Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels



GOBE DA NISA
Page 1
Na Pharty BB

BismillahilRahmaninRaheem


  Ahlin gaba ɗaya farin ciki suke da murna domin samun wannan karuwar abin da basu zata ba, wanda suke ganin abu ne mai wuya samun shi, duk da ya kasance murnar wasu a ciki suke hakan bai sa sun bayyana a fuskarsu ba suka bari a zuci. Ƙaramar walima aka haɗa a gidan, aka ci aka sha kowa na taya wacce abin farin cikin ya sameta murna.
  Idan ka dubeta kuwa yadda kyakkyawar fuskarta take annuri zai ba ka tabbacin tana farin ciki da wannan rana, burinta ya cika saura mafarkinta da kaso sittin shi ne abin da ya taimakawa rayuwarta tsawon rai. Jama'a da dama suna ganin hakan ba mai yiwuwa bane saboda kankantarta kuma mace ce.
  Sunanta ta ji an ƙira, ta juya tana amsawa wacce ta ƙirata cikin sanyin muryarta na marar son hayaniya. Kanwar mahaifiyarta ce Aunti Babie, cikin murmushi ta ce.
"Zamu wuce gida Mariya, Allah ya taimaka yasa a shiga a sa'a."

Mariyatul Kibdiyya cikin muryarta mai daɗin sauraro ta ce.
"Amin Aunti na gode. Sai na zo muku."

"Babu komai, ai ke yanzu babu zama."
Aunti Babie ta faɗa tana saka yaranta a gaba suka fita a falon, Zakiyyah tabi bayan mahaifiyarta tana yiwa sauran ƴan matan sallama sai bayan kwana biyu.
Suna fita Mariyatu, Haneefa da Ummi Aisha suka gyara falon ganin yadda aka mayar a hargitse.
  A haka kowa ya watse wanda suka zo tayata murna aka bar ƴan gidan. Suna gamawa ɗakinsu suka wuce, kai tsaye bathroom suka yi rige rigen shiga ganin magriba ta yi, alwala suka yi suka gabatar da sallah, kasancewar cikinsu a cike yake basu bi takan abincin dare ba kowace ta nemi guri ta zauna tana ɗaukar wayarta.
  Haka suka zauna suna chat suna hira jifa jifa wanda duk Haneefa da Ummi Aisha ne, Mariya daga umm sai a'a nata, haka har dare ya yi suka gabatar da sallar isha'i. Bayan sun idar suka fita suka yi wa Umma sai da safe suka dawo ɗaki suka kwanta.

  Washegarin ƙarfe bakwai da rabi cib Mariya da Haneefa suka gama shirinsu na tafiya aiki. Mariya yau ne ranar farkonta, wanda dalilin samuwar aikin yasa ahlin haɗa mata walima jiya a gida suka zo yi mata murna.
Haneefa cikin uniform din nurses fari, ta yi kyau abinta.
  Mariya kuwa cikin bakin doguwar riga baki, sai baby hijab fari da ya rufe kirjinta, ya haska farin fatarta ya fito mata da tsantsan kyawunta, duk da bai kamata ba hakan baya hana mutum hango zubin halittarta. Fuskarta fiyau babu wani kwalliya sai hoda da man baki da ta sanya don girmama dokokin aikinta.
Bayan sun gaishe da Umma a gurguje suka hau yin breakfast da mai aiki ta gabatar jera a dining.
Haneefa ce ta fara gamawa ta miƙe, ta kalli Umma da take zaune ta ce.
"Umma wai Abba bai farka ba."

"Yana falonsa."
Umma ta faɗa daga inda take zaune tana duba wasu kayyaki da aka kawo mata.
Haneefa ta juya kalli Mariya ta ce.
"Ki gama muje gaishesa sai mu wuce."

  Miƙewa Mariya ta yi don ta kammala kenan, ta ɗauki handbag ɗinta tabar gurin. Ganin haka Haneefa yin gaba Mariya tabi bayanta zuwa falon Abba, a hanya suka haɗu suka ƙarasa.
  Da sallama suka shiga gaba d'ayan su, Abba ya amsa musu yana zaune saman kujera hannunsa ɗauke da remote yana kallon labaran safe, yayinda yake sanye da jallabiya. Guri suka samu suka zauna, cikin ladabi suka gaishe dashi. Da fara'a a fuskarsa ya amsa musu tamkar koyaushe. Suka miƙe Haneefa tana cewa.
"Abba zamu wuce aiki."

