Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

takobin ya bayyana bayan ya gama gani kawai sai yaji ya kamu da tsananin farin ciki nan take yasa a ransa duk rintsi da tsanani sai ya mallaki wannan takobi da karfin tsiya koh da gama yanke wannan shawara sai ya fara Neman hanyar da zai yi yasa aljani damgaskus ya sauko kasa kawai sai dabara ta fado masa sai yayi tsafi kasa ta bayyana a hannunsa kawai sai ya karanta wasu dalasiman tsafi guda uku ya tofa akan kasar sannan ya watsa ta inda aljani damgaskus yake ta tsala gudu









Yana cikin wannan azababben gudun ne yaji kasa ta shigar masa idanu kawai sai yasa dan yatsa dan ta Ciro tsakuwowin amma sai Abu yaci tura kawai sai ya saki fuka fukan Sa yayi kasa koh da ganin hk sai murna ta kama sarki dizlan yacewa wannan aljani NASA duk inda aljani damgaskus ya sauka shima ya sauka agun daga nan bai kuma mgn ba shikuma wannan aljani ya cika umarni yabi bayan aljani damgaskus









Aljani damgaskus yana dira ya acikin wani gawataccen daji mai yalwar yayan itatuwa ga koramai garai garai inuwar bishiya mai sanyi sai yayi saurin sauke su sadauki aisar yana mai mitsike idanunsa kawai sai aryan ya daka masa tsawa yace ya xaka sauko damu kuma muna cikin tafiya wannan wane rashin hankali ne






Cikin biyayya aljani yace ka gafarceni y shugabana ina cikin tafiya naji tsakuwa ta shigarmin idanu nayi nayi na cirota taki shine na sauko kasa dan na cire yana kaiwa nan ya ciro tsakuwo win dukan su






Koh da ganin su sai sadauki aisar yace bani su mugani yana karba sai suka bace kamar basu taba wanzuwa agun ba koh da ganin haka sai yace gsky ne dama da walakin goro a miya taya tsakuwa zataje sama wani ne yayi aike kuma tabbas yana kusa damu kafin ya gama rufe bakin Sa sai ga sarki dizlan ya ratso wasu duhuwowi ya fito yana mai yin murmushin mugunta.........







Turkashi muje Zuwa dai yanxun aka fara




Plz comments and shared





Nakune dai ALIYU ISHAQ FAST class




WhatsApp number 08143314152





By fast class
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
      🏀 🏀🏀🏀🏀
            🏀🏀🏀🏀

TARTSATSIN WUTA
(adventure story)
            🏀🏀🏀
     🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀

Tsara labari da rubutawa

ALIYU ISHAQ
Β Β  (fast class )
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


Page 91to95



Daga marubucin
KAUNAR UWA
UMAR FAROUQ and now
TARTSATSIN WUTA
(adventure story)








Lokacin da sarki dizlan da aljani shabrul suka bayyana a gaban su sadauki aisar sai sarki dizlan ya tuntsire da Dariya sannan yace yaku wadannan kananun kwari Ku sani cewa duk Wanda ya rigaka kwana dolene ya rigaka tashi tabbas batun tsakuwar da ta shiga idanun wannan butulun aljani naku ba tsakuwa bace ba wannan duk shiri na ne a yanxun ni Abu daya kawai nakeso a gareku wannan takobi dake hannunku idan kun bani ita salin alin ZAMU rabu lpy idan koh ba haka ba fushina zai tabba ta a kan Ku






Koh da sarki dizlan yazo nan a zancen Sa sai sadauki aisar ya tari numfashin Sa ta hanyar daka masa tsawa yace kai tsohon azzalumi kasani cewa har abada bama gudar wa makiyin ki duk karfin dantsen Sa da iya yakin Sa takobi kuma ta karfi ce dan muma shi mukasa muka kwato idan kana da shi sai mu zuba mu gani da kai damu







