Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sa ta ɗan dakata,

"Kin san me? Cewa na yi mata ta zauna ta yi karatu, ko engineering ta y..."

Dariyar da ta taho mishi ce ya sa shi dakatawa, kafin ya ci gaba.

"Kin san me ta ce?"

Kai ta gyaɗa Cikin dariya,
"Wai Injimiyarum!"

Tare suka sake fashewa da dariya, sai da ta ɗan tsagaita sannan ta ce,
"To, kai ma sai ka haɗa ta da wani injimiyarum! Ina laifin ma asibiti ko banki ta sami kuɗi ta dawo da suwit Mai Unguwar ta birni."

"Banki kam! Da yake kuɗin kwasowa za ku yi ta yi ko?"
"Yo wa ya sani?"
"Ke." Ya faɗa da dariya.
"Kai dai Afirij."
"Ko kuma Labano ba."
Duk suka sake sa dariya,

Hajiya da ke ƙofar falon ta share ƙwallar da ta gangaro mata, tana tunanin irin yanayin da yaran za su ji, idan suka ji labarin mutuwarta.

Sallama ta yi, ta shiga falon, masauƙi ta yi kan kujera, tana kallonsu, suma ita suke kallo. Domin duk ƙoƙarin da ta yi wajen ɓoye damuwarta, sun gano damuwa maƙale a fuskarta.

Murmushi ta ƙaƙaro, ta ce,
"Hira a ke yi ne?"
Lubna murmushi ta yi Afreen ne ya amsa,
"Zainab ta tafi ta barmu da kewa Mommy. Goben za mu ta fi da wuri ko?"

Ya faɗa yana kollon Momyn, yana rausayar da kai.
Murmushin ƙarfin hali ta sake yi, ta ce,
"Abinda ya kawo ni kenan."

Ɗaga hannunsa na dama ya yi, ya dunƙule yatsun ya karkaɗa ya ce,
"Yauwa Momyna!" Ya ƙarasa faɗa yana kwanciya kan cinyarta.

Harara Lubna ta watso mai, ƙaramin filon dake kan kujerar ta ɗauka ta jefo masa, ta ce,
"Dubesa goɗai-goɗai da shi, ya wani mimmiƙe, Allah Mommy zai karya miki cinya."

Gwalo ya yi mata, ya ce,
"Gara ni ai, ke kullum kina kwance jikinta kamar wata kyanwa, ni ko sai idan autancin ya motsa."

"Ji! Wai auta. Tuff!!"
Ta tofar da yawu.
"Ya son ranki Labano?"
Ya fana yana ƙanƙame Momyn.
"Raina fes! Ban ji komai ba yaro."
Dariya duk suka sa, Mommy kam na jinsu.

Ganin hirar ta su ba mai ƙarewa ba ce, ya sa ta ce,
"Ya isa, yanzu dai ku je ku kwanta, gobe da asuba za mu wuce."

Tare suka tambayeta, suna zaro idanu,
"Da asuba Mommy?"
"Eh, harda Dadynku."
Da sauri Afreen ya miƙe, ya sanya hannayensa duk biyu ya dafa ƙafafunta, ya na kallon fuskarta ya ce,
"Mommy ya yarda zai je ya ba Baba Ilu haƙuri, ya bar mana Zainab ne?"

Idanunta suka cicciko, da sauri ta miƙe, ta juya tana tafiya, tana faɗin,
"Ku shirya da wuri, kun san Daddynku, ba zai tsaya jira ba, ku ɗebi kaya kuma don zamu kwan biyu."

Tana gama faɗi ta fice, hawayen da ta maƙale suka gangaro.

Tana fita, Afreen ya yi ɗan ƙaran farin ciki, da sauri suka nufi ɗakunansu domin shiryawa.

_Ummyn Yusrah_


*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ni Marubuci sarkin aiki, ni ke rayawa da kashewa, ni ne mai rushe dauloli in na so kuma in maido su, alkalamina ne alkali, mai shari'a ne mai yankewa, duk a rubuce nake yin wannan, sai ku tayani gurin aikawa, al'ummata bar kokwanto, duk kimata ba Marubuta._
#Wakar kare martabar Marubuta#

_Ummyn Yusrah_

_47_

Gidan da ya cika da kwaramniya ɗazu, a yanzu shi ne ya dawo gidan jimami da koke - koke.


Da yawan mutanen da suka naɗo tsummokinsu da niyyar zama sai bayan biki, a daren suka tattara suka gudu.

Duk wanda aka ce ya kwana da gawar Abulle, sai ya ce bari ya je gida ya dawo, ba ka ƙara ganinsa. Ciki kuwa, har da Umma Sakina.

Inno da ƙanwar mahaifiyarta ne a ɗakin, sai marigayiya.

Sallah kawai Inno ke yi wanda idan aka ce ta ƙirga, ba za ta iya sanin adadinsu ba, ita dai kawai yi take haɗi da addu'a da kuma nema mata gafarar Ubangiji. A haka ta shafe tsawon daren nan tana ibada, shi ma Ilu hakan take a garesa.

***

Kallo ɗaya za ka yi ma Mommy da Daddy, ka gane cewar ba su samu isasshen barci ba, duba da yanayin idanunsu da suka canza launi, da kuma rashin kuzari, ga kuma fuskokinsu da ke nuna alamar damuwa.

Sun fi minti goma zaune cikin mota, suna jiran Lubna ta fito, sai dai shiru.

"Kai! Fita ka je ka faɗa mata, idan ba za ta fito ba za mu tafi."
Mommy ta faɗa ma Afreen

Kafin ya kai ga cikin gidan, sai ga ta ta fito da sauri.

"Ke fa muke jira, kin je kin zauna."
"Mu je dalla!"

Alhaji da direba a gaba, Mommy da su Lubna a baya, suka ɗau hanyar Mai Ludaya.

***

Cikin shigarsa na riga 'yar shara na yadi da wando ya fito, hannunsa riƙe da ledar Viva, wanda ya sa kayansa kala ɗaya, sai burodi da ya sai ma Innarsa Talle.

Rufo ƙofar ɗakin na su ya yi, ya nufin wurin mai gidan hayansu, ya kai masa makullin ɗakin, akan zai je gida kwana biyu zai yi ya yawo.

Suka yi sallama ya nufi hanyar titi, domin samun abin hawar da zai kai sa tasha.

Ya yi tafiya sosai, don har ya bar unguwar da ya ke bai sami abin hawa ba, kasantuwar gari bai gama wayewa ba, ga kuma lokaci na sanyi.

Sauri ya ƙara, dalilin hango wani mai abin hawa da ya yi can nesa da shi, hawa titi ya yi da niyyar tsallakawa, sai dai, bai yi aune ba ya ji shi a sararin samaniya yana shawagi, daga bisani kuma ya ji an jefosa ƙasa tim! Ɗan ƙara ya saki, na zafin da ya ji.

Mai mashin ɗin da ya bugesa kuwa, ganin ba kowa ya sa ya ƙara wuta ya gudu.

Yunƙurawa Hamusu ya yi da niyyar tashi, sai me? Ji ya yi, ƙafarsa ta dama ta riƙe ya kasa miƙewa.

Ya yi ya taka ƙafa, ta ƙi, kawai sai ya koma ya kwanta, ya rufe idanu. Hawaye mai zafi ya gangaro masa ta gefen idanu, magana ya fara shi ɗaya.

"Me ya ke shirin faruwa da ni? Allah ka kawo min agaji, Innata ki yafeni, alhaƙinƙi ne ya fara kamani, ina shirin zuwa gareki, ƙaddara ta hana Inna! Gani a yashe kan titi babu mataimaki, na gudu domin ƙin ganin auren Abulle, yanzu gani ina son dawowa gareki amma ba hali, rayuwata Inna! Rayuwata za ta shiga garari."

Sharrr! Hawaye ya sake zirarowa daga idanunsa.

Ƙararrawar sanarwa ake ta kaɗa masa daga cikin moton, domin ya matsa sai dai ko gezau ya ƙi yi, sai ma gyara kwanciya ya yi, fatansa kawai motar ta bi ta kansa ya mutu ko ya huta, don ya san nan gaba sakayyar ba ta ma mahaifiyarsa rai da ya yi, sai tafi haka.

Cikin damuwa mai motan ya juyo ya kalli matar da ke kwance a kujerar baya, hannunta riƙe da ciki, sai murƙususu ta ke yi, ya ce,

"Sannu! Yanzu zamu isa asibitin, wani ne kwance a kan hanya, ina ga irin masu shaye-shayen nan ne ya sha ya yi tatul, ya zo ya kwanta kan hanya. Barin fita in samesa, sannu."

Ya ƙarasa faɗa, yana fita daga cikin moton.

"Haba Malam! Ka gama shaye - shayenka, ka rasa ina za ka yi masauƙi sai tsakiyar hanya? Don Allah ka matsa in wuce, tare nake da majinyaciya, ko kuma in jaka ta ƙarfi."

Mutumin da ke tsaye kan shi ya yi maganar, yana ƙoƙarin sunkuyawa ya janyoshi, ganin ba shi da niyyar tashi. Hakan ya sa Hamusu buɗe idanun da ke ta zubar da hawaye.

Yau shi ake ƙira da ɗan maye, shi da ko sigari bai taɓa sha ba, yau an ce da shi ɗan maye.

"Don Allah ka taimaka ka bi ta kaina ka wuce, a yanzu rayuwata ba ta da wani sauran amfani, na roƙeka da kaima ka bi ta kaina ka takeni ka gudu, kamar yadda mai mashin ɗin nan ya bugeni ya gudu. Don Allah ka taimakeni, idan na zauna haka ban san wa zai tallafi rayuwata ba, na sani sai dai in ƙare rayuwata a kan titi, amma babu mai cetona a garin nan, tunda duk na fuskacin ɗabi'u da halayyarku na son kai da rashin taimako duk ɗaya ne. Ka taimaka don Allah."

Ya ƙarasa maganar yana haɗa hannayensa biyu, yana roƙon mutumin.


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_Badiyya Adam (Beauty Queen) har kullum ba zan gajiya da miƙo saƙon godiyata a gareki ba, godiya mai tarin yawa, Allah ya saka da alkairi, ya ƙara miki lafiya._

_48_

Tausayin shi ne ya mamaye illahirin zuciyar mutumin, domin cikin maganar da ya yi, ya fuskanci yana neman taimako a yanzu, ya kuma fahimci bankesa da mashin aka yi aka gudu, ba wai shaye - shaye ya yi ya kwanta a kan hanya ba, kamar yadda ya faɗa.

"Zan iya taimakonka?" Mutumin ya faɗa.

Da sauri Hamusu ya buɗe idanu ya kallesa.

Kai ya gyaɗa ya miƙa masa hannu, ya ce,

"Ka yarda da ni, ka kuma sani cewar halayya da dabi'u sun bambanta, ba duka aka taru aka zama ɗaya ba. Ka daina yi ma mutane kuɗin goro, duk rintsi duk wuya sai an ɗebe tsakuwa a cikin ƙasa, domin kowa da halinsa. Asibiti zan kai matata da ta kwana ba lafiya, shi ya sa kaganni da sassafe, me yiwa wannan ita ce silar haɗuwarmu, Allah ne ya ƙaddara ni zan taimakeka, ba don haka ba, a gida zan yi mata komai, ni likita ne a babban asibitin garin nan."

Yana gama magana ya juya zuwa moto, har yanzu tana nan cikin mawuyacin hali.
Buɗe ƙofar bayan ya yi, ya sunkuyo daidai fuskarta.

"Ƙalbi mu tafi don Allah! Zan mutu, cikina." Ta faɗa cikin raunanniyar muryarta.

"Yi haƙuri, yanzu za mu tafi, wani aka bige da mashin aka gudu, shi ne zan taimaka masa sai mu tafi tare ko?"

Kai kawai ta ɗaga, ba tare da ta iya yi masa magana ba.

Da sauri ya koma gun Hamusu ya kamosa, da taimakonsa suka kai ga moto, domin da alama ƙafarsa ta dama akwai matsala. Yana sanyasa ya figi motar suka yi gaba.

****

Tukur direba gudu kawai yake tsulawa, domin Daddy ya sanar da shi yana son su isa da wuri domin su sami jana'izar.

Afreen da Lubna sai zuba hira suke, da kuma ɗokin ganin Abulle.

"Ku kam kun ishemu da surutu, addu'a a ke yi idan ana tafiya ba hira ba."

Mommy da ke ta jan carbi ta faɗa musu.

Duk suka ɗinke bakinsu, suka koma kallon yadda hanya ta ke, sai jefi-jefi suke magana.

Tunda suka fara karo da duwatsu akan hanya bakinsu ya mutu. Kafin su isa Guwal duk sun yi laushi, sakamakon karo da duwatsu da shiga gargadar da suke yi. Abinka da ba sabon ba.

Suna isa suka sami mashina, lokacin har tara ta gota.

****

Jama'a ne tun daga waje har cikin gida, domin tun a daren labarin rasuwar Abulle ya riski da yawan mutanen garin.

Mai Unguwa ma da tunda ya ji saƙon rasuwar, masassara ta kamasa ya rarrafo don sallatar masoyiyarsa da kuma rakata makwancinta.

****

Har ƙofar gida masu mashinan suka sauƙesu.

Daddy na sauƙa ya nufi dandazon jama'ar, Afreen da Lubna kallon mamaki suke yi ma juna na ganin taron jama'a.

"Za ka sallamesu su koma bakin aikinsu ne, ko za ka tsaya kallon juna?"

Mommy ta faɗa ma Afreen, ganin bai shirya sallamar masu mashinan ba.

Da sauri ya ciro dubu ɗaya ya basu, kowa ɗari biyar-biyar don Tukur ya tsaya zai yi sayayyar kayan abinci ya taho da shi.

Da sauri ya biyo bayan su Mommy, da ta tasa Lubna a gaba.

"Mommy dama yau ne ɗaurin auren?" Ya tambaya lokacin da ya iso garesu.

Kallonsa ta yi ba tare da ta ba shi amsa ba, sai ma cewa ta yi,

"Ka sami Daddy a can, mu zamu shiga ciki."

Tana kaiwa nan ta riƙe hannun Lubna, suka raɓe gefen mutanen suka shige ciki, shi kam ya kasa fahimtar komai, ga dai mutane da yawa a wajen, wasu sai alwala suke wanda ya kasa fahimtar ta mecece? Ga wasu kuma sai goge idanu suke, da alama kuka su ke yi, me ke faruwa ne wai? Ɗaurin aure ne ko rasuwa?

Dam!! Kirjinsa ya buga, take kuma ya shiga harbawa da sauri - sauri, tunowa da ya yi, mai mashin ɗin da ya hau, ya gwada masa inda aka yi hatsari jiya, har ma yarinyar ta mutu, ga jini kaca-kaca a wajen duk ya bushe.

'Abulle!' shi ne sunan da mai mashin ɗin ya ambata, wanda ko kusa bai alaƙanta mutuwar da Zainab ɗinsu ba, domin su da Zainab suke ƙiranta.

Kenan dai ita ce ta yi hatsari ta mutu? Kai! Ƙarya ne, ba mutuwa ta yi ba.

Bai san sanda hawaye ya fara zirarowa daga cikin idanunsa ba, ya kuma kasa motsawa a wajen, don isa ga Daddy ya amsa masa tambayoyin da zuciyarsa ke yi masa.

****

"Ayya! Ayya!! Abulle!! An yi taron biki ashe taron mutuwa ne, kina ta zaga dangi sallamar tafiya gidan miji, ashe sallama da duniya ce gabaɗaya, Allah sarki 'yannan, Allah ya jiƙanki ya sa mutuwa hutu ce, ya ba iyayenki da 'yan uwanki haƙurin jure wannan rashi naki, Allah ya y..."

Kuka ne ya hana matar ƙarashe maganarta.

Maganar da ta doki dodon kunnen Lubna kennan, daidai lokacin da suka shigo gidan.

Turus! Ta ja ta tsaya tana girgiza kai gami da kallon Mommy.

Janta ta yi sai dai ƙam! ta ƙame a wajen, ta kasa motsawa, sai hawaye da ke rige-rigen sauƙowa daga cikin idanunta.


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

    _Ummyn Yusrah_

  _49_

Wani irin kallo mai wuyar fassara, ta bi yamutsattsiyar tsohuwar da ke ta mamular goro a bakinta ta yi, ta kuwa sake maimaita magartata wanda ta ji a bazata.

Kallonta ta maida kan Mommy da ta ke riƙe da hannunta, kallon yanayinta, ya sa wani sashe na zuciyarta ta fara yarda da abinda ta ji daga shigowarta gidan.

"Mommy da gaske ne abinda kunnuwane suka jiyo daga shigowata? Da gaske ne taron mutuwar Abulle a ke ba taron bikinta ba?" Ta tambayi Mommyn a daidai lokacin da idanunta suka fara tsiyayar da ƙwalla.

"Mu shiga ciki, kinga nan kan hanya ne, mutane na wucewa."

Mommyn ta faɗa, a lokacin da ta dauke idanunta daga kanta, ba tare da ta ba ta amsar tambayoyinta ba.

"Mommy ki amsa mun tambayata."

Mannata ta yi da jikinta. Ta ce,
"Yi haƙuri, mu shiga ciki tukunna."

Tafiyar kawai take, amma sam, ba ta ganin gabanta, balle ta ga masu yi ma Mommy gaisuwa da barka da zuwa.

Shigarsu cikin gidan, ya yi daidai da fito da ita daga ɗakin da aka gama shiryata, aka sanyata cikin makara za a fita da ita a yi mata sallah a kaita makwanci.

"Ku dakata da ita Hajiya su yi mata addu'a." Umma Sakina da take ta sharar ƙwalla ta faɗa.

Tsugunnawa su ka yi a gaban gawar, Mummy ta yi mata addu'a, sannan ta buɗe zanin da aka rufeta da shi.

Fuskarnan a sake tamkar mai murmushi.

"Mummy! Wallahi ba ta mutu ba. Kalleta, kalleta fa. Allah murmushi take yi, wallahi ba mutuwa ta yi ba, ki ce su cireta a cikin abun nan, tana raye wallahi, ƙarya suke yi. Barci kawai ta ke yi, ki ce su kai ta ɗaki, ba ta mutu ba." Lubna da ke ƙankame da hannun Mommy ke faɗin haka, lokacin da ta leƙa ta ga fuskar Abulle.

Ganin tana neman fita hayyacinta, ya sa ta ƙarasa zama daga tsugunnon da ta yi, ta janyota gaba ɗaya ta kife kanta a jikinta, hannunta ɗaya ta yi musu alamar su tafi da ita.

"Lubna!!" Ta ƙira sunanta a saitin kunnenta.

Ta ɗora da faɗin,
"Ki tattaro natsuwarki, kin dai san mamaci baya buƙatar kuka ko? Addu'a za ki yi mata, kin ji ko?"

"Mutuwa? Mutuwa fa kika ce Mommy? Ki duba fa ki gani, ba ta mutu ba, ba yanzu za ta mutu ba, ki tasheta barci take yi." Ta faɗa cikin matsanancin kuka, a lokacin da ta ɗago kanta tana kallon Mommy.

"Lubna! Gudu ga harbabbe ai ɓata lokaci ne. Kwananta ya riga ya ƙare, wanda ya fimu sonta ya riga ya karɓi abinsa. Gata ɗaya za ki mata a yanzu, shi ne addu'a kin ji ko?"

Bakinta na rawa tana girgiza kai, hawayenta ta kasa tsayar da su. Ta ce,
"Mommy ba za ta mutu ba, sai ta yafemin abinda na yi mata. Ba ta mutu ba ko Mommy? Ki ce tana raye Mommy, tana raye ba ta mutu ba."

"Na ce ki saita tunaninki waje ɗaya ko? Ki kalli yadda kika tara mana mutane, ki tashi mu shiga ɗaki." Mummy ta ce a kausashe, ganin Lubna ba ta da shirin yin yadda ta ce.

"To! Ki ce su cireta cikin abin nan, ta tashi mu shiga ɗaki, kuma tare za mu koma da ita ko?" Ta ƙarasa maganar tana juyawa don ganin gawar.

Idanu ta shiga rarrabawa gani babu ita babu dalilinta, sai tarin mutanen da suka taru suke ta sharar hawaye.

Cikin tashin hankali ta juyo.
"Mommy! Ina take?"
"Mu je tana ciki." Ta faɗa tana miƙewa, don idan ba haka ta yi mata ba, ba za ta miƙe ba.

****

Ɗakin taimakon gaggawa aka shiga da Badiyya, matar Likita Kamal da kuma Hamusu.

An ba shi duk wani taimako da ya kamata, an kuma tabbatar da komai daidai, buguwa ce kawai da ya yi, zai ji sauƙi nan ba da daɗewa ba.

Zai kwana biyu kafin a sallamesa. Ita kam Badiyya tunda ta sha ruwa da magungunana ta ware.

***

"Kunsan Allah! Yau banga wanda zai hanani shiga duniya nemo tilon ɗana ba. Ina dalili kullum ku yi ta rainamin hankali? Kuna yi mini daɗin baki cewar kun tura Salele, ina ce shi Salelen kullum yana cikin gidan nan yana shawaginsa? Idan na rasa ido na rasa ji ne? Wallahi idan ba ka zo ka mai dani Mai Ludaya ba sai na ci mutuncinka. Ka fada min nan ɗin wace uwar nake tsinanawa? Me nake ɗauka, baya ga kulleni da kuke a ɗaki, kamar gidan kaso."

Inna Talle ne da ta fito ta yi tsaye a tsakar gidan ke ta zuba ruwan masifa. Baki cike da kumfa tana hargagi, ga shi babu idanu.

Kande dake tsaye cikin rashin sanin mafita ta ce,
"Yaya ki yi haƙuri don Allah! Malam yana iya bakin ƙoƙari wajen nemo yaron na..."

Cikin harzuƙa ta katseta.

"Ke Kande! Kin rufemin baki ko sai na sheƙa miki mari. Munafukar mata, kullum da na yi magana ki wani fiffiƙe ki gwadamin yana ƙoƙari akan hakan. Gwadamin ƙoƙarin, na ce gwadamin ƙoƙarin."

Gefe ta yi tana murmushi, jin za ta sheka mata mari kamar mai idanuwa.
"Allah ya baki haƙuri."
"Kema ya baki idan da daɗi, mara kunya kawai."

Sum-sum, ta wuce ta bar wajen. Dama ita ɗaya ta rage a gidan, sauran duk sun ta fi jeji.

"Ina nan, ina jiran dawowarsu, ba inda zan je gara yau a yi ta ƙare, idan da Salele ne ya ɓata da tuni kun ja mayafi kun shiga duniya nemansa. Ni kun barni kullum cikin zullumi da tunanin nawa ɗan." Ta sake gyara tsayuwarta, don zaman jiran dawowar mutanen gona.


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

*K'arshe*

_50_

Kowa ya tuba don wuya, ba lada.
Inna Talle dai tun tana iya tsayuwa, har ƙafarta ta gaza ɗaukarta ta nemi waje ta zauna, daga zaunen ma gyangyaɗi take hakan ya sa ta ja tsufanta ta yi ɗaki don sanya haƙarƙarinta a makwanci, har lokacin ba wanda ya dawo.

****

Tun daga yi mata sallah, zuwa kai ta makwancinta, zuwa yanzu da suke zaune ƙofar gida karɓar gaisuwa, gani ya ke, al'amarin tamkar almara, gani ya ke ba ta mutu ba. Idanu kawai ya zuba ma saitin ƙofar gidan, tamkar za ta fito, su zauna ta yi masa hirar shirmen nan nata. Addu'ar da ya ke, Allah ya sa ya farka daga wannan mummunar mafarkin da ya ke tun ɗazu.

Ga shi nan dai zaune kamar mutum-mutumi, abu ne mawuyaci ka iya gane halin da ya ke ciki. Baya ga fitar numfashi da kiftawar idanunsa, babu wani abu da ke motsawa a jikinsa.

"Haba Afreen! Kada ka bari tunani ya shige ka..."

Daddy da ya matso kusa da Afreen ne ya yi masa magana, ganin hawayen da ya ziraro daga idanunsa zuwa kan fuskarsa ne ya sa ya katse maganar.

Shiru ya yi na ɗan lokaci ya ci gaba.

"Haƙuri da juriya shi ya kama ce ka, ka yi mata addu'a Afreen! Shi ta fi buƙata, ba kuka ba."

"Me ya sa Daddy? Me ya sa tun a can ba ku sanar mana ba? Me ya sa kuka yi mana bazata? Ka fi kowa sanin wani hali Aunty Lubna za ta iya shiga a wannan lokacin. Na tabbatar idan ni na daure a matsayina na Namiji, ka sani ita ba lallai ta iya jurewa hakan ba. Da tun a can kuka sanar mana da komai, na san za ku taushe ta kafin mu zo..."

Kuka ne ya ƙwace masa.

Rungumosa ya yi jikinsa ya shiga bubbuga bayansa, yana magana.

"Gudun faruwar hakan ya sa muka ƙi sanar da ku, domin mun san shaƙuwar da ke tsakaninku zai iya jefa ku cikin wani hali. Ka yi ƙoƙarin riƙe kanka, ka ga taron mutanen nan duk kai su ke kallo. Ka shiga ciki ka duba wani hali su ke ciki."

Ɗago kan da zai yi, su ka yi ido biyu da Sarkin fada da ke ta galla masa harara, shi a dole yana taya Mai Unguwa kishi, gani ya ke kamar saurayinta ne.

"Zan shiga, ba yanzu ba. Daddy waye wancan da ya kima rawani, tamkar kullin kayan wanki?"
Ya tambaya yana kallon saitin da tawagar mai Unguwa ke zaune.

"Sarkin fada ne, wancan ɗayan kuma shi ne Mai Unguwa." Daddy ya ba shi amsa.

"Banza girman kato, ƙaramin mai hankali ya fishi. Idan ba zalunci ba, kamar wannan a ce shi za a ba Zainab? Ga shi ma Ubangiji ya karɓi abarsa. Shi ma Baba Ilun ko makancewa ya yi ne Ohho!"

Cewar Afreen da shi ma ke ta aike musu da saƙon harara, ga kuma wani kululun takaici da ya gama tokare masa maƙoshi, ji ya ke, kamar ya tashi ya je ya shaƙo wuyan tsoho mai budurwar zuciyar nan, domin shi ne sila. Da bai ballo zancen aure ba, da yanzu tana raye.

"Ranka shi daɗe! Anya ba za mu bar wajen nan ba? Sai ƙus-ƙus ake yi, kuma da alama duk kai su ke kallo, gani su ke duk kai ne sanadin komai, da ba a daga zancen aure ba da hakan bai faru ba."

Cewar Sarkin fada, da ya dawo da fuskarsa ga mai unguwa, bayan sake aika ma Afreen da wani mugun harara. Kansu na haɗe ya ke maganar cikin murya ƙasa-ƙasa.

"Allah ko? Gara mu zo mu tafi, nima duk a tsarge nake, ga kuma masassarar nan da ta dameni sosai."

"Mu yi musu sallama kawai mu wuce, tun kafin a fara aiko mana da makaman ƙare dangi ta ido. Ka ga wancan matashin da ke saiti na? Wannan da gani taƙadari ne, ina ga kuma saurayinta ne. Ja'iri mai kama da ƙosai."

"Na hangosa, sai saƙonni ya ke aikon ta ido. Sallamesu sai mu wuce."

Sallama su ka yi, bayan Sarkin fada ya sanar da su cewar, masassara ta dami mai unguwa sakamakon faruwar wannan al'amari.

*****

"Kinga ni ko? Na ce ki sassauta kukan nan kada ya ja miki zazzaɓi, amma tamkar zugaki na ke, dubi yadda kike ta ɓarin sanyi, kamar wacce aka izama shokin."

"Hajiya a bi ta a hankali, kin san irin wannan sabo na kwana kaɗan ya fi shiga jiki, ga kuma mutuwa ta farat ɗaya, dole abun ya dameta."
Inno da ke jan carbi ta yi magana ganin yadda Mommy ke yi ma Lubna da ke kuɗunɗune faɗa.

"Sai a ka ce ta yi ta kuka? Ashe ba za ta sanya ma ranta haƙuri ba? Duk wata shaƙuwa da suka yi, ya kai shaƙuwar da kuka yi ke da kika haifeta? Yanzu ina za a samu asibiti nan kusa?"

"Babu kam! Asibitin ɗaya ne, kuma ba ma'aikata. Akwai saiwa ai, idan za ta iya sha sai a kawo mata, a yi haƙuri a bi ta a hankali."

Da ƙyar aka samu ta sha maganin, ta koma ta kwanta.

***

"Ni fa ina ga kamar ƙafar nan akwai karaya, ba za a kai sa wajen Malam Ɗahe ya duba ba kuwa? Kwanansa biyu fa kenan da dawowa gida, bayan ya kwana ɗaya a asibiti. Ƙafar za ta yi masa tsami."

Cewar Badiyya da ke kallon Kamal, lokacin da suka shigo duba Hamusu, a ɗaya daga cikin ɗakunan dake gidan wanda suka yi masa masauƙi.

"Na yi tunanin hakan, na ga har yanzu ba ya taka ƙafar. Barin shirya sai in kai sa."

Ficewa su ka yi, ya ta fi shiryawa.

Hamusu da tun lokacin da aka ambaci karaya, ya ji damuwa ta ziyarcesa, fatansa kawai Allah ya sa buguwa ne ba karayar da suka ambata ba. Domin ko kwana biyu baya fatan ya kara a cikin garin nan, ba don rashin tafiyarsa

Please Login or Register in order to submit comment