"A dawo lafiya."
Ya faɗa yana binsu da kallo suka fita, musamman Mariya da yaga kwalliyarta ya karɓeta.
  Bayan fitar su adaidaita suka shiga kowacce ta wuce wajen aikinta.
  Mariya tunda ta hau mashin har ya sauƙeta bakinta da addu'o'i, yau ne ranar farkonta aiki bayan interview da suka sha aka tantance aka zaɓa masu ƙoƙarinm aka basu aikin, hakan yasa duk a tsorace take.
  Da bismillah ta saka ƙafarta cikin ma'aikatar, tana shiga ta fara bin harabar wajen da kallo. Ba wani ma'aikata bane babba amma tsarin gini ya fita mai kyau, ginin zamani ne hawa ɗaya bene. Kallon wajen ta ci gaba da yi idanuwanta suka hango mata waɗannan suka yi interview tare.
  Cikin sauri ta ƙarasa wajen su, ta musu sallama suka amsa mata daga nan ta ci gaba da tsayawa. Mintuna biyar da tsayuwarta taga kowa yana gyara tsayuwar sa, ita ma nata ta gyara tana kai kallonta kan mutanen da suka dumfaro su.
  Mutumin da ya musu interview ne tare da wasu biyu, wanda ɗayan lokacin da ake mata interview yana office din amma bai ko kalli inda take ba balle ya tofa, sai ɗayan da bata san shi ba.
Tsit gurin ya ɗauka bayan isowar su, baƙon fuskar cikin su ya musu sallama tare da fara gabatar da kanshi gare su da sauran cikin harshen turanci.
"Ni sunana Barrister Hamza, wannan Barrister Waliy Abubakar sai wannan oga kwata kwata Judge Nuhu. Barkanku da zuwa wannan kotun, da fatan za ku yi aiki tukuru kamar yadda ya kawoku, wanda muke sa ran kuma nan da shekara ɗaya kun zama baristocin kanku, ku fito gaban court a dama daku a fafata."

Kowa jinjina kai ya yi alamar gamsuwa, hakan yasa ya ci gaba da faɗin. "Follow me, a nuna muku office dinku."
Daga haka ya fara tafiya.
Suna ƙoƙarin bin bayan shi cikin amo mai ɗauke da daɗin murya suka ji maganar Barrister Waliy ya shiga dodon kunnuwansu.
"Kowacce ta nemi suit(coat), ba ma son wannan baƙin abayan."

  Gaba daya kallon shi suka yi, suka ga ya fuske tamkar ba shi ya yi maganar ba, sai ma juyawa ya yi ya fara ƙoƙarin barin wajen cikin takunsa na kasaita cike da kwanji.
  Da kallon mamaki ƴan matan musulman wajen suka bishi. Musamman Mariya da wannan dokar nashi yake ta kai kawo a kunnuwanta, tunani take ta ya ya za ta saka suit a yadda take.
  Tafiyar da suka fara domin bin bayan Barrister Hamza ya dawo da ita hankalinta. Da sauri ta bi bayan su, office aka kaisu wanda yake a floor ƙasa, yana da girma wanda yake ɗauke da table shida, kowanne da computer akai. Cikin su aka zaɓi mutum shida, uku maza da mata uku ciki har da Mariya. Sauran aka yi gaba da su.
  Sai da suka gama zaba sannan Mariya ta samu ta zaune kusa da mace. Dafe kanta ta yi tana tunanin anya za ta iya wannan aikin da ta ɗaukarwa kanta alƙawarin yi tun ba takai haka ba, wanda shi ne mafarkinta da burinta har tana ganin GOBENTA DA NISA wanda ba zai zo ba balle burinta ya cika. Amma yau ne ranar farko har ta fara sarewa.
  'Yanzu aka fara.' Wani sashe na zuciyarta ya faɗa mata haka, hakan taji ya ƙara mata ƙarfin guiwa kamar koyaushe idan ta sare zuciyarta tana bata kwarin guiwa.
Kanta ta ɗaga ta buɗe idanuwanta lumshasshu, da bismilla ta kunnan computer taga ya kawo. Bincike ta fara a ciki ko za ta yi gamo da wani abun a ciki, cikin mamaki kuwa ta hango folder ɗaya a gefe da alamar creating ɗinsa aka yi ko turawa, ciki ta shiga nan taci karo da case ne da ake so ta ƙarasa, ga gundarin jawabin kaɗan da zaman shari'ar da aka yi na farko, saura ta binciko da kanta, ga sunan mutanen da ake case din a kansu da sunan unguwa har da lambar waya. Idan ta gama ko tana bukatar ƙarin bayani ta tuntubi Barrister Waliy don shi ne akan shari'ar.
Numfashi ta sauƙe jin da wanda aka haɗata, ta ɗauke idanuwanta saman computer ta kalli sauran mutanen wajen, nan taga duk hankalin su yana kan computer alamun sun nuna suma sun gamu da irin nata ne. Kanta ta mayar ta ci gaba da karantawa daki daki tana fahimtar case ɗin akan wani ne ya yi wa bazawar cikin gidan da suke haya ciki, ita ta dage nashi ne shi kuma ya musa, shi ne iyayenta suka kawo ƙara.
Mariya abin ma dariya ya bata don yadda ta gano shekarun mutumin tsoho dashi, ita kuma ƙarama sosai yar shekaru ashirin da uku. Haka ta ci gaba da duba shari'ar da duk abin da za ta fahimta, ta ɗauki sabon folder da suke saman table ɗinta ta fara rubuta duk abin da tasan zai mata amfani.
Sosai ta dukufa a aikinta, babu mai yiwa wani magana cikinsu don babu sabo tsakanin su, hasalima yau ne haɗuwar su ta biyu. Basu samu kansu ba sai ƙarfe biyu, suka dakatar da aikin suka fita zuwa masallacin da yake ɗauke da gefen maza da mata.
Alwala suka yi suka shige kowanne ya gabatar da sallah, bayan an idar Mariya taji daɗin saka Abaya don ya taimaka mata bata sha wahalar neman hijab ba. Amma a hakan ana neman hanasu sakawa, dole kenan su fara yawo da hijab a jaka don yin sallah.
Fitowa ta yi bayan gama addu'o'inta, inda taga sun nufa wajen cin abinci ta yi ita ma. Bayan ta shiga ta zauna tasa aka kawo mata doughnuts da fresh milk mai sanyi, cikin nutsuwa ta ci ta kammala ta miƙe, ta nufi gurin biya ta biya ta bar wajen.
Office ta koma ta ci gaba da yin aikinta cikin nutsuwa, sai yanzu hankalinta ya fara kwanciya da wannan aiki nata, sam babu takura sai rashin sabo wanda tasan gaba kaɗan za ta saba har ta samu damar cikar nata burin da mafarki.
  Karfe biyar suka tashi, kowa jiki ya yi tsami don rashin sabo. Sallama suka yiwa juna kowa ya kama gabansa. Mariya napep ta shiga ta nufi gida, wani bacci bacci take ji sai lumshe lumshashshun idanuwanta take tana buɗewa wanda hakan ƙara mata kyau yake.
  Har ƙofar gida ya kaita ta sauƙa ta ba shi kuɗinsa ta wuce ciki, da sallama ta shiga ta hango motar Abba alamar ya dawo.
Ɓangaren su ta wuce ta shiga da sallama, Umma da Abba suka amsa mata. Umma tana faɗin.
"Manyan baristocin ƙasa."

Murmushi Mariya ta yi har dimple ɗinta suka lotsa, wanda ko ya ya tayi da fuskarta sai sun lotsa tsabar yadda suke da saurin shigewa. Ta duka tana faɗin.
"Ina wuni Umma?" Ta juya gefen Abba da shima sanyayyar murmushi yake binta da shi ta ce.
"Abba ina wuni."

Gaba ɗayansu suka amsa mata cikin kulawa da tambayarta aiki.
Cikin sanyinta ta ce
"Allahamdulillahi." Sannan ta miƙe ta wuce ɗakinsu.
Kwance ta samu Ummi Aisha, kasancewar ta yi sallar la'asar saman gadon ta zube ƙafafunta suna reto a ƙasa, cikin makoshi ta furta.
"Wash! Na gaji."

Ummi Aisha ta gyara kwanciyarta tana kallonta ta ce.
"Manya Barrister, sannu da ƙoƙari."

Da ƙyar Mariya ta ce. "Yawwa."
Ta miƙe tana cire baby hijab ɗinta ta ce."Aiki ko wahala."

"Ke kika sa kanki aikin maza. Bar ni da baking ɗina hankali kwance."
Faɗin Ummi Aisha tana dariya ta sauƙa a kan gadon.
  Mariya leɓbenta ta cije ba ta mata magana, bayan ta rage kayan jikinta ta miƙe ta shiga bathroom. Ruwa ta watsa ta fito ta saka doguwar riga na shan iska, ta saka ƙaramin hijab iya guiwarta sannan ta fita.
  Yadda ta barsu haka ta dawo ta samesu sai ma ƙarin Ummi Aisha da ta hango a dining, can ta nufa ta ja kujera ta zauna, ta buɗe warmers din saman dining ta ga akwai ragowar abinci. Plate ta ɗauka ta zuba sannan ta zauna ta hau ci ganin Ummi Aisha tana tare da ita.
  Sosai ta ci ta kwara da ruwa kafin ta miƙe, ta kai plate din kitchen ta fita, bata tsaya a falon ba ta wuce ɗakin su ta ɗauki wayarta ta kwanta. Haneefa ta ƙira ta sanar mata ta dawo, ita ma ta sanar mata tana da night duty sai safiyar gobe zata dawo.
  Daga haka suka kashe wayar, Mariya ta miƙe ta shiga bathroom ta ɗaura alwala ta fito ta samu Ummi Aisha ta shigo ɗakin. Sallah ta fara ita ma Ummi Aisha ta shiga bathroom ta yi alwala ta fito ta fara sallar.
  Bayan Mariya ta idar ta haye saman gado ta sake ɗaukar wayarta ta kunna data don ganin sakwanni da ba ta samu gani ba tun safe, ashe nutsuwa shi yake kawo mutum ya wuni yana chat.
  Babu wani dogon hira tsakinta da Ummi Aisha don Mariya ba ta son surutu sam, idan ana hira maganarta a kirge yake ko da cikin ƴan uwanta ne balle bare.
  Daga murmushinta mai kyau sai umm da a'a, hakan yasa mutane suke mata kallo ta cika jan aji da miskilanci, ita kuwa har ranta ba haka bane, tayi ta zuba surutu ne ba ta so balle tsiwa da bata sanshi ba sam, abin gabanta shi ne kawai a gabanta.
  Bayan ƙiran sallar isha'i Mariya ta miƙe ta gabatar, da ta idar ta ɗauki kayan baccinta na riga da wando ta saka ta haye gado. Addu'o'i ta yi ta shafa ta kwanta tana cewa Ummi Aisha."Sai da safe."

  "Aiki ya nukurkusa wata."
Faɗin Ummi Aisha tana dariya. Ita dai Mariya murmushi kawai ta yi ta rufe idanuwanta, don so take bacci ya ɗauketa ko don ta samu ta farka da wuri don tafiya aiki akan lokaci.

