Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciyarta sai ƙuna yake yi mata. Walaƙanci na ɗaya daga cikin abinda ta tsana, sai dai ta lura wannan Lubnar mutuwar 'yar walaƙanci ne. Amma, ba komai. Gobe i yanzu ma ta yi nisa da garin.

" 'Yammatan mai ludaya an sha kyau."
Bata ɗago kai ba, murmushi kawai ta yi. Sai dai idan ka dubeta zaka iya hango ɓacin rai maƙale a fuskarta."

"Yaya ba ki yafa mayafin ba, kika tukuikuyeshi a wuya?" Afreen dake tsaye ya sake tambayarta.

"Ƙauyanci mana. Kasan ko yaya baƙauye yake sai ya nuna halin nashi."
Lubna ta faɗa lokacin da ta iso falon tana ɗaura ɗankwali.

Kallon takaici bita da shi. Yanzu kam ta gama gano tsanarta ce ƙarara a fuskar Lubna.
"Hummm! Na gode Allah ina da tushe ba a kwararo aka tsintoni ba. Ki sani ko yaya mutum yake daraja ce da shi. Ɗan adam ba abun walaƙantawa bane. Idan ma kin yi haƙuri, gobe iyanzu babu ni a gidan nan."
Harzuƙowa ta yi, ta nufota gadan-gadan tana faɗin,

"Iye! Ashe rashin kunyar naki har ya kai haka ne? Har kin kai ki faɗamin magana?" Afreen da ya tare ta ne ya ce,
"Haba Anti Lubna! Abin da kike yi mata bai dace ba wallahi."

Kallonshi ta yi rai ɓace ta ce,
"To, mara kunya! Sai ka koyamin abin da ya dace." Tana kaiwa nan ta ja tsaki kan kujera ta zauna.

Ya juya da niyyar yi ma Abulle magana yaga bata nan. Da sauri ya nufi ɗakin Lubna.

Ji alamar motsin tafiyar mutum yasa ta yi saurin sanya bayan hannunta ta goge hawayen da ya wanke mata fuska.

Shigowa ɗakin ya yi, ganin ta canza kaya yasa shi tambayarta.
"Ya naga kin canza kaya kuma mu da zamu fita?" Ba tare da ta ɗago kai ta kalleshi ba ta ce,
"Ku je kawai."
"Me ya sa?
Ya sake tambayarta
"Akwai abin da zan yi ne."
"Ban yarda ba! Abin da Anti Lubna ta yi miki ne ya ɓata miki rai ko? Ki yi haƙuri kada abun ya dameki, rashin fahimtar juna yasa hakan da zarar kun kun fahimci juna komai zai daidaita ki yi..." Bai kai ga ƙarashe maganar ba muryar Lubna ta katseshi tana faɗin,

"Kai! Dallah ka zo, ka bar mutane tsaye a waje suna jiranka ka zo nan ka yi zamanka. Idan ba za ka kai mu ba ka bani makullin."

Tana kaiwa nan ta juya.

"Ki yi haƙuri kin ji? ki sako mayafinki ki zo mu tafi. Muna jiranki."
Ya fita.

Yana fita ta yamutsa fuska, ta ce
"Ko maton ubana Ilu ne, ba zuwa zan yi ba. Idan kun gaji da jira sai ku yi gaba."
Jakar kayanta ta janyo ta zazzage kayan ciki duka, ta shiga ɗaukarsu da ɗai-ɗai tana sake naɗesu, duk da a naɗen suke.

"Wallahi Mommy mu tafi, ta sanfa ita muke jira don iskanci ta je ta yi zamanta. Sama da minti goma muna zaman jiranta." Lubna dake zaune a bayan moto kusa da Hajiya ta faɗa.

"Fita ki je ki dubota. Meyuwa wani abun ya tsaida ita ko batasan mun fito ba." Cikin yanayin shagwaɓa Lubna ta kalli Hajiyar ta ce, "Mommy!"

Itama kallonta ta yi, fuskarta ba alamar wasa ta ce, "Eh!"
Ganin yanayin Hajiyar yasa ta fita da sauri badon ta so ba. A sonta a aiki Afreen.

Tana zaune a ƙasa, ta jingina bayanta da gado. Ta gama naɗe kayanta ta mayar cikin jaka, hotunan da ta ciro take kallo, wasu da ƙawaye, wasu 'yan uwa, wasu kuma ita da Hamusu. Jin motsin tafiya yasa ta yi saurin turasu ƙasan gadon ta rarumo jakarta tana ƙoƙarin jan zif ɗin ne aka buɗo ƙofar.

Fuskarta ba annuri ta leƙo ta ce,
"Malama ke fa muke jira, kin wani nemi waje kin zauna."
"Ku je, ba zani ba." Ta bata amsa
"Ya fi miki." Ta juya ta fita, ita kuma ta janyo hutunanta ta mayar cikin jaka ta zuge zif ɗin ta ɗauka ta koma ɗakin da tun farko aka yi musu masauƙi ita da Inno.

"Ina Zainab ɗin?" Hajiya ta tambayeta ganin ta shigo tana jan ƙofa zata rufe
Fuskarta a sake ta ce,
"Kanta ke ciwo ashe, na ce ta zo mu tafi, ta ce ba zata iya ba, shine na bata magani ta sha ta kwanta."
"Subhanallah! Ta sha maganin ta kwanta dai ko?"
"Eh!"
"Mu je mu dawo da wuri sai in dubata."
"Gaskiya kam, ta riga ta kwanta kada ki je yanzu ta tashi ciwon kan ya ƙaru."

Hannu ta miƙa daga baya ta zare abin sauraron sautin da Afreen ya toshe kunnuwanshi da shi, ta ce
"Mu je ko?" Ta faɗa tana ɗaga mishi gira
"Ina Zainab ɗin kuma?"
Ya tambaya lokacin da ya juyo.
Harara ta zabga mishi,
"Kanta ke ciwo ta sha magani ta kwanta."
Kai kawai ya gyaɗa, don yasan kwanan zancen, sai dai bai ɗauka yarinyar na da zuciya har haka ba.
Zama ya gyara, sannan ya ja suka tafi.


*Ummyn Yusrah*

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

     _Ummyn Yusrah_

_Matso kusa ku ji! Ko kuna da labarin shahararren kamfanin nan mai suna *RANDAWA MEDIA CONCEPT* kuwa? Kamfani ne ɗaya tamkar da dubu. Aiki cikin aminci, inganci, rangwame da kuma rahusa. Ku dai kawai ku tuntuɓemu ta wannan number domin samin biyan buƙata cikin sauƙi 08062176520. Ga kaɗan daga cikin aiyukanmu_
_1. Waƙar biki, suna, siyasa, ring tone da sunanki/ka, waƙe masoynka/ki, miji ko mata._
_2. Calendar da sticker  biki, suna sauƙar karatu, ko dai na wani abun._
_3. Tallata haja ko wakar ma aikata ko company._ da dai sauransu
_Kai tsaye ku tuntuɓemu ta numbermu dake sama don samun aiki cikin rangwame da rahusa, sai kun zo._

_28_

Ada baya tana son zuwa cikin garin Jinjin, sai dai a yanzu da take cikinsa duk ta ji ya fita mata a rai. Ta tsani garin gaba ɗayanta, ko kaɗan ba zata iya rayuwa cikinta ba. Gara ta koma inda ta fi wayo, gurin da aka san kimarta da darajarta.

Sai daf magriba Hajiya suka dawo. Kai tsaye ɗakin Lubna suka nufa dukansu, bata ciki, har banɗaki tasa Lubna ta duba bata ciki.

"Ina ta shiga to? Kika ce ta kwanta ɗazu, shigowarmu kum bata falo."

Hajiya ta tambayi Lubna da ta yi tsuru-tsuru da ita. Cike da tsoro ta ce,
"A nan fa na barta tana kwance."
Ta faɗa tana nuna gefen gado

"Barin dubata ko tana kicin ne."

Ta fice da sauri ta nufi kicin ɗin, duk tsoronta kada Hajiya ta ji abinda ta yi mata.

Tana fita Hajiya da Afreen suka bi bayanta.

"Ba ta kicin ɗin."
Lubna ta faɗa lokacin da ta sami su Hajiya tsaye a tsakiyar falo.

"Ba ta kicin? To, kodai sake fita ta yi ne irin na ɗazu? Kai Afreen tambayo Ɗayyabu, ke kuma duba ɗakin baƙin can."

Hajiya ta basu umurni

Da sauri dukansu suka fita.

Tana buɗe ƙofar ɗakin kuwa ta ganta kwance,
"Har kin tsoratamu, mun duba ɗaki bakyanan ashe nan kika dawo."

Ba tare da ta ɗago ba, ta ce
"Eh!"

"Ki zo Mommy tana nemanki to."

Bata amsa ba, kuma bata tashi ba.

"Na ce, Mommy tana ƙiranki."

Kaɗa kai ta yi, ganin har yanzu tana kwance yasa ta keɓe baki ta juya zuwa falon.

Zaune ta samesu yanzu a kan kujera, Afreen ya sanar mata saƙon Ɗayyabu cewar Abulle bata fita ba.

"Tana kwance a can, ta ce tana zuwa."

Sai da ta ɗau lokaci kafin ta fito, ta tsugunna can gefe.

"Shigo mana ki zauna, kin koma can gefe kin raɓe kamar wata baƙuwa."

Ƙara matsowa kaɗan ta yi,

"Ke dai akwai baƙunta Zainab! Ace mutum da gidansu ba zai saki jiki ba, sai ki ta ɗari-ɗari. Ko ba ki jin daɗin zama da mu ne?"

Girgizar kai ta yi,

"To mene ne?"

"Ba komai."

Ta faɗa a hankali

"To, ki saki jikinki kin ji?"

"To."

Murmushi ta yi,

"Yaya kan naki? Lubna ta ce kanki na ciwo, ta baki magani. Fatan kin ji sauƙi."

Kai ta ɗaga ta kalli Lubna, a zuciyarta kuwa cewa ta yi, 'Makira.' A fili kuma ta ce "Na ji sauƙi."
"To, Allah ya ƙara sauƙi."
Ƙiran sallar da aka fara ne yasa suka watse.

Ko da aka fito cin abincin dare ma, kaɗan Abulle ta ci, don gaba ɗaya tunaninta da hankalinta ya koma gida. Duk zaman gidan ya isheta.

***
Ba laifi, yau kasuwa ta buɗe ma su Hamusu sosai, har takai ga sun haɗa kuɗin ɗaki, sun kuma biya an basu. Yanzu zasu yi barci cikin salama.

***

Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin a kayi daga waje, daga bisani ya ce,
"In shigo?"
Kanta na kan waya tana kishingiɗe a kan gado ta ce,
"A a, ka yi ta tsayuwa."
Buɗe ƙofar ya yi ya shigo, ya janyo kujerar da ke gaban madubi ya aje kisa da gadon sannan ya ce,
"Ina abokiyar zaman taki?"
Keɓe baki ta yi, ta ce
"Ohho mata ba! Can ɗakin naga ta koma."
Girgiza kai ya yi, kafin ya fara magana.

"Anti Lubna dama magana nake so mu yi."

Sai sannan ta ɗago kai ta kalleshi

"Ina jinka."

"Daddy da Mommy suna son Zainab ta zauna a gidan nan, sai dai kuma abinda kike yi mata naga bata jin daɗinshi. A tunanina zaki jata a jiki ki yi farin ciki da murnar samun 'yar uwa, sai kuma naga akasin hakan. Don Allah Anti Lubna ki sassauta mata ko zata ji daɗin zama da m..."

"Dakata! Mara kunya. Tazarar shekaru nawa ne tsakani na da kai?"

Ta katseshi ba tare da ya kai ga ƙarshen maganarshi ba.

Mamaki ne ya kamashi jin ta ambato shekaru, bai ga zancen da ya yi da har zai kai ga hakan ba.

"Biyar!"
Ya bata amsa
"Ok! Ashe kana sane, kana da shekara ishirin ina da ishirin da biyar. Kenan kaga ba kai zaka gwadamin yadda zan yi rayuwa ta ba, idan ba zaka iya ganina a haka ba ka kau da ido."

Baki kawai ya saki cike da mamaki, daga bisani ya miƙe ya bar mata ɗakin don baida ta cewa.


A yi haƙuri da kura-kuran da ke ciki, ban bibiyaba gaskiya.

*Ummyn Yusrah*

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_29_

Yana fita ta miƙe ta ja tsaki, ta sa ma ƙofar makulli ta rufe.

Dawowa ta yi ta fara rage kayan da ke jikinta don shirin kwanciya. Abun hannunta ne ɗaya ya gangara zuwa ƙasan gado garin cirewa.

Tsaki ta ja, da nuna alamar gajiya sannan ta sunkuya da niyyar cirowa. Ba ta ganshi ba, ya yi nisa, sai wani farin takarda ta ci karo da shi.

Hannu ta miƙa ta ciro.

***
Yana fita kai tsaye ya nufi ɗakin da Abulle take, da sallama ya shiga yana faɗin
"Ba dai har amaryar mai unguwa ta yi barci ba?"

Tashi ta yi daga kwanciyar da ta yi tana faɗin,

"Tuni na kwanta, barci ya ƙi zuwa."

Dariya ya yi
"To, yaya za a yi ya zo, bayan lokacin yinshi bai yi ba."

"Ai so nake in tashi da wuri."
"Ai ko ba ki kwanta da wuri ba, gidan nan ba a makara. Dolen mutum ya tashi ya yi sallar asuba da zarar lokaci ya yi, idan ya idar sai ya koma."

'Ya koma barcin asara ba.'
Ta faɗa a zuciyarta

"Mu je falo akwai film ɗin da za a sa."

Kallonshi ta yi, ta ce

"Fin? Meye kuma wannan?"

Dariya ya yi,
"Ba fa fin na ce ba. Film!"

Dariyar da yake ne ya fara ƙular da ita,
"Uhmmm! Koma dai mene ne, ni barci zan yi, so nake gobe in tashi da wuri in shirya."
Ta jingina da gadon fuskarta na bayyanar da murmushi ta ce,

"Gobe kamar wannan lokacin ina gida."

Kallonta ya yi,
"Nan ma ai gida ne, mu da muke so ki zauna ko 'yar diplomar nan ki yi ki karanto mana engineering."

Zaro ido ta yi,
"In zauna a ina? Yasin a a! Kuma waye shi gudulomar da injimiyarum ɗin?"

Dariya ne ya kamashi har da riƙe ciki

"Ba fa guduloma ba! Diploma na ce da engineering, ina nufin ki zauna ki yi karatu anan har a kai ki jami a."

A tsarace ta ce,
"A ina ɗin? Yasin ba ni zama. Har wani jami a ma zani? Taɓ! Ashema so ake mutanen Mai ludaya su ƙirani da 'yar iska. Hu'umm! Ba da ni ba aradu."

Yau wannan yarinyar zata kasheshi da dariya, da zantukanta masu cike da shirme.

"Yau kam nan kuka tare da hirar ne?"
Hajiya ta katseshi lokacin da ta shigo ɗakin

"Yau mun ba falo hutu Mommy! Hirar nan ɗin ma ya fi na falon daɗi."

Ya ba Hajiya amsa

"Ai kam naga alama! Tun ɗazu nake jiyo dauriyarka. Zainab yaya kayin naki?"

"Na ji sauƙi Memi."

"Ankuma!"
Afreen ya faɗa

"Don Allah Mommy ki ji, Diploma fa na ce mata da engineering, ita kuma wai guduloma da injimiyarum. Ance Mommy ta ce Memi."

Kaɗan ya rage itama ta yi dariya, sai dai ta gimtse.

"To, ai bata iya ba ne. A hankali zata koya."

Har ta juya zata fita sai kuma ta juyo tana tambayar,

"Ina Lubnar kuma?"

Take fuskar Abulle ya canza

"Ta kwanta."

Afreen ya bata amsa lokacin da ya lura da sauyin da ya gani a fuskar Abulle.

Matse baki ta yi, ta juya ta yi gaba. Tasan halin 'yar tata na rashin son hayaniya, hala sun dameta ta korosu nan.

Shi kanshi ya sani mai zama inuwa ɗaya da Lubna sai ya shirya, ko kaɗan bata iya zama da mutane ba.

"Zainab! Nasan bakya jin daɗin zama da Aunty Lubna. Haka halayyata yake, duk mai zama da ita sai ya yi haƙuri..."

"Idan zaman ya zama dole ma mutum ba."

Ta katseshi

"Haka ne kam! Ɗazu nima na shiga mu yi magana kan yanda take yi miki, ko saurarata bata yi ba. Sai ma wani maganar shekaru da ta fara jeromin."

Ya faɗa yana jan ƙaramin tsaki. Da alama maganar ta konashi

"A rayuwa ai ba a duba yawan shekaru, abinda aka aikata a tsahon shekarun ake dubawa."

"Haka ne kam, na yi iya ƙoƙarina don ganin na saitata amma abun ya gagara."

Ya faɗa cikin damuwa

"Abune mawuyaci ka iya canza mutum lokaci ɗaya akan wata ɗabi a tashi."

"Haka ne kam! Na tabbata inda hakan na da tasiri da Aunty Lubna ta daɗe da canzawa. Sai dai hakan ya riga ya zama ɗabi arta. Ki tayata da addu'a sannan ki yi mata uzuri Allah ya bata ikon canzawa."

"Uhmmm! Amin."

***

Saida ta juyo taga hoto ne ashe. Ƙurama hoton idanu ta yi, kabanta na dukan uku-uku ganin kyakkyawan matashin saurayin da ke jikin hoton tare da Abulle.

_Goron Jumma a_

_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

     _Ummyn Yusrah_

_30_

Ga saurayi har saurayi, sai dai da gani ƙauyanci ya gama yi mishi ƙawanya. Da zai samu ya goge, ba ƙaramin nagartaccen namiji za a yi a wajen ba.

Wurgi ta yi da hoton kan durowar da ke gefen gadonta, da niyyar idan gari ya waye zata ba mai shi. Sai dai maimakon ya zauna kan durowar sai ya faɗa bayanshi.

Bata bi ta kanshi ba, gado ta haye ta ja bargo ta rufu. Ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita.

***

Duk wani rarrashi da magiyar da Afreen ya ma Abulle kan ta koma ɗakin Lubna ƙi sauraronshi, sai ma tsalle da ta daka ta ce ita da ɗakin Lubna sai a ƙiyama, ta barmata shi bari na har abada kuwa. Tana iya jure komai amma banda walaƙanci

Ƙarshe dai haƙura ya yi ya barta, nan itama ta bi lafiyar gado cike da ɗokin gobe tana garinsu.

Daren yau ya mata nisa, ta yi barci har ta gaji gari ya ƙi wayewa. Tun tana juyi har dai ta tashi ta zauna.

Agogon bangon da ke manne a jikin bangon ɗakin ta ƙura ma ido, gashi dai sai aiki yake yi, amma ita sam bata fahimtar me yake aikatawar, don ba iyawa ta yi ba.

Ita dai kawai bin ɗan dogon tsinken da ke ta zagaye a ciki take da kallo. Daga bisani ta keɓe baki ta ce,
"Agogo kenan! Sarkin aiki."
Da ta gaji da zaman sai ta sake jawo jakar kayanta ta sake zazzagesu tana kuma yi musu sabon naɗi tare da shiryasu cikin jaka.

Sai da ta gama tas! Ta sake ciro hotunan nan tana sake ƙare musu kallo. Wasu ta yi dariya, wasu kuma haka kawai sai su bata tausayi. Mussaman ma wanda suka yi a wani sallah ita da Inno, Ilu da ƙaninta Muntari. Duk sunci kwalliyar sallah. Ilu da Inno zaune a kan kujera, Abulle da Muntari kuma zaune a ƙasa a gabansu.

Kuka ne ya ƙwace mata wanda bata san dalilin yinshi ba.

Sosai take kewar iyaye 'yan uwa da illahirin mutanen Mai Ludaya. Haka nan kawai take jin wani irin janji a jikinta dama yanayinta. Ita kanta tana mamakin yanda aka yi Lubna ke cin bulus da yawa a kanta.

Duk da kasancewarta mai tsoro, bata lamunci rashin mutunci da raini ba. Da zarar ka ce mata kule zata ce cas!

Share hawayenta ta yi, ta ci gaba da kallon hatunan.

Sosai ta kura ma hoton idanu. Tsaye suke a bakin gona ita da Hamusu, yana sanye da rigarshi 'yar shara mai ruwan bula da na yadi da farin wando, ita kuma tana sanye da atamfarta riga da zani da ɗankwali mai kalar ruwan ƙasa da baƙi yayin da ta tamke kunkuminta da gyalenta.

Dukkanninsu rake suke sha. An ɗauki hoton ne daidai lokacin da suka kai raken bakunansu da niyyar gutsura.

Ta daɗe tana ƙare ma hoton kallo, ƙirjinta na dukan sha uku-uku.

Yau ce rana ta farko da ta fara nadama da da-na-sanin biye ma banzar zuciyarta wajen rabuwa da rabun ranta Hamusu! wanda a baya ko a mafarki basu taɓa tunanin hakan ba.

Yau ce rana ta farko da tayi Allah wadai da ƙin tsayawa ta saurari uzurinshi, sabida baƙin kishi irin nata.

Yau ne kuma ta tuna irin gangancin da ta yi na amincewa da auren Mai Unguwa sabida tsantsar ƙwaɗayi irin nata.

Inama tana da halin hana faruwar auren nan nata da Mai Unguwa? Bakin alƙalami ya riga ya bushe. Ta yi ganganci tun a karon farko, a yanzu bata isa ta je da zance fasuwar auren ba, don tasan hakan babban abun kunya ne, abune kuma da zai iya taɓa kima da darajar gidansu. Abune da zai kafa tarihi tun daga iyaye har jikokin-jikoki a gari. Domin abun kunya ne a saka auren mutum a ce an fasa. Gaba ɗaya gari da maƙota sai zance ya zaga kuma gidan sai ya shiga cikin tarihin garin.

Tunowa ta yi da ranar da zata tafi Mairangwangan ya biyota yana yi mata magiyar ta tsaya ta saurareshi, amma ta ƙi, sai ma maganganu da ta gaggayamishi wacce ya gaza haƙuri shima ya mayar mata. Duk da kasancewarshi mai haƙuri sai da ta kai shi maƙura.

Ta sake ɗauko wani hoto da suka yi a yammacin biyun sallah.

Tarin samari ne da 'yammatan garin, sun taru sun yi layi, mata sun tsaya a ɓangaren gabas, maza kuma yamma, dukkanninsu suna kallon juna.

Tafi aka fara tare da waƙa.

'Yammata a dandali da samari a dandali.

Kowa nata shaggali, yau ranar tamu ce

Abulle zo ki rausaya, Hamusu ne gwaninki ke.

Kowa ya san dashi, kema kin tsayar dashi.

An ɗaukeshi ne daidai lokacin da ta fito tsakiyar fili tana rawa, kai a ƙasa Hamusu ya fito yana tayata takawa.

Kuka ne mai ƙarfi ya ƙwace mata, da sauri ta toshe bakinta da hannayenta duka biyun, ta miƙe samɓal a ƙasa tana kuka mara sauti.


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

  _Ummyn Yusrah_

_To, me ma zance muku ne? Kawai dai na gode. Duk da nasan kalmar godiya ta yi ƙaranci a gareku masoya wannan labari._

_31_

Ƙauyen Mai Ludaya

A wannan daren da Abulle ke kewar mutanen garin Mai Ludaya, a garesu su shaida kawo kayan auren Abulle da Mai Unguwa suka yi.

Yau gidan nasu tun safe ba saka tsinke, hidima kawai ake yi, kai ka ce yau take ranar ɗaurin aure. Da dare bayan sallar isha i ne, jama ar garin mai Ludaya suka shaida kawowar fantimoti mai taya babba guda ɗaya, irin na 'yan burni, na auren Abulle da Mai Unguwa.

Atamfarta guda biyar, shadda ɗaya, mayafai biyu, takalmin ado biyu, silifas ɗin roba ɗaya, sai jakarta guda ɗaya irin ta wanzamai. Sai kayan kwalliya da sauran tarkace.

Duk inda ka gilma ji kake 'Abulle ta yi goshi.' wasu kuma cewa suke, 'Dama ƙaɗayi yasa suka ba  Mai Unguwarta.'  Zantuka dai iri-iri.

****

Rayuwa ta fara canza ma Hamusu. Daga kwana a rumfar shagunan mutane zuwa kwana a ɗakin haya.

Kwance suke a kan tabarmar  Ɗalliti, shikam ya jima da barci, Hamusu ko sai juyi kawai yake yi, tunani fal! Zuciyatasa. Gajiya ya yi da kwanciyar ya miƙe ya nufi ledar kayanshi ya ciro wani riga ya warwareta. Hotunansu ne ya bayyana, ya ɗauka ya shiga kallo da ɗai-ɗai tamkar yau ya fara ganinsu, duk da mafi yawan hotunan shi da Abullenshi ne.

Ji yake kamar ya yi fiffike ya isa garin Mai Ludaya, ya je ya gano Abulle ko zai sami sassaucin ƙuna da raɗaɗin da zuciyarshi ke yi mishi.

****
A hankali sautin kukanta ke fita, zuciyarta ƙuna take, ga kuma shauƙin son Hamusu da ya addabeta a yau. Lallai tayi ganganci da ta biye ma son zuciyarta, akan kwaɗayin Shinkafa ta guje ma masoyinta. Me ya sa tun a lokacin bata gane irin gangancin da tayi ba? Me ya sa bata tsaya sunyi fito-na-fito da Indo ba, ta ƙwace masoyinta.

Sake rushewa da kuka ta yi, a hankali ta fara waƙa,

'Rabuwa da masoyi ba daɗi, wannan cuta ce a zuciya.'

'Zan yi bankwana da kai, ka zamemin rabin jikina.'

'Zuciyata taka ce, kasance mai tallafawa.'

Rayuwata na yi zurfi, kaunarka ce ke sani nishaɗi.'

'Mun yi bankwana da kai, yau gashi raina yana ta ƙuna.'

Ta ƙarashe waƙar tana mai tsananta kukanta, ga zuciyarta da ya yi mata nauyi da zafi.

Inda da yanda zata yi a wannan daren, da ba abinda zai hanata tafiya garinsu ta gano abun ƙaunarta ko zata sami sassauci daga ƙuna da raɗaɗin da take ji.

Ta yi gangancin da batasan hanyar da zata gyarota ba, ba wanda zata iya fuskarshi da zancen canza akalar aurenta daga kan Mai Unguwa zuwa kan Hamusu. Lallai ta makaro, makara mara amfani ma kuwa.

Batasan tsawon lokacin da ta ɗauka a cikin wannan yanayin ba, sai da sanyin asuba ya fara ratsata ne, barci ya yi awon gaba da ita.

A firgice ta tashi, cikin tsoro da fargaba ta shiga ƙare ma ɗakin kallo.

Take mafarkinta ya dawo mata, nan ta shiga tunanin me ke faruwa a gidansu? Me ya sa mutane suka taru da yawa haka? Kodai mutuwa aka yi ne? Da sauri wata zuciyar ta tunatar da ita taron aurenta ake.

Ita har ta manta da wani aure ma. Tunanin Hamusu shi ne a ranta.

Cikin sanyin jiki ta tashi ta nufi banɗaki.

Hasken ranar da ya shigo ta tagar banɗakin ne ya tabbatar mata da rana ta yi batama sani ba, tana ta sheƙa barci.

'Wannan gida ko ina a rufe, ina ma mutum zai gane rana ta yi idan ba fita ya yi ba.'

Alwala ta yi ta fito ta duddungura, tana gamawa ta tattara duk wani shirgi nata a ɗakin ta fito falo.

Tsaki ta ja, haushi duk ya rufeta ganin ba kowa a falon.

Zama ta yi, ta ajiye jakarta a gefe don tasan zaman jira zata sha tunda masu gidan basu tashi a barci ba.

Ita a nata ra ayin ma, zuwa yanzu ta yi nisa a hanya.


_Ku yi haƙuri da wannan_

_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

  _Ummyn Yusrah_

_To, me ma zance muku ne? Kawai dai na gode. Duk da nasan kalmar godiya ta yi ƙaranci a gareku masoya wannan labari._

_31_

Ƙauyen Mai Ludaya

A wannan daren da Abulle ke kewar mutanen garin Mai Ludaya, a garesu su shaida kawo kayan auren Abulle da Mai Unguwa suka yi.

Yau gidan nasu tun safe ba saka tsinke, hidima kawai ake yi, kai ka ce yau take ranar ɗaurin aure. Da dare bayan sallar isha i ne, jama ar garin mai Ludaya suka shaida kawowar fantimoti mai taya babba guda ɗaya, irin na 'yan burni, na auren Abulle da Mai Unguwa.

Atamfarta guda biyar, shadda ɗaya, mayafai biyu, takalmin ado biyu, silifas ɗin roba ɗaya, sai jakarta guda ɗaya irin ta wanzamai. Sai kayan kwalliya da sauran tarkace.

Duk inda ka gilma ji kake 'Abulle ta yi goshi.' wasu kuma cewa suke, 'Dama ƙaɗayi yasa suka ba  Mai Unguwarta.'  Zantuka dai iri-iri.

****

Rayuwa ta fara canza ma Hamusu. Daga kwana a rumfar shagunan mutane zuwa kwana a ɗakin haya.

Kwance suke a kan tabarmar  Ɗalliti, shikam ya jima da barci, Hamusu ko sai juyi kawai yake yi, tunani fal! Zuciyatasa. Gajiya ya yi da kwanciyar ya miƙe ya nufi ledar kayanshi ya ciro wani riga ya warwareta. Hotunansu ne ya bayyana, ya ɗauka ya shiga kallo da ɗai-ɗai tamkar yau ya fara ganinsu, duk da mafi yawan hotunan shi da Abullenshi ne.

Ji yake kamar ya yi fiffike ya isa garin Mai Ludaya, ya je ya gano Abulle ko zai sami sassaucin ƙuna da raɗaɗin da zuciyarshi ke yi mishi.

****
A hankali sautin kukanta ke fita, zuciyarta ƙuna take, ga kuma shauƙin son Hamusu da ya addabeta a yau. Lallai tayi ganganci da ta biye ma son zuciyarta, akan kwaɗayin Shinkafa ta guje ma masoyinta.

Please Login or Register in order to submit comment