Koh da sadauki aisar yazo nan a zancen Sa sai sarki dizlan ya kuma kecewa da mahaukaciyar Dariya kana yace lalle yaro baisan wuta ba sai ya taka tun da haka kuka zaba ga maza nan bisa kanku








Yana gama fadin haka ya zare takobinsa ya ruga Kansu yana kururuwa koh da ganin haka sai suma suka taso masa kafin ya karasa kusa dasu kawai sai yayi nuni da Dan yatsansa izuwa kan sadauki Aryan kawai ga wata sarka ta daure shi tamau ta yadda koh dan ya tsansa baya Iya motsasa kawai sai sarki dizlan ya daka tsalle ya dira a tsaki yar su jaruma jumaima ya tarwatsasu da karfin tsiya duk suka zube a kasa koh da ganin wannan nasara daya samu sai ya kama kyakyata dariyar nasara yana cikin wannan dariyar ne yaji an dankara masa naushi a kumatu saida yayi juyi sau uku a gurin sannan ya zube kasa yana taba bakin Sa yaji jini sai ransa ya matukar baci







Bakowa ne yayi masa wannan naushi ba face jaruma jumaima tana tsaye ita da Dan uwanta sun jin gina baya kowa yana rike da addunan sa suna jiran suka ta inda zai kawo musu hari







Mikewa yayi cikin matukar Bacin rai ya kuma rugowa Kansu da mugun nufi suna haduwa suka ruguntsume da azababben yaki mai matukar muni ya wanzu mai kai musu Sara da suka cikin bakin zafin nama juriya da bajinta ta ban mamaki su kuma sun wanzu suna masu kare wa tare da mai da martani tako ina sun kunta ta shi amma sabida dakewar zuciyar yaki jaraya koh da ganin wannan abun da yake faruwa sai aljani damgaskus ya kalli aljani shabrul ya tuntsire da Dariya kana yace kana dai ganin abinda ke faruwa tsakanin masu Gida na da mai gidan ka kai dai nasan ba abinda ZAKA iya dan idan nace zan yi yaki da kai ma cin xakin ka zanyi sabida haka inason ka murdewa kanka wuya an an gurin tun kafin raina ya baci da kai







Koh da jin haka sai aljani shabrul ya dubi aljani damgaskus duban rainin hankali yace hb dai ai kai baka isa naji tsoronka ba shin kai waye ma daza ka bani umarni nabi koh da jin hk sai aljani damgaskus yace ni ubanka ne amma tunda naga baka fahimci hakan ba bari na fahimtar da kai





Koh da gama fadin haka sai ya zare rantsatstsiyar takobin sa sai kyalli take faman yi koh da ganin wannan takobi sai shima aljani shabrul ya zare tasa takobin zabgegiya sai fitar da jan haske takeyi a yayinda ta aljani damgaskus ke fitar da koren haske







A tare sukayi kan juna suna masu ihu irin nasu na aljanu suna haduwa suka ruguntsume da azababben yaki mai matukar muni da ban tsoro lokaci guda suka tashi hankalin dajin baki daya koh ina ya kama ci da wuta sakamakon wutar da kowa ke aikawa abokin gwaminsa idan ya kauce bata sameshi ba to fah koh akan dutse ta sauka sai duten ya narke sai da suka shafe sa a tara suna wannan yakin amma har yanxun dayan su bai sami nasara ba akan dan uwan sa abinda ya matukar bata ma aljani damgaskus rai kenan yaji zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata koh ne kawai sai yayi hulli da takobin sa ya dunkule hannunsa koh da ganin haka sai shima aljani shabrul ya dunkule hannunsa suka kuma kachamewa da azababben fada








Al amarin su sarki dizlan kuwa abin ba kyan gani dan yaki sukeyi kamar jikinsu bana jini da tsoka bane su biyu sun kunta tashi ta kai ta kawo da kyar yake iya kare hare haresu ma baya iya mai da martani ana cikin wannan yaki ne sadauki aisar ya shammace shi ya dan kara masa Sara a kafadar sa ta dama ya kwallah ihu sakamakon tsananin zafin da zugin dayaji kafin ya dawo haiyacin sa jaruma jumaima ta Kuma dan kara masa wani saran a cinyar sa ta hagu kawai sai ya zube a gurin tare da dafe inda ta sare shi kafin ya murmure sadauki aisar yayi wata katan tanwa a sama ya daki kirjin sa da kafarsa ta dama sabida karfin dukan sai da yayi sama kamar an janyeshi da igiya kafin ya diro kasa jaruma jumaima ta bishi saman da dage iya karfin ta tasa gwuiwar hannunta ta dankara masa a kirji koh koh motsin kirki bai kuma yi ba a gurin jaruma jumaima ce ta yi muni da hannunta zuwa inda sadauki Aryan yake take sarkan da ta daure shi ta bace sai ya zama na sun zama yan kallon fadan da ke shirin faruwa tsakanin aljani shabrul da aljani damgaskus................





WOHOHO MAZA SUKE MAGANIN MAZA WANI KAYAN SAI AMALE FANS KU DAI MUJE ZUWA YANZUN AKA FARA YANXU NE FARKO KARFA KU MANTA AKWAI DODO RAGAZALU KUMA HAR YANXUN BA A NEMO DAJIN MUTUWA BA KUDAI KUBIYONI A CIKIN WANNAN BOOK NAWA MAI TAKEN TARTSATSIN WUTA





plz comments and shared





Nakune dai ALIYU ISHAQ FAST class





WhatsApp number 08143314152




By fast class
nishadan tar daku ako da yaushe Aliyu Ishaq fast class




WhatsApp number 08143314152




By fast class
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
      🏀 🏀🏀🏀🏀
            🏀🏀🏀🏀

TARTSATSIN WUTA
(adventure story)
            🏀🏀🏀
     🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀

Tsara labari da rubutawa

ALIYU ISHAQ
Β Β  (fast class )
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Page 96to100


Daga marubucin
KAUNAR UWA
UMAR FAROUQ and now
TARTSATSIN WUTA
(adventure story)




Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  INTERMISSION

YANZUN AKA FARA FANS MUJE ZUWA YANXU NE FARKO






Cikin hadin baki aljani damgaskus da aljani shabrul sukayi kan juna da mugun nufi kowa ya dunkule hannun Sa SUNA haduwa suka ruguntsu me da azababben fada SUNA kaiwa junan su naushi da bugu cikin zafin rai nan take lbr yasha ban ban dan ban ban cin a bayyane yake a lokaci guda aljani damgaskus ya hadama aljani shabrul jini da majina dan yafi shi zafin nama nesa ba kusa ba kafin ya masa naushi daya ya masa biyar haka ya rika hada masa naushi ba imani wata damka da aljani damgaskus yayi wa aljani shabrul ya damko habarsa ya rika naushin Sa a baki da hanci bai daina ba har saida yaga ya daina Motsi sannan yayi wulli dashi kamar tsumma ya diro kasa bisa kafafun Sa yana mai cewa






Ya shugabana zamu Iya ci gaba da tafiya yanxun dan muna da sauran tafiya daga nan zuwa birnin kufah tafiya ce ta Sa a bakwai zamu Iya karasawa a Sa a biyar sabida haka ni Ku nake jira






Koh da jin haka sai su sadauki aisar suka Dane bayan aljani damgaskus ya tashi sama dasu ya na mai tsala azababben gudu





Al amarin boka kailur da aljani rabzik kuwa Ashe duk sunga abinda ya faru tsakanin su sarki dizlan da su sadauki aisar bayan gama wannan yaki ne su aljani damgaskus na tashi aljani rabzik ya rufah musu baya suka kyale su sarki dizlan a gurin cikin halin suma






Saida su sarki dizlan suka shafe Sa a uku a gurin nan basu farfadoba sai bayan wata Rabin Sa ar a sanda wata iska mai KARFI ta kada sannan sarki dizlan ya farfado yana bude idanun Sa ya kalli gabas da yamma kudu da arewa yaga ba su sadauki aisar sai ya takarkare ya kwarara uban ihu ya fashe da kukan takaici yazo mikewa kenan yaji hannun Sa da cinyarsa sunΒ  masa nauyi yana dubawa yaga sun kubura sun yi suntum wani hawayen takaici ne ya zubo masa kawai sai ya kalli inda aljani shabrul yake a kwance kamar gawa sai yaji ma duk ya tsane shi kawai sai ya dauko wata sandar ice dake gefen Sa ya daye bawon jikinta kana yaja jikin Sa da rufda ciki yaje inda jakar guzurinsa take ya zaro zare da allura ya hau dinke raunikansa yana dinki yana zab ga ihu Sa kama kon tsananin zafin daya ke ji wannan ihun dayayi ne yasa aljani shabrul farfadowa daga dogon suman daya tafi haka shima ya mike dakyar wata korama ya hango ya tashi kawai ya fada ciki koh kallon inda sarki dizlan yake baiba shiko yana gama dinke rauninsa ya Shafa mgn sai ya dan kishin Gida nan take bacci mai nauyi ya daukeshi bayan aljani shabrul ya gama wankansa sai yazo ya tashi sarki dizlan yace ya shugabana yanxun mene abinyi





Koh da jin haka sai sarki dizlan yace yanxun abinda ya kamata myi shine yanxun dai wannan ciwon na jikin mu bazai bari mu kuma wata tafiyar ba sabida haka mu bari mu dan kwana biyu a nan tukun kafin nan sunje birnin kufah sun HADU da sarki rukyan ni dai a sanin danayi wa sarki rukyan ba a taba shiga kasarsa ancishi da yaki ba ina tabbatar maka da cewa a yanxun hakan nan sarki rukyan yasan da zuwan su kuma ya musu mugun shiri ina tabbatar maka da cewa duk hatsabiban cin su bazasu iya dashi ba sabida hk mu tsaya anan bayan kwana biyu sai mu duba muga abinda ya wakana idan sunyi nasara sai mu kuma binsu idan kuma ya kashe su shikenan sai mu koh ma gida naje na hadu da waccen annamimiyar matar tawa wato sima wadda a yanxun hk ta dane karagar mulkina






Koh da sarki dizlan yazo nan a zancen Sa sai aljani shabrul yace maganarka dutse shugabana duk Wanda ya shiga fadar sarki rukyan to saidai gawarsa ta fito balle wannan tafiyar abun bautansa fah zasu dauko ai sai inda karfin Sa ya kare haka suka ci gaba da firar su har yamma sannan aljani shabrul ya hadama sarki dizlan tanti ya shiga ya kwanta shi kuma yana gadinsa,,,,








Al amarin su sadauki aisar kuwa saida suka shafe Sa a biyar cip kamar yadda aljani damgaskus ya fada sannan suka karaso iyakar birnin kufah anan aljani damgaskus ya sauke su dan tsayawa ya jirasu kuma ya fada musu suyi komai a sannu dan sarki rukyan ya fisu hatsabiban ci da wannan suka tunkari kofar birnin kufah ba tare da tsoron komai ba... ..........





IDAN NAGA COMMENTS ZAN CI GABA DA TYPING




nakune dai mai nishadan tar daku ako da yaushe Aliyu Ishaq fast class



WhatsApp number 08143314152



By fast class

🏀🏀🏀🏀🏀🏀
      🏀 🏀🏀🏀🏀
            🏀🏀🏀🏀

TARTSATSIN WUTA
(adventure story)
            🏀🏀🏀
     🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀

Tsara labari da rubutawa

ALIYU ISHAQ
Β Β  (fast class )
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com



πŸ…Ώ 101 ➑ 105



Daga marubucin
KAUNAR UWA
UMAR FAROUQ and now
TARTSATSIN WUTA
(adventure story)



Dedicated to A T K PALACE GROUP





Special gift to all my fans allah yabar kauna










WANNAN NAKUNE JAJURTATTUN MARUBUTA NA AREWA WRITER'S ASSOCIATION INA YINKU SOSAE ALLAH YA KARO BASIRA DA KAIFIN KWAKWALWA













A cikin birnin kufa kuwa sarki rukyan ne zaune akan karagar mulkin Sa fuskarsa cike da annuri kamar baisan abinda ke faruwa ba shi mamaki yake yi ta yadda za azo har cikin kararsa aci shi da yaki a dauki abin bautarsa a tafi dashi to shi yana ina kenan








Gaba daya mutanen fadar kowa hankalinsa a tashe yake sakamakon wannan yaki daya ke ta howa dan sun ga gwamin tagwayen da sarki dujalu sarki mai karfin iko da karfin mulki mai ji da sadaukan taka da jarumta amma yaran sun kaishi kasa takai ma har ya kashe kansa wannan shine kawai yake damun yan majalisar fadar duk hankalinsu ya tashi sabanin talakawan garin kowa Kuka yake yi da mulkin sarki rukyan su murna ma sukayi da zuwan wannan ranar









Sarki rukyan ya zuba wa koh wa idanu yana nazarin jama'ar tasa daya bayan daya sai daga bisani ya bada umarnin sarkin yaki ya je hada dakaru majiya karfi mutum dubu daya suyi sahu sahu a kofar fadar sarkin yaki yace an gama ya shugabana ya fita daga cikin fadar Zuwa filin fadar dan cika umarni








Bayan sarkin yaki ya fita ne sai sarki rukyan yayi nuni da hannun Sa Zuwa bangon fadar saiga hoton su jarumta jumaima ya bayyana suna tunkaro kofar birnin kawai sai sarki rukyan ya tuntsure da mahaukaciyar Dariya sai da ya dade yanayi kamar mahaukaci sabon kamu sai daga baya ya turbune fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa yace yaro baisan wuta ba sai ya taka kawai sai sarki rukyan ya hade hannunsa guda biyu agu daya ya karanta wasu dalasiman tsafi guda bakwai yana kammalawa ya watsashi hangar da su sadauki aisar suke shirin shiga garin ya kuma tuntsirewa da dariya







Al amarin su sadauki aisar kuwa sai da sukazo dai dai kofar garin kawai sai ganin wani wawakeken rami sukayi ya Burma a hanyarsu take wasu irin kunamai da macizai suka rika fitar burgu suna yin kan su sadauki Aryan ba shiri suka zare makaman su suna jiran ta kwana gaba daya halittun da suka fito acikin Ramin sai suka tsaya acikin iska su basu kai hari ba su basu koma inda suka fito ba sai da suka kusa Rabin Sa a acikin wannan lamari kwatsam sai gani sukayi wani bakin maciji ya tuntsure da dariya sannan ya fara yin mgn kamar haka





Ya Ku wadannan kananun halittu kusani cewa nine sarki rukyan mai mulkin wannan birni nasan duk shirin Ku a kaina kusani cewa koh duniyar nan za a taro bazasu iya rabani da koh da takobina ba ma balle abin bauta na kusani cewa yau saina shayar daku gidauniyar mutuwa ko wannen Ku sai ya ji ajikin Sa sannan zan muku kisan gilla shawara ta daya a gareku Ku koma inda kuka fito amma idan ba haka muddin dayan Ku yasa kafa ya shigo cikin wannan birni to fah sai dai uwarsa ta haifi wani koh da gama fadin haka sai wadannan halittu suka koma cikin wannan rami gurin ya koma yadda yake da kamar ba abinda ya faru a gun








A tare sadaukan suka kalli junan su kowa da abinda yake sakawa a ransa sadauki aisar ne yayi ta maza yace kada dayan Ku ya karaya da kalaman wannan mugun sarki musa a ranmu ba gudu ba ja da baya gurin cika burin mu Dana iyayen mu idan kukayi duba da ta yadda muka samu nasara akan sarki dujalu shima ba karfin mu ne ya Sa muka samu nasara a kansa ba kawai tsananin Sa a ce koh da yazo nan a xancensa sai ya tsuguna yasa ka hannunsa daya a kasa koh da ganin haka sai Aryan shima ya saka nasa itama jumaima ta saka








A tare suka Mike suna joyowa sukasa kafa suka daki kofar birnin ta fada ciki rikicha saiga dakaru masu tsaron kofa sunyi cirko cirko kowa yana rike da makamin sa na dakarun basu fi sy dari uku ba amma kirar jikin su gabza gabza ne sai kace mutanen farko fuskarsu ba kyan gani dukansu sai muxurai suke yi kamar saci babu wani gabjeje ne ya fito Wanda akaf cikin su yafi kowa girma da tsaho da fadi yana fitowa ya nuna su sadauki aisar yace naji kashedin da mai girma rukyan ya muku amma bakuji ba kunyi kunnen Uwar shegu to kusani cewa mu nan mune ajalinku ba sai mai girma rukyan yasaka hannu ba ma mu nan mun ishe Ku koh da gama fadin haka sai wannan gabjeje ya bawa dakarun nasa umarnin su afka musu bayason koh digon namansu ya gani a gun koh da jin hk sai wadannan dakaru sukayi fitar burgu Zuwa kan su sadauki Aryan koh da ganin mutuwa mararan sai suna suka tari dakarun aka ruguntsume da azababben yaki saida suka shafe sa a daya da rabi suna wannan yaki amma har yanxun su sadauki aisar koh mutum daya basu kashe ba sakamakon dakarun sun sami horon yaki mai kyau gasu da matukar zafin nama haka kuma basa gajiya da wuri dan a wannan lokaci ma su sadauki aisar sun fara gajiya koh da dakarun suka fuskanci hk sai suka kara kuntatasu ta koh ina ya zama na cewa sun hanasu yin koh mai sai kokarin kare kai................







ANAYI INA JIN DADI ANA KI INA JIN HAUSHI KAI FANS INASON IRIN WANNAN HARKAN HAKAN YAMIN WAI YA KARSHEN YAKIN NAN ZAI KASANCE NE FANS KUBIYONI A NEST PAGE DANJIN YADDA ZATA KAYA




PLS COMMENTS AND SHARED





NI DIN NE DAI ALIYU ISHAQ FAST CLASS




WhatsApp number 08143314152



by fast class
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
🏀 🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀

TARTSATSIN WUTA
(adventure story)
🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀

Tsara labari da rubutawa

ALIYU ISHAQ
(fast class )
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com



page 105 to 110


Daga marubucin
KAUNAR UWA
UMAR FAROUQ and now
TARTSATSIN WUTA
(adventure story)



MASHA ALLAH MASHA ALLAH



INA YIWA YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI BRK DA SALLAH INA FATAN ALLAH YA MAI MAITA MANA TA BADI DA RAI D LPY




KAMAR YADDA NAYI ALKAWARI CEWA RANAN 24/5/2020 ZAN CI GABA DA TYPING TO YAU NEHH WANNAN RANAN YA CIKA SABIDA HK INA FARAWA DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI SALATI DA DAUKAKA SU TABBATA AGUN FIYAYYEN HALITTU ANNABIN MU MANZON TSIRA ANNABI MOHAMMAD SALALLAHU ALAIHI WASALLA.








Lokacn da su sadauki Aryan sukaga sun kasa tsinana komai akan dakarun sarki dujalu sai jikin su yayi sanyi hankalin su yayi kololuwar tashi suka fara tunanin to su kuma dakarun dake cikin birnin ya zasu kasan ce kenan wadan nan masu tsaron kofah kenan fah







Ana cikin wannan azababben yakin nehhh wani badakare mai shegen naci ya shammaci sadauki aisar ya dan kara masa wawan Sara a kuybin cikin Sa gurin ya dare JINI yayi tsartuwa lokaci guda suka kwallah ihu shi da jaruma jumaima dan ji tayi kamar Ita aka Sara lokaci guda ya tafi kasa luuuuu zai fadi cikin bakin xafin nama jaruma jumaima tayi wani wawan tsalle ta tarwatsa dakarun da suka yanyameta ta tallafo dan uwanta da dafin takobin da aka sareshi ya fara masa aiki dan har idanunsa sun fara lunshewa








Da sauri ta Goya shi a bayan ta tasa wani mayafi NATA ta daureshi tamau sannan ta kwallah wani uban ihu wanda ya razana da karun suka fara ka da baya da baya damar data samu kenan ta suri addar da aisar ya saki yaje kasa shima sadauki Aryan damar daya samu kenan ta kara surar takobin wani badakare ya hada biyu ya gyara tsayuwarsa yana mai fuskantar dakarun







Koh da shugaban dakarun yaga sadauki Aryan ya dauki takobin daya daga cikin dakarunsa sai hankalinsa ya yi kololuwar tashi kawai sai ya kallo wani gabjejen badakare yayi masa nuni da Aryan nan take shima hankalinsa ya tashi kawai sai ya kada ma shugaban nasu kai lokaci daya kamar had in baki gaba daya dakarun sukayi kan sadauki Aryan








Koh da ganin haka sai jaruma jumaima ta kallo sadauki Aryan nan take ta gane abinda yasa sukayi kansa cikin daga murya tayi masa inkiya daya wullo Mata wannan takobin daya dauki lokaci dayaji sakon ta har dakarun sun karaso kusa dashi suna kururuwa mai firgita maza cikin bakin zafin nama yayi wata katantanwa a sama ya wullah mata takobin ta daka tsalle duk da nauyin sadauki aisar amma a hk ta ta shi sama ta chape takobin ta dira a tsakiyar dakarun ta dankarawa daya Sara a tsakiyar kansa take kan NASA ya rave Gida biyu takobin hannunsa tayi sama ya fadi kasa matacce koh da ganin hk sai sadauki Aryan ya daka tsalle ya chafe takobin






Yana fira ya hausu da Sara da suka cikin bakin zafin nama juriyada bajinta lokaci guda suka kuntata dakarun suka hanasu sakar tako ina rayuka suke dauka koh dashugaban dakarun yaga wannan barna da ake masa sai ya tsure nan da nan zufah ta ciko masa saida ya rage baifi saura mutum 50 ba sai suka cika wandonsu da iska har shugaban nasu koh da sukaga haka sai jaruma jumaima ta kwanto dan uwanta ta hau yi masa mgni sai da ya dauki Sa a daya da Rabi sannan ya farfado sabida tsumin da akayi wa takubban sun ratsashi yana mikewa yace ba zama dan idan MUKA zauna anan komai zai iya faruwa sarki rukyan ya wuce sanin mu sbd hk mu karasa shiga cikin birnin ayi ta ta kare kawai







Yana kaiwa nan yasuri takobin Sa cikin sauri sadauki Aryan yace ya kai Dana wannan takobin bazatayi tasiri acikin wannan birnin ba SBD hk ka karbi wannan tasun dan itace tayi mana amfani anan gurin cikin sauri aisar ya karba ya wuce gaba yana mai yafuto su da hannu





Achan fadar sarki rukyan kuwa koh da yaga abinda ya faru da dakarunsa masu tsaron kofah sai jikin Sa yayi sanyi ya tsinke da lamarin wadannan hatsabiban yara dan a tarihin birnin ma ba a taba cin su da yaki ba tun a kofah komai yake karewa dan da ka HADU da wadannan dakarun sai sun kashe ka sun je har birnin Sa sun kashe rushd garin sannan su kamo matan Sa su mai dasu bayi abinda mutane basu gane
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment