Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

aljanun suka tsorata suka fara waige waige suna cikin wannan hali nehh sukaji an fara musu ruwan kibbau tako ina amma duk a banza dan bata iya huda jikin su abinda ya bata ma aljanun rai kenan cikin bacin rai wani gabjeje a cikin su y kwarara uban ihu take dajin ya fara girgiza takoh bishiyoyi suka fara kadawa








Wani matashin saurayi nehhh yayi fitar burgu daga bayan wata bishiya yana mai falfalo wa da matsanan cin gudu yana tunkaro inda aljanun suke mutumin ya kasance ya nade kansa da wani farin rawani kuma tufafin dake jikin sa yakasan ce gari sol sai damarar yakin sa data kasance itama fara tas iya idanunsa kawai ake gani sakamakon rawanin daya sa a kan sa yana rike da wata zabgeguyar takobi mai matukar tsaho ita kadai sai sheki take da walwali







Koh da aljanun suka hangosa sai sukayi kansa cikin mugun nufi sabida kashe musu mai gida da yayi suna kusantar sa suna rabka ihu mai barazanar kashe dodon kunne amma shi koh a jikin yana gudu yana kwallah kabbara wadda itama ta cika koh ina a cikin dajin da amsa kuwwa suna haduwa suka kachame da masifaffen yaki mai matukar ban tsoro da muni..................







To fahh shin wai ya wannan yaki zai kasance nehhh kuma waye wannan mutumi mai fararen kaya daya yi yunkuri taimakawa su sadauki aisar muke ga nest page danjin cigaban lbrn






Idan naga comments zanci gaba da typing akasin hakan kuwa ina tunanin nikam zan dakata haka







Idan kanason book din daga farko saika nemeni ta wannan number 08143314152







By fast class
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
      🏀 🏀🏀🏀🏀
            🏀🏀🏀🏀

TARTSATSIN WUTA
(adventure story)
            🏀🏀🏀
     🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀

Tsara labari da rubutawa

ALIYU ISHAQ
Β Β  (fast class )
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

page 131➑135


Daga marubucin
KAUNAR UWA
UMAR FAROUQ and now
TARTSATSIN WUTA
(adventure story)









Azababben gudu yake zubawa ga takobin sa a hannun sa sai juyata yakeyi yana mai tunkarar aljanun kuma yana kwala kabbara suma basu fasa yin kansa ba SUNA nasu ihun mai barazanar fasa kunne suna haduwa wannan jarumi mai fararen kaya ya daka tsalle ya dira a tsakiyar dakarun aljanun ya hausu da Sara da suka baji ba gani gabas da yamma kudu da arewa nan da nan ya rikitar da aljanun suka rasa wani irin zafin nama wannan jarumi yake dashi ba amma duk da wannan jarumta da yake nunawa Sam ya kasa kashe koh da aljani daya hk suma sun kasa samun damar tabashi dan zullewr dayake yi da kauciya tamkar wucewar tauraruwa mai wutsiya







Sai da suka shafe sa a daya da rabi suna wannan gumurzu amma ba wani chanji abinda ya matukar bata ran wannan jarumi kenan ya dage iya karfinsa ya kwala kabbara ya yi wata katan tanwa ya tarwatsasu a saman bai yarda ya fado ba ya Dane hannun wani aljani daya kawo masa bangari aljanin ya wulashi sama a saman yayi wata alkafira ya dankarawa wani aljani Sara a tsakiyar kansa take aljanin ya wani kallah uban ihu wanda yasa dajin yin gurgiza nan take kwakwalwarsa ta dagargaje ya sulale kasa matacce koh da ganin wannan nasara daya samu Kuma ya gano lagon su sai y yi hamdala ga ya rika tashi sama tamkar ana janshi da majajkawa ya rika kade aljanun takoh ina








Nan take lbr ya chanza dan a wannan lokacin ne ya fara musu mummunar farna dan kafin su farga ya kai aljanu hamsin lahira nan take hankalinsu ya tashi ransu ya baci suka masa caaaaa kamar zasu cinye shi shiko ya wanxu yana mai aikasu inda ba a dawowa cikin bakin xafin nama juriya da bajinta









Sai da suka kuma shafe rabin sa a suna kwabxawa a wannan lokacin kuwa wannan jarumi ya kashe rabi da kwata na aljanun ya zame musu tamkar ifiritu kawai shawagi yake a Kansu koh da sukaga ba sarki sai ALLAH sai suka cika wandonsu da iska dan su tseratar da ransu








Ganin sun gudu nehh yasa shi saukowa kasa a hankali ya dira bisa turba cikin sauri ya isa inda su sadauki aisar suke kwance magashiyar ta fara ko Karin ceton rayuwarsu allaura ya fara sawa ya dinke musu raunin jikin su da gurin ya fara jagwal gwalewa ya sa musu magani sannan ya xauna yana kallonsu saida asuba ta kawo kai sanyi ya dan busa sannan jarumta jumaima ta kawo gwauron numfashi ta ajiye cikin azama wannan jarumi ya isa inda take y mai tallafo kanta chan kasa kasa yaji muryanta na fadin ruwa ruwa cikin sauri ya fidda battar ruwansa ya sa mata a baki saida tasha da yawa sannan tari ya turnuke tayayi saurin dauke battar daga bakin ta a hankali idanun ta suka soma budewa ta sauke su akan kyakykyawar fuskar wannan jarumi shima kallon tayakeyi wani irin duka yaji kirjinsa yayi a karon farko a rayuwarsa ya kafe ta da idanu itama irin wannan yanayin ta tsinci kanta a ciki kawai t kura masa idanu








Sai da suka jima a haka kawai sai yayi saurin dauke idanunsa daga kanta sannan ya saketa tunawa da yayi ba maharramar sa bace ya tafi gurin sadauki aisar da shima ya fara Motsi a hankali shima ruwa ya samasa a baki. Yasha da yawa tukun kana ya cire ya na mai kallonsa kamar yarda ya kalli yar uwarsa nan take ya hango kamar su nan take ya ayyana a ransa wadannan yan biyu ne to amma meya shigo dasu cikin wannan dajin ba amsa dan haka ya kama sadauki aisar y matsar dashi kusa da yar uwarsa y kura musu idanu saida gari ya soma haske sannan hankalinsu ya dawo jikin su sai dai ciwon dake jikin su da yanxun ya koma ya kame sakamakon maganin da wannan saurayi ya sa musu amma wani abin mamaki gaba ki dayan su sunki yin magana sai dai kallon juna shidai sadauki aisar tunani yakeyi taya ya suka kufita daga hannun wadannan fitunan nun aljanun amma daya kalli wannan saurayi sai ya daina mamaki dan ba mamaki shine ya koresu to amma abin dubawa shi wannan mutumi koh kasan baida kirar jarumai sai dai ya kasance kyakykyawa na gaban kwatance gashi fari tass kamar tsada haka dai yayi ta tunaninsa shi kadai ba amsa









Itama jarumta jumaima dai hk al'amarin yakasance kawai kallon wannan mutumi takeyi koh ba a fada ba tasan shine nan ya taimaka musu amma Kuma gashi baida kirar jarumai hk dai tayi ta zancen zucinta da tarin tambayoyi a danta.............








Comments and shared





Idan kana so daga farko kayiwa wannan number mgn 08143314152







By fast class
🏀🏀🏀🏀🏀🏀
      🏀 🏀🏀🏀🏀
            🏀🏀🏀🏀

TARTSATSIN WUTA
(adventure story)
            🏀🏀🏀
     🏀🏀🏀🏀🏀
🏀🏀🏀🏀🏀🏀

Tsara labari da rubutawa

ALIYU ISHAQ
Β Β  (fast class )
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


page 136➑140πŸ”š



Daga marubucin
KAUNAR UWA
UMAR FAROUQ and now
TARTSATSIN WUTA
(adventure story)





A GSKY INA JIN DADIN NUNA KAUNAR KU GA WANNAN BOOK NAWA INA GDY MASOYA DA AUNTY'S DINA DA KANNENA DA YAYYENA DA YAYA NA πŸ˜›



πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š






Lokacin da jaruma jumaima ta shagala da kallon wannan kyakykywan mutumi sai ta tsinci manta da kasa dauke kanta daga kansa haka shima bai daina kallon ta ba sai da suka dauki wani dan lokaci a cikin wannan yanayi tukun kana wannan jarumi ya tashi daga inda yake xaune ya tafi gurin wata koh rama mai ruwa garai garai ya tsuguna amma sai suka ga baisha ruwanba kamar yarda sukayi zato dan sunga ruwan battar sa ya kare baki daya ya jima a zaune a gurin tukun kana sukaga ya nade hannunsa ya fara wani irin Abu da ruwan wanda su basu taba gani wani mahaluki yayi ba cikin rashin fahimta suka ci gaba da kallonsa



Shi kuwa wannan jarumi ba komai yakeyi ba face alwala dan yaga lokacin sallah ya karaso bayan y idar da wannan alwalar sannan ya taso ya dan matsa gefe kadan ya shinfita wani mayafin sa ya tada sallah cikin matukar mamaki suke kallon yarda yake gabatar da komai nan take suka gane cewa Bauta yake yi duk tunani daya ne yazo musu wannan wani irin bautane a duniya amma dai sai duk suka bar abin a zuciyoyinsu da niyyar sai sun tambaye shi wannan wani addini nehh





Bayan ya idar da sallar sa nehh sai ya taso ya karaso gurin su tare da musu sannu da jiki kai kawai suka daga masa suka bishi da kallo shiko ya dan kushin Gida dan ya huta dan yasan wadannan mutane ba zasu iya koh da tafiya ba balle su yi mgn itako jaruma jumaima ji tayi a duk duniya wannan mutumin ya burgeta kuma zata iya yin duk abinda yake so indai zai zauna da ita shiko bai ma San tanayi ba yana chan yana harkan gabansaΒ  sun kusa sa a daya a cikin wannan yanayi tukun kana sadauki aisar ya dan kishin gida dan yadan huta nan take bacci ya daukeshi saida ya jima yana barcin nan jaruma jumaima na kallonsa itama tanason tayi baccin amma bazata iya ba sbd tanason ta ci gaba da kallon wannan saurayi






Shiko wannan jarumi tashi yayi yana dan tsagayawa kadan dan rangadi anan ya chinci wadannan kayan yaki da su sadauki aisar suka kwata a hannun sauran sarakan da suka kashe ya jima yana kallon su kana daga bisani ya dauko su ya da wo inda suke shima ya zauna a kusa da su dan yana basu kulawa sosae







Saida sukayi kwana biyu da yini daya sannan su jaruma jumaima da sadauki aisar suka samu lpy nan take wannan saurayi ya tambayesu daga inda suke da kuma abinda ya fito dasu daga Gida nan take suka bashi labarin koh mai da koh mai basu boye masa ba





Shima nan yake fada musu ni sunana sulaim na fito daga wani karamin birni dake yamma da wannan birni na sarki hashwan sunan wannan birni nurul Islam kusani mu mun kasance muna bautar ALLAH subhanahu wata'alah wanda shine ya halicci sammai da kassai ya halicci mutum ya halicci dabbobi da duk wani Abu mai amfani a doron kasa nasan cewa kuna da tambayoyi kala kala a game dani a cikin ranku amma nasan duk kunji amsoshin Ku ina muku tallan addinina idan kuna da sha'awar shiga sabida tafiyar mu ta daure tare da Ku Ku zama yan uwana Ku tayani yada addinnin ALLAH a sauran biranen dake wannan yanki kusani ni wannan shine burina kadai a duniya kuma dan shi na fito daga Gida







Koh da jin haka sai sadauki aisar da jaruma jumaima suka kama kallon kallon junan su kowa da abinda yake sakawa a ransa sukace kadan bamu lokaci muyi shawara tukun nan take yace wannan ai ba damuwa bace nan take ya tafi gurin wannan koramar ya tsuguna ya kama shan ruwa daga gareta





Suko su jaruma jumaima kallon kallo suka kamayi a tsakanin su na dan wani lokaci sannan sadauki aisar yace yake yar uwata kiyi sani cewa nasan duk abinda kikeji a game da wannan jarumi daya taimaka mana kuma xaki iya yin duk abinda ya sakaki a yanxun sabida kamuwa da kikayi da sansa amma abin bakin cikin shine idan mun karbi addinin sa ni a nawa tunanin batun daukar fansa akan sarki dizlan ya KAU kenan tunda birninsu zai tafi damu kinga ba ta yarda za ayi muga sarki dizlan har mu dauki fansar abinda yayi wa iya yen mu ni a shawara kawai ki cire abinda ke ranki yanxun mu kira aljani damgaskus ya dauke mu muci gaba da tafiya dan cika burin da dan shi muke raye har yanxun




Koh da sadauki aisar yazo nan a zancen sa sai jaruma jumaima tayi shuru tana dan tunani kana daga bisani tace tabbas duk abinda k fada gsky ne ya kai dan uwana amma kasani yarda na kamu da san wannan mutumin bana tunanin xan iya tafiya na.barshi kuma na rayu ni a tawa shawarar shine mu kirashi ya gwada mana abinda zai sa mu yarda cewa addinin sa shine addinin gsky akan tsafi da bautar gumaka idan mun gamsu da hujjojin sa ni na goyi bayan mu karba idan kuwa ban gamsu ba zamu tafi mu barshi a inda MUKA sameshi








Da wannan shawara sukayi amfani inda suka fada masa duk abinda suka yanke nan take ya amince kuma ya fada musu cewa idan ya shiga birnin Hindu ya kashe sarki hashwan ya dauke mashin sa ya basu sannan suka tafi dajin mutu wa ya kashe dodo ragazalu da ikon ubangijinsa nan zasu yarda dashi nan take kuwa suka amince dan sadauki aisar yasan wannan abinbba mai yuwuwa bane dan dodo ragazalu ya wuce yarda kuke tunani su Kansu idan sun nemo inda yake ba yakarsa xasuyi ba sato tsumin zasuyi su gudu amma wannan saurayi yace zai kashe shi to shi yaga yarda hakan zai faru





Jin da jaruma jumaima tayi dan uwan ta ya amince da wannan batu na jarumi suleim sai itama ta amince nan take kuwa suka datsi hanyar dazata kaisu birnin Hindu kai tsaya cikin sauri sadauki aisar ya ce zai kira abokin tafiyar su wato aljani damgaskus nan suleim ya ce masa y barshi shi baya sabga da aljan uban gijinsa zai kaisu lpy kuma ya kare su daga sharrin koh mai dake a kan hanyar






Nan aisar yake nuna masa zai rage musu tafiya nehhh shikuma yaki yarda yace shi yafi gane tafiyar kasa haka kuwa suka hkr suka bishi badan sunso ba cikin yardan uban giji sai gashi sun iso birnin Hindu a cikin sa a biyu kuma basuji wata yunwa koh kishi ba sakamakon addu'ar da jarumi suleim keyi a cikin zuciyar sa








An gwabxa yaki mai matukar muni da ban tsoro a cikin birnin Hindu inda akayi asar rayukan arna dan jarumi suleim da salama yajewa sarki hashwan ya masa tallan addinin sa amma yaki yarda nan ya yakeshi da taimakon mai duka ya kashe shi ya dauko wannan mashi ya bama su sadauki aisar suka hadawa makaman uku GU daya kuwa sai garin ya chan za launi baki daya nan take wani shirgegen aljani nehh ya bayyana mai siffar giwa kansa kuwa kan jemage nehh dashi aljanin na bayyana sai yayi sujjada ga wadannan kayan yaki dake hannun sadauki aisar sannan yace ya kai wannan jarumi kasani cewa ka karya duk wani sirihin tsafi dake duniyar nan baki daya kasani cewa duk wani sihirin tsafi na duniyar nan ya dawo cikin jikinka kai kadai ne kake da iko akan komai da kowa na wannan duniya kasani ni sunana aljani tsamratul labrul yau shekara budu casa'in da Dari dara da casa'in da Tara a duniya kuma duk wadannan shekaru dana kwashe su a duniya ba komai nakeyi ba face tsaron wadannan kayan yaki dake hannun ka kasani koh sanda wadannan kayan yaki suka rabu dga hannun mai gidana bayan yabar duniya ni nenan na rabasu duk inda ka gansu ni na kausu ina basu tsaro da naso a sanda kake yaki da wadannan sarakai zan iya zuwa na hanaka karbansu a gunsu amma danayi bincike sai na gani cewa kai ka dai ne zaka iya bawa wadannan kayan yaki tsaron da nake bukata







Kasani aljani damgaskus da kuk e tare dashi a matsayin abokin tafiya to Ku sani Dana ne na Dari da saba'in da Biyar nine nan na turo shi gareku dan ya Baku kariya kusani a yanxun hk aljani damgaskus ya koma Gida inda ya gaji sarauta ta ta sarkin aljanu na duk duniya baki daya






A yanxun hk dodo ragazalu yasan da zuwanku tare da wannan bakon jarumi amma bai isa yaga wannan tattaunawar tamu ba






Sai Abu na kashe wanda dashi xan muku bankwana koh da yazo nan sai ya kalli jarumi suleim yace an gaishe da jarumin jarumai kasani cewa ni da Baban ka manyan abokai ne kamar yarda kake musulmi haka nake musulmi kuma a gurin abbanka na karbi addinin gsky nayi yunkurin na yada addinin kamar yarda kayi niyya yanxun amma sai na kasa sabida wasu dalilai nawa amma yanxun ina maka albishir da dewa ka samu yan uwa wadannan tagwaye dasu zaki iya yada addinin ALLAH yana zuwa nan sai ya kalli su sadauki aisar yace







Kusani addinin wannan jarumi shine addinin gsky dan haka Ku gaggauta shiga dan ku samu rabo ranar gobe kiyama yana zuwa nan ya bace bat kamar bai taba wanzuwa ba







Bayan tafiyarsa nehhh su sadauki aisar suka nuna amincewar su akan addinin ALLAH nan take jarumi suleim ya biya musu Kalmar shahada suka mai mai ta nan take ya rungume sadauki aisar yana mai matukar farin ciki







Nan take jaruma jumaima ta bayyana masa soyayyarta nan take ya amince da alkawarin idan burinsu ya cika zai aureta







Basuyi wata wata ba suka durfafi birnin Istanbul acikin kwana biyu da yini daya suka isa a cikin wannan tafiya kuwa jarumi suleim ya koya musu yarda ake Bautar ALLAH da addu'o'in Neman tsari kala kala a kwana na uku ne suka riski dakin mutuwa inda suka iske dodo ragazalu yana jiransu yana ganin sadauki aisar da wadannan kayan yaki sai ya mika wuya shima ya shiga addinin Allah kuma ya tayasu yasa addinin a nahiyar baki daya inda su sadauki aisar suka riski sarki dizlan a dokar daji nan suka nuna masa ya shiga addinin ALLAH ya kuna kinsa nan suka kaddamar masa suka kashe shi shikuma aljani shabrul ya musulunta kuma ya mika wuya







Nan suka dunguma tare aljani shabrul nr ya dauke su sai birnin kisra inda su saduki aisar suka sadu da iyayen su nan suma suka musulunta sannan birnin hairil salad SUNA sun karbi musulunchi nan suka basu lbrn mutuwar sadauki Aryan sunyi Kuka daga karye suka masa addu'ar samun rahama







An daura auren jarumi suleim da jaruma jumaima inda suka dunguma har sadauki aisar sai birnin nurul Islam dan su raka amarya da ango





Iyayen jarumi suleim sunyi farin cikin ganin dan masu da kuma matarsa nan take sarki yayi murabus ya bama dansa jarumi suleim







Anan sadauki aisar yyaga kanwar jarumi suleim ya nuna yana son ta nan ta amince masa aka daura aurensu suka koma birnin kisra nan sarauniya sima tayi murabus ta bama danta yarima aisarΒ  suka zauna cikin farin ciki shida matarsa ............




Alhmdulillah masha Allah







Anan na kawo karshen wannan book nawa may SUNA tartsatsin wuta ina rokon ALLAH ya yafe mana kura kusan mu abinda mukayi dai dai ALLAH ya bamu ladan sa




sai mun HADU a sabon book dina mai suna SANDAR GIRMA




WhatsApp number 08143314152






By fast class


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment