakiyi breakfast ba Nabilah zaki tafi ki jira su dafa Miki ko indomie ce kici kar ulcer ta kama ki" kaita d'aga "to Daddy bari naje kitchen d'in" saida ta bud'e kofa ta fita Hajiya Fatima ta kalli Alhaji Tajuddeen tana cewa.

"Amma Alhaji nikam sai nake ganin abun nan kamar akwai damuwa a cikinsa fa ni Kuma bana son tashin hankali" da alamun tambaya Alhaji Tajuddeen ya kalleta yana cewa "abun me"? "Auren Sultan da Nabilah har yanzu bana jin farin ciki akan haka kuma ba kowa bane sila sai mahaifiyar shi lefin Hajiya Salmah ne domin tun farko itace ta 6ata abun Kuma nasan har gobe tana nan akan bakanta tunda ta rantse ta sake rantsewa ba karo d'aya ba cewa indai itace ta haifi Sultan a cikinta bazata bari ya auri Nabilah ba na rasa me yake damunta".

"Oh akan haka ne hankalinki ya tashi dan ta fad'i wannan aiko tayi 'karya zan nuna mata kuskuren ta a fili ta hanyar aurawa Sultan Nabilah naga wanda zai hana kaf danginta idan basu taru basu isa su juya min ra'ayi ba balle ita maganar rantsuwa kuma tayi a banza idan anyi auren an gama sai tayi azumin kaffara domin indai kinga ba'ai auren nan ba to dama can Nabilah ba matar Sultan bace dan haka ki 'kyale ta shirmen banza take tunda shi yaron yana so an wuce gurin ai duk wani ihu bayan hari da zatai a banza bata Isa hana muyi abinda mukai niyya ba Mukhtar tun kafin yasanta nake tare da d'an uwa na tsawon rayuwar mu kinga sama takai wata bazata zo ta lalata mana zumunci da gur6ata mata ahli ba" kai Hajiya Fatima ta d'aga tana cewa "gaskiya ne shikenan Allah ya bamu ji da gani na gari bari naje naga wadannan sun gama aikin had'a breakfast d'in ne koda saura" mi'kewa tai tana fita domin ta gano.

**Fitowar Nabilah Sultan ya kirata duk zaton ta yana gida saida ta fito main parlor ta ganshi a zaune yasha farar rigar likitoci yana sanye da glass a idonsa hankalinsa yana kan wayar dake hannunsa karasawa tai tana lekawa taga me yake gani har baisan ta fito ba cin karo tayi da photonta cikin mamaki ta tsaya kallon photon domin bata san ma dashi a duniya ba sai yau data gani da alama bata sani ba yayi Mata tunda hankalinta ya karkata xuwa wani gurin dabam murmushi tai tana jinjina kai kafin tasa hannu ta kar'bi wayar tana cigaba da kallon photon yayi matukar kyau d'agowa Sultan yayi yana kallon ta daidai ta zauna yace.

"Gimbiya sarautar mata kin gama shiryawa ne school xaki tafi"?.

Kaita d'aga "eh na gama komai tafiya zanyi" mi'kewa yai yana cewa "ok muje na kaiki da kaina yau dama badan aiyuka sun min yawa ba kullum nine zan ri'ka zuwa ina kaiki amma hakan za'ai saina ri'ka fitowa da wuri yadda bazan makara a hospital ba muje" ya fad'a yana yin gaba mi'kewa tai tana bin bayansa har gaban motarsa ya bud'e Mata ta shiga sannan ya zagaya shima ya shiga yana tada motar suka bar gidan hankalinta nakan waya bata fargaba har suka je kwanar gidan yarima Saida taji ya tsaya ta d'ago ganinsu a inda batai tunanin zuwansu yanzu ba tasan maybe Husnah bata cikin makarantar tunda jiya tace mata Momyn ta tayi tafiya idan an tashi a school gidan 'kanwar Momyn nata zata wuce kafin ta dawo tuna hakan datai yasa ta kalli Sultan tana cewa.

"Ya Sultan please dan Allah muje ka shiga Yalwawa kota sabon titin I.M.G (ai em ji) ne ka d'auko qawata a gidan qanwar Momyn ta" jin abinda tace yasa shi kallonta yace "amma tun da baki fad'a min ba da nabi ta wajen Hasinah hotel sai na 6ullo ta titin gidan man Awajil ai zaifi min sauri saboda karna makara a zuwa hospital yau Ina da aiki sosai gashi saida kika bari na kusa school d'in gaskiya bazan shiga Yalwawa ba" ya fad'a zai wuce ya shiga school d'in cikin shagwa'ba tace "ya Sultan kawai aje ni anan zan karasa cikin school d'in da 'kafata" ta karasa maganar tana shirin bud'e murfin motar ta fita ya dakatar da ita.

"Meyasa bazaki bari na karasa dake ba zaki tafi da 'kafa"?.

Turo baki tai tana qin kallonsa saida ya sake maimata tambayar dayai mata sannan tace "to bakace baza muje ka d'auko qawata ba kuma bani da kamarta fa" dafe kai yayi domin gaskiya idan tace saiya yi mata haka zata takura shi amma baida wani za6i tunda baya son 6acin ranta d'agowa yayi yana kallon ta yadda ta cika ta batse ga hannunta har lokacin yana ri'ke da murfin motar jira take ya bata amsa zai daukota kota fita sauke ajiyar zuciya yayi yana cewa.

"Ok sake murfi ki gyara zaman ki muje na d'auko miki ita shikenan hakan yayi miki koda 'kari"? Sakin murfin tai tana murmushi tace "yauwa ko kaifa ya Sultan shiyasa kake burgeni nake sonka akwai sau'kin hali" shima murmushin yayi Mata suna tafi suna hira kamar ba yanzu ta gama had'e rai ba har suka shiga anguwa bayan sunje kofar gidan yayi parking zata fita yace.

"Nabilah" tsayawa tai tare da juyowa tana kallon sa a marairaice yace "please karki dad'e" yadda yai maganar yasa tayi dariya tana tsokanar sa itama cikin marairaice murya tace "bazan dad'e ba ya Sultan" ta fad'a da sauri ta fita tana dariya ganin yadda ya zaro ido shiga gidan tai da sallama a zaune ta samu Hajiya Maryam a waje tana lissafin kayan da tayo sari bayan sun gaisa tace.

"Momy Husnah fa jiya tace min anan zata kwana yau ko"? Kai Hajiya Maryam ta d'aga tana cewa "eh tana nan shiga wannan d'akin tana ciki" to Nabilah tace tana shiga a kwance ta samu Husnah lullu'be da bargo kamar mara lafiya tsaye tai a bakin kofa tanai mata kallon mamaki kafin ta karaso tana cewa.

"Haba Husnah yada kwance karma kice min baki shirya ba"?.

Murmushi Husnah tai tana gyara kwanciya ta fuskanci Nabilan sosai tana cewa "ban dad'e da tashi ba kin gani tun daga sallar asuba na koma barci sai yanzu na tashi ko wanka banyi ba balle breakfast ki shigo man ki zauna idan na shirya saimu tafi" zaro ido Nabilah tai tana cewa "waye zai karaso ya zauna ya jira kin amma ba dani kike ba kinsan irin cakwakiyar dana had'a a waje ya Sultan nefa yau yaje gidan mu shine yace zai kawo ni school d'in har munje kwanar gidan yarima na rokeshi muzo mu daukeki da'kyar ya amince yana cewa zai makara a zuwa hospital Kuma yanzu nazo baki shirya ba humm yau akwai ya'ki idan muka fita so kike yace bazai sake kawoni school ba saidai idan munyi aure" Nabilah na rufe baki Husnah tai dariya tana tashi zaune tace.

"Yanxu fa ya kika ganni"?.

K'are mata kallo Nabilah tai a shirye take tsaf takalmi kawai zata sa da mayafi tace "oh wato dama kin shirya amma shine kika wani kwanta sad'e-sad'e kamar majinyaciya"? Mi'kewa tai tana d'aukar mayafinta da handbag d'inta ta d'auko takalmi tana cewa "eh man naji lokacin da kike cewa small Mom Ina nake lokacin Ina zaune zan sanya mayafi shine na kwanta da sauri na lullu'ba dan na tsokane ki" "ok taho muje kar ya gaji nasan zai iya tafiya ba karamin aikinsa bane niko da kika ganni ban fito da ko sisi ba" ta fad'a tana ri'ke hannunta suka fita sallama taiwa Hajiya Maryam sannan suka nufi bakin gate suka fita harya gaji da zama a motar ya fito yana jingine ya hard'e hannuwa a 'kirji karasowa sukai Husnah tai gaida dashi bayan ya amsa ya kalli Nabilah ya kalli agogon dake d'aure a hannunsa yana cewa.

"To yanzu kam bazan samu damar kaiku ba ku tare d'an napep ya kaisu school ni zan wuce saboda idan nace saina kaiku zan makara da yawa" jin abinda yace yasa Nabilah shagwa'be fuska tana cewa "kai dan Allah ya Sultan ka kaimu bafa nisa daga nan ko a qasa idan mutum yabi ta cikin maja zai iya zuwa" tana rufe baki yace "ok to kubi ta majar mana ai yanzu zakuje Kinga amsa wannan in tafi" kud'i ya mi'ko mata amma ta had'e rai taki kar'ba ita saidai ya kaisu kaiya jinjina yana mi'kawa Husnah yace "ku tari me napep ya kaiku" kar'ba Husnah tai shi kuma ya bud'e mota ya shiga yabar gurin Nabilah tana kallo yabi ta titin mechanic village har ya 'kule kallonta Husnah tai tana cewa.

"Kiyi hakuri Nabilah nice sila badan kince yazo ku d'auke niba da duk hakan bata faru" kai Nabilah ta girgiza tana cewa "haba Husnah ki daina d'orawa kanki lefi tun kafin mu had'u dake nasan halin ya Sultan saidai na fad'awa wani ko su Rasheedat qaninsa basu isa fad'a min wasu halayen nasa ba karki damu muje" wucewa sukai suna tafe suna hira sun d'anyi nisa suka tsare me napep suka hau ya kaisu daidai ya tsaya sun fita motar Sir Ahmad ta shigo makarantar tsayawa yayi a saitin su yana sauke glass d'in motarsa cikin mamaki daya tabbatar Nabilah d'ince sannan ya mayar da glass d'in yana jan motar yayi gaba saida suka biya me napep sun juya sun fara tafiya Husnah tace.

"Ke Beelat bakiga Sir Ahmad yadda yake mana wani irin kallo ba daga ni har ke to me yake tunani a kanmu"? ta'be baki Nabilah tai tana cewa "oho masa nasan ganin mu dayai a napep ne zaiyi tunanin ko mu irin 'yan qaryar nan ne masu aron kaya da aron mota dan mu burge mutune ace mu wasu ne aina gane manufar sa tuntuni sharesa nai" kai Husnah ta jinjina tana cewa "humm kedai bari kawai Beelat Allah Allah nake gayen nan yabar cikin school d'in nan tunda ranar na biyo ta wani block suna tsaye su uku naji kamar yana fad'a musu zai nemi transfer ya koma yanki garinsu ya gaji da zaman arewaci"

Cikin murna Nabilah tace "ya tafi d'in man da nafi kowa jin dad'i wallahi domin dama ya takura min mtwwww" ta karasa maganar tana jan zazzafan tsaki dariya Husnah tai tana cewa "uhm mutum ne shi me naci sai kace maye amma badan haka ba irin had'e masa ran da kike yaci ya daina kula ki".

"Karma ya daina Ina daidai dashi zansa ayi maganinisa".

Sun kusa shiga department d'insu suka ci karo dashi har yakai motarsa parking space ya dawo tsaki Husnah tai tana cewa "kiga maye nasan ke zaiwa magana tunda naga ya zubo mata wadancan idanuwan nasa" tabe baki Nabilah tai lokacin har sun kusa had'uwa tace "yaiwa kansa magana dai amma bani ba domin bazan sake kulashi ba idan ban fito masa a mutum nace masa mutunci ba bazai gane abinda nake nufi ba" tana rufe baki yana karasowa cikin muryarsa da 'kwararriyar hausa ba yace.

"Nebilah Sir Tejuddeeen".

Had'e rai tayi batare data amsa ba suna kokarin wucewa yace "Nabilah" ko sauraron sa batai ba kamar ma bada ita yake magana ba haka suka manna masa hauka suka wuce tsaye yayi a gurin ya kasa gaba ya kasa baya ganin yadda ta yarfa shi a gaban wasu d'aliban kai ya jinjina yana nuna saitin inda suka shiga da yatsa yace.

"Heyemm Nabilah Nabilah ni kikewa shariya kike wulakanta ni bakisan koni waye ba amma zan sanar dake ta hanyar 6ata sunanki a gari dana mahaifin ki idan nayi haka na tabbata zaki fini jin ciwon abinda kikai min na soki da gaskiya kin 'ki zan karbe abinda kike takama dashi na matantakar taki sannan na bayyana lokacin faruwar hakan a gari muje zuwa kici gaba da mun shariya zan nuna miki ke ba kowa bace a cikin Dutse" ya karasa maganar yana fita daga cikin school d'in ya gangara wani gidan cin abinci dake opposite d'in makarantar domin yayi breakfast.

Yauma jarrabawar da sukai taci lokaci domin har 'karfe uku da rabi suna ciki basu samu damar fitowa ba sai karfe hud'u sannan suka fito a gaggauce kowa yayi alwala sukai sallar azhar da la'asar suka mi'kewa suna fita a gurin humm kamar wanda suka sha maganin gano indai zasu fito su baro department d'insu to zasu had'u da Sir Ahmad abun kamar had'in baki saidai wannan karon ko inda suke bai kalla ba yayi gaba kallon juna sukai bayan wucewar sa suna murmushi kai Nabilah ta jinjina tana cewa.

"Kai alhamdulillah har naji dad'i wallahi da naga ya share ni haba yanzu ne zan sake a school d'in nan Allah yasa ya kusa tafiya ma na karasa hutawa".

"Amin domin Nima nayi mamaki da naga ya wuce wallahi na d'auka zaiyi miki magana humm dama irin su Sir Ahmad saika fito ka nuna musu 6acin ranka a fili suke ganewa ne amma koba komai yanzun ma kin samu salama ko nace mun samu domin nima yana shiga hakki na yana mugun takura min kiranki da yake yi".

"Komai yazo karshe ai tunda yayi fushi nasan na huta Allah yasa bazai sake kwana cikin Dutse ba a yau ya koma yankinsu".

"Amin Beelat Allah yasa" Husnah ta fad'a harda yafa hannu a fuska fitowa sukai bakin titi tuna babu wacce tazo da mota yasa Husnah ta bud'e handbag d'inta tana ciro kud'in da Sultan ya Basu su hau napep

Please Login or Register in order to submit comment