#newbook
#vote
#comment

GOBE DA NISA
Page 2
Na Pharty BB

Mariya Abaya baƙi ta saka wanda ba shi da wani kwalliya, sai farin hijab ƙarami da ya rufe mata kirji, takalminta baƙi mai tsini da handbag ɗinta ƙarami fari, ta yi kyau sosai duk da ba wani kwalliya ta yi a fuskarta ba, sai ɗaddaďan ƙamshin turare take mai saukar da nutsuwa a ruhi da gangar jiki.
  Tana gaishe da Umma ta fita a gida, bata tsaya gaishe da Abba ba. Napep ta tara sai court. Tana isa office ta wuce, ta samu maza ukun sun zo da mace ɗaya ita ma cikin Abaya kamar yadda take, alamu dai ita ma ba ta son suit ko ba ta saya ba.
  Da sallama ta shiga musu suka amsa, daga haka ta nufi table ɗinta ta zauna. File ɗin jiya ta ɗauka ta fara dubawa, yana nan tsaf yanda ta bari, abu kaɗan ya rage ta gama haɗa tambayoyi da za a gabatar a court, amma kafin nan sai ta yiwa wanda suka kawo ƙarar tambayoyi.
  Dafe kanta ta yi don dole sai taje, kuma dole ta sanar da wanda ya bata duba shari'ar cewa za taje. Ƙaramin tsaki tayi ƙasa ƙasa sannan ta miƙe, ta ɗauki file ɗin tare da handbag ɗinta ta fita.
  Zagaye wajen ta fara tare da duba office-office ko za ta samo office ɗinsa, sai dai kaf gurin irinta ne ƙananan ma'aikata. Har ta haƙura sai kuma tayi tunanin duba saman bene, hakan yasa ta nufi can.
  Tun daga harabar wajen yake da kyau da tsari, sosai gurin ya haɗu,  ga office a jere reras. A hankali take tafiya tana duba kowane office da taga sunan mai shi a rubuce a sama cikin style na calligraphy, cak ta tsaya ganin sunan da ba tayi tsammanin gani ba, ta kurawa jikin ƙofar ido tamkar wacce za ta hango shi tsaye, abubuwa dayawa suka fara kai kawo a zuciyarta da ƙwaƙwalwarta da ya haddasa mata bugun zuciya.
  Takun mutane da taji ya dumfarota yasa ta yi azamar ɗauke idonta, ta cije lips ɗinta jin yadda zuciyarta ta juya. Kafafuwanta taja tabar gurin cikin wani irin yanayi da ta tsinci kanta.
  Office ɗaya ta tsallake sannan ta samu wanda take nema, bakin ƙofa ta ƙarasa ta ƙwanƙwasa da ƙyar saboda tsoron da taji ya maye gurbin abin da taji yanzu. Tsawon mintuna ba'a amsa ba, hakan yasa ta sake ƙwanƙwasa. Da ƙyar ta iya jiyo muryar na ciki ya bata umarni ta shiga.
  Tura ƙofar ta yi a hankali tana shiga, bakinta ɗauke da sallama yayinda bugun zuciyarta ta ƙara ƙarfi. Tsaye ta yi ƙyam bayan ta daidaita nutsuwarta, ta ɗago a hankali ta kalli wajen da yake zaune, kansa a ƙasa yana danna computer tamkar bai san da shigowarta ba.
  Tsawon daƙiƙa ita ta kasa magana shi bai ɗago ba ya tambayeta dalilin zuwanta ba, sai shakar ƙamshin turaren juna suke kowanne a zuci yana mitar na juna ya dame sa.
Mariya har cikin ranta jira take ya nemi dalilin zuwanta a matsayinsa na oganta, ya bata dama ta faɗi abin da take tafe da shi. Shi kuma mamakin rainin hankalinta yake da tazo ta sa shi a gaba ta kasa faɗin komai.
  Fuska ya sake tamkewa ya ɗago ya mata kallo ɗaya ya mayar kansa kan abin da yake, tamkar ba zai furta komai ba da ƙyar ya buɗe baki ya ce.
"Idan ba ki da abin faɗa ki bar kaina."

  Jin muryarsa yasa Mariya ɗagowa ta kalle shi, taga tamkar ba shi ya yi maganar ba. Matsawa ta yi ta ajiye file ɗin hannunta a saman table ɗinsa.
"Da ma nace zan je na musu wasu tambayoyi ne."

"Wani case ne?"
Ya tambaya yana barin abin da yake ya ɗago ya kalleta.
Kanta ta ƙara rissinarwa ta ce.
"Na yarinya da tsoho da suke gidan haya tare."

  Kafin ta gama bayanin ya jawo ya buɗe, ya fara karanta abin da ta rubuta ganin yadda take fitar da harafi ɗaiɗaiya cikin sanyin murya. Bayan ya gama ya rufe ya ce.
"Babu buƙatar wannan, amma idan ta kama za kiyi hakan. Tambayoyin da kika tanada su kaɗai zasu yi aiki a court, don haka kin gama naki."

  Mariya jin abin da ya faɗa yasa ta ɗago ta kalle shi, ta ga ya miƙe. Numfashi ta sauƙe a hankali, sannan ta ce.
"Ok sir."
Ta juya ta fara ƙoƙarin barin office ɗin, har ta kama handle taji ya ce."Na sallameki?"

  Dakatawa ta yi ta dawo baya ta tsaya, kanta a ƙasa tana mamakin wannan isa da mulki, sai wani muzurai yake mata.
  Barrister Waliy ajiye file ɗin da ya dauko ya yi saman table ya tura gabanta.
"Ki je ki duba wannan. Sabbin case ne ba kamar wanda kika gama ba, duk da shi ma sai na zauna na duba."

  Mariya hannu tasa ta ɗauka tana faɗin. "Ok sir."
  Daga haka ta juya ta fita cikin sauri, fitarta yasa Barrister Waliy ɗago kai, ya kalli inda ta tsaya kafin ya mayar kansa kan file ɗin da ta kawo mishi. Daki-daki yabi duk tambayoyin da ta rubuta, tabbas ta yi ƙoƙari ganin ita ce ta biyu da aka bawa aiki suka fara kawowa, kuma ko shine irin tambayoyin da zai yi kenan.
  Bayan ya gama gani ya miƙe dauke da file din, ya adana a cikin files ɗin da gobe za a yi zaman shari'ar su.
...

  Mariya bayan barin office ɗinsa office ɗinsu ta wuce, zuciyarta cike da mamakin wannan aiki nasu, sai taji ma ya mata sauƙi da har tana cewa za taje musu tambayoyi.
  Tana shiga zama ta yi ta ajiye handbag ɗinta da files ɗinda ya bata, ta lumshe idanuwanta ta buɗe tana kai hannu ta jawo file ɗin sama ta buɗe na farko ta buɗe.
  Cikin nutsuwa ta fara karanta shari'ar da abin da ake ƙara, tabbas sabo ne kamar yadda ya faɗa don babu wani bayani ko ɗaya, dole ita za ta shiga ta fita ta nemo mafita.
'To kuma ya hanani zuwa musu tambayoyi.' Ta faɗa a zuci tana rufe files ɗin, ta ma rasa me za ta yi, duk yadda taso fassara kan aikinta ta ka sa, idan ya ɗauko zafi sai taga akasin hakan.
  Ga wannan case ɗin dole tana buƙatar yin tambayoyi duba da yadda wanda yake ƙara an kama yana cell a station.
  'To ni ya zan yi.' Ta faɗa a zuci, a zahiri kuma fuskarta ta bayyana damuwar da take ciki. Ta rasa mafita akan wannan abin, hakan yasa ta kasa tabuka komai akai, dole sai ta ƙara tunani akan mafita.
  Jinginar da case ɗin ta yi gefe, ta kunna computer gabanta, bincike ta fara anan taga ya turo mata case biyun da ya bata ta email ɗinta kamar na farko. Buɗewa ta yi ta gani ta fita ta kashe computer.
  Rasa abin yi yasa ta miƙe tabar office ɗin, masallaci ta nufa ganin ƙarfe ɗaya saura. Alwala ta yi ta shiga ganin akwai ɗaiɗaikun mutane, gefe ta samu inda babu mutane sosai ta zauna. Wayarta ta ciro a jaka tare da earpiece ta saka, ta nemo karatun Alkur'ani ta fara ji.
  Idanuwanta lumshe tana saurara, wani nutsuwa da kwanciyar hankali yana shigarta, a hankali zuciyarta ta dawo mata da abin da ta gani ɗazu.
  Buɗe idanuwanta ta yi da sauri jin yadda zuciyarta ta buga, sam ta daina fahimtar karatun jin zuciyarta ta faɗa wani tunani daban, hakan yasa ta zare earpiece ɗin kunnenta ta kashe, ta mayar wayar jaka.
  Ta jima cikin tunanin abubuwan da suka wuce, ganin za ta haddasawa kanta wani damuwar yasa ta miƙe don fita, sai kuma daidai aka fara ƙiran sallah, dole ta koma ta zauna har aka gama ƙira.
  Mintuna biyar da haka aka shiga masallaci don fara sallah, ire-irenta masu alwala suka yi jam'i suka fara bin sallah. Bayan an idar Mariya tayi addu'o'i ta shafa akan Allah ya cika mata burinta, ya bata mafita a kowane case. Miƙewa ta yi ta ɗauki jakarta ta fita a masallacin, wajen cin abinci ta nufa, bayan ta shiga ta zauna tasa aka kawo mata meatpie da drink na orange juice.
  Cikin nutsuwa taci ta kammala ta miƙe, ta biya su sannan ta fita. Office ta koma ta samu matan biyu suna nan sauran basu dawo ba, zama ta yi bayan ta ce musu sannu.
Ƴar gefenta ta ce.
"Ke wai ba kya magana?"

Mariya kallonta tayi, tai murmushin da ya bayyana dimples ɗinta tace.
"Ina yi."

  Baki ta taɓe jin amsar da ta bata, ta cigaba da aikinta. Haka ita ma Mariya ta ɗauke kanta ta cigaba da
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment