Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Me ya sa tun a lokacin bata gane irin gangancin da tayi ba? Me ya sa bata tsaya sunyi fito-na-fito da Indo ba, ta ƙwace masoyinta.

Sake rushewa da kuka ta yi, a hankali ta fara waƙa,

'Rabuwa da masoyi ba daɗi, wannan cuta ce a zuciya.'

'Zan yi bankwana da kai, ka zamemin rabin jikina.'

'Zuciyata taka ce, kasance mai tallafawa.'

Rayuwata na yi zurfi, kaunarka ce ke sani nishaɗi.'

'Mun yi bankwana da kai, yau gashi raina yana ta ƙuna.'

Ta ƙarashe waƙar tana mai tsananta kukanta, ga zuciyarta da ya yi mata nauyi da zafi.

Inda da yanda zata yi a wannan daren, da ba abinda zai hanata tafiya garinsu ta gano abun ƙaunarta ko zata sami sassauci daga ƙuna da raɗaɗin da take ji.

Ta yi gangancin da batasan hanyar da zata gyarota ba, ba wanda zata iya fuskarshi da zancen canza akalar aurenta daga kan Mai Unguwa zuwa kan Hamusu. Lallai ta makaro, makara mara amfani ma kuwa.

Batasan tsawon lokacin da ta ɗauka a cikin wannan yanayin ba, sai da sanyin asuba ya fara ratsata ne, barci ya yi awon gaba da ita.

A firgice ta tashi, cikin tsoro da fargaba ta shiga ƙare ma ɗakin kallo.

Take mafarkinta ya dawo mata, nan ta shiga tunanin me ke faruwa a gidansu? Me ya sa mutane suka taru da yawa haka? Kodai mutuwa aka yi ne? Da sauri wata zuciyar ta tunatar da ita taron aurenta ake.

Ita har ta manta da wani aure ma. Tunanin Hamusu shi ne a ranta.

Cikin sanyin jiki ta tashi ta nufi banɗaki.

Hasken ranar da ya shigo ta tagar banɗakin ne ya tabbatar mata da rana ta yi batama sani ba, tana ta sheƙa barci.

'Wannan gida ko ina a rufe, ina ma mutum zai gane rana ta yi idan ba fita ya yi ba.'

Alwala ta yi ta fito ta duddungura, tana gamawa ta tattara duk wani shirgi nata a ɗakin ta fito falo.

Tsaki ta ja, haushi duk ya rufeta ganin ba kowa a falon.

Zama ta yi, ta ajiye jakarta a gefe don tasan zaman jira zata sha tunda masu gidan basu tashi a barci ba.

Ita a nata ra ayin ma, zuwa yanzu ta yi nisa a hanya.


_Ku yi haƙuri da wannan_

_Ummyn Yusrah_


[11/17, 9:36 AM] Ummyn Yusrah🧚🏼‍♀: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

    _Ummyn Yusrah_

_32_

Gajiya tayi da zaman jira, ga barci da hamma duk sun dameta, dole ta sake komawa ɗakin da ta baro ɗazu don ta ɗan taɓa ko kaɗan ne, tunda daren jiya bata samu ta yi ba. Gashi gani take yau da gayya mutanen gidan suka ƙi tashi da wuri.

Tana kwanciya ba jimawa barcin da ta ci bashinsa ya yi awon gaba da ita.

Sosai take barcinta hankali kwance, tare da daɗaɗan mafarkai.

"Zainab! Zainab!!"

Cikin barci ta ji ana ƙiran sunanta a hankali, tare da bubbuga mata kafa.

Buɗe idanu tayi, Hajiya da ke tsaye, ta ce,
"Wannan barci haka kamar wacce ta kwana bata yi barci ba? Sau biyu Afreen na zuwa dubaki ba ki tashi ba, gashi har an yi sallar azahar baki ko karya ba."

Zaro ido ta yi, tana faɗin,
"An yi sallan Azahar? Na shiga uku! Shi ke nan na rasa moto."

Cikin rashin fahimta Hajiya ta kalleta, tare da tambaya.
"Moton me kika rasa kuma?"

Kuka tasa tana faɗin, "Moton Mai Ludaya!"

'Tirƙashi! Na manta ban sanarmata da zaman ta ya dawo nan ba.'

A fili kuma murshi ta yi, ta ce

"Ai na zo in tasheki ki shirya ganin baki tashi ba yasa na barki."

Kuka itakam take yi, don tasan yanzu ta rasa moto, kwana ya sake kamata.

"Tashi mu je ki wanke baki, ki zo ki ci abinci, zan tura Tukur direba ya je tasha ya duba ko sunanan. Kin ga kafin ya dawo kin shirya ko?" Cikin murna da farin ciki ta miƙe tana faɗin  "To!" Ta nufi banɗaki.

Ficewa daga ɗakin Hajiya ta yi, zuciyarta cike da tunanin yanda zaman nasu da Abulle zai kasance.

Cikin sauri take yin komai, abincin ma kasa shiga ya yi cikinta, haka ta ci kaɗan ta koma falo jiran dawowan Tukur direba.

Har yammaci babu Tukur babu dalilinshi, ga Hajiya ma ta ƙi fitowa daga ɓangaren Alhaji, Afreen da Lubna kuma sun fita tun safe.

Ganin magriba ya gabato yasa ta ja jakar kayanta ta koma ɗaki.

Kwanciya ta yi, sai kuka.

Sai bayan Isha Lubna suka dawo, ɗakinta ta wuce, Afreen kuma ya yi ɗakin Abulle yana ƙwalamata ƙira.

Yana buɗe ƙofar ya hangota zaune a ƙasa ta kifa kanta da jikin gado, sai kuka take yi.

A hankali ya tako har cikin ɗakin, ya zauna a gefen gadon.

"Zainab!"
Ya ƙira sunanta, bata amsa ba kuma bata ɗago ba, domin duk gidan haushinsu take ji. Da gangan suka ƙi tashinta har lokaci ya ƙure.

"Zainab! Me aka yi miki kike kuka?"

Ya tambayeta.

Kai ta girgiza mishi,
"Me ya sa ki kuka to?"
A hankali ta ce
"Ba komai."
"Ban yarda ba. Ki faɗamin kin ji?"

Ɗagowa ta yi, idanunta sun rine sun yi ja ta ce,
"Ni gida zan tafi."
Murmushi ya yi,
"Don za ki tafi gida sai ki zauna ki yi ta kuka?"
"To, ai yau aka ce zan koma."
Dariya magar ya bashi,
"Ai Daddy ya ce anan za ki zauna, ke da garinku sai dai ki kai ziyara ko baki son zam..."

Zaburar da ta yi, ta miƙe ne, ya hanashi ƙarasa maganar.

"Me haka?"
Ya tambayeta tare da miƙewa tsaye.

Kuka tasa,
"Wallahi ni kam gida zan tafi gobe, ko ba asani ba sai na gudu, ba zan zauna ba. Au Inno da Baba cewa suka yi in yi kwana biyu in dawo. Haka kawai a wani ce in zauna! Alƙur an gobe guduwa zan yi."

Ta faɗa tana mai ƙara rushewa da kuka.

Duk rarrashin da yake yi mata, kamar zugata yake yi, ganin ta ƙi ta yi shiru yasa shi fita ya nufi ɓangaren Daddy.

Tare ya samesu, ya sanar da su abinda ke faruwa.

"Je ka ƙiramin ita."
Daddy ya faɗa.

Da sauri ya koma ya ƙirata.
Tare suka taho tana sharar ƙwalla. Suna isowa ta ja burki daga bakin kafet ɗin.

"Zainab!" Daddy ya ƙirata yana kallon fuskarta.

"Me ya sa kike kuka? Ba ki son zama da mu ne?"

Kai ta girgiza,
"To, banason kukan nan, anan za ki ci gaba da zama, zan samo miki makaranta ki fara zuwa."

Hawaye ne ya sake gangaro mata ta goge, cikin rawar murya ta ce,

"Baf... fa! Sau... Ra...kwana biyar a..."

Ta kasa ƙarasawa.

Hajiya ta ce,
"A yi miki aure ko? Zainab ai karantun ya fi, idan kika ƙara girma kinga sai ki yi auren ko"

Bata amsa ba, kanta na kasa, sai Daddy da ya cigaba da cewa,
"Ni na rasa ma rashin hankali irin na Ilu! Ya rasa wa zai ba Mai Unguwa sai wannan 'yar. Wannan da hukumar kare hakkin ɗan Adam zasu ji sai sun kamashi."

"Ni da aki zancen auren na ɗauka ma tsaranta ne."

"Ina fa! Ke Zainab, tashi ki je, Allah ya yi miki albarka kin ji."

A hanzarce ta miƙe ba tare da ta amsa addu ar ba.

Afreen kam murna yake, kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha, ya bi bayanta yana ƙiranta.

Ko kulashi ba ta yi ba, saima shigewa ɗaki ta yi ta rufe da makulli.

Bugu yake a hankali yana faɗin,
"Baby filis ki buɗe za mu yi magana kin ji?"

"Daga ciki ta ce, ka je can ka sami Baby, ni ba yarinaya bace. Kuma tafiya gobe kamar na yi ta ne."

_Ummyn Yusrah_
[11/17, 9:36 AM] Ummyn Yusrah🧚🏼‍♀: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

    _Ummyn Yusrah_

_Jamila K Mashi na gode sosai da cover, ga kyautan shafi gareki in ji Abullen Gayu, Allah ya bar zumunci._

_33_

Ganin taƙi buɗewa ne, ya ce.
"Ki fito to, mu je mu ci abinci."

"Ba zan ci ba."
Ta bashi amsa daga ciki,

Cikin sanyi jiki ya juya, yasan faɗa kawai take yi, ba wani gudun da zata iya tunda ba sanin garin ta yi ba.

"Amma Alhaji ka sanar da shi Ilun kuwa?"

Hajiya ta tambayeshi,

"Idan zan yi iko da abin Ilu sai na nemi izininshi? Da ita da shi duk abun iko na ne don haka ba sai na roƙeshi da ya bar mun ita ba."

"Amma Alha...!"

Ya katseta,

"Amma me? Don Allah ki bar zancen nan, na riga na yanke hukunci."

"Shi ke nan!"

"Tunda gobe Litinin ne, kisa Afreen ya dubo makarantar da za a sata."

"To, Allah ya kai mu."

Tana son magana, sai dai ba hali, tasan halin mijin nata. Abu ƙaɗan ne zai tunzurashi.

***

Inno ce ta fito daga cikin kicin hannunta ɗauke da tire an jere kwanukan abinci a kai, ta ajiye a kan tabarmar da ke shimfiɗe a jefen ɗakin kwanansu.

"Muntari! Zo ka miƙa masu Malam abincin nan a waje."

Muntari da ya yanko lomar tuwo zai kai baki, ya ce

"Allah sarki Inno! Abinci fa nake ci."

"Kaga ɗan nema! Tun ɗazu ka iza ƙwano a gaba sai juya gaya kake cikin miya ka kasa cinyewa, kamar wanda aka aje ma abincin gari guda."

"Inno da zafi ne fa."

"Sai ka ajiye, ka zo ka miƙa musu."

Tasowa ya yi, yana suɗe hannu, yana ƙunƙuni.

Ta ɗaura mishi kenan, su ka ji an bugu ƙofar gidan.

Cikin sauri yake tafiya tamkar mai shirin tashi sama.

"Inno! Abullen ta dawo kuwa?"

Ya tambaya lokacin da ya iso wajen su Innon.

"Shiru dai Malam! Ina tunanin Alhaji ne ya tsaida ita, amma duk rintsi ai gobe nasan zata taho, ko kuma su taho gaba ɗaya goben."

"Allah ya kai mu. Ina salula ta? Ki fitomin da ita, da safe sai in je can bayan gari wajen da ake zamun zaren sadarwa in ƙira Yayan don in tabbatar."

Ta tafi ta ɗauko mishi a cikin fantimoti, ta miƙa mishi ya yi waje.

Muntari kuma ya dawo daga kai musu abinci ya koma kan ƙwaryarsa, ya ɗora daga inda ya tsaya.

***

Duk yanda yaso rabuwa da ita ya kasa, ya yi sintirin zuwa ɗakin nata ya fi a ƙirga ta ƙi ta buɗe.

"Shi ke nan, tunda kin ƙi buɗewa barin je in faɗa ma Daddy kin ce baza ki zauna ba. Kuma cikin dare za ki gudu."

Jin alamar tafiya ya sa ta taso da sauri ta buɗe, ya turo ƙofar yana dariya,
"Matsoraciya kawai."

Tsaki ta ja a hankali ta zabga mai harara.

Tahowa ya yi, yana faɗin,
"Lallai ma yarinyar nan! Ni kike yi ma tsaki da harara? Sai na yanke wannan bakin na kuma soke idanun da allura."

Ganin ya nufota yasa ta fara yi mai magiya,

"Don Allah Yaya ka yi haƙuri, ai dai ka san ba da kai nake yi ba ko?"

Tana maganar tana zaro idanu, tare da karkaɗa hannaye alamar kar ya ƙaraso.

"Idan ba da ni ki ke yi ba da waye? Mu biyu ne ai kawai a ɗakin."

"Nima ban sani ba, kawai dai ji na yi ya fito."

"To, kada ki sake yi min tsaki, ba kyau. Idan kika sake sai na murɗe bakin."

Rufe bakin ta yi,

"Bazan sake ba Allah."

Dariya ya yi, ya tsaya,
"Matsoraciya! Wuce mu je ki ci abinci."

"Ni na ƙoshi."
Ta faɗa tana share idanu.

"Me kika ci?"

"Ba komai."

"To, wuce."

"Allah Yaya na ƙoshi."

"Yau kuma Yaya? Ina Afrij ɗin?"

Ya faɗa yana kallonta, bata amsa shi ba, ya juya alamar tafiya,

"Barin je in ce ma Daddy kin fasa tafiya goben. Dama na riƙe shi ya barki ki tafi, tunda kin ƙi cin abinci shi ke nan."

Da gudu ta biyoshi,
"Don Allah Yaya kada ka faɗa, mu je zanci ka ji."


Kallonta ya yi, tana share idanu fuska sake, kamar ba ita ce mai kuka yanzu ba.

Girgizar kai ya yi, tare da murmushi, ya nuna mata hanyar fita

"Wuce mu je."

Har wajen cin abincin suka isa. Anan suka iske Lubna tana cin abinci.

Kai ta ɗaga kalle su ta matse baki, ta sake mai da kai ƙasa ta ci gaba da cin abincinta ba tare da ta tanka musu ba.


_Ummyn Yusra_

[11/18, 8:29 AM] B²: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_Mmn Nour da Beauty Queen kwament ɗinku na ƙara tunzurani, hanani dakatawa da rubutu yake, ku riƙa yi min sese-sese in samu in ƙarasa. Ina matuƙar godiya, Allah ya bar zumunci._

_34_

Ko kaɗan ba ta jin daɗin hanjin baturen (taliya) da take ci, duk da haɗuwarshi da ɗanɗanonshi, jinshi take yi kamar maɗaci.

Kaɗan ta ci, ta miƙe za ta tafi.

"Ina kuma za ki je?" Afreen ya tambayeta.
"Ni fa na ƙoshi ne."

Kallonta ya yi, "Kin ƙoshi? Tafiyarki ba gobe ba." Ya faɗa yana miƙewa,

Harara Lubna ta bisu da shi, ta ja dogon tsaki.
"Kai meye naka a ciki don ta ƙi ci? Cikin ta ne, idan ta ci ruwanta in ta ƙi ci ruwanta. Yunwa ai ba ƙanwar gyatumar mutum ba ce." Tana gama faɗa ta bar wajen.

Kallo suka bi ta da shi har ta ɓace. Afreen ya ce,
"Shareta dallah! Ki cinye wannan yanzu, barin je in samu Daddy zai ban aike ko za ki rakani?"

"Yaya don Allah to ka roƙarmin shi ka ji?"
"Idan kin ci abinci da yawa ba."


Yana barin wajen itama ta koma ɗaki ta sa makulli, zuciya fal! tunanin hanyar da za ta bi gobe ta gudu gida, don ta ga Afreen tsokanarta kawai yake yi.

Tunda ya je Daddy ya ba shi aika, bai dawo ba sai wajen goma da rabi, har ya nufi ɗakin sai kuma ya juyo don ya san yanzu kam ta yi barci.
Haka nan ya koma ɗakinshi ba don ya so ba, so ya yi su sha hira, ya kuma rarrasheta ta yarda ta zauna.

****
Ƙauyen Kurmawa

"Kun san Allah! Idan har ba ku nemomin Hamusu ba, gobe za ku wayi gari ku rasani." Cewar Inna Talle da ke ƙwance jiki ba baɗi, ƙaninta da matanshi biyu zaune a ɗakin.

"Yaya Talle ki yi haƙuri, gobe Salele zai je can Mai Ludayan ya ji ko shi Hamusun ya dawo, idan kuma bai dawo ba sai ya wuce can Jinjin ɗin."

"Wani Salelen? Ina tunda kuka zo kuka ɓoyeni a wannan ƙungurmin jejin ban sake jin labarin Mai Ludayan ba. Da barina kuka yi a can ni ya fiye min wannan waje da sai a shekara ba a ji me ke faruwa a gari ba."

"Yaya Talle ki yi haƙuri! Kinga ba lafiya ne da ke ba, ki kwantar da hankalinki, Hamusu zai dawo In Allah iyarda."

"Ke Talatu! Wani kwanciyar hankali kuma? Ai idan ba Hamusu na gani ba ba ni da wani kwanciyar hankali."
"Ki kwanta goben in Allah i kai mu za a tafi a nemo shi."
"Kin tabbata dai ko Delu?"
"I, Yaya."
"To, Allah I kai mu. Wannan yarinya ta cuceni, ita tana can da iyayenta hankali kwance, ni nan sun bar ni cikin kogin tunani."
Ta faɗa tana gyara kwanciyarta gami da sharar ƙwalla.

"Ai haƙuri Yaya, za a nemo shi."
"To, Hi ke nan ai, amma sai Allah ya sakamin duk wanda ke da hannu kan ɓacewar ɗan nan."
"Ai Haƙuri dai Yaya! Ai haƙuri."

Shi ne kawai kalmar da suke binta da shi.

***
Duk yadda ya so ya yi barci abun ya gagara, juyi kawai yake yi, ga kuma kewar Ɗanliti da ya tafi yau garinsu, ga kuma kewar sahiba Abulle da Innarshi.

Wunin yau duk bai ji daɗin shi ba, ga kuma daren ma ba daɗi, zai yi ƙoƙari ya tara kuɗin moto ko a ɓoye ya ga Innar shi ya dawo, don ko kaɗan ba ya fatan haɗuwa da wani da zai ba shi labarin auren Abulle. Gudun hakan ya sa ya daina zuwa tashar da zai haɗu da 'yan garinsu.
Amma kuma dole ya je ya ga halin da Inna Talle ke ciki, yana ji a jikinshi tana cikin wani hali. A haka har ɓarawo ya yi awon gaba da shi.

Bai jima da barci ba, ya tashi a firgice sakamakon wani irin mummunan marfarki da ya yi. Mummunan mafarki, kai! Tunda gani ya yi an taru ana ɗaurin auren Abullen shi.

Zama ya yi dirshan, ya cusa kanshi tsakanin cinyoyinshi ya shiga rabzar kuka mara sauti, haɗe da ƙunan zuciya. Duk da bai kasance mawaƙi ba, dalilin soyayyar Abulle ya tsinci kanshi da jero wasu baituka.

Ƙaunata taki ce, ina jiranki masoya.

Duk rintsi duk wuya, ƙaunarmu na nan ba rabewa.

Munyi nisa yau da juna, amma a zuci muna a tare.

Ya sake rushewa da kuka.

***

Yau ma dai haka Abulle ta tashi da shirin tafiya, duk da an sanar da ita ba tafiyar, sai dai tana ji a ranta ba abin da zai hanata tafiya a yau. Kawai zancen su suke yi, ai dai tana da Murtala taƙwas a bakin zaninta kuɗin adawo lafiya da mutane suka ba ta lokacin da za su taho da Inno. Shi za ta yi kuɗin babur daga nan zuwa tasha, idan ta isa ta san masu moton za su ɗauketa, idan ta hau babur daga Tasko ta shiga mai Ludaya za ta karɓi kuɗin su gurin Inno ta kawo musu.

Murmushi ta yi da ta gama wannan tunanin.

'Tashar ina za ki ce a kai ki to?' Zuciyarta ta tambayeta

'Ɗayyabu!' lta ce amsar da ta sake samu, wajenshi kawai za ta iya samun kwatancen tashar da kuma inda za ta sami moto, don ba za ta iya gane hanya ba idan ta fita, ta dai san titi.

Cikin farin ciki ta miƙe ta nufi ƙofar get.

_Ummyn Yusrah_
[11/19, 6:57 PM] Ummyn Yusrah🧚🏼‍♀: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_Wannan shafin gaba ɗaya sadauƙarwa ne gareku 'yan *Hazaƙa writer's association* Allah ya ƙara muƙu hazaƙa, basira, da ɗaukaka mafi daraja. Ina alfahari da ku kamar yadda Abulle ke alfahari da kasancewarta amarya a gidan mai unguwa._


_35_
"Innar Abu!"

Ilu da ya fito cikin shirin fita ya ƙirata.

Da sauri ta fito daga ɗaki, ta ɗan rusuna can gefe.

"Zan wuce, so nake kafin rana ta hudo na dawo, kin san kuma yau litini Yaya zai fita da wuri, gara in sanar mishi ya turota da wuri sabida yanayi na hanya."

"Da wannan kam! Adawo lafiya, idan an samesu a gaishesu."

Ya fice, itama ta koma ɗaki ta cigaba da gyara, don zuwa anjima gidan nasu zai cika, yau za a zo wanke-wanken amarya.

"Malam Ilu! Malam Ilu!!"

Daga can nesa ake ta ƙwalamasa ƙira, tsayawa ya yi, har mai ƙiran nasa ya iso, suka miƙa ma juna hannu alamar gaisuwa.

"Malam Ilu ina zuwa haka, kake ta zuba sauri ka nufi wajen gari?"

"Wallahi so nake in je wajen zaren sadarwan nan in ƙira Yayan Jinjin, kasan yarinyar nan ta je yi musu sallama, jiya muka yi zata dawo, na ji shiru shine zan lalubosu ta salular nan."

"Ayya! Biki ya ammatso. Nima nan itace na je ɗebowa, idan na kai musu zan wuce jana'izar ɗan gidan Ɗan Asabe."

"Ashsha! Rashi aka yi ne a gidan bani da labari?"

Malam Ilu ya tambaya

"I, wallahi. Jiya yaron nan Hudu da abokinshi sun tafi biki can Guwal, suna dawowa cikin talatainin dare suka sami haɗari a daidai tudun mun tsira."

Sallallami ya shiga yi, yana faɗin,
"Wannan waje ba kyau ko kaɗan. Allah ya jiƙansu, ai sai mu je, idan an kai su na dawo in yi ƙiran. Ban ji labarin mutuwar ba, sai yanzu."

Ya faɗa lokacin da suka rankaya cikin gari.

***
Tunda ya dawo daga sallar asuba yake ƙawance, tubka da warwara kawai yake, ga kuma wani irin yanayi da yake ji a jinkisa wanda ya kasa gane na mene ne? ga rana har ta hudo. Haka nan ya miƙe jiki ba ƙwari, ya ɗauraye ƙafafuwansa ya mulkesu da mai ya ɗau tiren gautarsa ya rufo ƙofar ɗakin nasu, ya nufi kasuwa gurin da suke sari. Zuciyarsa cike da tunanin Innarsa ko awani hali take.

***

Cikin wayo da dabara, ta yi ta tambayar Ɗayyabu tashan da ake shiga motar zuwa Mai ludaya, ba tare da ya kawo komai a ransa ba ya sanar da ita, har ma da abubuwan da bata tambayesa ba. Suna zaune Daddy ya zo wuce wajen aiki, Afreen ma ya fita.

Ganin haka yasa ta miƙe ta nufi cikin gidan. Ba kowa a falon, da sauri ta nufi ɗakin da take ta ɗauko jakar kayanta. Tana shirin fita daga ɗakin Lubna ta leƙo.

Kallon sama da ƙasa ta yi mata, a razane ta yar da jakar. (Abinka da mara gaskiya.)

"Ki zo inji Hajiya."
Ta faɗa ta juya

Haushi da baƙin ciki ne ya dirar mata lokaci guda. Naushin jakar tayi da ƙafarta ta yi waje.

****

Ya kai kusan minti ishirin a wajen yana kai komo a wajen, neman zaren da zai sadasa da Baffa, shiru ba labari. Ƙarshe dai sai da ya hau kan bishiya ya ɗaga wayar sama na ɗan lokaci kafin abinda yake nema ya samu. Magana ya shiga yi tamkar wanda ya tara bataliya guda, yake da burin kowa ya ji abinda yake faɗa.

Fuskarsa kawai zaka kalla ka tabbatar da cewar saƙon da yake son isarwa bai sami karɓu ba.

Bai kai ga ƙare maganar ba, daga can aka datse wayar, haka ya sauƙo ya nufi gida jiki ba ƙwari tare da tunanin yanda zai tunƙari Mai Unguwa da zancen da kuma yanda mutanen gari za su tasasu a gaba.

Turus! ya ja ya tsaya lokacin da ya iso ƙofar gida, take fuskarsa ta bayyanar da alamar mamaki.

****
Hajiya dake zaune a falo tana ta rarrashin Abulle da ta cire damuwa ta kuma saki jikinta wayar ta da ke jefenta akan kujera ya fara ruri, dagawa tayi, ganin sunan Alhaji yasa ta yin murmushi, ta latsa koren madanni ta kara a kunnenta.

"To, gani zuwa."

Amsar da ta bayar kenan ta miƙe, tana tunanin me kuma ya dawo da Alhaji gida a wannan lokacin, ƙarfe sha ɗaya na safe.

Miƙewa tayi, tana faɗin,

"Bari je Daddynku ne ya dawo, zan zo yau a bani labarin garin Mai Ludaya da Mai Unguwa."

Tana wucewa Abulle ta bi bayanta da harara, don duk maganar da take yi ba fahimta take ba. Yare ɗaya ne kawai a yanzu zata iya ganewa shi ne 'Shirya ki tafi gida.' ga dukkan alama kuma basu shirya hakan ba.

'Ki gudu kawai ba tare da kin tsaya ɗaukar jaka ba.'

Tana kai nan ta miƙe ta nufi hanyar waje, cikin sa a kuwa taga ba Ɗayyabu mai gadi a wajen.

A wankali ta buɗe ƙaramar ƙofar da ke jikin get ɗin ta fita.

Tana fita kuwa ta sa gudu iya ƙarfinta.

***

A tsaye ta sameshi a falon, rai ɓace.

"Alhaji! Lafiya kuwa?"

Ta tambayesa lokacin da ta ƙarasa shigowa.

Juyowa ya yi ya kalleta.

"Ina yarinyar nan?"

"Wacce? Lubna?"

"Zainab!"

"Au! Yanzu na barota a falo."

"Ta shirya, yanzu Tukur zai zo ya maida ita, ya je shan mai ne."

Ido ta zaro, ta ce

"Lafiya Alhaji?"

"Ke dai ki yi abinda nace kawai."


_Kun makaro, sai dai ku tura jakar kayan abulle._


_Ummyn Yusrah🧚🏼‍♀_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_37_

"Don Allah Alhaji me ke faruwa ne? Ka sanar da ni mana."

Ta faɗa tana kallon fuskarsa,

Zama ya yi, yana girgiza kai cikin takaici, sannan ya zauna.

"Da na ɗauka ina da iko da 'ya'yan Ilu a matsayinsa na ɗan uwana, sai dai yau ya gwadamin akasin hakan."

"Alhaji ban fahimta ba fa! Don Allah ka sanar da ni, me ke faruwa."

"Wai har ni Ilu zai ƙira ya ce in turo yarinyar nan gida?"

Zama ta yi, tare da jan numfashi. A tunaninta ma wani gagarumin al'amari ne, sai dai sanin halin mijin nata na mai da ƙaramin abu ya zama babba ya sa ta ce,

"Alhaji! Wannan ai ba abun tashin hankali da ɓacin rai ba ne, shi ya sa na ce tun farko a sanar da su zaman nata."

Wani irin kallo ya watso mata mai cike da jin haushi,

"Wannan ne ba abin tashin hankali ba? Ina yi mishi bayanin zata zauna a nan ta yi karatu, yana faɗamin an riga an sa mata rana, idan aka fasa hakan zai iya shafar kima da mutunci na gidanmu, sabida rashin wayewa irin na mutanenmu. Ki je ki sallameta, ko ɗaurin auren ma ba zan je ba. 'yarsa ce ya yi duk yadda ya so da ita."

Ido ta zaro,

"A dai yi haƙuri abi komai a hankali. Ya kamata ka karɓi uzurinsa, idan ya so, sai ka je can ɗin ka yi masa bayani yadda zai fahimta, idan ya so, sai a sami shi Mai Unguwar ya janye batun auren, inaga hakan zai fi."

"Ba inda za ni."

Ya faɗa yana ciro waya a aljihu, danne-danne ya yi, kafin ya kara a kunne.

"Kan ina?"
Abinda ya faɗa kenan, ya ɗan tsaya jim! Kafin ya sake magana.

"Ka dawo kawai an fasa zancen karatun, yanzu Tukur zai kai ta gida."
Ya katse wayar, ya sa hannu a aljihu ya ciro kuɗi.

"Ga dubu goma nan ki bata, idan zaku tafi sai in baku kuɗin da za a yi hidima da shi."

"Amma Alhaji sai naga kamar ka yi saurin yanke hukunci, da dai an je can ɗin an yi musu bayani in..."

Dakatar da ita ya yi,
"Bana son wani dogon zance, kema idan kinga ba ki da ra ayin zuwa sai ki zauna."

Miƙewa tayi, ta bar falon gaba ɗaya, don ta san yanzu sai ya dawo kanta.

Sam bata ji daɗin yadda ya yi saurin yanke hukunci ba.

Ɗaki ta nufa, manyan kwalaye ta ciro guda uku, ɗaya setin kula mai huɗu, ɗaya

Please Login or Register in order to submit comment